GAMAYYAH CHAPTER 14 THEND KARSHE

GAMAYYAH





CHAPTER 14 THEND KARSHE








Kasa motsi tayi tabi bayanta da kallo harta fice ta jima tana kallon qofar kafin ta maido kallonta kan abeel daya farka yana kallon fuskarta ta rintse ido tareda rungumesa tana jin wata sabuwar damuwar sbd rashin sanin abinda yafaru yanxun.

Ahankali ta lumshe idanuwanta mafarkin abbanta datai yau yana dawo mata.

“Ummu-rumanah kibi mijinki a dukkanin umarninsa matuqar basu saba addininki ba sbd shine gatanki kadai yanxu aduniya,
Ki gujewa mulki sbd haqqoqin dubban mutane da bazaki iya daukaba sbd rauninki na zamowa ‘ya mace kibarwa Allah komai ki gyara aljannarki.”””

Kalaman da mahaifinta ya sanarda ita a mafarki kenan saidai abinda takasa ganewa shine ta yaya zata sauka mulkin batareda ta kawo sauyi da zaman lafiya a qasar ba.

Bude ido tayi tareda jinjina shawararda zuciyarta ke bata dan kawo qarshen komai saidai hakan wani abune mai girma dayakeda matuqar hadari saidai dole zata aikata hakan koda hakan shine ajalinta zatayi dan kawo qarshen rayuwar da alummar qasar suka samu kansu.

Tabbas qaddararta itace ta koro iyayenta daga gida ta kawosu nan sbd gashi abinda yafaru tun qarnikanda ko kakanninta ba’a haifa Ashe tana cikin qaddarar gashi itace zata kawo qarshen abin.

Hawayen tausayin mijinta da ‘danta tareda ammy ne suka gangaro mata ta sauke kanta tareda sakin kuka ahankali sbd tasan sune zasufi kowa kukan rashinta arayuwa sbd sune wainda takeda matuqar mahimmanci arayuwarsa ta yanda rashinta zai matuqar ta6a rayuwarsu.

Sunansa ta furta ahankali cikin zuciyarta sbd tasan mutuwarta zata tarwatsa zuciyarsa zatabarsa cikin mawuyacin hali saidai tasan suhailat na nan zata kula dashi.
5

Miqewa tayi ta nufi dakinta ta kwantarda abeel ta zauna gabansa ta qura masa ido tana fidda sautin kuka ahankali sbd kukane takeyi sosai.

Tana fitowa sashen rumanah kai tsaye shashen ammy ta nufa bata nuna mata komaiba tasanarda ita zataje Mali.

Ammy dake fama da ciwon kai mai tsanani takalleta da idanuwanta ahankali tace,

Allah ya kiyayeki ya hadaki da alkairin dake cikin tafiyar.

Amin ta furta ahankali tareda juyawa ta fice dan dama su amah suna Mali tuntuni da aka fara wainan rudanin.

Motocin dazasu kaita airport na fitowa daga masarautar tasaki wani irin kuka ahankali tareda rintse idanuwanta tana furta Allah yabani juriya da danganar rabuwa dakai maheer

Suna isa airport basuyi minti ashirin ba suka tashi daga qasar Ethiopia zuwa mali.

Lokacinda ta wuce tabarsa daqyar ya iya fita yabar dakin ya nufi part dinsa yana qoqarin danne halinda zuciyarsa ke ciki amma yakasa saida jiri ya zaunar dashi kan kujera da qarfi ya rintse ido ga mamakinsa saiyaji kamar hawaye na neman zubo masa yayi saurin dafe kansa da hannu bibbiyu jin kamar zai rabe masa sbd yasan bazai ta6a iya cireta aransa ba.Ahankali ta qaraso bayansa ta tsaya tareda zuba masa ido tana sake danne hawayenta.. +

Bude idanuwa yayi ahankali sbd he can feel her presence.

Juyowa yayi suka hada ido atake takasa riqe kukanta tafara girgiza kai tareda sakin kukan
Ya ware hannunsa ‘daya alamar tahowa garesa da gudu ta qarasa ta fada jikinsa ya rungumeta sbd shikansa yana buqatarta kusa ayanxu.

Kukan datakene yafara bashi mamaki ya ‘dago fuskarta ya kalleta atake yaji kwanyarsa ta qarasa hargitsewa ya bude baki zaiyi magana tayi saurin ‘dora bakinta cikin nasa tana tsiyar hawaye.

Ahankali tasaki bakinsa tana kallon fuskarsa dake bayyane da damuwa cikin tsananin sanyin muryar kuka tace,

Ina sonka yarima maheer abdulshams,Kaine farin ciki da rayuwar ummu-rumanah bulama,
Kaine abinda zuciyata bazata iya jure rashinsa ba,
Ina maka qauna mai girma a tun ranardana fara ganinka agabana.,
Wlh bazan taba iya aikata kuskurenda zai nesantani dakaiba bare kwatanta rayuwa babukai.. +

Kasan mutuwane kawai banyiba a daren ranar daka furta rabuwa dani maheer abdulshams,

Ummu-rumanah bazata iya rayuwa babu kaiba sbd kaine jigonta kuma jagorarta..

Share hawayenta tayi tareda jan numfashi kukanta na rage sauti tace,

Wlh haryanxu zuciyata zafi da takeyi da zancen daka fadamin kana tunanin zan iya rayuwane wlh mutu…..

Maidata yayi jikinsa da sauri ya rungumeta yana girgiza mata kai dan bazai iya ko maganaba

Qanqamesa tayi tana cewa,

Na tuba ka yafemin.

Dora hannu yayi abakinta yana sake rungumeta ahankali ya furta,

Maheer abdulshams loves you ummu-rumanah bulama.,
Ummu-rumanah bulama kece mahadin rayuwar maheer abdulshams.

Murmushin qarfin hali tasaki ahankali tareda sake kwanciya ajikinsa.

Shiru sukayi dukkaninsu ajiyar zuciyarta kawai ke fita akai akai
Sai kuma shi dahar lokacin tunani da damuwar tafiyar suhailat ne kawai cikin ransa,
Tana buqatar shan iska zai barta tasamu sarari idan yagama da matsalar mineelik ya tabbatarda rumanah ta fita daga cikin wannan masifar zaije yadauketa su koma Georgia gabaki ‘dayansu. 9

A daren ranar nan ta kwana gurinsa tareda abeel saidai kusan dukkaninsu babu mai nutsuwar yin bacci saidai shiru sukayi a kwance kowannen da abinda yake damun zuciyarsa.

Washe gari koda aka tashi aka tararda Allah yayiwa mamani rasuwa
Koda aka dudduba dan tabbatarda meya kasheta aka gano saran maciji ne har guri biyu a wuyanta da gefen hannunta sbd wani irin canzawa da fatarta tayi takoma Kore Kore alamar qarfin dafin macijin mai ha’darine.

Lokacinda Jakadiya ta kawo mata saqon mutuwar suna zaune kan dining maheer na tilasta mata cin abinci.

Kallon Nuratu dake jera musu sauran abincin breakfast din tayi da sauri tareda miqewa tsaye sbd ganin halinda tashiga lokacinda Jakadiya tagama fadar saqon da sauri suka rungume juna nuratu na sakin wani irin kuka ahankali tareda rintse ido tana girgiza kai.

Hawayen tausayin nuratun ne itama suka ciko idanuwanta ta bubbuga bayanta cikin son daure kukanta dake zuwa na tausayin kansu sbd sun tabbata marayu iyayensu dasukazo nan suka haifesu sun rasu sun barsu ayanxu sune kadai ‘yan uwan kansu.

Cikeda tausayawa Jakadiya takallesu cikin sanyin murya tace,

Allah ya gafarta mata laifukanta ya sadata da rahamarsa ina miqo ta’aziya ga assultana da ‘yar uwarta nuratu akan wannan rashi.

Ganin tana neman rikicewa da kuka yasashi yiwa Jakadiya wani kallo
Atake tayi gyaran murya tana cewa,

Nuratu kizo muje kiyiwa mahaifiyarki addua kafin a fice da ita.

Sakinta rumanah tayi tareda kallon fuskarta tana hawaye tace,

Allah yabaki haqurin rashinta yasakamiki dauriyar yimata addua.

Kallon rumanar tayi sbd jin bata ambatarwa mamanin rahamar ubangiji ba ahankali ta bude baki cikin tsananin sanyin murya tace,

Ina roqorwa mahaifiyata yafiya ki yafe mata sbd qauna da amincin dake tsakanina dake dan……

Kije na yafe sbd qauna da amincin dake tsakaninmu saidai haqqin ran ‘yayana data dauka wannan tsakanintane da ubangijinsu shida ya haliccesu.

Ahankali ta furta,ina fatar Ubangiji ya yafe mata.

Juyawa tayi ta fice rumanah ta juya ta zauna tana qoqarin saita nutsuwarta kartayi kuka saidai Sam takasa sbd duk yanda mamani taqita takashe mata ‘dah ita din tatace.

Ta bayanta ya rungumeta jikinsa ahankali yana cewa,

Sorry luv.

Shigewa jikinsa tayi tana daina kukan dan tana buqatar rarrashin gabaki daya ta rasa ina ta dosa da rayuwarta.

Jin tayi shiru yasashi shafa kanta cikin sanyin murya yace,

Allah baya barin haqqin wani akan wani gashinan kin gani.

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sbd tunowa da abinda zatai dan kawowa kowa sauqi da qarshen masifar sbd a yanxu abeel dintane kawai ake jira ya gia yahau dan haka bazata taba bari ‘danta yahau wannan karagar ba sbd ajikinta tanajin masifa da balain dake cikinta yana yawo cikin jininta ita kadai tasan yaya takeji take daurewa sbd shirye take da yaqar komai akan qarfin soyayyar datakewa mijinta

Abu taji na fitowa ta hancinta ta taba ahankali tashafo taga jinine da sauri ta goge sbd kar Maheer yagani.

Shigowar ammy yasashi sakinta suka miqe gaba dayansu murya a tausashe suka gaidata ta amsa tana kallon rumanah dataga tayi wani irin fayau kamar ba jini a jikinta ta tsaya gabanta tareda riqo hannunta suka koma kan royal cushions dake palon suka zauna tana kallonta cikeda mamaki tace,

Rumanah ki fadamin gskia lafiyarki kalau?

Gefen Maheer daya kafeta da ido ta kalla ta sauke kai cikin sanyin jiki tace,

Lafiyata kalau.

Girgiza kai ammy tayi tace,

Rumanah wlh bakida lafiya wannan abun na cin jininki duba kiga kina canzawa rumanah karki rufeni kifadamin gskiar abinda kikeji.

Dawowa yayi kusada ita ya zauna yana zuba mata ido cikin tuhuma ya riqo hannunta zai duba tafin hannunta ta zame hannun tareda girgiza kai tace,

Lafiyata klau banajin komai….

Hancinta ya qurawa ido cikin daukewar numfashi yakai hannunsa ya shafo jinin dake gangarowa daga hancin ya kalla jikinsa na rawa ammy ma cikin tsananin tashin hankali take kallon jinin…

Ganin suna kallonta tayi saurin shafowa taga jini sosai ta miqe tsaye wani irin jiri ya dibeta ta yanke jiki gurin ta fadi idanuwanta rufe jinin na sake ballewa daga hancinta.Cikin masifaffen tashin hankali sukayi kanta ammy tuni tafara kuka tana kiran sunanta

Shikuwa daukarta yayi hankali amatuqar tashe yayi bedroom dinta da ita ya kwantar ya fidda waya atake yakira khaleefa dasu dr abeena tareda sauran manyan doctors nasu.

Tissue yasa yana goge mata hanci saidai Sam jinin yaqi tsayawa gashi tafara wani irin jijjiga a rikice ya qanqameta jikinsa yana kiran sunayen Allah ahankali muryarsa na rawa dan yasan bazai iya kwatanto rayuwa babu itaba. 3

A gigice dukkaninsu suka iso tareda nurses da duk wasu kayan aikinsu atake suka fara qoqarin tsaida jinin dan maqala mata oxygen sbd numfashinta daya fara mata wuyar ja.

Dafasa khaleefa yayi tareda kallon yanda duk jikinsa ya 6aci da jini cikin kulawa yace,

Kaje daga palo gurin ammy zakafi samun nutsuwar bari mu dubata.

Palo khaleefa ya rakosa ya zauna kusada ammy yakoma ciki shi.

Riqo hannunsa ammy tayi cikin tsananin damuwa da tausayinsa dana abeel dake rungume ajikinta tace,

Zataji sauqi insha Allah.

Jinjina mata kai kawai yayi sbd ko bude baki bazai iyaba bare magana.

Atake rashin lafiyar assultana ya yada koina nan koina gari yafara ‘daukar tsit sbd rufe shaguna da kasuwanni.
Acikin masarautar kuwa Sam ba wani dogon motsi tako wane bangare sbd jiran tsammanin farfadowarta.

Daqyar suka samu suka tsayar mata da jinin aka maqala mata oxygen tareda ruwa da sauran abubuwan da suka kamata amma har lokacin bata farfado ba.

Bayan duk sungama abinda zasuyi aka bar nurses uku dan kulada ita suka fice.

Lokacinda yashiga yaga yanda takoma lokaci daya
Ya zauna bakin gadon tareda ‘dora hannunsa kan nata ya rufe ido
Shikadai yasan radadi da ciwon da zuciyarsa ke ciki ganinta ahaka.

Ahankali yace,

Tana farfadowa zamu wuce bazan iya zama anan ba kuma.

Dafasa ammy tayi tareda yarda da abinda yafada dan itama tagaji da nan ‘din tana buqatar nutsuwar rayuwa kota maida hankali gurin istighfar ga ubangijinta

Sai tsakiyar dare ta farka tareda bude idanuwanta ahankali ta qurawa masa ido yana zaune bakin gadon hannunsa cikin nata a damke idanuwansa a lumshe saidai tasan ba bacci yakeyiba.

Ahankali ta bude baki da siririyar murya ta furta,

Abu abeel..

Bude idanuwansa yayi da sauri tareda tashi zaune daidai yana kallonta fuskarsa na bayyanarda tsananin farin cikin daya shiga na ganin ta farka.Murmushin qarfin hali tasaki tareda sake damqe hannunsa dake cikin nata tana kallon fuskarsa dashima ita yake kallo yana yiwa Allah hamdala cikin ransa. +

Tashi zaune takeson yi ganin kamar batada qarfin jiki yasashi tayarda ita zaune tareda cire mata cannula dake hannunta ya gyara mata zama sosai.

Cikin sanyin murya da kulawa yace,

Ya kikeji yanxu?

Girgiza masa kai tayi tana kallon fuskarsa.

Jakadiya ce tayi knocking qofar dakin ahankali ta sanarda zuwan sultana.

Zare hannunta tayi cikin nasa tareda lumshe ido sbd yanayin datakeji ajikinta har lokacin.

Cikin nutsuwa ammyn tashigo idonta kan rumanah din
Hankalinta ya’dan kwanta ganin ta farka harta tashi zaune.

Qarasowa tayi tareda miqawa maheer hannu ya kama hannun da hannunsa daya cikin nutsuwa yace,

Ina kwana ya ammy?

Murmushi tayi tace,

Lfy klau..tana kamo hannun rumanah tace,

Ya jikin?

Naji sauqi ammy”””ta fada cikin qarfin hali da danne ciwon datakeji.

Miqewa yayi ya fita yana amsa kiran khaleefa dake kiransa kan maganar test result ‘dinta dasuka fito.

Ammy dakanta ta kamata takaita toilet tayo wanka da brush tana fitowa taga doguwar riga mara nauyi akan dressing chair ta dauka tasaka ta shirya tana qoqarin busar da kanta sbd wankan tsarkin datayi na haihuwa ammy tashigo tareda nuratu dake daukeda babban tray Jere da breakfast ta ajiye zata juya rumanah takira sunanta ahankali.

Tsayawa tayi tareda juyowa cikin ladabi
Rumanah ta miqa mata hand dryer cikin sanyin murya tace,

Taimakamin.

Ammy na ganin hakan tasan magana zasuyi ta kalli nuratu tace,

Tayi breakfast.

Jinjina kai tayi alamar tou.

Ahankali take busar mata da gashin babu Wanda yayi magana acikinsu.

Tana gamawa ta daure mata gashin tareda ajiyewa a natse.

Miqewa tayi itama ta nufi inda take sallah tana idarwa ta dawo kan couch din dakin ta zauna har lokacin nuratu na tsaye kanta a sunkuye cikin tarin damuwa da kadaici.

Ahankali takamo hannunta ta zaunar da ita kusada ita ta kalli fuskarta kafin ta sauke kanta itama ta qurawa gabanta ido cikin sanyin murya tace,

Kiyi hakuri nabarki alokacinda kike tsananin buqatata,
Kin kuladani kin tayani kuka kin rarrasheni alokacinda na rasa nawa iyayen saidai ni nakasa miki hakan alokacinda kike buqatar wani ataredake..

Kallonta nuratu tayi hawayen datake riqewa suka gangaro mata tace,

Wlh idan nace miki bana buqatarki ataredani na miki qarya rumanah saidai yanayin rayuwa daya kawo bambamci arayuwarmu ayanxu rayuwarki daban take data baiwar datafi kowace baiwa baqin jini sbd mahaifiyarta data…..

Rintse ido tayi tareda budewa idanuwanta na cikowa da hawaye ta juyo ta kalleta cikin sanyin murya tace,

Ada damuke bayi rayuwarmu tafi kwanciyar hankali da nutsuwa tareda dadin gudanar da rayuwarmu,
Rayuwar bayi wata rayuwace mara yanci amma wlh wani lokacin tafi rayuwa irin wadda nasamu kaina aciki,Nuratu idan zaka roqi Allah abu ka roqi alkhairinsa sbd wlh rayuwata ina baiwa tafimin kwanciyar hankali akan yanxu. +

Gangaro mata hawaye sukayi sbd jin tausayin kanta da abinda zata fada tace,
Nuratu na ‘yantaki daga yanxu ke ba baiwa bace kinsamu ‘yancinki,
Babu wata rayuwar jin dadi da kwanciyar anan dan haka za’a maidaki gida acan zaki samu rayuwar kwanciyar hankali damukai burin samu idan ni bansamuba zan qoqarta gurin ganin ke kinsamu…

Kallonta nuratu takeyi hawayenta na tsananta gudu tace,

Tare mukayi alqawarin komawa gida…..

Zanzo wata rana nima idan nauyin alummar dake kaina ya sauka
Zanzo idan inada rayuwa da lafiya sbd burinane nima nahadu da dangin iyayena dan haka karkiyi wasa da damarki kice zaki jirani kije Allah zai sake sadamu da yardarsa.

Kuka nuratu ta fashe dashi tana girgiza kai tace,

Bansan ta yaya zan fuskanci mutanen da basusanniba nikadai nace musu dukkanin iyayenmu da sauran danginsu da akaje dasu sun mutu ba…

Itama kukan takeyi sosai saidai bazata iya cewa komaiba sbd wannan shine gatan datasan zata yiwa nuratu takoma gida ta fuskanci sabuwar rayuwa cikin amincin Allah.

Kuka sukeyi sosai na rabuwa da juna daqyar rumanah ta miqe ta bude wardrobe ta dauko wata jaka dake daukeda qatuwar sarqar zinari ta miqawa nuratu tareda juya mata baya sbd kukan datake riqewa tace,

Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi.

Ta baya nuratu ta rungumeta tana sakin sabon kuka tana cewa,

Kisani zan jira zuwanki har qarshen numfashina.

Daqyar suka saki juna suka fito palonta na biyu inda suka tararda ammy da maheer da khaleefa tareda Jakadiya suna jiran fitowarsu.

Fuskokinsu suka bayyanarda halinda suke ciki.

Ya qurawa fuskarta datai jajir ido kafin ya dauke kai yanajin damuwar ganinta hakan cikin zuciyarsa.

Gefen ammy ta qarasa ta tsaya ahankali ta bude baki tafada musu tafiyar Nuratu din zuwa qasarsu.

Ammy sosai ta yiwa nuratu addua da fatan alkhairi tareda cewa jakadiya nuratun ta sameta kafin washe gari ta wuce.Bayan fitarta khaleefa yabi bayanta da kallo kafin maheer yayi masa magana da ido suka fita. +

Bayan fitarsu ammy ta zaunar da ita tasa aka kawo wani abincin breakfast din.

A palon yarima maheer suka zauna cikin nutsuwa yace,

Khaleefa zaka karbi duk wani bayanin tarihin my queen da mahaifiyar nuratu ta bayar ka kaita har gida kafin ka karbi takardun iyayenta kayi amfani dasu ka nemomin asalinta.

Shiru khaleefa yayi yana sake tauna zancen sbd tafiyar ta jirgin ruwa ce sbd ta ruwa kawai zasubi su bulla garinsu nuratun kai tsaye a yanda akace gashi bai cika son tafiyar ruwa ba saidai kuma dole haka zai daure saidai suyi amfani jirgin dazasu isa cikin kwana biyu.

Acikin daren rumanah tayi kukan tafiyar Nuratu,
Iyayensu sunzo qasar dasu acikinsu gashi su zasu koma batareda ko dayansuba.

Washe gari bayan sallar asuba suka wuce bayan khaleefa yakarbi duk wani tarihi na asalinsu daga hannun anees mai haqqin tattara tarihin sarakunan masarauta Wanda aka ya karbi bayanan daga mamani ya rubuce a littafin tarihi kafin rasuwarta.

Bayan tafiyarsu takira Jakadiya ta miqa mata wani zungureren saqo a rubuce tace takaiwa harooun sarkin fada.

Lokacinda Jakadiya takaiwa harooun saqon yana gama karantawa jikinsa yayi matuqar sanyi da abinda ke rubucen saidai kuma yasan hakan datake shirin yi shine qarshen abinda yake bibiyar mineelik dan haka babu bata lokaci ya fita dakansa yaje gurin Negus sarkin qirar mineelik yayi masa bayani ya karbo littafin zanen karagar mulkin qarnikan baya yadawo yabawa jekadiya takai mata.
D
Lokacinda Jakadiya takawo mata shirgegen littafin mai nauyi ko budesa batayiba tace,

Kije na zabi lamba ta biyar.

Babu musu Jakadiya takoma ta mayar tana jinjina alamarin rumanah sbd idan Allah ya taimaka abinda take shirin yi shine daidai.

Acikin daren ranar Negus da yaransa suka fara aiwatarda aikin qera sabuwar karagar mulkin mineelik wadda basu ta6a qera abu mai kyau da darajartaba sbd abubuwan dasuka narka ana hadawa dasu gurin qirar.

Lokacinda Jakadiya ta sanarda ammy abinda yake shirin faruwa numfashi ammy tasauke cikin danne fargabarta dan batason tunanin faruwar wani abin saidai zataje tayi magana da sultan sbd shine yasan komai ciki da waje gameda komai na karagar fiyedasu.

Da daddare bayan ko ina yayi tsit sultana ta fito ta nufi sashen sultan kai tsaye aka barta tashiga sanin matsayinta gurin assultana.

Zaune yake hankali kwance yana karatun wani shirgegen littafin tarihi yana shan madara mai zafi da aka kawo masa kullum kafin ya kwanta sbd tana qara lafiyar qwaqwalwa.

Kallo daya yayi mata yasaki murmushi yana cigaba da abinda yakeyi.

Qarasowa tayi kusadashi ta zauna cikin girmamawa ta gaidasa tana kallon littafin dayake karatu tace,

Meyasa haryanxu bazaka sauke dukkanin wani tunani na sharrin shaidanba ka fuskanci gaskia ka bita,
Ka tubarwa ubangijinka ka ajiye duk wata niyya da qudirinda bana alkhairi ba wlh Allah zai karbi tubanka sbd shi mai yafiyane ga bayin dasuka tubarmasa.

Wani irin murmushi yasaki tareda rufe littafin ya ajiye gefe ya kalleta yace,

Baiwarki kuma matar ‘danki tayi babban kuskure na aikata abinda ta aikata sbd kaf tarihin mineelik babu wani sultan da aka taba muzantawa saini sultan abdulshams jinin ajani….

Numfashi tasauke cikin takaici da baqin cikin halinda mijinta yasamu kansa idanuwanta na cikowa da hawaye tace,

Son zuciyar kakannin kakanninka shine yasamu ahalinda muka tsintsi kanmu aciki karka bari zuciya takaika aikata irin kuskurensu…..

Katseta yayi da cewa,

Meya kawoki ki fada kai tsaye sbd nasan akwai abinda yakawoki a wannan lokacin.

Kallonsa tayi ganin Sam idanuwansa da zuciyarsa sun rufe..
Cikin sanyin murya tace,

Assultana na shirin canza mineelik gabaki ‘daya da wata……

Da sauri ya kalleta yana ajiye cup din hannunsa sbd girgiza da zuciyarsa tayi.

Cikin bayyanarda tsananin tashin hankalinsa yace,

Zata aikata wani babban kuskuren sbd rusa karagar gabaki ‘daya na nufin rusa rayuwarta sbd zata rushene tareda jininsu jamal na qarsh qarshe daya hau karagar yayi mulki akanta…… +

Shiru yayi zufa na karyo masa sbd yasan dagashi sai itane suka rage aduniya wainda suka taba zauna karagar har sukai mulki akanta,
A bangaren jini kuwa shikadaine jininsu na qarshe dayayi mulki akan mineelik ita ‘din ba jininsu bace akwai yiyuwar abin bazai shafetaba koya shafeta saidai ta nakasta amma shi babu tantama rayuwarsace ke rawa jinin qarshe nasu jamal.

Wannan rumanah gabaki ‘daya rayuwarta ta zame masa masifa mai barazana bai taba tunanin ko namiji zai iya fuskantarsaba ya girgizasa bare ‘yaya mata daya dauka marasa amfani saigashi ko acikin ‘yaya matan ma baiwace take barazaga rayuwarsa,

Bazai Bari su aikata hakanba dole ya juya musu zancen..
Gyara nutsuwarsa yayi cikin vasarwa yace,

Karku bari ta aikata hakan sbd rayuwartace acikin hadari dan kuwa haqqine na qarshe zai fita akanta…..

STORY CONTINUES BELOW

Murmushin baqin ciki ammy tasaki tareda girgiza kai hawayenta suka sauko tace,

Yanayinka da kulawar daka nuna yasamin kokwanto akan amsarka dan haka mun dangana munbarwa Allah komai zamu barta takawo qarshen mineelik duk abinda Allah ya qaddaro zamu runguma mu dauki dangana.

Miqewa tsaye tayi zata fice ya riqo hannunta akaro na farko dayaji tsoro da fargaba sun ziyarci zuciyarsa ya bude baki daqyar yace,

Karki bari ta aikata sbd rayuwatace a hadari kuma tatama na cikin hadari.

Hawayenta suka qara gudu ta sunkuyar dakai tanajin zuciyarta na karyewa sbd qaunar mijinta uban yayanta saidai kuma kodan sbd ‘yayanta da jikokinta zataso akawo qarshen masifar mineelik.

Zame hannunta tayi ahankali tace,

Allah yazaba mana abinda yafi zama alkhairi.

Ficewa tayi jiki asanyaye zuciyarta na sake karyewa saidai bazata bari ta karayaba hakan da rumanah zatayi shine daidai insha Allah.

Zaune yake bakin gadonsa yayi shiru tareda zurfi cikin tunani Sam bayajin nutsuwa a zuciyarsa wani irin rashin sukuni yakeji..

Ahankali tashigo dakin rungume da abeel jikinta amatuqar sanyaye sbd jikinta datake yana tsananta dan ko yanxu kafin tafito saidata yanke jiki ta fadi jini na fita hancinta saidai bata fita hayyacinta ba kuma ta hani Jakadiya fadawa kowa abin yafara tsanani.

Qarasowa tayi ahankali ta kwantarda abeel kan sofa tadawo gefensa ta zauna ahankali tareda dafa hannunsa takalli fuskarsa.

Shima ita ya kalla ta sakar masa murmushi ahankali tareda riqe hannunsa ta lumshe ido sbd abinda taji yana taso mata ta danne yanayin daqyar tasake qaqalo murmushi tana kallon hannunsa dake cikin nata ahankali tabude baki tace,

Karka saki hannuna har lokacinda zan shaqi numfashin qarshena a duniya,
Ka zamo jiqo kuma majingini arayuwata
Ka hanani ‘daukar hanyarda zata batardani zuwa duniyar daba tawaba,
Qarfin soyyarka yaci qarfin abinda nakeji ajikina saidai bansaniba ko hakan zai jima shiyasa a yanxu nake roqonka da har abada karka rabu da suhailat sbd itace macen da soyayyarta bazata taba barin cuta ta kutso kai rayuwarkaba..ni tamkar baquwace a rayuwarku ba lallaine na qarasa rayuwa acikinkuba…….

Matse hannunta dake cikin nasa yayi yana rintse idanuwansa dasukai jajir..

Hawayen datake riqewane suka 6alle mata ta kalli fuskarsa datai jajir ya rintse idanuwansa ta shafi fuskarsa hawayenta na tsananta tace,

Maheer abdulshams nagode da soyayyarka gareni..

Bude jajayen idanuwansa yayi yana kallon hawayenta dake gudu sosai yakasa magana sbd radadi da nauyin da zuciyarsa tai masa sai kawai ya rungumota jikinsa.

Ahaka suka kwana cikin wani irin sanyin jiki dana zuciya.

Kwanansu khaleefa biyu a ruwa aranar na uku da yamma sosai suka isa saidai kuma sunsha wahala sosai sbd tuni bakin ruwan yazama border saida sukasha wata irin wuya kafin suka samu wucewa da taimakon wani ‘dan asalin qauyensu mamani din.

Bayan wucewarsu duk yanda sukayiwa saurayin bayani bai ganeba sbd basajin hausa ko kadan har gwara nuratu tanaji kadan kadan sbd su mamani da umman rumanah sunayi musu tun suna qanana saidai ya jasu kan mashin dinsa sukayi wani irin mugun overload yajasu dan kaisu cikin qauyen qauyen daya samu canji ba laifi. +

Tafiya mai tsawo sukayi kafin suka isa qauyen mai tsananin girma da cikar mutane.

Gidan shugaban qauyen yakaisu cikin sa’a lokacinda suka isa yana gida.

Kallonsu aka taru anayi sbd ganin baqaqen labarawa musamman khaleefa dayake cikakken dan Ethiopian asali.

Bayan anbasu guri sun zauna ya fidda tambarin masarautar dasuka fito ya miqawa shugaban ya kalli nuratu yayi mata magana yace,

Kiyi musu bayaninmu yanda zasu gane ko yayane.

Gyara zama tayi muryarta na rawa tace,

Munfito daga qasar Ethiopia ne qarqashin masarautarsu,
Sun siya bayin dasuka fito daga wannan nahiyar tsawon shekara ashirin da biyar yanxu.,
Acikinsu akwai mamani da asma’u dasuka tafi da juna biyu acan suka haifi ‘yaya mata dukkaninsu Wanda ‘daya daga cikin ‘yayan itace ni ‘dayar kuma a yanxu itace sarauniyar qasar.

Da wani irin mugun mamaki suke kallonta musamman shugaban garin daya zamto kutti mijin mamani yasake kallon nuratu da gabaki ‘daya take kamar yar asalin Ethiopia itama.

Cikin nutsuwa yace,

Ke ‘yar wacece acikinsu?

Ni ‘yar mamani ce.

Wata irin kabbara tsoffin gurin suka dauka cikeda murna da mamakin wannan alamari kutti yace,

Ina iyayenku?

Dukkaninsu Allah yayi musu rasuwa mamani ko sati batayiba yanxu haka.

Sake daukar kabbara sukayi cikin jimami da tsananin girmama wannan alamari.

Ahankali ta zayyane musu komai gameda rayuwarsu kafin ta gabatarda khaleefa amatsayin Wanda zai karbi takardun dukiyar asma’u da bulama dan neman asalin sarauniya ummu-rumanah.

Bayan dogon koke koken saduwa da baqin cikin rashinsu mamani dasu bulama nan kutti yagabatarwa da su nuratu kansa amatsayin mahaifinta.

Duk wani zuriar gidan antaru an karbi nuratu da hannu Bibbiyu da zuciya daya da wainda suka San faruwar abin da wainda ma ko haihuwarsu baayiba nan dai kowa yataru ana farin ciki.

Ganin yanayin garin yasa khaleefa yanke shawarar wucewa dan sake kutsawa cikin Nigeria dan gabatarda abinda yakawosa.

Kutti ya basa takardun dasuka tsufa sosai ga sanyin ruwa daya soma lalatasu tun wancan lokacin saidai ba laifi yana iya ganin rubutun dake jikinsu atake ya karancesu daganan ya roqi alfarmar tafiya da wani yaron kuttin dayake jin yarensu kadan kadan sbd aiki dayakeyi a border dinsu.

Da mashin din salee suka isa inda zasu samu mota bayan sunyi tafiyar awowi akan mashin din.

Motar dazata kaisu Maiduguri kai tsaye suka hau inda duk hankalin khaleefa yatashi sbd ganin inda yasamu kansa dakuma wata irin azabar wuyar tafiya data fara gigitasa.

Gaf da asuba suka isa Maiduguri kai tsaye wani lafiyayyan babban hotel suka sauka anan yayi baccin wahala ga zazzabin dakeson kamasa na baqar wuyar dabai taba shaba.Duk yanda yaso yayi komai cikin lokaci yakoma hakan bai samuba sbd zazzabi mai qarfi daya kwantar dashi tsawon kwana biyu
Qarshe dai dole ya daure suka tafi kai tsaye companyn dake rubuce a jikin takardun da taimakon wani ma’aikacin hotel din suka isa. +

Da farko sunsha wahala kafin suka samu ganin shugaban companyn alhaji babaye salmanu bulama.

Kai tsaye khaleefa yafitarda takardun dayazo dasu ya ajiye gaban alhaji babaye.

Kallo daya yayi musu harzai dauke kai yayi magana yaga sunan dake jikinsu yayi musu wata irin damqa yana dubawa sbd basuyi masa kama dana yanxuba wannan rubutu da sunan company dinne tunna iyayensu na shekarun dasuka wuce.

Budesu yaringayi daya bayan daya haryakai qarshe ya miqe tsaye sbd tabbarda sune asalin takardun da ‘yayansa da matarsa suka tafi dasu.

Kallon khaleefa yayi da sauri tareda zagayowa daga table dinsa jikinsa na wata irin rawa tun kafin yayi magana khaleefa yaciro alamar masarautar daya fito ya miqa masa cikin turanci yace,

Nazone dan neman asalin sarauniyar qasata ummu-rumanah bulama..

Rawa jikin alhaji babaye yaqara yace,

Ina kasamo wainnan takardun?
Ina masu su suke?

Masu wainnan takardun sun rasu saidai ‘yarsu wadda itace sarauniyar qasarmu ayanxu….

Wani irin kuka alhaji babaye yasaki tareda rungume khaleefa duk da dai yasan dole yayi bincike akan hakan kafin yagama yarda.

Waya yaciro yakira qanwarsu hajiya yakurah yafada mata nan hankali ya tashi sbd farin ciki da murna tareda wasi wasin zamtowar zancen gskia.

Da kansa yakaisu gidansa akai musu masauki kafin yatabbarda zancen duk da yasan baza’a yimusu qarya dan a cucesu tun daga qasar Ethiopia ba kuma daga masarautarsu.

Washe gari cikin manyan motoci suka dunguma zuwa garinsu kutti dan sake tabbatarwa.

Sai tsakiyar dare suka isa kuma acikin daren aka tara duk dattijan garin dasukasan su bulama da asma’u tun zuwansu garin da duk abinda yafaru.

Kuka sosai alhaji babaye yayi dayaji irin rayuwar da ‘dan uwansa da matarsa sukayi saidai kuma yanzu babu abinda yakeson gani kamar ‘yar dan uwansa.

Daga alhaji babaye sai khaleefa suka koma sbd khaleefa jirgi zaibi yakoma bazai iya tafiyar ruwaba kuma sauran binciken da tabbatarwar idan sun haduda rumanah zasu qarasa tabbatarwa.

Koda suka koma gida sosai hajiya yakurah taso bin khaleefa suje tare saidai maigidanta yace tabari yadawo daga China saisuje gabaki dayansu da haka khaleefa yatafi sbd ciwo dake neman kwantar dashi sbd bai qaramar wahalaba yasha a tafiyar.

A yau saqon haroun ya iso gareta an kammala aikinta.
Shiru tayi bayan fitar Jakadiya sbd tunanin yaya maheer zai karbi zancen sbd dole tana buqatar aiwatarda abinda tayi niya dan tanaji jikinta yasaki sosai jininta qarewa yakeyi sbd tsananta da abin yafarayi ajikinta sbd jinin dataqi zubarwa har lokacin tasan daf take da rasa hankalinta dan wata irin zabura dake kamata yanzu duk da tana qoqarin boyewa ammy da maheer tanaji abin yafara cin qarfinta.

Kallon abeel dake kwance jikinta tayi zatai magana jini ya digo ta hancinta ya sauka kan fuskarsa tayi saurin goge masa tareda ajiyesa ta dauki tissue tana dafe kanta da jiri ke juyawa dashi.

Durqusa gurin tayi tana fidda wani irin nishi cikin azaba tsawon mintuna kafin tasamu taci qarfin abin tana kiran sunayen Allah harya lafa kafin tayi wani yunqurin miqewa ya turo qofar dakin yashigo cikin nutsuwa idanuwansa kanta yana kallon tissues din gabanta dasuke lalace da jini hakama hancinta zuwa bakinta duk jini.
Saurin goge hancinta tahau yi saidai kuma atake jinin yasake 6allewa ta rintse ido cikin wani irin hali tafara nishi mai wuyar fita.

Da wani irin gudu ya qaraso gareta tun kafi yakai hannunsa gareta idanuwanta suka fara qoqarin rufewa yayi saurin tarota jikinsa yana kiran sunanta da qarfi.Ganin tana neman fita hayyacinta yasa ya bude bedside drawer dinta yadauko maganin da negasi yabayar ariqa bata idan jinin yazo mata ya bude gabaki daya ya zuba mata abaki cikin tashin hankalin saidai jinin bai tsayaba amma idanuwanta sun bude tafara qoqarin tashi tana karbar tissue din dayake qoqarin kaiwa hancinta tace, +

Banda lokaci inason sanardakai abinda nake ashirin aikatawa ayau sbd banason na mutu abanza batareda na tsayarda abinda ke faruwaba…..

Wani irin tari tayi jini mai tarin yawa ya fito bakinta kamar amai
Atake ya rungumota abinda bai taba ba arayuwarsa hawaye suka gangaro masa yafara girgiza kai yana hanata magana..

Girgiza masa kai tayi awahalce tace,

Taimakeni na shirya muje mukawa qarshen matsalar sbd ‘yan baya su samu nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanarda mulkin adalci.

Kasa motsi yayi saidata saki kuka ahankali tana kallonsa cikin rawar murya tace,

Karka manta ka min alqawarin tsayawa dani dan kawarda matsalar data lalata farin cikinmu dana wainda basujiba basu ganiba.

Cikin wani irin hali yace,

Na miki alqawari amma banda sadaukar da lafiyarki ko rayuwarki meyasa z……

Rufe masa baki tayi cikin wani irin yanayi tace,

Mu barwa Allah zabi zai mana mafita.

Amatuqar wahalce ya taimaka mata ta shirya sbd tuni alummar mineelik da kewayenta suka hallara sbd mahimmin saqon daza’a bayyanar garesu.

Duk yanda yakeson daurewa kasawa yayi lokacinda zasu shiga inda dukkanin jama’arta zasu ganta jawota yayi ya rungume da qarfi cikin rawar murya yace,

Kisani har abada bazan saki hannunkiba zamu fuskanci duk abinda zai tunkaromu atare, ummu-rumanah bulama kece zuciyar maheer abdulshams so please fight this battle for my love…

Ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda zamewa daga jikinsa tana riqe hannun ammy dake hawaye gefenta Jakadiya dake gefensu tayi saurin miqawa ammy tissues ganin jinin yanason sake tsananta.

Ammy dakanta ta goge mata tana danne kukanta.

Murmushi tasaki tareda riqe hannun ammyn ta karbi tissue din tana goge hancinta zuwa bakinta da hannunta dake rawa sbd ko tsayuwa daidai bata iyayi abinda yafi daga hankalinsu kenan.

Sultan ma aranar da safe ta bayarda takardar sakinsa dan haka shima tuni ya fito ya halarci taron tareda sauran dattijawon masarautar duk da ayau jikinsa a sanyaye yake da abinda yake faruwar saidai a safiyar yau ‘din ya gana da dukkanin ‘yayansa dasuka zo dan halartar wannan taro kuma ganinsu ayau din da maganganunsu sun sanyaya jikinsa sunbar zuciyarsa da dana sani musamman maganganun maheer dayayi masa gameda mutuwar iyayen rumanah…
Hakan yasa ya ajiye dukkanin makaman yaqinsa akawo qarshen masifar duk da su sunriga sunbi sahu.

Tana fita ko ina yayi tsit dukkanin alummar gurin suka nutsu ahankali haroun yabada umarni nan take aka bayyanarda wata irin sabuwar karaga mai tsananin kyawu da kyalli mai daukar ido atake dukkanin jamar gurin mamaki da tsoro yakamasu musamman maheer dabaisan da hakanba yakalleta da sauri saiyaga tana qoqarin danne abinda takejine dan daidaita nutsuwarta yafasa maganar dayayi niyya ya damqe hannunta dake cikin nasa sbd har lokacin a tsaye suke taredasu ammy da jakadiya da masu tsaron lafiyarta.

Cikin wata irin budaddiyar murya sarkin fada haroun ya bude wata irin zungureriyar takarda mai daukeda tambarin masarautar mineelik dake daukeda saqon assultana yafara karantowa kai tsaye da qarfin muryarsa yanda kowa zaiji.”””” NI SARAUNIYAR MINEELIK UMMU-RUMANAH BULAMA AYAU SHA BIYU GA WATA NA BIYAR A SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NA SOKE KARAGAR MINEELIK DAN KAWO QARSHEN MULKIN ZALINCI INA GABATAR MUKU DA SABUWAR KARAGA GA WANNAN MASARAUTA…HAKA KUMA AYAU SHA BIYU GA WATAN BIYAR SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NI UWAR MAGAJI SARAUNIYA UMMU-RUMANAH NA SAUKA KAN MULKIN MASARAUTAR MINEELIK TAREDA ‘DORA SABON SARKI ABDALLAH ABDALLAH AMMED”” +

Atake dukkanin gurin yadauki wata irin kabbara da koke koken farin ciki da sbd wannan wani irin babban alamarine yazo musu na sauyi daga mulkin azaba musamman Abdallah Abdallah ammed mahaifin khaleefa mutum ne dazai kawowa rayuwarsu sauyi na adalci gashi shikansa baisanda zancenba.

Tsit aka sakeyi lokacin wasu irin majiya qarfin bayi kusan goma sha biyar suka ciccibo karagar mineelik Wanda keda wani irin girma tareda hularta.

Wani irin baro mai tsananin girma da fadi daukeda wani irin mahaukaciyar tukunta mai tsananin tiriri yaran negasi kusan su ashirin da biyu suka turo aka ajiye tsakiyar filin harabar.

Ta lumshe idanuwanta dasuka fara rufewa suna gani dishi dishi ta budesu daqyar ta iya ‘daga hannu ta bada umarni atake haroun yabada umarni aka ‘daga karagar aka saka ciki atake tafara nitsewa tana narkewa cikin ruwan dalmar tun tana gani dishi dishi sbd jinin daya balle hancinta atake idanuwanta suka rufe ruf ta yanke jiki ta zube gurin jini na qarasa balle mata ta hanci da bakinta.Saki jikinsa yayi sbd wutar data daukewa jikinsa da wani irin qarfi ammy ta jijjigasa tareda kiran sunanda da qarfi ya durqusa tareda jawota jikinsa ya dauketa gabaki ‘daya yabar gurin da ita. +

Anso tsayarda nadin sarautar amma haroun ya fitarda saqonta na gaba dake cewa duk abinda zai faru kar a tsayarda nadin dakuma takardarta tagaba dake cewa a raba mara masarautar biyu a rushe Rabin a gina masallacinda yafi kowane girma a qasar Ethiopia.

Hakan yasa aka cigaba da nadin yayinda sultan dake zaune har aka gama bai motsa daga inda yakeba saida aka watse aka gano ya rasu zaune agurin gakuma jinin da aka ganin ya digo daga hancinsa.

Lokacinda su negasi suka rufu akanta dan ceto rayuwarta alokacin ne aka zo da saqon rasuwar sultan Wanda ya girgizasu ya qarasa wargaza dukkanin sauran nutsuwarsu musamman ammy data kasa riqe kukanta maheer yayi saurin rungumeta yana riqe nasa hawayen sbd Allah yasani yana qaunar mahaifinsa duk mugun halinsa sbd koyaya ya zama mahaifinsane.

Cikin qanqanin lokaci rasuwar sultan da halinda assultana take ciki tareda canza karagar mineelik suka yadu ‘yan jaridu da kafafen yanda labarai sukaiwa masarautar wani irin dandazo ana yada abinda ke faruwa.

Dukkanin iyalan marigayi abdulshams sun halarto cikin tsananin baqin cikin wannan rana data riskesu musamman ‘yayan marigayiya adama dasuke ganin sun rasa uwa da uba.

Da maraice akai jana’izarsa inda dubban alumma na nesa dana kusa suka hallara inda yawan jama’arsa yasa maheer jin sanyi sanyi aransa tareda yiwa mahaifinsa adduar samun rahamar Ubangiji.

Duk damuwar dayake ciki ta halinda rumanah take ciki bai koma gurinta ba sai dare bayan an watse.

Kai tsaye sashen ammynsa ya nufa inda ya tararda ita tareda sauran ‘yan uwansa ya qarasa kusada ammyn ya zauna yana kallonta cikin nutsuwa da tausayawa ya riqo hannunta ahankali ya iya furta,

Allah yaji qansa ammynah.

Kwantarda kanta tayi kafadarsa tareda cewa “amin” da muryarta data shaqe kafin ta ‘dora da fadin,

Kaje gurin rumanah dan sanin halinda take ciki duk da meenah da jakadiya na gurinta.

Jinjina kai yayi jikinsa na qara sanyi da tuno wani tashin hankalin dayake ciki.

Lokacinda ya isa sashenta har lokacin bata farfado ba sai jinin daya tsaya Wanda suke sakaran jinintane yayi matuqar qasa sosai.

Zaune ya kwana gabanta yana mata addua cikin wani irin hali dabai ta6a tsintar kansa aciki ba.

Washe gari koda akaga bata farkaba hankula sukai matuqar tashi musamman da jikinta yayi wani irin fari fari Kore Kore ga ‘yan jarida dasuka kasa suka tsare a masarautar sunason ganawa da sarauniyar data kafa sabon tarihi a qasar daba tataba.Duk wani kalar likiti na turai da gargajiya an nuna qwarewa amma abu yaci tura gashi alamunta na sake 6aci ranar da akai uku aranar gabaki dayansu suka tattara suka nufi Georgia..shi,ammy da jakadiya data samu ‘yancin rayuwarta itama sai sauran ‘ya’yan da kowace takoma inda take aka bar sabon sultan dan gabatarda mulkinsa cikin aminci. +

Suna sauka kai tsaye motar asibiti tazo daukarsu aka wuce asibiti dasu cikin tashin hankalinda yafi na farko sbd saki jikinta daya farayi.

Matsayinsa a babbar asibitin garin yasa ana isa da ita dukkanin likitocin dake nan suka taru aka fara qoqarin gano matsalar cikin gaggawa cikin tashin hankali da mamakin yanayin matsalarta sbd basu taba cin karo da irin hakanba.

Ammy daqyar ta iya zama gida saidai gabaki ‘daya hankalinta da damuwarta na asibitin gabaki daya cikin kwana ukun ta rame tayi wani irin sanyi ko doguwar magana bata iyawa.

STORY CONTINUES BELOW

Har gari ya waye likitoci na kanta duk wata dabararsu da qwarewarsu sun nuna dan ganin ta farfado saidai Sam bata farfado ba saidai fatarta data fara komawa daidai sbd jinin da aka saka mata kusan leda biyu hakan yasa suke sakaran idan fatar ta gama komawa daidai ta farka.

Daqyar yake iya hadiye yawun bakinsa sbd tsananin bushewar bakinsa da maqoshinsa,

Duk wata nutsuwarsa da tunaninsa sungama barin jikinsa idanuwansa tuni suka qanqance ko gani bayayi sosai da idonsa dukkanin abokanan aikinsa sun tausayawa halinda yake ciki shiyasa suma gabaki daya hankalinsu tashe yake da ganin ta farfado ‘din.

Khaleefa aranarda suka wuce aranar yasauka Ethiopia ya tararda abinda ke faruwa kasa kwana yayi duk da rashin lafiyarsa washe gari yabi jirgin asuba sbd yasan aminin nasa na tsananin buqatarsa.

Har yamma bata farkaba khaleefa ma saukarsa garin alhaji babaye yakirasa sbd news din dasuka gani gameda abinda yake faruwa a qasar nan yaqara yasanardasu abinda yake faruwa nan hankalinsu yayi matuqar tashi suka fara shirye shiryen tahowa cikin gaggawa.Qarfe goma na dare ta bude idanuwanta dasukai wani irin shigewa sukai nauyi da ja.

Atake dukkanin likitoci suka sake hawa kanta cikin gaggawa da nuna qwarewa tareda fatar samun nasarar sanin matsalarta.

Kasa miqewa yayi sbd saki ga gabobin jikinsa sukayi sbd fargabar abinda za’a fada masa saidai khaleefa ne ya dafasa yana jinjina masa kai alamar qwarin gwiwa ganin halinda yake ciki.

Wasu sabbin dogayen hours suka ‘diba suna qoqarin gano matsalar wadda suka gano daga qarshe wadda tayi mummunan ‘daga hankalinsu haka suka ringa fitowa jiki amatuqar mace zuciyoyinsu ba dadi sbd dukkanin hotunansu da test test dinsu sun tabbatar musu da abu ‘daya.

Dr Edward ne yafito qarshe yana zare glasses dinsa yakalli maheer da khaleefa yace,

Can we talk in my office pls..

Tashi tsaye maheer yayi tareda kallon qofar dakin da take yakalli Dr Edward din yana rintse idanuwansa da abinda za’a fada masa yace,

Just tell me dr Edward I c……..

Dafasa Dr Edward yayi cikin tsananin tausayi ganin daqyar yake iya bude bakinsa yayi magana cikin sanyin murya yace,

I’m really sorry Dr m.a shams matarka ta rasa gangar jikinta bazata taba gara aikiba ma’ana tanada rai tana gani tana numfashi tanaji saidai bazata iya motsa jikintaba ko kadan bare magana har abada.

Wani mugun jirine ya dibesa khaleefa da Dr Edward sukai saurin nufarsa zasu taresa ta rigasu taresa cikin kulawa da tausayawa.

Khaleefa ne yakalleta cikin mamaki Dr Edward kuwa jinjina mata kai yayi alamar ta kula da maheer din yana buqatarta fiyeda koyaushe.

Shikuwa idanuwansa na ganinta baisan sanda ya sake fadawa jikinta yana qoqarin tsaida hawayensa saidai Sam basu tsaiduba saida suka zubo ya sake qanqameta yana cewa,

Suhailat please pray for me wlh zuciyata zafi takeyi I just can’t live without her sbd wannan ma baida banbanci da mutuwa agareta. 4

Murmushin tausayinsa tasaki cikin sanyin murya tace,

Insha Allah zata warke
Nayi maka alqawarin zamowa majingini agareka duk lokacinda kake buqatata wannan alqawarin yananan haryanxu kuma nayi alqawarin cika makashi har qarshen rayuwata kuma zan tayaka jinyarta harta ji sauki sbd sonka shine qaddarata maheer abdulshams..

‘Dagowa yayi kalleta da idanuwansa itama hawayen takeyi tana murmushi ahankali yaji wata irin soyayyarta mai tsafta tashiga zuciyarsa akaro na farko cikin wata irin rawar murya yace,
I love you suhailat sbd kece hasken rayuwata dakike tallafoni koyaushe.
Wasu hawayene suka gangaro mata ta rintse ido tana kwabar zuciyarta dake neman shegala da kamansa datasan ta samesune sbd nuna qaunarta ga rumanah saidai matuqar qaunarta ga rumanah zata jawo masa soyayyar mijinta to tabbas ta shirya samun soyayyar mijinta ta hakan.

Duk yanda ya ‘daga hankalin likitocin asibitin akan abinda sukace dole ya dangana yadauki qaddara sbd result din dayane.

Ko ammy saidata kwana ta yini tana kukan halinda rumanar ke ciki da Wanda yashiga sbd gabaki daya ya birkice musu ko abinci sai ammyn tayi kuka yake iya shan abu mai ruwa ga suhailat data zamo batada wata hidima saita kula da dukkaninsu sbd sundawo gida. 1

Idan yazo ya zauna kusada ita haka zai riqe hannunta cikin nasa ya qura mata ido
Itadai hawayene kawai ke iya gangarowa ta gefen idonta musamman idan ammy tasata gaba tana kuka kokuma shi idan yazo ya zauna yasaka gaba ya qura mata ido tana iya hango mawuyacin halinda yake ciki.Ranarda su hajiya yakurah suka iso aranar kuka yadawo sabo ganin halinda ‘yarsu dasuke ‘dokin gani take ciki…

Ko alhaji babaye dake dattijo saida ya zubarda hawayen baqin ciki da farin ciki.

Akwance take itama amma hawayene keta bin gefen fuskarta suna zuba Wanda hakan yaqara bawa kowa tausayi.

Duk da akwai Carolina sosai suhailat ke wahala sbd lalurar rumanah din.

Kusan satinsu alhaji babaye biyu kafin shi ya koma yabar haj yakurah dataqi dawowa tana jiran isowar mijinta dazasu tafi tareda rumanah sbd gwada nasu na addinin.

Satin alhaji babaye daya da tafiya alhaji mukhtar mijin haj yakurah ya iso kallo ‘daya yayi mata yagano lalurarta Allah takeson akomawa sbd lalurace ta iska nan take suka yanke shawarar tafiya da ita maheer kai tsaye ya nuna rashin amincewarsa
Saidai ammy dataga yana mutuwar tsaye kullum sbd lalacewa da rayuwarsa ke nemanyi dan ko aiki bai taba fitaba koyaushe yana gida ga suhailat data zamto abar tausayi gurin qoqarin kulawa dashi da rumanah duk ta rame tausayinta da qaunarta yasa kai tsaye ta zaunar dashi cikin nutsuwa ta fahimtar dashi kuskuren dayake jefa rayuwarsa da iyalinsa ciki dan haka yabar rumanah aje da ita ya tsaya ya gyara mu’amalarsa da rayuwar aurensa da suhailat.

Sosai jikinsa yayi sanyi kuma yasan matuqar yanason gyara rayuwar iyalansa ta inganta saiya boye soyayyar rumanah kwata kwata dan haka zai danne Zuciyarsa yafara daga yanzu.

Da haka ya amince aka tafida rumanah din amma hardashi suka tafi saidaya kwana biyu yadawo dan qoqarta gyara mu’amalarsa da suhailat.

Koda yadawo su ammy da jakadiya tareda abeel sun komawarsu Libya dan haka gidan dagashi sai suhailat sbd su amah ma suna Mali tabarosu dama itakadai tazo.

Aranar daya dawo lafiyayyan tarba tayi masa cikeda Dari darin yanda zai dawo yayi rayuwa a inda babu rumanah.

Ganin yanda take kama kanta dashi duk sai yaji ya muzanta ya tattaro jarumtarsa ya danne abinda ke ransa ya riqo hannunta ahankali tareda jawota jikinsa yana kallon fuskarta dake kallonsa yasaki qayataccen murmushi yajata suka zauna bakin gadon dakinta daya shigo yasameta hartayi shirin bacci zata kwanta.

Kallonsa takeyi tanason gano damuwarsa saidai takasa ganin komai sai murmushin dayake sakar mata
Wani irin sanyi da farin ciki taji na shigarta ahankali kenan kalamansa daga zuciyarsa suka fito lokacinda yafada matasu.

Rungumesa tayi da sauri tana sakin hawayen farin ciki ta murmushin jin dadi.

Dagota yayi tareda zare mata riga yana murmushi yace,

Banyi wankaba so yau kece zakiyi wannan aiki.

Noqewa taso yi tana murmushi yayi saurin riqeta yana kallon cikin idonta ya girgiza mata kai ahankali yace,
Don’t make that mistake again suhailat.

Kallonsa tayi tareda jinjina kai takama hannunsa ta nufi hanyar toilet dinta dashi suka shige.

Aranar wata irin rayuwa suka gudanar data mantarda suhailat dukkanin damuwarta ta dah inda sukai alqawarin dora sabuwar rayuwar aure ta fahimta,soyayya qauna da aminci atsakanin su uku da ‘yayansu daga yanxu.

**
Ahankali ake gudanar da adduoi da sauran abubuwan addini tareda sauke al-qur’ani da sadaka ana fatar samun sauqi.

Kulawa sosai da wata irin qauna da soyayya suke mata kaf zuriar banda zuriar gidansu aqeel data gama tarwatsewa babu wani nakamawa acikin zuriar gidansu shiyasa koda sukaji ‘yarsu bulama tadawo kuma a nakashe kota kan zancen basubiba.Su kuwa haj yakurah tamkar ‘yar data haifa da cikin ta takejin rumanah duk wata kulawarta da dukkanin hidimarta takoma ta rumanah shima alhaji babaye kullum saiyazo gidan sbd yayi yayi tabari rumanah takoma gidansa taqi yarda tabari. +

Watanta hudu a Nigeria yazo dubata babu adadi duk tareda suhailat suke zuwa Wanda itama tanajin farin cikin ganinsa da suhailat sbd ganin hankalinsa ya ‘dan kwanta sosai duk sukazo idan zasu tafi daurewa kawai yakeyi yakoma sbd alqawarin adalci daya daukarwa kansa.

Ammy kuwa kusan tamafi maheer din zuwa kuma takan dade idan tazo.

Ahankali tafara samun sauqi sbd wasu gurare dasuka fara motsawa ajikinta Wanda hakan ba qaramin farin ciki da qwarin gwiwa yasakasuba nan aka sake maida himma ga sauke al-qur’anai da sadaka da adduoi.

Ba’a rufa wata biyu da fara motsinta ba tafara magana ahankali har tana iya tashi zaune da kanta ta tashi.

Lokacinda wannan saqon ya iso masa aranar suhailat harda hawayen farin cikin ganinsa cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa tayi sbd Sam kasa boye farin cikinsa yayi.

Kafin sati biyu dukkanin kuzarinta sun dawo lafiya kalau saidai bata iya komai da sauri ko qarfi Wanda hakan shima ahankali zai dawo. 1

Washe garin ranarda umma yakurah da ammy suka fada masa samun lafiyarta yatafi wannan karon suhailat qin biyosa tayi sbd ganinta kusa zai hanasu nuna kewar junansu.

Sai dare sosai ya isa Wanda tareda khaleefa dazaije gurin nuratu sukayo tafiyar dole suka sauka masaukinsu kai tsaye sai washe gari suka nufi gidan guraren qarfe goma shima sbd khaleefa daya hanasu tafiya tunda safe.

A babban palo suka tararda su umma da ammy harmada Jakadiya da sabuwar mai rainon abeel suna ganinsa umma tayi murmushi sbd tanajin dadi da farin cikin yanda yake tsananin qaunar rumanah dinsu.

Ammy ma dariyar tayi masa inda aka gabatar musu da abincin breakfast saidai sunyi breakfast already.

Duk yanda yaso ganinta qin barin su kebe umma tayi qarshema anan palo tasa Nana aishat ‘yar autarta taje kairawo rumanah din tajima kafin yafito sanyeda dogon hijabi har qasa daya matuqar yimata kyau sbd wannan ne karo na farko daya ganta sanye dashi itama anan din takoya sakashi sai tanajin dadinsa.

Kasa ‘dauke mayun idanuwansa akanta yayi musamman yanda ta canza sosai takoma kamar ba rumanarsaba datasha wahalar rayuwa dan lokacin.

Wani irin murmushi yasaki Wanda shikadai yasan yayi abinsa sai ita data gani ta dauke kai tana gaidasu cikin yarensu sbd har gwara khaleefa yafara son koyar yaran Hausa sbd nuratu dayake yawan ziyarta shikuwa haryanxu yakasa koyan komai.

Koyaushe da turanci yake magana dasu umma da alhaji babaye hakama ammy.

Kwanakinsa uku amma Sam umma taqi barinsu kebewa hakan ya matuqar dama lissafinsa shiyasashi tattarawa yakoma gashi ko waya basayi bare yarage zafi.

STORY CONTINUES BELOW

Koda yadawo suhailat ta lurada bai cikin dadin rai da walwala saidai batai shishigin tambayaba tunda bai shiga haqqintaba.

Bayan sati biyu kai tsaye yakira alhaji babaye yasanardashi yanason rumanah tadawo tunda taji sauqi koda alhaji babayen yayiwa umma magana kai tsaye tace sai wani wata sbd zasuyi walima dakuma ‘yan shirye shirye.

Baisoba amma sbd ammy data basa hakuri saiya bari din badan yasoba.

Hidima sosai da gyara irin nasu na asalin ‘yan Maiduguri.

Taron biki sosai akayi tamkar yanxune zaa daura mata aure akai walima da yinin biki na alfarma inda ko nanma ‘yan jarida basuyi qasa da gwiwaba sunxo ganawa da tsohuwar sarauniyar qasar Ethiopia saidai maheer daya bada gargadi mai qarfi akan karta kuskura barin kowa yadauki hotonta ko fira da ita.

Lokacinda nuratu ta iso gurin bikin sosai sukayi farin cikin ganin juna dakuma auren nuratun da khaleefa keson yi.

Irin gyaran da akai mata da shirin da akai mata ita kanta burge kanta takeyi ga wani irin qamshi daya kama jikinta. 1

Dukiyarta kai tsaye tace suci gaba da kulawa da ita tabar musu halak malak bata buqatar komai.
Ranarda zasu tafi ammy ce da jakadiya sai umman da matar alhaji babaye da yaransu ‘yan mata da nuratu suka raka rakasu har Libya tareda dukiyar aure mai tarin yawa inda sukai kwana biyu suka juyo suka barota. +

Sabuwar rayuwa ta bude a Libya inda nanma ammy wani gyaran ta dora ranarda tacika kwana shida cif aranar aka sai mata ticket ta wuce batareda abeel ba.

Qarfe uku na yamma jirginta ya sauka suhailat ce tazo daukarta sbd ogan na hospital gurin aiki baimasan aranar zata dawoba ammy suhailat kawai tafadawa shiyasa tazo daukarta.

Cikeda farin cikin ganin juna suka rungume juna suhailat na mata sannu da zuwa da cewa,

Where is my abeel?

cikin farin ciki ta amsa tana cewa,

Ammy ce ba ruwana.

Wani gida na daban taga sun nufa Wanda yafi nada girma sosai tun a harabar gidan ta fahimci kowaccensu nada wadataccen gurinta yanxu.

Da gudu su amah suka fito suna mata oyoyo ta riqe hannun fammah data fara mantata tayi kissing goshinta tana cewa,

Famman mum ‘dinta.

Babban lafiyayyan qaton palonsu suka shiga nan suhailat ta rakata da luggage dinta har cikin dakinta dake daukeda parlour da two bedrooms aciki ga komai nata is white.

Bayan fitarsu wanka tashiga tana fitowa tayi sallolin dake kanta dasu magrib da akayi tana gamawa ta shirya cikin pencil skinny jean blue daya kama cinyoyinta da White shapeless top sai White club scarf data rufe kanta dashi ta fito fiddo wayarta daga handbag dinta taga misscalls dinsu umma da ammy harma dana nuratu tafara kiransu daya bayan daya tana cikin wayane da ammy suhailat tashigo tana murmushi itama cikin adonta na wani black straight skirt daya fiddota da red chiffon top gashinta daure saidai bata saka hula ba tace,

kiyi sallar ishai kifito muyi dinner already your ango is home.

Murmushi tayi tana cewa,

Ok ganinan zuwa.

Sallar ishai tayi tana gamawa ta gyara scarf dinta tareda fesa turare da humra mai sanyin qamshi ta fesa mouth freshner abakinta ta dauki wayarta ta fito.

Zaune yake kan dining din shidasu amah sai suhailat dake qoqarin zama ta gama zuba nata abincin
Ta bayansa yajiyo wani irin qamshi ya lumshe ido ya bude dan tabbas kodata canza turare kusancinta sanannene a zuciyarsa tana qarasowa gabansa abincin daya saka bakinsa ya sarqesa ya rufe baki yana tari da sauri suhailat tabashi ruwa tana dariya tace,

STORY CONTINUES BELOW

Easy karka illatamin kanka she’s really here ba gixo bane.

Karba yayi yasha yana watsa mata wani kallo yace,

Dake aka hada baki right…

Murmushi tayi tace,

Ba ruwana ammy ce.

Juyowa yayi ya kalli inda take cikin wani irin shauqi da tsananin soyayyarta dake fizgar zuciyarsa duk yunwar dayakeji ta bace.
Ita kuwa abincinta takeci hankali kwance duk da zuciyarta rawa takeyi sbd irin kallonsa datakeji yana yawo ajikinta.

Barin dining din yayi sbd zai iya bada kansa yakoma kan kujerun palon ya zauna yana canxa channel zuwa news duk da dai Sam baimasan meyakeyiba sbd halinda zuciyarsa take ciki.

Bayan sungama Carolina ta tattara gurin suhailat takaisu amah daki sukai duk abinda zasuyi suka kwanta saidata tabbatarda sunyi bacci tafito lokacin ba kowa palon kowa na dakinsa.

Dakin rumanah ta nufa kai tsaye tayi mata saida safe tareda sanarda ita kwana biyu biyu zasu riqa yi tace mata tou.

Tana sane ta sharesa taqi zuwa gurinsa ta tube ta dauko rigar baccinta zata saka saidata daga hannuwanta zata saka taji an zare towel ‘dinta da sauri ta juyo Ashe amatse yake da ita tana juyowa sai a jikinsa atare suka sauke ajiyar zuciya yana zare rigar hannunta yayi jifa yana kallon cikin idanuwanta dashi itama take kallo.

Jikin wardrobe ya matseta yana cigaba da kallonta zuciyarsa cikeda wani irin farin ciki ahankali yace,

Wani irin sone zuciyata ke miki ummu-rumanah bulama.

Kunnensa takai bakinta cikin wani irin salo tace,

Irin sonda ummu-rumanah kewa maheer abdulshams..

Wani irin murmushi yasaki tareda hade fuskarsu sbd tsikar jikinsa data tayar masa ya dora bakinsa kan nata yace,

I love you ummu-rumanah bulama.

I love you more maheer abdulshams.

Hade bakinsu yayi suka saki numfashi atare cikin tsananin kewar junansu ya cirata suka isa gadonta ya zura hannu ya kashe kashe wuta. +

Washe gari da wuri ya tashi yayi shirin office bayan sun gama lalacewarsu har gurin wanka.

Atare dukkaninsu sukayi breakfast kafin shiya fara fita tukuna yaran sai suhailat data futa qarshe.

Yaso dawowa gida da wuri amma sbd dorarta zaman lafiya da qauna tsakanin iyalinsa yafasa harsaida lokaci yayi yadawo.

A ranarma a dakinta suka bajewarsu saidai duk yanda yaso qin latti saidayayi sosai.

Watanta shida da dawowa tafara laulayin ciki Wanda take samun kulawa sosai daga garesu har Allah yasauketa lafiya tasamu ‘yan biyu mace da namiji.

Zaman lafiya kwanciyar hankali tareda aminci da qaunar juna mai cikeda fahimta suke gudanarwa tareda girmama juna. 1

ALHMDLLH nan nakawo qarshen tarayya da yardar Allah masoya ina miqa godia sosai sbd wlh yawanku bazai bari na iya batokuba.
Kusani dai mamuh takuce kuma natane. 4

Idan nayi kuskure ko mantuwa to kuyimin uxuri Allah yabamu ikon daukar darasin ciki.

FAHIMTARWA…
Idan marubuci yayi rubutu za’ace bai San abu ba baiyi bincike akan abu ba amma yaje yarubuta sbd shirme da rashin sanin meye rubutu..

Tou kuma idan mutum yayi binciken yarubuta yanda abin yazo ace baida ilimi..

Labarin tarayya yaxone akan tun asalinsu ba musulmai bane akwai kafurci jahilci ataredasu Wanda hakan duk shine silar komai dan haka dole sai an bayyanarda jahilcinsu da kafircinsu ta hanyar sunayensu da ayyukansu yanda labari zai tafi daidai…..ga masu cewa sunayen ciki basu halastaba kenan…
Masu cewa babu addini,babu riqo da addua da basu komawa Allah ba kuma ta yaya zasuyi hakan bayan anbayyanar dasu marasa sani acikin labarin idan lokacin yi da amfani da hakan yakai ai za’a sakane… dan Allah muriqa duba asalin tsarinda aka ‘doro labari mu riqa binsa daki daki dan sanin abinda zamu riqa cewa. 2

Nagode Allah yaqara sadamu gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *