GIDAN NAGOGGO COMPLETE BY FATEEZAH
Tsawar da naji shi ya dakatar dani da bude dakin Ammy na.
“wallahi Bahijja in kika shiga dakin nan sai na bata miki rai,Uban mai kika zo yi mini a gida,ki tashi ki koma inda kika fito,tunda baki daukeni a bakina komai ba “cewar Alhaji kenan.
Take naji wata wata fargaba ta ziyarceni,wai yaushe zan fara samun kwanciyar hankali da maslaha tsakanina da Mahaifina,maganar Ammy tace ta tsinke min dan gajeran tunanin da na shiga wacce take tambaya abunda ke faruwa.
Alhaji ne ya fara magana cikin fushi “Amina ki juya ki koma ciki, in ba so kike fushin wannan mara kunyar ya shafeki ba,in kuma ba haka ba wallahi zanyi mummunar saba miki”.
Da sauri na juya domin fita daga gidan don ganin Ammy na ta juya tana hawaye,ji nayi na tsani kaina,don tun ina Yarinya har girmana ta dalilina Ammyna ke zubar da hawaye.
Daga gefen gidan na tsaya ina kokarin tsaida hawayena da tunanin mafita.
Yanke hukunci nayi kawai akan na tunkari gidan Yaya Baffa wanda shine Babba a mazan gidan,don ina tunanin duk da ‘Yan Uba nake dashi zai iya taimakona ya rokan mun Alhaji duk da wannan karan bansan laifin da nayiba.
Achaba na tare na hau tare da fada mai Anguwan dazai kaini,cikin 10minutes muka isa gidan saboda bamu da nisa,kasancewa Alhaji yana Banzazzau shikuma Yaya Baffa yana filin Mallawa,sallamar dan Achaba nayi na karasa nayI knocking din gidan,after some seconds Gateman yazo ya budemin tare da mun sannu da zuwa na kutsa kai harabar gidan.
Gida ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo daya kayi ma gidan kasan mai gidan ya jiku da naira,hanyar da zata sa dani da main door din gidan na nufa,zuciyata na bugawa kamar zata tsago ta fito saboda shima bansan irin karban da zaya min ba.