GAMAYYAH CHAPTER 4

GAMAYYAH







CHAPTER 4






Bayan rasuwar amnah sosai suhailat tashiga damuwa shikuma gashi bai iya ya ake lallashi ba bare
Iyakacinsa idan zai fita yanasaka yin breakfast idan yadawo suyi dinner sbd bai cika lunch agidaba.
Hakadai ta dangana tacigaba da rainon sabon cikinta.

Sultan yayi yayi yaqara aure yamaqi dawowa qasar shiyasa yadauki mataki kaitsaye akansa.

Sultana tashiga damuwa matuqa jin amnah ta rasu batareda sun ta6a ganinba saidai a hoto kawai gashi tanason zuwa amma sultan yasa doka.

Jakadiya kuwa sosai tafara shirya shiryen na kullum tana sashe sashe duddubawa cikin dubara sbd sotake saita ringa fahimtar halayyarka sbd kar asamu magaji ta macenda batada nutsuwa ko ma’ana.

Kullum cikin kwantarwada suhailat hankali sultana take hardai taga ta warware itama hanakalinta ya kwanta.

Lurada jakadiya sultana tayi ta kalleta bayan ta kori dukkanin bayinta dake sashen sbd maganar datakesonyi da jakadiyar.

Rumanah ce kawai a bedroom din ammyn tana aikinta hankali kwance.

Cikin muryar bada umarni tace,

Inason sanin hukuncin da sultan ya yanke akan maheer sbd nasan me shirunsa yake nufi.

Sunkuyar dakai jakadiya tayi wani zufa ya tsatsafo mata cikin sanyin jiki da sanyin murya tace

Sultan yabada umarnin atanadarwa yarima sa dakoki har biyar akillacesu zai dawo bazai komaba yanxu sai ansamu qaruwa daga garesu.

Tashi zaune sultana tayi cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da takaici taringa maimaita innalillahi.

Kallon jakadiya tayi tana qoqarin ganin damuwarta bata rinjayetaba murya amatuqar sanyaye tace,

Har kin tanadesu ‘din?

Tukunadai ranki ya Dade saidai nima ina cikin tsananin fargaba da tsoron yanda zata kaya sbd aurensa ma ta yaya akasamu yayi bare yanxu mata har biyar.

Rintse idanu sultana tayi tareda budesu jajir tace,

Idan kin zabesu kafin ki gabatarwada sultan su ki gabatarmin dasu inason naga matanda wasu daga cikin jikokina zasu fito ajikinsu.

Jakadiya na fita ta bada umarnin abuga qararrawa atara mata dukkanin wata kuyanga dake masarautar.
Nan tafara dubasu cikin layi harbasa qirguwa sbd yawansu amma takasa samun ‘daya dazata ware duk wadda takalla saitaga komai gyara da kulawar daza’ayi mata batakai matsayinda yarima zai hada shimfida da itaba.

Da haka ta sallamesu tace gobe kowanne yayo wanka su sake zuwa subi layi.

Tana gama gyaran bedroom din tafito tazo gaban sultana ta durqusa cikin girmamawa tace,

Ammy nagama kinada buqatar wani abu?

Kallonta sultana tayi da idanuwanta dasukai jajir sbd baqin ciki ta girgiza mata kai.

Ganin halinda ammyn take ciki yabata tsoro ta miqe hartakai qofa ta waiwayo cikin damuwa murya asanyaye tace,

Saida safe ammy.

Asanyaye ta isa dakinsu ta tararda daga mamani har nuratu basu dawoba ta tube taso watsa ruwa amma jin batada gajiya kuma batai wani aikin wahalaba tayi kwanta

Tana qoqarin juyawa nuratu tashigo amatuqar gajiye ta zauna bakin ‘yar katifarta tana cewa,

Rumanah wlh tsufa da wuri zai kamani sbd wahala.

Murmushi rumanah tasaki ahankali kafin ta tashi zaune tace,

Me kike gudu da tsufa da wuri?

Harararta nuratu tayi tana zame kayanta tace,

Ke kuma mekike yiwa sauri da tsufa?
Nifa rumanah banason tsufa da wuri sbd bazan ta6a cire rai daga hangowa kaina wata irin kyakkyawar rayuwa,
Ke nifa har mafarki nakeyi nazama wadda tafi kusanci ga Wanda wai zai mulki masarautarnan anan gaba,
Kuma kinsan menene?
Mace nake gani amafarkina koda yaushe saidai adon zinarai dake jikinta tana hanani ganin fuskarta….

Mamani dake shigowa tayi saurin qarasowa ta riqota tana washe dukkanin haqoranta tace,

‘Yarda zaki haifawa yarima ce……Fusgewa nuratu tayi da qarfi tana cewa, +

Barni da zancenki mamani koyaushe bakinki baya tsayawa mmatsayinsa..

Sake washe baki mamani tayi tace,

Nuratuna dama nasan tuntuni jikina nabani kece zaki fitardani cikin wannan qasqantacciyar rayuwar,
Jikina nabani kece za’a zaba amatsayin sa ‘dakar yarima…..

Dariyace taxowa rumanah tayi saurin rufe baki sbd gudun masifa da balain mamani dazata iya kwana tana surfa mata.

Cikin takaicin halin mahaifiyarta nuratu takalleta tace

Lallai mamani bakya sona tunda harkike fatar nazama baiwarda za’a riqa kwana dani ina haihuwa ana karbe ‘yayan.

Cikin saurin mamani tace,

Kibar maganar baiwa daga ranarda kika hada shimfida dashi kintashi daga baiwa sbd duk Wadda ta haifo magaji sultan ya ‘yantata daga ranar kuma ita za’a miqawa matsayi dakuma kujerar zaman uwar sarki sbd tariga ta haifo sarki,
Duk Wanda taso nadawa yayiwa danta riqon qwarya shi zata nada har ‘danta ya girma abasa kujerarsa,
Idan kika haifi namiji nuratu babu Wanda zaki bawa riqon kwarya kece zakiyi mulkin da kanki,
Kece zaki hau kujerar sarauta da kanki,
Kece zaki mulki dubban ‘daruruwan sarakuna da daulolinsu,
Kece zaki zama mace ta farko dazatayi mulkin wannan masarauta da aka tsani haihuwar mata…..

Kasa riqe dariya rumanah tayi tasaketa tana kallon mamani data watso mata mugun kallo tayi saurin hadiye dariyar.

Nuratu ma dariyar tasaki tana kallon mamani kafin takalli rumanah suka saki wata dariyar.

Mamani tayi mugun hasala tayo kan rumanah nuratu tayi saurin riqota tana cewa,

Haba mamani nah kece fa uwar sarauniya nuratu kuma kakar magajin sarautar dariyafa kawai mukeyi ta farin cikin wannan mafarkin naki mai dadin gaske kokuwa ‘dayar mamar magajin sarauta.

Dariya suka qunshe suna kallon juna suna kallonta.

Ganin sun maidata mahaukaciya yasa qyaci ta fice ahasale.Bayan fitarta rumanah taja abun lullubewarta tana murmushi tace, +

Nuratu kinfa karyawa mamani gwiwa daga kawai tana mana fatar samun jin dadi da ‘yanci idan kika zama sarauniya…. 1

Kallonta nuratu tayi cikin tsananin sanyin jiki tace,

Rumanah ke kinamin fatar nazama baiwarda za’a riqa kwana da ita tana haihuwa Ana karbe yayan idan nazama haka me naqaru dashi arayuwata bayandai ta tabbata naza baiwa tahar mutuwa…

Qarasowa da sauri rumanah tayi ta rungumeta ganin hawaye na zubo mata tace,

Nuratu bana miki fatar wannan rayuwar ko amafarki bare afili,
Keda mamani kune ‘yan uwana kullum fatana da adduana musamu kubuta atare mukoma ga asalinmu domin kuwa saimun koma asalinmu zangano nawa asalin.

Cikin sanyin murya nuratu tace,

Rumanah bawa baida ra’ayin kansa ko abinda yakeso sai Wanda uwayen gidansa suka yanke akansa,
Shin kina tunanin qaddara zata iya zuwa kaina aza6eni cikin masu zuwa shimfidar yarima?

Girgiza mata kai rumanah tayi cikin son qarfafata tace,

Insha Allah bazamu ta6a wannan rayuwarba nuratu.

Rumanah ammy bazata ta6a bari kiyi wannan rayuwarba saidai ni banada tabbaci saidai Allah ya dubi rashin gatana.

Jiki sanyaye zuciya fal da tunani da zullumi suka kwanta har mamani tadawo cikin dare ta kwanta babu Wanda yayi bacci acikinsu sbd tunani.

Washe gari fuska ‘daure mamani ta tashi babu Wanda ta amsa gaisuwarsa acikinsu qarshema kan rumanah taso sauke haushinta Dan har marinta tayi daga gaisuwa.

Cikin sanyin jiki ta share hawayenta tareda girgizawa nuratu data bude baki zataiwa mamani magana kai tareda sakin murmushin dole mai ciwo kafin ta kammala shirinta ta fice tana cewa,

Natafi'”””cikin sanyin murya.

Kodata isa sashen part ammy cikin sanyin jiki tafara aikinta har qarfe goma tabuga lokacin ammy ta tashi
Kanta qasa tagaida kafin tahau gyaran dakin cikin rashin walwala da rashin kuzari sbd duk lokacinda mamani tayi mata Abu abin na taba zuciyarta ganin batada wasu ‘yan uwa kamarsu tunda sukadaine nata.

Ammy sosai ta lurada rashin walwalarta ta danne tata damuwar cikin kulawa takira sunanta.

Amsawa tayi tareda barin gyaran gadon datakeyi tazo gabanta ta durqusa kanta na qasa. 1

Qare mata kallo tayi taga yanda jikinta ke ‘Dan rawa tace,

Rumanah meya faru dake?

Mayarda hawayenta tayi cikin qarfafa muryarta tace,

Bakomai ammy.

Sam batason takurawa rumanah shiyasa ta kyaleta kawai.

Tundaga lokacin sabuwar tsangwana da muguwar tsana tashiga tsakaninta da mamani sbd gani takeyi itace take zugewa nuratu kunne akan tadaina wanka da tsafta sbd kar azabeta.

Duk yanda take daurewa kasawa takeyi saita kwana tana kuka sbd wani irin zagi da gori data sakota gaba dashi akan iyayenta dasuka rasu.

Tun tana boyewa tuni damuwa tabayyana ajikinta sbd ramar datayi.

Sultana duk datana cikin damuwar dawowar maheer dakuma hukuncin sultan Saida damuwar ganin halinda rumanah take ciki tadameta musamman ganin tana ramewa ta daina walwala kwata kwata ta mayarda kanta cikin bayi ‘yan uwanta duk wani aikin wahala tanayi Wanda yaqara hargitsata.

Duk yanda sultana tayi da ita tafada meke damunta ta nuna mata ba komai sbd idan tafada tasan azabardasu mamani zasusha zai iya sanadin rayuwarsu kuma bazai tsaya akantaba harda nuratu.

Jakadiya itace ta bincikowa sultana tsaf abinda ke faruwa da rumanah sosai ranta ya 6aci hartayiwa sultan Aiken abinda ke faruwa da rayuwar ‘yar amintaccen bawansa daya rasu saikuma ta dakatar sbd tasan hukuncinsa bazaiyi dadiba Dan rayuwarsuce ke lilo a sama kuma barinsu duniya tamkar barin asalin rumanah ne sbd mamani kadaice tasani.Qarfe biyar na yamma jirginsu ya sauka a qasar
Kasancewar ansan bayason rawar jiki da yawa yasa motoci uku kawai sukazo daukarsa da iyalinsa sai khaleefa dasuka zo tare bayan yazo gurinsu daga zuwa weekend yabiyosu suka dawo tare.

Tunda yafito ake zubewa ana gaishesa so daya kawai yadaga kai alamar amsawa hannunsa daya na aljihun wandonsa sai shades dinsa daya gyara.

Suhailat na gefensa ta saci kallonsa zuciyarta na nauyi sbd ganin tsantsar kyawu da kwarjininsa taji kishinsa na taso mata tayi saurin dauke kai tana gyara riqon handbag dinta .

Itada shine a mota ‘daya ‘dayar motar khaleefa dasu amah sai ‘dayar ta guards.

Koda suka isa masarautar tuni duk wani guard da manyan masarautar suka fito tarbonsa.

Cikin girmamawa ake zubewa ana gaidasa harya isa gaban mahaifinsa a hankali yasaki murmushin da iyakacinsa fuskarsata ya gaidasa sultana cikeda girmamawa da kewarsa.

Lokacinda isawarsu maheer ta isowa sultana sakin murmushi tayi cikin tsananin farin ciki kafin tayiwa wanda ya isoda saqon babbar kyautar yana ficewa suhailat dasu amma suka shigo part ‘din jakadiya na gaba.

Cikeda girmamawa suhailat taqaraso gaban sultana ta durqusa duk da cikinta daya fara girma ta gaidata.

Cikeda kulawa sultana ta amsa tana kallonsu amah dasuka zauna jikin mahaifiyarsu sbd rashin sabo dasu.

Tana kallon yaran tace,

Jakadiya aje asake dubowa part dinsu idan gyaran ya kammala sbd yaran sun gaji suna buqatar hutawa.

Washe baki Jakadiya tayi cikin girmamawa tace,

Allah yataimaki sarauniyar sarki kuma kakar sark ai tun asubar fari baiwa rumanah ta kammala duk wani gyara da’akasata a part ‘din daga part ‘din na yarima har part din gimbiya suhailat kuma kuyangi biyar nacan najiransu domin hidimarta data yara kuma anyi musu gargadin ko kallon part din yarima karsuyi bare tunanin shiga koda dasunan wanine ya aikesu.

Murmushi sultana tasaki tareda kallon suhailat tace,

Suhailat kuje kuhuta da yaran sun gaji sosai.

Miqewa tayi daidai fitowar rumanah daga bedroom din ammyn fuskokinsu suka sauka akan na juna daidai kuma shigowar yarima a palon na qurya Wanda qamshinsa yasasu juyawa qofar atare.

Saurin durqusawa rumanah tayi tareda sunkuyar dakanta ta gaidasu atare batareda ta bambamtaba.

Suhailat ce kawai ta amsa cikin wani mugun sanyin jiki daya saukar mata lokaci ‘daya.

Ammynsa ya nufa da wani irin murmushi da duk duniya itakadai yakewashi
Cikeda farin ciki da murmushin daya kasa 6oye farin cikinta ta miqe tsaye yana zuwa ya rungumeta.

Cikin rawar jiki rumanah ta fice sbd wani kallo da Jakadiya ta watso mata.

Itama jakadiyar ficewa tayi hakama suhailat sbd tasan qaidane idan zai gana da mahaifiyarsa kowa ficewa yakeyi sbd itakadaice takejin doguwar maganarsa bayan ita ko suhailat datake matarsa baya doguwar magana da ita,su bayi ma ko masu hidimarsa tun tashinsa bayajin yata6a yiwa bawa magana.

Bayan fitarsu Jakadiya takalli rumanah data nufi qofar fita babban palon farko tana qoqarin barin part din gabadaya takira sunanta.

Dawowa tayi tana sunkuyar dakai sbd ko iya dagowa takalli suhailat bata iyayi sbd faduwar gaban datake ji.

Ki kama yaran ki rakasu part dinsu ta huta akula da yaran kar abari su dameta sbd yanayinta.

Jinjina kai tayi cikeda ladabi ta miqe ta ‘dauki fammah tareda riqe hannun amah kuma ta ‘dauki handbag din suhailat din tabi bayanta.Suna isa part din na suhailat dake kallon na yarima itace tayi saurin matsawa ta bude mata qofar tashiga. +

Babban parlour ne daya tsaru sosai da uwayen nairorin da aka zuba masa gurin tsarasa,
Royal cushions ne purple and golden komai na palon qyallin adon kalar golden din. 1

Duk haduwa da tsaruwar part din sultana saidataga wannan ma na suhailat yayi kyau sbd ita atunaninta baza’ataba samun part dinda yakai na sultana tsaruwa da kyauba saigashi na suhailat dinma ya tsaru kamarna sultana duk da tanajin labarin haduwa da tsaruwar part din adama kasancewarta itama ‘yar adoce sosai.

Kuyanginda aka turowa suhailat ‘din sukayi saurin shiga taitayinsu suna mata barka da shigowa.

Hannu kawai ta ‘daga musu tareda kallon rumanah tana nuna mata ‘dakinsu amah tace,

Kije kiyi musu wanka da ruwa marasa sanyi kuma bamasu zafi sosaiba ki shiryasu sai abarsu su huta kafin anjima suci abinci.

Tana gama fadar haka tamiqa mata hannu ta bata handbag dinta ta shige bedroom dinta

Dakinsu ta nufa dasu tayi musu wanka ta shiryasu harzata fito suka maqale mata takaisu gurin mum dinsu.

Bata saba da yaraba batama ta6a zama da yaraba tun tasowarta
Daqyar tasamu ta lallabasu ta fito.

Tana fitowa part din tasaki ajiyar zuciya sbd gabadaya a takure take sbd tsoro da gudun aikata laifi.

Kodata koma part din sultana a palon farko ta ra6e sbd ganin alamun har lokacin yarima naciki.

Gab da magrib yafito tayi saurin zubewa amma ko lurada akwai mutum shibaiyiba ya wuce yabar part din da qamshinsa.

Sum sum ta nufi palon ciki ta tararda ammyn zaune har lokacin ta durqusa cikin girmamawa tace,

Ammy a table za’a jera abinci kokuwa anan?

Murmushi tayi cikeda farin ciki tace,

Ajera a table kuma ayiwa maheer honey pancakes da sugarless drink sbd bayacin abinci mai nauyi musamman yanxu da daddare
And kihada masa fruitsalad with less apple sai kikai masa part dinsa kisaka a fridge din Palo nasan idan yafito sallar magrib bazai komaba sai dare.

Wani irin yawu ta hadiye na muguwar faduwar data sameta jin inda aka aiketa itadai batason tayi laifi komai qanqantarsa.

Ficewa tayi tafara kawo abinci a second palo tana jerawa a dining jikinta amatuqar sanyaye.

Honey Pancakes din tayi tareda kawowa dining daidai lokacin aka shiga sallar isha takoma tahado fruit salad ta zuba a glassbowl ta ‘daura a tray ta nufi part ‘dinsa qafafuwanta har wani hardewa sukeyi sbd yanda jikinta ke rawa.

Tana isa kallo ‘daya tayiwa guards din qofar ta juya tayi part din suhailat ta saka cikin fridge tareda sanarda kuyangin palon su sanarda suhailat ankawo fruit salad din yarima.

Kodata koma sallah taje tayo tareda komawa part din sultana tana saka kai da sallama dashi idanuwanta suka faracin karo yana cin pancakes din yana yiwa mahaifiyarsa murmushi.

Juyawa tayi da sauri sultana ta lurada ita amma sanin bayi basa zuwa idan yana guri musamman idan abinci yakeci kozaici yasa tabarta takomawarta.

Sai qarfe tara yabar part din sultana yanufi nasa
Yana zuwa ya tu6e yashiga bathroom dinsa da aka cika masa bathtub da ruwa masu matuqar qamshi da ‘dumi ya lumshe fararen oily eyes dinsa tareda kwantawa yana sake jin nutsuwa.

Allah yayisa mutum mai tsananin son rayuwa musamman tajin dadi saidai suhailat bata cika son irin wannan rayuwarba itakuma sbd sunada abubuwan dasuka banbanta ra’ayoyinsu saidai suna qoqarin ganin hakan baitaba rayuwar aurensuba.Sam bayason wanka a shower saidai a bathtub sbd yafison koyaushe yakwanta cikin ruwa tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin kafin yayi wanka,

Itakuma suhailat Sam batason wanka a bathtub saidai shower shiyasa haryau baisamu irin rayuwarda yakesoba sbd basu ta6a wanka atareba
Kwata kwata batama shiga toilet din bedroom ‘dinsa sbd ‘duk girma da fadin toilet dinsa bayason ganin ruwa ko yayane a qasan toilet dinsa itakuma idan tashiga toilet saita gama jiqa koina take fitowa.

A bangaren rayuwar aurensu kuwa Sam bata iya kwana a ‘dakinsa sbd komai dare idan suka gama abinda sukeyi a bedroom dinta take kwana sbd daga ita harshi kowa yafison ya kwana shikadai akan gado shiyasa yawanci zata raba dare a bedroom dinsa susha love dinsu kafin tayo dakinta.

Bayan sun jima da aure yazo yasaba baya iya kwana sai ajikinta amma itakuma dukkanin cikin datakeyi bayason kwanciya dashi hakadai yama cirewa ransa kota haihu basa kwana tare saidai su raba dare tare.

Bude idanuwansa yayi ahankali tareda kallon ruwan sbd qamshin dasuke fitarwa yakalli gaban mirror din cikin toilet din yagansu kaloli kusan guda goma masu kalar qamshi dabam dabam.

Saidayayi mintuna kwance cikin ruwan kafin yayi wanka ya fito daureda brown towel sabo qal ya tsaya gaban mirror tareda goge jikinsa ya fesa Hugo black men’s spray tareda gyara sumarsa da lafiyayyar qasumbar dake kwance a farar fatarsa fuskarsa ya fesa mouth spray mint flavour ya nufi closet ya dauko kayan bacci white colour yasaka tareda nufar makeken lafiyayyan royal bed dinsa dayake gyare da komai white da kusan eight pillows masu laushi.

Wayoyinsa ya kashe tareda ajesu a bedside drawer ya kashe wuta yabar bedside lamps masu duhun haske.

Kwashe komai tayi tasake gyare palon tayiwa ammy Saida safe ta nufi gefensu na bayi anatse.
Tana zuwa babu kowa a dakin ta kwanta bayan tacire uniform dinta tasaka tsohon uniform dinta sbd sune tamayar na bacci dama idan akaga uniform dinka sun mutu ana baka wani.

Kodasu mamani suka shigo idonta biyu amma ta lafe tanaji mamani nata fada tana zaginta
Ta share hawayenta tareda rufe ido tana danne kukanta.

Tundaga ranar kusan itace take wahala da suhailat da ‘yaranta sbd kullum ita sultana ke aikawa tana yiwa yaran wanka takuma kaimusu abinci ta Jere a dining safe rana dare saiya zamto ayyuka sunmata yawa danma babu laifi suhailat na sakar mata fuska sosai hakama yaran ba laifi suna yarda da ita ba kamar kowaba sbd kullum ita ake sawa ta daukosu takawo gurin sultana su yini kokuma gurin sarauniya adama

*
Sati ‘daya da zuwansu yarima yana zaune gaban sultan sbd kiransa dayayi cikeda girmamawa yake sauraren mahaifin nasa.

Cikin iko da umarni sultan yace,

Aure zaka qara maheer ibn abdulshams.

Shiru yarima yayi cikin tsananin mamaki tsawon lokaci harsaida mataimakin sultan yasake maimaita masa kafin ya ‘dago manyan oily eyes dinsa yakalli haris abdallah mahaifin khaleefa kuma mataimakin sultan yace,

Ina bawa sultan da mataimakinsa hkr sbd babu sha’awa ko burin qara aure arayuwata.

Wani shu’umin murmushi sultan yasaki tareda sake maimaita zancensa.

Shima maheer cikin girmamawa yasake maimaita amsarsa.

Kallonsa sultan yayi yasan sarai waye maheer saidai bazai barsaba zaiyi amfani da qarfin ikon mulkinsa dakuma ikonsa na mahaifinsa akansa.

Batareda yakallesaba yace,

Maheer ibn abdulshams zabin farkone nabaka na qarin aurenka.

Rufe idanuwansa yayi ahankali yana danne 6acin ransa yace,

Ina qara bawa sultan hakuri akan wannan buqatar tasa sbd idan nayi auren bansan yaya zan iya kwatanta adalcin kulada mata biyu ba.

Murmushi sultan yasake saki tareda kallon sarkin gida dake tsaye da sauri yafice ya nufi hanyar part din sultana.

Mintuna qalilan akayiwa Jakadiya iso tashigo tareda zubewa qasa tana gaisuwa.

Cikin mulki da nuna ikonsa yace,

Jakadiya aje yau awanke masa baiwar datafi kowace kyau ‘daya cikin biyar ‘din danace agyara akai masa daga yau aringa kaita kowane dare harsaitayi ciki,
Kuma daga yau an dakatarda matarsa zuwa gurinsa sai baiwarsa tayi ciki Idan ya kaucewa umarnina Jakadiya ki sanarda sultana zaarah na sauketa daga matsayinta na sultana kiyiwa adama albishir da samun sabon matsayi. 2

Yana fada ya miqe nan dukkanin su haris abdallah suka miqe yashigewarsa palonsa na musamman.

Cikeda girmamawa Jakadiya tace,
Angama sarki mai adalci.

Miqewa tayi da sauri ta fice sbd ganin halinda yarima yashiga sbd tsananin 6acin ransa da baqin cikinsa daya kasa 6oyuwa.

Miqewa yayi yafice kai tsaye part dinsa ya nufa tareda bawa guards din qofar part dinsa gargadin duk Wanda yayi motsi mai qarfinda harzai shigo part dinsa yadamesa arufesa tsawon shekara guda.

Jin haka yasa akayi sanarwa tuni kowa ya nutsu yashiga taitayinsa.

Jakadiya kuwa cikin qanqanin lokaci tasa aka tara dukkanin wata baiwa dake masarautar mai shakatun dabasu wuce sha takwas,sha tara zuwa ashirin da uku da hudu.

Koda aka kira duk suka halarta banda rumanah dake bedroom din sultana tana jera kaya acikin closet.

Duk iya damuwa da rashin mafita sultana naciki sbd tun binciken farko Jakadiya tace bataga wadda ta daceba gashi sultan yace yau.

Zaune kawai take amma hankalinta nakan halinda maheer yake ciki yanxu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *