Gangar jikinsa na aura36

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 36

www.littafanhausane.com.ng
Da sassafe sai ga Iya Abu da *ya*yanta sun dira a gidan Iya Salma. Sun iske Hannah da Iya Salma
suna shan koko da kosai bayan sun gaisa sai Hannah ta bi kowannen su da kallo daya bayan daya, yamutsi sunan wani kaya. Duk sunyi kaca- kaca dasu kayan jikinsu dukkansu matan da mazan, nan fa aka hau koke-koke. Kallon Hannah
suke tamkar sun sami hoto saboda kyawun da tayi kamar gwal. Sai Hannah ta shiga yi musu nasihohi
tana basu shawarwari akan masu karuwanci, sace- sace da shaye-shaye su daina abu ne marar kyau. Ta kara da cewa harda rashin ilimi yake damunku babu arabi babu boko. Don haka su shiga makaranta su koyi karatun alkur’ani su yaki jahilci.
Daga karshe ta shaida musu zata bar musu kudi a wajen Iya Salma a hankali a samu gida mai dakuna
da yawa a saya musu su koma su zauna su rungumi Uwarsu sannan suyi aure, ta ce zata basu kudi akai Iya Abu asibitin kashi na Kano ayi mata maganin ciwon kafa sannan dukkan su zata ba su jari kowa ya samu sana’ar yi, kada su kara barin
Iya Abu tayi bara. Sai suka fashe da kuka dukkansu suna godiya. Iya Abu na kuka tana cewa “Na shuka tsiya na girbi tsiya, na cuci kaina
da *ya*yana na hana su karatu yau gashi sun tashi atutar babu. Hannah ki yafe min abun da nayi miki na yiwa Mahaifinki Allah Ya jikan Habi da Habu. Iya Salma ta ce “Allahu Akbar, albarkacin Hanne yau Malam Habu ya samu addu’a da dai ba’a taba yi masa ba.
Haisam ne ya shigo ya same su suna magana, Iya Abu na kwakwazon kuka tana nadama. Ya ce “Abu yi hakuri haka duniya ta gada ka so naka duniya ta kishi, sharri da jafa’i babu wanda baki dora akan Hannah ba, saboda tana
zuwa makaranta kin bi duk gari kina fadin iskanci take zuwa ba karatu ba a karshe kalmar iskanci sai ta dira akan *ya*yanki mata suna aure ma suka kaso auran suka zama karuwai, Allah Ya kiyaye
gaba. Iya Abu ta ce “Tone-tone ma ai a barshi Uncle Haisam kuyi hakuri dai Allah Ya baku ku bamu
amma bala’in duniya wanne ban gani ba, sakayya babu wacce Allah bai nunamin ba ni da *ya*yana
tun bayan tafiyar Hanne ban huta ba, zuciyata bata huta ba, sai bakin ciki kala-kala. Daga karshe Iya
Abu da *ya*yanta suka tafi da kudin da Hannah ta raba musu suna ta godiya. Hannah da Iya Salma da Wada suka zauna suna lissafi, Hannah ta bayar da kudin gidan da za’a kaiwa mai gari a sayawa su Iya Abu. Sannan ta dauko kudi mai yawa ta bawa Iya
Salma ta ce nata ne ta zauna a gida ta dinga cin Kaza da abinci mai dadi ta daina zuwa kasuwa talla,
sati na sama za’ayi bikin Wada ta bada kudin komai wanda za’a bukata na hidimar bikin. Ta shaidawa Iya Salma cewar nan da *yan watanni za’a gama
gina gidaje zata zo ta dauketa ita da Wada da matarsa su kaura Kano, katafariyar Super Market
zata bude shine take son Wada ya zauna mata a kantin yana kula da wajen. Murna tasa Iya Salma
kuka sai juya makudan kudin da Hannah ta basu take yi tana godiya.
Haisam da Hannah da direbansu sun fito daga Babban-mutum sai suka nufi Rigar da Malam Habu
yake, sun iske shi bai fita kiwo ba yana jiran isowarsu. Bayan sun gaisa Haisam yayi masa
bayani nan da sati uku za’a gama biza za suzo su dauke shi su tafi Makka. Sai farin ciki ya rufe Malam
Habu kudi mai yawa suka jifge masa, Hannah sai zarowa take tana tulewa a gabansa shi kuma
hanata yake yana cewa “*yar Baba kudin ya isa haka mai zan saya a Rigar nan da wadannan
makudan kudi. Shima Malam Sule sun shiga har gidansa sun raba musu kudi shi da matansa sai
godiya suke suna murna. Aka hadu a gidan aka yi ta hira har hira tayi hira Hannah ta gane ashe Malam
Sule kanin Malam Sale ne tsohon da ya bata abin busa a wajen kiwo tun tana yarinya. Aka rakata
gidan marigayi Malam Sale ta yiwa Iyalansa alheri mai yawa. Dakyar Haisam ya banbaro Hannah daga
rigar nan, bada son ranta ba ta baro mahaifinta.
*yan rigar suka fito kusan gaba dayansu wajen motar su Hannah suna daga musu hannu. Shehu
yaja motar suka tafi. Hannah zata fara hawaye saboda zata tafi ta bar Mahaifinta sai taga Haisam yana harararta, ya tsareta da ido baya ko kiftawa sai ta wayance ta fasa yin kukan ta hau yi masa
hira. Haisam yayi murmushi ya ce “Hannah kuka sunanki daga yau. Hannah ta kwanto a jikinsa ta
kashe murya ta ce “Kukan farin ciki zanyi Yaya, daka barni na yi, kadan fa zanyi hawaye daya biyu shikenan sai inyi shiru, suka kyalkyale da dariya dukkansu. Haisam ya ce “Kinyi digiri a kuka har kaiyadewa kike yi kenan.
Ba su tsaya a ko’ina ba sai a garin Kazaure kofar gidan Uwar biyu. Suka iske ta a tsakar gida tana
sakin danwaken siyarwa. Ciwon kafa ya hanata aiki a makaranta sai a gida take siyar da abinci
kala-kala na safe daban na rana daban na dare daban. Uwar biyu ta bude baki tana mamakin
ganin Haisam da Hannah. Haisam yayi dariya ya ce “Uwar biyu Hannah matata ce, munzo gaisheki ne.
Ta yi hawaye ta ce “Har Babban mutum naje neman Hannah da naji ance Mahaifinki ya rasu inyi miki
ta’aziyya, inga yaya zamanki yake da Iya Abu inda hali in dauko ki kizo mu zauna tare, sai aka cemin
kin koma Niger. Hannah ta ce “Allah Sarki Uwata ta kaina nima ina tunaninki kullum. Ta shimfida musu tabarma a gindin wata bishiya mai iska a tsakar gidanta, ta zubo musu ruwa da danwaken ta kawo musu sannan tazo ta zauna suka gaisa. Bayan sun
gaisa sai Hannah ta kwashe labarin Mahaifinta ta fadawa Uwar biyu cewar bai rasu ba yana nan da
ransa. Uwar biyu tayi murna ta taya Hannah murna matuka. Haisam ya dubi agogon dake daure a hannunsa ya ce “Yanzu sha biyu da rabi a Kano nake so muyi Sallar azahar muci abinci a gurguje
muka zo mu gaishe ki, sannan idan ba zaki damu ba Hannah tana so tazo ta dauke ki ki koma Kano
da zama tare da ita kibar wahalhalunnan. Yanzu haka tasa a gina muku gida a kusa da nata ki koma ke da Iya Salma. Uwar biyu ta fashe da kukan murna, kudi dumus taga Hannah ta debo daga
jakarta ta ajiye mata a gaba tayi godiya ta rako su har wajen mota suka shiga suka tafi.
Suna isa Kano basu tsaya a ko ina ba sai a filin jirgin sama Haisam ya cewa Shehu direba ya tafi gida da motar ya shaidawa Ramlah sun wuce Abuja nan da kwana hudu zasu dawo. Bayan sun sayi tikiti suka yi Sallah suka ci abinci a filin jirgin. Sun isa Abuja da yamma, direban ofis din Haisam yazo ya daukesu wato wajen sayar da motocinsa. Kai tsaye ya wuce
da su katafaren Hotel din nan wato Sheraton Hotel. Hakika hutu ya yiwa masoyan nan biyu dadi fiye da
na kasashen wajen da suka je. Saboda hankalin Hannah a kwance yake, sai farin ciki ya rufeta idan
ta tuna Maihaifinta na nan a raye bai mutu ba har tsalle take akan gado ta diro kasa ta fada kan
Haisam tana murna. Haisam sai ya zauna yana kallonta kawai yana murmushi domin farin cikinta
shine farin cikinsa.
Da yamma suna saukowa wajen swimming pool suyi ta wanka da safe kuma sai direban ofishin
Haisam yazo ya dauke su suyi ta yawo a cikin gari waje-waje na hutawa da wajen ciye-ciyen makulashe. Gidajen *yan Uwansa da abokan arziki duk sun zazzaga haka ake ta bawa Hannah
kyaututtuka. Sunje wajen sayar da motocin Haisam wajen ya kawata ga motoci galla-galla. Kamar da
wasa Hannah ta zabarwa Mahaifinta wata galleliyar mota ta ce idan ya dawo daga Saudia zata bashi, maimakon tayi godiya Haisam ne yake mata godiya saboda yaji dadi sosai yau Hannah ta tambayeshi abinsa. Kwanansu takwas a Abuja sannan suka
hau jirgi suka dawo Kano. A daren da suka dawo Ramlah zata haihu. Haisam da Hannah suka rakata
asibiti, ta haifo zukekiyar *yarta mai kama da Ubanta sak. Bayan kwana biyu Haisam ya tambayi
Ramlah wane suna za’a sawa *yar, abin mamaki sai ta ce asa mata sunan Hannah. Hannah tayi farin ciki matuka gata jininta ya hadu da *yar, bacci ne kawai yake rabo Hannah daga dakin Ramlah wajen *yar jaririyar. Ranar suna anyi bidiri Naira ta sha kashi an kashe Naira, an lika Naira. Taron mata kuwa harda wadanda ba’a gaiyace su ba, kasancewar Ramlah yanzu ta zama mai jama’a ana ta sanarwa a radiyo sai jama’a masu sauraron shirinta suke nemo inda take suna zuwa tayata murna.
Saboda hidimomin suna Hannah da Haisam basu samu dama sunje sunga Malam Habu a cikin satin
nan ba, sai sati na sama Haisam ya fara cuku-cukun neman bizar tafiya Makkah. Ya ba Hannah hakuri ta
bari in an samu bizar tafiya sai suje su dauko shi su wuce. Suna cin abinci suna hira suka sanarwa da
Ramlah halin da ake ciki cewar Mahaifin Hannah bai rasu ba, tayi mamaki kwarai ta taya Hannah murna sosai, sun shaida mata nan da sati mai zuwa zasu je
su dauko shi su kai shi Saudia. Haisam da Hannah sunje gidansu Haisam sun shaidawa Alhaji da
Hajiyar Haisam labarin Mahaifin Hannah, da farko Mahaifin Haisam da dariya ya tuntsire saboda labarin yayi masa kama da tatsuniya,, Mahaifiyar Haisam cemusu tayi yaushe muka zama Kakannin ku kuke mana wasan haka? Sai da suka ga da gaske suke har rantsuwa Haisam yake ya shaida musu zasu je su dauko shi sati mai zuwa su raka shi Saudia don ya ce ba zai biyo su ya zauna anan ba. Sunsha mamaki sun taya Hannah murna kwarai da gaske.
Bayan komai da komai na tafiya ya kammala Haisam da Hannah suka shirya suka nufi rigar da Malam Habu yake suna isa babu bata lokaci mai yawa suka dauko shi suka taho da shi Kano. Malam Habu yasha mamaki da ganin gidan Hannah ya bude baki kawai yana kallon kayan alatu, a bangaren Hannah aka sauke shi a dakin kasa.
Ramlah tazo ta gaishe shi sai da fuskarta ta fado masa a rai, ya hangota lokacin da tazo ta ci masa
mutunci akan Hannah ta rabu da Haisam, ya jinjina a ransa ya ce rayuwa kenan yau gata a durkushe a gabansa tana gaishe ni cikin girmamawa. Ya karbi *yarta yayi mata addu’a daga karshe ya nuna farin cikinsa da aka sa ma yar sunan Hanna.
Da daddare Mahaifan Haisam suka zo suka gaishe shi suka kawo masa farfesun dakwalan kaji da juice kala- kala. Bayan zuwansa da kwana uku suka nufi kasa mai tsarki. Kwanan su Hannah goma a Makka.
Bayan sun tabbata sun samarwa Malam Habu gidan zama wadatacce kudi mai dinbin yawa wanda zai ishe shi ci da sha da sutura sun daukar masa ma’aikaci daya da zai dinga kula dashi, wankin kayansa da kuma rakashi duk inda zaije kamar Madina ko Jeddah duk dai inda yake so ya je.
Mallam Habu yayi matukar jin dadi da ya bude ido ya ganshi cikin wannan kasa mai tsarki ga shi ga
Ka’aba, zai je duk inda yake so a cikin kasar Makka babu mai kamashi saboda sun yi masa igama ma’ana takardar izinin zama a kasar har lokacin aikin Hajji.
Bayan su Hannah sun dawo Nigeria ba dadewa jarabawar Jamb dinsu ta fito kai tsaye suka bata
Medicine saboda points dinta ta cancanci idan course din da yafi Medicine ne a bata, murna a wajen Haisam abin baya musaltuwa har ya fi Hannah murna. Haisam ya taya ta yin registration,
bayan registration ba dadewa suka fara lectures. Karatu tukuru ta sa a gaba musamman ma idan ta
tuna irin yadda karatun Medicine yake da muhimmanci a wajen taimakon al’umma. Tana da burin ta ga tana taimakon talakawa a rayuwarta.
Ginin da ake yiwa Hannah yayi nisa, duk da ba’a kare ginin ba amma zaka san katafaren gini ne mai
kyan gaske. Shinfideden masallaci, daya bangaren makarantar Islamiyya ta matan aure da yara ga
bandaki nan a gefe. Can baya kuma wata kofa ce inka shiga zaka tarar da gidaje iri daya guda biyu,
masu dauke da katafaren falo da dakunan barci uku-uku kowannensu da bandakinsa a ciki da kicin. Haisam ya sayawa Hannah da Ramlah wani katon fili a Ahmadu Bello way inda kowacce a cikin kudinta ya ke gina mata katafaren kanti kamar yadda Hannah ta ce tana son super market a kusa da nan ake gina mata wani ofis na tallafawa
marayun yara. A kusa da shi katafaren kantina biyu ne na Ramlah, daya na sayar da kayan Senegal dinkakku (ready made) daya kuma na sayar da takalma da jakunkuna *yan waje.HaiRamHannah! HaiRamHannah!! Bayan an gama ginin an kawata
shi da fitilu da tiles sai akayo odar kaya wasu daga kasar waje wasu daga kamfanonin nan kasar. Dai-
dai lokacin an gama ginin Masallaci. Islamiyya da gidajen Hannah sai aka zuzzuba kayan da suka
dace a cikinsu. Hannah da direba suka nufi Babban-mutum don dauko Iya Salma da Wada da matarsa, *yan kayayyakinsu na sawa kawai suka tsinto sababbi suka shigo mota suka biyo Hannah,
suka bi ta Kazaure dan dauko Uwar biyu. Daman ta gama sanarwa danginta zata koma Kano Haisam da Hannah sun yi alkawarin zasu dau nauyinta gaba daya har bayan ranta. Suna zuwa awa biyu tayi yawa Uwar biyu ta dauko dan buhun kayanta ta yiwa Makwabta sallama daman babu wanda ta
ajiye banda *yarta Halima kuma tayi wani sabon Auren a Daura, ta shigo mota suka tafi. Sun sha
mamaki suna ta kallon katafaren gidajen da akace nasu ne komai da komai akwai a gidan. Kowanne
daki an shimfida kafet da makeken gadaje da mudubai da waduruf din jikin bango. Haka falo ansa kujeru da kayan kallo. Kicin ma da cooker
gas, fridge da duk abubuwan amfani, komai sabo fil a ledarsa. Hatta kayan sawarsu Hannah tasa an dinko musu atamfofi an zuba a cikin waduruf. Sanyin A.C ko ina ya gauraye gidan, masu aiki biyu
aka ajiye a gidajen daya mai girki daya mai shara da wanke-wanke da wankin bandaki. Ga mai
wanki da guga nan duk sati zaizo ya dinga dauka yana wankowa. Wada ya gigice a lokacin da Hannah da Haisam suka kaishi katafariyar super market din, anan
akace ya dinga kula da ma’aikatan wajen yana sa ido akan yadda ake gudanar da cinikin.
Kasancewar yayi makarantar sakandire ya iya karatu da rubutu. Hannah ta kara masa da cewa “Yanzu baka san gari ba kuma baka iya mota ba za’a dinga kaika ana dauko ka da motar kantin,
nan gaba zan saya maka taka ta kanka. Wada yana ta murna yana godiya haka Iya Salma da Uwar
biyu sun sha koke-koke don murna suna ta godiya. Wada da matarsa Jidda a gida daya, Iya Salmai da Uwar biyu a gida daya kowacce a daki daya, daki daya ne babu kowa aka kulleshi. Su ci, su sha suyi wanka a kunna musu kallo shikenan
aikinsu suyi ta hira. Wani lokaci Iya Salma ta ce azo a danno mata lamabar Malam Habu a Makka su
gaisa. An huda kofa wacce zata kaika gidansu Hannah, kullum Hannah sai ta shigo gidan tsofaffin
nan ta tayasu hira bayan ta taso daga makaranta,
gaba dayansu suna cikin tsananin farin ciki da nishadi ko ba’a gaya maka ba idan ka kalle su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *