GAMAYYAH
CHAPTER 9
Sheraton bamako hotel forth floor room 302 shine dakinsa da ako yaushe yake sauka idan yana qasar. +
Babban suite ne dayaji tsari irin na rayuwar dayakeso akoda yaushe.
Zama tayi a darare kan sofa tareda aje handbag dinta tana kallon tsarin dakin
Tun kafin ya isa yayi musu shopping kayan buqatarsu shiyasa yakalli agogon hannunsa yana 6ata fuska .
Knocking akayi ahankali sbd gudun kar ayi disturbing dinsu
Ga mamakinta ganin tayi ya miqe ya nufi qofar bayan tasan abaya budewa kowa qofa idan kagaji da knocking ne kashigo koka jira amma saigashi yatashi yaje yabude kuma hannu kawai yasa yakarba ya rufe qofar ya aje kan gado yafara 6alle ma6allan rigarsa.
Sauke kai tayi ganin murdadden jikinsa yafara bayyana
Yana gama tubewa ya nufi toilet.
Ya jima yana wanka kafin yafito yabude kayan ya dauki brush da toothpaste yakoma yayo brush yana dawowa ya fitarda turarrukansa da yayi shopping yayi shirin bacci bayan ya fitarda fararen kayan baccin daya siya yasaka ya fidda wayarsa yakira suhailat datun dazu take kiransa.
Miqewa tayi itama tashiga toilet tayo wanka ta fito daureda towel gashinta daure tsakiyar kai sbd karya jiqe gurin wanka.
Duk wani nauyi da kunyar duniya jitake kamar suna kanta sbd mayen kallon daya tsareta dashi tun fitowarta kuma lokacin waya yakeyi da suhailat.
Rigar bacci tagani kan kujerar gaban mirror tadan juyo takallesa ya dauke gira ‘daya yana cigaba da wayarsa.
Da mamaki take kallon turaren Prada royal pink for women da shine turarenta,
Ya akayi yasan sunan turaren datake shafawa gashi tamazo da nata suna cikin handbag
Wanda ya siyo din ta shafa ta dauki rigar tadaga batai mamakin ganin yanayin rigarba datafi kama da babu sbd tun a mineelik da ake sakata sakasu tasaba dasu. 1
Daga zaunen ya miqa mata hannu na musu tazo ya jawota ya ajeta kan cinyarsa ya zare ribbon ‘dinda ke ‘daureda gashinta gashin ya zuba yacigaba da wayarsa da suhailat yana cusa hannunsa cikin gashinta zuwa wuyan rigarta. 1
Cikin nutsuwa suhailat tace,
Zan kiraka gobe insha Allah gud night.
Aje wayar tayi tareda rintse ido da qarfi hawayen dasuka ciko mata suka gangaro kan fuskarta sbd yanayin yanda maganarsa ke fita qasa sosai ta tabbarda akwai abinda yakeyi da matarsa dan mum ta sanarda ita da rumanah yaje. 11
Share hawayenta tayi tareda miqewa ta nufi ‘dakin yaranta takwanta kusada fammah tareda jawota jikinta a hankali tace,
Ya Allah kabani ikon juriya da adauke kai kan abinda bazai shiga haqqinaba nima kodan karna barwa ‘yayana abin takaici da kunya. 3
Rumanah dake lafe jikinsa ta ‘dago takalli fuskarta dake kallonta qasa qasa da murya yace,
Kinsa matata ta ajemin waya for the first time banine na aje mata ba. 3
Wani irin lumshe idanu tayi Wanda yasashi kafeta da ido kafin yakai bakinsa kunnenta qasa qasa yace,
Are you trying to seduce me da wannan idon? 4
Qanqamesa tayi qarfi ba shiri sbd tsananin kunyar da maganar ta bata ya lumshe ido yana sake shigar da ita jikinsa yace,
Karki damu suhailat is kind hearted ba duka zata hanaki mijintaba. 1
Miqewa tayi da sauri zata bar jikinsa yasake dawo da ita ta fado masa ya matseta suna kallon juna fuskarsu daf da juna har dogayen hancinsu na gogar juna
Wani irin murmushi tasakar masa akaro na farko
Bakin dayayi smiling din yakalla kafin yakalli cikin idanuwanta da itama nasa take kallo ya daga mata gira ‘daya sai abin yasake sata murmushi
Daqyar ya furta nifa mijin aurene. 2
Rufe bakinta tayi da sauri sbd wannan karon murmushinta dariya yaso zama takalli cikin idanuwansa dasuka riga suka bayyanarda kasalar dayake ciki murya qasa qasa tace,
Sorry.
Murmushin gefen baki yasaki ahankali tareda ‘dan juyar dakai
Cikin shagala da murmushinsa da bata taba ganiba takai hannunta kan kumatunsa ta shafo Tana murmushin dake fitowa tun daga cikin zuciyarta. 2
Dafe hannunta yayi tareda dora hancinsa kan nata yana kallon cikin idonta ya dora bakinsa kan nata suka lumshe idanuwa atare tareda qara matse junansu musamman ita dataji hannunsa cikin rigarta
Sun jima a sofa suna abubu abubuwansu kafin suka nufi gado dama tun a sofa akayi wurgi da rigar baccin dake jikinta. +
Qarfe shida na safe ta fito wanka daureda towel gashinta ya mammanne mata a gefen fuska yana tsiyayar ruwa ko gaban mirror taba isaba ya fito daga toilet din shima yana tsane kansa dake jiqe ya suka tsaya gaban mirror yakalleta ta cikin mirron ta ‘dauke kai tana maqala maqala hand dryer datun a jiyan da ita yayo shopping.
Ita tayi drying masa kansa sbd yanda ya zauna ya baice komaiba yasata tasan itace zatayi masa.
Saidaya shirya tsaf kafin tasamu damar shiryawa cikin wani royal blue skinny armani jeans daya matuqar kama hips dinta harzuwa qasanta ya lafe ya matuqar fidda shape dinta sai wata farar Louis Vuitton shapeless chiffon top sai gashinta data saki sbd bayan ta daure ya zare mata band alamar bayason hakan tayi mamakin yanda yasiyo kayan bayan itadai bata taba saka irinsuba saidai batada wani zabi arayuwa sai abinda yace ko ya nuna buqata. 1
Shima blue armani jean da farar Louis Vuitton wideneck ce ajikinsa sai gashinsa daya saki bai daureba sai qamshin turarukansu dake tashi cikin sanyin AC na dakin. 2
Breakfast aka kawo shidai black tea da toasted bread kawai yaci itakuma taci fried egg da vegetables sai fresh milk da ammy tasabar mata dasha kullum.
Qarfe bakwai suka fito bayan ta ‘daura kimono black akan kayanta wadda ta qarawa shigarta da jikinta kyau suka fito hannunta na cikin nasa.
Babu Wanda yadamu dasu baresu da ko fuska babu daga gurinsa ita kuwa Sam batada damuwa akan duk abinda yanuna.
Mota suka shiga babu 6ata lokaci suka bar bamako sai airport sbd tun jiya sunyi bankwana dasu mum.
A jirgi wannan karon tsuru tayi sbd tsananin ciwo da nauyin da qafafunta suka fara yimata.
Kallo ‘daya yayi mata yakalli qafafunta dayaga tana kallo kamar zatayi kuka.
Kallon qafafun yayi dan ta cire qafarta daga loafers din dake qafarta yaga sun ‘dan kumbura yadawo da kallonsa kan fuskarta yayi mata kallon mintuna uku kafin ya riqo hannunta batareda yace komaiba. 1
‘Dan sanyi taji sbd kobaiyi mgn ba yanxu tana gane abinda yake nufi wannan sigace ta lallashi yake mata. 1
Daurewa tayi tasaki jiki duk da vatajin dadin qafafun.
Sai yamma suka sauka direct masaukinsu motar da tazo daukarsu tayi dasu amatuqar gajiye tayi wanka daqyar tayi sallah ko abinci bataciba sai bacci.
Wanka yayi shima yashirya yafice bayan yasa ankawo mata abinci batareda yatasheta daga baccinba.
Sai magrib ta tashi tana ganin abincin tasan bayanan ya fice ta tashi tayo brush tazo tafaracin abincin tana lumshe ido sbd yunwar datake damunta dama.
Saidata qoshi takuna ta tashi tayo alwala tayi sallah tana gamawa tadan zauna tana kallon TV ta nutsu tana sake daukar kalaman turancinda Mr aarib ke koya mata.Lokaci ta duba ta tashi tayi sallar ishai tana gamawa tayi wanka tayi shirin bacci ta kwanta nan take bacci mai dadi yadauketa. +
Koda yadawo tayi nisa a bacci yayi wanka kawai shima ya kwanta tareda kashe wutar dakin ya dora kansa a pillonda kanta yake ya rufe ido shima bacci yayi gaba dashi.
Washe gari bayan yashirya zai fita ya jawota jikinsa yana kallon idonta ya saka mata wayarsa daya a hannu murya qasa yace
Ammy na nemanki idan takira saiki sanarda ita abinda takeson ji.
Baki tasaki tana kallonsa harya fice yaqi juyowa kar bashi yayi maganarba to ita mezata cewa Ammy? Ko wayarta ma bazata iya dagawaba sbd kunyar rashin komawarsu bare harta iya mata bayani.
Aje wayar tayi tana kallon wayar akai akai hardai takoma tayi baccinta.
Kwanansu biyu kullum yana fita aikin dayazo yi shiyasa ta samu Hutu.
Yauma sai dare yadawo saidai koda yadawo idonta biyu cikin laushin murya tace masa,
Sannu da dawowa.
Aje wayarsa da shopping bags din hannunsa yana kallonta kafin yadawo gabanta yana kallon shigarta ta wata red mini dress dake jikinta ya ‘dauke gira daya yace,
Kinason ki lalatawa Ammy yarone shiyasa kikaqi bari akoma. 7
Zaro ido tayi tareda saurin juya masa baya tana dafe qirjinta da kusan rabinsa yake a bayyane ya zuro fuskarsa ta wuyanta bakinsa a kunnenta yace,
Naga bayan tunshigowata ai.
Da gudu ta bar gurin ya riqo hannunta tareda dawo da ita ya dauketa cak ya nufi toilet.
Ajeta yayi tsakiyar toilet din ya tsareta da ido tasaki boyayyan murmushi sbd tasan manufarsa
Hannu tasa tafara cire ma6allan rigarsa har ta kai qarshe ta zame masa rigar ya shiga cikin bathtub yakwanta cikin ruwan sumi tareda lumshe ido yabude ya miqa mata hannu ahankali tazame rigarta ta kama hannunsa tashiga ruwan ta kwanta saman jikinsa. 2
Qarfe uku na dare ta farka da ciwon qafa tun tana daurewa harta zame daga jikinsa ta tashi zaune tareda kunna lamp din gefenta ta kalli qafafunta.
Tabasu tayi ta juyo takalli gefensa suka hada ido sbd tun tashinta ya farka.
Hawayen datake riqewane suka gangaro mata ya tashi zaune yana kallon qafafun da kai yayi mata alamar tahowa garesa ta fada jikinsa tareda sakin siririn kuka sbd ciwo suke mata sosai jitake kamar zata gurgunce.
Jin kukanta yakasa tsayawane yasan ciwonne yayi mata yawa yakai hannunsa ahankali yana matsa matasu ahankali
Ta sake shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Koda gari ya waye kasa tafiya tayi shine ya dauketa yakaita toilet yakuma dawo da ita wunin ranar kusan shine yakeyi mata komai duk da ya duba qafafun yakira Dr vin yayi magana dashi akan maganinda zai mata sbd ba 6angarensa bane.
Haryasa ankawo masa maganin saiga kiran Dr vin lokacin tana zaune ajikinsa tana bacci shikuma yana duba wasu takardu.
Hello Dr M.A shams I think you should confirm if she’s not pregnant first before given her the drugs….
Akaro na farko dayaji zuciyarsa ta girgiza ya qurawa fuskarta ido yaga yanda fatarta take glowing ya daga hannunta yaqurawa tafin hannunta ido take ya rufe ido tareda dafe goshi cikin wani irin yanayi. 2
Ya jima yana kallonta cikin wani irin yanayi da shikadai yabarwa kansa sani kafin ya dauki na shafawa kawai ta shafa mata kadan ahankali kafin ya tashi da ita rungume ajikinsa ya nufi gadonsu ya kwantar da ita kafin ya zauna bakin gadon tareda rufe ido yana shiga tunani
Washe gari koda ta tashi taji sauqi sosai saidai kuma yini tayi duk motsinda tayi idonsa nakanta tayi mamaki dukda tasan kallo a gurinsa ba baqon Abu bane agurinta amma na yanxu ya banbanta. 1
Abinda yafi qara bata mamaki shine yanda yakasa rabuwa da jikinta dole kawai ke tadashi sosai ta lura akwai abinda yake ransa.
Bayan kwana biyu ta warke sosai harya fita da ita sukaje wani babban eatery dakuma shopping sbd ganin zama guri dayane yafi saka qafafun ciwo shiyasa akwanakin kullum da inda suke zuwa musamman beach sbd ta lurada yanason ruwa.
Satinsu biyu cif suka koma Libya.
Da yamma sosai suka iso
Motar dataje daukarsu bata dawo gida direct ba saida suka biya wani babban pharmacy aka siya mata magungunan dabatasan na meyeba kafin suka nufi gida. +
Suna isa taji sabon nauyin ammy yarufeta batasan ta yaya zata hada ido dasuba har gwara s salma suna ‘dan wasa wani lokacin.
Lura yayi da yanayinta yasaki Murmushin gefen baki kafin yadan ranqwafo yace,
Ina gaida ammynah kafin nashigo anjima.
Yana fadar haka aka bude masa motar yafita batareda yasake waiwayowaba ya nufi sashen sultan jalaluddeen.
Bayansa tabi da kallo tana jinjina alamarinsa kafin aka bude mata ta fito ta nufi hanyar sashen s salma.
Sa’ar dataci ammy bata gurinta nan ta zauna tana gaidata tareda kasa cewa komai duk tsokanarda s salma din ke mata saidai kawai tayi murmushi qarshe dai miqewa tayi ta nufi palonsu.
Da sallama tashiga ammy dake zaune tasaki murmushin murnar ganinta tana cewa,
Munsamu dai yau kundawo.
Sauke kai tayi tana Murmushin dole sbd kunya tace
Ammy ina wuni?
Murmushi ammyn tayi tace,
Lfy kalau rumanah jeki ki huta nasan agajiye kike idan kinhuta saimu gaisa.
Babu musu ta nufi hanyar dakinta masu aiki biyu suka bita da luggage dinta ammy tabisu da kallo wainda sukaje bada kayaba saigasu da akwati.
Ajiyar zuciya tasauke lokacinda tashiga daki ta zauna sbd Allah yagani taji kunyar ammy tun kafin su dawo.
Wanka tayi tai salloli kafin ta fito ta nufi dakin ammy nan dai suka sake gaisawa ammyn nasake tambayarta jikin mumyn suhailat.
Suna cikin fira sama sama saigashi yashigo babu kunya ya nufi ammyn kai tsaye ya ‘dan rankwafa yayi kissing forehead dinta yana cewa,
Ammy barka da hutawa.
Ya zauna kusada ita tareda yiwa rumanah wani irin kallo tayi saurin Sauke kai sbd ganin ammy.
Kasa 6oye mamakinta ammy tayi tace,
Maheer baka taba zuwa dubiya irin wannan ba kokuwa dan kaje da ‘yata ne?
Murmushi yayi batareda ya’dago daga duba wayarsaba yace,
Tambayi ‘yartaki.
Da sauri rumanah ta miqe ta nufi qofa ta fice tana mamakin iya cabo maganarsa. 1
Kallon ammy yayi yace,
Gobe insha Allah zan koma.
Kallonsa tayi tace,
Allah yakaimu.
Fira suka dingayi sama sama duk da itace mai maganar iyakacinsa kallo sai daga kai sai sa’a yake bude baki yayi wata maganar
Da daddare harta kwanta ta tafito taje kicin ta dauko ruwa sbd wani lokacin tana tashi shan ruwan dare.
Kodata dauko ruwan takoma daki kasa bacci tayi ta tashi zaune tareda rufe ido tana kamar daga sama taji qamshinsa acikin dakin ta bude ido da sauri amma babusa ta dafe goshi tareda sake kwantawa ta rufe ido tana fatar bacci ya dauketa.
Daqyar ta samu bacci yadauketa kodata farka da asuba da ciwon kai ta tashi ta lallaba tayo alwala tayi sallah.
Tana gamawa zazzabi ya kwantarda ita agurin ta kwanta ga sanyin AC amma ta kasa tashi.
Jirgin qarfe goma sha biyu zaibi amma tun asuba idonsa biyu yakasa bacci.
Ammy data kwana tunanin basa rumanah yaje da ita kokuwa aa tana gama sallar asuba ta fito ta nufi dakin rumanah dan cewa ta shirya sutafi tare
Tana shiga taganta kwance a inda tayi sallah yanayin yanda ta dunqule gu ‘daya ya tabbar matada batajin dadine.
Cikin kulawa ta isa tana kiran sunanta
Ta tashi zaune daqyar tace,
Ammy ina kwana.
Lfy meke damunki?
Babu komai ciwon Kaine kawai.
Fita ammy tayi taje dakinta tadauki wayarta ta danna masa kira kamar bazai daukaba saikuma ya dauka kai tsaye tace
Kazo yanxu kadubamin ita batada lafiya.
Aje wayar yayi tareda lumshe ido ya bude dan yasan za’a Rina.
Wanka zai shiga amma ya fasa ya mayarda jallabiyarsa ya fita ya nufi palonsu dan har lokacin gari bai gama haskeba.
Koda ya isa palon ammy na tsaye tana jiran shigowarsa palon.
Da qaramar murya yace,
Sabhaul khair ya ammy.
Kai kawai ta daga masa sbd masiffen tashin hankalinda tasamu kanta aciki na fargabar kar ace tunaninta na cikine da rumanah ya tabbata.
Dakinta takoma ta zauna jira ganin yashiga dakin tareda turo qofa.
Zaune take bakin gado tana ganinsa taji idanuwanta sun ciko da hawayen muguwar kewarsa datayi batasan lokacinda ta miqe ta fada jikinsaba ya lumshe ido tareda qara shigarda ita jikinsa. 7
Jin zafin jikinta yasashi dagota yakalleta cikin wata ir irin murya yace,
Qafan ne?
Girgiza kai tayi tana kallonsa.
Da gira ya yayi mata tambayar then wat is it.
Zamewa tayi taje bakin gado ta zauna cikin sanyin murya tace,
Ciwon kai.
Zama yayi bakin gadon tareda dago fuskarta yayi kissing bakinta yasake taba jikinta yaji zafin
Baice mata qalaba ya zare rigarsa tareda ajewa ya kwanta kan gadon tareda lumshe fararen idanuwansa
Saidata aje numfashi ahankali kafin ta nufi gadon ta hau tashige jikinsa tareda qanqamesa sukai shiru kowanne najin bugun zuciyar dan uwansa yanaji zafin jikinta na shiga jikinsa ahankali ya saki wata irin boyayyar ajiyar zuciya.
Daga haka baccin dabasuyiba adaren ya daukesu ammy dake zaman jira tashigo dakin tayi saurin juyawa ganin yanda sukai bacci hankali kwance. 4
Kasa zama tayi ta kasa tsayuwa sbd idan har cikineda rumanah to yazama dole aciresa sbd tsoronta na bata rumanah zata iya haihuwar namiji Wanda hakan shine babbar masifar dazata tono abubuwa ciki harda yanda iyayen rumanah din suka rasu.Zama tayi tareda rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta
Abu ‘daya tasani shine tana tsananin qaunar rumanah kamar itace ta haife musamman a yanxu datake hango soyayyarta mai tsanani a idanuwan Maheer ‘dinta saidai duk wannan qaunar da yardar zata rushe tazama qiyayya da tsana mai tsanani idan sirrin rasuwarsu asma’u da bulama ya bayyana ga rumanah abinda bazatasoba kenan. 3
Qarfe goma da mintuna goma sha biyu suka farka yatashi zaune tareda tayarda ita zaune yana gyara mata gashinta daya barbaje.
Kallonsa tayi tareda sakin kasalallen murmushi
Ya shafi gefen fuskarta tareda bude baki yace,
Yaya?
Lumshe ido tayi cikin laushin murya tace,
Yayi sauki yanxu banajin ciwon kan.
Lumshe ido yayi tareda jinjina kai kafin yakalli agogo yace,
Ya salam” yana sauka daga kan gadon.
Tare suka shiga toilet din dakinta sukayi wanka Wanda yadaukesu dogon lokaci sbd tsayawa shiririta.
Koda suka fito kan cinyarsa ya zaunar da ita tana goge masa ruwan jikinsa yana kallon gashinta dake ‘digo masa ruwa sbd wasan dasukai acikin bathtub yasa dole suyi wankan tsarki.
Riqo hannunta dake goge gashinsa yayi tareda Shafo gashinta har zuwa fuskarta ya zarce cikin towel dinta ya shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi da galabaita da zuciyarsa ke ciki.
Daqyar ya bude baki cikin wani irin taushin murya yace,
I have something precious inside you so daga yanxu bazaki sake ganin albinon malaminkiba sbd gudun daukar jajayen ido da qaton baki. 4
Murmushi zancensa yasa tasaki tareda zare hannunta taci gaba da goge masa gashi batareda tace komaiba.
Sake riqe hannunta yayi yana tsareta da ido yace,
I will miss this smile dakikeyi danki hanawa suhailat mijinta. 2
Kallonsa tayi gabanta na faduwa sbd jin sunan suhailat yasatajin faduwar gaban ta sunkuyar dakai tareda tashi daga jikinsa ta dauko hand dryer ta jona tafara busar masa da gashinsa mai tsananin laushi.
Shidakansa ya shiryata cikin pink gathered neck top da black straight skirt ta Sanya black hula ta fito ta nufi dakin sa ta dauko masa kayan dazai saka takawo masa yasaka suka fito palon hannunta na cikin nasa tanata 6anbare hannunta amma takasa ahaka yajata har gaban ammy dake sintiri a tsakiyar bedroom dinta tana ganinsu tasaki murmushin qarfin hali tana qarajin tausayinsu dan ko ayanxu datake ganin yanayinsu bama zasu iya rabuwa da junaba saidai duk soyayyarsu qila basuda rabon hada zuria sbd bazata so rumanah ta zamto itace zata fara haifarwa maheer namijiba gwara dai wata kokuma suhailat duk da itama bazataso wani Abu yasametaba saidai so sone amma sonkai yafi. 2
Cikin kulawa tace,
Rumanah yajikinki?kan yadaina ciwo ko?
Kai ta daga tana sake janye hannunta amma Sam kamar bashine riqeda hannunba.
Abinci sukaci a dining ammy madai hartafi rumanar jin kunyar abinda maheer din kemata kuma ko ajikinsa tamkar bashine yakeyiba. 1
Daqyar sukaga sungama ammy tarigasu barin gurin tana girgiza kai sbd batasan haka ‘danta yake ‘dan duniyaba. 1
Ammy na barin gurin takallesa kamar zatayi kuka yazuba mata ido tareda sakin wani miskilin murmushi kafin ya miqe tsaye ya ranqwafa yayi kissing kanta yace,
Ki kula.
Ya fice yana duba agogon hannunsa sbd lokacin tafiyarsa yayi sosai.
Bayansa tabi da kallo hawayen datake riqewa suka gangaro tasa hannu ahankali tashare tareda miqewa ta nufi dakinta ta zauna bakin gado sai kawai siririn kuka ya kufce mata. 1
Yini tayi adaki kwance bayan sallah babu abinda ke tayarda ita ko abinci yau ammy daki tasa aka kai mata sbd ta fahimci halinda take ciki na tafiyar maheer ‘din.
Da daddare ma kasa bacci tayi harsai kusan asuba ya saceta koda ammy ta leqo taga bacci takeyi bata tadataba sbd tasan balallaine tasamuyin bacci da daddare ba.
Koda gari ya waye sosai guraren qarfe goma ammy tadawo ta tararda ita cikin wani zazzafan zazzabi nan hankalinta yafara tashi musamman yanda jikinta yayi wani mugun zafi banda amai babu abinda takeyi
Ganin abin na girmama yasata sanarda s salma nan aka kirawo Dr faduwa tazo tadubata tared fara mata pregnancy test dan karta maganin da baikamacetaba awon farko ciki ya tabbata nan ammy taqara shiga damuwa ga farin ciki ga fargabar abinda zai iya zuwa yadawo. 3
Magani tarubuta tareda Wanda zaita tasamu dan bacci kota huta daga aman.
Kallonta ammy tayi bayan fitar Dr faduwa tasauke ajiyar zuciya tareda mata sannu cikin tsananin kulawa da qaunarta.
Abinci ammyn tasamu taci daqyar kafin tayi sallah tayi wanka ta kwanta wani sabon baccin yayi gaba da ita.
Tunda yatafi bata sake lafiya ba sosai ciwo ya kwantarda ita komai taci baya zama cikinta
Duk inda hankalin ammy yake ya ninka tashi drip kuwa tasha ledoji qarshemadai daina samata ruwan akayi.
Batasan ‘daga masa hankali kokuma shiga haqqin suhailat shiyasa bata fada masa saidai duk yanda taso tare alamarin fin qarfinta yayi dan yanxu wata biyu da tafiyarsa ga mamakinta cikin harya fara tasawa gashi har lokacin ko zaman arkiqi bata iyayi koyaushe akwance take. 1
Gyara zama tayi ta fuskanci Dr faduwa cikin nutsuwa da damuwa tace,
Yanxu wata hudu kenan cikin yake?
Abinda scanning dina yabani kenan”” dr faduwa tafada tana sake kallon takardar scanning din. 1
Cikin tsananin damuwa sultana takalli Dr fadwa tace,
Inason axubarda cikin tunda yaqi bata lafiya wuyardatake sha tayi mata yawa banason wani Abu yasameta tunda mijinta baisan dashiba. 5
Kallonta Dr tayi cikin nazarin zancenta sbd tanaga idan anyi hakuri duk wannan wuyar zata wuce duk da itama tana tsananin tausayin rumanah din.
Cikin nutsuwa tace,
Inaga tunda haryakai wata hudu aqara hakuri idan yakai wata bakwai duk wannan wahalar zata rage sosai.
Girgiza kai ammy tayi cikin damuwa tace,
Acire kawai shine abinda nakeso yanxu. 2
Kallonta Dr tayi cikin nazari kafin ta bude jaka ta fiddo takarda ta rubuta allura tace aje yanxu akawo zatayiwa rumanah din sai zuwa dare idan ciwon mara yataso idan tafara zuba sai akai mata ita asibiti.
Cikin qanqanin lokaci ammy tasa akaje aka kawo allurar nan suka nufi dakin rumanah dake kwance tana baccin datasamu yadan dauketa.
Yawu masu ‘dacin damuwa da wasi wasi ammy ta hadiye cikeda tsananin tausayin rumanah dakuma takaici da baqin cikin abinda zatayi 1
Bude ido rumanah tayi cikin wani irin laushin ciwo suna hada ido da ammy
Ammyn tayi saurin sunkuyar dakanta sbd tasan haqqoqan rumanah bazasu barsuba komai daren dadewa saidai idan har zubar mata da ciki shine abinda zai kare mata ita daga masifar mineelik to ashirye take data ringa zubar mata da ciki idan tasamu.Cikin tausayawa Dr ta kalli rumanah tace,
Sannu rumanah,
Allura za’ai miki kisamu ‘dan qarfin jiki. +
Murmushi qarfin hali tasaki daqyar tareda ‘dan muskutawa tabada bayanta cikin nutsuwa tasoka mata allurar tayi mata tana mata sannu. 2
Saurin barin dakin ammy tayi sbd hawayen dake qoqarin ciko idanuwanta
Cikin tsananin sanyin murya takalli Dr faduwa data fito dakin tace, 3
Awa nawa allurar zatayi kafin cikin ya lalace yafara zuba sbd……..
Wani wawan jiri taji yayi mata muguwar diba tana kallon qofar palon saida Dr ta riqota tareda juyawa itama sukai ido biyu dashi tsaye yana kallonsu babu mai iya gane yanayinsa acikinsu shiya mugun tayarda hankalinsu.
Ammy ya qureda idanuwansa dasuka mugun qara sanyata damuwar abinda tayi muryarta na rawa takira sunansa daqyar. +
Ya lumshe idanuwansa yasake kallonta Dr faduwa na ganin haka ta sulale ta fice dan ita ko kallo bata ishesaba.
Gaban ammy yaqaraso ya tsaya cikin wani irin yanayi na tsananin 6acin rai da bata ta6a ganinsa acikiba yace,
Bantaba samun tarba irin wannan ba ko sakin fuska babu bare murmushinki da murnarki.
Da mamaki ta kallesa da sauri zuciyarta na qara tsinkewa dan kuwa abinda take hangowa acikin idanuwansa ta tabbarda yajisu.
Murya cikin sanyi da tsananin damuwa tace,
Maheer nasan kaji komai amma dan Allah inaso ka fahimci manufata tayin hakan dan nikaina ba’ason raina nayi hakan ba wlh zanfi kowa farin cikin ganin rumanah ta haifa maka ‘yaya saidai I can’t risk her life…….
Oh please ammy karki fara kawo maganar risking life anan sbd babu Wanda ya isa yahanawa bawa shiga qaddararda Allah ya dora masa,
Ammy kinsan meyasa kuke wahala da masifar mineelik haryansu shine sbd kuna sake qarfafawa abin ne,
Meye alaqar ‘yayana da wannan tunanin naki dazaki min haka?
Meyasa zaki rabani da abinda ko hannuna bai shigaba?
Shin ammy ina iliminki da saninki yayi dazakiyi tunanin namiji zata haifa bayan bakida masaniyar hakan…… 4
Cikin ‘daga murya da takaicin abunda ke faruwa ayanxun tace,
Kana tunanin ina nuna kamar nasan zata haifi namijine shiyasa nayi hakan?
Amatsayina na uwa nayi hakan sbd sanin matsayin dazata hau idan ta haifi namiji Wanda kasan mezata zama idan harta zauna wannan matsayin musamman da jinininta bai zamto na sarautaba saitafi wainda suka gabata zama baraza da abin fargaba……
Cikin tsananin baqin ciki ya katseta da cewa,
Rumanah har abada bazata ta6a hawa wannan kujerarba koda ta haifi namiji koda hakan na nufin ni nakar6i mulkin zan karba ni nazama masifar…… 2
A tsawace tace,
Ka riga karasa wannan damar ta zauna throne ‘din mineelik tun lokacinda kace baka karbi magajin mineelik ba dan haka ko kanaso kabaka ayanxu atarihince ‘dankane yanxu yakeda cikakken ikon karbar mulkin mineelik kuma kafin ya girma mahaifiyarsace kawai takeda ikon bawa duk Wanda taga damar riqon qwaryar mulkin ‘danta idan kuma taso ta itace dakanta zata…….
Idan angansu kenan a mineelik ‘din…yafada zuciyarsa na qarasa daukar zafi.
Itama cikin zafi tace,
Wannan ne baka isaba sbd labarin cikin na isa a kunnen sultan bazata qara ko kwana biyu ba’a mineelik ba dan haka zabi ya rage naka kodai acire wannan cikin kodai rumanah ta rasa rayuwarta amatsayin rumanarta……
Ayau da wanine agabana bake mahaifiyata ba da bazai sake ko minti ‘daya da kansa a gangar jikinsaba,
Zuciyarsa tariga tagama ‘daukar wuta bazai iya cigaba da maganaba ya wuceta ya nufi dakin rumanah dake kwance lamo tanaji mararta na murda mata ahankali saidai ko wani qwaqwaran motsi bata iyayi saidai jikinta dayayi mummunan sanyi hakanan takejin maraicinta na taso mata. 2
Qamshinsa taji yashiga hancinta ahankali ta bude idanuwanta dasukai laushi takalli qofa tagansa tsaye cikin yanayin dabata ta6a ganinsa ba ta lumshe ido sbd tasan idanuwanta ne kawai ke ganinsa sbd zuciyarta tasamu sukuni.
Qarasowa yayi baice komaiba ya dauketa cak ya nufi qofa da ita ya fito ammy dake zaune palon ta rafka wani mugun tagumi cikin tsananin damuwa da zullumi
ta miqe tana kallonsa yazo yatsaya gabanta cikin danne halinda yake ciki yace,
Komawa zanyi idan ta sauka zankawo miki ita. 1
Kafin tayi wata magana ya wuce yabarta da baki bude idanuwanta dasukai jajir suka ciko da qwallan damuwa ganin tun yanxu alamura na neman ca6ewa. 1
Wani babban private hospital ya nufa da ita tun ahanya yasa akai musu booking flight koda suka isa harta fara fita hayyacinta sbd jinin daya 6alle mata sosai.
Cikin gaggawa aka fara dubata dan tsaida jinin dayake suma doctors din asibitin qwararrine yashiga cikinsu dan baibari kowa yataba masa itaba,
Cikin ikon Allah suka samu nasarar tsaida jinin batareda cikin ya zubeba saidai kwata kwata baza’aso taringa babban motsiba sbd anr anriga antaba lafiyar cikin dole saiya kwana biyu yasake qarfi. +
Adakin datake kwance yashiga toilet ya wanke jikinsa tareda canxa shirt sbd sosai jini ya 6atasa.
Sunsamu ticket din da asuba jirgin zai tashi shiyasa yasake mata wasu injections sbd motsin daza’ai da ita
Yana zaune sofa din dake dakin akai kiran asuba ya tashi yayo alwala yayi sallah yana idarwa babu bata lokaci akai rubuce rubucen daza’ai suka nufi airport cikin ambulance ko mintuna ashirin basuyi da isaba jirginsu ya ‘daga.
Da rana tsaka suka isa Georgia direct motar asibitinsa tazo ta daukesu suka nufi asibitin nan aka fara bata sabon treatment likitocin basu zaunaba saida suka sake tabbatarda komai is back to normal.
Baibar asibitin ba saidata farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi takallesa tareda lumshe ido sbd ba qwari ajikinta sosai.
Matsowa gabanta yayi yatsaya tareda kallon cikin idonta ya riqo hannunta tareda sakar mata siririn murmushi ahankali ya furta,
Hey yene konjo(my pretty) 1
Kallonsa tayi fuskarta na bayyanarda farin cikin ganinsa dakuma sunan daya kirata dashi.
Da kansa ya dagata yadauketa yakaita toilet yayi mata wanka yacanza mata kaya patients sabbi ya rasa yanda zaiyi ya daure mata gashinta dole yahaqura yabarshi asake yabata tea tasha yabata magani da sauran injection dinta kafin yayi kissing goshinta yafice.
Koda ya isa gida qarfe tara na dare lokacinda suhailat tagansa bude baki tayi tana kallonsa cikeda mamakin ganin jiya yatafi amma yadawo yau bayan batasaka ran dawowarsa da wuriba.
Rungumesa tayi cikin danne mamakinda tace,
Hey welcome.
Rungumeta yayi tareda sakin ajiyar zuciya da 6oyayyan numfashi sbd shikadai yasan halinda zuciyarsa ke ciki ayanxu sbd tabbas yasan akwai rigima agaba saidai bazai ta6a bari rumanah ta Shiga abinda kakannin kakanninsa suka aikatoba koda hakan na nufin shi yafadawa abinda yayi gudu tun qurciyarsa matuqar hakan shine zai kare rumanah da abinda zata Haifa so be it. 1
Bedroom dinsa suka nufa ya tube yashiga wanka itakuma ta nufi kicin tacewa Carolina ayi abincinda akasan maheer din naci.
Daga haka takoma dakinsu amah tasanardasu dadynsu sundawo suka fito da tsallen murnarsu.
Sakin fuska da jiki yayi sosai dan gudun shiga haqqin suhailat ‘din da yaransa saidai cikin zuciyarsa damuwace mai tarin yawa duk da kasancewar cikin ya tsaya damuwa batabar zuciyarsaba musamman dayasan dole zasu koma mineelik sbd ammynsa takoma ‘dakinta badan hakaba bayajin rumanah zata koma mineelik.
Sosai suhailat ta lurada akwai abinda yake ransa na damuwa duk da abune mai wuya ka iya gane yanayinsa.
Batason tana shiga abinda bai shafetaba musamman yanxu dayakeda wata matar kuma ‘yar ‘dakin ammynsa dan haka shishigi kan abinda babu ruwanta ba nata bane sbd kartajiyo abinda zai sakata damuwa. 1
Fruits kawai yaci koda suka zauna dining kuma harsuka gama bai yiwa kowa maganaba duk da ko yaransa sunsaba da miskilancin daddyn nasu sbd kosu wani lokacin idan abin ya motsa baya iya yimusu doguwar magana saidai idanuwansa dake ladaftar da mutum.
Da daddare koda yakira wayar Dr olie yasanar masada tasamu bacci tundazu.
Kallonsa suhailat dake kwance jikinsa tayi still taqi tambayarsa meke faruwa bayan taji da hospital yake magana batai la’akari da ko ammynsa ceba dayake yasaba da haka take shiyasa bai tsaya tunanin banxa akan hakanba da haka tai bacci cikin jikinsa ya qurawa kyakkyawar fuskarta ido hakanan yakejin tausayinta sbd ba ita yakeji cikin tsakiyar zuciyarsaba,
Bayajin fitar kowane numfashinsa da ita aciki saidai tanada wani irin girma da qima a idanuwansa ta yanda bazai iya barin ta quntatu akan abinda yake tsananin so ba.Rufe idanuwansa tareda dakin 6oyayyar ajiyar zuciya. +
Qarfe bakwai yafito wanka yakalli suhailat data shigo dakin batareda yakalletaba yana gyara gashinsa yace,
Carolina ta hada breakfast na mutum ‘daya a basket and it should be something light.
Kallonsa tayi tana zaunawa gefen gadonsa tace,
Ok amma pls who is the patient?
Batareda yabar abinda yakeyiba yace,
‘Yar ammy.
Da mamaki ta kallesa tace,
Bansan waye haka ba.
Then kibarshi idan anyi discharging nata zaki ganta.
Miqewa tayi tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa yana saka rigarsa tace,
Ok zanbika muje tare nadubata ko waye tunda hanyar zuwa office dina ne.
Baice komaiba yagama shirinsa suka sauko tana maqale da hannunsa.
Da gudu su amah dake qoqarin zama a dining sukayo gurinsa yasaki fuska cikin kulawa yayi pecking kowannensu yana cewa,
Good morning to sweets angels.
Good morning to you too daddy””suka fada suna kissing kumatunsa both sides.
Dining suka nufa dukkaninsu sukai breakfast
Shidai daqyar ya iyacin toasted bread one slice da black tea yamiqe
Suma dai dayake sun gama suka dauki school bags dinsu suka fito dukkaninsu Carolina tabiyosu da basket ‘dinda aka shirya breakfast dinda yace.
Motarsu amah daban driver yafara wucewa kafin yashiga Lamborghini dinsa suhailat tashiga yaja suka fice daga gidan.
Koda suka isa asibiti suna shiga reception yatsaya batareda yajuyo gefentaba yace,
Kije room 36 zanzo idan naga dr Andrew.
Ok tace tareda kissing hannunsa ta wuce da basket din ahannnunta.
Shikuma kai tsaye office dinsa ya nufa.
Tana isa qofar dakin ta tsaya tareda Sauke ajiyar zuciya dukda batasa waye acikiba ta murda qofar tashiga.
Zaune take tsakiyar gadon nurse na gyara mata kanta daya barbaje yana damunta.
Tsayawa tayi tsakiyar dakin qafafunta na rawa gabanta yayi mummunan faduwa ganin rumanah ce,
Ahankali tasauke idonta kan qaramin cikinta daya fito ga wani haske mai firgitarwa dataga tayi.
Fita numfashinta yafarayi dasauri wani irin zufa ya karyo mata amma saitayi saurin kiran sunayen Allah acikin zuciyarta kafin tasauke numfashi mai sanyi tasaki murmushin qarfin hali tareda qarasowa bakin gadon inda rumanah ta tsareta da ido itama numfashinta na fita da sauri amma ganin tasaki fuska yasata qaqalo murmushi tana cewa,
Sannu da zuwa.Aje basket din hannunta tayi tana sake qaqalo murmushi tace, +
Ashe kece babu lafiya baby baifadaminba kawai yafadamin numbern dakin ne,
Sannu ya jiki?
‘Daga kai tayi ahankali tana cewa,
Alhmdllh.
Shiru dukkaninsu sukayi babu wacce numfashinta bai fita da sauri sbd ganin ‘yar uwarta.
Suhailat cikin jikin rumanah din take satar kallo dan kuwa batasan haka take kishin mijintaba saidataga cikin dan kuwa Allah ne kadai yasan irin ciwo da radadin datakeji axuciyarta saidai tana qoqarin fincikewa sbd batason zubarwa da kanta qima a gurin mijinta da ‘yayanta harma da rumanar datake kishiyarta.
Rumanah kuwa jitayi duk atakure take da wanzuwar suhailat din gashi nurse tagama abinda takeyi ta fice.
Hakanan takejin bata iya kallonta sosai sbd ganin take zuciyarta da shaidan zasu hasaso mata maheer atareda suhailat din Wanda hakan na matuqar girgiza zuciyarta.
Cikin kulawa suhailat ta miqe ta bude basket din ta hada mata black honey tea sai pancakes da toasted chicken datai laushi sosai ta zuba matasu a plate tareda aje matasu yanda zata iya ci.
Cikin sanyin murya rumanah tace,
Nagode amma inaso zanshiga toilet….
Wayar suhailat dince tayi ringing ta sauka da sauri sbd mum ‘dintace batareda taji mai rumanah din ke fadaba ta fita dan amsa wayar.
Ganin ta fita yasa rumanah sauke qafafunta qasa ahankali ta sauko ta nufi toilet din dake dakin ahankali sbd jiri.
Tana kaiwa tsakiyar dakin wani irin jiri ya dibeta daidai shigowarsa dakin.
Saida tajita jikinsa tayi saurin sakin ajiyar zuciya sbd ta sadaqarda cikinta yagama zubewa idan ta fadi.
Bude idanuwanta data rintse tayi takallesa cikin fargaba sbd ganin kallon dayake mata murya na rawa tace,
Toilet zanshiga.
Yanda ya dauke gira daya yasa tasan menene azuciyarsa tayi qasa dakai cikin tsananin sanyin murya tace,
Yi hakuri bansan zan…..
Just shut up”””yafada yana daukarta gaba ‘daya ya bude toilet din suka shige.
Sauketa yayi ahankali kamar kwai
Ta dago takalli fuskarsa taga ba wasa tasaki 6oyayyan murmushi cikin zuciyarta tana cewa,
Ko fushi kyau yake masa. 1
Brush ya miqa mata ta karba tayi tana kallonsa sbd kallonsa yanxu matuqar nishadi da nutsuwa yake bata tana gamawa ya miqa mata towel tareda jawota jikinsa yazare mata kayan jikinta itadai ido kawai take binsa dashi sbd yau ko ta6insa nutsuwa yake bata.Da yake shower ce bai shigaba ita kadai tashiga tayi wankan shikuma yana tsaye gaban mirror yana goge inda rigarsa ta baci da ruwan allurar dayaje yiwa wani patient kafin yashigo dakin. +
Tana gama wankan ta dauki towel ta daura tareda zare shower cap din kanta ta tsaya gaban madubin da yake dubawa tana fuskantarsa.
Wasu kayan yasanya mata saidai bada bra ba duk saiyaji ransa yabaci da yanda kayan patients din sukai mata kyau amma bai nunaba yasake gyara mata gashinta ya dauketa suka fito tana kallonsa gira ‘daya ya dauke yace,
Wannan kallon fa matata tana nan so be carefull bata hadani da komaiba.
Murmushi daya bayyana fararen haqoranta tasaki tareda sake qanqamesa tana fitarda sautin murmushinta ahankali
shima murmushin gefen baki yasaki suna kawowa tsakiyar dakin sukai ido hudu da suhailat dake zaune tayi musu kallo ‘daya ta dauke kai tana qoqarin danna kira awayarta.
Saurin saukowa jikinsa rumanah tayi sbd taji nauyin suhailat din sosai koba komai ka girmama mai girmama kansa ta zauna bakin gado tana suuke kanta qasa.
Kallo ‘daya yayiwa suhailat yagano halinda take ciki yaji tabasa mugun tausayi sbd baisan lokacinda ta dauka azauneba gashi sun dade aciki gashi qila batasan yana cikiba.
Hannu yakai yakamo hannunta tareda miqar da ita ya matsota gabansa yana kallon cikin idonta datake qoqarin 6oye halinda take ciki cikin kulawa yace,
Are you ok?
Kai ta ‘daga masa batareda yakallesaba
Yayi kissing forehead dinta yace,
I will be in my office””yasa kai yafice yabarsu.
Jawo abincin rumanah tayi tafara ci hannunta na rawa sbd rawar da zuciyarta keyi.
Suhailat ma batareda takalli fuskar rumanah din ba tace,
Zantafi office am getting late Allah yasauwaqa.
Tana gama fada ta dauki handbag dinta ta fice hawayen datake riqewa suka gangaro mata ko office dinsa bata biyaba ta wucewarta saidata isa office dinta ta rufe siririn kuka ya balle mata amma dannesa tashigayi sbd bataga dalilin kukanba tunda dama tasan tanada kishiya meye abin jin zafi dan taganta da ciki bayan itama Allah yabata nata ‘yayan ba juya yayitaba.
Saidata samu nutsuwa tayi masa text tace ta wuce office and she’s very late so shiyasa bata biyo office dinsaba.
Tana ficewa rumanah ta aje breakfast din sbd dama turawa kawai takeyi.
Yana gama karanta text dinta ya aje wayar tareda lumshe fararen oily eyes dinsa.
Yinin ranar dukkaninsu a darare sukayisa sbd kowanne da abinda ya maqalewa zuciyarsa.
Baibar asibitin ba yau sai qarfe goma na dare lokacinda rumanah tayi bacci kenan.
Koda yakoma gida suhailat bata nuna damuwar komaiba a fuskarta itada ‘yayanta su maqalqalesa suna masa oyoyo
Yayo wanka bai sauko cin abinciba sbd yaci pizza tareda rumanah a asibiti.
Koda suhailat taji cewar yayi dinner murmushi kawai tayi tace,
Ok bari nacewa Carolina tasaka a fridge. 2
Kodata dawo dakin yana kwance wayarsa a kunnensa yana magana da antynsa wadda yake biwa tana qara basa haquri akan abinda yafaru shidai kunnuwane kawai nasa baya iya zuba dogon zance.
Kwantawa tayi ajikinsa tareda rungumesa ta rufe ido alamar bacci
Yayi mamaki sbd basu cika kwana daki dayaba koman dare wani lokacin dakinta take komawa ta kwana.
Koda yagama wayar tayi bacci yakalli fuskarta kafin ya lumshe idanuwa fuskar rumanah daya baro tana barci tafado masa yasake rungume suhailat ajikinsa yana kamar rumanah ce ajikin nasa. 9
Washe gari ma tare sukaje asibitin saidai ko zama batayiba gaisawa kawai sukayi ta wuce gurin aikinta sbd ganin irin kallon da maheer kewa rumanah sbd sai yanxu cikinta yafito dakyau sbd kayan da aka canxa mata sunso kamata saikuma basu kama ‘dinba.
Bayan wucewar suhailat nurse ‘din dake kula da ita ta fita sbd idan yashigo fita sukeyi.
Kallon ‘dan cikinta yayi batareda ya amsa gaisuwartaba ya dauki file dinta yafara dubawa.
Qamshinsa daya cika dakin ta shaqa tana lumshe ido cikeda qaunarsa mai zafi dake cin zuciyarta.
Yana gama dubawa ya kalleta a miskilance yace,
Did you bleed today?
Girgiza masa kai tayi kala kallonsa ya juya yafice baisake cewa komaiba.Numfashi tasauke a sanyaye ta zame takwanta. +
Kwananta biyar a asibitin akayi discharging dinta tunda suka kamo hanyar gida numfashinta ke fita da qarfi
Jin tayi tafison komawa Libya gurin ammy hankalinta zaifi kwanciya acan. 1
Suhailat ma tunda tasan zasu dawo gida anyi discharging dinta jikinta yake sanyaye.
Carolina tagyarawa rumanah dakinta tun na farko sosai.
Qarfe goma sha biyu suka iso tareda driver sbd shi theatre zaishiga.
Koda suka iso gidan tuni kayanta dayayi shopping online suka iso har ankai mata dakinta
Itadai suhailat tana bedroom dinta sbd ita bata iya munafurciba arayuwarta bazata iya tsayawa tana rawar jiki akan abinda tasan ba haka bane cikin zuciyarta,
Abinda tasani shine bazata qi rumanah ba bakuma zatai munafurcin nuna mata soyayyar qaryaba saidai zata mutumta ba sbd mijintane ya ajiyeta kuma as along as babu Wanda ya wulaqanta wani acikinsu to zasu zauna lafiya babu takura saidai batai alqawarin ringa zaunawa suna fira tareba gwaradai nesa nesa da juna saisunfi mutunta junansu. 4
Carolina ta tarbota daga mota suhailat na dakinta suka shigo kai tsaye daki rumanah ta nufa ta zauna bakin gado tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.
Ta jima a zaune kafin tamiqe tashiga toilet tayo wanka tazo tasaka doguwar riga mara dogon hannu ta daure gashinta ta saka qaramar hula mara nauyi tayi sallar ishai da akai tana gurin wanka tana idarwa ta fito palo tana qoqarin sakin fuskarta ta nufi kicin inda tajiyo muryar suhailat tana waya taje daukar Abu a fridge.
Gama wayar suhailat tayi ta juyo tana Murmushi tace,
Patient ya jikin?
Barka da dawowa gida.
Jiki alhmdllh naji sauqi sosai
Ina su amah banji hayaniyarsuba gashi naga lokacin dawowarsu daga school haryayi nisa da wucewa.
Sundawo tun dazu suna study room sbd Anfara musu exams.
Jinjina kai tayi tareda ficewa tabar kicin din
Itama suhailat tana gama abinda takeyi ta fice.
Yini guda adaki tayi abinta ko abinci ma daki Carolina ke kai mata.
Ita kuwa suhailat abinda ke gabanta kawai takeyi ba damuwar komai.
Baidawo gidanba sai cikin dare lokacin kowa gidan yayi bacci sama ya nufa dakinsa kai tsaye yashiga yayi wanka harya gama shirin kwanciya ya kwanta babu suhailat bare rumanah da dama baisa ran zata iya zuwaba.
Washe gari koda yayi shirin office harya wuce rumanah na dakinta bata fitoba saida dukkaninsu ta tabbatarda suntafi gurin aiki ta fito.
A dining ta yi breakfast dinta ita kadai tana gamawa tadawo palo ta zauna tana kallo duk da hankalinta ba akan kallon yakeba duka.Ahaka dai ta wuni ita kadai sai Carolina dake dan tayata fira sama sama sbd ba laifi Carolina din tafi sakewa da ita akan suhailat sbd tafi sake mata. +
Suhailat ce tafara dawowa da yamma lokacin tana palon zaune tana gyaran farcenta sanyeda blue skinny jean da red loose top sai gashinta dake dunqule cikin hula red cikin sakewar fuska sosai tayi mata sannu da zuwa.
Cikin sakewa itama ta amsa tana cewa,
Duk kadaici ya dameki babu kowa sai Carolina kuma ita bawani sakewane da itaba.
Nikuma naji dadin kasancewa da ita sbd ba laifi muna sakewa da juna sosai.
Dakinta ta nufa tayi wanka ta sanyo white skinny jean da white chiffon shirt tareda black hula ta fito palon ta zauna kusada rumanah tana cin pancakes suna kallo.
Sallar magrib tasa rumanah barin palon ta nufi dakinta.
Sallah tayi magrib tayi bata fitoba saida tayi sallar ishai ta shiga wanka tana fitowar Carolina tayi knocking ta sanarda ita ana jiranta suci dinner.
Straight skirt tasaka black da black d&g shirt hasken fatarta yafito sosai cikin black shigar ta dauro siririn black scarf tafito tana fidda siririn qamshi ga cikinta daya fito cikin kayan sosai.
Tana fitowa kallo daya suhailat tayi mata ta dauke kai tana murmushi tace,
Ok everybody time for dinner.
Suka miqe fammah na maqale da hannun rumanah suka nufi dining suka zauna.
Abinci sukeci cikin nutsuwa itadai dama tafadawa Carolina noodles With veg zataci saigashi bata wani ci sosaiba saima papaya drink datake ta sha.
Coat dinsa riqe ahannu yashigo palon yana waya.
Kallo daya yayiwa dining area ‘din yaji gajiyar daya ‘debo ta ninku.,
Da gudu suhailat ta taso ta rungumesa tareda basa peck tana cewa, 8
Welcome baby.
Rungumeta yayi shima yana kallon idon rumanah datai saurin ‘dauke ido akansu jikinta na rawa.