FETTA CHAPTER 4

FETTA




CHAPTER 4



Kawo Sule ya dinga matsawa Hajiya Tumba da kira kan sadaki, Dan dole ba da son ranta ba, Taba driver ta ya kai, Ya amshe yana washe baki. +

Cikin gida ya samu Yelwa, tana tatar k’ullun kunu, Yace “Ga sadakin yar’ki dubu hamsin”, Sakin matacin tayi, Ta rafsa gud’a ” Ahayye Allah nagode maka, ya’ta tayi goshi, sai a saka rana ba tare da d’aukar lokaci ba”, “Sati biyu nace”, ” Yawwa haka ya dace, dama na dad’e ina mata tariya, kuma a irin dukiya ta Suraj, ai bai ci ace taje da kayan d’akin ba, ko dan zumunci”, “Hakane amma ko yaya ne mu k’ok’arta mu kai ta da wani abun gudun gori”, ” Gaskiya ne, Allah dai ya nuna mana ranar aure”, “Amin”, Ta shiga rawa da juyi.

Kawo Sule da yaje wa sauran yan’uwan sa da batun, Sunyi murna a fili, but da yawa cikin zukatan su tsantsar bak’in ciki da hassada ta mamaye su, Kowa yar’ sa yayi wa kwad’ayin auren Suraj.

Aunty Jummai da labari yazo mata wata ashariya ta danna, Aminiyar ta tace ” Kin tsaya sanya gashi an miki tsakiyar da ba rana”, “Ko yanzu basu ci bulus ba wallahi”, ” Hmm meya rage yau fah saura sati biyu a d’aura aure”, “Ai wallahi ko ranar d’aurin auren ne sai a fasa, rashin cikakkiyar hujja yasa tuni ban sa auren ya lalace ba, amma ina nan ina had’a hujjoji, k’wakk’wara d’aya nake nema”, ” Ki dai tashi tsaye, arzik’i muna kallo ya wuce mu”, “Kwantar da hankalin ki Aminiyata”, ” Idan kinga hankalina ya kwanta, auren nan da Bilkisu akayi”, “Anyi an gama”, ” Toh Allah yasa”, “Amin”

Aunty Jummai nata faman jijjiga kai, tana kad’a k’afa, da cije baki.

Karima ta tattara ta koma gidan su, Mahaifiyar ta ta shiga aikin gyara ta, Duk wani gyara da tasan ana wa ya’ mace idan zata yi aure shi take mata, Kullum sai ta mulke mata jiki da dilka ta hanata fita gaba d’aya, a cewar ta kada tasha rana.

Tafasar ya’yan bagaruwa ta sauke, Ta k’wala kiran Karima, Daga d’aki ta amsa, “Kizo ki d’auki ruwan bagaruwan nan ki zauna a ciki”, Ta amsa da ” Toh”, Tana fitowa,

 Kamar an jefo Aunty Jummai ta fad’o gidan, tana jefan su da matsiyacin kallo, Ta kalli ruwan bagaruwan tace “Duk gyaran da za’a mata, ba za’a tab’o maido da budurci ba dai, an gama kwararu a titi, za’a kai mishi ragowar wani”, A kaf’ule Yelwa tace ” Ke Jummai rashin mutuncin ki ya fara isa ta, dan kin bani shekaru bashi zai sa kizo gidana kina mun yadda kika ga dama ba”, “Ahh lallai Yelwa, wuyan ki ya isa yanka, ni kike fad’awa haka”, ” An gaya miki, tunda ke baki san mutunci ba”, “Zan shayar dake mamaki, daga nan gidan Hajiya Tumba zani, na sanar mata duk irin iskancin da yar’ki ta dad’e tana yi”

   Dariya tayi tace “Wacce hujja gare ki, baki da dai hoton ta da wani, balle ya zama shaida”, Aunty Jummai tasan hakane ko ta fad’awa Hajiya Tumba ba lallai ta yarda ba, tayi kwafa ta fita, a zuciyarta tana tunanin ina zata samu hujja.

    ” Umma nifah ina tsoron taje ta had’a wani k’ullin”, Karima ta fad’a da damuwa d’auke a fuska, “Kwantar da hankalin ki, ba abunda zata yi barazana ce, nima ai a tafin hannu na take”, Natsuwa taji, ta d’auki rubar ruwan bagaruwan tana nufar toilet.

     Suraj kwanan sa uku ya koma Lagos, Baya son ko kad’an ana masa maganar auren Karima, Hajiya Tumba kullum addu’a take idan ba alkhairi bane, Allah yasa ya lalace.

   Burinta Suraj ya auri yarinya mai natsuwa, hankali da tarbiya, mai asali mai kyau wacce zai samu natsuwa daga gare ta.

   Kawo Sule da yan’uwan Yelwa kad’ai ke ta shirin aure, Hajiya Tumba ba wani shiri da take, ko yan uwan ta bata sanarwa da zancen auren ba, Suraj ma bata k’ara tuntub’ar sa da maganar ba, ko tace ya dawo, gashi saura kwana biyar a d’aura aure.

STORY CONTINUES BELOW


     Aliya ta fito tana yafa mayafi, ko ba’a fad’a maka ba, daga shigar da tayi zaka san unguwa zata, ” Fetta yi sauri ki fito, Su Rakiya nacan na jira na”, Da sauri ta fito tana gyara d’aurin ta, “Inyee gaskiya kinyi kyau, nan gaba ba k’aramar budurwa za’a yi ba, motoci sai sun rik’a layi bakin gidan nan”

    Dariya tayi tasa hannu tana rufe fuska, “Sarkin Kunya, mu tafi”, Napep suka tara ya kai su unguwar su Aliya koki, K’anwarta ce ta haihu, haihuwar fari a gidansu ake taron suna, Yan’uwa duk sun had’u, A bakin k’ofa suka had’a da Mu’azzam dan’ mijin yayarta yana cikin mota, ga dukkan alamu kawo su yayi yana jiran su, Fitowa yayi daga motar, ya duk’a ya gaishe da Aliya, Ta amsa tace ” Mu’azzam kana gari?”, “A’ah Aunty jiya na shigo”,

  ” Allah Sarki, Ya karatu?”, “Alhamdulillah, mun kusa gamawa”, ” Toh Allah ya taimaka”, “Amin”, Ya kai duban sa ga Fetta, Yace ” Aunty ina kika samo yarinya mai kyau haka”, “Ya’ta ce”, Yana sosa k’eya yace ” Ina kamo, dafatan za’a bani”, Dariya tayi tace “An baka”, ” Godiya nake, kada a juya mun baya fah”, “Kaga gata ai”,

    Fetta da ta fuskanci zancen su, Kunya ta kamata, ta saka hannu tana rufe fuska, ” Yarinyar mai kunya ce”, Ya fad’a, Aliya tayi dariya tace “Haka take da kunya, bari mu shiga ciki”, Suka shige, Mu’azzam yabi bayan Fetta da kallo, shi har cikin zuciyar sa da gaske yake, Yarinyar ta tafi da imanin sa, Bai tab’a ganin mai kyawun ta ba, Duk da kasancewar ta k’arama tana da hankali, Fatan shi da addu’ar shi ta amince dashi nan gaba.

    A gidan sunan duk wanda yaga Fetta sai ya tanka kyawon ta, da tambayar Aliya wacece, Ganin bakin mutane yayi yawa, Ta kaita k’uryar d’akin Mahaifiyar su tace ta zauna anan.

   Fetta tana mamakin wannan kyau nata da mutane ke fad’i, tasan tana da kyau, amma bata ganin shi kamar yadda mutane ke fad’a.

    Basu bar gidan ba sai ana gab da magrib, A gajiye Aliya ta koma gida, tasha hidima, Fetta bata tare da wata gajiya, tunda wuri d’aya ta zauna.

      Kiran gaggawa da aka ma Suraj ana neman sa Kano, Yasa yaron sa Sabeer, ya mishi booking flight, Ba b’ata lokaci aka samu, Harka ta kud’i, Ya biyo jirgi zuwa Kano, Ko Hajiya Tumba bata san da zuwan sa ba, Sai ganin sa tayi, Tayi murnar ganin sa, Ya zauna suna tattauna abunda ya shafe su da kasuwancin sa.

   Karima kwanakin kullum da zazzab’i take kwana, Da safiya ta waye, ya sauka, Bata sanarwa kowa ba, dan a ganin ta ba wani ciwo ba ne.

    Yau kam har safiya ta waye zazzab’in bai barta ba, Tana kwance amai ya taso mata, Ta fito waje tana shek’awa, A rud’e Yelwa ta fito tana tambayar lafiya, “Zazzab’i ke damuna kwana biyu, sai yau na tashi da amai”, Hannun ta ta kama, ta duba tafin hannun, ta gwale idon ta bud’e tana kallon ciki,

   Sakin ta tayi ta rafsa salati tace ” Ciki! yanzu wani cikin kika kuma yi Karima, ba kince mun kin tuba kin daina ba”, Gabanta yayi mummunan fad’uwa tace “Wallahi na daina Umma, yau wata biyu banyi mu’amala da da’ namiji ba”

    “Na k’arshen da kika yi ciki ya shiga, shin cikin waye ma?”, Tana sharar k’walla tace ” Bashir”, “Tsinanne shege, Allah ya had’a shi da masifa, zama bai ganmu ba, tashi ki d’auko mayafin ki muje a zubar dashi”

    Hijabi dukan su, suka saka, Suka shiga napep zuwa wata k’aramar asibiti, Likita da ta saba musu aiki suka samo,

    “Wai ke karima meyasa bakya jin magana, ba zaki daina neman maza ba, ko yi zaki yi ai sai ki nemi abun kariya daga d’aukar ciki, sau nawa za’a zubar miki da ciki”, ” Kiyi hak’uri Aunty daga wannan ba zan k’ara ba”, “Komai yazo k’arshe, ba za’a iya zubar miki da ciki ba, dan an ta zubar miki, wannan karan zaki iya rasa ranki, ko ki rasa mahaifa, ko ki kamu da cutar yoyon fitsari”

    Karima wani sabon kuka ta fashe dashi, Yelwa salati ta rafsa tana fad’in “Shikenan kin tona mana asiri, kin goga mana tsiya, munga samu mun ga rashi, ai sai ki tashi mu tafi, kayan kunya ne dai zamu sha shi”

     Har suka isa gidan tana zuba mata ruwan masifa, Da Kawo Sule yaji zancen kusan mutuwar tsaye yayi, zagi da duka ba irin wanda bai mata ba, Har kusan tsine mata yayi.

    Bakinta ya suntuma yana jini saboda duka, Yace “Dan’ gidan uban waye ya miki cikin?”, ” Bashir na gidan Alhaji Hamisu”, “Tashi muje, dan uban sa sai ya aure ki”,

   Ya tasa ta gaba, a hanya sai zagin ta yake ” Shegiyar yarinya mai k’ashin tsiya, arzik’i na kiran mu, kin kore shi”, Ya haure ta da k’afa, sai da ta kusa fad’uwa.

    Bashir suka tarar zaune tsakar gidan su, Yana danna waya.

     “Kaine shaid’anin daka mata ciki, to gata na kawo maka ita ka aura”, Mik’ewa yayi yace ” Mallam daga ina?, wacce yar’ taka”, “Kai dan’ duniya Karimar ce baka sani ba” , “Ni gaskiya ban santa ba, kaje can ka nemi wanda yama yar’ ka ciki”
    1

   “Bash nice karima baka sani ba”, ” Ke dalla malama, kika k’ara kiran sunana zan zubar miki da hak’ora”, “Kinga halin samarin zamani ko, ya d’irka miki ciki, ya nuna bai sanki ba”, Ya juya kan Bash ” Kotu zata rabani da kai”, Dariya yayi yace “Ina jiran sammaci, babu uban da ya isa ya sani amsa cikin da ba nawa ba”, ” Haka kace koh, mu zuba ni da kai”, Ya hankad’a ta yace “Wuce mu tafi”Amma Bashir anyi tsinanne, yanzu cewa yayi ba cikin sa ba ne”, Yelwa ta fad’a fuska ba annuri, ” Baki ga rashin mutuncin da ya mana ba, cewa yayi shi bai ma san ta ba”, +

    Ta dungure kan Karima tace “Mai k’aton kai kamar k’odago, Kin ga abunda kika ja mana, ai sai ki zauna ki rainin cikin da babu Uba, ni na cire hannu na a lamarin ki”,

   ” Ni bak’in cikina, ta kore mana arzik’in da muke fatan samu”, “Kasan wani yaron da k’ashin tsiya ake haihuwar sa, toh Karima nada shi”, ” Tabbas na yarda, kin cuce mu Karima”, Yasa k’afa ya haure ta ya wuce cikin d’aki.

    Karima kuka ta fashe dashi, na takaicin irin iyayen da Allah ya bata, su bama cikin da tayi suke ma bak’in ciki ba, Fasa auren ta da Suraj wanda suke tunanin zasu samu wani abu, Haushi da tsanar rayuwar da take ciki taji.

    Labarin yabi mak’wabta Karima tayi ciki, Yaran mak’wabta sun shigo wurin su Binta, suka ji ana rikicin, Suka kwasa suka kaiwa iyayen su.

    Gidan Aunty Jummai da Kawo Sule babu nisa, gida hud’u ya raba su, Aminiyarta ce ta shigo, wacce gidan shine na uku a layin.

    “Albishirin ki Aminiya”, ” Goro fari tass”, “Karima tayi abun da ta saba”, ” Kina nufin ciki?”, Ta fad’a tana zaro ido, “K’warai kuwa, yanzu haka magana tabi unguwa”,

    Mik’ewa tayi, tayi juyi tace ” Kai Allah nagode maka, burina ya cika, ai sai ayi auren mu gani”, “Ai baki ji dad’in da ya sameni ba, da labarin yazo mun”, ” Wallahi labarin nan yafi mun Komai dad’i, ji nake kamar an sani a aljanna”, (Nace hmm daina murna rigar wani ta kama da wuta)

    Gyale da takalmi ta zura, Bata zarce ko’ina ba, Sai gidan Hajiya Tumba.

    Suna zaune falo ita da Suraj, Su Feena na gefe, Suna jefo bakin a hirar tasu.

     Aunty Jummai ta shigo, tana hawaye, Suka shiga gaishe ta babu wanda ta amsa gaisuwar sa, Sai faman jan majina da take,

   “Lafiya dai Jummai”, Cewar Hajiya, ” Ina fah lafiya, Karima ta jawo mana abun kunya da b’ata suna a gari”, “Subhanallah me tayi?”, ” Ciki ta k’unsa”

    Suraj a razane yace “What Ciki! Karima”, Hajiya Tumba kasa cewa komai tayi sai jikinta dake tsuma, ” Wallahi ciki dan’ nan”, Ta fad’a tana k’ara sautin kuka,

    “Chabb Allah ya taimaki Yaya, bai jawowa kansa ba, dama daga ganin idonta sai tayi shaid’anci”, Cewar Su’ad, ” Shine aka so k’ak’aba mishi, Allah ya kubutar dashi”, Feena ta fad’a tana tab’e baki,

     Suraj ya k’ara tsorata da lamarin mata, Kallon salihar mace yake wa Karima, Lallai tsoron Allah a zuciya yake ba fuska ba, Da yawa yan’ matan yanzu sun lalata rayuwar su, Ya tsani zina ya zina mai aikatawa.

     Mik’ewa yayi da shirin barin falon, Kawo Sule da Yelwa suka shigo falo, Kallo d’aya zaka musu kasan hankalin su a tashe yake, Ganin Aunty Jummai hanjin cikin su ya kad’a, Duk saurin da suke kada ta riga su, ta iso, Suna da tabbacin ta kawo labari, daga ganin irin kallon da mutanen gidan ke musu.

    Cikin k’ask’antar da kai yace “Nasan labari ya kawo muku, amma Wallahi fyad’e aka mata, Ku….”, Suraj ne ya katse shi cikin d’aga murya Yace ” Fyad’e ko ba Fyad’e ba, Na fasa auren yar’ ka, ba zan tab’a auren wacce da’ namiji ya santa ba”, Yana fad’ar haka ya fice, Matsayin sa na Yayan mahaifinsa yasa bai keta mishi rigar rashin mutunci ba,

STORY CONTINUES BELOW


    “Hajiya ki saka baki dan Allah”, Yelwa ta fad’a, ” Ba wani abu da zan iya cewa, nayi iya k’ok’ari na wurin ganin an had’a zumuntar nan, tunda abu yazo da haka sai muce Allah ya kyauta”, Ta mik’e tabar falon,

   Aunty Jummai share hawayen munafuncin ta tayi, Tace “Dama k’arshen alewa k’asa, sai a koma ayi rainin ciki, sai munzo cin hanji”, Maganar ta matuk’ar k’una ransu, amma ba yadda zasu yi, Suka tafi jiki a sanyaye rai a jagule.

Aunty Jummai murna fal ranta, tabi bayan su da dariya, har ta hango Bilkisu a matsayin matar Suraj.

    Labarin cikin Karima ya kai sashen masu aiki, kowa yana ta mamaki da al’ajabi.

    Aliya dawowar ta daga gidan aiki, Ta cire hijabi ta sak’ala a igiyar shanya dake tsakar gida, Tace ” Hmm abun mamaki duniya baya k’arewa”, Malam dake kwance gefe yana sauraren radio yace “Meke faruwa?”, ” Wallahi Karima yarinyar dan’uwan marigayi wacce ake shirin had’a auren su da Suraj, tayi cikin shege”, “Subhanallah, yaran yanzu basu da tarbiya”, ” Hmm ba zaka ce zata aika ba, sumi-sumi da ita”, “Allah ya tsare mana zuri’a”, ” Amin Amin, gashi ya fasa auren ta”, “Dama ina zai aure ta, ai duk namijin da yasan kansa ba zai auri wacce ta gama yawon banza ba”, ” Allah ya k’ara killace muna yaran mu”, “Amin”

   Fetta dake wanke-wanke, Tana jin su, A zuciyarta tana mamakin yadda mace zata je tayi ciki babu aure, ita dai ko hannun ta ba zata yarda namiji ya tab’a ba, Dan tun babanta na raye yasha gaya mata, Da namiji ya tab’a mace ciki ake, Shiyasa bata magana da mazan ajin su, ko magana suka mata shiru take, Suna ce mata mai girman kai, ita ba yar’ kowa ba.

    “Dan’ iskan yaron nan kotu zan kai sa”, ” Kotu kuma, kana so duniya ta gama ji kenan, Mahaifin sa zaka samu ka sanar dashi, a rufawa juna asiri ya aure ta”, “Hakane, Anjima zanje na same sa”, ” Yawwa, Karima ta cuce mu”, Kawo Sule jijjiga kai yayi cike da takaici.

    Aunty Jummai ta samu Kawo lamido dama tasu tafi zuwa d’aya, Duka yaran sa maza ne, Tace ya saka baki Suraj ya auri Bilkisu, Yayi na’am da zancen yasan shima zai samu wani abu.

    Hajiya Tumba lamarin bai mata dad’i ba, Taji bak’in cikin Karima tayi ciki, Lallai iyaye na sakaci da tarbiyar yaran su, wani lokaci kuma yaran ke mamayar iyayen su, Allah ya tsare mana zuri’a.

    Kawo lamido yazo wa Hajiya Tumba da zancen, Ya nuna mata bai kamata a bar zumuncin ya tafi haka ba, Ganin Bilkisu ba yar’ sa bace, kuma bai tab’a nuna musu wani hali na kwad’ayi ba, Yasa tayi na’am da zancen sa, Ta yaba da hankalin Bilkisu dan ko a cikin su itace shiru-shiru, Aunty Jummai ce da matsala, kuma mijinta na taka mata burki, ba kamar Kawo Sule da Yelwa ba, da ya zama duk halin su d’aya.

    Tace “Toh Lamido naji zancen ka, kuma na gamsu, ranar da akayi niyyar d’aura auren Suraj da Karima, sai a d’aura da Bilkisu”, ” Wannan abu yayi dai-dai, Allah yasa a k’ulla alkhairi”, Ta amsa da “Amin”, ” Ni zan koma sai na sanar da sauran yan’uwa”, Ya fad’a yana mik’ewa.

     Yana fita Suraj ya shigo, Sun had’u a waje suka gaisa.

   Zama yayi k’asan carpet kamar kullum, “Suraj”, Hajiya ta kira sunan sa, ” Na’am”, Ya amsa yana tattaro hankalin sa gare ta, “Kawon ka Lamido, yayi nazari yaga bai kamata a bar zumuncin ya tafi haka ba, a d’aura auren ka da Bilkisu”, ” Bilkisu kuma, haba Mama, abun Karima kad’ai ya isa ishara, itama bilkisun ai ba’a san halin ta”, “Karima da Bilkisu ba d’aya suke ba, ni ke zaune dasu ina lura da halin kowaccen su, Mahaifin Bilkisu tsayayyen mutum ne ba kamar na Karima ba, Kayi hak’uri ka amince da addu’ar nan, Addu’a ta na tare da kai”

    Shiru yayi, Zuciyar sa na k’una, Sam auren ta bai kwanta mishi a rai ba, kamar shi kad’ai ne namiji a family, Da za’a ce dole sai ya auri wata a cikin su, Rai a jagule ya mik’e ya bar falon.

    Aunty Jummai shiri sosai take ba kama hannun yaro, Sauran yan’uwa na taya ta, Yelwa ko sau d’aya bata taka gidan Jummai ba, Bak’in cikin duniya ya ishe su.

   Suraj yace ba za’a mishi event ko d’aya ba, d’aurin aure kad’ai za’ayi, Su Aunty Jummai ba haka suka so ba, sun so a gwangwaje amma ya suka iya, dole su lallab’a a samu ayi auren.

      
         *Rana bata k’arya*

   Yau asabar bayan sallar azahar aka d’aura auren Suraj da Bilkisu, Kowane ango ranar d’aurin auren sa farin cikin yake, sab’anin Suraj da ya had’e rai, ana gama d’aurin aure, ba tare da sanin kowa ba, Ya sille, Driver sa ya kai shi airport, Ya d’aga zuwa lagos.

   Masu kid’an kwarya nata kid’a, Aunty Jummai na taka rawa ana mata lik’i, Amarya Bilkisu baki yak’i rufowa.

    Gidan Hajiya Tumba ma jama’a sun taro ba laifi, ba wani gayya tayi ba, ita kanta bata san meyasa bata wani d’okin bikin, Ta amince da auren amma hankalin ta ya kasa kwanciya.

    Aliya ana ta shige da fice, Fetta na gefen tana kallon yadda mutane ke ta hidima, Aliya ta sata dole tazo ba dan ranta yaso ba, A ranta tace “Masu kud’i na sha’anin su”, Kaji, drinks da abinci iri-iri haka mutane ke loda, Fetta duk da yunwar da take ji, bata yi yunk’urin tashi ta d’iba ba, Sai da Aliya ta zubo ta kawo mata, Tace ” Ohh Fetta akwai ki da miskilanci, idan kina abu kamar wata yar’ gidan sarauta”, Fetta tana da sanin ciwon kanta, duk abunda zai sa a raina ta bata yin shi, tana ajiye kanta inda Allah ya ajiye ta.

    Bayan sallar isha’i aka kawo Amarya, Har lokacin su Fetta na gidan.

   Tana rakub’e gefe wurin da ba mutane, ashe saitin window d’akin su Feena ne, Ta jiyo su, suna magana,

    “Suna ta wani rawar kai sun kawo Amarya gidan arzik’i”, Cewar Su’ad, ” Yau zata yi kwanan gwauranci, naji suna waya da Mama ya koma Lagos wai ana neman sa”, Su’ad ta tuntsire da dariya tace “Nasan halin Ya suraj, ba neman sa ake ba, amaryar ce baya ra’ayi”, ” Ni tausayi take bani, dan duk macen da ta auri Ya suraj zata gane kuskuren ta, ko jin kansa kad’ai abun takaici ne”, “Chabb ni ba tausayin da take bani, gara ta gasu, ba kwad’ayi ba”, ” Har na hango Ya suraj na cin ubanta”, Suka tuntsire da dariya,

   Idan ta fuskanci zancen su, baya sonta aka had’a su, A ranta tace “Nima ta bani tausayi wannan mugun, ta yarda ta aure shi, ai wallahi ko da kud’i da mota bazan auri mai girman kai ba, balle ma wanda baya sona”,

” Kina nan ina ta neman ki” cewar Aliya , “Hayaniya tayi yawa na dawo nan”, ” Tashi mu tafi gida, rik’e mun ledojin nan”, Ta mik’a mata ledojin dake shak’e da abinci, drinks da snacks, Ta karb’a ba dan ranta yaso ba, sam bata so a ganta da ledojin abinci, a raina ta.

     Yan kai Amarya kowa ya watse, Sai ita da Aminiyar ta Zulaihat a d’aki,

   “Ni dai ki rik’e mun alk’awarin da kika d’auka”, Cewar Zulaihat, ” Baki da damuwa Sweety, na rik’e hannu biyu”, “Har naji natsuwa”, Tayi dariya tace ” Baki da sauk’i”, “Ai da gaskiyata, bari na tafi dare nayi, Sai da safe”,*Bayan wasu shekaru* +

   A cikin shekarun abubuwa da dama sun faru, ciki hadda girman Fetta, Ta zama tsaleliyar budurwa, Kyawun ta ya k’ara fitowa, Ga diri da cikar dukiyar fulani, Da zata samu hutu ba k’aramin kyau fatar ta zata k’ara ba, Shekarar ta 17 tana ajin k’arshe a secondary, Shirin zana Waec suke.

    Mu’azzam tuni ya bayyana soyayyar sa gare ta, Yasha wahala kafin ta amince, Soyayya suke zubawa kamar ba gobe, Duk bayan kwana biyu yake zuwa wurin ta zance, Duka yan gidansu sun san da Fetta, Mahaifiyar sa bata goyon ba, a cewar ta bata da asali, kullum yana k’ok’arin fahimtar da ita da saka mata k’aunar Fetta.

    Suraj tun da aka d’aura auren sa da Bilkisu babu wata alak’a da ta shiga tsakanin su ta aure, Ya rage zuwa Kano sosai, Hajiya Tumba babu yadda bata yi dashi ba, ya rik’a tafiya da Bilkisu, ya kawo mata excuses, Ta kawai k’yale sa ne ba dan ta yarda ba, Bilkisu bata damu ba, arzik’in ta take ci hankalin kwance, babu abunda ta nema ta rasa, Aunty Jummai ma ta shaida yar’ta ta auri Suraj Sa’idu, Taci mai kyau tasha mai kyau.

   Mutane sunyi ta tsegumi Shekara biyar da aure babu haihuwa, Da yawa sun d’auka matsala ta rashin haihuwa, d’ayan su ke d’auke da ita, Wanda sunfi zargin Suraj, a cewar su da Bilkisu ce, da tuni ya k’ara aure.

    Zulaihat kullum tana gidan, watarana ma anan take kwana.

    Mahaifin Bashir bai yarda Dan’ sa yayi ciki ba, Haka Karima tayi ta rainon ciki tana shan kyara da hantara wurin iyayenta, Har Allah ya sawwake ta lafiya, Ta haifi yaronta namiji, Da k’yar Kawo Sule ya siya rago aka yanka aka saka mishi suna Aliyu, Ta cigaba da jego, Yanzu Shekarar sa hud’u, ita ke wahalar yi mishi komai da taimakon Hajiya Tumba.

    Tsaye take bakin madubin dake manne jikin bangon d’akin, Powder ta ta shafa a fuska, sai lipstick, Lips d’inta pink ne sai ka rantse ta saka janbaki, Ta yafa mayafin ta, Tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba.

    Yana zaune a dakalin soron gidan, Sanye yake cikin yadi da ya mishi kyau, Mu’azzam nada kyaun sa daidai gwargwado, shi ba bak’i ba, shi ba fari  ba, Za’a iya kiran sa da chocolate color, Mutum ne shi mai sanyin hali da yawan far’a, Hakan yasa ya k’ara shiga zuciyar Fetta,

   Cikin tafiyar ta mai d’aukar hankali ta shigo da sallama, Fuska d’auke da murmushi ya d’ago ya amsa “Sarauniyar mata barka da zuwa”, Tana dariya mai d’auke da kunya ta zauna tace ” Ina wuni?”, “Lafiya lau mai kyau, kullum k’ara kyau kike, fad’a mun sirrin”, Hannu tasa tana rufe fuska, ” Sarkin Kunya”, Ya fad’a yana jin k’aunarta na sake shigar sa.

   “Bari na kawo maka ruwa”, ” A’ah zauna abin ki, idan ina buk’ata zance ki kawo mun”, Tace “Toh” Tana k’ara gyara zama,

    “Kullum na ganki sai naji na k’osa ayi auren mu”, ” Yar’ k’arama ta dani zanyi aure sai na k’ara girma”, Ta fad’a da shagwab’a, Ba k’aramin burge sa shagwab’ar ke yi ba,

“Wai aiko ba zan yarda ba, latecomer yazo yamun k’wace”, ” Ashe kai ba jarumi bane a fagen soyayya in har kana tunanin wani zai k’wace maka”, “Aikuwa ni sadauki ne idan akan soyayya ne, ba zan yarda wani ya k’wace mun sarauniyar mata ba”, Dariya tayi tace ” Yawwa haka nake son ji”

    Haka suka cigaba da hirar su ta masoya, Da zai wuce ya mik’o mata leda mai d’auke da kwali,

   “K’aramar waya ce na siyan miki, da zamu rik’a waya ko bama tare, zata rage mana kewar juna, akwai sim a ciki”, Ajiye mishi tayi kan cinyar shi tace ” A’ah Ya Mu’azzam, ka barshi, idan kazo ma yi hirar, ko ka rik’a kirana ta wayar Umma”,

STORY CONTINUES BELOW


    Ya b’ata rai, amma k’asan zuciyar sa yaji dad’in yadda tayi kuma ya k’ara yabawa da hankalin ta,

   “Haba Fetta, dan na miki kyauta shine wani abu, ashe baki d’aukeni Yaya kuma masoyi ba”, Ta girgiza kai tace ” Ba haka bane Ya Mu’azzam”, “Toh ki d’auka, bana son jin wata magana”, D’auka tayi, ta shiga yi masa godiya, Ya hanata, A zuciyar sa yana k’ara bata matsayi da addu’ar ta zama mata a gare sa, uwar yayan shi.

    A tsakar gida ta tarar da Aliya, Ta nuna mata, Tace ” Ohh Mu’azzam baya gajiya da hidima, jiya fa ya aiko mun katin d’ari biyar”, “Umma da kin hana shi hidimar nan da yake mun tayi yawa”, ” A’ah, Kyautatawa ce ai, hakan yana nuna ko kunyi aure zai kula da ke”, Ta sunkuyar da kai tana jin kunyar maganar aure, “Allah dai ya sanya albarka, kuma ki kula, kada ki yarda wani namiji ya samu number ki, mazan yanzu yan iska ne, na sanki da kiyayewa, ki k’ara kinji”, Cike da ladabi ta amsa da toh,

   Ta d’auki leda ta shiga d’aki, Bud’e kwalin tayi waya ce Techno k’arama irin wacce ake sawa memory card, Kunnawa tayi, chajin ta full yake, Bata tsaya wani binciken ta ba, Ta ajiye tana shirin bacci.

    Ta kwanta kenan, Wayar ta shiga ringing, ” Future Zawj”, Yayi appearing kan screen d’in, Murmushi tayi sanin Mu’azzam ne, shi yayi saving da haka.

    Ta d’auka da sallama, Ya amsa, Suka shiga hirar soyayya, Har bacci ya d’auke ta, Jin saukar numfashin ta, Tayi bacci, Ya kashe wayar cike da k’aunar ta.

Suraj ya k’ara zama cikakken mutum, Kwarjini da haiba ta k’ara bin jikinsa, Ga wani kyau da fresh da ya k’ara, Hutu da kud’i na aiki a jinin jikin sa, Kullum arzik’in sa k’ara habbak’a yake, Bashi da ra’ayin zama cikakken magidanci wato ya amsa sunan mai aure kuma ya ajiye yara.

    Kewar Mahifiyar sa ta dame sa, Ya yanke shawarar zuwa Kano, A cikin jirgi, Ya jingina kansa a kujera Ya lumshe ido, tuna maganganun da zai riska akan Bilkisu yasa shi jan tsaki, Sam mantawa yake da ita, Ga Mahaifiyar sa da ta taso shi gaba akan  son sanin meye matsayin auren su da Bilkisu, da zata yarda da ya sawwak’e mata, Ya lura ba son shi take ba, bata damu dashi ba, ta dukiyar sa take.

    K’arfe 6:00 na yamma jirginsu yayi landing, Tuni drivers d’in sa na airport suna jiran saukar shi, Ba b’ata lokaci ya shiga mota suka nufi gida.

    Bilkisu bata sanin zuwa da tafiyar sa, Baya sanar da ita, wani lokaci har yazo ya koma bata saka shi a ido ba.

   Yau ma bata san da zuwan sa ba, Birthday party ta had’a a sashen, K’awayen ta sun taro an saka disco ana ta sharholiya.

     Gajiyar da ya kwaso yaji yana buk’atar fara watsa ruwa, kafin yaje wurin mahaifiyar sa.

   Tun daga bakin k’ofa, Yake jiyo sautin disco na tashi, Da mamaki ya tura k’ofar, Yan’ mata ne cike da falon babu mai shigar arzik’i, Wasu ma da bomb shot, Ido duk suka zuba maza, kowacce a ranta tana yaba kyawu da had’uwar sa.

    Ran sa ya kai k’ololuwa wurin b’aci, Socket na speakers d’in ya fisge, Jin kid’a ya d’auke kowa ya maido duban sa gare sa, A tsawace yace “Kowacce Yar iska tayi gidan ubanta, na k’ara ganin k’afar wata a gidan nan, wallahi na lahira sai ya fita jin dad’i”

   Tsawar ba k’aramin gigita su tayi ba, Tuni suka yi k’ofa, ana rige rigen fita, Ya maido duban sa ga Bilkisu da duk a tsorace take,

    “Ke Dan uwarki abunda kike aikatawa kenan idan bana nan, kinfi kowa sanin SURAJ baya d’aukar rashin tarbiya”, Dakewa tayi tace ” Birthday ne fah, sunzo tayani murna, ni ka wulak’anta mun k’aw…..”, Bata k’arasa ba sakamakon saukar marin da taji a fuskarta, Sai da ta kai k’asa, Kafin ta d’ago ya k’ara mata wani.

     “SURAJ baya magana a mayar sa”, Ya wuce ciki ya barta tana kurma ihu, Gyalen ta dake gefe ta yafa, Ta fice zuwa sashen Hajiya Tumba,

    Kuka take hadda birgima, A rud’e Hajiya dasu Feena suka fito.

    ” Lafiya Bilkisu, meya faru?”, “Ya Suraj ne ya kamani yana ta duka”, ” SURAJ d’in, yaushe ya dawo?, me kika masa?”, “Dan nayi birthday da k’awaye na”, ” Tashi daina kuka, barni dashi zai zo ya sameni”,

    Feena da Su’ad sai dariya suke da fad’in Allah ya k’ara, Suka had’a ido da Su’ad, ta mata gwalo tana dariya, Harara ta watsa mata rai a b’ace.

     Wanka yayi, Yayi shirin sa cikin natsuwa, Kaya marasa nauyi ya saka, Ya fesa turaruka, Ya fito yana k’amshi kamar kullum.

    Ya gaishe da Hajiya tak’i amsawa abunda bai tab’a gani ba, “Akan me zaka kama Bilkisu da duka?” Ta fad’a rai b’ace, “Yarinyar bata da tarbiya, bata da mutunci”, ” Ya zama na farko kuma na k’arshe da zaka k’ara d’aga hannun ka a kanta, Mata bata duka ake ladabtar da ita ba, Nasiha ya kamata ka mata, idan bata ji ba fad’a, Duka ba d’abi’ar miji nagari ba ne”

    Had’iye b’acin ran da yaji yana taso masa yayi yace “Toh”, Ya mik’e ya fice.

    Fetta dake bakin k’ofa duk abunda ake tana ji, Aliya ta aiko ta, Tayi saurin lab’ewa bata son had’uwar su, Jin kamar motsi ya shiga waige-waige, Bayan k’ofa ya duba, Tana rakub’e kamar munafuka, Idonsu ya sark’e cikin na juna, Fad’uwar gaba yaji wanda bai tab’a jin irin sa ba, Fetta wani kwarjini ya mata, tayi saurin janye idon ta,

    ” Wacece ke? Kuma me kike anan? “,(Shi sam ma bai gane itace yarinyar da ya mara ba) Ya jefo mata tambayar cikin dakewar murya, ba alamar wasa a tare dashi.

   Wani tsoron sa taji, Murya na rawa tace ” Wurin Hajiya aka aikoni”, “Shine kika lab’e bayan k’ofa kina jin sirrin mutane”, Kanta ta shiga girgizawa, ” Next time da zan kama ki, kina ma mutane lab’e, sai na cire kunnen masu saurare, Fito ki wuce”, Ya fad’a a tsawace, Jiki a sanyaye kamar wacce aka kama tayi sata ta fito, Ya wuce cikin takun sa na k’asaita, Tabi bayan sa da harara tana murgad’a baki tace “Ai sai ka cire kunnen”,

    Ganin ya juyo, ta d’auka yaji, Ta shige ciki a guje, (Matsoraciya😂) Tsaki yayi ya girgiza kai, Ya juya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *