GIDAN SARAUTA CHAPTER 5

GIDAN SARAUTA






CHAPTER 5




Asma’u ne tace lafiyarki Afiya?…..
turo baki tayi tana nida Yaya Almustapha ne wallahi,nakai mishi tea yanaji inata bubbuga kofa amma yaki kulani,cikeda damuwa Asma’u tace yakarbi tea dinne?…..
Gyada mata kai tayi,kekikayi tea din?…
Aa daga cikin gida akayo tanabata ansa tayi shigewarta cikin dakin Ummi,dasauri Asma’u tayi hanyar dakin cikeda damuwa batareda tayi sallama ba ta bankada cikin dakin wannan karan ah zaune yake jikinshi sanye da wando sekuma singlet fara hannunshi rikeda tea din yakai baki…………
Batasan sanda hawaye suka fara bin kuncintaba…


Zuciyarta ne tashiga dukan uku uku……..
Setaga kuma yacire cup din ah bakinsa yamaido da hankalinsa gareta sakamakon banko kofar datayi,hamdala tayi ah zuciyarta sannan tashiga takawa cikin dakin batareda tasan abun yiba……..

Shikuwa kura mata idanu yayi yana mamakin karfin hali irin nata,karasawa gabanshi tayi tana wasa da yan yatsunta,tsaki yayi sannan yadauke kai gareta yana shirin kuma kai shayin bakinshi cikin sauri ta wabce cup din wanda har seda kadan yazuba ah hannunshi……….
Tashi yayi rai bace”lafiyarki?”…..
Rasa abun fada tayi tana muzurai sekuma tayi azama tace
Shayina ne cikeda rashin gaskiya sannan takara da miyasa zaka shamun shayi ka debo naka mana takarashe maganar tana murkuda baki……
Tsayawa yayi yana kallonta cikeda mamaki yayinda 99% na zuciyarshi ke raya mishi duk yanda akayi yarinyar nada tabin kwakwalwa mika mata hannun shi yayi alamar tabashi shayin shi amma taki,taku yashigayi zuwa gabanta yayinda zuciyarta ke mugun bugu tana ja da baya……
Cikin cool voice dinsa yace”give me my tea”,yanda yayi maganar bazaka taba tunanin ranshi bace yakeba………
Baya takuma yi tana”shayina ne banaka ba”…….
Damko hannunta yayi cikin sauri don hakurinshi ya kare yana shirin kwata ganin dagaske yake kawai setayi wulli da cup din yafadi can gefe,hamdala tayi ah zuciyarta yayinda afili tace”ai wallahi sede kowa kada yasha shayin nan”………..
Sakan baki yayi yana kallon tea din dake zube ah kasa yayinda cup dinma ke gefe,ganin attention dinshi baya kanta tayi saurin kwasa aguje tafita ah dakin zuciyar ta na dukan uku uku don tasan tabbas tashiga hannun Almustapha yau me kwatanta se Allah……..
Abakin kofar dakin takusa cin karo da Dad,cikin sauri tashiga mutsu mutsu don tarasa ta’ina zata fidda kanta awannan mess din ace Dad yaganta ah dakin Almustapha tana fitowa kuma aguje what will he think of her…….
Cikeda da in ina tace D…a…d, murmushi yayi sannan yace calm down Asma’u kizo muyi magana kinji……..
Gyada mishi kai tayi dukda kuwa irin rawar da jikinta keyi,juyawa yayi yayinda tabi bayanshi jikinta ah sanyaye harzuwa wata yar karamar parlour wanda bata taba sanin dashiba acikin gidan Mom tagani zaune kan daya daga cikin royal chairs din dasuka sha ado tana sakar mata murmushi tsayawa tayi ah bakin kofa har Dad din yasamu guri yazauna Mom ne tace”yakika tsaya ajikin kofa,zoki zauna mana Asma’u”,simi simi cikin takunta ahankali tasamu jikin daya daga cikin royal chairs din ta rakube tana wasa da hijabinta…….
Shiru kakeji ah parlourn inbanda Tv dake aiki, examining dinta Dad yakeyi yalura gabadaya ah takure take cikin sanyin murya yace”Asma’u”…..
Azabure tadago tana kallon shi kafin tamaida kanta kasa sannan ta ansa”na’am”…..
Murmushi yayi sannan yace kinga nakarya alkawari ko,nace zankai ki gida amma haryau shiru kiyi hakuri wallahi abubuwane sukashamin kai bawai namanta bane,kina raina wallahi and munyi magana da mahaifinki i told him kina nan gida……
Dagowa tayi cikin sauri cikeda mamaki gyada mata kai yayi alamun eh……..
Kafin yace”meya hada ki da Almustapha,naganki ah dakinshi dazu?”…….
Adaburce tadaga hannunta tayi folding tuni kuma hawaye suka shiga zubowa”kayi hakuri don Allah ban shiga dakin shi dawata manufa ba i went there to protect him”…….
Murmushi Dad yayi ganin yanda take stammering yace”calm down,I believe you kidaina tsoro kaman wanda kikayi wani mummunan laifi I was there watching you two so don’t worry,just feel free and tell me everything”…..
Jitayi hankalinta yakwanta kadan sannan tashare kwallarta kafin tashiga bashi labarin abunda taji dakuma zuwa dakinshi datayi don hanashi shan shayin, ahankali tace we’re not in good terms with each other Dad nasan kona fada mishi ba lallai ya yarda daniba shiyasa nayi behaving that way……

Dad da tunda tafara magana yake sauraronta yace”nagode Asma’u,nagode sosai da taimakon ki kuma bakiyi laifi ba sema taimakon mu da kikayi”. ..
Dan numfasawa yayi sannan yasake gyara zamanshi yana mamakin wani irin haline Magajiya kedashi hakanan,anya tanada zuciyar Imani ah tattareda ita kuwa,kallon Asma’u yayi sannan yace dabadan keba bansan mezai faruba yau amma alhamdulillahi Allah yatakaita abun, Almustapha abun tausayine dagashi har kannensa dama mahaifiyarsa they’ve gone through alot Asma’u,dan kallonta yayi sannan yace kowa yanayimishi kallon mutumin banza basusan cewa Almustapha from the inside mutumin kirki bane,kowa yana mishi kallon Dan iska and all sort of things, they’re blinded by Magajiyas lies batareda sunsan Almustapha is a pure guy with pure heart ba sharri ne da hatsabibancin munafukai yasa akeyimisu wannan kallon ahankali Dad yashiga bama Asma’u labarin Almustapha dasu Amira tundaga farko harzuwa yau babu abunda takeyi se aikin kuka,duniya inazaki damu mutane babu Imani abunda tadin ga ayyanawa aranta kenan, shiyasa yake nisantar kansa da mutane ashe ita daman she never believes that he’s a bad person, Dad ne yakuma dubanta sannan cikin muryar tausayi yace he needs someone to be with him,yana bukatar wanda zaidawo mishi da *FARIN CIKIN SHI* ,yana bukatar support,yana bukatar metayashi fighting for his right hakanan yana bukatar abokin rayuwa dakuma abokin shawara shiyasa nayi tunanin nema mishi matar dazai aura and banga wanda yadace dashiba irinki Asma’u,I know you’ll support him through all his endeavours, nasan you’ll always be there for him daga yanda naji labarinki dama kuma abunda kikayi yau I’m indeed very grateful to you……..
Bazan takurakiba Asma’u hakanan bazan saki doleba it’s just a Fathers request indai zaki iyayimin wannan taimakon,nasan mahaifin ki sanin gaskiya sabida munyi hulda dashi ah Indonesia bantashi sanin shine ba se bayan munje gidanku ana cikin bikin nan naga bancika miki alkawari ba shine nasa Sulaiman yanemo min number sa da full name dinsa don Inkirashi tunda naga sunan naji kaman shidinne sede bazaka tabbatar ba tunda suna yakan zama daya bawai mutum daya ke bearing suna shi kadaiba anasamu different people with same name and family name as well….
Bayan mungaisa his voice sounds familiar that was when I decided to ask him shine yake fadamin shine,mungaisa sosai sannan nafada mishi kinanan and yace zeturo ah daukekima nace masa aa I’ll bring you by myself ai munjima ma bamu haduba,dan numfasawa Dad yayi sannan mahaifinki mutumin kirkine bawani jimawa muka yi dashiba amma munsaba sosai munyi kasuwanci dasu ah company danake aiki I was the manager back then damuna gaisawa daga bayane mukayi loosing contacts na juna………….
I’ll take you home tomorrow in Sha Allah, kishirya maganar auren ‘Dana I won’t stress you komiye ansar ki zan ansheshi hannu bibbiyu Asma’u………
Yanda yayi maganar muryarshi ah karye setaji tausayinshi, she want to help them amma kota auri Almustapha basonta yakeyiba na daya and na biyu ita bataga metake dashiba dahar zata taimakesu dashi,bazata iya duban Dad tace mishi bazata auri danshi ba hakanan bazata iya duban Dad din tacemai directly tayarda ba tasani batada haufi ko kadan indai don ta taimaki Almustapha ne zata aureshi sede Daddy fa?…
Zeyarda ne after all that happens,wata zuciyar Kuma tace tunda haryace zeturo ah dauketa kenan yasauko daga fushin dayakeyi kenan……..
Dad ne yakuma cewa,kinyi shiru bakice komaiba kodanma tashi kije you can think about it duk sanda kikasamu ansar bani I’ll wait……….
Kanta akasa tace nibanida matsala Dad indai Daddyna ya yarda,wani kayataccen murmushi Dad yayi sannan yace Allah yayi miki albarka,thank you so much Asma’u gobe zamuje gidan ko?..
Gyda masa kai tayi sannan yace tatashi tafita hartabar dakin albarka yakesaka Mata murmushi Mom tayi tana cewa yarinyar akwai hankali ga kunya………….
Murmushi Dad yayi sannan yace inaji ajikina Asma’u alkhairi ce agaremu tun farkon ganina da’ita hakanan inaji ah jikina zata zamo sanadiyar gyaruwar masarautar nan dayardar ubangiji…..

Story continues below

Murmushi Mom tayi sannan tace, Allah yasa….
Amin yabata ansa kafin suka canza wata hiran kuma…..

Shiko gogan naku tunda tabarshi tsaye agurin be motsaba bare yabi bayanta,don gani yayi jama kanshi raini zaiyi and he’ll surely advice Sulaiman daya taimaka yamaida ta gidan su tun wuri afara mata treatment kar abun yayi worse she always behaves strangely,farkon haduwarsu she keeps following him duk inda yaje,tadinga mishi naci and abunda yafi bashi mamaki ta tsallake iyayenta tazo tamaikonshi da safiyar Allah,baya tunanin sensible mutum zeyi hakan bayan kowa yasan waneneshi,bayan kuma ga irin kallon da jama’a keyi mishi on top of that tazo tana ignoring dinshi and all of a sudden today tacanza mai lokaci daya,shidai dari bisa dari zuciyar shi kefada mishi she’s not normal and she’s not physically stable………
Sake kallon trash din data hadamai ah daki tayi,tsaki yayi don shiba mutum bane maison kazanta don duk talaucinsu bazaka taba shiga dakinshi kaji yana tsamiba kokaganshi ba a gyareba kullum kannenshi ke gyaramai tunda sunsan hali,yanzukuma bayajin ze iya fita yakira su suzo suyi cleaning trashi din shima kuma bayajin yi din sede sanin halinshi inbe goge ba abun ze dameshi yadinga irritating dinshi don haka yashiga bathroom yasamo abun gogewa yazo yagoge tas kafin yakoma bakin gado yakwanta donyin bacci because baida zeal din yin karatun kuma anymore………..

***

Tunda takoma daki take tunanin what has she gotten herself into data fadama Dad yanemi izizin Daddy,what if Daddy yayarda yazatayi da auren wannan marar mutuncin sede wata zuciyar tafi bata kwarin gwiwa kan cewa Daddyn ma ba lallai ya yardaba dawannan tunanin ta kwanta gefen Sumayya datayi bacci kan kafet da alama chat take bacci yadauketa……..
Tana cikin haka ne taji sallamar Sulaiman, murmushi tayi tatashi tazauna karasowa yayi yana kallon sleeping Sumayya ah kasa murmushi yasaki sannan yace “rigimamman nan anan tayi bacci?”…..
Gyada mishi kai Asma’u tayi sannan tace nima yanzu shigowa na nasamu tana bacci inaganin chat take baccin yayi awun gaba da’ita……..
Dauko pillow yayi kan bed din sannan yadan daga kan Sumayyan yasaka mata pillow sannan yadauko blanket ya lulluba mata tareda rage gudun fan tunda ga AC ma kada suyi mura,dawowa yayi gaban Asma’u din sannan yace nazo yimaku saida safe kinga harsunyi bacci abunsu yakarashe maganar yana kallon Ummi fuska cikeda damuwa…….
Eh wallahi,sannan tace niko Yaya Sulaiman inba matsala inason yi maka magana kan rashin lafiyar Ummi…….
Inajinki yayi maganar yana zama don ya lura serious magana zatayi,wasa tashigayi da hannunta tana contemplating kotayi magana ko kartayi sannan kuma tace”inaganin yakamata ah hada da addu’a bawai kawai ayi relying ah magungunan asibiti ba,Dad yafada min komai Yaya Sulaiman nikuma anawa ganin kuna facing irin challenges dinnan yakamata akama Allah sosai adukufa dayi mata addu’a ace mutum yana kwance for so many years baya magana kuma likitoci ma sunce basusan dalilin rashin maganartaba and other pains datakeji ah jikinta abunda kawai suka sani tasamu stroke wannan kadai ya isa cewa something is going on……
I’m sorry if I’ve said something wrong amma anawa ganin please mugwada bama addu’a da rokon Allah karfi ga malamai da dama muma kuma mutashi in sha Allahu za asamu cigaba……….Dad becema Asma’u Magajiya mahaifiyar Sulaiman bane ah labarin daya bata don duk ah tunaninta mahaifiyarsu daya dasu Amira din shiyasa tafada mishi abunda keranta…..
Tunda take maganar sulaiman ke murmushi ahankali yace wannan is a good point nima daman tunanina kenan wallahi Asma’u,nagode kwarai da shawararki nalura munyi sake sosai da addu’a cikin lamuran mu bayan kuma munsan muna bukatar taimakon gurin mahaliccin mu in Sha Allah za agyara nagode sosai barinaje gurin Amarya kada tayi fushi…..
Smile tamishi sannan tamishi saida safe tana ka kashe wutan inzaka fita,aikuwa yakashe dayazo fitan don switch din na kusa da kofa kwanciya tayi tana saka da warwara ita kadai tare kumada farin cikin gobe zataga yan gidansu………..

****
Tunda yayi sallar asuba baikoma bacci ba don seyakeji kodan runtsawa yayi abunda yafaru dashi kowani shekara abaya su zasu sake faruwa dashi,wanda yayi sannan yadauko daya daga cikin usual four set dayake dashi yasaka don haryanzu bawai yanada wasu kayan bane daga kayan sarautar da aka bashi ranar yasaka se gezna guda biyu sabbi dasuka sha dinki mekyau da Sulaiman yabashi yasaka ah biki,tunda aka gama bikin ya ajiyesu at side kaman wanda aikinsu yakarene… ko breakfast beyiba yafita ah sashin nasu don yalura basuma tashiba se bayine dake ta kai kawo,koda yafita duk inda yabi dogaraye zubewa suke kasa suna mika mishi gaisuwa dukda kuwa bawani kayan kirki bane ajikinshi hakanan wasu daga cikin dogarayen da bayin sukanzo daddaya suna bashi hakuri wanda sukasan abu yataba hadasu har suka mishi maganar banza,shiko kalma daya yake cemusu”it’s okay,yawuce”….
don aganinshi mezai ce musu kowa yayi nagari donkanshi besides shibama damuwa yayi da sarautarba bare ace and harga Allah berikesu da komaiba……..
Almustapha successfully ya’isa school yana duba agogon hannunshi seven thirty lokacin murmushi yayi yana tuna statement din Sulaiman najiya”I’ll be here by 7:00am inkaika school zanjiraka har saika rubuta exams mudawo gida”,ah zuciyarshi yafurta”ango seven din kenan!”…….
Exams venue din yaje inda har invigilators sunzo students da dama sunyi mamakin ganinshi don anriga ansani he always miss the exam and that’s what makes him always fail inbahakaba Almustapha mutum ne me kwazo dabawai yadauki carryover din sabida rashin ilimi bane ba, alhamdulillah yashiga sunyi practical din successfully ya fito wani hamdala yadingayi aranshi hakanan yakejin wani free sabida yasani dayardar ubangiji banadai kam yagama da ABU inbadai wani iko na Allah ba……..
Shagon Mallam Hudu yayi deciding yaje don kwana biyu baijeshi ba,aikuwa yasameshi kuma ba customers sosai don haka suka gaisa Mallam Hudu yayi musu murna sosai se fatan alkhairi yakeyi mishi,Yana kaga ribar hakuri ko in Sha Allahu nan bada jimawaba komai zai dawo daidai dayardar ubangiji…….
Gyada kai Almustapha din yayi lokacin aka gama hada ma wani customer daya sayi kaya me uban yawa kayanshi gefe guda,daukan kayan Almustapha yashigayi yana kai mishi mota da daddaya Mallam Hudu nata hanashi murmushi kawai yayi batareda yace komai ba yayinda azuciyarshi yakecewa inbaiyi haka ba mezeyi ah rayuwa, this’s his job miyasa Mallam Hudu zai hanashi yi yaudin…….
Bebar shagon ba se bayan laasar yayima Mallam Hudu sallama yatafi…….

Story continues below

Labari kuwa ya fara karada gari cewa Mai Martaba yayi accepting Almustapha as his very own Son sannan ma har ana shirin bashi crown prince kunsan dai rade radin jama’a da insuka ji labari sesun kara da manda akai daga masu fadar wannan semasu fadan wancan har kunnensu waziri wanda har yanzu Mai Martaba bai sanar dasu komaiba dubada yaushe ma aka gama bikin yafison kowa yahuta tukunnan…….
Waziri dasauran mutanen fada basuyi magana ba don sundanyima Mai Martaba din uziri tunda sunsan komi zeyi ze tuntunbe su……..

Bangaren Magajiya kuwa tana nan hankalinta kwance kanyau Almustapha beyi exams ba sabida tasa ansaka mishi maganin bacci ah tea dinsa,hakanan baiwar data hada tea din bataga sanda Almustapha yafita ba shiyasa ma tayi tunanin yana daki don haka tacema Talatu aiki yayi kyau aikuwa har kyauta akayi mata mai tsoka………
*****
Bayan an idar da sallar laasar Dad yashigo tareda Sulaiman yace ah kira masa Asma’u,jikina bari tafito daga dakin don tun safe tayi wanka tazauna zaman jiran sa murmushi yayi da ganinta sannan yace” Yar Daddy yau sai gidan Daddy ko?”…..
Dariya tayi sannan tasamu guri ta rakube”Ina wuni Dad”…..
Lafiya Lau kinshiryadai ko?…
Cikin sauri tace eh, Amira, Afiya da Sumayya na gefe duk ransu ba dadi don sunsan zasuyi kewar Asma’u inta tafi dukda kuwa kebe kanta datakeyi ah daki,jin yarinyar suke sosai aransu, Sumayya ne tace zanbiku Dad…..
Sulaiman dake zaune gefen Dad yace babu inda zakije wayace miki anafita ah gidan nan kasafai?……..
Turo baki tayi kaman zatayi kuka hakanan tanajin kaman ta shake shi don ta tsani shishigin dayake mata yanzu,dariya yayi sannan yace Asma’u mutafi ko gwanda inje indawo kada Amarya tayi fushi…….
Jijjiga kai Mom tayi tana”Amma dai Sulaiman anji kunya”……
Sa tafukan hannunshi yayi yarufe fuskarshi waishi adole yaji kunya,dariya sukayi duka yayinda Dad, Asma’u da Sulaiman din suka fice bayan rakiyarda su Mom suka musu bakin kofa sunayiwa Asma’u sallama Mom harda bata kyauta ah leda dabatasan na menene ba……..
Hawayenta ta goge jin Sumayya tanacewa”zamuzo in Sha Allah friend”, Ummi ne tafado mata arai she’ll surely miss her tasani…………
Haka suka shige mota suka kama hanyar gidansu Asma’u din,horn sukayi mai gadin yabude musu gate don Mubaraq yace masa daman Daddy yana expecting baki yau da yanma…….
Kallon gidansu tadingayi tanajin wani irin dadi aranta dukda kuwa batasan irin tarbar daza ayimataba, parking sukayi yayinda Dad da Sulaiman suka fito Itama tafito daga motar jiki ah sanyaye ganin yanda take ne Dad yace “don’t worry, everything will be alright ko?”…..
Gyada mishi kai tayi yayinda suka nufi bangaren Daddy din daga waje ta tsaya batama shigaba don gani tayi bekamata taje tazauna dasuba aikuwa Daddyn baya side dinshi daga side din Mommy yafito bakin kofa yaganta ta rakube kamar munafuka, Asma’u yakira sunanta ahankali cikin sauri tajuyo take kuma taji kwalla sun shiga zubowa ganin Daddyn ne yakira sunanta yau da bakinshi……..
Dakyar ta iya tsayar da kukan tace Ina wuni, fuskarshi babu yabo babu fallasa yace lafiya sannan yace kiwuce cikin gida maza, harta juya zata tafi taji yace su Almustaphan suna ciki ne?,gyada mishi kai tayi don batajin wani word ma zai iya fita daga bakinta she’s just yearning to see her Mother and her lovely siblings……….
Dagudu tayi side din Ummin(wayaga akuyar daure tasamu sake)…….
Ba ita ta tsayaba se ah tsakiyar parlourn inda tayi arba da Ummi da Sadiq suna zaune suna kallo yayinda Munir da Munira sunacan gefe se musu sukeyi kan abunda batasan menene shiba sune suka fara ganinta dagudu sukayo kanta suna”Adda Asmeey”……
Rungume juna sukayi cikeda kewan juna ita kuka su kuka, Ummi ma dake gefe seda kwallar tazubo tana nadamar abubuwan datayi nakin jan yarta ah jiki….
Ahankali Asma’u tasaki kannen nata takarasa gaban Ummi…..
Hawaye na zuba ah idanunta, kallonta tayi ahankali sannan tace “I’m sorry Ummi,wallahi bazan sake…..ba”, ta karashe maganar muryarta na stammering………….
Rankwashi Ummin tayi mata kafin ta rungumeta cikeda son yartata tace”hankalinki daya kuwa,kawai seki fita kibar gida do you have any place dayafi nanne?”……..
Bata tsaida kukan nataba tace”kiyi hakuri Ummi nayi kuskure”, Ummin ma cikin kuka tace inkika sake daukar mataki batareda kin nemi shawarataba sena kakkarya ki Asma’u……
Murmushi tadanyi”I love you Ummina,nayi kewarku”……
Nima nayi kewarki yata don kuwa yau Ummi ajiye kunyar yar fari tayi ah gefe ta rungumi yarta don ta lura inta biyema hakan itane zatazo tana dana sani daga baya.breaking hug din tayi ahankali sannan tace ga abinci can kije kiyi wanka kizo kici kiga duk kin rame…….
Sadiq dake gefene yace”Adda Asma’u don Allah kada kisake tafiya kibar gida batareda izinin kowaba,bakisan yanda hankalinmu yatashibane shiyasa”….
Dan jan karan hancinshi tayi”in Sha Allah Sadiq bazan sake ba”, murmushi yamata kafin sukayi hugging juna ba ajimaba sega su Mommy da Asiya sunzo don su Munira sunje sun fesa musu nanfa aka shiga maida zance take basu labarin yanda akayi, Ummi ne tace aiharyau hankalin Suwaiba ba akwanceba barima insa kati inkirata infada mata dawowarki sannan takarada kije kiyi wanka kisauya kayan nan banason ganinsu sunyi datti sekizo kici abinci, Asiya ne tace Ummi nima zanci abincin dariya Ummi tayi sannan tace gaki gashi ai sewanda kika zaba don tunda jiya da dare da Daddy yaga damuwarta tayi yawa yafada mata Asma’un zata dawo gida yau yanasane da inda take shiyasa tatashi tun safe tashiga girkama yartata favorites dinta……..

Story continues below

Asiya ne taja hannun Asma’u sukayi daki tana kiyi wanka semuci abincin tare Sis, Mommy da Ummi ne suka bisu da kallo cikeda jin dadi ganin yanzu yaran sunfara hada kansu……..
Bangaren Daddy kuwa koda yashiga parlourn murmushi yasaki ganin Dad din sannan yakarasa cikin sassarfa”yau Almustapha ne agidana,ikon Allah ashedai darabon sake haduwarmu ah rayuwa”,dariya Dad yayi sannan yace kabari kawai ai in akwai Allah babu abunda is not possible……..
Mika ma juna hannu sukayi suka gaisa sannan aka shiga tambayar juna iyali, Sulaiman ne yagaida Daddyn cikeda ladabi yayinda Daddy ya amsa sannan yace wannan ma danka ne…..
Dariya Daddy yayi sannan yace yes he’s my Son Yarima,shine wanda akayi bikinshi Saturday daya wucen nan shida Sister dinshi cikeda confusion Daddy yace kana nufin you’re related to Mai Martaba don dai nasan Ya’yanshi ya aurar ….
Dariya Dad yayi sannan yace”wana ne uwa daya uba daya”,cikeda mamaki Daddy yace ikon Allah nidai ince Daddy’s girl kawai nasani but like serious ku Yan uwane,sekuma lokacin yaga kamarsu sosai seyayi dariya, Allah sarki bantaba saniba wallahi cewar Daddyn don duk zamansu Dad din betaba ambata ba nanfa suka shiga zancen data tarasu kuma bayan ancika musu gabansu da kayan motsa baki……
Dad ne yace Asma’u tadawo gida I’m sorry for all the inconveniences biki yasani ah gaba……
Murmushi Daddy yayi sannan yace babu komai Almustapha daka cemin tana wajenka hankalina bai tashiba kwata kwata sabida nasan she’s in a safer hands………
Nagode cewar Dad din sannan yace”maganar misunderstanding dasuka samu da Dana haryasa tabar gida shima we’re sorry it’s not her fault kasan gida irin namu se ahankali kowa burinshi yaga ya muzanta dan uwanshi don shi yazama yana gaba,to hakan yake Almustapha tun yana yaro yake fuskarta irin wayannan matsalolin daga yaddikonsa her goal is to ruin his image ah idanun kowa, she’s capable of doing anything,I know you might not believe me but in Sha Allah watarana gaskiya zai bayyana shiyasa bazanyi emohasizing ba kawai dai inason kayarda da yarka, continue to trust her the way you used to sabida I’m sure kasan irin tarbiyar dakayi mata,kasan abunda zatayi dawanda bazatayiba nidai abunda nasani Dana da Asma’u sharri akayi niyar yi musu shi akayi niyar hadashi da jama’ar gari itakuma akayi niyar hadata da nata iyayen sabida wata manufa nasu…..
Tabbas nasha mamakin irin tsatsauran hukuncin daka dauka kan Asma’u don gaskiya raina yabaci tunkan insan kaine sabida hukuncin daka dauka kwata kwata baidace da’ita ba,karka manta macece once she’s ruined shikenan wallahi in namiji kayima irin hukuncin nan babu wanda zai dama amma mace she’s a rare diamond that yakamata ah ajiyeta safely,mace nada value dabai kamata ana exposing dinta to the world ba,bekamata ana hankada ta inda marasa Imani suke nema ba sabida Muhammadu yaran mu nayanzu basu san darajar kansu ba bare na mace you’ve to control your anger please next time………
Cikeda nadama Daddy yace In Sha Allah zangyara nima naga kuskurena and alhamdulillah dabata fada hannun marasa kirkiba,I feel grateful for your kindness towards my Daughter and for giving her shelter…….
Kai Kai Muhammadu miye abun godiya anan don Allah ai Da na kowa ne wallahi Allah dai yacigaba da kare mana su shine addu’ar dazamuyi…….
Amin suka amsa dukansu yayinda Dad yace nida za abani ita ma Dan nawa ma inaso,nasan nayi shishigi dawuri sannan nasan Almustapha did not deserve someone like Asma’u aganin mutanen duniya but kaina ah kasa nakawo kokon barana inanema ma Almustapha aurenta nayi maka alkawari bazaka taba nadamar yin hakan ba……
I wouldn’t pressure you, kawai nafadi abunda keraina ne sabida munzauna da ita kwana biyu naga halayenta na gari dakuma sanin yakamata irin nata shiyasa bazanso inrasa yarinya irin Asma’u ah matsayin sirika ba,wallahi Muhammadu da inada Da namiji bayan Almustapha babu abunda zai hana ni nema masa aurenta sabida ma kasan cewa alheri nikeson ta dashi bawai inason hada ta dawan bai dace bane ……..
Murmushi Daddy yayi yana kallon Dad din daya kaskantar da kansa yana masa wayannan magan ganun,shiyanzu ya isa yace baya sone koyanada bakin cewa bazai aura ma Asma’u Danshiba sabida bashida tarbiya,inyayi haka beyi masa adalciba yasani sannan kaman yanda kawu yace inma Asma’u wrong choice takebi she’ll regret it herself so yanason tayi going through this test bawai beyarda da ita bane aa sede turawa sunce”there is no smoke without fire”, Asma’u might be innocent sede babu yanda zaayi babu kasonta ko kadan ah ciki shiyasa yabudi baki yace banida matsala da wannan Almustapha, Allah yazaba mana abunda yafi alkhairi inkun shirya kuzo godiya sosai Dad yayi sannan yace in Sha Allah za a turo kwana kusa we want to settle things kafinnan yara sesu fahimci juna Kuma……
Daddy dai aranshi cewa yayi wani fahimtar juna zasuyi bayan wanda sukayi ah baya ah fili kuma bece komai ba se murmushi dayayi shiko Sulaiman Allah Allah yake akoma gida ya zolayi Almustapha don har ji yake kaman yayi flying…….
Daganan kuma su Daddy suka barke da hirar Bussiness shidai Sulaiman gabadaya ya kosa ah tafi Daddy ne yalura da shirun da yayi yadaga wayarshi yakira Aliyu ba ajima ba segashi yashigo yatsuguna har kasa yagaida Dad din sannan Daddy yace ga bako nan kaje dashi side dinku I guess he’ll be more comfortable there…..
Dad ne yace laaa mukam dazamu wucema,dariya Daddy yayi sannan yace 15minutes yarage akira sallah zakace zaku tafi……
Kabari inmunyi dinner anyi isha seku tafi abunku…..
Aa Muhammadu ayi haka kuwa,dariya Daddy yayi ayi Almustapha sede in rena tuwon gidana zakayi daganan Dad yaja bakinshi yayi shiru don ya lura Daddyn dafa gaske yake sesun zauna din nan Aliyu yaja Sulaiman sukayi bangarensu kan kace me sun saba dasu Musa don Mubaraq bayanan,sunsan Sulaiman sede labarinshi suke ji kan yanada girman kai shi bayama zama ah kasar ya rena Nigeria gani yake yan nan ba sa’o’in yinshi bane,seyau dasuka zauna dashi na awanni kadan suka gane ba hakabane kwata kwata,aran Aliyu kuwa cewa yake mundau alhakin bawan Allahn,mutane are so judgemental basuda tabbacin abu sundinga fada kenan suna bata ma mutum suna without knowing their through colours……..shiyasa just believe in yourself don inkace zaka damuda abunda mutane kefada akanka you’ll never succeed….
Sulaiman da Daddy se bayan Isha sukabar gidan su Asma’u bayan sunci hadaddiyar tuwon Mommy da miyar egusi se santi sukeyi……….
Asma’u kuwa dadi ranar kaman tayi yaya don yayunta sundan fara sake mata ba kaman da ba…..

Tun dare Mai Martaba yasanar da Magajiya cewa tasa ayi abincin shi da yawa don yau tare zaiyi karin kumallo da Ya’yanshi Maza……..
Bakaramin kututun bakin ciki tajiba don cewa ma tayi ita bazata sa ayi dinba sede data tuna dakyar fa ta shawo kanshi kuma tace mishi zatayi abunda zaisa yayi alfahari da’ita, atleast this is a chance for her don haka tadaure zuciyar ta tashiga aiwatar da abunda yasakata din,abinci yakai kala shida akayi aka jeresu akan darduma ah makeken parlourn Mai Martaba, Sulaiman da Almustapha ah tare suka shigo bayan artabur da akayi da Almustapha din kafin ya yarda yazo samun guri sukayi suka zauna suna jiran isowan iyayen nasu maza……. Kusan atare suka shigo fuskarsu daukeda annuri kafin suka zauna,cikin ladabi da biyayya Sulaiman yagaida both Dad da Abba din yayinda Almustapha ma yagaidasu kanshi ah kasa yayinda fuskarshi tamke babu annuri ko kadan…………..
Sulaiman dakanshi yayi serving dinsu don da bayin suka farayi yace subarshi zeyi seda yazuba ma kowa sannan suka shiga cin abincin jefi jefi Mai Martaba yana satan kallon Almustapha din sede yalura tunda aka ajiye mishi abincin beciba harsuka gama shi daman dondai Dad yatakurashi yazo ne da babu abunda zai kawoshi,ganin kowannensu yagama ci yatashi yafice ah parlourn ai daman purpose din zamansu kenan tunda angama shikenan, Dad bin abincin Almustapha din yayi da kallo yanajin ranshi ba dadi sannan ya kalli kanin nashi da fuskarshi plane babu wata expression dazaisa yace ranshi yabaci dan dafa kafadarshi Dad yayi sannan yace”don’t worry everything will be alright”…..
Murmushi kawai Abba yayi batareda yace komai ba Sulaiman kanshi beji dadin abunda Almustapha yayiba yaudin haryaji ranshi yabaci sosai…….
Mai Martaba ne yacanza zance da anjima akwai zama dazamuyi tareda mutanen fada you’ve to be there Yaya magana ce akan wanda ze karbi karagar mulki bayan ni anfara gutsuri tsomi ah gari wanda haryasa waziri dakanshi yazo yayimin magana jiya,inaganin dakyar in al umma zasuyi na’am dahaka balle azo ga mutanen fada, let’s keep that at side Almustapha nalura bashima da interest akan abun he’s not helping matters yanda yakeyi dinnan shiyasa nakeson kaima kazauna ah zaman asan yanda za ayi don ni I’m just trying to follow your wish bawai don inason Almustapha yahau mulki baneba………
Murmushi Dad yayi sannan yace”Allah yakaimu anjima din zanzoni in Sha Allahu”….
Gyada kai Mai Martaba yayi sannan Dad yagyara zaman shi ni akwai magana Mai mahimmanci danakeson muyi ma tukunnan………………
Full attention Mai Martaba yabama Dad din yana jiran jin mai zai fada, ahankali yace maganar auren Almustapha ne yasamu mata inason akai tambaya sati mai zuwa in Allah ya yarda, cikeda mamaki Mai Martaba yadubeshi”Mata kuma Yaya?”…
Gyada masa kai Dad yayi yana murmushi sannan yace har munyi magana da mahaifinta ma,ikon Allah shine abunda Mai Martaba yafada yayinda aranshi kuwa gani yake Yayan nashi is rushing things ba agama maganar Yarima bama ankawo maganar aure kuma,shi ganima yakeyi baza ayarda abama Almustapha mata ba don zeyi wuya dubada hali irin nashi daya sha encountering…….
Dan numfasawa yayi sannan yace”Yaya baka tunanin ana rushing abunnan, yaushe ma yadawo hannun mu harmun fara tunanin aurensa”……
Abdulrahman bakaga Almustapha bane he’s thirty fa yanzu Ina maganar sauri anan,I want him to be happy like everyone……..
Gyada Kai kawai Mai Martaba yayi sannan yace Allah yakaimu wani satin yanzu dai muyi handling nagaban mu tukunnan.haka sukacigaba da tattaunawa duk kan batun Almustapha din Sulaiman kuwa tuni yatafi yabasu waje don komawa ganin aikin da akeyi ah bangaren su Almustapha din don Dad yayima Mai Martaba magana kan agyara bangaren Ummi nada sukoma can tunda suna tareda mahaifiyarsu dakyar Mai Martaba ya yarda don cewa yayi shikam wannan Matar bazata zauna mai agidaba,seda Dad yayi mishi nasiha dacewa inmutum ya nufeka da sharri kaikuma sekamishi alkhairi kanuna mishi duniyar bakomai bane sannan yakamata yayi la’akari da condition dinta indai yanason zaman Ya’yanshi cikin masarautar to dole su zauna da ita tunda babu maiyi Mata bauta inbasuba kuma suma bazasu taba yarda subar kusa da ita ba tofa da wannan ne akasamu Mai Martaba ya yarda akafara gyaran bangaren nasu wanda yanzu har ankusa gamawa…….

Story continues below

*****
Yau tun sassafe Hajja tatashi tayi wanka tashirya cikin daya daga cikin sabbin atamfanta,tana cikin ciro kudin ta dake kulle jikin daya zaninta Asiya tafarka daga bacci tana karema Hajjan kallo,seda tagama mutstsuke idanunta sannan tatashi tazauna tana mamakin Hajja din don tasanta intayi sallar asuba bata komawa bacci tadinga addu’o’i kenan har sai rana tafito kuma bata yarda adameta shiyasa yau take mamakin ganinta da safiyar Allah tana shirin fita,cikeda curiosity tace Hajja fita zakiyine?……
Uhmmm Asiya ai fitar dolece takama ni,iyi fita zanyi takarashe maganar tana kulle kudinta ajikin zanin dake jikinta yanzu sannan tasaka hijabi tace saina dawo Allah yasa shegiyar nan tatashi……..
Asiya binta tayi abaya tana inazakije wai Hajja?…..
Asibiti zamuje Hajja tabata ansa kai tsaye,cikeda damuwa tace wani ne ba lafiya kuma?……
Harara Hajja tayi mata sannan tace ke harma tambayana kike dan kin rainani to Asma’u zankai asibiti daganan tayi gaba tabar Asiya tsaye gurin tana mamakin meya samu Asma’u din don itadai jiya lafiya lau tabarta bin bayan Hajjan tayi harzuwa bangarensu Asma’u dako budewa basukai gayiba da alama basu tashi daga bacci ba kwankwasa kofar tashigayi kamar yaki tana wai Ina Maryam dinne, tsabar rashin kunya kinaji Ina kwankwasa kofa ma bazaki tashi kibude minba don wulakanci……….
Ummi dake kan sallaya tana karatun alqur’ani taji kaman ana kwankwasa kofa tashi tayi don zuwata bude nannefa taji Hajja nata mita da buga kofa kamar yaki, mamaki ne sosai yakamata donkuwa tasan Hajja bazuwa bangarenta takeyiba inko tazoma to ba alheri ke kawota ba jiki ah sanyaye tabude kofar tana cewa Hajja ki iso ciki mana…..
Mangareta Hajja tayi sannan takaraso cikin parlourn tana”aiko bakice inshigo ba zanshigo tunda gidan Dana ne inada raayin shiga duk inda naga dama….
Itadai Ummi batace komaiba sema bin Hajjan tayi zuwa tsakiyar parlourn tatsuguna tana mika gaisuwa amma ah banza sema cewa da Hajja tayi ina tsinanniyar yarkinnan take me fuska biyu?……
Cikeda damuwa Ummi tace wacce Hajja,barina kira miki su tafadi hakan don karta jama kanta wani abun amma dukda haka bata tsiraba don Hajja cewa tayi”au tambayata ma kike wacce cikinsu tsabar bakida da’a,koso kike kicemin bakisan yarki me fuska biyuba,dadin abun inada kafafuna da idanuna tana karasa fadin haka tayi cikin gidan direct dakinsu Asma’u tashiga samunta tayi kan gado tana ta sharara bacci hankali kwance don tana fashin sallah shiyasa ko farkawa sau daya batayiba…..
Jijjiga ta Hajja tashigayi tana “ke tashi bazaki bata min lokaciba”, Asiya dayanzu shigowarta tace Hajja an kibarta bacci takeyi inta tashi basai kuje inda zakuje dinba……..
Hajja bata kula Asiya ba sema wani makan data kai mata dede lokacin Asma’u tatashi don bakaramin zafin dukan tajiba ganin Hajja tayi ah kanta”don ubanki kitashi mutafi asibiti,natashi tun sassafe sabida ma kada musamu layi”……..
Cikin sauri Asma’u tatashi tana mamakin ganin Hajja din dama kuma yaushe hartadamu da harkokinta bare har azo da maganar asibiti kumadai ita ah iya saninta lafiyarta kalau don haka tace”lafiyata kalau Hajja mezamujeyi ah asibiti kuma da safen Allahn nan wanine ba lafiya?”…..
Asiya dake gefe tace”ah to nimadai tambayar danayi mata kenan”…….
Rai bace Hajja tace nidai baza ayi abun kunya daniba wayasan mekikaje kika kwaso daga yawon iskancin naki don haka kitashi muje ah dubaki tun wuri inma akwai abunda za ayi se ayi don banshirya ganin ana batama Dana sunaba……
Daga Asiya har Asma’u they’re very shocked by abunda sukaji Hajjan tafada Asma’u kuwa wasu hawayene suka shiga zubo mata babu shiri cikeda bacin rai Hajja tace banason kukan munafurci kina bata min lokaci ai duk ganinku nike daga ke har iyayen naki da yan uwan naki sewani murna suke da dawowarki kamar wadda taje aikin Hajji tayo aikin Allah tadawo…..
Maza kika tashi muka tafi, stubbornly Asma’u tace nidai babu abunda nayi kuma babu asibitin dazanjeni wallahi…….
Ummi dake bakin kofa tana goge kwallarta tace”Asma’u baki da hankaline haka akeyiwa babba magana,maza kitashi kujeku”…..
Cikin kuka Asma’u tace lafiyata kalau mezai kaini asibiti newai Ummi kode kema baki yarda danibane?……
Goge kwallah Ummi tayi sannan tace I trust you amma still kibita sabida ki goge zargin da Hajja keyi miki,cikeda damuwa Asma’u ta gyadama mahaifiyarta kai sannan tayi hanyar bandaki don wanke fuskarta nanfa Hajja tace babu wanke fuskar dazatayi tana bata mata lokaci babu yanda ta iya haka tazari hijabinta fuskar cubu cubu suka fice Asiya tana amma dai Hajja wannan ba daidai bane wallahi…..
Harara Hajja tayi mata tana kema sun asirceki ko,tosekiyi tayi wallahi don ko ubanki be isa ya hanani zuwa asibitin danayi niyaba yau……….
Cikeda bacin rai Asiya takoma bangarensu don sanar da Mommy dukda kuwa tana tunanin Mommyn bata fito daga bangaren Daddy ba haryanxu….
****
Tun safe suka dami Mom kan yauma seta koya musu wani samfarin abinci…………
Cemusu tayi seta gama harkokin gabanta tukunnan aikuwa seda tayi wanka taci breakfast sannan takirasu tanajin dadin yanda Asma’u da Amiran ke son koyon abubuwa kala kala bakaman Sumayya ba da sede tayi chat takwanta bacci batason duk wani abu dazai wahalar da’ita………..
Yanzu haka suna kitchen suna girki tana gwada musu yanda zasuyi yayinda bayi masu girkin ma suna tsaye suna gani don tsintan wani abu daga ciki,seda suka gama tas sannan suka zuba ah plate sukazo parlour sunaci samun Sumayya sukayi tana chat ah wayarta as usual…….
Amira ne tace sauko muci abinci, kai nikam anya zanci,don akoshe nike,tashi tayi tazauna sannan tadubi Mom tace”Mom Simran nata kirana tun jiya ankusa fara test and I’ve missed alot yakamata inkoma Jakarta hakanan”……
Dan shiru Mom tayi sannan tace”kibari in Dad dinku yazo seki fada mishi ko”…….
Gyada ma Mom din kai tayi dede lokacin Sulaiman yashigo yanajin duk conversation dinsu,karasowa yayi cikin parlourn yasamu guri gefensu Amira yazauna sannan yashiga cin abinci dasuke ci din seda suka cinye tas sannan yadubi Sumayya din,”komawa makarantar me zakiyi kuma?”…..
Cikeda takaicin shishigin shi tace”munkusa fara test shiyasa”…….
Kai tsaye yace babu inda zakije ke kadai,hararanshi tayi irin kana wasannan…
Tashi yayi yana kada kiyi tunanin wasa nikeyi I’m serious,za anema niki transfer anan ABU ma suna industrial design din ae…….
Take idanunta suka ciko da kwallah tace”nikam sena koma,aidai bakai ke iko daniba so you’ve no right to stop me from going back bari Dad din yadawo zanfadamishi ae”….
Dad ne dake bakin kofa yaji last statement dinta yace”what were you saying Sumayya,haka nakoya miki kinama nagaba dake magana?”…

Story continues below

Mom dake gefe tace Kai is sangartar da ita ai gashi tanayima nagaba da ita magana yanda taga dama without even thinking twice……..
Cikeda bacin rai Dad yashigo yana kallon Sulaiman”meya hada ku?”…
Jiki ah sanyaye Sulaiman yace it’s nothing just let her be Dad…..
Nace kafada min ko,Dad din yayi magana in a serious tune shiru yayi nan Mom tamaida mai yanda akayi,cikeda bacin rai Dad yace shine kikecewa baida right akanki?….
Shiba Yayanki bane,yau in babu ni babu Abban naku waye kukedashi dayafi Sulaiman da Almustapha din,banason raini Sumayya just because I let you do whatever you want bahakan yana nufin kiraina yayunki ba besides this’s a different environment you’ve to learn some manners kina jina…
Gyada ma Dad din kai tayi tana hawaye don this’s the first time da Dad yayi mata tsawa kuma duk adalilin Sulaiman…..
Share kwallarta tayi sannan tace”Simran tayita kirana kan I’m missing a lot shine fa nake fada ma Mom inason komawa cikin satin nan”…..
Batareda Dad yakulataba yadubi Sulaiman din yace “miyasa kakeson tadawo nan din,kuma samun transfer din zeyi wuya ai from another country fa?”….
Cikeda damuwa Sulaiman yace,zanbincika Dad if it’s possible i want her to study here cikin yan uwanta can intaje babu ku that means she’ll be alone waye zena controlling dinta?……….
Nidin yarinya ce Yaya Sulaiman, please stop acting as if you’re my husband I’m 20 for goodness sake I can take care of my self tayi maganar tana kuka sannan tatashi tafita tabar parlourn bin bayanta yayi shima jiki ah sanyaye yarasa dalilin dayasa yake wannan over protectiveness din akanta…….
Mom ne tace ma Dad let them be he’ll calm her down and besides ni inaganin da gaskiyar Sumayya mutane nawa iyayensu ke turasu karatu wajen kuma babu abunda yake samunsu bare Sumayya datasan kan gari she can stay wherever she wants too ga gidanmu akwai masu aiki intayi niya zata iya zama can gidan kakanninta ko sister na cewar Mom din,gyada kai Dad din yayi sannan yace zanyi magana da Sulaiman din baisan yan uwanki nacan ba that’s why,sede karki fada mata i want to teach her a lesson she should learn some manners……
Gyada kai Mom tayi yayinda Dad yayi dakin Almustapha bayan yatambayi su Amira ko yana nan nan suka cemasa bejima da shigowa ba…….

Tunda tashiga dakin ta banko tarufe tasa key, knocking yashigayi yana kiran sunanta amma ko kulashi batayi ba,dan dafe kanshi yayi yana regretting actions dinshi gashi yabata mata rai yanzu shima seyaji gabadaya ranshi ah jagule take,yajima tsaye agurin ko Allah zaisa tabude amma taki don haka yajuya yatafi bangarenshi,su Gimbiya Zaliha an hakimce akan kujera yayinda bayinta wasu namata fifita wata kuma nazaune gabanta tana gyara mata fruits tana mika mata tanasha……
Sekuma larai dake can gefe tana karanta mata wani littafin hausa wanda daga masarautar su tazo da’ita don tafi kowa sanin abubuwan datafiso kuma sunfi shakuwa,sewani lumshe idanu takeyi hankalinta kwance…..
Shigowa yayi sashin nasu ranshi bace don ko ansa gaisuwar da dogaraye keyi mishi baiyiba yawuce dakinshi,Laurene ta tsaida karatun littafin tace Gimbiya ta Allah yayima Yarima isowa yanzu yawuce yashiga daki, ahankali tabude idanunta tafi minti goma zaune bayan Laure tafada mata sakon sannan tatashi cikin takun kasaita tayi dakinshi,samunshi tayi zaune bakin gado yadafe kanshi alamun yashiga duniyar tunani karasawa tayi bakin gadon tazauna gefenshi tareda kwantar da kanta jikinshi cikeda damuwa yace”Zaliha I’m not in the mood please kibarni tukunnan”…..
Bataji dadin kalamansa ba amma se bata tashin ba takamo hannunshi tana dan mammatsawa cikeda kisisina tace”meke damun ka Yarima,inbaka fadamin damuwarkana honey wazaka fadawa?”……
Dagowa yayi yana kallon ta da idanunshi dasuka canza kala sannan yace”Sulaiman please,kidainacemin Yarima”….
Nanma kauda zancen tayi don bayau yafara cemata bayason sunan n
ba ita kuma takasa daina kiranshi dashi……
Batabar mammatsa hannun nashiba hakanan tacigaba da tambayarshi damuwarsa,ganin tanason rikitashi yace”it’s Sumayya Zaliha,bansan miyasa takejin haushina ba sabida kawai nafada mata gaskiya”……
Jitayi gabanta yafadi don kuwa yauna uku kenan tun bayan aurensu yana mataa maganar Sumayya din and ga hotunan ta dayawa ah phone dinshi,daurewa tayi tashigayi mashi salo tana kasan kannen nan se ahankali dole se muna hakuri dasu tafadi hakane don taji ko blood sister dinshi ne amma seya gyada mata kai kawai yayinda tarungume shi nanfa aka shiga wata duniyar kuma don Sulaiman mantawa yayi dawata Sumayya ma yasamu abunda yakeso………

Story continues below

****
Har dakin Almustapha din Dad yaje samunshi yayi kwance yazura ma bango idanu zama yayi bakin gado gefenshi sannan yace”Son tashi muyi magana”……
Ahankali Almustapha yatashi yazauna babu musu sannan yagaida Dad din akaro na biyu…..
Juyowa Dad yayi batareda ya ansaba yace”yau kabatamin rai son bazan boye maka ba, I know why you’re doing all this sede inason kasani cewa abunda kakeyi din will not help matters at all”…
Kai akasa Almustapha yace”I’m sorry”,dukda kuwa baisan laifin dayayiba acewarshi……
Dad ne yace sorry bashine abunyiba if you’re really sorry you’ve to change your ways Son,nasan you’re hurt you’re still angry with your Dad sabida abubuwan dasuka faru sede inason intuna maka cewa shima fa ba laifinshi baneba tunda nasan kasani sede inmantawa kayi waye Magajiya and what she’s capable of….
Almustapha dayanzu ranshi tafarfasa yakeyi jin Dad na sidding Mai Martaba atake idanunshi sukayi jazir yace”he don’t know, Dad kanason kacemin Mai Martaba baisan abubuwan dayayi ba,he threw my Mother out of this place,he turn his back on us bayan yasan Mahaifiyata only loves him for Allahs sake,she cares for him and stand for him but what did he do?…..
Alokacin Almustapha couldn’t hold his tears sabida baitaba fadama kowa how he felt ba, baitaba fadama kowa haushin Mai Martaba dayakejiba,baidamu da hawayen ba yadaga hannunshi yana alama da yatsarshi “just one evidence ruin everything,just one evidence yasa yamanta who my Mother is,just one evidence yasashi manta the trust they have for each other,we went through alot Dad you won’t understand,my sisters suffered alot basusan dadin uba ba ah rayuwarsu,ajiyar zuciya yayi sannan yace and even now my Mother is still suffering dago manyan idanunshi yayi yadaurasu kan Dad yace if you were in my shoes will you forget all these things so easily?…….
Dad tsayawa yayi yana kallon Almustapha din daga ganin idanunshi yasan yaron nacikin rikici sosai and he’s very angry ahankali Dad din yayi engulfing nashi in a very warm hug still Almustapha baidaina kukan ba wannan karan harda shesheka, this’s the 3rd time dayayi kuka tun bayan faruwar abun,abun nabashi haushi wai miyasa za ace ba laifin mahaifin shi…..
Seda Dad yatabbatar yadan rage kukan sannan yashiga goge mishi kwallarshi yana are you feeling much better now?..
Gyada masa kai Almustapha yayi don kuwa bayan yanuna bacin ranshi yaji sauki aranshi sosai sannan daya rungumi Dad din seya sakejin wani saukin seyakejin kaman his real father yarunguma don baya kallon Mai Martaba amatsayin Uba yanzu….
Dad ne yace nasan kana ganin laifin Abbanku sede inason kasan he can’t remember anything now,besan cewa ku Ya’yanshi bane seda akasanar dashi,mesuna sekace bakasan waye Magajiya ba,I think you should know her more than anyone and you should know that she’s capable of doing anything,mahaifinku na tsakiya Almustapha he need your help to recover his memory and remember everything yana bukatarmu bawai kawai kajuya mishi bayaba, he’s trying to show you some love try and reciprocate for it, he’s your Father no matter the circumstances yakamata kana mutun tashi,inason muyi Joining hands mukawo karshen abunnan I hope zaka taimaka min,I hope zaka daina taurin kankan nan and be free with everyone, it’s time to seek revenge and it’s time mufitar da Magajiya cikin rayuwarmu,kobakaso Umminka tasamu yancin kanta Almustapha,fadamin kobakason tadawo cikin koshin lafiyarta,cikeda damuwa Almustapha yadubi Dad batareda yace komaiba dukda kuwa azuciyarshi bashida wani buri daya wuce wannan ayanzu,dan numfasawa Dad yayi sannan yace I know you want that sede hakan bazai faruba harsai mun hada hannu munyi aiki tare, it’s going to be a difficult task but to reunite our family and be one dole semunyi hakuri mun manta baya mun fuskanci future…..
Gyada kai Almustapha yayi don jiyakeyi babu abunda bazai iyaba don ganin mahaifiyarsa tayi recovering don ayanzu yacire mahaifinshi aranshi tunda yariga yayi sabo da rashin shi don haka yace I’ll do everything so far as beyi going against my religion ba..
Murmushi Dad yayi sannan yace, I’m fighting for you to be the crown prince sabida wannan shine burin kanin ka and you deserve it kuma that’s the only way dazaka goge duk wani kazafi da Magajiya tayi maka hope zaka bani hadin Kai?..
Gyada Kai yayi ahankali yayinda wasu abubuwa azamanin baya suka fara dawo mishi, Dad ne yakuma tabashi, you’ve to respect your Father kaji kana zuwa kana gaidashi every morning kaman yanda Sulaiman keyi,inya kiraka kaje please kada kana shan kamshi….
Gyada kai kawai yayi,godiya Dad yayi masa sannan yatashi yafita yabarshi don yalura Almustapha din needs to be alone to think over it…
******
Mai Martaba ne yasaka aka kira mishi Magajiya,cikeda ladabi tazo tagaidashi sede talura fuskarshi babu annuri ko kadan ahankali yadubeta sannan yace ina kudin dana baki ajiya?…….
Barina dauko ranka shi dade, gyada mata kai yayi sannan tafice cikin sauri kiran Talatu tayi data isa bangarenta sannan tace tadauko mata kudin datasa ta ajiye ah safe dinta,jikina bari Talatu tadauki keys din safe din taje tabude amma wayam babu kudi jitayi gabanta yafadi yayinda cikin sauri tadawo gurin Magajiyan tana zufa……
Hararanta Magajiya tayi ganin tana abu kamar munafuka?…
Meye ya faru kuma….
Talatu na stammering tace”Uwargijiyata babu kudin aciki”…..
Tashi Magajiya tayi tana zare idanu”don ubanki me kikace?”……
Kaman Talatu zatayi kuka tace wallahi Uwargijiyata agurin na ajiye bansan waya bude yadauka ba……
Mutuwar tsaye Magajiya tayi don batasan dawani baki zata dubi Mai Martaba ba tace masa miliyan goma yabata kuma kudin mutane for that matter…….



Dakyar ta iya takawa zuwa gaban safe din gabadaya illahirin jikinta na karkarwa karema safe din kallo Magajiya tayi nanfa taganshi empty,wani duba tayima Talatu sannan tace”so kike kicemin kudin nan yabata komi?”….
Talatu na hawaye tace wallahi Uwargijiyata kudin nan na ajiyesu inda suke bansan waye yadaukaba…..
Kan uban nan cewar Magajiya din kafin tasamu bakin gado tazauna don talura kafartama bazata iya daukartaba sa hannunta tayi ah both side of the bed tana tunanin abunyi inka ganta kace meshirin shiga labour room ne…..
Waye zeyi mata sata tasan dai cikin masarautar nan babu mai guts din da zai shigo hardakinta yayi mata sata batareda bayinta sun fada mataba,damuwanta daya harda nata kudin aka diba dake cikin safe din separately wanda tana iyacewa batasan adadin suba sede tasan basukai na Mai Martaba yawaba,kallon Talatu takumayi cikeda tuhuma don ita gani ma take Talatun ce tadauka tunda dai babu wanda yakeda access da key din se Talatu……..
Talatu datayi tsumu tsumu da Ido tashiga bada hakuri tana rantsuwar baita tayiba, Magajiya ne tace cikin rudani”nifa babu ruwana dama koma waye yayi satan kudin nan damuwana daya shine afito min da kudi sannan babu wanda yake da access da keys dina seke Talatu,miyasa zaki cuceni,haka amana tace fisabilillahi Magajiya tayi maganar murya karye kafin tazare idanunta rai bace”wallahi tallahi kije kifito da kudinnan nanda minti goma inbahaka ba se insa ah nakada miki dukan tsiya”……
Kuka Talatu keyi kaman wanda ranta zai fita,don itadai tasan batayi komaiba koza akasheta tajima tana bautawa Magajiya mezaisa tacuceta bayan tunda batayiba seyanzu rantsuwa tadingayi wanda ya hassala Magajiya din tace itafa babu ruwanta kawai tafita tanemo mata kudi ganin Magajiyan nashirin kai mata duka tafice tana kuka……
Zama Magajiya takoma tayi tareda dafe kanta abun duniya ya ishi rayuwarta,batasan metama Talatu ba dazata saka mata da haka wata zuciyar kuma tace dakika barta ta fita inta gudufa cikin hanzari tatashi tabi bayan Talatu tana kwala mata kira,ah gaban sashinta tasamu Talatun tana sheshekar kuka cikeda takaici tace au don ubanki xama ma kikayi zaki tashi kinemo kudinnan ne kosenayi ball dake, dogareyen dake tsatsaye suna jin meya ke faruwa sede babu halin kallo don kowa na tsoron kada ahada fashi,ball Magajiya tayi da Talatu ganin tayi shiru bata kulataba,cikin kuka Talatu tace wallahi Uwargijiyata bandauka ba,bansan waye yadauki kudinnan ba wani ball din Magajiya tasakeyi da ita sannan tace don ubanki inni baki fadamin ba inmunje gaban sarkin zakiyi masa bayani inani kika cuta Magajiya tayi maganar tana nuna kanta kafin ta kalli dogarayen dake kusa da’ita tace kukaita karamar fada yanzu yanzunnan yau saikinyi dana sanin messing up with me…..
Jiki na bari suka dibi Talatu sukayi gaba da ita tana kuka, Magajiya nabinsu ah baya ranta bace,wani kututun bakin ciki takeji yau inbata hukunta Talatu ba hankalinta bazai kwantaba don haka tace aje ayi ringing bell kowa yataru ah fadar masarautar…….
Dakin Mai Martaba tawuce yana zaune yanda tabarshi se huci takeyi “Mai Martaba, kafito kayima yarinyarnan hukunci harni zatayima sata,shekara da shekaru nariketa amana amma ni zata cuta, jijjiga kai yayi yana shirin magana cikin sauri takama hannunshi tana don Allah kafito kagani babu musu yabi bayanta harzuwa karamar fada inda bayi sunfara taruwa yayinda wasu daga cikin ahalin masarautar ma sun fito…….
Kallonta Mai Martaba yayi in desbelief yana and what’s all this?……
Bata kulashiba sema komawa datayi kusa da dogarayen dasuka kawo Talatu harta fara fita hayyacinta tsabar janta da sukayitayi ah kasa…..
Jan dankwalin Talatu tayi sannan tace”yanzun zaki fadi inda kudin yakene kosai kinji na jaki?”…..
Nibanyi komaiba Uwargijiyata wallahi banina daukaba, Magajiya bata bari takarasaba ta make bakinta tana cema dogarayen su shiga cin ubanta da dorina zatayi confessing kota ki kota so……..
Dukanta dogarayen suka shigayi Talatu na kuka tana rantsuwar ita batayi komaiba,Mai Martaba dake gefe yana mamakin Magajiya ranshi bace yace stop all this nonsense,I said stop!…..
Kowa shiru yayi ah gurin yayinda Mai Martaba yakaraso gaban Magajiya yana kallon ta cikeda mamakin how she can stoop so low, yana kuma mamakin yanda take hukunta wani akan laifin da ita tayi,her very own trusted slave for that matter,beyi niyan yimata magana publicly ba amma ita tajama kanta,cikeda bacin rai yace”miyasa kike hukunta Talatu akan laifin ki,tell me why are you doing this,ko kina tunanin bansani bane Magajiya…..
Are you trying to blackmail me,kifada min yayi maganar cikin tsawa har jijiyan wuyarshi na tashi Galadima dake can gefe yaga baidaceba yanda Mai Martaba yakeyi din cikin jama’a ba yatako cikin sauri yanama Mai Martaba rada ah kunne kan yabari su shiga ciki tukunnan…..
Rai bace Mai Martaba yace”I’m sorry Galadima ita tafara,ita taso inyi gaban mutane and i don’t want anyone to interfare in this matter………
Juyawa yayi kan Magajiya datayi tsumu tsumu gabadaya ruwan jikinta ya tsaya,she don’t know what is going on too,bamagana nakeyi mikiba,why are you doing this kindauka bansan mekikayi da kudin bane kike kokarin dorama wani laifi?…
I never expect you to do this Magajiya nayarda dake shiyasa nadauki kudin mutane da aka kebe sabida samo musu hanyar samun ruwa cikin kauyikan dasuke fama da scarcity na ruwa,kinba ni mamaki gaskiya…

Story continues below

Magajiya da kanta kewani irin sarawa tace menayi Mai Martaba,menayi da kudin nifa babu abunda nayi dashi kayarda dani shiyasa nakeson tayi confessing sabida ita kadai tasan inda nike ajiya takarashe maganar yayinda idanunta suka canza kala lokaci guda,she cannot take this anymore wannan embarrassment din yayi yawa juyawa tayi zata tafi cikin bacin rai Mai Martaba yace inamiki magana zaki juyamin baya,for how long will you lie?………..
Nifa bandauki kudiba,stop all this please?……
Batareda yace mata komaiba yakarbi envelope daga hannun Galadima yayi mata wurgi dashi gabanta nanfa papers suka zubo kasa,dauka tayi ahankali yayinda zuciyarta ke bugu takardun ownership na napeps ne guda biyar kuma sunan tane akai kan ita tasaya harma tabada hayansu…..
Yanzuma ki musa min you’ve nothing to do with this Magajiya Mai Martaba yayi maganar ranshi ah matukar bace,jitayi idanunta sun ciko da kwallah wallahi sharri akamin bansan waye yayiba,tunkan takarasa Mai Martaba yadaga mata hannu sannan yace Galadima yasa ashigo da masu napep din guda biyar,ba ajimaba segasu Mai Martaba ne yace waye yabaku hayan machine?……
Atare suka ce wancan hajiyar ce,gyada kai Mai Martaba yayi sannan yace tun yaushe tabaku kuma kuna kawo mata kudin aikin ne?…..
Daya daga cikinsu ne with full confidence yace”eh Mai Martaba,yanzu wata biyu kenan dayin hakan kuma kowani sati mukan kawo mata cinikin damukayi…….
Juyawa Mai Martaba yayi yadubi Magajiya”I gave you this money two months back right?”…..
Wato ke ashe tun lokacin kike biyan bukatanki dashi,you couldn’t even think twice cewa ba kudina bane hakkin mutane ne?….
Why will you do such a thing?….
Rai bace Magajiya tataho kamar kura tayi kan masu napep din tana don ubanku nina baku hayar napep waye yasaku kumin sharri,kuyi magana mana tayi maganar tana zazzare idanu,dariya suka shigayi mata sukam ma, Mai Martaba ne cikeda takaici yacema dogarayen su tafi da Magajiya she should be under house arrest because he cannot stand this anymore sabida it’s such a disgracement for him amatsayinta na matarshi……
Kallon Mai Martaba tayi in desbelief tana”miyasa za arufenin banyi laifin komaiba,wallahi babu wanda ya’isa juyawa Mai Martaba yayi yabar gurin bayan yacema Sarkin gidan yari sutafi da’ita he has no any other option than to do this,dole seya hukuntata akan abunda tayi shibama kashe kudin bane yafi bata mishi rai aa yanda takeson yima wata sharri akan abun, azuciyarshi cewa yakeyi dayanzu bawan Allahn nan be kawo mishi takardun ba bazai saniba sede ya hukunta Talatu, yadauki alhakin ta……
Magajiya ihu takeyi ganin dogarayen sunyo kanta tana kiran Mai Martaba kan yadawo,ko kallon inda take beyiba sema shigewa parlourn sa dayayi rai ah jagule Sarkin gidan yari ne yace Uwargijiyata ba mwason yimiki na karfi don Allah kibi abunda Mai Martaba yace tundama ah gida za a ajiyeki kawai dai bazakina fita bane,hararanshi tayi tana huci sannan tayi gaba dogarayen sukabi bayanta,bayi se kallonta suke wannan suce wannan wancan suke wancan duk daga masu Allah yakara se masu shine daidai da’ita atleast zasu samu freedom for some days….
Talatu dai kuka takeyi tarasa nayi don ah iya saninta Magajiya bata hada wani plan ba to miyasa hakan yafaru,who could be behind this…….

*****
Tunda suka bar gidan suka wuce asibiti itadai Asma’u se sharar kwalla takeyi,Hajja kuwa cewa tayi sekiyi ai babu abunda za afasa wurin gwaji suka je Hajja tace ayi mata gwaji ko tana daukeda juna biyu………….
Nanko akayi mata,cewa akayi se anjima result ze fito Hajja tadage sesun jira sannan sutafi don fa yau bazasu koma gidaba setaji meke tattareda Asma’u….
Likitan cikeda mamaki yace susamu guri suzauna sujira,itadai Asma’u shiru tayi tana mamakin walakanci da kiyayya irinna Hajja……
Se wurin shabiyu sannan aka kirasu suka karba,likitan yace bata dauke da ciki bata rai Hajja tayi sannan tace”ka tabbata likita”….
Gyada mata kai yayi,hararar Asma’u tayi sannan tace nifa banyarda dakeba don nasan inbaki dauko cikiba to kilan kya daukomana cutar kanjamau don haka shidinma se anmiki gwaji……..
Sabon kuka Asma’u tafara tana Hajja nifa banida komai don Allah kidainamin sharri da zargi hakanan,duban likitan Hajja tayi batareda takula Asma’u dinba”ayi mata na kanjamau”,kai tsaye likitan yace sede sudawo gobe dasafe don sun rufe yin test din segobe kuma hamdala Asma’u tayi aranta don tasan Hajja indai se anyi din kumafa sesun jira result wata zuciyar ne tace aikuma goben ma tana iya takura miki kudawo,haka suka koma gida Hajja nata tsan gwamarta ah napep……….
Mommy da Asiya tafada mata bakaramin baci ranta tayiba sede bata fadama Daddy ba don tasan at the end zeyiwa Hajja magana ne and they’ll end up having problems,abudaya tasani Asma’u is clean and pure so,miyasa zasu damu kansu koma kwajin meye suje ayi ita Hajjan ne da wahala ai………

Story continues below

***
Hindatu da Jamila dasuke bayin Ummi tun ah zamanin da tanada lafiya lokacin da take tareda Mai Martaba yanzuma su Sulaiman yasaka amatsayin bayin Ummin don sucigaba da kula da ita tunda sunfi kowa sanin abubuwan da takeso and they’re true to her suna sonta tsakani da Allah haryanzu…..
Hindatu nazaune tanayima Ummi Massage akafa don su amira sunje yin lunch yayinda Jamila ke nade kayan Ummin data debo daga wanki tanasawa ah drawer, Sulaiman ne yashigo dakin da sallama hannunshi rikeda farar jarka cikeda ruwa,cikin sauri Jamila data fara ganinshi takarasa takarbi jarkan tana gaida shi, ansawa yayi fuskarshi daukeda murmushi sannan yace” sannunku,yajikin Ummi din?”…..
Dasauki alhamdulillah cewar Hindatu din,ajiye jarkan yayi sannan yazauna gefenta sukuma suka tashi suka fita ba ajimaba se ga Amira da Afiya sun shigo don kuwa suma tundazu suke dakin fita sukayi don yin lunch……
Gaidashi sukayi da tambayar ina Amarya, murmushi yayi sannan yace “she’s fine,bata shigo muku bane yau?”….
Bata shigoba cewar Amira,may be seda yanma don inbatazo da safeba takanzo da yanma,alama yamusu da hannu kan suzo karasowa sukayi sukazauna sannan yadago ruwan yace wannan ruwan rubutune aciki wanda wani Malami yayi yabani yace anabama Ummi yazamanto shine ruwan shanta,take note please nasan kuke bata abinci yawanci kada kumanta kuna bata please inya kare akwai wani aguna I’ll give it to you……..munyi magana dashidin I told him abubuwan dake damunta yacemin urgent tafiya yasame shi dayazo yadubata dakanshi amma daya dawo he’ll surely come but before then shine yabani…..
Murmushi Afiya tayi sannan tace thank you Yaya Sulaiman…
Shafa kanta yayi sannan yace”banason iyayi,dariya tayi tana daukar cup don zubama Ummi ruwan aciki tasha, yayinda Amira tace kaje gun mutumiyarka kuwa Yaya Sulaiman?…..
wace mutumiyata yayi maganar yanason sanin watake nufi, Sumayya mana Yaya tayi fushi dakowa taki cin abinci tun safe……
Zare idanu yayi sannan yace are you really serious?…..
Gyada masa kai sukayi ah tare tashi yayi ahankali yafice ah dakin shifa yamanta meya faru jiya ita miyasa bazata mantaba, kitchen yaje yacema bayin dake aiki sukawo mishi abinci dakin Sumayya…….

Ahankali yatura kofar dakin nata,tana zaune kan gadonta tajingina jikin pillow tana danne dannen waya tundaga bakin kofa yake karemata kallo tana sanye da sleeping wears riga da wando buje yayinda rigan kamar vest take kanta kuwa babu dankwali se gashinta data kama ah tsakiyar kai,wani irin feelings yadinga ji ganin yanda idanunta suke ah kumbure alamun tasha kuka seyaji ba dadi aranshi, he’s d one that caused her pain and yanacan yana harkokinshi itakuma tananan tana wahala, karasawa yayi cikin dakin sannan yace”I’m sorry”,batareda yazauna ba kodagowa batayiba dukda kuwa taji shigowanshi kuma daman tasan shine don daga kamshin turarenshi tagane shi………
Baiwar data kawo abincin ne tayi sallama,ansawa yayi sannan yakarbi tray din abincin yakarasa bakin gadon yazauna tareda ajiye tray din kan wani dan karamin stool……..
Kizo kici abinci Sumy……
This’s the first time daya kirata da suna haka,setaji tanason sunan lokaci guda amma seta basar taki kulashi tacigaba da pressing phone dinta……….
Sa hannu yayi cikin sanyi yakarbi wayartata cikeda masifa tabiyoshi tana shirin karban wayar,kamota yayi tareda janta zuwa jikinshi wani irin electric shock sukaji dukansu yayinda zuciyarsu tashiga beating so fast,wani irin feeling ne yaziyarci Sulaiman feeling din dabai taba jin irinsaba dukda kuwa irin huldan dayaitayi da yan mata kala kala bangaren Sumayya ma haka takeji gakuma kamshin turarenshi mai sanyaya rai datakeji,dagowa yayi yakalleta kafin ahankali yakai bakinshi kusa da kunnenta cikin muryar dabaisan yanada irinta ba yace”I said I’m sorry ko,kidaina hukunta kanki da yunwa I’ll be worried too”…….
Dan bugun kirjinshi tayi ahankali sekuma tafashe da kuka, subhanallahi nashigesu ni Sulaimanu shine abunda Sulaiman din yafada yana shirin lallashinta gashi kukanta kara rikitashi yakeyi wata zuciyar ne tace Sulaiman what are you doing?…
Cikin sauri yadan ja baya yayi make sure akwai dan distance ah tsakaninsu yana istighfar ah zuciyarshi sabida bemanta alkawarin daya daukar ma kanshiba, he’ll make sure zeyi going away from everything that will lead him to yin zina kuma tunranar dayayi nadamar abubuwan dayayi yadinga rokon Allah gafara don samun dacewa,yasan Sumayya is his sister dukda ba blood Sister ba sede besan miyasa yakejin irin
wayannan abubuwan tattareda itaba,dubanta yayi uncomfortably “please kici abinci, I’m very very sorry”,yakarashe maganar tareda dauko tray din abincin ya ajiyemata ah gabanta………
Gyada mishi kai tayi, murmushi yamata sannan yace I’ll comeback in 5 minutes inason Inga plate dinnan empty please!……
Gyada mishi kai kawai takuma yi don batajin tana da bakin yimishi magana after abunda yafaru,fita yayi ah dakin dasauri tatashi tarufe kofarta don ma kada yadawo don gani take inyadawo din her heart will explode hakanan bataki cin abinciba daman wata muguwar yunwa takeji stubborness ne yahanata cin abincin………

Story continues below

*****
Dad yana bangarensu abunda yafaru da Magajiya yafaru besaniba seda yashiga gun Abba din yake labarta mishi aranshi jiyayi inama yanagun dayayi enjoying kallon show din,she think she’s smart sede abunda bata saniba ba Allah yafita aiba kullum bane kake succeeding yaudai taga downfall dinta and he wished that daga yau tacigaba da encountering irin wayannan abubuwan sabida that’s what she deserve on the other hand kuma inya tuna Sulaiman seyaji wani iri,no matter what she’s his Mother inyaji irin wannan labarin bazai ji dadiba and he’ll feel somehow sede yazasuyi,babu…..
Duban Abban yayi sannan yace what are your plans akanta?…
Dafe kai Mai Martaba yayi sannan yace”seriously I don’t know Yaya,what she did was unimaginable,bantaba tunanin Magajiya can do something like that ba besides ba itane ah gaba na ba yanzu I’m looking forward for our meeting this evening I’ll decide abunda zanyi mata later,tashi yayi yana saka takalminshi”for now she should stay under house arrest”……
Gyada kai Dad yayi sannan yace hakane,shall we?…
Murmushin dayafi kuka ciwo Mai Martaba yayi sannan yace yes,abubuwa sunyi masa yawa ga Magajiya ta bata mai rai,ga maganar crown prince dinnan yalura su waziri bazasu bada goyon baya ba and on the other hand Almustapha is given him a very tough time ……
Haka suka taka shida Yayan nashi zuwa fadan dogaraye nabinsu wanda inkagansu sesun baka sha’awa wani ma zai iya cewa yan biyu ne sede inkayi musu kallo mekyau zaka gane cewa Dad yagirmi Mai Martaba din dukda tsufarshi batawani nuna kaman na Mai Martaba dinba sede akwai fuskar manya dayake dashi…..
Kirari aka shigayi har sarki yasamu guri yazauna yayinda aka shiga gaidashi kafin kowa yasamu guri yazauna,bude taron akayi da addu’a yayinda Mai Martaba yafara magana cikin nutsuwa…….
Nasan dukkanninku anan kunsan purpose din haduwar mu wanda baiwuce kan jita jitan da kukeji ah gariba na maganar Almustapha ‘Da na…..
Gyada kai sukayi dukansu cikeda gamsuwa kafin ahankali yace,wasun ku baswanan sanda nayi magana acikin Masarautar nan sabida kunje halartar bikin Sulaiman anma yanzu Allah yayi kundawo lafiya kuma nasan by now kunsan da dawowar Yayana Almustapha tareda su yara kuma wanda daman sunjima anan cikin masarautar,munyi magana ne akan dawowarsu kawai bamuyi magana akan wazai karbi sarauta ba in public sede mutane sunje sunata yada jita jita kukuma sanin kanku ne bana yanke hukunci batareda na tuntube kuba, inban nemi shawarar kuba miye anfaninku?…
We’re all here together to make our society Happy sannan mu hada Kai gurin ganin komai yatafi daidai,I might be the king kuma inada right din yanke hukunci inna gadama sede bana abu batareda naduba yanda mutanena zasuyi benefitting ba,bana kuma yanke hukuncin dazaisa mutanena suwahala,tabbas Yaya yanuna yanason Almustapha yakarbi karagar mulki bayanni sabida right dinshi ne yagirmi Sulaiman sede nayi kokarin fahimtar da Yaya cewa Almustapha is not the right person sabida nidaku munsan waye Almustapha Kuma munga duk abubuwan dasuka faru,but still he insist and I trust him dukda bansan dalilinshi nayin hakanba sede ina bayanshi sabida nasan bazai taba zaban Almustapha bayan yasan bazaiyi abun kirkiba…
Waziri dake kusada sarkine yace”Allah yaja da tsawon kwana amma ni inaganin ana duba dacewane bakuma shekaruba, Almustapha baidace da karagar mulkin nan ba”…..
Sauran yan fadan ma cewa sukayi tabbas wannan haka take,yayinda Galadima yace “ni inaganin abar Sulaiman din tunda al umma nason shi kuma anriga ansa mishi ah ranshi, yau in ance za’a daukemai wannan right din tabbas zai kawo rikici tsakanin su biyu din,mukuma bazamu so hakaba…….
Sardauna ne yace”ae bawannan akedubawa ba tukunnan Galadima dukda kuwa zancen ka gaskiya ne amma abunda yakamata aduba shine cancanta dakuma dacewa kaman yanda waziri yafada, Almustapha bedace da sarautarnan ba kwata kwata mutane bazasuyi na’am dawannan zancen ba”……
Dad dai da Abba shiru sukayi sunajin kowa nakawo suggestion dinshi seda suka gama tas sannan Dad yayi gyaran murya yace”nasan duk abubuwan da kuke fada,sannan nayarda da duk zancen ku sede inason kusani Almustapha ba abunda kuke tunani bane,kuma ina tabbatar muku cewa babu wanda ya cancanta yakarbi mulkin nan kaman shi”……..
Waziri ne yace”Yarima Almustapha(don shine sunan dasuke Kiran Dad haryabar gida adacan baya),ni inaganin bekamata kana tsauwala zancen nanba tunda kajima bakanan,bakasan waye Almustapha ah garinnan ba shiyasa………
Murmushi Dad yayi sannan yace,nafika sanin abubuwan dake wakana ah masarautar nan wanda kai bakasaniba,dazakubani dama inason ku gwada Almustapha kafin kuradashi as the crown prince,inyaci jarabawarku to inko beci ba shikenan nina janye maganata…..
Galadima ne yace”wace irin jarabawa zamuyi mishi,mu mutanen mu mukeji baswasonshi bazakuma suyi na’am dashiba koda kuwa mudin munyi hakan”……
Nidai nace kubashi dama nikuma namuku alkawari su mutanen dakansu zasuzo su nuna shidin sukeso bawaniba maganar sulaiman kuma shiya nuna bayason sarautar…. 
Galadima yana shirin yin magana waziri yayi saurin cewa”shikenan babu komai zamu bashi dama yanuna nasa bajintar”….
Murmushi Dad yayi sannan yace nagode da wannan damar,bakomai cewar wazirin kafin yace sunason ganin Almustapha din zasuyi magana dashi zuwa gobe….
Godiya Dad yayi sannan yace in Sha Allah zaizo….. daganan aka rufe taron sannan aka koma kan wasu harkokin kuma………

Story continues below

******
Nigaskiya Yaya Yarima nagaji da rashin wayarkan nan Sulaiman yakarashe maganar hannunshi rikeda kwalin waya daya cirota daga drawer din Almustapha yanzunnan…….
Zama yayi gefen Almustapha din sannan yace,yau zamu hada wayarnan kuma nidai inbaso ake inyi fushiba adinga riketa….
Hararanshi Almustapha yayi,yayinda Sulaiman yamake kafada,nifa se an hada wayarnan atleast zatana debema kewama amma kullum sede kayita zama ah daki only god knows what you’re thinking kuma fa irin haka nada hadari ah rayuwarka besides yakamata kafara tara yanmata yanzu,you don’t know how it feels ace kowace mace daye maka takeyi Sulaiman din yayi maganan dreamingly…….
Jijjiga kai Almustapha yayi sannan yace”you’re unbelievable Sulaiman,Kuma kamaida wayarnan because I’m not going to use it’s”…

Turo baki Sulaiman yayi sannan yace”inma bakason magana damune don muna gida ai Matar dazaka aura tanason jin muryarka all the time so it’s final you’re going to be using this phone from this very day onwards…
Sakan baki Almustapha yayi yana kallon Sulaiman din sannan yace”to sannu Yaya Sulaiman”….
Dariya Sulaiman yayi,it feels good wallahi daka kira sunannan, Allah yasan manufan jaki dabaiyishi da kahoba because da I’m older than you all this miskilancin seka ajiye shi gefe wallahi…..
Murmushi kawai Almustapha yayi tareda jan hancin Sulaiman din playfully yana jijjiga kanshi,auchh it hurts Yaya…..
Serves you right cewar Almustapha din sannan yatashi daga zaunen dayake don barin dakin, Sulaiman azuciyarshi cewa yake Allah yakawo Asma’u tamin maganinka………
Kicibis Almustapha yayi da Dad abakin kofa,dan baya yayi sannan yagaida shi,shigowa dakin Dad yayi sannan yace dukanku kunanan ashe………
Gaida Dad Sulaiman yayi yayinda Almustapha yasake dawowa cikin dakin….
Sulaiman ne yace Dad wallahi yaki anfani da phone dinshi haryanzu, kallon shi Dad yayi sannan yace Almustapha yayadai,wayar batayi maka bane?….
Jijjiga kai yayi sannan yace aa Dad, I’ve no interest in using phone shiyasa……
Duban Sulaiman Dad yayi sannan yace kadaiji meyace ko,toseka barshi Almustapha dake bayan Dad yayima Sulaiman gwaliyo yana yar dariya kasa kasa,turo baki Sulaiman yayi sannan yace”Dad anma ai anfani da waya is very important bawai for his interest ba akwai sanda zaa nemeshi ah gida we can get him through the phone and akwai so many circumstances that phone helps wurin solving dinsu dakuma wurin passing information muma ai sabida wannan dalilan ne muke rike wayar”…..
Cikeda gamsuwa Dad yace kumafa hakane ko Almustapha?…
Yayi tambayar yana kallon Almustapha din,gyada kai Almustapha yayi yana dan hararan Sulaiman, murmushi Dad yayi daman wayau yayi mishi don haka yace”tunda Dan uwanka yafadi anfaninta senaji yakamata kaima kana rikewa atleast for communication with us and your friends right?”…..
Gyada Kai Almustapha yayi kawai,yanajin kaman yayi punching Sulaiman ah kumatu,dariya Sulaiman yadingayi sannan yashiga hadama Almustapha wayar yana”barina maka saving contacts din dukanmu sannan asaka na future wife ko Dad?”…….
Jijjiga kai Dad yayi sannan yace Sulaiman case, bazaka barni inyi maganar data kawoni ba?…
To Dad zanbarka ammadai yakamata muje muga Anty Asma’u ko?…..
Dansa hannu Dad yayi ah baki yana tunanin sannan yadubi Sulaiman din”good idea Son, yakamata kuje kam kada Babanta yaji shiru yadauka ‘danmu basonta yakeyiba”, directly Dad yace to Almustapha za aje ganin sabuwar gimbiyar tamu kuwa?….
Gyada Kai kawai Almustapha yayi alamun to…
Dariya dukansu sukayi yayinda Dad yakamo hannun Almustapha din suka zauna bakin gadon don yasan begane komai ba tunda shi baiyi maganar dashiba….
Wannan karan in a serious tune Dad yace,kasan mun maida Asma’u gida ko?…….
Eh yace ma Dad din, ahankali Dad yace to Babanta abokina ne kuma dan zaman damukayi da’ita senaji halinta yakwantamin  shiyasa na nema maka izini gun mahaifinta kuma ya amince har muna shirin kai tambaya ma kwana kusa inafatan bazaka watsamin kasa ah Ido ba?….
Almustapha da zuciyarshi tadinga dukan uku uku tunda Dad din ya ambaci Asma’u yayi shiru,shiyasan ancuce shi ankuma gama dashi wannan wane irin danyen hukuncine,yacema Dad yanason wancan wawiyar yarinyarne….
Dad ganin yayi shiru yace Almustapha bakace komai ba?….
Lumshe idanunshi yayi zuciyarshi nayi mishi zafi,yayarda da komai da Dad zesashi yayi amma bazai yarda da maganar auren Asma’u bakam,not even in his dream…..
Daga Sulaiman har Dad din zuba mishi idanu sukayi sunajiran jin mai zaice….
“I’m sorry but I don’t like her”……
Shiru Dad yayi sannan yace”miyasa Son,is she not your type ko batada kyau ne,koko halayenta ne bakaso?”….
Shiru yayi yana tunani tareda tambayar kanshi yama fuskarta take don shi koza akasheshi bazai iya describing fuskar taba, betaba yimata kallon dahar zesan ya take ba bare yace tanada kyau ko batadashi and maganar hali kuma aganinshi batada hali mai kyau dukda kuwa tayi abu daya dayayi impressing dinshi and as from that very day yayi correcting mistake dinshi don yanzu baya barin Ummi tayi missing sallah ko daya don duk lokacin sallah seya tabbatar tayishi………
Jin yakuma yin shiru Dad yace toshikenan tunda bakaso baza ayimaka doleba, Sulaiman zaka fadama Abbanku abunda yacedin yanzu ko?….
Shikuma seya fadama su waziri dasuka shirya zuwa tambaya next week,nikuma zanfadama mahaifinta though I know he’ll feel disappointed sede bazan iya barin Dana ya cutuba besides koranshi yabaci nibandamuba tunda su wazirima sesunyita gutsuri tsoma kan anki auren Danmu shiba mulki ba bare samun Mata……
Almustapha yanajin yanda Dad din ke magana seyaji tausayinshi,it means that sunriga sunyi preparation nakomai he can hurt anyone but not Dad in particular har Dad yatashi zaitafi yace “wait”, victorious smile Dad yayi sannan yajuyo…..
“I accept”, Almustaphan yace dukda kuwa deep down bahaka yasoba, murmushi Dad yayi sannan yarungumeshi cikeda jin dadi sekaje kaganta during the weekend ko Sulaiman zai rakaka and tomorrow ana nemanka ah fada in the morning,kaxo and I know you know what’s right ko?….
Gyada Kai Almustapha din yayi, kissing forehead dinshi Dad yayi sannan yace Allah yayi muku albarka nan yafice  yabar dakin…

*****
Tunda aka kawota dakin take feeling so suffocated,jitake kaman takama dogarayen da duka dazata iya,ah zuciyarta kuwa jitake babu wanda tafi tsana irin Mai Martaba yanzu sabida yazubar mata da mutuncinta yau gaban kowa,mutunci da girman datajima tana tanadawa kanta and it even hurts more akan laifin dabatayiba,her next target is Talatu and Mai Martaba seta ci ubansu don ita zuciyar ta tagama bata Talatu is behind this don bata tunanin wani zaiyi mata,daga stool din dake gefenta tayi tayi wulli dashi tana huci ……..
Daya daga cikin dogarayen ya leko yana shirin mata magana galla mishi harara tayi wanda yasashi juyawa cikin sauri don kadama tarike fuskarshi tabbas intafita ah gurin nan kashinsa zai bushe ………
Wani takaicine yakuma dibanta da Sulaiman bezo yadubata daman shine hope dinta don duk ya’yanta sunkoma gidajensu,jifa tasakeyi da tray din dake gabanta wanda aka kawo mata lunch ne kai ko tabawa batayiba nan abincin suka zube ah kasa…..
Abunda batasaniba shine Sulaiman baisan komaiba don Dad baifada mishi ba hakanan Mai Martaba,su Amira ma basu saniba don bayin ah tsakaninsu suke gulmar baswa yarda wani yaji don kada ah hukuntasu…..
****
Tunsanda Laure tabar filin bayan an tafida Magajiya tashiga gudu zuwa gidan tsohon Galadima marigayi don kaiwa Hajiyarta labari mai dadi,sanda ta’isa dakinta har haki take tsabar gudun datasha, kyakyawar mata nagani zaune kan gado wanda bazata wuce sa’ar Magajiya dinba, murmushi tayima Laure sannan tatashi tadauki jug din ruwa tazuba ah cup tamika ma Laure din tana sannu karbi kisha ruwa……
Karba Laure tayi tashanye ruwan tas sannan tadan ji dama dama”Hajiyata albishirinki?”….
Dariya Matar tayi sannan tace Laure kibari kidawo daidai nariga nasan abunda zaki fadamin basai kin wahalaba kuma kyautarki zaki samu dayardar Allah…….
Gyada kai Lauren tayi yayinda matar tace”Ina cikin farin ciki marar misaltuwa yau laure sabida burin dana dade inason cikashi yaunafara ganin yuyuwarsa,in Sha Allahu Laure senaga bayan Magajiya banida wani buri daya wuce Inga bata numfashi ah doron kasarnan…….
Shiru Laure tayi tana mamakin me Magajiya tayima Hajiya din har 
Intana maganartama ranta baci yakeyi,cikeda curiosity Laure tace niko Hajiya nataba tambayarki miyasa kikeson ganin bayan Magajiya amma baki fadaminba….
Shiru matar tayi donkuwaa bama tason tunawa,bama tason tuna baya sabida wounds din dasuka jima da healing tasan zasu dawo sabone…………




Another chappy dearies….

topha su Magajiya under house arrestfans kuzo kuyi ceto i know you people are kind-hearted……

su Almustapha za aje ganin Gimbiya Ma’u,suwaye zasuyi rakiya?….


Tunani takeyi wayene haka Daddy yazaba mata,isn’t it so soon yaushema tadawo gida dahar za ace zatayi bako sekace wanda aka gaji da ita shigowar Munira ne ya katse mata tunaninta”Adda Asmeey tunanin mekikeyi haka?”…
Tabe baki Asma’u tayi sannan tace babu Munira badai har kun taso daga islamiyar ba, Asma’u tayi mata tambayar tana kallonta………
Bamu taso ba kekam ninedai nadawo gida,kikadawo yin me agida Munira Asma’u tayi tambaya fuskar ta daukeda dumbin mamaki don ah iya saninta Munira bata wasa da maganar Islamiya……
Banbada hadda mekyau ba shine Mallam Isma’il ya koreni ah aji nikuma naga bazan iya zaman wajeba shi yasa nataho gida,cikeda bacin rai Asma’u tace hankalin ki daya Munira koshi Malamin sa’an kine tukunnan ma yaushe kika baci da rashin bada hadda mekyau don dai niba haka nasan kiba……
Munira kaman zatayi kuka tace bantaba yin mistake ba inzan bada hadda seyau ai seyayimi uziri ni abunda yabatamin rai kenan…….
Kallonta Asma’u tayi sannan tace zoki zauna,zuwa tayi tazauna gefen Yayartata yayinda Asma’u cikin rarrashi tace “to ai don ya koreki bekamata kiyi zuciya kitaho ba seki tsaya kibashi hakuri idan yabar ajin hakan dakikayi kin nuna masa ke baki da kunya kenan kuma wato be isa yasaki abu kiyiba, Munira Mallam Isma’il Malamin ki he has the right to punish you when you’re wrong besides it’s for your well being kilan yaga kindaina focusing ne sosai akan karatun naki shiyasa ya hukunta ki daman gobe inkinkoma makaranta kije har office dinshi kibashi hakuri kinji?…..
Gyada kai Munira tayi sannan tace nagode Adda Asma’u……
Murmushi Asma’u tayi”you’re welcome my darling Sister,sede ki tabbatar kin iya haddan kafin goben yana iya cewa kiyi…….
To cewar Munira
sannan tafita daga dakin don zuwa tacire uniform din islamiyar….

*Around 3:45pm*

Ummi ne tashigo parlour inda tasamu Asma’u a zaune tana kallon *Arewa24* ana *Dadin kowa* sakan baki tayi”yanzu fisabilillahi yarinyar nan tun dazu bakije kinyi wankan ba?”……
Tashi Asma’u tayi daga kwancen da take tana yatsina fuska don ita gabadaya batasan dalilin dayasa Ummi tadamu da wannan visitor dinba”nafa yi wanka dasafe Ummi”….
Dakuwa Ummi tayi mata”Allah inbaki tashi kinwuce bandaki yanzunnan  kinyi wanka ba zan matukar bata miki rai,nifa banason shashanci fa I told you he’ll be coming this evening amma kina kwance abunki”, Ummi tayi maganar ranta bace haka Asma’u bataso tashiga bandaki tayi wanka tafito already daman tayi sallar laasar kafin Ummin tazo tasamota ah  parlour………
Zama tayi gaban mirror tana goge jikinta Asiya tashigo tana dan murmushi hannunta rike da waya da alama phone call tagama yi………
Asma’u ne tace Aseey daman andawo miki da wayarki?…..
Sa hannu Asiya tayi akan lips dinta tana shhhh slowly, alaman Asma’u tayi maganar ah hankali,rage murya tayi”meya faru zanyi magana ahankali?”….
Zama Asiya tayi bakin gado kafin tace banason wani yaji mana Daddy bedawo min da phone dina ba wannan wata wayace daban,ayya cewar Asma’u din tasowa Asiya tayi daga zaunen da take takaraso gaban kanwartata”kinata abu sime sime harsai yazo,naji Ummi tace dayanma ne bakon zezo ai yakamata kingama shiri yanzu kam”….
Fuskar tausayi Asma’u tayi”yanzu don Allah Aseey hardake amasu cemin in shirya, wani shiri ma zanyi tunda banmasan waneneshi ba……..
Kiyi hakuri cewar Asiya din cikeda tausayin kanwartata nidai abudaya nasani Daddy bazai taba miki zabi marar kyau ba kilan ma Yaya Mukhtar ne……..
Dasauri Asma’u tace Allah ubangiji yasauwake gwanda ah aura min wanda bansani ba akan Yaya Mukhtar sabida already ya zargeni and shida kanshi yazo yace yafasa so ni banama son yadawo…..

Story continues below

To Allah yazaba miki abunda yafi alkhairi kawai…..
Amin ya Allah Asiya,canza maganar Asiya tayi dacewa wani kayama zakisa tukun?…..
Ware hannu Asma’u tayi alamun bata saniba,bude wardrobe din Asma’u Asiya tayi tana karema kayayyakin kallo can idanunta suka hango mata wata hadaddiyar lace da Daddy yasiyo musu ah Lagos as tsaraba same design sede colours din ya banbanta nata maroon na Asmau kuma black ne da touch off na peach colour yayinda bakin lace din takasa anyi design  using white colour ciroshi Asiya tayi bakaramin kyau lace din yayiba gawani irin hadadden dinki da akayi masa Asma’u dake gaban mirror tana shafa mai tadubi Yayartata”Aseey menake gani precious kayan nan kikeson insaka sekace wanda zanje wani occasion?”……
Hararanta Asiya tayi tana nidai kigama shafa man inzo inmiki light makeup……
Cabdi cewar Asma’u Allah babu abunda za amin and kima maida kayan nan basawa zanyi ba……
Asiya ne tatashi tace”ba inje infada ma Ummi inaga in ita tamiki magana zakiji”…..
Hartakai bakin kofa Asma’u tayi saurin rikota tana fuskar tausayi,don Allah kidawo yanzu Ummi zatazo tafara scolding dina…..
Ajiyar zuciya Asiya tayi”okay then,amma on one condition”….
Naji cewar Asma’u din ….
You’ll do as i say, Asma’u ranta baiso ba amma da Ummi tazo tana mata tsawa gwanda kawai tayarda Asiyan tamata yanda taga dama don haka tace to nayarda……
Murmushi Asiya tayi sannan tabude drawer din Asma’u taciro makeup kit dinta daman Yaya Aliyu ne yasiyo musu tunwani tafiya dasukayi shida Daddy shine ya tmbayesu tsaraba sukace mishi make-up kit sukeso aikuwa yakawoma kowa nata ita da Asiya din…………
Sosai tagyara mata fuska very light makeup tayi mata wanda ya amshi fuskarta sannan tasaka kayanta dube dube tashigayi ah dakin, Asiya ne tace mekike nema ne wai?…
Yatsina fuska tayi”my niqab,kuturuuuu cewar Asiya tana zare idanu tareda rike kugu”tukunnan ma mezakiyi da niqab din” …….
With serious face  Asma’u tace zansaka mana…..
To wallahi baki isa ba inyi waisting time dina gurin gyara miki fuska kice zaki wani sa nikabi tsabar gulma…………..
Aseey kema kinsan dai bana fita da kwalliya ko,I always feel uncomfortable….
To yau zakifara kuwa,ai ba fita zakiyi ba acikin gidane Asma’u nasonyin magana sega Munira, Munir da ikram sunshigo aguje…….
Yaya Aseey bakin sun iso wallahi kuma harda fadawa fa,haba cewar Asiya yayinda tayi hanyar windown dakin Asma’u don tasan tana iya ganinsu daganan daga labulen tayi inda tahango motoci guda uku ah jere guda biyu Prado black sekuma ta tsakiyar Benz ce hadaddiya grey colour se yalki takeyi gani tayi fadawa sunfito daga  Prado guda biyun wasu daga cikinsu sukayi saurin bude Benz din ta both side of the door din lokaci daya Asiya taga samari biyu sunfito cikin shigarsu ta alfarma irin ta sarauta ihu Asiya tayi cikeda excitement ah fuskarta”Asma’u don Allah zo kiga  maza, ninama rasa wanene nakin aciki?”….
Itadai Asma’u zuciyar ta bugu tashiga yi tun sanda su Munira sukazo sukace harda fadawa akazo which means Yan *GIDAN SARAUTA* ne……..don haka bataji me Asiyan ma kecewa ba,kallon samarin tashigayi yayinda taga shigar dasukayi ma ba daya bane ba don daya Normal attire na sarauta yasaka yayinda dayan data lura taka kasa ma dakyar yakeyi da alama yanaji da sarautar shidin harda rawani akansa which means yanada wani post may be, bakaramin tafiya da imaninta sukayiba tana gani Yaya Mubaraq yafito sukayi musabaha sannan yayi leading nasu to parlourn saukan baki wanda yake gefen bangaren Daddy……..

Story continues below

Jiki bakwari tashiga takawa zuwa guest room din,the more she gets closer to the room the more she feel his presence batasan miyasa ba indai Almustapha na guri jikinta yakan bata gawani irin scent dinshi datakeji aduk sanda yake guri shidai scent din bana perfume ba just special one that she cannot explain,dan tsaki tayi tanason sama zuciyar cewa bashi din bane why will he be here kuma ae cewa akayi daga *GIDAN SARAUTA* suke tasan Almustapha ah gidan sarauta yake sede batayi expecting he should be like yanda su Asiya ke exaggerating ba dakuma fadawan data ganima dawannan tunanin takarasa shiga ciki batareda zuciyar ta tadaina bugun dayakeyiba………

Sulaiman dake zaune kan seater din dake facing kofa ne yafara ganinta cikin kayatattacen  murmushinshi yace”And here comes the Princess, Aunty Asma’u ina wuni?”…..
Kunyane yakama Asma’u lokaci guda dukda kuwa bugun da zuciyarta keyi don yanzukam tabbas tasan Almustapha ne yazo bawaniba to amma ya akayi haka shine tambayoyin data dinga yima kanta…….
Gaisheta Sulaiman yasakeyi ganin tana tsaye dagacan kusa da kofa,yar murmushin yake tayi”Yaya Sulaiman kadaina sani jin kunya please, karasowa tayi parlourn tareda zama can nesa da Almustapha din don tafi kusama da Sulaiman tace Ina wuni Yaya Sulaiman?”……
Dafe kai yayi yana kashh,your highness kidainamin haka kada kisa Yaya ya lillisani inmuka koma gida yau……
Dariya kawai tayi to yasu Amira, Asma’u da Sumayya nayi kewarsu sosai…..
Suma sunyi kewarki Your highness,sunce ingaida ki they wanted to come nahana su,inbanda gulma irin nasu suntaba gani anje hira da Mata ne yayi maganar playfully……….
Itadai murmushi kawai tayi yayinda Munira tashigo hannunta daukeda tray wanda kayan motsa bakine akai,gaidasu tayi cikeda ladabi Sulaiman ne kawai ya ansa yayinda gogannaku dake hakimce kan kujera Smilling kawai yamata wanda ita kadai tagani don kuwa Asma’u har ranta baci yayi dayaki ansa gaisuwar kanwartata tareda gode Allah dabata gaishe shiba datasha kusa Itama,aranta tana “Munira kema Allah yahada ki da arrogant Mr Taciturn guy yau”………
Seda Munira tafita sannan Sulaiman yace is she your blood Sister?….
Gyada masa kai tayi, murmushi yayi she looks exactly like you…..
Wa Muniran?Niko bana ganin kaman mu,keba amma nikam nagani kamar wata exact replica dinki fa cewar Sulaiman din dariya kawai tayi sannan tatashi tadibi juice tasa ah glass cup tamika ma Sulaiman din girgiza mata kai yayi”I’m okay nikam ba bako bane innatashi zan diba daman Yaya Almustapha ne naji yana cewa yanajin kishi sanda muke tahowa kibashi zesha”,badan ranta yasoba tayi inda Almustapha din kezaune tana mika mishi wani look yayi ma Sulaiman din don sharrin dayaji yayi mishi dariya Sulaiman yayi sannan yaciro wayarshi yashiga daukansu hoto batareda sun saniba,sa hannu Almustapha yayi yakarbi glass cup din ah hannunta wanda seda hannunsu yayi clashing gabadaya wani electric shock sukaji ah tare……..

Maida hannunta tayi cikin sauri bayan yakarbi cup din, Smilling Sulaiman yayi sannan yatashi don dama jira yake yamusu hoto yafice yabasu guri…..
Kallon Sulaiman Asma’u tayi alamun inazakaje, Allah yataimakeshi Zaliha tashiga kiranshi ah lokacin nuna mata screen din wayar yayi”sweetheart dina na kira nima”,zuwa yayi gab da Almustapha yamishi rada ah kunne”All the best Bro”….
Harara Almustapha yasakar mishi yayinda Sulaiman yafice yana dariya abunshi,shiru parlourn yayi kaman wanda babu me numfashi cikinta ita shiru Almustapha ma shiru sede talura gwanda shi he’s busy pressing his phone itada bata dashi seta shiga wasa da jikin carpet din dake gabanta abunda bata saniba Almustapha dinma awkwardness dinne yasashi danne dannen wayar yau dannata kawai yake batareda yasan meyema aim dinshi na danne dannen wayarbw sunfi 15minutes ahaka sega ikram tashigo tana sanye dawata doguwar riga yar kanti wanda iya gwiwanta take gashi rigar fara ce duk tabata da manja,sakan baki Asma’u tayi cikeda bacin rai tace Ikram mekikeyi anan?…
Batareda ikram takulataba cikin dan gudu gudu nayara takarasa gaban Almustapha tana mishi smiling…….
Tabe baki Asma’u tayi ita damuwarta daya kada Almustapha ya rainasu yace su kazamaine dubada yanda kanwartata take cikin datti sekuma Almustaphan yacikata da mamaki  ahankali yamikama Ikram din hannu alamun tazo gareshi babu musu yarinya takarasa kusa dashi dagata yayi yadaura akan cinyarshi batareda yadamu da dattin dake jikinta ba dukda kuwa how sensitive he’s when it comes to datti sa yatsanshi dayayi yashiga goge mata gefen bakinta ahankali itakuwa ikram se kare mishi kallo takeyi kafin ciki sauri tadubi Asma’u tace yaaaa Adda Asma’u ashe shine mijinnaki dazu damuka leka ta window dasu Yaya Aseey har muke cewa bamusan wannene shiba…..
Asma’u jitayi kaman ta kurma ihu,what will he think of them gashi daman shikam ya iya judging mutane directly…..
Almustapha murmushi kawai yakema yarinyar lokaci daya yaji takwanta mai arai,yanason yara arayuwanshi they’re very innocent and open minded…….
Ina wuni Uncle cewar Ikram din tana daga mishi hannu alamar hi inda tadawo dashi daga trance dinshi, murmushi kawai yakuma yimata yayinda tasa hannu tadauki wayarshi tana karema wayar kallo da mamaki yaga tashiga pressing dinta harda dube duben applications gani yayi tashiga wani app na game wanda Sulaiman ne yayi installing masa jiya……
Seda taga ma setting komai sannan takalleshi “can I play game with your phone?”…..
Gyada mata kai yayi yayinda tasauka daga jikinshi cikeda murna zata fita ah parlourn Asma’u ne tayi mata tsawa kan tadawo jiki na bari tadawo parlourn fuska kyabe kadan take jira tafashe da kuka”mayar mishi da phone dinshi”, Asma’u tayi maganar tana  directing Ikram to side din da Almustapha ke zaune…….
Kuka Ikram tafarayi yayinda Almustapha yace “Go with it ikram,go and continue playing your game kinji?”….
Cikeda jin dadi tafice ah guje, dawoda kallonsa kan Asma’u yayi yana hararanta”and what was that?”…..

Story continues below

“Inta bata wayar fa, she’s a kid”…..
Kai tsaye batareda Almustapha ya kalleta ba yace”Naki ne wayar so,that shouldn’t be your bussiness i guess”…
Wani irin takaici ne yaziyarce ta jitake kaman tafashe da kuka,ahakan akeson ta auri wannan dako magana mai dadi bai iyaba ahankali kuma tashiga tunowa da maganar dasukayi da Dad zuciyarta ne tashiga bugawa badai Daddy ya yardaba, indai Daddy ya yarda to itakam nata yakare don ta amsama Dad dinne cikeda confidence din Daddy bazai yardaba wata zuciyar ne kuma tace mata tabbas inma Dad zezo nema ma Almustapha aurenta seda izinin Almustapha din don haka tayi deciding tambayar shi miyasa yayarda zai aureta tunda bashiri sukeyiba…
Budan baki sukayi atare”miyasa kika/ka yarda zaki/zaka aureni”,sekuma suka dago suka kalli juna wani irin bakon al amari sukeji dukansu biyu din……
Cikin cool and soft voice dinshi medauke da nau’i kala kala yace”you go first”….
Jijjiga mai kai tayi alamar aa shiyafara magana dede nan sukaji an bankado kofar Hajja ce anci ado kanta rataye da gyale karasowa tayi cikin parlourn fuska babu annuri tadubi Asma’u tace ke tashi kifita ko ance miki bakon gurinki yazo ne?……
Asma’u dukda taji haushin furucin Hajja amma ita taimaka mata tayi wurin barin wannan arrogant mutumin,tashi Asma’u tayi zata fita inda Hajja tace dawoma don ubanki yarinya babu tarbiya ko kadan bare da’a…..
Dawowa Asma’u tayi jiki ah sanyaye kaman zatayi kuka shide Almustapha kallon ikon Allah yakeyi ahankali Hajja tadubi Almustapha sannan tashiga washe baki kaman ba ita ta murtuke fuska yanzun ba”Ina wuni ranka shidade?”…..
Alama yayi mata dakai na lafiya,bata damu da rashin maganar shiba don ita burgeta ma yayi,madallah to ya gajiyar hanya fa?…
wannan karan ne yabudi baki yace lafiya Lau,to Masha Allah cewar Hajja din sannan tace ranka shi dade kayi hakuri bawannan bace yarinyar daka keson gani din sannan tajuya ga Asma’u din tace don ubanki wayasaki zuwa nan,ke Asma’u wato bazaki tsaya inda Allah ya ajiyekiba ko?…
Inake Ina wannan tsarkakken bawan Allahn fisabilillahi inbanda rashin kamun kai irin naki da rashin sanin yakamata,wato abun naki be tsaya akan Dan Sarkin garin nan din kadai bako harma kina neman shigema wani nuna ta da yatsa Hajja tayi sannan tace”to bari kiji baki isa ba,kima cirema ranki auren wannan yaron Asiya zai aura bake ba, Hajja tafara kukan munafurci take tana goge kwalla”ni wallahi bantaba ganin masifa irin wannan ba kirasama wanda zakiyima bakin ciki se yayarki uba daya ba laifin ki bane ba laifin uwarki ne datake goya miki baya,tana kukan tadubi Almustapha dake zaune kan kujera he’s very confused wallahi ranka shi dade da ace yarinyar nan yarinyar kirkice babu abunda zai hana ni barinka ka aureta amma bata dace dakai ba kwata kwata hakanan bata dace da irin rayuwarka ba yarinyar nan batasan ciwon kantaba hulda take da Dan Sarkin garin nan da babu wanda besan shiba wurin lalata ya’yan mutane,yarone da bashida tarbiya bare ta ido harma tunani mukeyi ko ciki gareta sabida kusan satinta daya ah gidanshi yau ni inazan bar babbam mutum kamarka ya cutu bayan inada wanda zanbaka…
Almustapha is speecchless and out of words se sauke idanunshi dayayi kan crying Asma’u,se kuka takeyi helplessly kaman ranta zai fita Hajja ne tayi kanta tana don ubanki kukan munafurcin mekikeyi?…….
Kinason kinuna masa karya nikeyi komiye,tashi kifita ah parlourn nan yanzun nan….. 1

Tashi Asma’u tayi tana kuka zata bar parlourn tarasa metayi ma Hajja datakeyi mata irin wannan tsanar tayi tunanin in Ummi nada laifi ah idon Hajja bekamata ita yashafetaba tunda sun hada jini, she’s her granddaughter for goodness sake,miyasa Hajja kenuna musu banbanci despite knowing all this……
Kukan nata jinshi yakeyi ah kirjinshi kaman wanda ana soka mishi kifiya,cikin cool voice dinshi yace “Asma’u wait”,tsayawa tayi cak takasa cigaba da tafiyan sabida this’s the very first time daya kira sunanta setaji babu wanda ya’iya pronouncing sunan kaman yanda yayi it sounds so different and unique dukda kuwa irin halin da take ciki tsugunawa tayi agurin sabida kafarta takasa daukarta ahankali yadinga taka kan lallausar kafet din har ya iso in take shima tsugunawan yayi ahankali………..
Bata daina kukan ba hakanan shima baidaina jin yanda kukan nata keyi mishi araiba cikeda tausayawa yace”look at me Asma’u”……
Batasan sanda tadago tadubeshi ba to wayema ita data isa ta yi ignoring muryar Almustapha me shegen amo dakuma commanding gawani coolness kuma duk sun hadu guri daya…….
Sunkai Three minutes suna kallon idanun juna Haajjadake gefe tasaki baki tana kallon ikon Allah har yawu nashirin zuba,ciro hankerchief yayi daga aljihunshi sannan yamika mata”stop crying and wipe your tears”……..
Karba tayi batareda tasan ma takarba dinba nan tashiga goge kwallarta dukda kuwa sunki daina zuba shikuma seya juyaga Hajja yana mata wani irin kallo da’ita kanta takasa gane na menene kuma takasa gane wani irin expression fuskarshi keson nunawa itadai kawai tasan gwiwarta tashiga yin sanyi lokaci guda……….
Ahankali cikin wata irin muryar datake nuna cewa beji dadin abunda Hajjan tayi ba yace “Inna nasan wacece Asma’u,inasane da duk abubuwan dakika fada and despite knowing all this I still want to marry her,dan girgiza kai yayi ahankali ya karada ina nufin dukda sanin hakan danayi inason in aureta sabida haka kibamu guri inason yin magana da ita in private………..
Ba Hajja kadai tasaki bakiba harda Asma’u din kallon shi kawai takeyi yayinda kalamanshi keta sake yawo cikin kwanyarta barinma “I still want to marry her” dinnan daya fada shiko gogan naku besake bi takanta ba don yariga yayi fixing idanunshi kan Hajja yana jiran yaga zata fitan ko bazata fitaba, Hajja jiki ah sanyaye tatashi tafita don tama rasa nafada because bata taba tsanmanin irin wannan response din daga bakon ba……….
Yajima yana bin kofar da kallo kafin yamaido da kanshi kan Asma’u dake kallonshi tana kuka kaman ranta zai fita,dan tsaki yayi yana mamakin wacece wannan tsohuwar dako kunyar shigo musu batajiba……. 
Ah sanyaye yace”who is she and why is she saying all that?”…..
Asma’u rasa mezata cemishi tayi don aganinta abun kunya ne tabudi baki tacema Almustapha Hajja kakarta ce don haka tatashi tafice cikin sauri tana kuka……. +

Binta yayi da kallo harta bacemai dagani,it seems like she likes crying alot wata zuciyar ne tashiga cemishi kenan kallon da akema Asma’u kenan ah gida komi? sabida dai Hajja akwae alamun they’re related tunda ga kamar jini karara tattare dasu furzar da iska yayi ahankali”he hope that she’s not going through alot of hardships because of him”…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *