Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter22
Kowa ya gyara zama dan yaji labari
cike da mamaki da tausayin Ramlah
kowa ya zubo mata ido yana kallo
musamman Hananah. A zuciyarta
cewa take wai shin ko mafarki nake ne ba gaske bane ni Ramlah ta
nemowa Haisam. Yau zanga Haisam
kenan? Ikon Allah, Allah Mai Girma,
Allah na gode maKa, ko bazan auri
Haisam ba in ganshi ma na gode wa
Allah. Ramlah ta ci gaba da cewa “Babban-mutum garinku na nufa na
rasa gidan naku ma sai da muka yi
tambaya don ban manta sunan
Mahaifinki ba Malam Habu. Na ce yana
da *ya Hannah wata fara. Da afarko
basu gane ki ba da Hanne suka fi saninki ashe ko *yar Baba na ce kece
sannan aka kaimu gidan naku. Ashe
Mahaifinki ma ya rasu? Hannah ta
gyada kai ta ce “Yafi shekara biyu ma
da rasuwa. Ramlah ta ce Allah Ya
jikansa. Mahaifiyar Haisam babu abinda take
iya cewa sai kuka kawai take yi kamar
ranta zai fita, Mahaifiyar Ramlah ce
take rike da ita tana lallashi itama
kukan take. Ramlah ta ce “Sai matar
Babanki muka iske take cemun suma basu san inda kike ba, kanin
Mahaifiyarki ya zo ya dauke ki tun
bayan rasuwar Mahaifinki kun tafi
kasarsu Niger. Na tambaya wanne gari
a Niger ta ce Dashi. Na dan sha wuya
kafin na gano inda kike. Munyi kwana biyu a gidan wani bawan Allah a garin
muna yiwa matansa kwatance sai can
daya daga cikin matan ta ce Hannah
matar marigayi Bello Madu custom. Na
ce mijinta ya rasu ne? Suka ce ya rasu
harta fita takaba, naji dadi da suka ce a yanzu baki da miji don zan iya tahowa
da ke. To amma yaya zanyi gashi baki
sanni ba, *yan Uwanki da *yan uwan
mijinki ba zasu bari in taho da ke ba.
Na tambaye su *ya*yanki nawa yanzu
suka ce baki taba haihuwa ba watanki bakwai da aure mijinki ya rasu ya
barki. Sai kawai na tuno wata dabara
na ce to tunda mijinki ya rasu bari ince
daga gwamnatin jihar Kano matar
gwamna ta aikoni don in kafa wata
kungiya da za’a tallafawa matan da mazajensu suka rasu suka barsu da
marayun *ya*ya. Haka kuwa akayi
nasa aka rakani fadar mai gari ni da
direbana muka hada baki muka ce
tare aka turomu. Dajin haka mai gari
da jama’ar gari suka yi farin ciki da wannan ziyara tamu. Washe gari yasa
akayi shela aka tara mana matan da
mazansu suka rasu suka barsu. Kallo
daya nayi miki na gane ki, saboda na
sanki a hotuna a wajen Raudah
kanwata tun kuna aji daya har aji shida. Tunda nasan kin iya rubutu
sauran basu iya ba sai na ce kowacce
tazo ta rubuta sunanta. Basu iya ba, na
ce to wacce ta iya tazo ta dinga
rubutawa suka nuna ki kika zo kika
rubuta. Na babbaku taimakon da zan baku sannan na ce tunda kin iya
rubutu to ke zaki dinga wakiltarsu
kina karbo musu taimako daga Kano
na nemi da ki biyoni Kano. Na ci sa’a
kuwa *yan uwanki suka amince kika
biyoni. Don kawai in kawo ki wajen Haisam.
Wannan karon Hannah murmushi ne
ya kece mata saboda tsananin farin
ciki. Ta sake tattara hankalinta wajen
Ramlah tana sauraronta. Ramlah ta ci
gaba da hawaye ta ce “Hannah gaki a tsakiyar falon gidan Haisam don kece
kadai maganin da zaisa Haisam ya
warke daga wannan matsanancin
ciwon zuciyar da yake fama dashi. Ta
sharbe hawaye ta ci gaba da cewa.
Haisam ya sha wuya Hannah a sanadiyyar tsananin sonki, Haisam ya
rasa walwala a rayuwarsa a
sanadiyyar tsananin sonki. Haisam mai
kaunarki ne fiye da duk wani mai
sonki a duniya. Sai yau Hannah ta ji
amsar wannan kalmomi da ta dade tana nema dalilin da ake cewa Haisam
yafi kowa sonta a duniya. Mahaifinta
ne ya fara fada mata, Bello Madu ya
fada mata haka, sannan Ramlah ta
fada mata. “Lallai na yarda Haisam yafi
kowa sona, Hannah take fada a zucitarta. Ramlah ta sake rushewa da
kuka mai tsanani ta ce “Ban sami
soyayyar Haisam ba ban barshi kuma
ya auri wacce yake so ba. Hannah ta
matso ta rungume Ramlah tana
lallashinta tana bata hakuri itama kukan take yi. Ramlah ta ce “Hannah
dole nayi kuka dole na dauwama cikin
bakin cikin dana jefa Haisam na
cuceshi na cuci kaina. Hannah ta ce
“Aunty Ramlah daina cewa haka Allah
Ya rubuto sai anyi haka amma bake kika sa haka ta faru ba, Ramlah ta
dago ta kalli Hannah ta ce “Haisam
yasha wuya, kullum yana tunani
kamar ya zautu don wani lokaci sai
kaga yayi murmushi ya ce Hannah
kenan saboda tsananin tunaninki da yake. Ni dai kawai ina tare da GANGAR
JIKIN Haisam ne amma zuciyarsa na
wajenki. Ramlah ta sake rushewa da
kuka ta ce “GANGAR JIKINSA NA
AURA!!! Zuciyarsa na wajenki Hannah.
Ke kadai ce maganin ciwon nan na Haisam Hannah kece kadai zai gani ya
warke.
Hannah tasa hannu tana gogewa
Ramlah hawaye can cikin zuciyarta
kuma cike take da farin cikin da ta
dade bata ji irinsa ba cikin sanyin murya ta ce “Yanzu ina Yaya Haisam
din yake, ku kaini in ga jikin nasa..
Gaba daya falon suka dauki kuka mai
tsumama zuciya Hannah cike da
mamakin me yasa suka sake rushewa
da kuka kuma. Hannah ta dubi Ramlah ta ce “Lafiya kuka sake
rushewa da kuka? Ramlah ta dafa
kafadar Hannah ta ce “Hannah sai dai
kiyi hakuri Allah Ya yiwa Haisam
rasuwa jiya Yaya Habib yayo waya.
Zasu taho da gawar a yau da daddare zasu iso.
Hannah ta zabura ta mike tsaye yayin
da zuciyarta ta fara dukan uku-uku
kanta ya fara sarawa kamar zai fashe
ta dora hannu aka yayin da jiri ya
dauke ta ta koma ta zauna, Ramlah ta riketa. Izzidin kanin Haisam ne ya
katse Hannah daga tunanin da take
ciki yazo gabanta ya durkusa yana
mai tsananin kuka da hawaye ya ce
“Ni nake zaman jinyarsa ya ce min duk
ranar dana ganki na baki wannan. Ya mikowa Hannah tsakiyoyinta da abun
busarta. Cikin sanyin jiki tasa hannhu
ta karba tana jujjuyawa ta gansu gar
da su kamar yau ya karba daga
wajenta. Sai ta tuno ranar da aka kai ta
makaranta tana zaune akan akwati, Haisam na kan benci yana mata
tambayoyi har ya karbi wadannan
tsakiyoyin. Sai hawaye ya dinga
digowa daga idanuwanta. Izziddin ya
ce “Bayan tafiyar Ramlah jikin Yaya
Haisam ya rikice sosai har aman jini yake yi. Ashe Yaya Habib yana ta
cuku-cukun zai fita dashi turai. Bayan
tafiyar Ramlah da kwana biyu Yaya
Habib ya tafi dashi London. Ranar da
suka isa da dadddare Allah Yayi
ikonsa Yaya Haisam ya rasu. Gingirin Hannah ta tsaya tana kallon Izziddin
tamkar wata gunki. Izziddin ya ci gaba
da cewa “Yaya Habib yana kuka yayi
waya ya ce yau da daddare gashi nan
zai juyo da gawar Haisam shine
wannan taron da kika gani anan jiran isowarsu muke. Kiyi hakuri Hannah
haka Allah Ya rubuto miki. Haisam
yasha wuya a sanadiyyar son ki. Kowa
yayi shiru babu abinda kake ji a falon
sai sautin shesshekar kuka kowa nayi.
Can Hannah ta rushe da kuka tana cewa “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un
haka Allah Ya rubuta min Allah haka
Yake so ya ganni na godewa Allah.
Yanzu babu Babana, babu mijina Bello
Madu haka babu Haisam din da a
kullum nake saka ran zan ganshi duk daren dadewa. Hannah tana rusa
kuka tana basu labarin rayuwarta tun
ranar da Mahaifinta ya kaita
makaranta suka gamu da Haisam har
izuwa aurenta da Bello Madu har zuwa
rana irin ta yau da aka bata labarin mutuwar Haisam. Ta ce ta dauka ita
kadai take haukarta Haisam yana can
da matarsa ya manta da ita tunda ya ce
min ya cika burin daya kudira a kaina,
na inyi karatu ya dawo gida yanzu zai
cika alkawarin da ya dauka. Sai na dauka Haisam ya manta da wata
Hannah ashe ina like a ransa. Hannah
kuka wiwi Jama’ar dake a falon
Iyayensa da Iyayen Ramlah daginsa
da dangin Ramlah da makwabta duk
suka ji tausayin Hannah fiye da kansu. Hannah ke akayiwa mutuwa. Inji
Mahaifiyar tace Haisam ya ce min Hajiya ku
barni in auri Hannah, Hajiya Hannah ce
rayuwata amma naki fur ashe kuwa
da gaske yake yi gashi yanzu babu
shi. Inama Haisam na da rai yazo ya ga Hannah. Sai duk falon aka dauki kuka
gaba daya.
Hannah ta kankame tsakiyoyinta da
abun busarta a cikin gyalenta ta mike
dakyar tana hada hanya tana tafiya
dakyar ta nufi cikin wani daki ashe dakin Haisam ne, can lungun
gado ta shige ta zauna yayin da
idanuwanta suka fada wani katon
hoton Haisam dake like a jikin bangon
dakin yayi kyau sosai yana dariya a
hoton. Taji gabanta ya yanke ya fadi ta kurawa hoton ido kem yayin da taji
wani ruwa daga hancinta yana zurara
ta cikin kanta numfashinta yana
kokarin dauke mata abunda zata iya
tunawa kenan, ashe suma tayi.
Amratu kanwar Haisam aka turo tazo dakin taga wanne hali take ciki karta
nemi ta halaka kanta, sai kuwa tazo ta
ganta a jingine a lungun gado a zaune
ido babu baki sai fari ta kafe. Amratu
ta kwalla ihu sai duk suka shigo aka
tarar da Hannah cikin wannan hali, ba ayi wata-wata ba aka daukota ana
salati aka yayyafa mata ruwa ta
farfado.
Tana bude ido taga dandazon jama’a
har sunfi na dazu mata da maza an
idar da sallar magariba an sake taruwa ana jiran isowar gawar Haisam. Kofar
gida cike taf da maza. Hannah tayi
salati ta shiga ta zauna tana tunanin a
ina take ko dai mafarki takeyi dazu
ance mata Haisam ya mutu. Allah Yasa
mafarki ne, amma ta mutsike idon ta goge ruwan dake fuskarta taga zahiri
ne ba mafarki bane Haisam ya rasu, ya
rasu da gaske ne. Hannnah taji sai
sannu ake yi mata yayin da taji wasu
na tambaya ita ce Hannah? Wannan ce
Hannar? Wadanda suka zo yanzu kenan. Hannah ta ce a zuciyarta wato
kowa ma ya sanni kenan kamar
yadda nima acan duk wanda ya sanni
sai yasan Haisam. Hannah ta matsa
kusa da Mahaifiyar Haisam ta zauna sai
ta ji Mahaifiyar Haisam tasa hannu ta goge mata hawaye, ta ce mata
“Hannah kiyi hakuri Allah Ya kaddara,
haka fatana ki dinga yiwa Haisam
addu’a kinji ko? Allah Ya jikansa ya
gafarta masa. Allah Ya hadaki da mai
sonki fiye da yadda Haisam yake sonki. Hannah ta girgiza kai ta ce “Har
abada ba’ayi ba, baza ayi ba kuma
Hajiya, na rasa mai sona, nima na rasa
wanda nake so. Sai su dukka suka
rushe da kuka. Kan Hannah akan
cinyar Mahaifiyar Haisam tana kuka kamar ta shiga cikinta don tsananin
son da taji tana yi mata tamkar Haisam
tunda ita ta haifi haisam. Itama
Mahaifiyar Haisam ta dafa kanta jin
Hannah take kamar Haisam ita tunda
Haisam na son Hannah itama har ga Allah taji Hannah ta shiga ranta. Amma
aikin gama ya gama Haisam din daya
hada ya tafi ya barsu.
Can Hannah ta dago ta ce “Zanje inyi
sallar magariba. Hajiyar Haisam ta ce
“Eh jeki kiyi. Hannah ta mike dakyar ga tsananin faduwar gaba da ciwon
kai, ita kanta baza ta iya misalta yadda
take ji a wannan rana ba. Ta shiga
dakin ta kalli wajen da hoton Haisam
yake manne taga an cire shi sai ta
wuce ta shiga bandaki ta dauro alwala tazo ta fara sallah. Bayan ta idar da
sallar magariba ta tashi ta fara jero
nafiloli sai taji gaba daya an dau salati
tun daga *yan kofar gida har matan
dake falo sai taji ana cewa sun iso, an
iso da gawar. Tana tsaye tana sallah sai taji ta sulmiye ta zauna kafarta ta
kasa daukarta gabanta ya yanke ya
fadi. Ta ji duk tsikar jikinta tana tashi.
Kukan da yaki zuwa dazu ya kece
mata tamkar ranta zai fita. Can taji
salatin da ake ya lafa sai ta rike bango ta tashi tsaye da kyar don ta fita falon
taje taga gawar abun kaunarta don
idan taga fuskarsa yanzu ita ce kadai
zata dinga tunawa har karshen
rayuwarta.
Duk dama taji a jikinta
itama ba dadewa zata yi ba a duniya zata bi Haisam dinta. Tunda damuwa
da tunani ne ya kashe Haisam a
shekara biyu ita yanzu yadda take ji ya
linka yadda Haisam yake ji don haka
zuciyarta zata iya fashewa a wata uku
ta mutu ta huta. Tana tafiya a hankali dan karta fadi
har ta fita daga dakin, tana fitowa taga
gaba daya daruruwan mutanen da
suke zazzaune a falon sun juyo suna
kallonta gaba dayansu. Idonta ya dira
akan wata fuska wacce take tunanin ba gaskiya take gani ba gizo ne.
Haisam ta gani zaune akan doguwar
kujerar da ke falon, Yaya Habib a kusa
dashi. Ta sake zare ido tana kallon
Haisam taga dai shi din ne haka taga shima yana murtsike ido yana kallonta
yayin daya jawo hannun Mahaifiyarsa
ya ce “Hajiya ga Hannah can a mafarki
ina ganinta. Mahaifiyarsa ta rushe da
kuka ta ce “Haisam ba mafarki kake yi
ba Hannah ce. Ya zabura zai mike da sauri Yaya Habib ya rike shi don baya
iya tashi tsaye, ya mayar da shi ya
zaunar. Ramlah ce taje wajen Hannah
ta riko hannunta ta nufo da ita wajen
Haisam ta ce “Haisam ga Hannah,
Hannah ga Haisam da gaske ne ba mafarki ku keyi ba. Hannah ta rushe
da kuka ta rungume Ramlah tana
cewa “Ramlah daman ba da gaske
kuke yi ba da kuka ce Haisam ya
mutu. Ashe zan sake ganin Haisam da
idona? Hawaye ne yake zubowa daga idanuwan Hannah da Haisam. Yaya
Habib ya nisa ya ce “Ikon Allah
Hannah yi hakuri daina kukan yanzu
duk jama’ar nan sauraro suke suji
yaya akayi aka ce musu Haisam ya
mutu kuma gashi yazo da ransa. Sami waje ku zauna. Hannah da Ramlah
suka sami waje suka zauna babu abin
da Haisam yake sai kallon Hannah ko
kiftawa baya yi itama kuma ta manta
da a gaban jama’a take duk idonsu
kuma a kansu itama wani irin kallo take yi masa mai dauke da tsantsar so
da kauna, Mahaifin Haisam da sauran
jama’ar duk suma sun shigo.
Yaya Habib ya ce “Kamar yadda kowa
ya sani Haisam na cikin tsananin ciwo
muka bar kasar nan ranga-ranga muka tafi London. To muna isa can
nayiwa asibitin da zamu kwanta waya
suka aiko da motar asibiti aka
daukemu muka tafi. Likitoci na ganin
yadda jikin yake baki da hanci jini sai
suka ce zasu wuce dashi tiyata. Na sa hannu akan na amince ayi masa. Ina
bugo waya ina sanarwa da Baba duk
halin da ake ciki. Bayan sun gama
masa tiyatar ne suka yi suka yi ya
farfado yaki farfadowa suka sa masa
iskar kara numfashi (oxygen) don a jawo lumfashin amma abu ya faskara
sunyi iya kokarinsu na su nemo
lumfashin sun kasa. To ni kuma da
naga haka sai na rikice na bugowa
Baba waya ina kuka nace Haisam ya
rasu. Wani likita yayi-yayi kada in bugo waya har sai anyi wasu awanni
a gani ko zai dawo saboda akwai
alamar bai mutu ba, na ce ina ai babu
sauran wata rayuwa a jikin Haisam. A
take Baba ya yiwa abokansa dake
London waya akan suzo su sameni a asibiti suyi kokari a bamu gawar a
gobe mu juyo gida Nigeria ba sai an yi
ta dogon bincike ba har kwana da
kwanaki. Tunda ya rasu azo gida ayi
masa sutura a binne. Abokan Baba
suka zo aka hau dogon turanci likitoci suka ce sai an basu awa goma sha
biyu suga ko zai farafado dansu basu
yarda ya mutu ba doguwar suma ce in
har bayan awa goma sha biyu bai
farfado ba to saisu bamu gawar. Mun
dauka duk haukarsu ce ta nasara mutuwa ai daya ce kuma kallo daya
zaka yiwa Haisam kasan ya mutu,
ganin babu inda yake numfasawa a
jikinsa. Su ashe sunga akwai wata
jijiya a hannunsa da suka ji tana dan
harbawa shine suke sa ran zai dawo ya rayu.
Muna kirgawa awannin da suka dibar
mana sun cika su bamu gawar mu
taho shine nayi waya nace gabannin
magariba zuwa isha’i zamu iso azo a
taremu. Da rana karfe uku jirgi zai tashi daga London zuwa Nigeria haka
kuma da karfe biyu awannin goma
sha biyu zasu cika da suka dibar mana
sai mu taho. Muka sayi akwatin saka
gawa, na cike form din zan tafi da
gawa. Karfe biyu na cika cikin ikon Allah akaga numfashinsa ya fara
dawowa. Likitoci sukayi-sukayi mu
barshi suci gaba da ceto rayuwarsa
naga gara kawai mu taho tunda dai
sunyi masa abunda zasu yi masa
shikenan sauran sai a barwa Allah ikonSa. Tunda acan gida nace ya mutu
gara dai mu taho din idan ya rayu
Alhamdulillahi idan kuwa ya mutu
dama nace musu ya mutu shikenan.
Muka taho a haka sunan dai yana da
rai wasu daga jijiyoyinsa suna harbawa amma ko motsi bayayi. Naga
gara nayi shiru kada ince bai mutu ba
kafin mu karaso ya mutu gara ace
kafin mu karasa ya farfado. Kuma
cikin jirgin ma akwai likitocin da suka
yi ta taimaka masa wajen jawo numfashi. Cikin ikon Allah muna dira a
garin Kano ya fara numfasawa sosai.
Mun sashi a cikin mota zuwa nan
gidan ya bude ido yayi salati. Shine
yanzu da yaga wannan taron jama’a
yake tambaya me ake yi, aka ce ai an dauka ka rasu shine *yan jana’iza
suka taru, shine yayi karfin halin ya
tashi zaune ya jingina.
Farin ciki a zuciyar jama’a abun ba zai
misaltu ba musamman Mahaifan
Haisam da Ramlah da Hannah. Tamkar anyi musu albishir da gidan Aljannah
Alhamdulillah jama’a ke cewa. Don da
aka ga Haisam an dauko shi da idonsa
kiri-kiri yana kallon mutane wasu da
yawa har sun fara rugawa a zatonsu
sunga fatalwa. Wani abin kunya ma ba mata kawai ba har wasu mazan a
kofar gida sun fara rugawa. Nan fa
kaji falo ya hargitse da Kabbara da
Hamdala. Ana ta taya Mahaifin Haisam
da Mahaifiyarsa murna da fatan Allah
Ya bashi lafiya da tsawan kwana mai amfani. Murmushi kawai Haisam keyi
murna ce ta cika masa zuciya haka
kawai ya tsinci kansa yana mai
tsananin farin ciki badan rashin karfin
jiki ba da tsalle zaiyi ya taka rawa don
murna. Murnar kuma ita ce ga Hannah yau a gabansa, kusa dashi tana
kallonsa tana masa murmushi.
Hmmm