GAMAYYAH
CHAPTER 12
Soyayya da cin Amana haɗi da Yaudara suka, kafa daular, asalin masifar ya fara ne, daga ranar laraba ga watan maris 1836. Mafarin rigimar daga mutane huɗune, jigogin masarautar, Musaman Sultan Jamal wanda shi ya haifar da kome…. 5
Tafiya suke a gajiye ga dare ya fara rabawa, yunwa da kishirwa ya addabesu, dan haka suka yanke hukuncin da zaran sun sami, wani guri a can gaba zasu yada zango kasancewa sun fito daga yanki sham, fatauci duk cikinsu babu wanda yake iya magana sai Jamal, sabida Allah yayoshi mutune magananne, da kuma son raha,
“Kayyasa! Ajani karda ka gaji da tafiyar dan naga kaman rakuminka ke janka ba kai kejanshi ba.”
“Wai shin Jamal baka gajiya da magane, haba tun da muka fito kaiɗai ke surutu gaskiya kacika surutu kayi mana hakuri haka dan yunwa muke ji.” inji Kojo
“Shi kenan kojo nayi shiru kuma bazan sake magana ba, amma kusan matuƙar muka ce zamu shiga Ehtophiea a wannan daren akwai damuwa mu yada zango anan gaba.”
Shirun da sukayi ya tabbatar da amincewar sauran.
Tafiya sukayi sosai har suka isa dajin kurfa, wanda yake cike da ababen tsoratarwa, ɗan tafiya kaɗan sukayi ɗayansu amari yaga wani irin Haske mai tsananin kyalli cikin duhu ya ware ido sosai yasake kallawa domin kuwa ya tabbatarda mage yake gani mai shegen hasken nan kamarna zinari cikin zaquwa da fargaba yace
“Ku dakata naga wani abu, kamar Zinari.”
“Amari nima nagani tsoron siffar abin yasani shiru gashi can kamar mage ko?” Inji Jamal, 1
Linzamin rakumarsu suka ja, suka tsaya Jamal da Amari suka sauka, daga bisa rakumansu, Ajani da Koja suna tsaye suna kallonsu, tafiya sukayi me ɗan nisa suna niman Zinarin basu ganshi ba,
Tsaki Ajani yayi wanda ya kasance shine babbansu, cikin fushi yace.
“Dalla kuzo mutafi kusan inda muke ciki wannan dajin kurfa cike yake da al’ajabi da ban tsoro matumar kuka ce zaku bi na gane gane mutuwa zamuyi ku fito muje.”
Murmushi Amari yayi cikin nutsuwa yace.
“Na rantse da abin bautana bazan bar dajin ba, Jamal idan zaka bisu ba damuwa amma ni sai naga abinda ya turewa buzu naɗi” 1
Shiru sukayi sunsan Amari da kafiya da kuma taurin rai, matukar yace zai yi abu ba makawa sai ya aikata,
Cikin laluma kojo yace.
“Shikenan zamu tayaku nima! Ai duk cigabanmu ne, Ajani kayi hakuri mu tayasu niman zinariyar.”
Tsaki Ajani yayi sannan ya koma inda suka ajiye rakumansu, suka kafa tanti karan dake wajen dajin suka tsinta, suka kunna wuta suna shan ɗumi,( bawai dan lokacin sanyi ba’a mutanen da suka kuna wuta su zauna suna hira, musaman fatake matafiy idan suka yada zango.)
Zama sukayi a gurin, sannan suka ciro guzirinsu suka fara ci, bushashiyar gasashiyar fulawa sai bushashen inabi, sai ruwa suna ci suna hira, har dare ya raba sannan kowa ya koma tantinsa.
Kasancewa dajin mugun gurine koda suka shiga sai da suka kafe ilahirin gurin dan kar wani mugun dawa ya iya shigowa ya cutar dasu.
Asalinsu wadanan, Fataken yan garin Ethiopia ne, sun kasance marayu basu da uba basu da Uwa, sai wani marikinsu wanda shima bai jima da mutuwa ba.
Ajani shine babba a cikinsu sai mai binshi Kojo, sai kuma Amari da karamunsu jamal.
Dukda kasancewarsu marayu haka bai hanasu kaunar junansu ba, dan ko ciwo ɗaya keyi duk sai sun kwanta kamar marasa lafiya, dukda haka suna da mabanbanta halaya, Ajani baida yawan magana, amna kwai saurin fusata sai amma haka bai sashi ya gaza zama mai hakuri ba,
Sai Kojo, mutune mai matukar fahimta ga daɗin zama da kowa kuma duk inda zai zauna zai matukar wuya kaji ance ana rigima dashi, sabida ya iya zama da kowa, sai Amari, masifaffe mara hakuri amma kome zaiyi akan gaskiyarshi yake, yana da matukar taurin kai, dan shi duk abinda yasaka agaba toh sai yaga bayanshi, amma mutune mai me tsage gaskiya.Sai Autansu Jamal wanda ya kasance mutum ne hakuri da juriya ga barkwace da iya zama da mutane, kuma yana da shiga rai dan duk inda ya zauna sai kasamu ana alfahari dashi, sai dai yana da abun dariya dan idan yazauna kusada kai sai ya cika maka cikinka da barkwace da raha.
Wannan kenan….
Washi gari da safe duk suka tashi, nan suka karya a gurguje suka shiga dajin, niman zinarin nan, har rana takusan faɗi basu gani ba, tsurawa dajin ido amari yayi yace.
“Jamal jiya ba’a nan muka ga kyalin zinarin mai sufar mage.” +
Gyaɗa mishi kai Jamal yayi cike da bashi kwarin gwiwa, murmushi Ajani yayi sannan yace
“Amari zan tura kojo gari ya sayo mana kayan aiki sai mun tono wannan zinarin na yarda da kai”
Cikin farin ciki Amari ya rungume Ajani yana cewa,
Yene dan uwa.
Gurin tantinsu suka dawo suka ciro kuɗi silalar akabawa Kojo, yaje ya sayo kayan aiki.
Tafiya ce ta wuni guda dan haka ya haye rakuminshi ya kutsa cikin gari, bai isa ba sai da duhu ya fara rabawa, sannan ya isa gidansu anan ya kwana washi gari ya shiga kasuwa ya sayi abinda suke bukata wanda, na kayan tono,
Yana gamawa ya aza kayan akan rakuminshi,sannan yabar garin,
Tafiyar kaman dai yanda yazone sai da dare ya fara ya isa gurinsu dan ba iyakar kayan aikin yasaya ba, har da kayan abinci yasaya musu,
Zama sukayi a gurin suka ci abinda ya kawo, sannan suka shiga hira yanda zasu tono rijiyar zinarin.
Suna gurin har dare ya farayi sannan suka shige tantinsu.
****
Washi gari suka je inda suka hango zinarin suka shiga tonoda kwashe kasa, a hankali suka ta aikin tono har dai sukayi nisan zango ga dare yayi dole suka hakura zuwa gobe.
Washi gari ma haka suka cigaba da tonon ba dare ba rana har sai da suka shafe kwanaki goma sha takwas da yini daya babu zinarin babu labarinshi karshe hakura sukayi da tono, duk suka zauna jigum, cike da bakin ciki Amari ya fashe da kuka, wanda ya kashe jikin yan uwanshi, rarrashinsa suka shiga yi, kafin yayi shiru mikewa yayi yace.
“Dole sai na isa ga, Ebo sarkin bokaye dan shine zai iya duba min abinda idanuna ya gani.” 2
Cikin son mara mishi baya suka mike take suka nufi cikin gari, dukda dare ne haka bai hanasu tafiya ba, har suka shiga garin gidansu suka nufa, suka kwana washi gari suka tashi dukkansu suka nufi gidan Ebo.
Sarkin bokayen garin, tun daga bakin kofar gidanshi suka hangoshi kwarjale, irin wanda mahajata ke raɓawa akafaɗarshi hannunshi rike da sandar tsafi, goshinsa yashafa bakin gari, inda yaja jan gari a goshinsa
“Lalle lallae da zuwan sarakunan karnin farko, barka da zuwanku, a koda yaushe k’addara kamar zare ce mai kaifi, amma shahara da ɗaukaka tana biye a bayanta ku shigo ciki.”
Jikinsune yayi sanyi, zama sukayi akan fatar zakin dake shimfiɗe, a tsakar ɗakin, shi kuma ya koma kan kujeranshi.
“Ina jinku.”
Yace musu, tunda suka ɗauko niyyar zuwa gurinshi, yaji haka ajikinshi sai dai lokacin da ya hangosu yaga tagomashin ɗaukaka wanda yake ɗauke da duhun na ban mamaki.
Cikin zakuwa Amari ya buɗe bakinshi zaice wani abu m, take bokan ya dakatar dashi ya kalli Ajani, ya masa alamun yayi magana.
Cikin nutsuwa ya faɗa mishi abinda suka gani.
D’auko wata yar jaka yayi, ya buɗe bakinta, ita wannan jakar da fatar jimina akayita, sabida ajiyar abubuwa kananu.Wasu duwatsune a ciki wanda suke cakuɗe da wuri, wasu kalamai bokan yayi sannan ya jijjiga duwatsun ya watsa, a tsorace yakalle su baki ɗaya sake ɗiba yayi ya watsa, a firgice ya mike yace.
“Shin kungatane?”
Suma atsorace suka kalli juna, sannan suka kalleshi, kaman haɗin baki suka ce.
“Wa kake nufi?” +
Komawa gurin zamanshi yayi a nutse, yace.
“Sarauniya Mineerlik?”
“Mineerlik kuma? Sarauniya kuma ai mu bamu ganta ba, kawai mage muka gani ita kuma ta zinarice.” 2
Suka faɗa mishi haka a tsorace.
“Tabbas ita kuka gani, itace tafito dan sau ɗaya take fitowa ashekara, kuma ta tafi bazaku sake ganinta ba sai wata shekara idan da rabon haka kuma ko wace shekara da kalar siffar datake fitowa amma tabbas k’addaranku ce takaiku gurin har kuka ganta.
Shiru sukayi cike da damuwa, suka shiga kallon juna Kojo shi yayi karfin halin tambayar bokan yace
“Wacece ita haka.?”
“A’a ɗan saurayi wannan duniyace ta taskar arziki, daula ce ta musaman Sarauniya Mineerlik sunanta sunan kujeranta.”
“Toh Ebo taya zamu sake ganinta? Tunda ake kaddaranmu ce ta haɗamu da ita domin kuwa wannan zinarin saimun mun mallakesa” Inji Ajani,
Gyara zama yayi cikin yarda da abinda zaice.
“Wato wannan dajin da kuke gani ba daji bane, kamar sauran da dazuzzuka, shi ɗin alkarya ce ta aljanu ko nace muku duniyar aljanu ce, shi yasa yake cike da abubuwan al’ajabi, masana tarihi sun tabbatar da cewa, babbar masarautane a gurin me ɗauke da babbar fada na sarkin aljanu Penya, shine mamallakin fadar da kuma alummarsu ta aljanu, lokacin da cutan ajali yazowa penya sai ya bar wasiya, koda ya mutum Kalsh shine shine magajinshi, alakacin matar Kalsh Sultana Neelah tana ɗauke da tsohon cikin, haihuwa ko yau ko gobe….
Bayan kwana biyu jikin mai martaba penya yayi tsamari, haka duk wasu likitotin gargaji suna fama dashi, tashin hankali yayiwa Kalsh yawa domin a lokacin aka sanar mishi, Sultana Neelah tana, kan gwiwa,
Hankalinshi yayi matukar tashi, ana cikin haka Sarki Penya ya mutu, hankalin Kalsh yayi matukar tashi ga rashin Uba ga matar a wani hali gabi ɗaya sai ya shiga kiɗima, ana hidima kai mahaifinshi amna shi ya koma kofar ɗakin karɓan haihuwa, ya zauna.
Sai da Neelah tashafe kwana biyar sannan ta sami nasaran haihuwar Y’arta mace, mai tsananin kyau wacce tunda ake haihuwa azuri’ar ba’a taɓa samun y’a kamar yarinyar ba, sai dai abin takaici kwanar Sultana Neelah ta mutu sakamakon ciwon cikin haihuwa, gashi a ranar aka bawa Kalsh mulkin garin, ga murna ga bakinciki, fito mishi da Yarinyar jakadiya tayi ta zube a kasa cikin kuka tace.
“Sultan ga yarinyar nan, ta rasa uwarta a daren jiya.”
Idanunshi cike da zubda kwalla ya karɓi Yarinyar ya ɗagata ga Alummarshi yace.
“Sultan Kalshe Penya, Nasamu Y’a mace naka mata Suna Mineerlik, haka kuma kujeran mulkina shima sunansa kenan Mineerlik, da fatan ku sanya mata albarka.”
Cikin maɗaukakkiyar murya alummar aljanu sukace mun ji mun amince da abinda kace munawa Sultana Mineerlik, Barka da zuwa da kuma albarka ya cika rayuwarta.”
Juyawa Sultan kalsh yayi rike da jaririyar, zuwa cikin gida ya isa har ɗakin da gawar Sultana Neelah, yana shiga ya zuɓa gwiwarshi cike da zubda kwallah yace.Neelah kin ɗaukar min alkawari baki cika ba, Ina soyayyar da kika fada min zamu shimfiɗa ina kaunar da kika min alkawarin zamu nunawa abin ciknki Neelah ya zaki tafi kibarni da ɗawainiyarta, Ina soyayyar da kika min alkawari min, abar kaunata kin tafi kin barni da kewarki da soyayyarki wanda yake tankar gubace a gareni.” +
Kuka yake cike da damuwa da ɗimauta, ruwan kwallar dake zuba daga idanunshi yana sauka akan fuskar mineerlik, a hankali ta buɗe idanunta tana kallon mahaifinta, sai ta rufe, sabida ɗigar kwalla, jakadiya ce tazo amshi Sultana Mineerlik a hannunshi wacce take motsi da kuka kasa kasa, na alamun yunwa, dan har tasaka hannunta abakinta….A gaggauce.
Mineelik nada kwarjini da wani irin haske na tsananin kyawu Wanda yasaka Sam babu mai ganinta daga mahaifinta sai mai kulada ita shiyasa bakowane yasantaba musamman daya zamto itace kujerar mulkin mineelik ayanda abin yake mahaifinta yariga yayi amfani da wani irin sihiri akan karagar da sunan mineelik yanda ko bayan mutuwarsa babu Wanda zai iya raba mineelik da karagarta kuma barinta a nahiyar na nufin mutuwar duk Wanda ke nahiyar kuma babu Wanda yasan da hakan sai ita mineelik din da mahaifinta sbd ganin bai haifi namiji ba yasa aka fara farautar karagar mulkin.
Mineelik na zama cikakkiyar budurwa qannan mahaifinta su hudu suka hada kai suka kashe mahaifinta mutuwar wulaqanci sbd wani irin zalamar son hayewa karagar saidai bayan kashesa suka kashe junansu agurin sbd kowa nason shine zai hau.
Lokacinda mahaifin mineelik zai mutu saida ya shafawa karagar jininsa dake zuba na suka hudu dasukai masa cikin tsananin azaba da taurin zuciya tareda fushi mai tsanani ya daf karagar yace,
Ni penya maqagin wannan karagar ayau jinina ya zuba sbd wannan dazata zamewa duk wani makusanci agareta masifa ayau ina mata baki mai hadeda tsinuwa duk Wanda zai hauta tazamo ajali mai masifa agaresa matuqar ba MINEELIK-ASSULTANAH bace take kanta har ranar dazata na’da wani akai da kanta sbd jinina da aka zubar akanta daga wannan qarni nawa ta haramta ga dukkanin qarni masu zuwa. 2
Lokacinda mineelik ta fito bayan mutuwar mahaifinta aranar duk Wanda ke bousk yaganta sukaga zallar kyawun halittar dabasu taba ganiba saidai cikin rashin sa’a fitowarta tasaka rayuka da dama mutuwa dan kuwa wani irin haskene da maganadisu atareda ita dake jan mutane zuwa gareta Wanda wannan abin shine atareda karagar mai janyo mutane da rufewar zuci da ido akan hawanta.
Ranarda mineelik tahau karagarta amatsayin assultana aranar akayi wani irin tashin daya faru aranar shine koda gari ya waye duk Wanda ke nahiyar babusa.
Tashin hankali data shiga shine tabarwa datayi alamun mulkintane bazaiyi kyawuba sbd karagar tayiwa jininta qarfi kasancewarta mace.
Ita kadai tayi rayuwa mai tsayi,shekaru masu tsayi batareda kowaba,
Kadaici,qunci,baqin ciki da kewa sune abokanan rayuwarta sai karagar wadda ahankali take zuqe mata tausayinta sbd babu wani Wanda za’a yankewa hukunci a zubarda jininsa shiyasa abin yake cinta itakadai makari ‘dayane mahaifinta yasanarda ita na wannan karaga shine soyayya mafi qarfi amma idan idan sadaukarwar abu mafi soyuwa tashigo.
Sanin kaf acikin duniyarta babu Wanda zai iya ko ‘dago kai yakalleta sbd kwarjininta bare ya iya samun soyayyarta saidai ta tabbatarda wannan azarbabin da gaggawar tareda rashin tsoro da kwadayin sai bil adama.
Wannan shine burin
Hakan yasa ta rufe daularta babu wanda yake ganinta sai ita tafara fitowa duniyar bil adama domin kuwa babu abinda take buqata da tsananin buri kamar soyayyar da babu irinta a qarnin.
Aduk shekara da kalar suffan datake fitowa saidai bata taba dacewaba amma alqawarine bazata daina neman soyayyaba harsai ta mutu.Shiru sukayi dukkansu kowanne najin zuciyarsa a bushe babu wani tsoro ko fargaba sbd dama nema suka fita duniya dan haka su sunga zinari kuma bazasu danganaba harsaisun mallaki wannan karaga Ajani ne ya gyara zama yayi gyaran murya yace, +
“Toh shi zinarin yana tare da ita kenan?
Gyara zama aqoob yayi cikin muryan da ta manyanta da tabbarda abinda zai fada yace,
“Ita da kanta itace zinarin sbd itace kujerar mulkinta,sunanta sunan karagarta daularta itace arziki da kowa ke fatar samu saidai hadarin dayayi Katanga wa arzikin shine soyayyarta wadda itakaice mukulli ga wannan taskar arzikin.
Kallon kallo suka shiga yiwa junansu saidai babu Wanda alamar tsoro ko fargaba yake ataredashi Jamal ya kalli cikin idon aqoob yace,
Shirye muke da mallakar wannan dukiyar kota halin yaya koda soyayyar tatace mun shirya nema.
Murmushi bokan yayi yana jinjina qarfin zuciya da buried tareda rudu irin nasu sannan yace,
“D’ayanku zai faɗa soyayya da ita amma kafin nan sai kunyi jiran shekara ɗaya, wanda haka zai kasance kamar ganganci da wasa da rayuwarkune sbd hadarin dajin dakuma tsawon lokacin dakuma mataki uku masu matuqar hadari,
idan kuka tsallake mataki uku da zai faru kafin bayyanarta toh tabbas soyayyar ɗayanku zai kulu da ita, sai dai ba soyayyar bace mai muhimmanci dukiyarce mai mahimmanci domin sonda zai gwada mata shi zai sanyanta buɗe mishi alkaryanta da taskar mineelik.
Kallon juna suka sakeyi kowannensu idanuwansa acikeda rashin tsoro ajani yace,
“Toh boka matakai uku da zamu bi dan samun kusanci da ita menene fa’idar haka.”?
Mikewa bokan yayi tsaye, ya shiga zagayesu har ya tsaya a tsakiyarsu murmushi yayi yace,
Zakusansu da sharadin taskar arzikin tamuce muduka.
Kallonsa sukayi cike da mamaki da jinjina kwadayinsa saidai zasu iya yin komai da mallakar taskar kojo ya kallesa yace,
“Mun amince, zamu raba da kai.
Dariyar jin dadi yayi yace,
Tareda yarana biyu za’ayi wannan tafiyar tareda rubuta sheda a faifan fatar raqumi da jinin dukkaninmu za’ai rubutun kowa zaibada nashi arubuta a ajiye tarihi ya shaida wannan taskar arzikin mineelik tamuce mu duka.
Babu musu kowanne yafitarda ‘yar qaramar wuqarsa dake some a qafafunsu suka ‘diga jininsu a ‘yar qwarya akai rubutun atake ya ratayesa a bangon dakin.
Yaransa biyu suka shigo yonas da haji yakallesu yace,
Gasunan kuma tabbas akwai haske mai disashe duhu akwai duhu mai disashe haske.
Dayake zuciyoyinsu a shirye suke sun kafe kwaɗayi da son zuciya ya rufe musu ido ba tare da wani bata lokaciba suka amince Jamal dake gyara zaman wuqaqensa dake shanye da dafi kala dabam dabam na macijai da kunamu harma da dafin kada yace,
Tunda nine zan fara aikin kwada soyayyata dole kasona yazamo mafi nauyi a raqumi.
“Jamal kasonka shine mafi nauyi a raqumi sbd kaine zaka bamu gudunmawa mafi girma a cikin tafiyar,
abinda zai faru idan kuka isa dajin domin jiranta akwai tsoratarwa daga muyagun aljanu da dabbobi masu firgitarwa da suke yawo cikin dajin, 2
matakin farko zai farane daga kwanaki uku kafin bayyanarta zaku kasance kamar makiyan juna a ranar farko,
Zakiji tsana da qarfin son kashe juna mai qarfi na shigarku saidai karku bari hakan yaci qarfinku sbd dayafi qarfinku zaku kashe junanku cikin rashin imani.
rana na biyu kuwa bazaku ga giftawar tsuntsaye ko wata dabba ko dayaba ko wni iri har kukan namun dajin bazaku ji ba.
a rana na uku da zata bayyana wani mugun zafi da kishirwa zai buwayeku kamar zaku mutu, domin zaku ji har cikin jikinku zai koma kamar babu ruwa da jini a ciki, zuwa yamma ko dare zata bayyana, kai Jamal aikinkane kutsa kai cikin dajin domin haɗuwa da ita duk rintsi duk tsanani babu waiwaya.
Shiru sukayi cike da al’ajabi suke kallon kallo sabida jin abinda zai faru dasu wanda suke gani kamar faɗar bokane,
Kallon bokan jamal yayi cikin nutsuwa yace.
“Wannan indai shine sharuɗan mun amince.
Murmushi boka yayi sannan yace,
Tafiyace mai zuwa babu tabbacin dawowa abin bautarku ya kubutar daku.
“Toh ni dai har yanzun abinda nakeson ji shine me zamu mata musamu dauko dukiyar mu mallaketa” Inji Amari.
Kallon Jamal bokan yayi cikin murmushi ba shi yayi tambayar ba amma ya maida idanunshi kan jamal,
ɗaukar duwatsunshi yayi ya watsa har lokacin idanunshi nakan jamal, juyawa yayi yace,
“Lokacine zai nuna mana abinda zai faru ynz zan baku wasu madaurin dantse ku ɗaura gudun karku cutar da kanku.
“Wannan zai kareku daga cutar da juna, sannan babu wani abinda zai cutarku nagama daku sai ranar da yasamu nasaran isa birnin Sarauniya mineelik, zamu karasa aikinmu nakarshe.”
Mikewa sukayi baki ɗaya suka fita koda suka isa bakin kofa, kallon jamal yayi cike da tausayi, sannan yace.
“Duk bayan lokaci mai dan tsayi ina son Babbanku yazo ya faɗa min cigaban da kuke samu.”
Kallon ‘yayansa yayi ya jinjina kai cikin muryar jarumta da bankwana yace,
Abin bauta yasa musake haduwa.
Haka sukayi bankwana dashi suka tafi.
****
Tunda suka tafi, kaman yanda bokan ya faɗa musu haka ya faru, sabida sun ɗaura ɗanbar wani kudiri a ransu, ranar farko, suna kwance sai suka fara jin shashekar kuka, kamar na yaro kaman na babba haka aka cigaba da razanasu da wani irin mahaukacin kuka, kafin aka samusu dariya irin na bantsoron nan, can da dare yayi tsakiya, sai kana kwance a cikn tantinka za’a zo ana kiranka daga kan ajani aka fara,yana kwance ya dunkukune a marufinshi yaji an tsaya abakin tantinsa ana cewa.
“Ajaniiiiiiiiiii”
D’auke numfashinsa yayi cak, tsabar tsoron, haka aka kewayasu ana razanasu. +
Wasa wasa sai da suka kwashi fiyye da wata biyar ana tsoratasu da abubuwa a gurin tuni suka saba da rayuwa adajin sbd dama dukkaninsu sunsaba da rayuwa a daji dan haka yanzu gida suka dauki dajin sbd burinsu abune dazasu iya komai akansa.
lokacin da suka cika wata shida Ajani yaje ya faɗawa boka abinda ya faru, nan ya zauna ya faɗa mishi abinda zasuwa Mineelik dazaran ta faɗa soyayya da Jamal. Bokan ya cigaba da cewa,
” Matuƙar mukace muna son dukiyar baxata bamu cikin lumana ba. Karshe rabaku xatayi da ɗan uwanku amma idan mukayi haka toh babu wata damuwa sannan zan nema muku abubuwan da zakuyi amfani dashi, karka bari ɗan uwanka yaji labarin dan matukar yaji bazai yarda yayi aikin ba.”
Gyaɗa kai ajani yayi sannan yabar garin ya koma dajin, nan suka cigaba da zama ga tsoratasu da ake ga kwanakin kamar baya tafiya, duk sun kaqu da faruwan haka,
Da zaran sun zauna hiransu kenan, akan yanda zasu juya dukiyarsu da suka samu, daga gareta, a hankali lokacin yana tafiya wasa wasa sai gashi har saura kwanaki bakwai zata bayyana,
……
Bayan kwana huɗu wata rana da safe suka tashi da mugun faɗa kaman zasu kashe junarsu, kaman dai yanda bokan ya faɗa musu, karshe rabuwa dasu Jamal yayi ya koma gefe dan ya hassaso wannan rigimar yana cikin alamomin bayyanarta nan yatunatar dasu nan kowa yayi nesa da ‘dan uwansa suna fidda wani irin gumi najin wani irin qarfi mai razanarwa na son kashe dan uwansa.
rana tabiyu kuwa sun tashi da babu giftawar tsuntsaye ko ɗaya tareda wani irin tsoro mai firgitarwa dayake shigarsu wanda suka tabbarda natane amma haka suka dinga daurewa cikin wata irin jarumta.
Rana mafi tashin hankali shine ranar bayyanarta tsananin zafin da ake yaja sukaita fad’uwa, gashi sun shanye ruwansu, dakyar Jamal ya mike yace.
“Yaku Y’an uwana wannan itace rana mafi hadari ageremu saidai ina fatar mana samun nasara.”
Daqyar su kojo suka rarrafo gurinsa suka rungume juna cikeda tsoron rabuwa da juna saidai burinsu ya zarce komai.
Daqyar suka rabu da juna yana rangaji yana faduwa yana tashi sbd yunwa,zafi da qishirwa dake neman lahantasu ya nausa dajin inda ranar suka fara ganinta baisan inama yake jefa qafafunsa ba sbd azabar dayake ji cikin hanjinsa da cikinsa.
Duhun dare nayi yana isa gurin saidai ba’a cikin hayyacinsa ba sbd tuni yafara ficewa hayyacinsa atake ya yanke jiki gurin yafadi yana fitarda numfashi daqyar.
Ahankali kunnuwansa suka fara jiyo amo da sautin sarqar zinarin qafarta sanye take cikin kaya ruwan makuba fuskarta na fitarda wani irin annuri duk da cikin duhune atake yaji wani sanyi na yaye masa yunwa da wahalarsa suna barinsa ahankali.
Cikin wani irin takun nutsuwa da wata irin haiba ta nufo hanyar taku kadan tayi ta tsaya cak tareda lumshe fararen kyawawan idanuwanta.
A hankali ta juyar da kanta tahangosa kwance ba alamar yana numfashi.
A hankali takalli jikinta ahankali ta rikide ta sauya zuwa wata kyakkyawar bafulatar baqar Ethiopia sarqoqin jikinta na zinari suka koma duwatsun dandaye masu qaramin kyau ta nufosa numfashinta na wani irin sarqewa sbd wannan shine karo na farko data taba ganin wani biladama wadda take tabbarda shine Wanda ta dibi shekaru da qarnika tana jira.
A hankali ta durqusa gabansa tareda daga daga dogon hannunta ta ta6a goshinsa atake ya bude idanuwansa yana kallon fuskarta bai san lokacin da ya sume ba,
ruwan dake cikin goranta ta fulanin daji ta ɗauka ta watsa mishi, a hankali ya buɗe idanunshi sai akan fuskarta.
Cikin idanunta ya kalla kamar wanda aka ɗiga mishi ruwan gold, lumshe idanunshi yayi.
“Sannun ko” tace mishi…
Wani irin sauti yaji daga muryarta wanda yakusan sake sumar dashi yayi wani irin jarumtar daidaita numfashinsa da nutsuwarsa yayi kalar wanda ke cikin tsananin wuya ya daga mata kai daqyar alamar amsawa yana jan numfashin qarya daqyar.
Kasa wata maganar tayi tasauke kai tana kallon qafafunsa dake cikin takarmin fatar damisa.
Sunkuyar da kanshi yayi ahankali kwalla na zuba daga idanunshi cikin muryar tsananin damuwa da baqin ciki rayuwa yace.
“Me yasa kika taimakeni?
me yasa baki barni na mutu ba? na gaji da rayuwar duniya gwara na mutu nabar duniyar nan.”
Kallonsa tayi cikin sauri da nutsuwa da laushin murya tace,
“Koma Ya-yane dai rayuwarka tana da amfani,
ka daina cire tsamani da rayuwa, dan ko badaɗe ko bajima zaka amfani rayuwarka tana da amfani.”
Kuka ya fashe da shi yans kwaɗa kanshi da bishiya yana cewa,
“Kaicon rayuwa dan ina maraya shine bazanyi rayuwa kamar kowa, gwara mutuwata.”
Duk ya jiwa kanshi ciwo,
tausayinshine da mamakin bil adamane ya kamata musamman ace yaganta mace cikin wannan dajin da tsakar dare amma bai nuna shakku ko tsoro da fargaba ba kodai yasan da fitowartane?
Satar kallonta yayi yaga alamar tunani da nazarinsa takeyi yasan dole yayi dubarar hanata zarginsa hadiye wani mugun yawu tareda zabura gefe jikinsa na wani irin mazari ya nunata da hannunsa dake mugun rawa a tsorace da rawar murya yace,
Ke…keee…ke wacece?
Me…mee kikeyi anan ke daya?
Kallonsa tayi ahankali cikin nutsuwa ganin yanda yarude yake neman zaucewa atake tasaki numfashi mai Sanyi tasaki murmushin daya sakasa zubewa kan gwiwoyinsa.
cikin sanyi murya tace.
“Nima marainiyace kiwo yakawoni kusadanan 6atan hanya yasakani shigowa nan hanyata nake nema amma nakasa ganewa.
Cikin dubara yayi baya alamar tsoro ya buga kansa da bishiya sosai nan take yafadi Jini na fita goshinsa.
Hannu ta daga ahankali zata shafa ciwon danya warke ta dakata sbd karya sake tsorata idan ya farko.
Tashi tayi ta fara niman ganyayyaki tashiga haɗa mishi magani, tasaka mishi a ciwon,
Sun ɗauki kwanaki biyu a gurin tana kula dashi, tun ranar da duka haɗu sukayi magana bata ce mishi kome ba, tsakaninta dashi ido duk abinda majinyaci ke bukata take mishi. Zaman kuramen da suke ba karamin, haifar musu da wani shakuwa yayi ba, dan zata zauna a fakaice tana kallonshi, ko shi yayita kallonta, da zaran sun kama juna take kowanensu zai shiga kame kame, ba yanayin da suke yana tafiya da wani irin tsari na musaman,
Jakarsa ta kaya ya bude ya buga tantin rumfarsa itace take kwana aciki shikuma yana kwanciya da wajen.
. . A hankali suke iya faɗawa junansu magana ko kuma hira sama sama, a wata safiya ya tashi ya zauna dake ciwon jikinshi ya warke yace mata.
“Zan koma cikin gari, amma baki faɗa min sunanki ba, ni dai sunana Jamal ni maraya ne, zanje sake komawa gurin dangin iyayena dana gujewa.
Kura mishi ido tayi cikin nutsuwa tace,
“Nima marainiya ce bani da kowa,sai kai da na haɗu da kai gashi zaka tafi kabarni Sunana Mineelik.”
Wani irin bugawa qirjinsa yayi sbd ambatar sunan kawai musamman duka kwanakin yayisu ne babu ko kyaftawar ido bare bacci sbd yasan rayuwarsa na tsakanin mutuwa da rayuwane idan yabari yayi kuskure dan qanqani taganosa.
Cikin tausayawa yace.
Bakyason nabarki cikin dajin nan ne na zauna?
“Zanyi fatar haka idan ta kasance amma bazan maka dole ba.” tace mishi.
Shiru sukayi, suka cigaba da satar kallon juna, a hankali shakuwar da sukewa juna ta sake samun matsaya na musaman ma inda ta rikiɗe ta koma soyayya mai matukar ɗaukar hankali tare suke farautar abinda zasu ci, idan zatayi wani abu zama yake ya kareta, gabaki ɗaya jamal ya sadaukar da lokacinsa sabida ita,, musaman suke zama suyita hira da zaran yaga ta fara alamun jin barci zai barta ta shiga ta kwanta yana gadinta. +
Tausayinsa ne mai tsanani yashiga rayuwarta sbd kaf baida abinda yake sai kulada ita tamkar sarauniya duk da baisan wacece itaba tabbas zata taimaki rayuwarsa kodan soyayyarsa data ginu a zuciyarta.Shiru tayi tana kallonshi cikin nutsuwa, ta rasa ta inda zata fara taimakonshi satar kallonta yayi cikin nutsuwa, sannan ya sauke numfashi yace.
Rayuwarsu a dajin wani irin rayuwa ce, mai ɗauke da soyayya da wani irin kulawa ba daga itaba har zuwa ita kanta. Mafi lokuta takan zauna tayita tunani anya ba wani kuskure bane yake shirin afkuwa na amincewa bil’adam, sai wani ɓangare na zuciyarta ya tuno mata tarin alkhairin da Jamal yake mata, +
Wani lokaci suna zaune ta kalleshi, a nutse kafin tace,
“Menene silar barowarka daga gida ka shigo wannan dajin har kake tunanin kashe kanka da rayuwarka.”
Kirjinshine ya bada wani irin sauti, kura mata ido yayi yana qoqarin qin barinta gano yanayin daya shiga cikin daidaita nutsuwa sai ya sunkuyar da kanshi cikin nuna baqin ciki yace,
Idan kika san abinda ya baroni da dangina sai kema kin gujeni, labarina ba labari bane sbd cike yake da bakin ciki.
Dafe goshinshi yayi yana dauke kai yana girgizawa cikin damuwa mai tsanani sannan ya cigaba da cewa,
“Idan kika san koni waye guduna zakiyi gwara mubar maganar haka dan babu alkhairi a ciki.
Wani irin qayataccen murmushi tasaki cikin qasaitar mulkinta dabatamasan tayiba tace,
Kayi min halacci zama tareda ni kana kula dani tamkar nauyina yana rataye akanka dan haka bazan gujekaba fadamin.
Girgiza kai ya cigaba dayi yana cewa,
Karki so jin waye ni, karki so jin waye ni, labarina cike yake da kayan haushi da bakin ciki.
“Ko baka yarda dani bane, dan idan ka yarda dani ai babu abin bakin ciki a jin kai waye saima karin amintaka a cikin zamanmu.
Gyara zama yayi zuciyarsa cike fal da farin ciki dan abinda zai fada mata shine matakin nasararsu.
“Kamar yanda na faɗa miki ni marayane bani da uwa bani da uba, amma akwai kawunaina, kasancewar iyayena sun mutu basu bar min ko ‘dayaba koda kuwa kaza ce yasa na zama abin tsangwama a cikin mutane, sannu a hankali na fara niman nawa na kaina sai dai…
Kura mata ido yayi cike da jin ba daɗi da kuma hango yarda da Amana da tabashi sai ji yayi akaron farko bazai iya cika wani mugun kudiri a kanta ba, sunkuyar da kanshi yayi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki wanda bawai dan maganar da yake mata bane sai dan akaro na farko da zuciyarsa ta hango masa kuskure da suke shirin tafkawa ne Wanda zai iya bibiyarsu har jikokin jikokinsu na qarni mai zuwa. 1
Cikin nutsuwa tasake kiran sunansa tace,
Karka damu nimai riqe sirrinkace.
“A’a mineelik ina tsoron karki guje nine.
“Ina tare da kai nace ka yarda dani.
Gyaɗa kanshi yayi sannan yace,
“Nayi kokarin neman nakaina amma abu yaci tura daga nan kome na taɓa sai ya lalace kai ko kayan mutane na taɓa ya tashi aiki sbd baqin Jini da baqin qashin tsiya da’ake cewa inadashi daga nan mutane suka shiga jifana da mai kashin tsiya bani da albarka a rayuwa haka bai isheni ba sai na faɗa niman aure nanma mutane suka shiga korata a kofar gidajensu suna goranta min ynx waye zai yarda ya bani auren ɗiyar shi yanda tsiya da fatara ya kewaye rayuwata,
Qarshe ko qofar gidajen mutane sunhanani bi idan nabi qofar gidan mutum aranar saiya rafka babbar hasara tou tsangwama da qyama yasa nabar garin nashigo duniya shi yasa na shigo dajin nan sbd jin labarin ha’darinsa naso koma meyene aciki ya kasheni.
Abin tausayi abin dariya yar karamar dariya tayi wanda ya bayyanar da jerun kyawawan hakoranta farare.Ganin irin kallon da yake mata yasa ta ɗan rufe bakinta cike da qaunarsa mai qarfi dake zuciyarta tace, +
“Tabbas akwai abin dariya a rayuwar bil adama sbd kamar munfisu yarda da qaddarowar Allah ne.
Kallonta yayi da sauri cikin rawar murya yace,
Mekike nufi da bil adam ke kincire kankine daga bil adaman?
Kallonsa tayi cikin takaicin zancen datayi ta girgiza kai cikin son gyara zancen tace,
Dukanmu bil adama ne saidai wasunmu kamar basuda daukar qaddara sbd banga abin gudu da qyama ananba.
“Hmm kece kike ganin haka amma abin ba haka bane, aiku mata baku ɗauki kome da muhimmanci ba, tunda ba damunku abin yayi ba.
Girgiza kai tayi ni na amince zan aureka a duk yanda kake sile ‘daya sun wadaci sadakin auren.
Mikewa yayi a razane tare da tsorata sbd baitaba kawo wata maganar aure atsakaniba yace,
Banda komai dazan inganta rayuwarki na kare martabarki amtsayin mijinki dan haka bazan iya lalata miki rayuwa ba.
Jikintane yayi matukar sanyi har tana dana sanin fada masa hakan sbd har cikin ranta takejin damuwarsa sbd tausayinsa mai qarfi da yayi wasi zuciyarta kamu tareda soyayyarsa mai qarfin gaske dan haka zata inganta masa rayuwa,
Zata basa kaf arzikinta saidai zata daukesa sunkoma duniyarta rayuwa acan zaifi musu dadi.
Ahankali ya furta idan har kin amince da aurena a yanda nake dinnan tabbas zan sadaukar da rayuwata gurin nema dan inganta miki rayuwa.
Yarda dashi yasa take kwanciya tayi baccinta batareda sakin dukkanin jintaba shikuma yana ganin tayi nisa a bacci yasaci jiki ya nausa yamma da saurinsa da gudunsa sai tsakiyar dare sosai ya isa inda su Ajani suke tun daga nesa yake musu kukan wata tsuntsuwa dansu gane shine tafe dan karsu harbo masa hari daga nesan.
suna jiyosa cikin bacci duk suka mike
Suka fito rumfarsu yana isowa gabansu ya zube a wahalce yana fitarda numfashi tareda sakin ajiyar zuciya. +
Amarine ya rungume shi cike da kewar kanin nashi yace,
“Da fatan anyi nasara?
Murmushi yayi ya nemi guri ya zauna, sannan yace,
Nasara tazo ne tareda matsala sbd tace na aureta.
Nan ya faɗa musu komai.
Shiru sukayi kafin Haji yace,
Toh ba zaiyu bane mu karɓi dukiyar da karfin cin tuwo basaika auretaba.
Wani mugun kallo amari yasakar masa zaiyi magana yonas dan boka yace,
Meya hana kai kaje gurinta sauka karbo da qarfin cin zaki bama na tuwo ba.
Zaburowa haji yayi tareda fisgo takobinsa mai tsananin kaifi ya nufi wuyan yonas Jamal yayi saurin tarewa yace,
Ba yanzu zakuyi wannan ba kubari mukarba daga baya kun kashe kanku,kafin ya kalli haji din cikin ido da Wani irin kallon banza dayayi masa cikin rashin jin daɗi abinda yace,
Lallai kusani koda barazana bazan karɓi dukiyarta ba sai da amincewarta.
Arazane suka hau kallon juna cikin wani irin mamaki da tabbarwa da maganar da boka yafada musu bayan tafiyar Jamal din da dayansu yaje.
ganin irin kallon da sukewa juna yasa shi shan jinin jikinshi sbd kuwa ya tabbatarda akwai wani abu dasuke boyewa.
Kuna qoqarin boye min wani abune akan mineelik?
Babu Wanda ya basa amsa sai kojo dayace masa,
Ko ‘daya kashirya gobe zamuzo amatsayin nemanka muke daga nan zamu daura auren muyi abinda yakawo mu muje wata harkar sbd idan muka tsaya sanya zamu qarasa rayuwarmu ne a wannan dajin.
Juyawa yayi zuciyarshi bata aminta dasu ba ya fice yana tunane tunanen abinda suke boye masa dan kuwa yasan tabbas akwai abinda suke boyewa.
Bayan tafiyarshi Kojo ya kalli Ajani cikin bushewar zuciya da takaici yace,
Aqoob yayi gaskiya na cewar Jamal zai iya fara sonta na hango damuwa a cikin idanunshi ba jarumta ba kuma da zaran yasan da kudirinmu akan mataqin qarshe na mallakar dukiyar toh ba zai taɓa yarda damu ba kuma komai zai lalace.
Shiru sukayi dukkansu sbd bazasu taba bari banzar soyayyarsu ta kaisu ga rasa abinda suka sadaukar da rayuwarsu gurin nemaba.
Koda ya isa asuba tayi har haske ya’dan fara yayi saurin kwantawa yana wasi wasi akan mineelik da abinda suke boye masa,
hango wautarshi yayi da ya amince da bukatar ya yaudareta sbd yadaura ko a tsakaninsa da bil adama yar uwarsa ne haqqi baya barinka bare sarauniyar aljanu mafi hadari ko acikin sarakunan.
yana gurin har gari ya waye kafin tafito ya shiga daji nima musu abinda zasu ci.Koda ya dawo taga rashin walwala akan fuskarshi tambayarshi tayi ko akwai wani matsala yace, +
Babu kai tsaye yana juya mata baya sbd bayason kallon fuskarta yanzu jin yake zuciyarsa na karyewa da abinda suke shirin yi yanajin kamar bazai iyaba.
Shiru tayi ta cigaba da zama tana satar kallonshi da zaran sun haɗa idanu zata ɗauke kai tana murmushi haka shima yake qaqalo murmushin qarfin halin.
Kusan ita tayita janshi da hira, har ya sake da ita suka cigaba da hidimarsu can suna zaune sai suka jiyo sautin muryan mutane na doso inda suke mikewa tayi ta koma bayanshi tana leka inda take jin muryan mutanen.
Shikuwa dayasan da zuwansu bai wani nuna damuwaba saidai fargaba da wasi wasin abinda sukazo ayi wato auren.
Tabbas yanajin wani irin tsoro, fargaba shakku da wasi wasin aikatawa.
Cikin nutsuwa suka tunada gargadin boka aqoob dayace saisunyi matuqar taka tsantsan karta zargi wani abu ko taganosu dan kuwa rayukansu zasu rasa dukkansu idan aka samu matsala shiyasa
Su ajani ne suka iso har inda suke ja yayi da baya a tsorace su kuwa suka diro raqumansu da wani irin tsuma da far in ciki jikin na rawa suka qaraso gabansa cikin babbar murya kojo yace,
Jamal kasan abinda kayi da halinda kasamu ciki daka gudu aka rasaka?
Fiyeda kwana hudu muna yawo cikin dajin nan nemanka bayan mun share satittika muna yawon qauyuka nemanka mekakeyi wannan hadararen dajin….?
Kuka ajani ya saka cike da bakin ciki yace,
“Yau da ɗan uwanmu na raye ai kafi karfin wulakacin badan haji yace mu shigo ta daji ko kazo ka rataye kanka ba,
Gidanmu ya qone qurmus bayan barowarka shiyasa muka tabbatarda zamanka a gidanma kuma wata rahamace kayi hakuri mu koma musan yanda zamu dora itace muyi wani gidan bazamu sake bari a wulaqantakaba zamu samo maka mata mu daura maka auren dakakeso.
“Babu inda zani dan ni na sami wacce zata aureni da zuciya ɗaya bata damu da dukiya ko arziki ba.
Cikin Sauri da ‘doki yonas yace,
Zamu aura maka ita yanzu dai kazo muje gida idan munje a daura maka ita acan tunda yanzu idan anyi bakada gurin sakata.
Shiru yayi alamar nazarin zancen kamar gaske.
Ita kuma cikin nutsuwa takallesa ganin yashiga tunani ta dafashi ahankali ya matsa mineelik ta bayyana daga bayanshi.
A tsorace sukayi baya zuciyoyinsu na rawa saidai jaruman gaske ne bazasu bari kyawunta da kwarjininta ya rikitasu ba.
Cikin sauri kojo yace wannan ba irin matarka bace bazata zauna dakaiba idan taga talauci zai illatata.
“Na rantse da abin bauta bazan barta ba ina sonta kuma zan aureta idan kuka ce bazaku barin na aureta ba zan kashe kaina na huta.
Cikin fusata Amari yace.
“Ka daɗe baka mutu ba wannan matar tafi karfinka ka nemi wata mana kokuma mu munema maka wata.
Ahankali ta matso kwarjininta da wata irin haiba dake fitowa daga gareta na girgiza zukatansu saidai buri da kwadayinsu yasa suke kannewa cikin jarumtarsu cikin wata irin murya mai dadi tace, 1
Ku auramin shi nikuma na muku alqawarin taskar arzikinda dar qarnin qarshe zuriarku bazatai talauciba,
Ina sonsa zan auresa ahaka kuma nayi alqawarin ko bayan mutuwa zan qaunace bazan barsaba wannan alqawarine daga sarauniya datafi kowace sarauniya mulki,
wannan son dayake min yafi min kome a duniya.
Wani irin kallo sukayiwa junansu cikin gamsuwa da burinsu yazo a sauqin dabasu taba tsammaniba.
Kojo ne ya matso gabanta suna fuskantar juna cikin rashin tsoro yace,
Mun amince zamu daura muku aure a yanxu basai anje koina ba saidai bawai dan kinada arzikin dazaki bamuba dan da alama kema nema kikeyi.Murmushi tasaki ahankali tareda kallonsa takalli sauran dakuma raqumansu tace. +
Idan sarauniya tayi alqawari bata canxawa,
Alqawarinta kamar rubutu ne akan dutse har abada baya canxawa.
Murmushi yonas yayi tareda kallonta cikin ido yace,
Mukuma alqawarinmu idan muka dauki burin abu kamar rubutu ne ajikin dutse baya goguwa sai muncimmasa.
Murmushi tayi tace,
Buri da alqawari basa haduwa sbd ‘daya saiya danne ‘daya yake tabbatuwa amma Ku sani zaku tuna hakan wata rana.
Kallonta sukayi a ‘dage kafin amari ya kalli Jamal daya qura musu ido cikeda tunani kala kala aransa game dasu yace,
Yanxu za’a daura aurenka da sarauniyar ranka saidai kasani soyayya gubace mai kaifin gaske kafadawa ‘yaya da jikokinka wannan.
Shigewa tayi tantinsu tana jin wani irin yanayi na farin cikinda bata taba jinsaba sbd tana yiwa Jamal wata irin soyayya da qauna mai qarfi dazata iya sadaukar da komai kansa ciki harda rayuwarta.
Atake suka rabu biyu suka wakilci ango da amarya aka daura auren da sadakin sile ‘daya.
Bayan daura auren ne sukace zasu tafi su dawo sbd boka aqoob dayace idan andaura suzo yabasu matakin qarshe.
Bayan tafiyarsu da daddare yana zaune ya kafawa wutar daya kunna ido shikadai gabaki daya zuciyarsa cikin wata irin dana sani da qunci take sbd abinda yakeji gameda mineelik bazai iya cutatar da itaba saidai kuma bazai iya fada mata komaiba ko yayi gangancin bari tagane sbd rayuwar ‘yan uwansa dan yasan shi tana masa so mai tsananinda bazata iya kashesaba ko illatasa.
Ahankali yakejin sautin qarar sarqar qafa da taku na nufosa tareda wani irin haske da niimtaccen qamshin mai tareda sanyi na shigarsa ya ‘dago ahankali ya qurawa gurin ido baiga fuskartaba sbd wani irin kyallin zinari dake fita daga wuyanta da kanta tareda damtsen hannunwanta da qafafunta sbd adon sarqunan dake jikinta.
Saidatazo gaf dashi ta tsaya cikin ainihin suffarta tana sakar masa wani irin murmushi mai qayatarwa ta miqa masa hannunta cikin wata irin murya mai dadi tace,
Ina tayaka murnar zama attajirinda babu kamarsa a wannan qarnin,
Ina taya murnar zamtowa mijin sarauniyar da babu tamkarta a wannan qarnin,
Soyayyace farko kuma soyayyace qarshe,
Zan rayu dakai na bauta maka domin Kaine sarki a masarautata saidai cin amana,qarya da yaudara basa cikin soyayyata basa cikin abinda nake dubawa amatsayin kuskure koda ga abinda nafi so ne.
Murmushin takaicin rayuwarsa yasaki sbd yasan tunda ya bari zuciyarsa takamu da soyayyarta rayuwarsa na tsaka sbd bazai iya rabuwa da ‘yayan uwansa ya 6ata musu buriba sannan bazai iya bari acutatar da itaba.
Cikin sanyin murya data nuna zallar damuwar dayake ciki yace,
Wacece ke?
Ahankali ta furta,
Sarauniya mineelik,aljanarda aljanu da mutane suka buri da fatar gani kuma matarka ta har mutuwa.
Rintse ido yayi akaro na farko yaji jarimtarsa ta 6ace ya sauke kai cikin rawar murya yace,
Meyasa kike sona har haka bayan bakida cikakken sani akan abinda yake zuciyata.
Ahankali ta ‘daga hannuwanta sama tayi budesu idanuwanta akansa tace,
Barka da zuwa masarautar mineelik.
Miqewa yayi cikin wani irin mugun tsoro da firgici yake kallon koina yana jujuyawa kamar wuyansa zai cire sbd ganinsa Cikin wata irin masarauta mafi girma da kyawun dabai taba ganiba duk yawon duniyarsu.Adon ne zaibar zinari da wani irin gini mafi kyau da tsari
Wasu irin kujeru ne a Jere na sarauta sunsha ado wani irin ni’imtaccen kamshi na tashi daga yanayin jerin kujerun da tsarinsu yasa ya tabbatarda nan ne asalin fadar wato dakin taron sarauta. +
Wani irin qyalli yaringa gani yana hasko bayansa yayi saurin Juyawa a kidime yaja da baya tareda zubewa qasa kan qafafunsa yana kallonta cikin wani irin tsoro da firgici..
Zaune take kan karagar mineelik tafito masa Zak amatsayin sarauniyarta atake wani irin tsoronta da firgicin dabai taba jiba yasashi sauke kai yana girgizawa.
Ta bayansa yaji andafasa a zabure ya juya yaga itace yayi saurin kallon karagar yaga bata kai ya juyo yasake kallonta ta sakar masa murmushi mai sanyi tace,
Banason sanin sirrin dake zuciyarka sbd idanuwanka sun tabbarmin da abinda nake nema daga gareka wato soyayya mai qarfi dan haka masarautar mineelik takace kaima daga yau dakazama mijin mineelik.
Murmushin baqin ciki yasaki tareda miqewa ya juya mata baya cikin tsananin damuwa yace,
Idan ‘yan uwana sunzo basu ganmuba zasu…….
Masarautar mineelik ta bayyanane ga dukkanin Wanda ke wannan nahiyar sbd duk girman wannan dajin da mutum zaiyi tafiyar kwana bakwai bai gama fitaba acikinsaba ba daji bane duk girman masarautar mineelik ne dan haka ayanxu mutane na kusa da nesa suna hanyar zuwa kallon masarautar dabasu taba gani ba ta mineelik data bayyana ga kowa.
Zai sake magana taga duk cikin tashin hankali yake mai tsanani
Ahankali ta riqo hannunsa cikin nata tsananin laushi da ni’imar fatarta yasashi kasa magana yabita tamkar raqumi suka nufi turakarta datafi kowace kyawu.