FETTA
CHAPTER 10
Kakarin magana take ta kasa, idonta sun firfito, “Zaki fad’a mun meye tsakanin ku ko sai na aika ki lahira?”, Ya fad’a yana k’ara matse ta, +
Hawaye ya shiga zirya kan kumatun ta, Tana girgiza kai, Ya saketa tayi baya ta bige da bango, Yana huce kamar bajimin zaki.
Ta rik’e mak’oshin ta da take ji tamkar zai cire, Kuka mai cin rai da zuciya ta shiga rairawa, Ba zata tab’a gafartawa masu hannu a k’ulla mata sharrin zina, tana budurwa bata aikata ba sai yanzu da igiyar aure a kanta.
” Da igiyar aurena a kanki ba zan lamunci kici mutuncin shi ba, idan baki san darajar aure ba, nasan darajar aure, Ashe ke jahila ce”, Cikin shesshek’ar kuka tace “Allah shine shaidata”,
” Ba zaki yaudareni da kalaman ki ba, a yau zan koya miki darasi, kafin na kora ki gidanku, ba zan zauna da mazinaciya ba”, Cikin d’acin rai tace “Ka daina jefata da kalmar da ban aikata ba, Allah shine shaidata ban tab’a kusantar zina ba”,
Dariya yayi mai cin rai yace ” Wallahi sai kinsan kinci mutuncin aurena, na biya sadaki, Ni Suraj matar dake amsa sunan MATATA tayi mu’amala da wani k’azami, kud’i, kyau aji bai kama k’afata ba”, Ya fusgar da iska,
Buttons na rigar sa ya shiga b’allewa, yana matso ta, A matuk’ar tsorace ta mik’e tana yin baya, Ya fisgota da k’arfi ya jefa kan gado,
“Kayi hak’uri Dan Allah kar kamun komai”, Hannu yasa ya bige bakin, ” Shut up! kin saba tsoron me zaki ji”, “Wallahi ban tab’a ba, kayi hak’uri”, Ta fad’a tana kuka mai tsuma zuciya,
” Yau zan baki azabar da baza ki k’ara marmarin tarawa da wani da’ namiji, Yau zan more sadaki na”, Ya fad’a yana k’ok’arin cire dogon wando,
Zuciyarta tayi mummunan bugawa, Tashin hankali ya lullub’eta, Tana k’ok’arin mik’ewa, Ya daki kafad’un ta, Ya saukar mata kasala, Ta kasa m’ikewa, Rigar dake jikinta ya yaga da k’arfi, Dukiyar fulaninta dake cikin bra, suka bayyana, tuni ya b’alle hannun bra, Cikin tsananin tashin hankali tasa hannu tana karewa, “Kaji tausayina, Dan girman Allah kada kamun komai, Wallahi ban tab’a ba”
Hannunta ya janye da k’arfi, Ya kai musu chafka cike da mugunta, Ta saki ihun azaba, Yasa hannu ya toshe bakin ta, Ya kai bakin shi saman su, yana sha cike da mugunta, Ya cijeta, Hawayen azaba ya shiga zarya kan kumatun ta,
Komai Suraj ke yi da mugunta yake mata, Maganar Sahabi ke yawo a k’wak’walwarsa, tana k’ara habbak’a haushi da takaici, da son koyawa mata darasi a ransa.
Fetta ba k’aramar wahala tasha wurin sa, babu irin rok’o, yakushi da cizo,da bata masa ba, Bai sauraren ta ba, sai da ya fitar da ita sahun yan mata, Ta shaidata bashi da imani da tausayi, Ta k’ara jin haushi da tsanar sa.
Suraj mamaki, natsuwa, da farin ciki yaji na ratsa shi da ya fuskanci cikakkiyar budurwa ce, Mace ce mai d’auke da tarin ni’ima.
Kallon ta yayi, Fuskarta tayi jajir, Hawaye manne kan kumatun ta, Ga shatin yatsun sa, marin da ya mata data cije shi, Tana baccin wahala, A hankali take saukar da ajiyar zuciya, Kawar da kansa yayi gefe, Ya mik’e ya shiga toilet yayi wanka, Ya d’auro alwala, Ya gabatar da sallar magriba.
Hajiya ta kasa natsuwa, Zuciyarta na k’arya mata Fetta ba zata yi ba tunda har Suraj ya yarda da ita, Yayin da wani b’angare na zuciyarta ke son gaskata mata, Jin su shiru, ta kira wayoyinsa a kashe, Ta aika Su’ad tace mata a rufe, Tayi knocking ba’a bud’e ba, Addu’arta Allah yasa lafiya, Natsuwar da take ji Suraj ya kare Fetta, duk da ta hango tsantsar b’acin rai a k’wayar idon dan’ ta.
STORY CONTINUES BELOW
Aunty Jummai da Bilkisu na cike da zullumi, ganin yadda ya kareta a gaban su, Fatan su Allah yasa Hajiya ta umarce shi ya saketa, Sun k’i tafiya suna jiran yadda zata kaya, Suna da tabbacin Sahabi ba zai karaya ya fad’i gaskiya ba, akan kud’i zai iya komai, Sarar takobin dake jikinshi yafi a k’irga.
Feena da Su’ad sun rasa tunanin me zasu yi, but suna k’ara zuga Hajiya akan ta aikata, Sai da ta kwab’e su tace su bata wuri, Suka tafi suna fad’in dukkan alamu yau bararoji za’a tafi.
Masu aiki da yawa basu yarda ba, wasu kuma na cewa gaskiya ne, Da yawan su Suraj ya burgesu yadda ya kare ta, sun shaida yana sonta.
Yan sanda cell suka jefa Sahabi, Suraj yace kar a masa komai, Sai yazo, Iskancin sa kawai yake, Ya fiddo sigari yana busawa.
Tea mai zafi ya had’a yana sha, Jikinsa is weak, ta mishi birgima, Da k’yar ya samu ya aiwatar, da ya sakar mata k’arfi, Kan kujerar dake d’akin ya zauna, yana jefanta da kallo a kai-kai.
A hankali ta bud’e idonta, Da sauri ta mayar dasu ta rufe, sun mata nauyi da yaji tamkar an zuba mata barkono, Abunda ya faru ya shiga dawo mata kai, Hawaye ya shiga bin gefen kuncin ta, “Allah ya isa”, Ta fad’a tana motsa baki, ” Mijin ki ne yana da hakk’i a kaina”, Zuciyarta ta fad’a mata, “Bata hanyar mugunta da zalunci ba”, Ta fad’a tana jin tamkar ta mik’e ta shak’e shi.
Kofin ya ajiye bayan ya shanye, Toilet ya shiga, Ya fad’a ruwan zafi, Ya dawo saitin ta, ” Tashi kiyi wanka”, Wani haushin sa taji na sake shigarta, “Ki tashi mana”, Ya fad’a a d’an tsawace, Bata tanka sa ba, sai ma kwanciyarta da ta gyara,
D’agota yayi, Ya zaunar da ita, Idonta a rufe, bata son ganin sa, ” Bud’e idon ki”, Ta k’ara damtse su,
Ya duk’a saitin fuskarta, Tana jiyo fitar numfashin sa, Tayi saurin bud’ewa ido cikin nasa, Wani kallo ya rik’a jefar ta dashi, data kasa fassara ma’anar sa, “Tashi”, Ya fad’a cikin sassauta murya, Ta mik’e dan ya barta, azabar da taji yasa tayi saurin zama, tana matsar hawaye,
Rik’ota yayi ta fisge ” Ka k’yaleni mugu”, “Nine mugun”, ” Toh da fah, azzalumi Allah sai ya saka mun”, “Dan na karb’i hakk’ina na zama mugu”,
” Kasan hakk’i ne, zalunci kad’ai Ka sani”, Murmushi yayi duk da kalmar ta masa zafi, Ya fice daga d’akin,
“Wallahi ba zan tab’a yafe maka ba”, Ta shiga rairawa kuka, Kusan minti 15 tana yi, Ta mik’e tana dafa bango, ta shiga toilet, Ruwan da ya tara mata ta zubar, bata son duk wani abu da ya dangance shi, Ta tara wasu, ta zauna ciki tana ihun azaba.
Awa d’aya ta d’auka, ta fito bayan tayi alwala, Doguwar rigar bacci ta saka, ta fesa turare, Ta gabatar da magrib da isha’i, A sallah sai da ta rok’i Allah ya saka mata, A wurin bacci ya d’auke ta.
Suraj sashen Hajiya ya nufa, A falo ya tarar dasu Aunty Jummai, Kallo d’aya ya musu ya wuce ciki, Bilkisu tabi bayansa da kallo tana jin tamkar ta had’iye sa tsabar so.
” Suraj ka fito”, Hajiya ta tambaya, “Eh Mum”, ” Ina Fetta?”, “Tana can”, ” Kana ganin abunda yaron can ya fad’a gaskiya ne”, “Makirci ne Mama, ki bar komai hannu na”, Ta sauke ajiyar zuciya tace ” Allah ya kyauta gaba, but kada a bar sa ya tafi free”, Yayi murmushi “Sai ya gwammace mutuwar sa” Ya fad’a a ransa, “Ki gargad’i ma’aikata kada maganar ta sake ta fita, a tabbatar musu sharti ne”, ” Ina da niyyar hakan, kada a b’atawa marainiyar Allah suna”, Sun tab’a hira, Ya fice.
Jin shiru Aunty Jummai, suka tattara suka tafi, rai a jagule da fatan samun nasara.
*9:15pm*
Suraj ya shigo rik’e da leda, Fetta nata sharar bacci, wanda na wahala ne ba dad’in sa take ji ba.
K’afarta ya bubbuga, Ta mik’e firgigit, “Tashi kici”, Ya fad’a yana tura leda gabanta, ” Na k’oshi”,
Taja hijabi ta gyara kwanciyar ta, Shareta yayi baya jin zai iya bin kowacce mace, ya lura yanayin yarinyar akwai rainin wayo, kamar ba hakk’in sa ya karb’a ba, Kazar ya bud’e ya fara ci hankali kwance.
Duk da yunwar dake damun cikinta, banda kukan yunwa ba abunda yake, Ga k’amshi ya cika mata hanci, ba zata ci ba,
Mik’ewa tayi tana d’angyasa k’afa, Yabi bayanta da kallo, Yaji ta basa tausayi, Kitchen ta nufa ta had’a tea, tasha da bread, Ta hau kujerar falo tayi kwanciyar ta.
Jin ta shiru, Ya lek’o ya ganta kwance, A tunanin sa bacci take, but zubar hawaye take na bak’in cikin ya rabata da budurcin ta, bayan ba sonta yake ba, itama bata son shi, rabuwa zasu yi, Masoyinta na gaske wanda take fatan zama dashi na har abada, take burin ya amshi budurcin ta, but rana d’aya wani ya karb’a cikin mugunta da nuna iko, babu lallashi, balle appreciating na ya sameta cikakkar budurwa, a zamanin nan da dai’dain ku mata ke rik’e nasu.Ya koma d’aki, Ya kwanta, k’wakw’alwarsa cunkushe da tunani kala-kala. +
Fetta a haka bacci ya d’auketa, bata farka ba, sai ana kiran sallar asuba, Da k’yar ta mik’e, jikinta is weak, Ta shiga d’aki,
Ya fito toilet yana sharce ruwan alwala, Ya kalleta ya kawar da kai, Ko kallo bai isheta ba, Ta shiga band’aki, Ruwan zafi ta tara, ta sake gasa jikinta, Tayi wanka, ta d’auro alwala,
Ya tafi masallaci, Taji dad’in shiryawa ba takura, riga da skirt d’inkin lace ta saka, Ta gabatar da sallar asuba, A wurin ta zauna tana karatun Qur’ani.
Tun daga falo yake jiyo k’ira’a mai dad’i na tashi, “Mashaa Allah” Ya furta, Zama yayi yana saurare baya so ya shiga, yayi interrupting d’inta, Karatun sosai yake shigar sa yana tsuma zuciyar sa, Ayar k’arshe ta kai, Yaji tamkar kar ta daina.
Ya mik’e ya shiga d’akin, Tana folding sallaya, “Ina kwana?”, Da matuk’ar mamaki ya bita da kallo, despite abunda ya mata take gaishe sa, Tayi hanyar fita ya amsa ” Lafiya lau”, Ta fice ta nufi kitchen,
Dauriya take, jikinta baya mata dad’i, Breakfast ta fara k’ok’arin had’awa.
Kwanciya yayi ya d’aura kansa kan pillow, yana kallon pop, Tunani da nazarin ta yake, Yaja siririn tsaki ya mik’e, Ba zai samu baccin safe ba, akwai mutanen da zai had’a dasu 7 na safe.
Cikin awa d’aya ta kammala kunun gyad’a da fanke, Ta jera masa kamar kullum, Ta shiga gyaran gidan.
Tana turara turaren wuta, Ya fito sanye cikin shadda coffee colour sabuwa dal, Ko mai hassadar mutum k’aryarsa ya kushe Suraj, yana cikin jerin maza ajin farko, masu ji da tsantsar kyau, gayu, kud’i da k’uruciya.
“Ina ma yadda yake da kyawun halitta haka yake da na hali”, Cewar Fetta, Tana cigaba da zagayawa da turaren wuta, zaka rantse bata lura dashi ba, but tsaf ta kalle sa ba tare sa ya sani ba, Da wutsiyar ido yake kallon ta, Ya zauna dining table, Ya cika cikin sa,
” Zan zo da bak’i anjima, kiyi abinci dasu”, “Allah ya kawo su Lafiya”, ” Amin”, Ya amsa yana gyara zaman hular sa, Hular ta zauna daram a gashin kansa ta k’ara masa kyau, Ya fita ya bar falon da k’amshin turaren sa.
“Ya Allah ka zab’a mun abunda yafi zama alkhairi a rayuwata, Ya Allah ka shige mun gaba akan dukkan al’amurana”, Fetta ta fad’a tana d’aga hannun ta sama, ” Amin”, Taji muryar Aliya ta amsa,
“Umma yaushe kika zo?”, Ta fad’a tana rungume ta, ” Shigowa ta kenan, jiya nayi mafarkin ki, na kira wayarki bata shiga, nace bari nazo na ganki”, “Allah Sarki Ummana, Ina Ali?”, ” Yana koki ya tafi hutu”, “Shine baki kawo mun ba”, ” A’ah kiji da mijinki”, “Uhmm, bari na kawo miki karin kumallo”, ” A k’oshe nake wallahi”, “Kai Umma”, ” Allah kuwa”
Ta nisa tace “Fetta”, ” Na’am”, “Idan har kin d’aukeni mahaifiyar ki, ina so ki fad’a mun wane irin zama kuke da Suraj, mafarkin da nayi jiya yasa na kasa samun natsuwa”, ” Lafiya lau muke Umma”, “Fetta kalleni”, Ta d’ago ta kalleta, ” K’arya kike, k’wayar idonki ta nuna kina cikin damuwa, ki fad’a mun matsalarki ni mai baki shawara ce”, Tabbas tana neman wanda zatayi sharing problems d’inta dashi, tana neman mai bata shawara, but bata so Aliya ta shiga damuwa a dalilin ta.
“Ke nake saurare, nayi alk’awari zan taimaka miki”, Bata b’oye mata komai ba, ta fad’a mata, Cike da tausayinta ta rik’o hannun ta, Tace ” Meyasa baki sanar dani tun farko ba?”, “Bana so ki shiga damuwa”, ” Matsalarki ai tawa ce Fetta, duk abunda ya shafeki ya shafeni”, “Kiyi hak’uri Umma”, ” Ya wuce, hakan da kika yi ya nuna zaki rik’e sirrin mijinki”,
STORY CONTINUES BELOW
Sallamar Yasmeen, duka suka juyo suka kalleta, Tare da amsawa, Ta zauna kusa da Fetta,
“Kuyi hak’uri, ba lab’e na muku ba, na shigo naji Fetta na fad’a miki, ban koma ba, na tsaya na saurara, dan ina so na taimaka mata, wallahi haka nake jin ta tamkar jinina”, Fetta tayi murmushi tace ” Banji haushi ba dan kiji, amma ina rok’on ki kada zancen yaje wani wuri”, “Baki da damuwa Sister”,
Aliya ta nisa tace ” Shawarar da zan baki, ki cigaba da hak’uri da addu’a, Allah yana sane dake, shi zai miki zab’in alkhairi, ki cigaba da kyautata masa, kada ki tab’a masa rashin kunya haka kada ki tab’a bari ya raina ki, ina ji a jikina Suraj zai soki so mai tsanani, Kyawun ki kad’ai ya isa yasa a soki, balle kin had’a da halaye nagari”, “Umma soyayyar sa bata da amfani tunda ni bana son sa”, Ta dafa kafad’arta tace ” Wuyarta ya fara sonki, kema zaki so shi”, Kar taga ta mata musu yasa tayi shiru, but bata jin zata tab’a son shi.
“Ni zan koma, na bar ayyuka gida”, “Toh Umma nagode”, Ta mata rakiya har bakin gate, ta dawo ciki.
Yasmeen tace ” Fetta ina so ki bani aron kunnen ki”, “Ina sauraren ki”, ” Kiyi amfani da hikima da baiwarki ta ya’ mace wurin k’watar ma kanki yan’ci”, “Ban gane ba”, ” Suraj ya karb’i budurcin ki, bata hanyar data dace ba, kuma duk mutumin da ya amshi budurcin ka yasha da kai, ni bana so ku rabu, ina so kuyi rayuwa mai dad’i ta ma’aurata”,
Kallon baki san abunda kike ba ta jefa mata, Yasmeen ta d’aga kanta sama tace “Yes Fetta, mutuwar aure bashi da dad’i, yanzu ke at your young age kike so kiyi zawarci, you are just 17 fah haba sister kiyi tunani, Suraj ya matuk’ar dace dake amma kafin hakan yasan darajar ki”, ” Yasmeen bamu dace dashi ba, bana so mu dace, bana son sa, bana son zama dashi”,
“Fetta ki natsu ki fahimceni, Ke mace ce zaki iya canza Suraj, ko ba komai budurcin ki da ya karb’a ta k’arfi, ya gane kuskuren shi”, ” Taya?”, “Ki kwantar da kai, ki rik’a masa ladabi da biyayya, da kyautatawa, idan ya miki abu ki mayar da komai ba komai ba, ta haka zai shigo hannun ki, ki rama abunda ya miki, ki juya sa tamkar waina a tanda”, Fetta tayi murmushi babban burinta, ta nuna Suraj talaka nada daraja, ba kowane talaka ke da kwad’ayi ba,
Yasmeen ta cigaba da bata shawarwari, Ta tayata da aiki, ta girka abinci, Fried rice da coslow, sai pepper chicken, da fruits juice, Ta fito zata rakata, Suraj ya dawo, A hanya suka ci karo dashi, Yabi Yasmeen da kallo, Ta gaishe sa, bai amsa ba ya wuce ciki,
” Fetta kinga kallon da mijinki yabi ni”, Tayi murmushi tace “Na rainin wayo ba, da ya sabawa mutane”, “Ni sai naga yamun kama da wani”, ” Da kansa ya miki kama, ba kina ganin sa a TV ba”, “Oh hakane fah”, Ta rakata bakin gate, ta koma ciki, 1
Sashen Hajiya ya shiga, ya sanar da ita zuwan abokan sa, Tace ” Allah ya kawo su Lafiya”, “Amin”, ” Ya zancen yaron nan?”, “Ban samu zuwa cell ba, sai anjima”, ” Toh, amma abunda ya bani mamaki jummai da tace ta gansu tare”, “Zan binciketa dan ban yarda da ita ba”
Kafin Hajiya ta bashi amsa wayarsa tayi k’ara, “SS gamu bakin gate”, ” Ku k’araso ciki”, Ya kashe wayar yana fad’in “Sun iso”,
Shi ya musu jagora zuwa ciki, Abokan sa ne su 5 da yayi karatu dasu a UK(a can yayi degree), Sashen Hajiya ya fara kaisu, suka gaishe ta tare da ajiye mata alkhairi mai yawa,
Ya nufi sashen shi dasu, Fetta na jin su ta shige d’aki,
Ahmad yace ” Ina Amaryar ko b’oye mana ita ake?”, Lukman yace “Yama isa, bayan ya gama kalle namu”, Suka kwashe da dariya sab’anin Suraj da yayi murmushi, Yace musu ga abinci, Suka mik’e suka nufi dining, suna fad’in ” Bari muci muji idan Amarya ta iya girki”, Suraj a ransa yace “In dai girki ne ba daga baya ba”,
Kowanensu ya zuba ya fara ci, Lukman yace ” Wai wai wannan delicious haka, abokina kana kwasar dad’i fah”, Yusuf yace “Ai ni na kasa magana”, Nan kowa ya shiga yaba girkin, Suraj yaji kansa yayi k’ato, ta siyan masa girma a wurin a abokai, Ya tuna lokacin da Ahmad yayi aure sukaje gidansa, ba wanda ya iya cin abinci, akayi ta tsegumin sa baiyi dacen mata ba.
Tas suka take kulolin, ” No wonder SS ya fara ajiye tumbi”, Ahmad yace “Zan kawo Asma’u ta koya”, ” Ai nima zan kawo Maryam”, Yusuf ya fad’a, “Ku kaisu catering school, matata ba caterer bace”, Ahmad yace” Bak’in ciki zaka mana, ai wallahi sai na kawo ta”, Suraj yace “Sai a koya mata mu gani”, Lukman yace ” Ni dai a kira mana ita mu gaisa, ko ganin ta ma rowa za’a mana”
Wani littafin tarihi take dubawa, Ya shigo, “Ki fito ku gaisa, ki saka hijab”, A ranta tace ” Ko baka ce ba”
Hijab ta zura, ta biyo bayan sa, Cike da jin kunya ta gaishe su, suka amsa suna zuba mata ido, “Ashe ba girki kad’ai ba, har a fuska wannan kyau haka”, Lukman ya fad’a, ” Gaskiya abokina ka mana wayo, sai ka auro balarabiya”, Tijjani ya fad’a, Haka sukayi ta yaba kyanta, “Ke kuma ciki”, Ta koma ba musu, dama bata jin ta daidai yadda suka tsare ta da ido da surutu.
Yusuf yace ” SS kishi yake, muna yaba matar sa”, Ahmad yace “Da bai aureta ba, da na k’ara ta biyu”, Suraj ya had’e rai, maganganun nasu sam baya masa dad’i.
200k suka ajiye sukace ya bata ladar girki, Kamar yace su d’auke abun su, kar suga rashin mutuncin sa yasa yayi shiru, A tare suka fito, Suka wuce.
Ya shiga mota zuwa police station, Ya umarci a fito da Sahabi, Ya fito yana wani busar iska,
” Waya aiko ka?”, Ya jefo masa tambayar, Dariya yayi ta shaid’anu yace “Na fad’a maka, matarka budurw…”, Ya katse shi ta hanyar daka masa tsawa ” Kada ka k’ara danganta Matata da kanka, ko ka bak’unci lahira”, Duk da ya tsorata ya dake yace “Sai dai kayi hak’uri, amma na rigaka sanin Fetta”,
Kafin ya rufe baki, Suraj ya kai masa naushi, Ya kai k’asa, yana k’ok’arin d’agowa ya k’ara masa wani, ” MATATA TAWA CE NI KAD’AI, duk dan’ iskan da ya danganta kanshi da ita wallahi zai bak’unci lahira”, Yan sandan wurin suka rik’e shi suna bashi hak’uri, Ya fisge ya chafko wuyan Sahabi, ” Ka fad’a mun wanda ya aiko ka?”,
Sahabi tarin azaba ya shiga, Da k’yar suka raba hannun Suraj da wuyan sa, Suka shiga basa hak’uri, Ya fice, idan yana ganin Sahabi zai iya kaisa lahira, A 360 ya fisge motar shi kad’ai yazo ba tare da driver ba.
Cell suka mayar da Sahabi, suka shiga jibgarsa, Ya dad’i gaskiya, Yak’i magana.
Suraj wurin wani shak’atawa ya nufa, Akwai swimming pool, Ya tub’e ya shiga ciki, Swimming na cikin hobby d’in sa, Yana kawar masa da damuwa,
“K’arya kake munafuki, ni kad’ai na Santa a matsayin ya’ mace, wallahi sai ka gwammace mutuwar ka”, Ya danna kansa cikin ruwan, Yana swimming.Ya d’auki lokaci yana swimming, Ya fito ya shiga wani k’aramin d’aki, Ya goge jikinsa ya saka kaya, Ya shiga mota zuwa gida. +
Kud’in da suka bata, a wurin da suka ajiye anan ya tarar dasu,
Zaune take ta tattara dukkan hankalinta wurin kallon kwana casa’in, Kallonta yayi tana sanye cikin doguwar riga ta english wears, ta kamata, dukiyar fulaninta sun d’an fito ta gaba, jelar gashinta da tayi packing, ya fito zuwa tsakiyar gadon bayan ta, Fuskar ta d’auke da murmushi,
Wani abu yaji ya tsigar masa, Yayi saurin kawar da kai, Yana nufar d’aki, Sai a lokacin taji motsin sa, “Sannu da zuwa”, Ya juyo ya sauke idonsa cikin nata, Wani far da ido ta masa, Yayi saurin janye nasa yana jin fad’uwar gaba, ” Yawwa”, Ya amsa a gaggauce ya shiga d’aki,
Ta biyo bayan sa, Direct toilet ta shiga, ta had’a masa ruwan wanka, Duk da yadda k’irjinta ke bugawa ta dake tace “Ga ruwan wanka na had’a maka, kana buk’atar wani abu”, Mamaki ya hana sa ce mata komai, ” Sabon salo”, Ya fad’a a ransa,
Kayansa ya tub’e, ya shiga wanka, Sosai yaji dad’in ruwan, hadda abun k’amshi ta saka masa, Yayi luf ciki yana lumshe ido,
Ta kwashe kayan da ya cire, ta saka a laundry basket, Ta fiddo masa wasu na shan iska, ta feshe su da turare, Ta fice d’akin,
Tab’e baki yayi yace “Kilibibi”, Ya d’auki kayan zai mayar, wata zuciya tace ” Daga taimako, kyautatawa ce”, Ya d’auka ya saka, Ya bud’e drawer ya jawo wasu takardu yana dubawa.
“Su’ad kina ganin Ya Suraj zai soni kuwa”, Tasleem ta fad’a, ” Me zai hana ya soki, ai babu wanda ya dace da shi kamar ke, yarinya yar’ manya, me zai yi da bararojin banza, yar’ masu aiki Mara asali”, Tasleem ta kwashe da dariya tace “Friend baki da sauk’i wallahi”, ” Bana son yarinyar sam bata mun ba, bansan me ya shiga kan Hajiya ta aura masa ita ba”, Feena tace “Wallahi asiri ta mata, Waya kai bararoji sihiri”, Tasleem tace ” Zai karye, zuciyata ta kamu da son Ya Suraj, sai na zama matar sa, ban tab’a neman abu na rasa ba”, “Yawwa Friend, kiyi duk yadda zakiyi Ya Suraj ya aure ki, mu kori matsiyaciya”, ” Baki da damuwa”, Sukayi shewa.
Bilkisu tana zaune tsakar gida tana tsintsar wake, Zulaihat ta shigo, “Ai na d’auka kin daina yayi na”, Bilkisu ta fad’a tana hararar ta, ” Wane ni da tsohuwar Zuma ake magani, na d’aga k’afa ne saboda surutun mutane”, “Wallahi da nayi fushi sosai”, ” Me ya hana ki nemeni”, Bilkisu tace “Hmm Umma bata bari na fita”, ” Ayyah ni kuwa da yake na koma gidan Inna, a can babu ruwan kowa dani, nayi yadda nake so”, “Kinji dad’i abun ki”
Ta jawo kujera ta zauna, tana tayata tsintsar wake, suna hirar yaushe gamo, da tsara wurin da zasu had’u suyi abunda suka saba, ba k’aramin kewar juna suka yi ba.
Aunty Jummai ta fito tana fad’in “Suraj yak’i sako Sahabi daga cell, kuma bai d’auki wani mataki akan Fetta ba”, Ganin Zulaihat tayi turus, Ta duk’a har k’asa ta gaishe ta, Ta amsa babu yabo babu fallasa, ” Na fara tsoro ya tona asiri”, Bilkisu ta fad’a, “Nasan Sahabi yasha yi mana ayyuka bazai tab’a fad’a ba”, Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya cike da gamsuwa tace “Fatan mu ya sako sa”, ” Nasan abun yi”, Cewar Aunty Jummai, Zulaihat da kallo ta bisu, bata gane inda zancen nasu ya dosa ba.
STORY CONTINUES BELOW
Aunty Jummai hijab ta zura ta nufi gidan Hajiya Tumba, Tana falo zaune, Samee na kwance kan cinyarta, tana mata hirar school d’in su, Ta shigo tamkar an jefota, Bayan sun gaisa, Hajiya tace “Dama ina neman ki”, Hanjin cikinta suka murd’a abun ku da mara gaskiya, ” Toh Toh gani Lafiya dai koh?”, “Kince yaron nan tare kika gansu supermarket”, ” Eh kamar shi amma bani da tabbas”, Hajiya tace “Bana tunanin shine, Suraj ya tabbatar sharri ne”, Ta had’iye miyau da k’yar tace ” Allah yasa”, “Yama sa”, Hajiya ta fad’a,
Bata cika minti goma ba, Tace Zata koma zata biya kasuwa, Hajiya ta mata Allah ya tsare tare da bata dubu biyar, Sam bata zargeta ba.
Aunty Jummai wani yaro ta samu ta aika Police Station da aka kai Sahabi, tace yaje matsayin Dan’uwan sa idan ya samu ganin sa, Yace masa yace Yelwa ta saka shi, dan ya lalata auren, Tasan dole za’a bincike shi dan jin wanda ya saka shi, Ba zata so sunanta ya fito ba, kuma dama tana son lalata zumuncin dake tsakaninsu dasu Yelwa.
Fetta na wanka, D’agowar da zatayi, taga k’aton k’adangare saman window, cikin dabbobi tafi tsoron sa zata iya suma, A matuk’ar tsorace tayi ihu, ta fito a guje ko towel bata tsaya d’aurawa ba, jikinta kumfa,
Jikin Suraj ta fad’a ta mak’alk’ale sa, Ihun ta da yaji ya nufa bayin, Kanta ta cusa jikin shi, ” Wayyo gashi nan, wayyo Allah na”,
“Waye?, Me?”, Ya tambayeta a tsawace, Sai a lokacin ta dawo hankalin ta, Ganin ta ba kaya manne jikinsa, Ta buga wani ihu, Ta shiga jan rigarsa tana rufe jikinta, tamkar zata nutse k’asa, ” Wayyo Dan Allah rufe idon ka, kada ka kalleni”,
“Ba zan rufe ba, kina so na kalle ki tunda kika fito haka”, ” Wallahi bana so, tsoro naji na fito ban sani ba”,
K’ok’arin raba jikinta da nashi yake, tana k’are manne masa, kar ya kalleta,
“Kina so na k’ara miki kenan”, ” Me zaka mun?”, “Kinfi ni sani”, Ta gano me yake nufi, Tayi saurin cewa ” A’ah wallahi bana so”,
Ganin ta haka da manne masa da take a jiki, ta jefasa a wani yanayi, Duk yadda yake k’ok’arin hana kansa ya kasa, Hannun sa ya d’aura saman jikinta, Ya shiga shafawa ta tsala ihu, tana turesa, Sake matse yayi jikinsa, Yace “Ke kika kawo kanki, dan haka yimun shiru”,
” Wayyo Allah na, wallahi ban kawo kaina ba”, Bai saurare ta ba, D’aukarta yayi cak, ya kai saman gado, Ya shiga aiwatar da abunda ya girmi tunanin ta, Kuka ta shiga raira masa, bai saurare ta ba, sai da ya tabbatar ya samu natsuwa, Ya mirgina gefe, Fetta toilet ta shiga ta saka key, Tana kuka da birgima Tasha wahala wurin sa but ba kamar ranar farko ba,
“Dan’ iska haka kawai ka dinga taushe ni, kana mun mugunta”, ” Kina jin dad’i kina pretending “, Toshe kunnen ta tayi, Tace ” Bana son ka, wallahi ni ka barni na koma gidan mu”
“Kinyi kad’an yarinya”, Ya fad’a yana murmushi, Shi kad’ai yasan nishad’in da yake ji, Ba k’aramin natsuwa ya samu a tare da ita ba, Rasa kansa yake a duk lokacin da ya tara da ita,
” Kiyi sauri ki fito”, “Bazan fito ba”, ” Idan na bud’e wallahi sai na k’ara wani round”, Jin haka tayi saurin mik’ewa tayi wanka, Ta fito tana had’e rai, Dariya ta basa yadda ta had’e girar sama da k’asa, Ya shige toilet ba tare da ya tanka ta ba,
A gaggauce ta shirya ta fice daga d’akin, Kanta ke masifar sara mata, Ta kwanta kujerar falo cikin mintuna kad’an bacci ya d’auketa,
Ya fito cikin shirin sa, Ya kalleta tana sharar bacci “Bacci baya mata wuya” Ya furta,
Zama yayi kan kujera, Ya kamu tashar NTA yana kallon news,
Bata d’auki lokaci tana bacci ba, Ta farka da addu’ar tashi a baki,
STORY CONTINUES BELOW
Ta kalle sa, ta galla masa harara, “Wallahi ba zan k’ara yarda yayi ba, kamar wata sex machine”, Charaf a kunnen sa,
” Sadaki na nake fanshewa”, Yayi maganar hankali kwance yana kallon TV, Baki ta murgud’a a ranta tace “Mu zuba mu gani, ai jikina ne ba na kowa ba”,
Mukullin mota ya d’auka ya fita, Tabi bayan sa da harara, ” A banza ka dinga haye ni, kayi na k’arshe”, Ta mik’e ta canza channel zuwa arewa24.
Driver ya taso zai bud’e masa k’ofa, Ya dakatar dashi “Am going alone”, Ya koma ya zauna, Sauran drivers d’in suma suka zauna,
*Police Station*
Ya buk’aci ganin Sahabi, aka fito dashi, Fuskar sa ta canza kamanni saboda duka,
” Zaka fad’a mun wanda ya saka, ko sai na zubar maka da hak’ora”, Sahabi yace “Zan fad’a”, Da hannu ya masa alamar ina ji, ” Wata mata mai suna Yelwa tace nayi haka dan na lalata mata aure”, “Sunnar Manzo SAW kake son lalatawa”, Suraj ya fad’a yana cije lips na k’asa, ” Na tuba ranka ya dad’e sharrin zuciya da shaid’an ne”
Murmushin gefe baki yayi Ya umarci yan sanda su hora shi na kwana d’aya su sake shi,
“Yelwa wannan karon bazan k’yale ki ba, Meye had’in ki da rayuwar aure na, wallahi ba zan duba matsayinki na matar Yayan Mahaifina ba, zan miki hukunci daidai da laifin ki”, Ya fusgar da iska cike da takaici.
Wayarsa ya jawo, Yayi dialing number wani yaron sa yace ya kawo masa Yelwa gidan gonar sa(Yana da gidan gona da yake kiwon kajin turawa, da shanu ana sarrafa masa madara da yoghurt, SS milk and Yoghurt), Suraj mai sana’a goma, komai da ruwan ka.
Yelwa ta fito gidan mak’wabciyar ta, Zata shiga gida, Rabi’u yasha gabanta ya shak’a mata abu, ta sulale wurin, Ya jefata mota.
Ta farfad’o tana sallalami, Suraj ta gani a gabanta yana zaune kan kujera yayi crossing legs, Fuskar sa d’aure kamar bai tab’a dariya ba,
” Suraj Kaine, me nayi ka kawoni nan?”, Jikinta na tsuma, “Ki d’auka ba Suraj da kika sani bane a gabanki, kamar yadda ba Yelwa da na sani bace”,
” Kayi hak’uri ka maida ni, bansan me nayi ba”, “Meye dalilin ki na shiga rayuwar aure na?”,
A daburce tace ” Wallahi ban shiga ba, Ni wani abu aka ce maka”, Da hannu yama Rabi’u alamar ya kora mata bayani, Rabi’u yayi gyaran murya ya fad’a mata yadda aka yi da Sahabi, Ta fashe da kuka tace “Na rantse da Allah sharri ake mun, bansan komai ba”
Suraj yayi murmushin gefen baki yace “Ba kare kanki nace kiyi ba, dalilin ki nake son ji”, ” Ban aikata ba, wallahi ban aikata ba”, “Rabi’u”, ” Na’am Ranka ya dad’e”, “Ayi mata hukunci yadda gobe ba zata k’ara ba”,
Kafin tayi magana, wasu k’attin mata sun fito, Suka rufe mata baki da salatif, Suka d’agata sama zuwa wani d’aki, Suka kwantar da ita flat, Wani gabjejen k’ato, Ya shiga zuba mata bulala, kuka take ba damar ihu baki a rufe , “Hukuncin Sharrin zina kenan” K’aton ya fad’a, Bulala ashirin ya mata masu masifar zafi, hadda fitsari ta saki a wando, Suka d’auketa suka jefa mota,
Hanyar gidansu suka yadda ita, Da k’yar ta mik’e, Fatar bayanta kamar zata b’are tsabar azaba, Fuska jajir ta shigo gida, Karima tayi kanta tana tambayar lafiya, ” Allah ya isa, Allah ya tsine musu”, Shine abunda take fad’i, Band’aki ta shiga, Ta tsaftace jikinta, Da d’aurin gaba ta zauna tsakar gida, Kawo Sule baya nan.
“Mama meya sameki haka?”, Tana sharar k’walla ta zayyane mata, Karima tace ” Wallahi sharrin su Aunty Jummai ne, tabbas jiya naje gidan Kawo lamid’o naji suna hira da Matar sa”, Wata ashariya ta danna tace “Shine ta k’ulla mun dan ta wanke kanta, Wallahi billahil lazi sai na k’ulla mata sharrin da sai ta tsani kanta da duniyar gaba d’aya, zata san ba’a tab’a Yelwa yar gidan Tabawa a kwana lafiya”, Ta buga k’irji.
Suraj gida ya koma, bai sanarwa Hajiya Yelwa ce da hukuncin da ya mata ba, Fetta na sashen Hajiya suna hira, Ya duba bai ganta ba, Yasan bara ta wuce can d’in ba, Drawer da kud’in suke ya bud’e zai d’auki abu, Yadda ya ajiye su haka ya gansu,
” Bata buk’ata kamar yadda ta fad’a”, Zuciyar sa ta fad’a mishi, Ya kwashe ya saka a majiyar kud’in sa, wanda Fetta bata san dashi ba.
Sallamar ta ya jiyo a falo, Ya amsa daga d’aki, Zamanta tayi falo tana game a wayarta,
Tsayuwar sa taji a kanta, bata d’ago kai ba, dan bata so su had’a ido, K’amshin turaren ta na dukar mishi hanci, “Akwai son turare”, Ya fad’a, (Nave kamar kai ba)
Kud’in dasu Yusuf suka bata, Ya mik’a mata yace ” Ladar girki inji su Lukman”, Kallon kud’in tayi tace “Nagode banyi dan a biyani ba”, ” Bani na baki ba, balle kiyi pretending bakya so”, “Kowa ya bani bana buk’ata, ban saba rik’e mak’udan kud’i ba, kuma me zanyi dasu, ina ci ina sha ina da sutura, Alhamdulillah hakan ya wadatar”, Da kallo yabi ta, Karon farkon da kalaman ta suka burge shi,
” Good”, Ya fad’a yana barin falon, Ta k’ara gyara zama.
Sahabi yaci ubansa, Gaba d’aya an canza masa kamanni, Fuskar sa ta kumbura tayi jajir, Yana d’ingishi ya fito police station, Direct gidan Aunty Jummai ya nufa, Yaro ya aika yace a kira ta, Tana jin Sahabi ne, Ta zura hijab tayo waje, Zaure ta shigo dashi,
“Ki bani kud’in asibiti”, “Cinikin da mukayi da kai babu kud’in asibiti”, ” Waya ja mun toh?”, “Kai kayi sakacin da aka kama ka”, ” Haka kika ce Wallahi zan tona asirin ki”, “A’ah ba za’a yi haka”, Ta kwance zani ta zaro dubu uku ” Ga wannan kayi manaji”, Ya fisge ya wuce abun sa, “Tsinanne kud’in cefanen yau ya karb’e”, Ta koma cikin gida tana mita.