GAMAYYAH
CHAPTER 11
Kallon adama dake qoqarin saukowa gado yayi yaga yanda jikinta ke rawa saidai Sam bata tata yakeyiba mafarkinsa ya girgiza tunaninsa da zuciyarsa matuqa sbd su mutane ne dasuka yarda da mafarki,
Basason ‘yaya mata sbd muguwar aqidar dasuke ciki ta wani irin mulki da ake gudanarwa na tsantsar iko kowa yasan mulkin mace a mineelik masifa ce dabaza’aso maimaitawaba sbd jinin matansu bazai iya controlling na abinda yake tareda throne dinba kamar namiji shiyasa mulkinsu yake zama tamkar masifa ko annoba sbd mulkine na tsantsar zubarda jini Wanda babu yaro ba babba bare mata bare maza,ba tsoho ba tsohuwa. +
Alqawarine yadauka bazai taba bari mace ta mulki mineelik ba koda zai rasa ransane sbd yasan duk macen dazata hau zaiyi wuya basuyi ajalin junaba dayaga haka ya roqi Allah yayi gaggawar daukar ransa.
Cikeda rudu adama takallesa tana goge fuskarta dahar lokacin take gumi tace,
Sultan nayi mugun mafarkinda gwara nayi mutuwar qasqanci a hannun 6arayi dana fuskanci irin abinda Nagani a mafarkin.
Bai kalletaba bare yatsaya sauraran abinda take fada sbd tunanin daya cika zuciyarsa akaro na farko arayuwarsa dayaji mulki yafara fita ransa sbd duba da irin mutuwar da sarakunan mineelik keyi yayi tunanin zai iya tsallakewa ya sauka mulkin salin alin batareda fuskantar irin qarshen sauran sarakunan ba shiyasa ya tattara duk dagewarsa akan ganin maheer ya karbi mulkin amma yaqi gashi matarsama ta haifi namiji arabasa da wannan masifar abu yaqi yiyuwa ta wani 6angare ga daular shiefffs na jiran rashin magajinsu su zamo bayi a qarqashinsu Wanda yafison ya sare kansa daga gangar jikinsa dayaga wannan baqar ranar yanzu kuma ga wata masifar nason 6ullowa sbd baisan me mafarkinsa na assultana yake nufi ba.
Hannunsa ya daga ahankali ya shafo fuskarsa cikin mamaki saiyaga zufa ne ke tsatsafo masa,
Rabon da yayi zufa a rayuwarsa harya manta.
Irin tarbarda akayiwa isowarsu ta qara sanyaya jikin rumanah sbd tafara fargabar itama me zata Haifa sbd ganin irin dubban jama’ar dasuka dogara da abinda zata haifa.
Lokacinda mamani tayi ido biyu da rumanah da cikin dake jikinta wani mugun jiri mai qarfi ya ‘dibeta nuratu tayi saurin tareta tana kallon idanuwanta dake cikowa da qwallar baqin ciki tace
Mamani lafiya?
Kasa riqe hawayenta tayi sbd baqin cikin daya rufe zuciyarta tace,
Har abada bazanyi lafiyar zuciya ba sbd bulama da asma’u har bayan barinsu duniya basu bar kurwata ta zauna lafiya ba bayan duk balain dasuka sako rayuwata aciki dan haka wlh bazan zauna nashaqi numfashi mai dadiba sai ranar dana gama lalata dukkanin zuriar da suka bari aduniya….
Sakinta nuratu tayi cikeda mamaki da baqin cikin halin mahaifiyar tata muryarta na rawa tace,
Mamani dazaki cire abinda yake ranki gameda rumanah dakin cire sbd zai kaikine matakin halaka sbd yanxu tariga ta taka wani matsayinda duk Wanda yayi mata wani ganganci zai iya rasa rayuwarsa sbd dukkanin burin daular nan da zagayenta akanta da cikinta yake dan haka ki nesanta kanki da ita sbd gujewa rasa rayuwarki..ke mahaifiyatace ina sonki fiyeda komai amma bazan iya kallo ki cuci rumanah ba dan haka karkiyi abinda zai barni da rashin zabi face na fadi gaskiyar dazaki rasa rayuwarki.
Tana gama fadar haka tabar gurin cikeda damuwa
Duk murnarta da farin cikin ganin rumanah din ya 6aci sbd mamani
Kukan 6aqin ciki mamani tasake tana tsinewa bulama da asma’u ta juya ta nufi gurin adama da sai alokacin zata fito tarbon.
Kallo daya tayiwa cikin rumanah taji tari mai qarfi ya sarqeta kamar ranta zai fita
take ta gigice da gudu akaje aka kawo mata ruwa ta karba tasha idanuwanta dasuka firfito sukai jajir sbd tari numfashinta na fita da sauri ta juya tabar gurin nanma idonta ya sauka kan na suhailat dake tsaye gefen Maheer ai take taji qaramar hauka na neman kama zuciyarta tana isa palonta na farko dukkanin bayi da kuyangin part din suka fice sbd gudun laifi lurada halinda take ciki.
Mamani data sake biyota da ruwa ta miqa mata har lokacin itama jitake kamar ta cinnawa mineelik wuta kowa ya babbake ya ya mutu ko zataji abinda ya tsaya mata a maqoshi ya fada. +
Karbar ruwan tayi tasake sha tana cewa,
Burina dana gina tun ina budurwa bazai taba rushewaba kan baiwa ‘yar bayi,
Babu Wanda bazan iya raba gangar jikinsa da kansaba kan burina sbd burina shine burin karagar mineelik..
Cikin tsananin damuwa da baqin cikin mamani daya kasa dannuwa aranta tace,
Duk inda bulama da asma’u suka sauka saisun bar masifar data addabi kowa awajen
Shiyasa bazan numfasaba saina tabbarda na tarwatsa rayuwar rumanah da abinda ke cikinta.
Kallonta adama tayi da jajayen idanuwanta baqin cikinta na ninkuwa tace,
Ko bulama ne aduniya bai isa ya shiga tsakanina da hawa throne din mineelik ba bare ‘yarsa dan haka ni adama ayau ina sake daukarwa kaina alqawarin kawarda ko wanene ya shiga hanyata ta cimma burina
Idan nace ko wanene ina nufin ko wanene ciki bancire kowaba
Cikin takaici mamani tace,
Allah yasa gurin haihuwa ta mutu daga ita har abinda zata haifa kowama ya huta.
Kobata mutu gurin haihuwa ba ta haifi namiji saiya mutu kozan rasa rayuwatane”””adama ta fada tana miqewa tsaye.
Tsayawa tayi tareda juyowa takalli mamani itama mamani ita takalla sai alokacin kowannensu yadawo nutsuwarsa jiki na rawa mamani ta zube tana sunkuyar dakai
Adama fuskewa tayi sbd duk duniya daga ita sai bokanta ne suka San da sirrinta sai yanzu da 6acin rai yasata fadar abinda ke ranta saidai kuma ga alama tasamu wadda zata riqa amfani da ita Dan cimma burinta musamman da kusancinsu da rumanar zasuyi amfani tunda tana yiwa mamani kallon uwa.
Wani irin babban sabon sashe da aka zubawa tsaro na musamman aka kaita Wanda yake gefen part din yarima maheer duk wani abin jin dadi da hutawa anxuba mata shi ga kuyangi na musamman da aka kawo mata.
Bayan duk wata aladar tarbonsu anyi angama da daddare bayan tayi wanka ta saka kayan bacci ta kwanta bakin gado tareda lumshe idanuwanta ta bude ahankali tareda kiran sunansa cikin zuciyarta.
Suhailat kuwa sbd yanayin jikinta da gajiya yasa tana kwantawa bacci ya dauketa cikin tsananin gajiya.
Abincin da aka aikawa kowaccensu daga part din sultana zaarah babu wadda tasamu damar ci har gwara suhailat tasha madara mai zafi sbd sanyi datakeji kamar zai kamata.
Rumanah kuwa kwance take tayi lamo cikin zurfi a tunani da tsananin son ganinsa sbd har lokacin takasa daina tuno yanayin dasuka rabu ‘dazun hakan na raunana zuciyarta da kuzarinta ahaka bacci yadan ‘dauketa tanayi tana farkowa hardai akai asuba tayi sallah takoma ta kwanta nanne tasamu baccin yadauketa sosai.
Qarfe goma ta fito palonta anan ta tararda dining shaqe da kalolin abinci ta kalli qofa kamar tana jiran isowar wani hardai tagaji ta nufi dining tana fidda wani irin qamshi mai dadi.
Fara cin abincinta kenan taji muryar data sakata dakatawa ta juyo da sauri suka hada ido da nuratu dake cikin tsananin farin cikin ganin rumanah din.
Miqewa rumanah tayi zata nufeta Jakadiya data kawo mata nuratu din tayi gyaran murya dole ta tsaya tana kallon nuratu cikeda farin ciki
Nuratu ‘dince taqaraso gaban rumanah tana kallon cikinta tana sake bayyanarda farin cikinta zata zube qasa rumanah ta riqota tareda Rungumeta duk da tsinin cikinta baibari sun rungume juna sosaiba.
Cikin tsananin murna rumanah tace,
Tun jiya yakamata ace ke nafara gani da mamani amma shine kikaqi zuwa sai yanzu danace anemoki ina mamani?
Baki washe tace,
Mamani qila wani aiki ya hanata zuwa nima sbd tun jiyan nake yawo a hanyar sashen nan sbd kawai naganki amma bansamu damaba yanxu ana cewa kekenemanmu na aje aikina nazo bakisan yanda na matsu nagankiba rumanah nayi kewarki sosai kinbarni cikin kadaicinki…
Hawaye suka sakata kasa cigaba da maganarta
Rumanah ma hawayen ne suka ciko mata idanuwa ta riqe hannunta tace
Nayi kewarki nima nuratu saidai bayanda zanyine sbd kinsan da zabi ake bawa mutum nafison zama taredaku duk da ayanxu komai ya canxa arayuwata saidai matsayinku nanan keda mamani bazan ta6a canzakuba arayuwata.
Murmushin qarfin hali nuratu tayi tace,
Mamani bazata taba datace, +
Mamani bazata taba daukarki ayanda kika dauketaba.
Ni zan cigaba da daukarta matsayin yayar mahaifiyata har qarshen rayuwata bazan taba duba abinda takeminba tunda na saba.
Karkice haka rumanah sbd yanxu akwai banbanci bazanzo na rasataba sbd yi miki wani abu yanxu daidai yakeda rasa rayuwarta.
Karki damu da wannan yanxu zo muci abinci tare nayi kewar hakan sbd bansaniba kozan sake samun irin wannan damar tacin abinci tare dake.
Zama sukayi a babban dining din mai kujeru goma sha biyu nuratu na ‘dar ‘dar rumanah najanta da magana sbd tasaki jikinta ahaka sukaci abinci nuratu taci abinda takeso ta qoshi suka nufi palonta na qurya nan suka fara fira
Nuratu takalli cikin rumanah dayayi mata kyau matuqa musamman sbd bai sakata qiba ba tsawo yayi sosai.
Murmushi tayi cikin kulawa tace,
Nayi farin cikin ganin rayuwarki ta canxa rumanah gashi zaki haifar mana ‘yaya jinin sarauta.
Kallonta rumanah tayi tasaki murmushi kawai sbd tunaninta ba akan firar tasu yakeba.
Agurinta nuratu ta wuni sai tsakar dare ta tafi koshi da sharadin gobe Jakadiya zata saka acanza mata aiki adawo da ita gurinta.
Mamani kuwa sunyi jiran zuwanta harsun gaji bata zoba gashi dokace akan rumanah bazata fita koinaba idanba da qwaqwaran daliliba harsaita haihu
Washe gari aka dawo da nuratu aiki gurinta duk yanda taso hanata aiki tabarwa sauran kuyangin qi tayi saidatayi.
Kowace safiya da maraice sai Ammy ta Aiko mata da madara mai zafi itada suhailat harsukai kwana uku inda tun tana dannewa harsaida damuwarta ta daqushe kuzarinta matuqa dan ita kadai tasan halinda zuciyarta take ciki na rashin ganinsa gashi da alama bazata sake ganinsa ba saita haihu qila hakan ke sata kwantawa tayi kukanta sbd ji take nutsuwarta na neman gagararta abincima tun nuratu na iya yinta dan ganin taci har abin yafi qarfinta ta sanarda Jakadiya rashin cin isashen abincinda rumanar keyi.
Lokacinda Jakadiya taje ta sanarda ammy hakan yarima na tareda ita bai ‘dagoba amma ammy kallo ‘daya tayi masa tagano halinda yake ciki musamman dama tana lureda shikansa miskilanci da mulkine yahana agano halinda yake ciki na rashinta.
Jakadiya tayiwa wani irin kallo nan take tagano me take nufi ta gyada kai ta wuce zuciyarta fal tsoro da mamakin irin sonda yarima kewa rumanah haka ta wuce taje kitchen ta bada umarnin ayi dukkanin girkinda akasan yarima maheer naso a shirya a palonsa na musamman zaici abincin daren tareda matansa.
Da daddare koda Jakadiya tazo kiranta cin abinci cikin yanayi na rashin walwala tace batajin dadin cikinta bazata iyacin abinciba yanzu sai zuwa anjima.
Ba musu Jakadiya ta tafi
Koda yafito cin abincin cikin wata irin shiga ta musamman ta kayan shan iska qamshinsa na fita ahankali.
Suhailat dake zaune da cikinta ya kalla cikeda kewarta da tausayinta ya ware mata hannu ta taso ahankali tashige jikinsa ta rungumesa tareda sakin ajiyar zuciya.
Cikin kulawa ya dagota tareda kallon fuskarta da cikinta ya shafi fuskarta ahankali yace,
Hey hw are you?
Murmushin mai ciwo tasaki na qarfin hali tace,
Lafiya klau I missed you””ya fada tana zamewa daga jikinsa ta zauna kan dining sbd ita kadai tasan me ta hango a cikin idanuwansa.
Zama yayi yana sake kallonta ganin jikinta yayi sanyi lokaci ‘daya duk saiyaji lissafinsa na sake kwancewa abincin gabaki daya yafita ransa
Itama abincin fita ranta yayi saidai hakanan ta tsakuri kadan taci ta miqe tazo tayi kissing forehead dinsa tace,
Gud night””ta fice tana mayarda hawayen idonta.
Harta fice bai motsaba sbd damuwa da takaicin kansa dayaji akaro na farko. 1
Saqone yazowa Jakadiya daga yarima maheer cikin gaggawa ta nufi sashen rumanah ta bada umarnin duk wata baiwa dake sashen rabarshi cikin mintuna biyu kacal.
Babu 6ata lokaci dukkaninsu suka watse bayan koina yadauki sabon qamshi sai masu tsaron qofar shigowa ne kawai.
Kwance take lamo bakin gado idanuwanta a rufe tayi nisa cikin tunani.
Ahankali taji qamshinsa yana shiga hancinta ta bude ido tareda lumshewa zuciyarta na sake shiga damuwa sbd tasan ha har abada bazaizo sashentaba sbd atarihin sarautar mineelik ba’a taba yin sarki ko yariman dayaje ‘dakin matarsaba saidai ita taje to mezaisa shi yazo gurinta. +
Shafo fuskarta yayi ahankali cikeda kulawa yana kallon kyakkyawar fuskarta tayi saurin bude idanuwanta dasuka ciko da hawayen ganinsa saita samu kanta da mayarda idanuwanta ta rufe.
Rintse ido yayi cikeda mamakin kansa ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa murya qasa qasa yace,
Are you angry?
Bude ido tayi takallesa sbd bata taba tunanin zai kulaba harya tambaya.
Idonta dake kansa yakalla yana sake matse hannunta cikin nasa yace,
Tashi zaune.
Ba musu ta tashi zaune ya saki hannunta ya fito palo tabisa da kallo zuciyarta na qara mutuwa a sonsa,
Jin soyayyarsa takeyi har cikin jini da ruwan jikinta kowane bugawar zuciyarta da sonsa take fita tana fata da roqon Allah yasa kar soyayyarsa tasakata kaucewa hanya takoina koda kuwa sonsa da kishinsa zasu kasheta.
Jakadiya na ganin fitowarsa tayi saurin qarasowa tace
Allah yataimaki uban magajin mineelik akwai abinda ake buqatane?
Hannayensa ya zuba cikin aljihun wandonsa cikin wani irin miskilanci yace,
Ahado abincin cin mutum biyu.
Cikin qanqanin lokaci ta dibi abincin cin mutum biyo ta jero a tray takawo masa ga mamakinta hannu yasa yakarba ya juya dakin yabarta da baki sake sbd tsananin mamaki.
Duk yanda yaso tasakar masa fuska qi tayi yasamu ya lalla6ata taci abincin ganin shi baici ba yasata daukar abincin itama ta basa babu musu yaringa ci harsaidata kwatanci ya qoshi ta ajiye tana kallonsa da mamaki yadauki tray din yamiqawa Jakadiya dake palo ta fice da kayan.
Brush yakaita har toilet tayo suka dawo ta zauna bakin gado ya zauna kusada ita tareda kallon fuskarta dahar lokacin take kadaran kadahan duk saiya rasa me ke masa dadi baimasan mezaice mataba sbd baisan menene yake faruwaba gabaki daya ta qarasa dame masa lissafi ya dafe goshinsa tareda rintse ido ya bude ya miqe zai tafi kawai yadawo yajawota jikinsa ya rungumeta batareda yace komaiba.
Rungumesa itama tayi tareda barin hawayenta datake riqewa suka gangaro tana sake qanqamesa.
Tun jekadiya na jiran fitowarsa harta gane ba fitowar zaiyiba tabar palon takoma palon farko ta dasa sabon jira.
Tunda tabaro gurinsa mararta tafara ciwo ahankali tana shiga bedroom dinta takwanta tana qoqarin danne ciwon datake ji amma alamarin yafara qarfafa kafin tayi wani yunquri ciwon mara ya taso mata gaba ‘daya gashi cikinta yanxune yashiga cikin wata na bakwai.,
Cikin qanqanin lokaci ta tabbarda naquda ce ta taso mata mai tsananin azaba sbd bata taba jin irin wannan ba a duk haihuwarta tun tana boyewa tuni yaci qarfinta koda Carolina taji kamar nishinta a dakin da sauri ta fita zuwa neman mutane duk da dare ya tsala sosai har anyi kiran farko.
Asubar farin yabaro part din yakoma nasa ita kuwa zazzabi ne mai qarfi ya rufeta bayan wankan datayi da asubar amma bata nuna masaba saida ya fice takwanta tana rawar sanyi mararta na mata ciwo ahankali.
Qarfe takwas na safe ta shirya daqyar tana daddaurewa sbd ta masa alqawarin zuwa gurin ammy yin breakfast su hadu acan.
Nuratu na lureda kamar batajin dadi amma tayi shiru sbd ganin kamar batason yin ko magana suka fito suka nufi sashen sultana ana biyeda ita bayi kuwa sai zubewa sukeyi suna bata hanya cikin tsananin girmamawa.
Jakadiya nacan tareda masu karbar haihuwa sashen suhailat hankulansu duk atashe sbd haihuwar tazo mata da gardama matuqa
Shikansa lokacinda labarin ya iso masa hankalinsa ya tashi dan haka ko gurin ammy bai nufaba ya kira doctors din dake karbar haihuwar kasancewar yasansu duka matane suke karbar haihuwa a masarautar in brief sukai masa bayanin haihuwa ce zatayi ta wata bakwai kuma tazo da gardama sosai
Kafin su isa sashen ammy ta lurada akwai abinda yake faruwa a masarautar sbd koina yayi tsit babu dogon motsi nuratu ce ta sanarda ita suhailat ce ke naquda.
Faduwa gabanta yayi zuciyarta na cikeda mamaki da tausayin suhailar da ita kanta batace komaiba sai sanyi da jikinta yayi tana mata fata fatan haihuwa lafiya.
Cikeda kaduwa da rashin sukuni ammy ta kalli Jakadiya tace,
Ya Allah karabasu lafiya saidai ina cikin damuwa da fargabar yaya haihuwar rumanah zata zo itama Allah kadai yasan mezata haifa.
Numfashi mai qarfi da sanyin jiki Jakadiya tasaki cikin rashin sanin abinyi itama tace,
Mafita ‘dayace itace idan har anason sirrin mutuwar iyayen rumanah yazamo sirri daga gareta muyi adduar kar asamu namiji daga gareta idanma ansamu namijin mutuwarsa itace mafita.
Kallonta sultana tayi da sauri tana sake shiga rudu tace,
Mutuwarsa na nufin qarasa bankado komai Wanda kinsan hukuncinda zamu fuskaanta agun sultan zaifi musan hanyarda zamubi musan wannan sirrin yacigaba da zama sirri kamar yanda sultan yafada tun farko…
Saidai kuma zuciyata na quna da fargabar yanda zan fuskanci rumanah ranarda tasan mune sanadin mutwar iyayenta….
Da qarfi ruwan haihuwa suka 6alle mata lokaci ‘daya sbd masifa da tashin hankalinda tashiga lokaci ‘daya
Cikin tashin hankali suka juyo cikeda mamaki da tashin hankalin abinda taji kafin suyo kanta ta durqushe agurin cikin tsananin azabar ciwon mara nan take naquda mai qarfi ta taso mata.A gaggauce.
Dafe cikinta tayi cikeda tsananin azaba da wani irin juyi da cikin keyi mata.
Arikice Nuratu ta riqota tana kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali
Su ammy atare sukayo kanta cikin sobon tashin hankali da fargaba
Ammy ta riqota tana kiran sunanta cikin damuwa take kiran sunanta. +
A gaggauce suka kamata sukai sashenta da ita inda tun kafin su isa ta qarasa rikicewa sbd azabar naqudar.
Cikin gaggawa Jakadiya ta isa gaban sultan dake zaune cikin royalhall suna jiran haihuwar suhailat ta zube qasa kanta qasa ta sanarda shi ummu-rumanah ta shiga naquda yanxunan.
Da wani irin kallo ya dubeta zuciyarsa na shiga wani sabon farin cikin sbd yasan cikinsu biyun dole asamu namiji insha Allah.
Wani murmushi yasaki na qasaita cikin nuna isa yace,
Kije idan akasamu namiji a mineelik yau namiki na miki alqawarin dukiyarda bazaki iya qirgata da kankiba sai antayaki.
Cikin fargaba tayi godia ta fice hankalinta tashe sbd daga ita har sultana a gigice suke basa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali sbd fargabar haihuwar rumanah dakuma babban sirrin dataji Wanda basusan ta yaya zasu fara fuskartartaba saidai abinda suka sani kome zatayi wannan sirrin bazai fadu garetaba babban tsoronsu da tashin hankalinsu kar Maheer yaji wannan alamari.
Kai tsaye sashen yarima ta nufa lokacin yana zaune palonsa na farko zaune ya dora qafafunsa kan table din dake gabansa ya rufe idanuwansa kallo daya zaka masa kasan kadaici yake buqata baya buqatar hayaniya sbd yanayin naqudar suhailat dayake cinsa musamman yanda yasan ta wahala haihuwarta ta qarshe gashi yanxu har lokacin bata haihuba yana iya sensing azabar datake ciki.
Gabansa Jakadiya ta tsaya tareda rusunawa cikin jimami tace,
Allah yataimaki uban magajin mineelik uwardakina ummu-rumanah ta shiga naquda yanxunan..
Idanuwansa dake rufe ya bude ahankali ya zuba mata suna sake canxawa sbd dama tuni suka canxa sbd zaman jiran na kashesa.,
Miqewa tayi ta fice jikinta a sanyaye sbd gabaki daya ta rasa nutsuwarta jitake kamar zata zauce sbd fargabar tashin hankalinda zai biyo baya idan rumanah ta haihu ta tambayi abinda taji ayau din.
Wayarsa daya kashe ya dauka ya kunna tareda kiran Dr ammenen muryarsa na bayyanarda tsananin damuwarsa da tashin hankalinsa yace mata tabar Dr noorah da nurse agurin suhailat taje gurin rumanah takuma babbatarda tana basa bayanin komai harta haihu idan kuma taga da damuwa takirasa kawai zaizo yakarbi haihuwar da kansa duk abinda zai faru yafaru.
Aje wayar yayi zuciyarsa kamar zata buga,
Yanxune yake sake takaicin haihuwarsu anan sbd acan shine zai karbi haihuwar kowaccensu da kansa musamman ita datake ta farkonta tana tsananin buqatarsa.Dafe goshinsa yayi ya miqe yayi ciki ganin kamar zai iya rasa hakurinsa yaje musamman dayaga anfara jan lokaci babu wadda ta haihu. +
Duk iya galabaituwa kowaccensu ta galabaitu sbd kowacce gadan gadan naqudar ta taso mata babu sauqi,
Duk Wanda ke cikin mineelik hankalinta a tashe yake tsit koina ana jiran tsammani
Sultan ma wannan karon saida hankalinsa yatashi shi fargabarsa kar doguwar naqudar tasa a rasa ‘yayan dake cikin. 1
Ammy duk inda nutsuwa da kwanciyar hankali suke basa tareda ita ko zama takasayi addua tajeyi tana qarawa musamman datake jiyo irin azabarda rumanar ke ciki sbd tana palo suna ciki tareda masu karbar haihuwar.
Zufa mai zafi Jakadiya ta sharce lokacinda Dr ammenen takalli nurse tace,
Get ready ga babyn nan fitowa yanzu Ku kawo komai kusa.
Zufa Jakadiya ta gogewa rumanah data fice hayyacinta cikin tsananin tausayi da tashin hankali take mata sannu.
Cikin wata irin rikitacciyar azaba tayi wani irin nishi mai qara Atake baby ya fado Dr ammenen ta qarasa jawosa tareda yanke uwa ta ‘dagasa sama ya buga wani irin kukan jarirai babu qaqqautawa.
Kadan yarage Jakadiya bata fadawa rumanah ba sbd rudewa da ganin abinda aka haifa.
Miqa mata shi Dr tayi jikinta na matuqar tsuma ta karbesa aka nado cikin farin zanin auduga mai tsananin laushi ta qura masa ido tana jera ajiyar zuciya ba qaqqautawa.
Wata sabuwar azaba ta tasowa rumanah cikin tashin hankali Dr takalli cikinta tana cewa nurse wani babyn na zuwa.
Jiki na rawa Jakadiya ta fito ammy data jiyo kukan jariri ta matso bakin qofar jikinta na ‘dan rawa zuciyarta kamar zata fado sbd bugawar datakeyi a qofar sukayi karo da jakadiya hannunta na rawa ta karbi jaririn tana qoqarin budewa taga menene cikin rawar murya Jakadiya tace,
NAMIJI NE. 3
Da sauri ammy ta dago ta kalleta tareda hadiye yawu ta qurawa yaron ido jajir dashi babu inda ya dauko rumanah Sak maheer ne saitaji bazata iya cutatar dashiba.
Nurse ce tazo ta karbesa sbd aankeshi dazasuyi su kintsashi kafin dayan babyn yafado sbd naqudar takoma qasa tsananin wahala take sha ko ayanxun.
Jiki na matuqar 6ari Jakadiya ta isa qofar sashen maheer tun a qofar ta zube tareda ‘daga murya tace,
Allah yataimaki uban magajin mineelik ummu-rumanah tasauka lafiya ansamu magajin mineelik da yardar Allah.
Zabura yayi daga kishingiden dayake yana sakin ajiyar zuciya da qarfi yana rufe ido sbd zaman jiran dayake shine abu mafi azabtuwa a tsawon rayuwarsa ayau ya raina zamtaowarsa likita tunda bai taimaki matarsaba lokacinda takeda tsananin buqarsa. 2
Fitowa yayi cikin wata irin qasaita hannuwansa zube a aljihunsa ya tsaya nesa da jakadiyar yana kallonta kamar tana daukeda abinda aka haifar yace,
Kije ina miki albishir da zama jakadiyar magajin mineelik tareda kyautar werik’i(gold)
Murna fal cikin ranta tace,
Ameseginalehu(godiya) 1
Miqewa tayi zata fita abakin qofa taci karo da ‘yar saqo daga sashen suhailat ta durqusa qasa cikin girmamawa da rawar jiki tace,
Gimbiyar yarima ta sauka ansamu NAMIJI saidai likita tace sanarda yarima bazata sake haihuwaba mmahaifarta tasamu matsala wannan itace haihuwarta ta qarshe.
Zaro ido Jakadiya tayi cikeda tsananin mamaki da farin ciki tareda tausayin suhailat tajuya takoma gurin maheer tasanar dashi atake ya sake lafta mata wata kyautar zuciyarsa na harbawa da qarfi
Ya zauna ahankali tareda lumshe ido yana yiwa Allah godia.Koda Jakadiya takoma sashen rumanah haihuwar tazo gadan gadan nan wani babyn ya fado Dr ta ciresa nanma sukaga namiji atake aka shiryasu jikin Jakadiya babu inda baya rawa ta zube gaban sultan kanta qasa cikin tsananin farin ciki tace,
Allah yataimaki kakan magajin mineelik ummu-rumanah ta sauka lafiya ansamu ‘yan biyu duka MAZA sai gimbiyar yarima itama ta samu ‘da namiji
Ina yiwa sultan farin cikin ganin wannan rana mai tarin cikar buri da biyan buqata,
Ayau mineelik ta samu qaruwar ‘yaya uku uku duka maza ina sake taya sultan murnar ganin wannan rana.
Wani irin murmushi yake fitarwa mai bayyanarda farin cikin da zuciyarsa ke ciki bamai misaltuwa bane
Dukkanin Wanda ke royalhall din farin cikine mai tsanani a fuskarsa nan take aka buga bell din mineelik aka sanarda haihuwar magajin mineelik atake labarin farin cikin ya bazu koina Ethiopia ta dauka kowa farin ciki yake da wannan burin na qasar daya cika.
Dayake ba qaramar wuya dukkaninsu suka sha ba ana kimtsasu sai bacci banda rumanah data rufe idone kawai zuciyarta cikeda tashin hankali da fargaba tareda baqin cikin abinda kunnuwanta sukaji mata ammy na fada da bakinta.
Hawayen idonta suka gangaro batareda tadamu da gogesuba ta bude idanuwanta dasukai ja hawayen nacigaba da 6alle mata.,
Idan kunnuwanta sun jimata daidai ammynta ke fadar sune suka kashe mata iyaye kenan ba mutuwar Allah sukayiba qarfi da yaji aka rabasu da rayuwarsa,aka rabasu da ‘yarsu,Ashe shiyasa aka ‘yantasu???
Girgiza kanta tayi hawayenta na tsananta tace,
Ammy bazatayi hakaba nice banji daidaiba,ammy bazata iya kashe kowaba bare iyayena.
Sakin siririn kuka tayi tareda kifa kanta a pillow.
Suhailat kuwa bacci tayi sosai sbd ta galabaita fiyeda yanda ta tsammata saidai tana haihuwar taji batajin komai.
Lokacinda aka kaiwa maheer yaran duka yana tareda khaleefa daya iso ranar khaleefa ne yakarbi sauran biyun maheer kuwa Wanda aka fara haihuwa ya karba akaro na farko dayaji jikinsa yayi sanyi sbd soyayyar yaron dayaji shima yau yahaifi magajin kansa bama na mineelik kawaiba.
Qura masa idanuwansa yayi ganin yaron shine Zak sai lips din mahaifiyarsa daya dauko ya sa hannu ahankali ya shafo lips din tareda sakin wani irin murmushi qasa qasa yayiwa yaron addua kafin ya furta,
ABEEL HASSAN.
Kallonsa khaleefa yayi cikeda farin ciki ya maimaita sunan yana jinjina kai kafi ya karbesa ya miqa masa babyn suhailat da ba’ason motsasa sosai.
Qura masa ido yayi cikeda tausayinsa da qaunarsa mai qarfi shima shiya dauko Zak saidai zamansa qarami sosai yasa yafisu haske.
Addua yamasa sosai cikin rada rada ya furta,
Jemaal.
Koda ya karbi Hussain din abeel abrar bayan yamasa addua ya rada masa,
ABEEL HUSSAIN
Koda aka kaisu gurin sultan kowa saida yatabbatarda yau ranar daban take arayuwarsa ya ‘dagasu daya bayan daya yayi musu addua kafin aka sanar dashi sunayen da yarima maheer ya rada musu sultan mai damuba sbd ayau angama masa komai arayuwa ya ‘daga abeel cikin babbar murya yace asanarda kowa ga magajin mineelik ABEEL HASSAN.
Atake akaje dakin tarihi aka saka sunansa da sunan mahaifiyarsa nan aka fara shagulgulan haihuwar.
Har dare ammy bata samu ganin rumanah ba sbd tunda tayi wanka take rufe a dakinta tace bata buqatar kowa Hutu take buqata.
Lokacinda aka kawo mata yaranta qura musu ido tayi hawaye na gangaro mata sbd idan bar aka iya raba iyayenta da ita za’a iya rabata da ‘yayanta saidai batajin hakan zata iya yiwuwa koda zata rasa rantane.
Rungumesu tayi tareda rufe ido qaunarsu data mahaifinsu na shigarta tako ina.
Da daddare lafiyyan abinci kala kala aka aika gefen kowaccensu aka jera.
Duk yanda Jakadiya da ammy sukaso ganinta qin bari tayi ta dasun shigo zata rufe ido tana bacci idan sun fita zata cigaba da kukanta.Kukane takeyi na rashin Sanin abinyi sbd ko ganin kowa batason yi. +
Lokacinda labarin haihuwar tasamu adama da ‘yar dakinta mamani kadan yarage adama bata yanke jikiba mamani kuwa kasa daurewa tayi saidatayi kuka taji sauki sauqi cikin ranta.
Koda aka kawo mata yaran saka musu albarka saidata kai zuciyarta qololuwa gurin bugawa kafin ta iya kallonsu idanuwanta na cikowa da hawayen baqin ciki tasaka musu albarkar dole.
Suna fita ta miqe batareda takalli mamani dake matsar hawayeba cikin tsananin tashin hankali tace,
Duk yanda za’ayi ayi yaran nan bazasukai ranar sunansuba batareda sunbar duniyaba kije yanxu ina buqatar kadaici gobe zan fada miki abinda zakiyi sbd inason alhakin mutuwarsu ya rataya akan kakarsu da jakadiya sbd inason qulla gaba mai tsanani tsakaninsu da yarima tareda matansa kuma inason sultan ne da kansa zai yankewa sultana hukuncin kisa ta yanda abin zai riqa bibiyarsa yana damunsa da haka zansamu sauqin aikina akansa.
Acikin daren yakira suhailat yaji yajikinta tareda jemaal duk da khaleefa yadubasa sosai yafadi dokokin daza’abi kafin suna shi dole za’a koma Georgia dashi sbd yanayinsa acan za’a fara kula dashi.
Duk yanda yaso ganinta yasan abune mai wuya saidai kuma bayajin zai iya bacci bai dubotaba bayan baqar wahalar dayasan tashiga yau gurin haihuwa saidai koda ya aika asanarda Jakadiya taje tayi ma sashen isonsa ta sanardashi har lokacin bata fitoba taji jiki sosai hutawa takeyi haka ya hakura saidai asubar fari ya isa dakinta lokacin tana zaune bakin gado tasaka yaran agaba hawaye nabin fuskarta.
Qamshinsa yasata rintse idanuwanta hawayenta na sake gudu.
Zama yayi kusada ita tareda riqo hannunta baice komaiba ya kwantarda kanta jikinsa sai kawai tasaki kukan datake ruqewa ahankali
Cikeda mamaki da damuwa ya kalleta zaiyi magana ta zame daga jikinsa tana tsaida hawayenta cikin dasashiyar murya tace,
Kaina na ciwo ina buqatar hutawa.
Da mamaki yakalleta saidai baice komaiba ya miqe ya fice
Ta saki sabon kuka cikin rashin Sanin abinyi.
Duk inda hankalinsu ammy yake yatashi dashi kansa maheer din sbd kwana uku da haihuwar ko kadan rumanah takasa bari ko ‘dayansu ya ganta duk wani tashin hankali suna ciki
Ta hargitse tarasa abinyi gabaki daya ta birkice shikansa ta hanasa ganin kanta bare yasan meke faruwa babban tashin hankalin daya riskesu shine sanarwar da akayi za’a bawa uwar magajin mineelik kujerarta ta uwar sultan.
Sam ammy ta rasa ina zata saka kanta shikansa baya cikin nutsuwa sbd bazai taba bari ta karbi sunan uwar sultan ba gashi dole zata karba itace zata bawa duk Wanda takeso riqon kwarya.
Yau kwanansu biyar da haihuwar dukkanin yaran suna sashen ammy tun safe.
Tunda sukazo abeel hassan ke kuka sosai anmayardashi gurin hamaifiyarsa saima qara birkicewa da yayi nan hankula suka tashi tuni sultan yasa atara duk masu magani da likitocin mineelik amma sai qara rikicewa yakeyi nan hankalin rumanah itama yayi masifar tashi ta rikice.
Cikin tashin hankali suka dunguma zuwa royalhall inda ake duba yaron kowa hankalinsa atashe yake.
Kallo daya yayiwa rumanah yaji lissafinsa yasake kwancewa kafin yayi wani yunquri sarkin gida yossouf Kaleb yashigo jikinsa na matuqar rawa ya zube gaban jakadiya yayi mata magana qasa qasa hankali tashe jikinsa na wani irin mazari.
Zaro ido Jakadiya tayi cikin sabon tashin hankali jikinta yadauki muguwar rawa kowa hankalinsa nakanta anajiran jin saqon menene
Ta zube gaban sultan tareda sauke kanta jikinta na tsananta rawa cikin muryar tashin hankali da tsananin fargabar rasa rayuwarta tace,Allah yataimaki sultan ina cikin baqin cikin sanardakai ankama baiwa mamani da dafin baqin maciji tabawa abeel Hussain da jemaal antabbatarda sun rasu saidai ankamata. 7
Rumanah dake zaune ta miqe a firgice jikinta na rawa saidai ko daga qafa batayiba ta yanke jiki ta fadi agurin.
Cikin tashin hankali yayi kanta kai tsaye yadauketa yabar palon su ammy na mara masa baya hankali tashe musamman sultana da a sashenta suke shaf tashin hankalin abeel hassan yasa suka mantasu acan.
Sultan kuwa numfashi ya sauke cikin wani irin yanayi ya miqe tsaye idanuwansa na canzawa.
Suhailat na zaune tana shan magani daqyar sbd ciwon ciki da jirin datake fama dashi tun safiyar yau din
Jakadiya ta shigo mata.
Murya na rawa tace,
Ina neman afuwar saqon baqin cikin danazo dashi Allah yakarbi ran jemaal……..
Bata qarasaba suhailat ta miqe tsaye atake jini ya 6alle mata ta yanke jiki ta fadi.Cikin tsananin tashin hankali Jakadiya tasa akayiwa Dr ammenen kiran gaggawa koda ta iso itama hankalinta tashe yake da jin abinda yafaru atake suka fara qoqarin tsayar da jinin daqyar yarage zubowar sosai saidai bata farkaba sbd allurar dasukai mata sbd jininta yayi matuqar hawa mai muni idan ta farka awannan halin zata iya samun paralyz. +
Sai bayan sunbaro gurinta aka sanarda maheer abinda yasameta lokacin yana qoqarin ganin rumanah ta farfado sbd duk iya abinda zaiyi ta farfado yayi bata farfadoba tashin hankalinda yake ciki yanxu yafi kowane tashin hankali na rayuwarsa,
Rasuwar yaransa gakuma halinda rumanah take ciki yanxu kuma ana fada masa suhailat ma…dafe goshinsa yayi tareda fitarda numfashi mai qarfi da zafi idanuwansa na sake canzawa.
Ammy sbd tashin hankalinda take ciki ko tsayuwa sosai bata iyayi tsaye take gaban gawarwakin yaran a palonta kallo daya tayi musu ta dauke kai hawaye na ciko idanuwanta sbd ganin yanda kalar jikinsu takoma mai duhu sbd dafin daya shiga jini da jijiyoyinsu sosai.
Zaman dirshan Jakadiya tayi tareda dora hannu ‘daya akai tana jinjina wannan baqar rana data zo musu koda suke tsananin buqatar haihuwar maza gashi ansamu mazan amma tun ranarda aka fara naqudarsu masifa tafara saukar musu saidai wannan masifar dasuke ciki yanxu mai hadari ce sbd koda misali sunanka yafito cikin wannan zancen mutuwace hukuncinka..
Jikinta na rawa ta miqe ta dauki gawar su biyun ta nufi fada qafafunta na wani irin rawa daqyar ta iya kai kanta gaban sultan ta zube tareda shimfidesu ahankali tana furta,
Tuba nake da kawo mugun gani gaban sultan da muqarabansa.
Kallo daya yayiwa likitan gargajiyansu ya taso yazo gaban yaran ya durqusa yadauki abeel Hussain yadubasa tareda zura hannu cikin bakinsa ya Ciro yakalla ya kalli sultan ahankali ya sunkuyar dakai ya girgiza kai alamar yariga ya rasu.
‘Daukar jemaal yayi yaduba shima ya tabbar musu da yarasu.
Atake sultan yakalli kaleeb cikin zallar 6acin rai da nuna ikonsa yace,
Akai mai laifin kurkuku mafi tsanani ahadata maciji mafi hadari har zuwa gobe kafin tafadi Wanda yasata sbd bayin kantabe batada isar dazata iya yiwa ko bawan mineelik kallon banxa bare iya kashe jinin sultan.
Cikin zaquwa kaleeb yace,
Angama sultan…ya fice yana kwatanto irin azabar dazasu ganawa mamani.
Cikin wani irin mummunan yanayi na firgici da tashin hankali ta farka tareda miqewa zaune jikinta na bata irin rawa tafara qoqarin tashi yayi saurin riqeta yana son kallon cikin idonta amma taqi tsayawa gabaki daya bata cikin hayyacinta fixgewa takeyi da qarfi yasake riqeta tareda girgizata da qarfi yakira sunanta.
Tasaki wani irin kuka mai qarfi tareda fixgewa daga jikinsa ta zube qasa tafara kuka sosai tana qanqame jikinta sbd wani irin ciwo da ra’dadi mai zafi takeji cikin ranta kamar zuciyarta bazata iya daukaba.Sake riqota yayi ya rungume jikinsa da qarfi duk yanda taso qwacewa kasawa tayi tacigaba da fidda kuka mai radadi. +
Wani irin ciwo da baqin ciki takeji na cin zuciyarta numfashinta har sarqewa yakeyi gurin kukan.
Kasa magana yayi sbd radadin da zuciyarsa ke ciki na rashin ‘ya’ya biyu lokaci ‘daya dakuma ganinta cikin wannan halin.
Ammy kallon Jakadiya tayi idanuwanta na qoqarin boye qwallarta tace,
Ya akayi mamani tashigo nan harta bari aka kamata domin na tabbarda tana sane tabari aka kamata akwai abinda take nufi da hakan Wanda shine tashin hankalina.,
Meyasa bata kashesu a dakunan uwayensuba sai agurina?
Innalillahi, allahumma ajirni fi musibati
Wannan wace irin masifa ce mai wuyar cinyewa.
Cikin sanyin jiki a raunane Jakadiya tace,
Alqawarin Allah ne zai tabbata sbd sbd ayanxu alamu sun fara bayyanar mulkin mace a mineelik Wanda hakan na nufin ba’a zubarda jiniba yanxune za’a zubar dashi.
Girgiza kai ammy tayi da sauri cikin tsananin fargaba da rudu tace,
Rumanah bazata taba zama mai zubarda jinin bayin Allah ba,
Nayi gudun haka kowa yakasa fahimtata,
Na roqi Allah a zuci da fili akan kar rumanah ta haifi namiji idanma ansamesa yazo babu rai amma hakan bata faruba yanxu bansan ta ina kuma wannan masifar ta 6ullo ba.
Duk yanda yaso ganin rumanah tadawo nutsuwarta abin ya gagara saima zuru datayi da ido kukan yadaina fita saidai hawaye kawai ko motsin kirki bata iyayi ta rakube gefe guda ta takure kanta.
Lokacinda aka shigo aka sanarda ita zuwan ammy dubata bata motsaba saima rufe idanuwanta datayi hawayen ciki suka gangaro tunani abubuwa da dama na dawo mata,
“” mafita ‘dayace karta haifi namiji idanma ta haifesa mutuwarsa itace mafita””
“” yaya kike tunanin zan fuskanci rumanah ranarda ta San cewar mune sanadin mutuwar iyayenta””
Rintse idanuwanta tayi da qarfi nauyi da zafin zuciyarta na qaruwa saidai batason barin zancen yashigeta a irin yanayin datake ciki yanxu sbd tanason tayiwa ammy fahimta mai kyau bazataso abinda kunnuwanta sukaji mata ba yazama gaskia.
Ammy kasa haquri tayi ta nufi dakin lokacin maheer yaje dubo suhailat.
Har ammy taqaraso gabanta bata motsaba daga inda take takure idanuwanta jajir.
Cikeda tsananin kunya da tausayinta murya na rawa tace,
Rumanah har abada bazan iya cire qaunarki arainaba sbd qaunace Allah yasakamin cikin raina Wanda kisani har abada bazan iya yin abinda nasan zan cutatardake ina fatar zaki riqe hakan aranki…Allah yaji qan abeel Hussain.
Juyawa tayi ta fice jikinta asanyaye sbd tana iya hasaso wasi wasi azuciyar rumanah.
Tana fita rumanar sulale ta kwanta agurin tasaki sabon kuka tana dafe qirjinta dake mata zafi da wata irin tafasa.
Cikin wata irin kaca mai tsananin nauyi da zafi aka na’do mamani da nauyin kacar yasata tafiya ahankali a duqe sbd ko qafarta daqyar take dagawa sbd nauyin kacar datake ‘daureda ita. 1
Aka bude wani tsohon kurkukun dayafi shekara goma ba’a shigesaba aja jefata ciki da qarfi kanta ya bugu da bango take goshinta ya fashe da jini ta fitarda numfashi daqyar sbd azaba gashi batada hannun shafawa taji sbd irin ‘daurin da’akayi mata ko numfashi daqyar take fitarwa.
Ta lumshe ido cikin azaba ta bude idon takalli qofar dishi dishi take gani sbd ba qaramar buguwa tayiba gashi anyi mata wani irin duka na rashin imani dan kariya biyu akayi mata a hannu ‘daya.
Wani irin kwando aka bude tareda jeho abinda ke ciki aka rufe qofa
Wani irin baqin maciji tagani ya bude kansa yana fitarda huci.
Mummunar faduwa gabanta yayi wasu irin hawayen azaba da tsoro tareda baqin ciki suka gangaro mata jikinta ko qarfin dazaiyi rawa bashidashi sbd ti6is akayi mata.Tana kallo macijin ya kwantarda kai yayi cikin wani qaton rami dake gurin Wanda shikansa ramin baza’a rasa wani macijin acikiba ko abinda yafisama.
Maganarta da adama ta tuno tana fargabar kar komai yaqi tafiya yanda suka tsara.
“”” idan kikai nasarar basu wannan dafin suka sha zasu mutu atake kuma ki tabbatarda ankamaki duk wuya da azaba karki ce nice kice sultana ce Wanda kowa yasan hukuncinta na kisa ne kafin akasheta za’a bani matsayinta na sultana nikuma zanyi amfani da wannan matsayin na hana akasheki kuma daga lokacin namiki alqawarin matsayin Jakadiya kintashi daga baiwa har abada saidai kuma idan kika fadi sunana kisani babu 6ata lokaci dukkaninmu za’a kashemu amma idan kikace itace nizan kubutar dake kinga burinki na shekara da shekaru yacika ga ‘yanci da dukiyar kanki dazaki tara”””” 5
Numfashi tasaki a wahalce tana sake qarfafawa zuciyarta dan cika sauran aikin dan kuwa koda ta mutu tasan burinta akan zuriar bulama da asma’u yacika. 2
Suhailat data farfado ahankali hawaye kebin fuskarta suna sauka kan qirjinta idanuwanta arufe sbd ko hannunta daqyar take iya motsasa.
Qunci ne arayuwarta da zuciyarta,
Rayuwarta ta lalace batada wani sauran farin ciki,
Ta rasa mijinta badan ya rasuba,
Ta rasa rayuwar aure mai farin ciki,
Ta rasa lafiyarta,
Ta rasa mahaifarta gurin haihuwa ga abinda ta haifa ta rasashi mai zaunawama ya rungumeta ya rarrasheta ta rasa
Wace irin rayuwace mai tattareda garari take ciki? 8
Wani irin kuka mai qaramin sauti tasaki zuciyarta na mata ciwo mai tsanani
Kewar iyayenta da ‘yayanta takeji sbd sune kadai sukasan zafinta da damuwarta. 2
Qarasawa yayi bakin gadon tareda Rungumeta da sauri yana jin tausayinta fiyeda kansa sbd yasan tafi kowa cutatuwa sbd tafi rasawa tunda ba wata haihuwar zata sakeba.
Akaro na farko arayuwarta taji batason kusancinsa agareta sbd nauyi hakan ke qarawa zuciyarta saidai ko motsi sosai bata iyayi bare ta zame jikinta hakan yasa wani sabon kukan qunci zuwar mata ahankali.Sosai ya lurada batai farin ciki ko jin sanyi da ganinsaba akaro na farko arayuwar aurensu daya hango wani yanayi daban akansa wanda ba sonsa bane atareda ita ya rufe ido cikin wata sabuwar damuwar yanajin tausayin kansama sbd wata jarabawace Allah yake jarabtarsa da ita akan rumanah wadda idan baiyi taka tsantsanba zai tashi da Rabin jiki ranar lahira saidai kuma baisan yaya zaiyiba sbd sonta yazama halitta ajininsa. 1
Ahankali ya furta,
Allah yaji qan jemaal.
Sakinta yayi ya miqe tareda ficewa batareda ya qara kalma ‘daya ba. 1
A wannan daren mineelik ba kowa yasamu damar kwantawaba bare ya rintsa sbd dukkanin dole da masautar na cikin tasa kalar damuwar.
Rumanah dai duk yanda akayi da ita taci abinci ko motsi taqiyi daga inda take idanuwanta sun bushe sunyi jajir ko gani sosai batayi sbd kumburin idanuwanta.,
Suhailat kuwa har lokacin bata iya kwakwaran motsi sai hawaye da ciwon qirji dayake cinta ita kanta anyi anyi taci abincin amma ko bude ido taqiyi sai hawaye take zubarwa.
A rayuwarsa wannan ne karo na farko dayaji yayiwa sarauta da gidan sarauta wata irin muguwar tsana sbd yasan son mulkine yasa akai hakan,
Ya tabbatarda kisace ta tabbata akan baiwar datayi da wainda suka sakata saidai bayajin zai tsaya ganin hakan gobe zaayi hidimar radin sunansu a goben zasubi jirgin dare su koma dan idan yananan zuciyarsa zata bugane da halinda matansa suke ciki musamman suhailat datake buqatar kulawa sosai.
Ammy da jakadiya kusan a zaune suka kwana ko ruwan arziki babu Wanda ya iya sakawa maqoshinsa sbd tashin hankalin dazai iya faruwa gobe sbd duk Wanda sunansa yashiga koda misali ne cire kansa ya wajabta gashi a sashen ta abin yafaru shine babban tashin hankali da damuwar dasuke ciki musamman dasukasan wacece mamani.
Ayau mineelik acike takeda duk wata masarautar dake zagaye da maqwaftaka da ita tareda wasu sarautun wasu qasashen da dama sbd gabatarda sunan magajinnta dakuma miqawa uwar magajin mineelik kambun saukewa da ‘dora sabon sultan.
Wannan matsayin daza’a bata ayau shine abu mafi ha’dari da tashin hankalinda yake ciki ayau
Ammy duk yanda taso daurewa kasawa tayi saida hawayen baqin cikin datake ciki suka gangaro mata tun a daren jiya ta hana su ganta bare ta sanarda ita hadari da kuma illar abinda zata fada.
Saidai alqawarine shi ya daukarwa kansa zai tabbarda ta miqa mulkin nan ga sultan ya dauketa sunkoma adaren yau din.
Lokacinda aka hallara dan qaddamarwa saqo ya isowa sultan uwar magaji batada lafiya bazata iya fitowa.
Kai tsaye aka fara qaddamar da komai aka radawa abeel Hassan sunansa tareda qaddamar da sunan ummu-rumanah acikin littafin tarihin mineelik amatsayin uwar magaji.
Nan take masu rubuta tarihi aka bude paging fara rubuta nata.
Daga ammy har yarima maheer babu Wanda ya halarci taron kuma sarai sultan yagano manufarsu tayin hakan zasu fuskanci hukuncinsa daga baya ayanxu baiwa mamani ce agabansa zai bata wata irin mutuwa mai firgitarwa itada wainda suka sakata ga ‘yan baya.Koina yayi tsit jiran hukuncin sultan akeyi lokacinda mamani ta tabbatarda Jakadiya ce tasakata amatsayin itama sultana ce ta aikota.
Tsita akayi kowa wuta ta dauke masa musamman sultan da mamakin baiwa mamani yakamasa sbd yafi kowa sanin sultanarsa bazata aikata hakanba,
Tabbas wannan baiwa mai taurin raice saidai ji da ganin hukuncin sultan kawai tajeyi batasan waye sultan ba. 2
Kallo daya yayiwa kaleeb cikin babbar murya yace,
Aje ajefawa zakuna ita su cinyeta da ranta akawo qashinta asa ‘dakin kayan tarihin mineelik…
Da ido adama dake dake gefensa tayiwa sultan aqeel magana ya gyara zamansa tareda kallon sauran sarakunan dake Royal hall din yace,
Idan aka kashe wannan baiwa batareda ta fadi wainda suka sakataba baka kai qarshen matsalar a mineelik ba sbd gobe ko jibi magajin ne da kansa za’a kashe kuma hakan zaisakawa mutane wasi wasin hukuncinka tunda ta fadi wainda suka sakata anshare anyi kamar bata fadaba.
Ido cikin ido yakalli sultan aqeel yace,
Babu Wanda ya isa yayi wasi wasin hukuncina a qarqashin mulkina da ikona ko wanene batareda na ciyar da namansa ga dabbobinaba.
Murmushin mulki sultan aqeel yasaki yace,
Hakane kuma idan kanason hakan yacigaba da faruwa saika nunawa mineelik Kaine sultan kuma Kaine kake yanke hukunci kowane irine akan ko wanene.
Nan take sauran sarakunan suka marawa gaskia baya suka qalubalanci sultan akan adalci idan har sultana ce tasakata to ayi adalci ayanke hukunci daidai yanda yakamata. 1
Atake mutane suka fara kallon kallo da hayaniyar abinda aka fada nan mamaki ya kama sultan kenan har akwai wainda zasu iya tambayar hukuncinsa su qalubalanci yanayin mulkinsa
Atake yace aje a kama Jakadiya arufe ya ‘daga hukuncin zuwa gobe duk me hannu aciki kafin faduwar rana baya duniya.
Lokacinda akaje aka kama Jakadiya aka rufe
Sultana kuwa rufe sashenta akayi tareda aje masu tsaron qofar da doka mai qarfi daga sultan babu Wanda zai shiga gurinta ajira hukuncinsa zuwa gobe.
Lokacinda zancen ya isa kunnen maheer kai tsaye gurin sultan yanufa akai masa iso lokacin anwatse sai gobe a shaida hukuncinda zai iya yankewa.
Kallonsa yarima yayi cikeda takaici da baqin cikin yanda yasan sultana bazata aikata hakan ga yayansa ba amma ya yarda haryana iya tunanin yanke mata hukunci
Kai tsaye yace,
Amatsayina na uban magaji zan kar6i mulkin mineelik har lokacinda zai girma ya karbi da hannunsa.
Wani irin murmushin takaici sultan yasaki batareda yakallesaba yace,
Mulkin mineelik da za6ar mai mulkin na mutum ‘dayane yanxu dan haka ka rasa damarka,
Mahaifiyarka kuma koni bazan iya kubutarda itaba idan har bincike ya nuna da hannunta aciki.
Yana fadar haka ya shige tabarsa zaune idanuwansa na kadawa jajir.
Duk inda tashin hankali yake masarautar na ciki dan shi kansa sultan jinjina alamarin yake aransa yana jaddadawa yana kuma fatar bincike yasa kar asamu hannun sultana aciki.
Acikin daren babu kalar azabar daba’a bawa mamaniba tace Jakadiya tasaka ta.
Jakadiya aka hau bawa baqar azaba amma daqyar take iya furta babu saka hannunsu aciki. 2
Acikin daren saqon neman sulhu da sassaucin hukunci yazo daga masarautar Libya dakuma wasu masarautun duk sai alamarin yasake girmama ya sake cabewa sultan gashi komene adaren ne sbd gobe dolene zai yanke hukunci.
Nuratu datun jiya take kuka da tashin hankalin halinda mamani ta fada koda bincike yazo kanta ba qaramin rikicewa tayiba saidai tafada musu komai na dangane da zancen dasukaji su Jakadiya nayi da sultana itada rumanah akan basuso ta haifi namiji.
Atake aka kaiwa sultan wannan zancen hankalinsa ya matuqar tashi saidai har lokacin yanada wasi wasin zancen ga asirinsu na 6oye daya fara shigowa cikin zancen Wanda tonuwar dolema yayi gaggawar yanke hukunci sbd kar maganar ta bankado atake ya yanke hukuncin kisa ga dukkaninsu ukun gobe.Acikin daren hankula suka masifar tashi jin anyekewasu sultana hukuncin kisa washe gari. +
Duk wata zuriar masarautar tun acikin daren suka fara isowa musamman ‘yayan sultana da kuka sunyisa na zuci dana fili hankalinsu amatuqar tashe yake.
Yarima maheer Kansa ya rufe adaki duk yanda yake tunanin masifar ta wuce nan abu ‘daya yasani bazai mahaifiyarsa ta fuskanci hukuncin kisar wulaqanciba.
Kwance take lamo idanuwanta jajir ko kukan bata iyayi duk abinda yake faruwa bata saniba sbd ta hana abar kowa shigowa gurinta.
Ahankali taji antsaya akanta batareda tadagoba ta lumshe ido tareda budewa taji muryar suhailat cikin wani irin yanayi tace,
Nazo neman alfarma agurin sbd kece kawai zaki iya tsayarda abinda ke shirin faruwa.
Tashi zaune tayi ahankali batareda takalli suhailat dinba
Itama suhailat sauke kanta tayi sbd batason kallon rumanah dan ganinta ke tuno mata da ba itace zuciyar mijintaba.
Hawayene suka gangaro mata tasaka hannu ahankali tashare taci gaba da cewa,
Nice uwar datai rashin abu biyu lokaci daya kuma zuciyata cike takeda neman adalci,
Ina roqonki amatsayina na uwar data rasa ‘da da mahaifarta akan adalci zanso ganin anmin adalci saidai bazanso akashe Wanda bashine mai laifinba sbd mai laifin zai cigaba da aikata 6anna aboye har wadda tafi wannan.
Cikin dasashiyar murya da sanyi tace,
Adalcin nima nake nema amatsiyana na marainiyar da aka raba da iyayenta dakuma uwar da aka rabata da ‘danta tun bata gama warkewa daga zafin naqudarsaba.
Asubar fari yashigo dakinta idanuwansa da yanayinsa suka karya mata zuciya ta dauke kai daga kallonsa tareda mayarda kanta kan gwiwoyinta.
Tsayawa yayi agabanta zuciyarsa cikeda baqin cikin kasancewarsa shine zai roqi wani yabasa sarautarda shine ya gada saidai yasan kubutarda ammynsa na nufin ya karbi sarautar ayau yazamo shine zai yanke hukunci sbd yagano sultan sbd 6oye wani sirrinsa yakeson yanke hukuncin da gaggawa ayau.
Kallonta yayi da idanuwansa dasukai jajir yace,
Inason kibani sarautar mineelik ayau.
Kallonsa tayi da sauri da jajayen idanuwanta dake budewa daqyar sbd kumburi.
Juya mata baya yayi yace,
Ki shirya ina jiranki kafin lokacin yanke hukuncin su ammy yayi.
Ficewa yayi tabisa da kallo zuciyarta na harbawa.
Cikin wani irin yanayi na sabon tashin hankali ta ‘dauki abeel hassan ta fito palo takalli nuratu dake rakube tun acikin daren tana jiran fitowarta tayi kuka har batada qarfin yin wani.
Kai tsaye tace,
Meke faruwa?
Da sauri nuratu ta tashi ta zube gabanta tana hawaye tace,
Ina neman afuwa akan shaidar dana bayar akan sultana da jakadiya gashi zasu rasa ransa sanadin shaidata saidai wlh ina rantsuwa da rayuwata mamani bayin kantabane sakata akayi saidai wlh bansan wayake sakataba dana fada nan fitardasu sultana dan haka ashirye nake da daukar hukuncinki.
Da wani irin sabon baqin ciki da takaici takalli nuratu saidai takasa cewa komai ta nufi qofa ta fice kai tsaye sashen suhailat ta nufa.
Zaune take a dakinta taqurawa akwatinanta data saka Carolina hadawa ido idanuwanta jajir.
Tsayawa gabanta rumanah tayi tareda miqa mata abeel hassan idanuwanta na cikowa da hawaye tace,
Duk duniya ayanxu kece kawai na yarda dake akan ‘dana sai Ammy dan haka ina riqonki daki riqesa har sai lokacinda kikaji zuciyarki ta gamsu da adalcin dazan baki,
Na miki alqawarin duk Wanda yakeda hannu aciki ayau zai fuskanci hukuncinsa.
Ficewa tayi kai tsaye ta nufi sashenta tashiga wanka zuciyarta na wani irin zafi tana fitowa tagansa tsaye cikin ‘dakin idanuwansa jajir ya kalleta ta ‘dauke kanta tareda isa gaban madubi ta zauna.
Cikin zafi ya jawota gabansa cikin ‘daga murya yace,
Me kike nufi da abinda kika fadawa suhailat?
Bata kallesaba tace,Kubutarda uwata. +
Sakinta yayi da sauri tareda kallon cikin idonta yace,
Kinsan abinda kike fada?
Kinsan abinda hakan ke nufi?
Bana buqatar ki shiga komai abu ‘daya nace kiyi shine ki bani matsayin danace inaso.Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta cikin rawar murya tace, +
Nima bana buqatar ka saka kanka cikin ha’dari dan haka bazan taba baka mulkin mineelik ba koda hakan na nufin rasa rayuwatane….
Riqota yayi da qarfi tareda girgizata yace,
Idan kina sona bazaki taba bari ataba mahaifiyata ba sbd itace rayuwata dan haka dole zaki bani mulki.
Hawayen dasuka cika mata idone suka gangaro mata ahankali tace,
Namaka alqawarin babu abinda zai samu uwar data haifi halitta mafi soyuwa arayuwata kozan rasa raina.
Shiga jikinsa tayi ahankali tareda rungumesa hawaye na tsinke mata.
Rintse ido yayi tareda rungumeta ahankali ya furta,
KECE RAYUWATA UMMU-RUMANAH BULAMA. 4
Dagowa tayi takallesa hawaye far in ciki na tsiyayo mata saidai bazata iya cewa komaiba.
Ruwan kan table din dake tsakiyar dakin ta dauka tareda kaiwa bakinsa tana tsiyayar hawayen tausayinsa dana kanta.
Ahankali yasha yana kallon cikin idonta.
Ahankali ta furta,
Karka gujeni kome zanzama arayuwa dan allah,
Ko bayan raina kayi kayi alqawarin tunawa dani.
Lumshe ido yayi jikinsa na mutuwa idanuwansa na fara gani dishi dishi a firgice yake kallonta sbd gano wani abune tabashi saidai kafin yayi wani yunquri ya zube kan gadon ta durqusa ta gyara masa kwanciyarsa tareda shafa fuskarsa ta miqe.
Dukkanin wani maison sheda hukuncin sultan na cikin qasar da wajenta sun hallara sultan na fitowa guri yayi tsit ya zauna kan kujerar mulkinsa atake aka fito da mamani da jakadiya dukkaninsu babu mai iya tsayuwa sbd azaba da ‘daurin dake jikinsu.
Kukan baqin ciki Jakadiya takeyi sbd irin mutuwar tozarcin dazasuyi tareda sultana.
Mamani na ganin masu jiran umarni sun tsaya akansu da takobuna suna kashe ido sbd laifi da qyallinsu hankalinta yatashi tabude ido daqyar tanason magana kaleeb ya take mata kai.
Ana jiran ana fitoda sultana cikin wani irin ama aka sanarda fitowar uwar magaji.
Atake kowa yayi tsit sultan yayi saurin kallon qofar
Tafito cikin wata irin doguwar ethiopiany royal gown red colour mai tsananin tsawo da adon black stones wuyanta da kanta na kyallin farin zinari kallo ‘daya zakayi mata kasan tana cikin baqin ciki.
Cikin wainda ke tareda ita Dan tsaron lafiyarta ta kalli gefen daya jiki na rawa ya fidda bayananta dake rubuce jikin fatar rubutu ya miqawa sarkin na’din sarautar mineelik.
Budewa yayi tareda fara karanto da qarfin muryarsa yanda duka alummar dasuka halarci gurin zasuji.
“” NI UMMU-RUMANAH BULAMA MATAR YARIMA MAHEER UWAR MAGAJIN MINEELIK AYAU KWANA ‘DAYA DA NADIN SUNAN MAGAJIN MINEELIK NA SAUKE SULTAN ABDULSHAMS ABDALLAH DAGA MULKIN MINEELIK NA KARBA HAR ZUWA RANARDA ‘DANA MAGAJI ABEEL HASSAN ZAI KARBI MULKI DA HANNUNSA..””” 6
Tsit koina yayi sbd firgici da mamaki
Sultan da adama kusan atare suka miqe tsaye tsabar firgici.
Ammy da ake fitowa da ita kadan ya rage ta yanke jiki ta fadi sbd jiyo sanarwar.
Jiki na rawa sarkin nadi tareda duk sauran sarakuna da wazirai suka miqe ta nufi kujerar mulkin mineelik gabanta da numfashinta na fita da sauri
Sultan dayayi mutuwar tsaye ya zare hular mulkin ya miqawa sarkin gida atake aka dauko kayan rantsarwa aka rantsar da ita atake ta zauna kujerar mineelik aka saka mata hular.
Lumshe jajayen idanuwanta tayi wani irin baqon yanayi mai qarfi na shigarta
Wani irin qarfin zuciya da taurin zuciya taji yana shigarta tsawon lokaci ahaka duk anyi tsit anajiranta.
Ahankali ta bude idanuwanta dasuka bushe nan take tagyara zama takalli inda sultan yake zaune yana kallonta cikin isa shima yanajiran jin nata hukuncin ta juyo takalli indasu mamani suke cikin daga murya tace,
Akawo abinda mamani tafiso aduniya.
Cikin gaggawa aka jawo nuratu aka durqusar tsakiyar gurin kai tsaye tace,
Ku yankata agabanta uwarta idan bata fadi Wanda yasakataba cikin seconds uku.Arazane sultan,adama,ammy,da baqin sarakunan dasukazo suka kalleta
Babu Wanda ta kalla acikinsu tayiwa kaleeb kallo ‘daya idanuwanta na sake bushewa cikin gaggawar cika umarninta kaleeb ya daga shar6ebiyar takobinsa mai cire kai lokaci ‘daya ya ‘dora a wuyan nuratu dake hawaye ta qurawa rumanah ido. +
Numfashin wahala mamani ta fitar cikin tashin hankali ta bude baki zatai magana adama datai mutuwar zaune tayi sairi tashi tsaye jikinta na wata irin tsuma zatai magana rumanah ta ‘daga hannu batareda takalleta tace,
Duk Wanda yayi magana batareda hukunci ya gama tabbatuwaba abakin rayuwarsu ko wanene. 9
A gigice adama tasake kallonta cikin wani sabon tashin hankalin takoma ta zauna zufa na karyo mata jikinta na wata irin tsuma.
Tayar da ita akayi tana numfashin azaba takalli takobin datake qyalli a wuyan nuratu takuma tabbarda yankata din za’ayi.
Ahankali rumanah ta ‘dagawa kaleeb kai alamar yacika aiki.
Atake ya ‘daga takobin cikin wahalalliyar murya mamani tace,
Gimbiya adama ce. 1
Cak kaleeb ya tsaya sbd harya ‘dora takobin a wuyan nuratu harma saida ya’dan yanketa.
Arazace sultan yakalli adama data jiqe jagaf da zufa jikinta na tsuma tanason kare kanta gashi ance duk Wanda yayi magana bbakin ransa kuma tasan tsaf rumanah zata iya sbd tasan abinda ka cikin karagar zaifi shigarta kasancewarta mace dan haka zatafi rashin tausayi da imani.
Sarakunan dake gurin duk ita suke kallo cikin mamaki yayanta kuwa kuka suka fashe dashi gashi babu ikon ko qwaqwaran motsi.
Rufe ido rumanah tayi wani irin yanayi na tsuma zuciyarta gawar ‘danta da iyayenta tana mata yawo ido da irin tozarcinda ammy ta fuskanta akan hakan
Fuskar maheer ce ta fado mata da irin tashin hankalinda tagani ataredashi tsakanin jiya zuwa yau ta bude idanuwanta dasukai jajir tace,
Ni sarauniya ummu-rumanah bulama na halastawa takobin kaleeb adana jinin adama kisheer ayau agaban mijinta da ‘yayanta tareda sauran alumma duk Wanda ko a fuska ya nuna hukuncina baimasaba a shayar dashi dafi daidai irin Wanda adama tashayarda qannen magajin mineelik., 4
Baiwa mamani arufeta mai rubuta tarihi yaje tabasa tarihin sarauniya rumanah arubuta atarihin mineelik tana gamawa bazata qara minti biyar aduniyaba a shayar da ita Kofi ‘daya na daafin macijin dayafi kowanne kaifin dafi,
Sultana zaarah da jakadiya sunfita da zargin da ake musu. 2
Sultan abdulshams arufesa a turakarsa babu shiga babu fita aabisaga zarginsa na qoqarin yanke hukunci batareda bincikeba harsai angama bincike akan niyarsa sultana zaarah ce kawai keda damar shiga da fita agurinsa sai yarima maheer.Arikice sultan yakalleta ransa na mummunan 6aci da baqin ciki ace rana ‘daya cikin mintunan dabasu wuce biyarba baiwa wadda bama asalin ‘yar qasaba ta saukesa akan mulkin daya gada iyaye da kakanni,
Ta yankewa matarsa kisan wulaqanci agaban dubban jama’ar dasuke shakkar ko kallon inda yake sannan yanxu tace arufesa a turakarsa wannan shine tozarci mafi muni arayuwa… 4
Yanxu ta karbi mulki idan tagano shine asalin dalilin mutuwar iyayenta akwai masifa sosai sbd yanda sihirin karagar nan ke shigarta nan cikin qanqanin lokaci zata zamewa kowa masifa mai matuqar hadari musamman shi saidai duk masifa duk balai bazai bari yayi mutuwar wulaqanci a hannuntaba koda hakan na nufin hada hannu da balain da aka binne shekaru tun kafinsu. 2
Kama adama akayi aka fara janta tayi saurin kwacewa ta isa gaban rumanah ta zube tana kukan tashin hankali jikinta na mugun karkarwa saidai takasa magana sbd umarninda rumanar tabayar ko kallonta rumanah batayiba ta kalli su kaleeb atake suka fara yiwa adama jan wulaqanci.
Jikin ammy ne yadauki rawa cikin sabon tashin hankali take kallon rumanah tana girgiza kai sbd matuqar tafara mulkinta ayau da zubarda jinin wani to tabbas zaiyi wuya bata zamewa mutane abin tsorobas.
Qoqarin isa gurin rumanah din tayi aka dakatar da ita ta hanyar tareta tayi saurin kallon rumanah data rufe idonta tanajin wani irin baqon yanayi shigarta.
Cikeda rashin imani da tausayi kaleeb ya daga takobinsa yacire kan adama data mutu tana ihu da fizge fizge. 6
Tsit gurin yayi sbd tsoro da firgici sbd duk mulkin sultan ba’a taba kashe mutum agaban alumma ba sai yanzu nantake kowa yaji tsoro da fargaba tareda tashin hankali na shigarsa atake kaleeb ya ‘daga takobinsa dake ‘digar jinin adama sama ta bude idanuwanta ahankali takalli jinin dake diga qasa ahankali tasauke ajiyar zuciya ta miqe tsaye. 1
Cikin wani sauti da babban sauti sarkin na’di yace,
Dogon zamani MINEELIK ASSULTANA UMMU-RUMANAH UWAR MAGAJI.
Juyawa tayi wasu irin samudawan masu bata tsaro da kuyankinta mata suka mara mata baya tashige.
Tafiya kadan tayi ta tsaya cak sbd abinda takeji ajikinta
Wani irin abu takeji kamar yana tafiya da motsi ajikinta ta dafe qirjinta da takejin yana quna.
Ammy tayi saurin nufota aka sake tareda
Rumanar ta ‘daga musu hannu daqyar alamar subarta ammyn tayi saurin qarasowa kafin tayi yunqurin ta6ata sukaga ta yanke jiki ta fadi jini na fita ta hancinta atake hankalinsu yayi masifar tashi ammy na qoqarin ‘dagota suka gansa kansu idanuwansa jajir jijiyoyin sun firfito ya durqusa ya dauketa ya nufi sashenta da ita cikin qanqanin lokaci aka zuba wasu irin tsaro tundaga qofar sashenta har zuwa qofar masarautar atake labarin halinda take ciki ya yadu nan mutane suka sake shan jinin jikinsu atake aka rufe duk wata qofar shige da fice dake mineelik aka dauko duk masu bada maganin sarauta na asalin gargajiyarsu nanda nan aka hau dubata suna qoqarin tabbatarda abinda suke tunani.
Cikin wani irin tashin hankali da damuwa yake,
Zafi sosai yakeji acikin xuciyarsu akaro na farko dayaji zuciyarsa na karaya akan abu saidai yasan mutuwace kawai zata rabasa da rumanah dan haka duk abinda zata zama ayanxu ashirye yake daya sadaukar da rayuwarsa akan cetota daga masifar dake tattare da wannan karagar.Jini ne sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani irin sauti negasi yace,
Karka kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.
Cikin wani mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan. 24
Ammy dake zaune tareda sauran ‘yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka haukaceba idan ka farka.
ASALIN MINEELIK……