GIMBIYA HAKIMA CHAPTER A
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_STORY AND WRITING BY_
_Jameelah Jameey_
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoyan ta.🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_____________________________
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’+
”’SISTER JAMEEY DAN ALLAH KI FARA YIMANA POSTING THIS MONDAY AM BEG YOU SISTER JAMEEY WALLAHI GIMBIYA HAKIMA KO BA’A FADA BA ZAIYI DADI SOSAI DAN ALLAH KIYI HAKURI KI FARA POSTING THIS MONDAY DAN NEXT WEEK YAYI NISA SOSAI MUNA NEMAN WANNAN ALFARMAR😰”’
_Ko dan wanna baiwar Allah zanyi posting yau Monday, Amman ban dai cewa komai 😉😙_
Page 01&02
“Ranki ya daɗ’e Gimbiya Hakima, Fulani tayi aike, tace tana son magana dake,”..
“Lantana aje ace mata yau bani san yin magana da kowa”….
“Maryamu, yau Gimbiya Hakima tace bata son yin magana da kowa”..
“wai Allah kice yau an tabo jaraba a cikin gidan nan? “Aiko dai”…
“Lantana! Lantana!! Lantana!! “..
“Na bani Maryamu, Gimbiya na kirana, ni yau na shiga ukku, yau buguna ne Kawai baza tayi ba”…
“Allah ya kara maki lafiya, rainki yadaɗ’e uwar marayu uwargijiyata, ina neman sausaci rain Gimbiya ya dade”…
“Lantana, mai kika tsaya yi waje ina ta kiranki kin gyaleni?”..
“Ina neman a fuwarki ya uwargijiyata’..
“Yi man shiru ba wanann na tambaye ki ba, “nace uban me kika tsaya yi a waje?”…
“Eh naje nakai sakonki ne, “wani sako? “Na baki san yin magana da kowa yau”.
“Shine kika yi ma mutane wannan uwar tsayuwar, ke Bilkisu”…
“Naam Allah ya ja da rain uwar marayu Allah yaja da tsawancin kwana Gambiya Hakima”..
“wuce maza ki kiran man Sarkin bulala, yanzun nan”..
“Ton Allah ya taimakeki”
Nan Bilkisu ta tafi kiran sarkin bulala cikin rawar jiki tana tausayin Lantana dan bata san wani kallar hukunci Gimbiya Hakima zata yi ma Lantana ba..
“Dan Allah Gimbiya ki man rai, ki duba tsufa na, kiyi hakuri, kuskurene nayi ina neman afuwa”..
Tas! Tas!! Tas!!!
Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana cewa..
“Yi man shiru tsohuwar banza, tsohuwar wofi, ke har wani tsufa ne dake da za’a kalla aji tausayinki, to ni *GIMBIYA HAKIMA,* bani tausan Yaro balle tsoho”..
Suna cikin wannan yanayi sai ga Sarkin bulala yazo..
“Ran Gimbiya ya dade, gani na ansa kiranki, yake uwar Marayun masarautar kano”…
STORY CONTINUES BELOW

“Sarkin bulala, ina son yanzun kayi ma Lantana bulala hamsin, indan ta sosa ta zube, ko kuma tayi kuka, itama ta zube, bayan ka gama, ka kai ta gida Maza, tayi sati biyu, ana yi mata horo mai tsanani”…
“Angama uwargijiyata, Yanzun ko zani zartar da hukuncin da kika bani”..
nan Sarkin bulala ya fara zane Lantana, ko dogon tausayi babu a idonshi, sai da yayi ma Lantana tsinanan bugu, sannan aka dauke ta zuwa gidan Maza…
“Allah ya taimekike Gimbiya Fulani “..
“Maryamu, lafiya naga kin shigo haka, hankalinki tashe? “Allah ya taimakeki, Allah ya kara maki nisan kwana, da man Gimbiya Hakima ce tasa ake yi ma Lantana hukunci…
“Subuhanalillah! mai tayi mata? “Da man dan ta dad’e, da ta ce aso ace man nace maki yau bata son yin magana da kowa, shine tace ta dade, ta barta tana ta magana”…
“Allah sarki, je ki kira man sarkin gida”…
“To Ranki ya dade”, Nan Maryamu ta wuce jiki na rawa ta taho da sarkin gida..
“An gaisheki, Amaryar sarki, daga ke ba kari”..
” Sarkin gida, kai dai baka rabuwa da zolaya, kaje kace ma Hakima nace ta soke wannan hukuncin da tasa ayi ma Lantana, in ba haka ba ranta zai mumunan baci, kuma kace tasan tayi maza tazo kiran da nayi mata”…
“To Ranki ya dade, nan Sarkin gida ya tafi, yana zullumin yanda zai hadu da Gimbiya Hakima, dan ya san lamarin ta ba mai sauki bane…
Nan Sarkin gida yana zuwa, ya aika ayi mashi neman iso,”Gimbiya Sarkin gida, yana son ganin ki”…
“Bilkisu kice mashi na ya san ida dare yayi mashi kafin raina ya baci”…
“Allah ya taimaki Sarkin gida, Gimbiya tace yau bata son yin magana da kowa”…
“Kije kice mata Fulani ta aiko ni, “Gimbiya yace sakone daga wajen Fulani, “kije kice ya shigo, ya jira ni gani nan zuwa”…
Sai da Sarkin gida yayi awa biyu zaune, yana jiran fitowar Gimbiya Hakima, amman shiru kake ji, ba bu Alamunta..
“Bilkisu, dan Allah kije kice ma Gimbiya Hakima ina jiranta”..
“TO sarkin gida, “Allah ya gafartama Gimbiya Hakima uwar marayu”..
nan Bilkisu tana shiga ta tadda Gimbiya Hakima tana chatting hankalinta kwace, “Ke lafiya kika yi man tsaya? “Allah ya huce zuciyarki yar sarki jikar sarki, da man sarkin gida yace yana jiranki, “je kice mashi ina zuwa, “to Gimbiya, nan taje tace ma sarkin gida, “sarkin gida tace tana zuwa”…
Tafiya take cikin takama da jin kainta da kuma Izza da mulki, tana tafiya tana harbin iska, tana busa hanci..
“takawarki lafiya yar’masu gida, “yauwa sannunka Sarkin gida, lafiya kake nema, sai kace biyan bashi?”..
“Allah ya huci zuciyarki Gimbiya, da man Fulani ta bani sako, “wani kallar sako ne? Bana ce yau baniyin magana da kowa ba? “Allah ya huci zuciyarki, “naji mai tace maka? ka cika ni da surutun banza marar anfani”..
“Da man tace ki maza ki soke hukuncin da kika yanke ma Lantana, tun ranku keda ita bai kai da baci ba”….
“Je kace mata naji, amman sai gobe zani sa a fiddo ta”..
“Godiya muke Gimbiya Hakima ikon Allah, nan gani nan bari, kinyi ma makiya nisa,”..
“Da kata haka sarkin gida, kana iya ta fiya dan ka matsa man da shirmainka na banza da wofi mtsss”..
Nan sarkin gida ya tashi, jiki duk a sanyaye, yana mamakin yanda Gimbiya take gaya masu magana san yaranta, ko dan ta ganta ita yar sarki ce…
“Ai a haife na haifi kamar Hakima sau ukku, amman dan ina karkashinta take zagina, baki daya bata biyo halin iyayenta ba, Allah dai ya shirya”…
STORY CONTINUES BELOW

Sarkin gida ke faɗin haka sannan ya wuce sheshen Fulani dan isar da sakon Gimbiya Hakima..
“Allah ya taimaki Fulani, “sarkin gida, ya kuka yi da ita? “Eh tace zata saketa amman sai gobe, kuma tana kan bakarta na yau bata son yin magana da kowa”..
“Hmmm shikenan, sarkin gida, Allah ya shirya mana zuri’a, ka haifi ɗ’a baka haifi halinshi ba”…
Nan dai Fulani ta kama fada tana mamakin halin ɗiyar tata, ta rasa inda ta gado wannan bakin halin na wulakanta tallaka, tana mamakin yanda Hakima bata son tallakawa ko daya…
rayuwa kenna, haka dai fulani ta gama faɗin ta sannan ta wuce sheshen Gimbiya Yakumbo…..
“Ranki ya dade Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Fulani, tana neman iso, “kuje kuce mata ta shigo,nan Gimbiya Fulani ta shigo ita da kuyunganta suna take mata baya…
“Sannu da hutawa Yaya, “yauwa sannu da zuwa Fulani, naji ance Hakima ta yanke ma baiwarta hukuncin sati biyu a gidan maza”..
“Hmmm hakane yaya, amman yanzun tace gobe zata sa a fiddo ta”..
“Gaskiya Fulani, Hakima tana bukatar gyara, ban san ina ta samu wannan halin ba”..
Hmmm! “wallahi nima Yaya wannan halin na Hakima yana damuna ban san ya zanyi da ita ba, kai haifi ɗ’a baka haifi halinshi ba”…
“To kuma naji ance tace yau bata san yin magana da kowa, “Eh hakane ai yanzun sheshenta zan wuce dan ya zama dole ta tsaya ta saurare ni, tun kafin maimartaba yaji abunda tayi a yau”..
“Gaskiya ya dace ai, “to ni na wuce Yaya”…
Nan Gimbiya Fulani ta tafi sheshen Gimbiya Hakima dan sunyi magana da ita..
“Ran ki ya dade ga mai girma Gimbiya Fulani a hanya, “to naji wace ki ban waje”..
“Nan Bilkisu ta fita jiki duk a sanyaye, tana cewa haka dai zamuyi hakuri da uwargijiyar tamu..
“Fulani sannu da zuwa”.
“Yauwa Hakima, ai ke keda sannu tunda kin nuna ban isa da ke ba kin nuna ban haifeki ba , to ni gani na taso da kaina”..
“Fulani zan fiddo Lantana gobe dan har umarni na bada na fiddo ta a gobe”..
“Ni ba wannan ya kawo ni ba, inkin fiddo ta kanki inma baki fiddo ta ba shima kanki, tunda kinfi kowa anfana da Lantana”..
“Nazo ne nayi maki bayanin addimission dinku ya fito, dan haka Maimartaba yace ki fara shiri ko wani lokaci kina iya ta fiya makaranta”..
“Haba Fulani, taya za’ayi Baffah yayi man haka?”..
“Yanzun kamar ni *HAKIMA* ace a rasa inda zaniyi university sai a Nigeria, Nigeriar ma wai wata A. B. U. Zaria, salon tallkawa su rai nani su dauka matsayin mu daya dasu Fulani”..
“Ke wacece inba mutun ba kamar su? Wai Hakima maiyasa baki san tallakawa? Basan ina kika dauki wannan mugun halin ba, shi tallaka ba mutun bane?”..
“Ke ba kowa bace face *GIMBIYA HAKIMA* , daga nan baki wuce komai ba, kuma ba zamai maki dole ya zaman ki dole kije karatu kasar zauzau, ni naji dadi da Maimartaba yace baki fita kasar waje”..
“Ya zama dole ki koyi huda da tallakawa , dan baku da banbanci a wajen Allah nidai ina gaya maki gaskiya Hakima”..
“Amman gaskiya Fulani ni bani zama hostel, “wanna kuma, ni na wuce, “to a huta lafiya”..
Haka Fulani ta baro Gimbiya cikin bakin ciki da bacin rai dan Gimbiya tasan Maimartaba baya wasa idan yace bai fidda da ta kasar waje karatu to baya chanza wa..
“Kash ni Hakima wai maiyasa Maimartaba yake san yana hadani da tallakawa, bayan ni ya san na tsani tallaka amman yanzun wai a rasa school din da ni *GIMBIYA HAKIMA* zani sai wai *ABU ZARIA* , amman shikenan”..
Haka dai Gimbiya Hakima ta kama yan maganganun ta..
“Bilkisu!
“Naam Allah yaja da ran uwargijiyata, gani ina jiran umirninki na aiwatar”..
Sai da Bilkisu tayi kusan minti goma tsugune tana jiran umirnin Gimbiya Hakima sannan tace..
“Ni kike jira naje na hada ruwan wankan da kaina kena?”..
“Tuba nike ranki ya daɗ’e..
“Yi man shiru duk baku da wani anfani a wajena, da zaran na hukuntaku ace ban yi maku adalci ba, bayan duk baku san aikin ku ba”..
“Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausaci rainki ya daɗ’e, anyi man afuwa insha Allah haka ba zai sake faruwa ba”..
“Yi man shiru wawiya kawai dake, ku baku kama girmanku kurkure har na nawa kuke yi man cikin gidan nan? dan haka tashi kiyi aikinki kice ma yan uwanki gobe ina san ganinku dan haka tashi ki bani waje useless woman..
Nan Bilkisu ta tashi jikinta na rawa tana godema Allah da hukuncin Gimbiya Hakima ya tsaya iyakar zagi da bata yi mata hukuci irin na Lantana ba”..
Haka ta shiga toilet ta hada mata ruwan wanka..
“Ranki ya daɗ’e, na gama hada ruwan, haka Bilkisu tayi tsaye tana jiran tashin Gimbiya, tana jin ina ace tana cikin masu yi ma Gimbiya girki ko gyaran gida da yanzun ta can ta na hutawa, amman yanzun su ke hadama Gimbiya ruwan wanka da kuma bata labari har sai tayi bacci ita da Lantana, sai da Gimbiya ta gadama sannan ta tashi ta shiga wanka, kafin ta fito Bilkisu ta gyara gado ta fiddo mata kayan sawa.
“Je ki hado mani tea ki taho man da tufa”..
“Angama ranki ya daɗ’e, Bilkisu ta tafi jikin na bari ta hado ma Gimbiya Tea mai kyau da dauko mata tufa harda ayaba ta kawo mata, nan ta bare mata ayaba ta miko mata, sannan ta zuba mata Tea din a cup ta mika mata..
Kawai sai Bilkisu taji an watsa mata ruwan zafi a fuska cikin bacin rai Gimbiya ta fara magana..
“Dan mai zaki hado man Tea ki sa man sugar?”..
“Allah ya huci zuciyarki, naga haka kika ce adinga samaki sugar in za’a hado maki shayi”.
Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wankama Bilkisu mari tana wurga nata ayaba a jiki da sauran Tea din da ya rage tana ce mata..
“Dan nace ku ringa sa man sugar sai nace maku kullun ko? “..
“Aa Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausacin hukunci gurin uwargijiyata uwar Marayun masarautar Kano..
“To ubanwa zai gyara maki wajen? “Ina neman afuwarki yar masu gida, yanzun nike jiran umirnin tashi Gimbiya”..
“Tashi maza ki goge wajen ki ban waje ki sheda ma shashasun masu Aiki bangarena irinki gobe karfe shiddan safe ina bukatar ganinku kafin kowace ta fara Aiki”…
“To insha Allah, godiya muke Gimbiya uwar-adalci ga tallakawanta, nan ta tashi tayi mopping din wajen sannan ta wuce tana godema Allah da ya kubutar da ita daga mumunan hukunci Gimbiya Hakima..
_By jameelah jameey 🖋__
Share and comment pls
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
03&04
Tunda Asuba su Bilkisu suke tsaye jiran Gimbiya Hakima, hankalinsu duk a tashe yake baki dayan su suna tsoron hukuncin da zata zartar a kansu..
“Wai Ba’ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya Hakima?”..
“Wallahi A’bu nima bansan mai mukayi ma Gimbiya Hakima ba, amman karki so kiga yanda jiya ranta ya baci, ko nima nan dakal nasha dan harda mari sai da na sha cikin daren nan”..
“Yanzun Ba’ba Bilkisu ke din Gimbiya Hakima ta mara?”..
“Yo sau nawa ankayi Murja ai sai dai kar’asake indai marine munsha shi wurin Gimbiya Hakima nida Lantana yunzun kinga Lantana tana gidan hukunci dan ma Allah yaso ta yau za’a fiddo ta, da sati biyu ta yanke mata”..
“Wai dan Allah maiyasa Gimbiya Hakima bata biyo halin iyayenta ba? baki daya Gimbiya Hakima bata da tausayi balle imani, da tana da tausayi da bata mari kamar su Ba’ba Bilkisu ba”..
“Hakane gaskiya Ladi, shiyasa na godema Allah da nike wajen dahuwa kawai, shiyasa kullun nike kiyaye wulakancin Gimbiya Hakima, domin bata gani girman kowa cikin masarautar nan”..
“Aiko Larai, kinga yanzun har karfe goma na safiya yayi amman har yanzun bata yi lokacin mu, itada tace tun shiddan safe take san ganinmu, amman shiru kuke jinta”..
“To ya zamuyi Ba’ba Bilkisu, ai hakuri zamuyi tunda haka Allah ya kaddari rayuwarmu, “aiko dai ai hakuri ya zama dole Larai..
Su Ba’ba Bilkisu suna can tsaye tun asuba, amman Gimbiya ta gyalesu kuma sarai ta san da tsayuwarsu a bakin shashenta saboda tun takwas din safe take ido biyu tanata chatting dinta sai da goma tayi sannan ta shiga wanka, bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata purple din doguwar riga sannan ta fito tana tafiya cikin isa da mulki irin na sarauta..
“Sai yanzun kuka gadamar zuwa kenan?”.
“Muna neman afuwar Gimbiya, uwar Marayu, tun dazun muke nan muna jiran isowarki”..
“To maiyasa bakuje kuka yi man magana ba?”..
“Allah ya huci zuciyarki, ai bamu da ikon zuwa turakarki batare da wani dalili ba, kuma ai kina bacci shiyasa”..
“Matsalarku ce wannan, kuna jina?”..
“Eh muna ji uwargijiyarmu, muna jiran umirni daga gareki”..
Mtssss”wai ku wasu kallar jahilai ne dabobi wanda basu da gwakwalwa basu da lisafi da basu san inda yake yi masu ciwo ba? “…
“Allah ya huci zuciyarki, suka fada kansu a duge suna tsugune a kasa suna sauraren cin fuska da wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..
STORY CONTINUES BELOW

“In ba kuna wawaye ba mararsa Ilimi ba, Wanda basu san daidai ba, yo ina anfanin zama da wanda basu da Ilimi, taya zakusan ya kamata bayan bakuda Ilimi?”..
“A fuwan uwar Marayu, Gimbiya Hakima diyar sarki jikar sarki uwar sarki insha Allah, muna neman sausaci ran Gimbiya Hakima, matar sarki insha Allah”..
“Maiyasa baku san aikinku ba? Ku fi san kullun na kama yi maku magana daya sai kace wasu dokuna?”..
Su dai basu ce komai ba, dan yanzun su sunbar Mamakin halin Gimbiya Hakima, dan inda sabo sun saba da zagin wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..
“Dan haka ku bude kunnuwanku da kyau zan sake maimaita maku ka’idojina, dan na lura ku jaikayene da man jaiki shi ake maimaitama magana”..
“Daga yau karku kuskura na sake taraku akan magana ɗaya, kunajina ko?”..
“Eh muna ji uwargijiyarmu, Allah ya kara tsawaucin kwana”..
A’bu ke da Murja daga yau ku zaku ringa yi man sauwar abinci , karfe bakwai na safe na tadda kun gama hada man abinci, karfe biyu na rana kungama na rana, karfe bakwai na dare kungama na dare, kunji ni ko?”..
“Eh muna ji, insha Allah, bazamu sake mu sake karya umurnin Gimbiya ba”..
“Dan haka ku tashi ku bani waje, salan na kama maku da laifi, kusan hukuncin da zan yi maku, “insha Allah zamu kiyaye”..
“Ladi da Larai ku kuma daga yau aikin gida ya dawo kanku, dan na gaji da cin jagwalgwalon abincin ku da kullun sai kun cika mashi gishiri sai kace ba yan-mata ba”..
“To godiya muke Gimbiya yar’masu gida”..
“Ku tabbatar kafin na tashi bacci kun gama gyara ko ina cikin gidan nan banda dakin da nike bacci shi daya ne ban yarjemaku da ku shiganman daki ba, dan ba daukar kazantarku banzaye kazaman banza kazaman wofi, ku tashi ku bani waje”..
“Godiya muke Gimbiya Hakima”..
“Bilkisu ke kin san aikinku ai ke da Lantana, dan haka sai ku kara hinma, dan na lura yanzun kuma kuna san ku sa lalaci cikin aikinku, idan kuma ku ka bari raina ya baci bansan abunda zan yi maku ba, dan haka wuce ki karaman Sarkin bulala”..
“To Gimbiya, nan Ba’ba Bilkisu ta tashi ta tafi kiran sarkin bulala”..
“Sarkin bulala, Gimbiya Hakima tana san ganinka”..
“Lafiya dai ko? “Eh lafiya lau tana san ganinka dai, “to gani nan zuwa, nan Ba’ba Bilkisu ta taho gaya ma Gimbiya sako..
“Ranki ya dade gashi nan zuwa, “naji tashi ki ban waje kika yi man wani tsugune gabana”…
“Gimbiya Hakima, uwar Marayun masarautar kano, gani na ansa kiranki, ina mai jiran umarninki na zartas”..
“Sarkin bulala, ina san kayi ma Lantana bulala goma, yanzun in dan ta motsa ko tayi kuka bulalar ta zube a sake wata daga farko, in dan ka gama hukunta ta a sako ta ta dawo bakin aikinta”..
“Angama ranki yadade, yanzun zani zartas da umirninki”..
Nan sarkin bulala yaje, ya fiddo Lantana yayi mata hukuncin da Gimbiya Hakima ta bashi umirni sannan yace tace ta wuce ta koma bakin aikinta..
Haka Inna Lantana ta taho, tana mamakin halin Gimbiya Hakima yanzun ace wai bakin aiki zata koma, bayan duk wahalar da tasha, haka ta koma shashen Gimbiya Hakima..
“Godiya nike Gimbiya nagode da sausaucin hukuncin da na samu daga gareki”..
“Lantana daga yau ki kiyaye duk abunda zai bata man rai, tashi ki ban waje”..
Nan Gimbiya Hakima ta shirya, ta dauki hanyar Shashen Gimbiya Yakumbo daga nan ta wuce Shashen Gimbiya Fulani dan ta gaidasu,da kuyangirta Aisha tana biye da ita a baya..
Bayan Gimbiya Hakima sun isa bakin turakar Gimbiya Yakumbo, nan aka yi masu iso wajen Gimbiya Yakumbo sannan Gimbiya Hakima ta shiga..
“An tashi lafiya Momy? “Lafiya lau Daughter, fatan ki tashi lafiya?”.
“Lafiya lau Momy, wai Momy yanzun tsakani da Allah Baffah yayi man adalci?”.
“Daughter ba yanda banyi da Maimartaba ba akan ya kaiki Turkey karatu, amman yace shi a dole nan kasar zakiyi karatu to ya zanyi dole sai dai muyi hakuri, kawai in kinje ki maida hankali kayi karatu da man ban jinki a famnin karatu, dan haka ki fidda komai a ranki Hakima ki maida hankali kiyi karatu”..
“Nidai gaskiya ba’ayi man adalci ba, ace ni Hakima zani university a Nigeria, duka karatu na a nan kasar nayi shi, shi ko Yaya Annas yana can yana karatun shi Dubai, niko za’a hadani da tallakawa su gogeman zufar tallauci”..
“Daughter ki tuna tallaka da mai kudi da mai sarauta duk Ubangiji Allah ya hallicemu, bamu da banbanci a gurin Allah sai wanda yafi bauta mashi, dan haka ina bukatar ki gyara kalamanki”..
“Afuwa nike nema Momy, “shikenan akiyaye gaba, kinje kin gaida Fulani?”..
“Aa daga nan zan wuce wajenta, “to yi maza ki tashi kije ki gaidasu dan Baffanki yana shashenta, “to ni zan wuce a huta lafiya, “Uhmm”..
Nan Gimbiya Hakima ta wuto Shashen Gimbiya Fulani dan gaidata itama, suna zuwa aka yi mata iso nan ta shiga ta samu waje ta zauna..
“ina kwana Fulani? “Lafiya”..
“Fulani ko na yi maki laifi?”..
“Ko daya mai kika gani Hakima?”..
“Naga duk kin chanza mani baki daya, wallahi Fulani baki sona kamar bake kika haifeni ba, Yakumbo tafi sona”..
“Hakima tashi ki bani waje tunda mun gaisa, haka kike so na soki baki jin tausayin bayin dake cikin gidan nan balle tallakawan waje?”..
“Haba Fulani, ni kullun sai kunce man naji tausayin tallakawa da bayin gidan nan, to ya kuke so nayi bayan ina iyakar bakin kokarina”..
“Naji Hakima, tashi ki ban waje, karki manta ki fara shiri kafin Maimartaba ya ce ki fito”…
“To shikenan Fulani, amman ina Maimartaba na gaidashi Yakumbo tace yana na?”..
“Eh! Yau bai san yin magana da kowa, yau ko fada baya fita, “to an gaidashi ni na tafi”…
Nan Gimbiya Hakima ta koma shashenta, tace ma su Lantana yau bata san ganin kowa, sannan ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta kwanciyarta…
*Follow me on my wattpad account :-JameelarhSadiq*
*Facebook:-Jameelah Sadiq*
*instagram Jameelah Sadiq*
_By jameelah jameey ✍🏻_
*Share*
*and*
*comment*
*and*
*Vote*
*pls*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
05&06
Wacece Gimbiya Hakima!!
Masarautar kano, Babbar masarautace wanda tana daya daga cikin masarautar da take babba a Nigeria..
Sarki Abdulsamad Abdulrazak shine mahaifin Sarki Abdulhadi Abdulsamad, sarki Abdulhadi Abdulsamad shine mahaifin Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad…
Sarki Abdulhadi Abdulsamad adalin sarkine, yana mulki cikin Ilimi da adalci baya san yaga tallakawanshi cikin hukubar yunwa ko wani abu na wahalar rayuwa..
Wannan kyaukywan hali na sarki Abdulhadi Abdulsamad ya gajeshine a wajen mahaifin shi Sarki Abdulsamad Abdulrazak..
Mahaifin Abdulhadi su biyu ya haifa shida da kaninshi Yarima Annas, sun taso cikin kulawa ta sarauta, mahaifinsu ya koya masu yanda ake mulkin adalci ya tusa masu soyayyar tallakawa a cikin zuciyoyinsu..
Sunan Mahaifarsu Hakimatu, gimbiya Hakimatu ta ba yaranta da Allah ya bata guda biyu tarbiya iyakar bakin kokarinta, ta koya masu gwamawarar rayuwa ta bada gudun muwa wajen gani soyayya ta shiga tsakanin su da tallakawa domin ita macece mai tausayin na kasa da ita..
Abdulhadi yayi karatun addini dana boko, shida kanin shi Annas..
Annas yana final year yayi accident ya rasu, haka su Sarki Abdulhadi suka yi kukan rashin dan uwa da sukayi suka barma Allah lamarinshi..
Mahaifiyarsu diyar sarkin katsina ce Gimbiya Hakimatu tana da faranfaran da mutane, ta zauna da sirikarta lafiya har mai rabawa tazo ta raba su..
Bayan Abdulhadi ya gama karatu ya auro yar’sarkin suleja Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Yakumbo Allah ya albarkace su da d’a daya Yarima Annas daga shi Allah bai sake ba Gimbiya Yakumbo haihuwa ba..
Bayan Sarki Abdulsamad yayi murabus ya maida mulki a hannun Yarima Abdulhadi da shekara hudu, sarki Abdulhadi ya auri yar’sarkin Adamawa Gimbiya Aisha ana kiranta da Gimbiya Fulani…
Gimbiya Fulani ita ta haifi Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad..
Gimbiya Hakima ta taso cikin gata da kulawa a wajen Yakumbo, dan Gimbiya Hakima bata san Fulani ce mahaifiyarta ba sai da ta girma sanann ta san ita ce mahaifiyarta.
Fulani da Gimbiya Hakima ba wani shiri suke yi sosai ba, duk da mahaifiyarta ce, amman Fulani tace mundun bata chanza halinta ba, to basu taba zama inuwa daya.
Gimbiya Hakima ta tashi da wani kallar hali wanda ya girgiza iyayenta, domin Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan, tun tana yarinya indan su Inna Lantana suka dauke ta, to suna ajiyeta sai anyi mata wanka inba haka ba bata iya bacci a ranar..
STORY CONTINUES BELOW

Tun Yakumbo na ganin kamar Gimbiya Hakima tana da kyamane, sai daga baya ta lura baki daya Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan…
Sunyi mata fadi amman bataji saboda ita acewarta bai dace a sun haɗa hanya da tallakawa ba, domin su masu mulki da kudi ne, wannan shine dalilin da yasa Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan..
Bata jin komai ta wulakanta tallaka, ko waye duk tsufanshi kuma duk yarintarshi, haka suke ta hakuri da halin Gimbiya Hakima tun tana karama take haka har yanzun gashi ta girma ta mallaki hankalinta..
Gimbiya Hakima, tana bala’in san taje kasar turkey karatu, wannan yana daya daga cikin burinta na taje kasar turkey..
Tun da sarki Abdulhadi ya fahimci Gimbiya Hakima, tana san zuwa turkey karatu shi kuma yace indai tana san ya kai ta turkey to sai ta chanza hali domin baya san halinta baki daya..
Gimbiya Hakima, tayi iyakar kokarinta na ganin ta rake abunda take amman ta kasa, duk da a haka tayi sanyi sosai akan da..
Ba yanda batayi ba sarki ya fahimta shida Fulani ta chanza hali, amman sunce su dai basuga wani change ba, shiyasa Maimartaba Abdulhadi ya samar ma Gimbiya Hakima addimission a A. B. U zaria yanzun haka yasa ana yi mata registration jira yake ayi resume ya hada mata kayan ta ta wuce makaranta dan so yake ta san maiye rayuwa..
Shi kuma yarima Annas yanzun haka yana dubai karatu yana karata engineer..
”’Wannan kenan kunji wacece Gimbiya Hakima in Summary dan bani san mu bata time wajen bata labarin da gwara kawai muyi mai anfani.. 😎”’
Back to story 🏃🏻♀️🏃🏻♀️
“Lantana!”..
“Naam, Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima uwar marayun masarautar Kano”..
“Yau bani san fita parlour cin abincin rana, dan haka Ina san keda Bilkisu ku kwaso man abincin dasu ka dafa Yau a shigo man da shi ciki”..
“To, angama yar’sarki jikar sarki, nan Inna Lantana ta tashi ta fita..
“Tashi bacci bai ganki ba, “na shiga uku ni Bilkisu wani abu muka sake yi ma Gimbiya Hakima, tunda naji ta kiraki hankali na yake a tashe?”..
“Kwantar da hankalinki, ba abunda mukayi sai dai yanzun muke san janyo ma kanmu bala’i, kin san dai Gimbiya Hakima bata san jira indan ta sa aiki, dan haka tashi mu shigar mata da abinci cikin uwar’daki, Yau bata san cin abincin a parlour sai cikin uwar’daki”..
“Alhmdulh, wallahi Lantana har hankalina ya kwanta, bansan abunda zai hadani da Gimbiya Hakima dan ita bata gani tsufanka zata ci maka mutunci ba ruwanta”…
“Yanzun zaki tashi mu kaimata ko har sai ta ne maimu? “To na tashi Allah ya fiddo mu lafiya, “Amin ya Allah Bilkisu”..
Nan su Ba’ba Bilkisu suka kama kwasar abinci suna kaima Gimbiya Hakima a bedroom dinta sai da suka gama kai mata komai sanann suka zuba mata..
“Bilkisu! “Naam Allah ya taimakeki, “maza kije ki Kira man A’bu da Murya suzo ina bukatar ganinsu komai suke su ajiyeshi su zo”..
“Angama uwar marayu, Allah ya huci zuciyarki, nan Ba’ba Bilkisu ta wuce kiran su A’bu..
“Lantana! “Naam Gimbiya Allah ya da tsawancin kwana”..
“Yau wa zai wanke wannan bayin?” koni kuka ajiye na wanke maku?”…
“Allah ya taimakeki, ai mun wanke shi da kika tafi shashen su Gimbiya”..
“A haka kuke nufin kun wanka bayin? “Muna neman Sausaucin Gimbiya Hakima mai farar Aniya”..
STORY CONTINUES BELOW

“Tashi ki sake wanke shi, har sai nace ki barshi haka, “to Gimbiya angama”..
Haka Lantana ta shiga toilet ta fara wanke shi, toilet din da sai ka kwanta kayi bacci cikinshi saboda wankuwa da yayi Amman Gimbiya Hakima tace bata ga wanki a nan ba🥺..
“Sannunku! Yan Madafa, “Aa Ba’ba Bilkisu kece da kanki da kafafunki, kice har yanzun Gimbiya Hakima bata fito waje ba?”..
“Waya gaya maku Murja? To Gimbiya Hakima ke san ganinku yanzun tace komai kuke ku ajiyeshi ku zo tana bukatar ganinku”..
“Inalillahi wa’inna’alaihirajiun! Allah yasa dai lafiya Ba’ba Bilkisu Gimbiya Hakima ke neman mu?”..
“To nima wallahi ban sani ba A’bu kawai dai tace tana san ganinku, dan haka ni kunga tafiya sai kun iso”…
“Tashi mu tafi Murja karda laifin ya kara nunkuwa, dan nasan Gimbiya Hakima bata kiran arziki, in dai Gimbiya Hakima ta kiraka to rashi mutunci da cin mutunci zata yi ma mutun”..
“Hakane A’bu, Allah yasa dai Gimbiya Hakima ba wulakantamu zatayi kamar dazun da safe ba, kinga dai yanda taci mana zarafi gaban shashenta Yau din nan da safen nan”..
Haka suka taho duk hankalinsu tashe, jiki duk a sanyaye dan sun san kiran Gimbiya Hakima ba alheri bane..
“Ranki ya dade, na isar da sakonki, ga sunan zuwa, “Bilkisu zo ki tausaman kafar naji ta ba yanda nike san ta”..
“To Gimbiya, nan Ba’ba Bilkisu ta fara yin ma Gimbiya Hakima tausa..
Lantana sai wanke kewaye take, ta gaji sosai ga daman abunka da jikin tsufa, ga dukuwa ba dadi, ta wanke yafi sau goma sha hudu, amman Gimbiya Hakima tayi burus da ita, ta nuna bama ta san da ita cikin toilet din ba..
“Ranki ya dad’e, ga mutanan madafa nan sun iso, “je Bilkisu ki shigo da su, “to ranki yadad’e”..
“Har kun iso Kenan? “Wallahi ko Ba’ba Bilkisu mun iso, “to bissimilla ku shigo cikin, “har ciki zamu shiga? “Eh ko insha Allah, ku taho”..
“Ranki ya dade gamu mun ansa kiranki cikin gaugaugawa”..
“Bilkisu! “Naam Gimbiya Hakima, “sake zubo man sabon abinci ki kawo man”.
“To Gimbiya, Nan ta sake zuba mata wani sabon abinci ta bata”..
“Gashi Uwargijiyata, “ajiye shi nan, sake zubo wani, “to Yanzun ko Gimbiya, nan ta sake zuba mata wani sabon abinci, “gashi ranki yadade”…
“Mika masu, “to angama Gimbiya yar’sarki jikar sarki”, Nan ta mike masu abinci tana kallon ikon Allah.
“A’bu! Murja! “Naam ranki yadade, “kuci abincin nan yanzun gabana, “to”.
Nan suka fara cin abinci, su dai basu ji abunda abincin yayi ba..
“Allah ya taimakeki munci, “ai na gani, ko kinga ana yi man jagora?”..
🤨 haba gimbiya magnar arziki mutun bai iya samu🙄
“Allah ya huci zuciyarki”..
Nan itama Gimbiya Hakima ta fara cin abinci, tana ci ta ya mitse fuska ta furzar da abincin bakinta akan fuskar A’bu, sanann ji kake…
Tas!!! Ta wanke Murja da wani lafiyayen mari sannan ta fara magana”..
“Ni zaku kashe?”..
“Ranki yadad’e muna neman agaji da Sausauci wajen Gimbiya Hakima uwar marayu”..
“Bana gaya maku bana san yaji yayi yawa a cikin abinci ba? Sannan kuma kun cika man mai cikin abinci, wato na mutu ko?”..
“Allah ya taimakeki, ai mu yau muka dawo madafa da girki, wallahi su Ladi basu gaya mana ba”..
“Ku baku da hankalin da zakuyi aiki da kwakalwarku ehye? Maiyasa ku wasu kallar dabbobine ku baku aiki da hankali?”..
“Ayi hakuri ba zamu sake ba”..
“Dallah can kuyi man shiru, wawayen banza wawayen wofi, ku tashi ku kwashi tsiyarku ku barman waje salan in kun tashi yin na dare ku juye buhun barkono a ciki”..
“Tuba muke nema Gimbiya Hakima, godiya muke, nan suka kwashe kaya suka fita dasu waje”…
“Lantana fito ya wanku, yanzun, “to godiya nike Gimbiya Hakima, uwar marayu da gajiyaryun Kano”..
Nan Ba’ba Bilkisu ta kama yima Gimbiya Hakima tausa, ita kuma lnna Lantana ta na bata labari haka suka kama yi mata har bacci ya kwasheta sannan suka fita waje..
“Wai Lantana yau su A’bu sun ga masifara Gimbiya Hakima, “kedai bari Bilkisu ai halin Gimbiya Hakima sai mu kawai zamu iya dashi, yanzun muje muci abincin da tace bata ci, “aiko dai”..
“Sannunku Murja, Allah ya baku hakuri, “Hmm! Ai yau Ba’ba Bilkisu munsha wulakanci baki ji kumatuna ba yanda suke yi mani zafi ba”..
“Hmm! Ai Murja ki gode ma Allah da hukuncinku ya tsaya iyakar nan, ni daga ta kirani sau uku tasa Sarkin bulala yayi man bulala hamsin da kaini gidan horo”..
“Hakane fa Inna Lantana, Allah yakara bamu hakuri, ga abincinku can kuma kuci tunda ita tace bata ci mun cika barkono da mai”…
Nan suka ci abinci suna labari, sai da mangarid sanann kowace ta koma bakin aikinta, su kuma su Lantana sune basu bar shashen Gimbiya Hakima ba har sai da tayi bacci sanann suka dawo shashensu na bayi…
*Wattpad Jameelarhsadiq*
*share*
*Comment*
*vote*
*please*
_By jameelah jameey_ ✍🏻
Share and comment pls
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
07&08
“Ni wallahi Hakim kina bani mamaki, “mamaki name kenan Aliyu?”..
“Kai dai rayuwarka haka kake ba ruwanka kamar ba dan sarki ba”..
“Hmmm! Aliyu kenan to miye dan ina dan Sarki? Ai duk daya muke a wurin Allah banbancinmu shine wanda yafi bauta mashi”..
“Hakane amman duk da haka maganar gaskiya kana bani mamaki ace ɗan sarki kamar kai dan Sarkin ma na Zaria amman kana rayuwa cikin tallakawa gaskiya ina mamaki ko ni da nike ɗan waziri ai bani kallar wannan sai dawowarka nike shiga cikin su”…
“Kenan da baka shiga cikin tallakawa? “Gaskiya bani shiga ai sai su renani”..
“Kaga niko ina shiga cikin tallakawana dan nasan mai suke bukata, sanann nasan maiye rayuwa inasan nasan maiye babu, kasan ko saboda mai nake san yin lectured a A. B. U?”..
“Aa nidai nayi mamaki ace kamar ka kake wani lecturer a wata A. B. U, da daman ina san nayi maka maganar kawai fuskace ban gani ba”…
“To na zabe yin lecturer saboda nasan wani hali al’ummar kasar Zaria ke ciki, san nasan wani hali tallakawa ke ciki, mai suke bukata ayi masu, mai ake yi masu wanda basu jin dadinshi, sai kuma ina kara yin expressed akan halin mutane”..
“Kaji dalili, Alhmdulh naji ance ankusa koma wa hutun Season kaga za’a kawo new inters student kuma ni zan dauki yan Chemistry”..
“Gaskiya kaji dadi halinka yana bugerni, wanda bai san halinka ba sai yace baka da tausayi balle imani”..
“Amman Hakim maiyasa baka dariya cikin tallakawa? Kuma kana san shiga cikin su dan kaga matsalarsu?”..
“Dan ina shiga cikin su shine zai sa nayi masu dariya ko sakin fuska sosai, ko ka manta nidain Yarima ne?”.
“ai naga tunda kana ma’amula dasu sosai ya dace ka zama mai sakin fuska garesu sosai”..
“Hmmm! Ai kai kasani haka Allah ya hallicine ban cika magana ba, ko da ko ina gaban Gimbiya Fulani, dan haka ba laifina bane yin Allah ne”..
Hmmmm! *YARIMA* *HAKIM* kenan, dan sarkin Zaria matashi maiji da samartaka ga kuma haiba da kyau da jinin sarauta dake yawo jikinshi..
Yarima Hakim, missikiline na ajin karshe dan bada kowa yake magana ba, inka ga maganar shi to shida mutun uku ne, daga Fulani mahaifiyarshi kenan sai kuma Maimartaba sannan abokinshi tun na yarinta Aliyu Haidar, da wannan mutanan biyu suke ganin maganar shi mai tsawo, ko kannanshi Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya basu ganin maganar shi balle dariyarshi abunda ke hadasu shine kawai su gaisa, ba wai wulakanci ke sashi haka ba Aa halinshi daga Allah ne wannan kenan….
STORY CONTINUES BELOW

________________________________
Washe gari tun da asuba Kuyangan Gimbiya Hakima suka fara aiki, kamar yanda ta bukata..
“Ladi, “Naam Larai..
“A gaskiya Ladi muna bautuwa a gidan nan, muna yi ma Gimbiya Hakima bauta amman bata gani, yanzun ji yanda muke ta wanann wahalar tun da asuba muke abu daya yanzun har bakwai tayi kuma tace kafin karfe takwas mu gama komai”..
“To ya zamuyi Larai tunda munfito a bayi? Ai hakuri ya zama dolenmu, kuma ai daga wannan mopping din mugama sai mu jira fitowarta ta bamu umirnin mu tafiyarmu”..
“Aiko dai Ladi, ai mu mungode Allah da ta fidda mu a madafa da Jiya mu zata wanka ma mari taci mana mutunci kamar yanda ta saba”…
“Eh mana, da man su A’bu basu cika haduwa da itaba tunda gyaran gida kawai suke suna gamawa kuma inta gani zasu kama gabansu ba kamar muba dasu Inna Lantana da ba mu rabuwa sai dare, kinga ai munfisu shan wahalarta”..
“Sosai ma, su daga Jiya kawai fa har sun fara koke-koke sun bani su ya zasuyi basu iyawa da aikin madafa, shine nace masu muma haka muka sha wuya har Allah yasa ta chanza mana aiki”…
“Ku ina fatan kun gama ga maigirma Gimbiya Hakima nan fitowa”..
“mun gama yanzun muka gama, sai yanzun kenan Allah yayi zata fito yar-mulkin!”..
“Ke Larai ba ruwana, ki gyara kalamanki yanzun indan tajiki kiyi ya?”..
“Sai tasa a hukuntani, kuma hukunci na nawa ne bangani ba indai na Gimbiya Hakima ne”..
“Nidai ba ruwana kunga tafiya wajen masu madafa naga har yanzun basu fara fito da abincin ba ga shi har Gimbiya Hakima ta tashi na niyar fitowa ma”…
“To Ba’ba Bilkisu a dawo lafiya, “Allah yasa Ladi ni na barku lafiya”..
“Ku yan madafa Ina fatan kungama dai ko?”.
“Eh mun gama yanzun muke shirin kai abincin wajen cin shi”..
“To barkan ku, kutaso mu tafi kawo na taya ku dauka A’bu”..
“To Ba’ba Bilkisu mungode, ni tunda dazun rabon da naga Inna Lantana, “kin san aikin Gimbiya Hakima ba karewa yake ba, tana can ta shafa mata mai”..
“Allah sarki Inna Lantana, duk dai sannunmu da bauta, “yauwa kunga har mun iso, nan suka jera abinci a bisa dining table bayan sungama, duk kowace ta gama abunda take suka zauna zaman jiran fitowar Gimbiya Hakima…
Gimbiya Hakima itace bata fito ba sai karfe goma, bayan su kuma tun karfe takwas kowace ta gama aikinta…
“Takawarki lafiya yar’masu gida, Gimbiya Hakima uwar marayu, Yar sarki jikar sarki”..
“Bilkisu! “Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima anfito lafiya?”..
Gimbiya Hakima bata ansa ba sai da tayi kusan ten minutes sannan tace “Lau, Ina fatan kowa ya gama aikin shi?”..
“Eh Alhmdulh duk sungama umirnin Gimbiya kawai suke jira ta aiwatar a garesu”..
Sai da ta mula tasha iska sannan ta tashi Bilkisu da Lantana suna biye da ita suka duba masu shara, sai dai suka gama zagaye sannan suka dawo ta zauna wajen abinci..
“Ace ma masu Shara su tafi su ban waje, “angama Uwargijiyata, nan Ba’ba Bilkisu ta fito main parlour inda suke tsugune tace..
“Ku su Larai, Gimbiya Hakima tace ku tashi ku tafi aikin ku yayi kyau, “godiya muke, nan suka tashi suka tafi suna Alhmdala cikin zuciyarsu sun rabu da Gimbiya Hakima lafiya ba tare da ta ci masu mutunci ba…
“Lantana! “Naam uwar marayu, “Uhmm, abunda Gimbiya Hakima tace kenan Amman har Inna Lantana ta gane abunda take nufi🧐..
Wai ashe tana nufin ta tashi ta zuba abinci ta fara ba su A’bu suci sannan ta ci itama wai Gimbiya Hakima ba dai masifa ba😁..
“Ranki yadaɗ’e angama zubawa, kallonta kawai Gimbiya tayi, nan take Inna Lantana ta shiga taitayinta..
“Murja bissimilla ga abinci, “to Inna Lantana, nan suka ansa suka ci sai da kowace tayi three spoon sannan suka ajiye..
Sai dai Gimbiya Hakima ta mula tasha iska sannan ta yi ma Lantana nuni da hannu..
“Gashi ranki yadaɗ’e, nan Gimbiya ta fara cin abinci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, sai da tayi two spoon sannan tace, “ku tashi ku tafi ku bani waje, “godiya muke Gimbiya Hakima”…
Bayan Gimbiya Hakima ta gama cin abinci ta aika sako wajen jakkadiya tana san yin magana da Maimartaba..
________________________
“Hakim! “Naam Ranki yadade, “nifa Hakim ina mamakin yanda ka makale sai kayi wannan koyawar a jami’a”..
“Fulani ya kamata ace yanzun kinyi hakura da wanann maganar dan Allah ki saman albarka cikin lamarin nan”..
“Shikenan naji Allah yayi albarka, “Amin Fulani godiya nike, ni zan wuce massalaci, “to adawo lafiya…
Nan ya fitowa shashen Gimbiya Fulani dogarawa suka goya mashi baya sunata yi mashi kirari nan suka shiga massalaci sukayi sallah bayan sun fito yaga sun kara biyo shi nan ya tsaya yace..
“Wai dan Allah bana ce maku kubar yi man wannan abun kamar wani abu”..
“Allah yaja da ran Yarima dan sarki jikan sarki, ka hanamu binka cikin gari nan ma kana cewa mubar binka, ai wannan shine aikinmu kare lafiyar Yarima sarkin gaba”..
“To naji, amman ai ni nace na hutar daku ko? “Eh ranka daɗ’e, “to dan haka ku wucewarku nagode”..
Haka suka tafi suna mamakin saukin hali irin na Yarima Hakim shi dai bai damu da mulki ba..
“Wai Kilishi ya ina maki magana kinyi shuru, tunanin mai kike?”..
“Hmmm! Kedai bari Gimbiya Zulaha, ina tunanin yanda zamu kauda wanann dan iskan yaron kullun da abun nike Kwana muke tashi, duk hanyar da muka bi bata bulewa, kullun sai fi yaran mu yake”..
“Wannan abun nima yana damuna Kilishi, ban ƙina bude idona naga Hakim baya numfashi a doran kasa”…
“Baki daya Yaro shida uwarshi kallon banza suke ma kowa cikin gida, wato dan sun samu boka wanda yafi namu aiki shiyasa, sun mallake gida kina ga Maimartaba baya jin maganar kowa cikin gidan nan sai ta uwarshi”..
“Kuma muma mun haifa cikin gidan nan fa, kuma nice babba cikin gidan nan, dan kawai an rigani haihuwa sai a daukeni sakara cikin gida ko magana ta ba’atsayawa a saurara”..
Gimbiya Zulaha ta ida maganar cikin bakin ciki da ɓacin rai..
“Karki damu Gimbiya Zulaha zan san abun yi, dole *YARIMA HAMID* zai gaji mulkin Maimartaba ba *YARIMA HAKIM* ba, dan Yarima Hakim da wata hudu ya girma Yarima Hamid kinga ko ya zama dole mulki ya fito dakin matar farko ba ta biyu ba”..
“Aiko dai Gimbiya Kilishi, shiyasa nike sonki, dan kina gane gaskiya”..
Haka sukai ta tautaunawa yanda zasu samu su kawarda Yarima Hakim a duniya duk saboda mulki..
______________________________
“Ranki yadaɗ’e Jakadiya ta aiko da sako, “mai tace Bilkisu?”.
“Cewa tayi Maimartaba yana san ganinki”.
“To ace mata gani nan zuwa, “angama Uwargijiyata”..
“Uwani kije kice tace gata nan zuwa, “to shikenan Lantana”..
Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi..
*Wattpad :- JameelarhSadiq*
*facebook:- Jameelah Sadiq*
*instagram:- Jameelah Sadiq*
_By jameelah Jameey ✍🏻_
*Share*
*Comment*
*Vote*
*pls*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
09&10
Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba ita da kuyanganta…
Bayan sun iso Jakkaddiya tayi mata iso har gaban sarki..
“Ranka yadade Allah ya ja da tsawancin kwana, na barku lafiya, “Uhmmm, abunda yayi mata kenan Jakkaddiya ta kama gabanta, ta koma bakin aikinta..
“Baffah ina kwana, “lafiya Lau Mamana,”Baffah da man nazo ne akan maganar makaranta, “to inajinki Mamana, mai kike so ayi maki?”..
“Da man ina neman Sausaci wajen Sarki mai adalci akan hukuncin da ya yanke man na yin karatu nan kasar Nigeria”..
“Kin gama Hakima, sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji yau Maimartaba ya kira sunanta ba tare da yace Mamana ba..
“Eh Baffah na gama!”..
“To daga yau karna sake jin kin zoman da maganar baki san karatu nan kasar, ya zamai maki dole kiyi karatu a kasar Zaria, can nike bukatar kiyi karatu, ko kuma na maidoki nan Kano kiyi karatun”..
“Allah ya huci zuciyarka, Amman, “ya isa haka Hakima kinsan bani magana biyu, dan haka ki shirya nan da kwana biyu zaki wuce makaranta dan na gaji da zamanki gidan masarautarnan kina shiga hakin bayin Allah”..
“Godiya nike Baffah, Amman ina neman alfarma ta biyu, “Uhmmm ina jinki, “da man nace ayi man adalci, adalin sarki, kar a barni na zauna hostel””..
“Da man ba hostel zaki zauna ba, na sa ankama maki gida, dan ba zaki zauna gidan Sarkin Zaria ba, ki zunda man mutunci kina wulakanta masu bayi””…
“Dan haka ina mai maimaita maki Hakima nan da kwana biyu zaki tafi makaranta, kije kiyi karatu nasan tarbiyar da muka baki, tashi ki tafi Allah yayi maki albarka”..
“Amin, godiya nike Baffah, ni na wuce”..
Haka Gimbiya Hakima ta fito turakar Maimartaba ranta bace tana mamakin yanda Fulani da Maimartaba basu ansar uzurinta a rayuwa su dai sunfi san bayin gidan nan akanta…
Tana cikin tafiya wata baiwa daga shashen bayi tafito bata bata lura da Gimbiya Hakima ba ta shafen mata gefen alkelba..
Tas! Tas!! Tas!!! “Ke wata kalar kidahuma ce da zaki taho kamar wani doki kike san bankadeni?”..
“Inalillahi! Ranki yadade kiman rai, wallahi banga tahowarku ba uwar marayu”..
“Ke Azima, “Naam Allah ya taimakike, “maza kije ki kira man Sarkin bulala, “ke kuma in samaiki bakin shashena, “to Allah ya taimaki Gimbiya Hakima”..
STORY CONTINUES BELOW

Haka wannan baiwar take gudu-gudu sauri-sauri, jiki na rawa haka ta isa shashen Gimbiya Hakima, ita ko Gimbiya Hakima tafiya take cikin kwaciyar hankali har dai tayi kusan awa sannan ta iso shashenta dayake da dan nisa tsakaninta da shashen su Maimartaba..
“Sarkin bulala, Gimbiya Hakima na bukatar ganinka, “To Allah sa dai lafiya? “To kawai za’ace kaima kasan indan Gimbiya Hakima tayi kiranka ai hukunci zata yanke kaima kasani, “to ai laifinkune, tunda kunsan halinta ba tausayine da ita balle imani, to dan mai zaku kama yi mata laifi, nidai indan ta ban umirni dole na bi, dan haka mu tafi”…
“Allah ya ja da ran Gimbiya Hakima, gani na ansa kiranki, “sarkin bulala, ina san kayi ma wannann kidahumar baiwar bulala Hamsin, indan tayi kuka ta zube ko kuma ta sosa balle motsawa”..
“Angama uwar marayu, godiya take, nan Sarkin bulala ya tashi ya fara zula ma wanann baiwa bulala sai da yayi mata bulala hamsin sannan ya tsaya, “ranki ya dade nagama cika umirninki”..
“Akaita gidan horo, ayi mata horo na tsawon sati, angama uwar marayu”..
Kai kai kai!!! Gimbiya Hakima ya kamata ki tausaya bayin nan fa😚, suna ce maki uwar marayu, Amman baki tausayinsu hukuncinki yayi tsanani fa💁🏻♀️, kudai muje zuwa my fan🥰
“Lantana!”..
“Naam Allah ya taimakeki, kije kice ma Barde a shirya man dawakai yau zani shakatawa da karfe biyun rana”…
“Angama, Allah ya ja da tsawancin kwana”..
Nan Inna Lantana ta tafi wajen Barde..
Nan Gimbiya Hakima ta shiga ciki, su Bilkisu suka fara yi mata tausa, azima tana karanta mata novel, kafin anjima su shirya mata zuwa shan iska…
______________________
“Lanto, “Naam Allah ya taimaki Gimbiya Zulaha, “ya kukayi da boka Dasheshe? “..
“Cewa yayi ya zama dole sai ansa ma Yarima Hakim wannan maganin cikin abinci yaci yana ci zai mutu, amman sai in zai kwata bacci za’a bashi abincin yace, yanda ana wayar gari a tashi da gawarshi”…
“Da kyau aikinki na kyau Lanto, Allah yasa wannan karan karda ya bata mana aiki, kinsan shi wani kalar mutun ne uwarshi ta ɓatashi da rashin kunya”..
“Gimbiya kibar komai a hannuna wannan aikin nawane, yanzun ma zan tashi naje na kai ma Mino kinsan tana daya daga cikin masu dafama Yarima Hakim abinci, na san zata yi aikin yanda muke bukata”…
“Hakane Lanto, ni na manta da Mino bangaren Hakim take dafuwa, to tashi ki kai mata amman kice ta kiyaye dan Hakim wayau gareshi, sannan ta kula da idanun mutane”..
“Angama ranki ya dade, na barki Lafiya”..
Nan Lanto ta tafi shashen Yarima Hakim, wajen masu girki.
“Ranki yadade Gimbiya Zulaha, Yarima Hamid yana san magana dake, “ace mashi ya shigo”..
“Allah ya taimakike, “Hamid sai yau ka gadamar dawowa cikin masarauta? “Haba Gimbiya to mai zan tsaya nayi cikin masarautarnan basu da mata babu abun sha sai lemu da tufa”..
“Wai Hamid sai yaushe zaka daina neman matan banza da wannan shaye-shayen da kake yi?”..
“Gimbiya very Soon na kusa dainawa, “haka kake san abaka sarauta kana wanann halin, ai kasan Maimartaba ba zai yarda da haka ba, shiyasa yafi san Hakim sama da kai”..
“Shi Hakim din kunsan abunda yake aikatawa indan ya fita waje? Ai gwara ni na fito da halina kowa ya gani, kuma dole na zama *SARKIN ZARIA* ko suna so ko basu so”..
STORY CONTINUES BELOW

“Kai dallah can matsa, muna yin abun mu cikin natsuwa da kwanciyar hankali zaka yi man hauka, waya gaya maka zakayi mulki mundun Hakim yana numfashi a doran kasa? to baka ba mulkin kasar Zaria mundun Hakim yana yawo bisa doran kasa”..
“To ni ki barni na tafi da wuka na tafiyar mashi da kai uban kowa ma ya huta”…
“Rufaman asari Hamid, ba ruwanka kai dai kawai ka samana ido, ni nasan abunda nike yi, indai Mulkine sai kayi shi indai ina numfashi a doran kasa, dan haka kaje kayi hidimarka nima ka barni da tawa”..
“To shikenan, na barki da hidimarki ni na wuce marace yayi zan hadu da wata baby yau ta shigo gari, kin san yan university sun fara dawowa”..
“Wuce ka tafi, Amman Hamid ka kiyaye, saboda makiya, “na barki lafiya”..
“Mariya! “Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Kilishi”..
“Ya kukayi da boka, “eh yace Yarima Hakim abashi kwana biyu zai fara aiki kanshi saboda yana da rikon addini da wuya aljanu su je wajenshi, kuma bai zina balle ko wajen zina suzo su shigeshi suyi aikin domin dole aikin da za’a yi sai da aljanu za’a yi shi”…
“Naji, to shi wannan sakaran fa shida sakaran uwarshi?”.
“Eh Yarima Hamad yace anbarshi da wannan halin na shaye-shaye da bin mata, ita kuma Gimbiya Zulaha yace abarta ta gama bin bokayen sannan zaiyi aikinsu ita da Hamid bayan ya gama mai wahala aikin Hakim”..
“To shikenan Mariya gaskiya naji labari mai dadi da marar dadi , taya za’a yi mu hana Yarima Hakim yawan wannan ibadar da ya daukarma kanshi?”..
“Shine abun dubawa, ki kwantar da hankalinki uwargijiyata ko da masifa sai *YARIMA* *HUMAD* yayi sarautar masarautar Zaria, sai kin zama uwar sarki kema wannan alkwarin boka ne”..
”’Wata sabuwa inji yan ca-ca kuma kowa kenan kanshi ya sani Gimbiya Kilishi tana ma Gimbiya Zulaha zagon kasa😝”’
“Naji, tashi ki tafi bakin aikin ki, ki kula sosai da abunda fulani dake ciki ita da wannan banzan yaranya nata, “insha Allah ranki yadade”..
“Allah ya taimakeki Gimbiya Kilishi na neman iso, “ace mata ta shigo”..
“An wuni lafiya Gimbiya Zulaha, “lafiya Gimbiya Kilishi, “ya Lanto ta dawo daga wajen bokan? “eh tadawo harma anyi sa’a, “anyi sa’a fa kika ce Gimbiya Zulaha? ,”eh anyi sa’a gobe da safe ki tashi da shirin zaman makokin *YARIMA HAKIM* , “taya haka ta kasance?”.
Nan Gimbiya Zulaha ta gaya ma Gimbiya Kilishi yanda akayi da boka yace masu, ba karamin farinciki tayi ba, dan tana ganin cikin sauki zata ida kauda Gimbiya Zulaha da *YARIMA HAMAD* cikin lokaci kadan tunda sun kauda mata Yarima Hakim, “dole sai Humad yayi mulki, Gimbiya Kilishi ta fada cikin zuciyarta tana murmushin farinciki tace, “gaskiya Gimbiya Zulaha aji tsoranki aikin ki yana kyau, “Hmm Kilishi kenan angaya maki ni ta wasa ce, sai dai ba sunana *ZULAHA* ba..
Tace cikin isa dan gani take boka baya faɗin karya balle boka Dasheshe da yake aikinshi kamar yankar wuƙa…
Haka suka gama maganarsu sai da dare ya fara sannan Gimbiya Kilishi ta wuce shashenta cikin farin ciki..
______________________________
“Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima, Barde yace angama komai fitowarki yake jira”..
“Uhmmm! Abunda Gimbiya Hakima tace kenan..
Gimbiya Hakima ta cigaba da abunda take saida ta sha iska tayi ma Lantana nuni da alkaibarta, nan Lantana ta tashi ta sanya mata sannna Azima ta dauki wayoyinta da post dinta suka fito, da yake lokacin sanyi ne Gimbiya Hakima rigar sanyi ta dogan wando ta sanya dan maganin sanyi, ga kuma alkaibarta da aka daura mata, Gimbiya Hakima ba karamin kyau tayi ba, sannan suka fito ta hau doki su Lantana suna kasa suna take mata baya har suka isa wajen shakatawar Gimbiya Hakima..
“Azima, “Naam Allah ya taimakeki, “miko man wayata wanda nike chatting da ita, “angama uwar marayu, nan Azima ta mika ma Gimbiya Hakima waya, nan Gimbiya ta cigaba da chatting sai da taji duk bakin cikin da Maimartaba ya cusa mata shida Fulani ya gushe sannan suka dawo gida….
Bayan sun dawo wanka tayi tasa kaya mararsa nauyi ta kwanta aka cigaba da yi mata tausa ita kuma tana chatting, sai da dare yayi sannan aka kawo mata Tea da chaps taci sannan ta kwanta aka cigaba da yi mata tausa Azima nayi mata karatu sai da tayi bacci sanann suka dawo suma suka kwanta dan su huta…
______________________________
“Kina jina ko Mino? “Eh Lanto ina sauraranki”..
“Anshi wannan maganin ki tambatar kinsa ma Yarima Hakim a cikin abinci yanzun na dare nan ba sai gobe ba”..
“Aiki mai sauki mana, yanzun a gabanki zan sanyashi ba sai kin matsa ba, “yauwa Mino shiyasa nike san aiki dake, “aiko bari ki gani, kinga na sa ko baki daya na juye shi ma”..
“Na gani kinyi kokari, na na wuce, “to mu kwana lafiya”..
Lanto na lafiya, Mino ta dauki abincin da tasa ma Yarima magani ta juye shi a shara ta zubdo shi ba Wanda ya sani, sannan tace ma wanda suke aiki tare ita daya ta kaima Yarima Hakim abinci yau ta hutar dasu, bayan sun tafi tayi sauri ta dafa mashi wani sabon abincin sanann ta kai mashi..
Su Lanto nacen suna jiran gobe da safe suyi zamab makoki🤣
Bayan Yarima Hakim ya dawo daga massallaci sai da ya biya yayi ma Fulani sai da safe sanann ya wuce shashenshi, bayan ya sha tea da yake haɗawa da kanshi, dan daman shi baya cin abincin masu girki sai na Fulani, kuma bai cin abincin dare daman yana hada ruwan zafi da kanshi ya sha sanann ya cigaba da Ibadodin shi yana neman tsari daga sharin makiya..
_By jameelah jameey✍🏻_
Share and comment pls
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=what
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
”’
A GASKIYA BA NI DA BAKIN DA ZANI YI MAKU GODIYA SAI DAI NACE ALLAH YA BAR KAUNA MASOYINA DOMIN COMMENT DINKU YANA SANI FARINCIKI SOSAI DA SOSAI 💃🏼💃🏼💃🏼❤️❤️”’
*Ga mai bukatar shiga group 08160508316 yayi ma wanna number magana banda kira pls*
+
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
11&12
Washe gari bayan Yarima Hakim ya tashi daga bacci yayi wanka sannan ya yayi addu’ar fita, ya fita sannan ya wuce shashen Fulani..
“Fulani ina kwana, “lafiya Lau Hakim ka tashi lafiya? “Lafiya lau Alhmdulh”..
“Fulani ni zan wuce office,”to Hakim, Allah ya tsare ya baka sa’a, “Amin Fulani”..
“Hakim ka biya shashen Gimbiya Zulaha da Gimbiya Kilishi ka gaishesu kaji?”..
“Fulani kin san matan nan ba son mu suke ba, mai zanje nayi wajen su”..
“Kaje ku gaisa Hakim ai kafi su har gun Allah,dan haka ka wuce ku gaisa”..
“To shikenan ni na wuce dan yau inada lectures, “to Allah ya baku sa’a”..
Nan Yarima Hakim ya fara shiga shashen Gimbiya Zulaha, nan yasa akayi mashi iso sannan ya shigo..
“Antashi lafiya? Lafiya, wani abu ka shigo man waje tunda safe? Dan nema”..
Dan Gimbiya Zulaha Tayi mamakin ganin Yarima Hakim, ai ita ta tashi da niyar ganin gawar Hakim, to wai shi Hakim wani kalar mutun ne wannan, mutun yaci guba amman ya tashi lafiya lau kamar kowa, tana cikin maganar zuci taji yace…
“Kwantar da hankalinki matar sarki, kema kin san bin umarni ya kawo ni wajenki, ba dan haka ba ba abunda zani yi a wajenki”..
Gimbiya Zulaha taji zafin maganar da Yarima Hakim yayi mata, amman sai ta daure bata nuna mashi komai ba tace.
“Ai daman ana san yaro mai biyaiya ga iyaye kayi kokari sosai Hakim”..
Haka Yarima Hakim da Gimbiya Zulaha suka kama gaya ma juna magana a fakaice sannan ya taso ya wuce Shashen Gimbiya Kilishi..
“Antashi lafiya Aunty? “Lafiya lau Hakim, ana nan anata kokari ko?”.
“Alhmdulh Aunty ni zan wuce na barki lafiya,”to shikenan..
Haka ya fita yana mamakin halin Gimbiya Kilishi, ita bata nuna ma mutun tana jin haushin shi ba kamar Gimbiya Zulaha ba da bata iya boye kishinta ba, bayan tare suke duk wani tungu acikin gidan..
STORY CONTINUES BELOW

Haka Yarima Hakim ya tafiyarshi gun aiki yana mamakin halin mutanan gidan su, na bala’in son mulki su dai su gaji sarauta..
“Ranki yadade Gimbiya Kilishi tana san shigowa, “je kice mata ta shigo, nan Gimbiya Kilishi ta shigo tace..
“Gimbiya Zulaha ya naga haka? “Hmm! Abun ya bani mamaki Kilishi, wai shi Hakim wani kalar mutun ne?”.
“Nima abunda nike tunani kenna, Amman anya da gaske Mino tasa ma Hakim magani? anya dan gaskiya ina kokonto Gimbiya Zulaha”..
“Wallahi Kilishi a gaban idon Lanto Mino tasa maganin, Kawai dai ina tunanin shi Hakim din wani kalar Mutun ne?”..
“To rabu dasu, in sun san wata ai basu san wata ba, wannan aikin kawai ki barshi a hannuna Gimbiya Zulaha”..
“Aa Kilashi wannan aikin dole mu duka biyu zamuyi wannan aikin dan naga alama ba aikin mutun daya bane”..
“Gaskiya hakane kin kawo shawara mai kyau kema Zulaha, to ni zan wuce Humad na can yana jirana zamuyi magana da shi”…
“To shikenan, ai da safe shi Humad din ya shigo gaidani, “ni kwana biyu kenan banga Hamid ba”..
“Eh jiya ai gida ya wuni, kenan baije ya gaidaki ba? “Eh banganshi ba, “to wani uzurin ne ya hana shi zuwa wajenki na sani, “hakane ni na wuce”..
“Humad, “Naam Ma’ma barka da shigowa, “yauwa Humad sannu da hutawa sarki mai jiran gado”…
“Haba Ma’ma sau nawa zani gaya maki akan ni bani san wanann mulkin da kike neman tusaman, kuma ga sarki can mai jiran gado Yaya Hakim, Amman sai zaki cema wani”..
“Humad anya kuwa kasha Nono na? Anya Humad kaine Humad nifa na haifeka, Amman ace baka biyo halina ba, Ina bata yuyuwa”..
“Nidai gaskiya Ma’ma ya kamata ki duba wannan maganar da wannan kudin da kike kashewa a banza wajen saɓon Allah ai gwara ki gina massallaci da kudin duk wanda yayi sallah zaa baki Lada”..
“Yi man shiru, Humad na gaji da sauraran bakin cikin nan naka ace yaro bai da zuciya ko kaɗan baka yi gado na ba, to tsaya kaji ko kana so ko baka so dole sai kayi sarkin Zaria, kafi kowa cancanta kayi sarki ba Hamid da Hakim ba, dan haka tashi kaban waje shashasha marar zuciya, wanda yayi Amai kare ya lashe”..
“Allah ya huci zuciyarki, na barki lafiya, nan Yarima Humad ya tafi ya bar mahaifiyarshi da bakin ciki, tana bakin cikin yanda Humad baki ɗaya baya kwadayin Mulki ko kadan, “anya Humad ba asiri aka yi mashi ba, Gimbiya Kilishi ta fada tana mamakin wannan abun…
________________________________
Bayan Gimbiya Hakima ta tashi bacci, su Lantana suka shirya yata yanda take bukata, sannan ta fito ta zagaya cikin gida sanann ta dawo taci abinci..
“Lantana!
“Allah ya taimaki Gimbiya, “dauko man alkarbata zamu shiga kasuwa zamuyi sayaiyar makaranta”..
“An gama ranki ya dade, nan Lantana ta dauko ma Gimbiya alkaiba, sanann suka wuce kasuwa..
Gimbiya sayaiyar Makaranta tayi a kasuwa sai da ta saya komai sannan suka wuce gida bayan sun dawo gida, nan Lantana ta shiryama Gimbiya kayan ta dan gobe zata wuce…
Bayan Lantana ta gama shirya ma Gimbiya kaya, sannan ta wuce itama ta hada kayanta ita da Bilkisu da Azima dan dasu za’ayi tafiya Sai da suka gama hada kayan su sannan suka kwanta bacci…
Washe gari da wuri su Lantana suka tashi suka ida hada duk abunda basu hada ba, sannan suka hada ma Gimbiya Hakima ruwan wanka, sannan suka fita suna jiran ta tashi daga bacci sai ta shiga wankan…
“Ba’ba Bilkisu, “Naam Azima, wani abu naga kamar kina cikin damuwa?”..
“Wallahi tsoro nike ji sosai, da Ina murna Gimbiya Hakima Zata tafi makaranta zamu hutu har sai ta dawo sannan zamu cigaba da bauta, amman ina cikin wanda Gimbiya Hakima ta zaɓa zata tafi dasu karatu”..
“To ya zakiyi Azima, ai ni daman nasan dani Gimbiya Hakima zata tafi zaria wannan karatun nida Lantana, dan baki bina bashin rantsuwa ko gidan miji damu Gimbiya Hakima zata tafi saboda ta saba da aikinmu Azima”..
“Niko gaskiya banji dadin wannan abu ba, na gaji da wannan bautar dan kawai ba yanda zaniyi”..
“Aiko kima saba, keda kika fara yima Gimbiya Hakima hidima daga baya, ni nan nida Lantana tun Hakima tana yar’shekara biyar muke yi mata hidima har yanzun maganar da nike yi maki”..
“Wai gaskiya? sannun ku kunyi kokari amman duk da haka Gimbiya Hakima bata raga maku, balle mu”..
“Ai haka halin Gimbiya Hakima yake sai dai hakuri, “to Allah ya bamu hakurin zama da ita tunda mudai yanzun muka fara, ko taya zamuyi zama da ita a Zaria? “Wannan ansar sai munje zaria zamu ganta”.
“Ku taso ga Gimbiya Hakima nan ta fito ku, nan suka tashi suka marama Gimbiya Hakima baya zuwa shashen Maimartaba, suna zuwa nan ta tadda Fulani da Yakumbo…
“Barkanku da hutawa, “barka Daughter har kin shirya ko? “Eh na shirya Momy”…
“To Daughter kiji tsoran Allah, indan mu bamu ganinki, to kisani Allahn da ya halliceki yana nan yana kallonki ko da karkashen kasa kika shige kika boye”…
“Sannan kiji tsoran Allah kiji tausayin bayin da zaki tafi dasu Daughter, dan Allah karki cucesu kamar yanda kike yi masu, kinga yanzun karatu zaki tafi”..
“Insha Allah Momy, zan kiyaye, “yauwa Allah ya yi maki albarka, “Amin Momy”…
Bayan Yakumbo ta gama yi ma Gimbiya Hakima wa’azi nan Fulani da Maimartaba suka yi mata fatan alkhari, sannna maimartaba yace…
“Na baki direba, sannan kin zabe kungangai gudu uku, na baki masu gadi guda hudu, dan haka Mamana akiyaye, in kinje kiyi abunda ya kawoki”..
“To shikenan insha Allah Baffah, nan dai suka gama yi mata wa’azi sannan aka sa kayan Gimbiya Hakima cikin mota nan suka dauki hanyar Zaria, da mota hudu akayi ma Gimbiya Hakima rakiya dan harda Gimbiya Yakumbo sai da ta raka Gimbiya Hakima makaranta…
Bayan sun sunka gidan da aka kama mata, sannan suka dawo gida..
Gidane flat house, babban parlour ne da bedroom guda uku, sannan boys quater, nan masu gadi da direba zasu ringa kwana, Gimbiya Hakima da su Lantana kuma zasu ringa kwana cikin gida, amman bedroom din Gimbiya Hakima daban…
_By jameelah Jameey✍_
*Share*
*Comment*
*Vote*
*Like*
*Please*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
13&14
Washe gari tun da asuba Inna Lantana ta tashi ta hadawa Gimbiya Hakima ruwan wanka..
“Allah yaja da tsawancin kwanan Gimbiya Hakima uwar marayu, ga ruwan wanka nan yana jiranki”..
“Ina Bilkisu take? “Ranki ya dad’e ai Bilkisu suna madafa suna nema maki abunda zaki karya kummallo kafin ki wuce bokon”..
“Maza kije kice mata, ta sallami Azima ta taho ta taya ki fiddo man kayan sawa, dan ita Azima tafi ku sanann kyau”…
“Angama yar’sarki, matar Sarki da yardar mai duka, “zaki tashi kije ki ban waje ko tsayawa zakiyi ki isheni da wannan maganganun naki, wanda basu da dadin sauraro?”..
“Tuba nike uwargijiyata, “maza tashi ki ban waje kije ki kirata ko kun dawo”…
Nan Gimbiya Hakima ta shiga wanka da suna da eight, Lantana tayi mamakin yanda Gimbiya Hakima tayi mata yau, wai yau Gimbiya Hakima bata zageta ba da tace mata matar Sarki, bayan Gimbiya Hakima bata san ace mata haka tunda ita bata da niyar yin aure, tafi san ta zauna gida tana zuba mulkinta yanda ta gadama, Gimbiya Hakima kenan..
“Harma kun gama kenan? “Wallahi kin san halin Gimbiya Hakima, bata cin abu mai nauyi da safe shiyasa muka soya mata biredi sai dankali da Tea”..
“Sannun ku to, ke Azima taso muje fidda mata kayan sawa har ta shiga wanka”..
“Wai Inna Lantana kina nufin Gimbiya Hakima ce ta tashi tun karfe bakwai saura?”..
“Nima nayi mamaki, dan tun ina gyara cikin dakin baccinta naga ashema idonta biyu, kawai dai tana wasa da waya sai da na gama hada mata ruwan wanka sannnan nayi mata magana”..
“Ku har mamaki kuke kenan? “…
“Ai abun mamaki ne Ba’ba Bilkisu,”to ku daina Mamaki ke Lantana kin manta yanda Gimbiya Hakima ke da san karatu? “Aah nasan tana da san karatu mana ban manta ba”..
“To Azima bari na gaya maki wani hali mai kyau na Gimbiya Hakima, “to Ba’ba Bilkisu ina sauraranki, Amman bari muje mu fiddo mata kayan sawa kafin ta fito”…
“To shikenan nima kafin ku gama na gama jera mata abinci, “to mun tafi, nan su Lantana suka tafi fiddo ma Gimbiya Hakima kaya, ita kuma Bilkisu ta jera mata abinci, bayan sun fiddo sanann suka dawo”…
STORY CONTINUES BELOW

“Ba’ba Bilkisu na dawo ina sauraranki wallahi ni kasa fiddo kayan nayi sabo da zumidin naji kyan halin da Gimbiya Hakima take shi, matar da nasan bata da kirki da tausayi”..
“Tabbas Azima maganarki dutsi, Gimbiya Hakima bata da tausayi Amman tana da hali mai kyau, kin san maiyasa nace maki haka? “..
“Aah Ba’ba Bilkisu sai kin fadi, “To bari kiji, Gimbiya Hakima tana san karatu quri’ani dan hadda ma gareta, idan dare yayi lokacin da ina kwana wajenta kafin ta ida girma, wallahi karfe biyun dare take tashi sallahr dare bata kwanta sai bayan ta gama azkar din safiya sannaan take kwantawa bacci”…
“Wai Gimbiya Hakima jiya kenan sallahr dare ta tashi da naga haske a dakinta? “..
“Kwarai kuwa, ai duk daren duniya Gimbiya Hakima bata bacci, shiyasa zakiga karfe taran dare ta kwanta bacci”..
“Ni sai nai ta mamaki, nace ita ta riga kowa kwantawa bacci, Amman itace karshen tashi bacci, Ashe saboda da sallahr dare take kwantawa tun tara? “..
“Eh, sannan kinsan maiyasa aka bata uwar marayu? “Aa nidai ina mamaki ace Gimbiya Hakima itace uwar marayun kano”..
“Tana bala’in tausayin marayu, dan Gimbiya Hakima tana da gidan Marayu ko ni kaina ban san adadinsu ba a cikin garin Kano, kuma ita take ciyar dasu, ta kuma yi masu dinkin sallah, sannan kuma ta sasu makarantar arabi da boko”..
“Allah ya saka mata da alkhari, Amman maiyasa bata tausayin mu bayinta?”..
“Wannan kuma a jininta yake, haka Allah ya hallinceta da izzar mulki, jinin sarautar kenan, dan ma iyayenta suna yi mata wa’azi, nan ai haka Gimbiya tayi sauki tunda har take bude baki tace yi kaza”..
“Wai kina nufin Gimbiya Hakima da bata yin magana? “..
“Eh haka nike nufi, da in zata saki aiki da ido take kallonki kin san abunda take nufi, kuma indan zata sa ayi horo sai anwatsa maka ruwanzafi ko na sanyi sannan ake yi maka bulala, bayan angama yi maka bulala tasa a daureka jikin wani abu sai kawuni sannan a kanka gida ladabi har na tsawon wata, sai da Maimartaba yayi tsaye sannan ta chanza hali”.
“Wai Allah mun gode maka, “ku ga Gimbiya Hakima nan fitowa”..
“Takawarki lafiya uwar marayu, “Bilkisu mai kuka dafa? ”..
“Soyayyan biredi sai dankali da tea”..
“Uhmm, nan Gimbiya ta zauna tayi breakfast, sannan suka rakota ta shiga mota sai A. B. U. ZARIA..
“Ranki yadad’e antashi lafiya? “..
“Lafiya da man kaine driver din da Baffah ya bani?”..
“Eh nine uwargijiyata, “ok Uhmm, nan ya bude mata back sit ta zauna, sannan ya zaga ya mazaunin drive ya tada motar, nan yayi horn masu gadi daman already sun wangale gate nan *GIMBIYA HAKIMA* suka dauki hanyar makaranta…
“Kana jina Bala? “Allah ya taimakeki ina jinki”..
“Bance ka tafi ba indan ka ajine, ka tsaya har sai nagama lectures sanann zani mutafi gida tare”..
“Angama Ranki yadad’e, Allah ya baku sa’ar karatu”..
“Uhmmm! Abunda Gimbiya Hakima tace kenan ta cigaba da chatting dinta, gashi ta makara dan yanzun har takwais da minti talatin, Amman hankalinta kwance..
______________________________
Woow wani santalelen handsome guy ne wadda Aqqalah ba zai wuce shekara 26 ba, dugone Amman ba irin sosai ba, farine sosai amman kwancecen haske gareshi irin na larabawan makkah,mai matsakaitan idanu Samanshi dauke yake da dogayen gashin idanu, girarshi a ciki take ta kwanta lufff, fuskarshi dauke take da dogon Hanci yayin da pink din bakinshi ya kasance karami dashi, Fuskarshi manne take da glass Amman class din na kara lafiyar idanu wato medical glass..
Lecture yake cikin natsuwa da kwaciyar hankali, Wanda duk rashin ganewar mutun idan prof *HAKIM ABDULMATALAK* ya koya maka sai ka gane saboda yana da method of teaching…
Ajin shiru kake jinshi kowa ya maida hankalinshi waje prof Hakim, ana sauraran lecture ga shi kuma lecture din ta dauki dadi, har ma wasu daga cikin student din basu san lokaci yayi ace ya gama, wasu daga cikinsu yan matane, wasu kuma serious student ne wanda suka abunda ya barosu daga gidan iyayensu gaba ɗaya…
Ji suke tashi kas! Kas!! Kas!!! Na tashi baki daya aji kowa waiga yayi yaga wace yar hutuce Wanan da take shigowa lecture yanzun anyi awa daya da fara lecture Amman ita sai yanzun take shigowa, kuma hankalinta kwace tana tafiya kamar bata makara ba, ta nuna bata san da akwai malami a cikin ajinba balle ya samu alfarma tambayar excuse..
Tafiya take cikin mulki da isa, sai busar iska take tana bada fadi, har ta isa wajen wani sit zata zauna sai kawai taji ance”Hey get out of my class, Gimbiya Hakima yi tayi kamar ba da ita yake ba, sai ji tayi ya sake cewa”I said get out of my class, you am talk to you”..
Yayi pointing ɗinta da hannu..
Haka Gimbiya Hakima ta tashi zata fita, yanda ta shigo cikin isa da takama, haka tazo fita ba ta yarda ta nuna taji haushi ba, tazo dai dai fita taji yace”lock at you, useless girl stupid kawai”…
Wanna abun shi ya kara ba Gimbiya Hakima haushi ta fito ta tsaya wani waje tana jiran fitowarshi dan sai ya gaya mata shi *DAN GIDAN UBAN WAYE* a cikin garin Zaria da zai ce mata useless, bayan duk korarta da yayi mata bai isheshi ba, ita shiyasa bata san harka cikin talakawa, dan talaka bai iya cin arziki ba dan ya samu yana lecturer shine yake san gaya mata maganar, “ina kamar ni *GIMBIYA HAKIMA* wani banzan talaka bai isa ya gaya man magana ba”..
Haka Gimbiya Hakima ta kama magana tana jiran fitowar *YARIMA HAKIM* ta sauke mashi kwadon rashin mutunci🤣..
Muje zuwa my fan, Team Hakima kun dai ba Hakima shawara karta janyo maku August nidai babu ruwa na lol☺️😚🤷🏻♀️.. .
_By Jameelah Jameey✍🏻_
*Share*
*Comments*
*Vote*
*Like*
*Please*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
*@JameelarhSadiq Wattpad*
15&16
Shi kuma Yarima Hakim, tunda ya kori Gimbiya Hakima waje, sai kowa ya kara shiga taitayinshi a class din, dan sun lura da alama baya daukar nonsense, dan haka sai ko wace mace mai shirin shigarmai rayuwa sai gwiwoyin su suka yi sanyi, Amman duk da haka wasu daga cikin su suna kan bakarsu..
Yana mamakin rashin tarbiya da rashin kunya da Wannan yarinyar da ya kora take da ita, dan ga dunkan alamu yarinyar bata da kunya dan ya ga zahiri a cikin idanunta, “aiko bamu shiryawa da ita, dan ko wacece ita ba zan dauke nonsense ba” haka ya faɗi a zuciyarshi..
Haka Yarima Hakim yaita mamaki, sannnan ya cigaba da yi ma yan class darasi, bayan ya gama ya hada takardunshi ya fito yayi hanyar office din shi..
Tunda ya fito Gimbiya Hakima ke bin bayanshi a baya, bai lura da ita ba dan shi har ya manta da ya kori wata yau a class din shi..
Yana bude office din shi ya shiga ya zauna, yana zama ko suit din shi bai cire ba, saboda anfara yin zafi shiyasa yake san ya rage suits din jikinshi..
Sai kawai ya ji an bankado door din office din shi, dagowar da zaiyi sai ya ga yarinyar da ya kora a class tana nuna shi da yatsa tana cewa..
“Kai dan gidan uban waye cikin garin zaria da zaka koreni a class har kana ceman useless?”..
Yarima Hakim tsayawa yayi kallon Gimbiya Hakima yana mamakin furincinta, wai shi Hakim take mana question na shi dan gidan uban waye, cikin zafin nama Hakim yace.
“Indan baki barman office ba sai kinyi danasin shigowarki office din na, ke bama danasin shigowarki office dina ba, sai kinyi danasanin haihuwarki duniya, wawiya marar tarbiya”..
“Kai harka isa kace man zanyi da na sani? To bari kaji ni Hakima ba wanda ya isa yace man zanyi da na sanin haihuwata duniya, balle Kai,ji baika dan Allah kamar wani almajiri, sannnan kaine baka da tarbiya ba dai ni ba”..
Kafin Hakim ya tashi yayi ma Gimbiya Hakima wani abu, har tayi ficewarta, dan daman a tsorace take dashi tana kallon idonshi da ta shigo office din shi taji tsoranshi ya kamata, kawai dakewa tayi ta mayarmai da ansa, dan bata iya daukar bakin ciki ita daya kwara suyi two two, daga office din Hakim wata lecture din ta wuce, Allah ya sota lecturer din bai Kai da shigowa ba, ta samu waje ta zauna taci kunu.
STORY CONTINUES BELOW

(Gaskiya Gimbiya Hakima baki da sauki, ya kamata ki gyara fa, dan Yarima Hakim ba kyaleki zanyi ba! Nidai gaskiya na gaya maki nida yan Team Hakim😎🙃)..
“Hmm! Mai zanyi ma yarinyar nan naji dad? “..
Yarima Hakim ya ke fadin haka yana ta zagaye cikin office din shi, dan tunda yake bai taba ganin wanda taci mashi mutunci ba kamar Hakima..
“Ni wanann yarinyar zata cema dan gidan uban waye cikin garin zaria, to ita waye ubanta? Ko waye ubanta cikin garin zaria sai na gyara mata zama, ta koyi yanda ake iya magana da mutunta na gaba da ita, dan na fahimci uwarta da manta da wannan aikin, tunda ta manta ni zan koya mata”..
Haka Yarima Hakim ya gama tunanin wulakancin da zaiyi ma Gimbiya Hakima, sanann ya hada komai shin ya tafiyarshi gida..
Itako Gimbiya Hakima ranta tas, dan ta rama abunda Hakim yayi mata, shiyasa ta maida hankalinta wajen lecture din da akeyi..
Alhmdulh Gimbiya Hakima taba yan class din su mamaki, dan duk question din da malamin nan yayi Gimbiya tana daga farko wajen tashi ta bada amsa, Amman cikin isa da takama da kuma nuna mulki take bada amsa..
Ba yan class kawai ba harta malamin yana mamakin halin Gimbiya Hakima, dan ya lura yarinyar zatayi ji da kai sosai, sai dai inda ta burgeshi tana da ilimi dan ya ga alama ta san abunda takeyi..
Bayan ya fita wata tazo ta zauna kusa da Gimbiya Hakima, tace mata, “sannu fa, Gimbiya Hakima kallonta kawai tayi bata sake kallonta ba, sai da tayi kusan minti biyar sannan tace “Yauwa”..
“Sunana Maryam Bello, Babana ne V. C din makarantar nan, sai da Gimbiya Hakima ta gama danna waya sannan ta juyo tace mata, “you are welcome, “thank You, kefa ya sunanki?”..
“Hakima Abdulhadi Abdulsamad,”wow nice name, kema yar nan zaria ce, “Aa kano, wani abu? “Aa bakomai kawai dai naga kinyi man shiyasa, ina san mu zama friend inba matsala”…
Sai da Gimbiya Hakima ta gama yi ma Maryam kallon raini sannan tace, “ur wclme, “thank You Hakima”..
Nan suka zauna ba wata magana sai ita Maryam take jan Hakima da labari, amsa daya ce take samu wajen Hakima daga Uhmm sai Aa.
Haka dai har sukayi exchange ɗin digits sannan suka yi Sallama, Maryam ta shiga motar ta, tana kallon yanda Bala drive yake budema Gimbiya Hakima mota, kamar zan duga mata da yanda take yi sai da tayi mamaki,amman ita dai Gimbiya Hakima tayi mata duk da taga ba halinsu daya ba, Amman zatayi hakurin zama da ita, har Allah yasa taga ta chanza mata hali, dan wannan ba hali bane mai kyau na wulakanta mutane..
Bayan Gimbiya Hakima sun koma gida wanka tayi sannan ta fito parlour ta zauna, su Lantana suka fara yi mata tausa(messaging), bayan sun gama ta ci abinci sannan suka fara bata labari…
_______________________________
“Sannu da hutawa, Ranki yadad’e, “yauwa Hakim, har andawo? “Eh Allah ya yarda, wallahi duk na gaji Fulani sosai”…
“Ai dole ka gaji, tunda ka daukarma kanka aiki, “Fulani nidai kisa albarka, “ai Hakim kullun ita muke sawa”..
“Yaya sannu da zuwa, “yauwa Maryama ina Sadiya take maiyasa bakuje school ba?”.
“Bamu da lectures yau sai gobe, “ok, Fulani ni zan wuce na gaida Maimartaba, “to adawo lafiya, ka dai ci abinci ko? “Eh naci, “karka kuskura kaci abincin gidan nan ina kara maimaita maka Hakim”..
“To ina kokarin kiyaye wa Fulani, na barki lafiya”..
Nan Yarima Hakim ya wuce Fada dan ya gaida Maimartaba yana cikin tafiya yaji an ingijeshi, waiga war da zaiyi sai yaga Yarima Hamad yana yi mashi wani kallo…
“Hamad ina wuni? “Ban ganshi ba, da ban wuni ba da ka ganni? “Uhmm, abunda Hakim yace ma Hamad kenan ya wuce ya barshi tsaye..
Aiko Hamad ya dunga masifa, dan ba haka yaso ba, ya so Hakim ya biye mashi..
Yarima Hakim yana zuwa fada, ya mike gaisawa wajen sarki, sannan fadawa suka mike mashi gaisuwa cikin mutuntawa, domin suna jin dadi hudɗarsu da sarkin nasu mai jiran gado..
“Gimbiya, wallahi raina ya baci, sai na kashe Hakim”..
“Kai Hamad wai sai yaushe zaka gane kashe Hakim sai anbi a sannu, eye? Dan ba abu bane mai sauki ba”..
“Wani abi a sannu ni ki barni na dauke kanshi da wuka a gaban uban kowa”..
“Kana san wahalar da mukayi a baya ta zama a banza? Ko kuma kana san na haukace? “..
“To Gimbiya ni na gaji da ganin Hakim cikin masarautarnan, wallahi na tsaneshi, yanzun haka yana fada fa”..
“Duk da ka tsaneshi hakuri zakayi mu kasheshi a sannu,,dan idan ka kashe Hakim gaban mutane kai ma kashe ka za’ayi Hamad gaban kowa, kaga kenan mulki zai tashi daga hannunmu ya koma wajen Kilishi dan Humad kawai za’aba mulki, ina bani fatan ganin wannan bakar rana”..
“Dan haka kabar komai a hannuna Hamad, wannan maganar ta zamu ta karshe tsakaninmu”..
“To naji Gimbiya, ni na wuce, “ka biya shashen Kilishi ka gaidata, “to na barki lafiya”..
Haka Yarima Hamad ya fito shashen Gimbiya Zulaha ranshi bace, dan yaso ta bashi goyan bayan kashe Hakim, Amman ya fidda hannu kamar yanda ta bukata shi dai yana jiran mulki…
Bayan ya gaida Gimbiya Kilishi ya wucewarshi hidimar gabanshi, dan su da sake ganinshi sai hali kuma..
“Ranki yadaɗ’e Gimbiya Kilishi, Gimbiya Zulaha tana san magana da ke, tana bakin kofa, “Mariya je ki shigo da sakara shasha, “to angama Ranki yadaɗ’e”..
Nan Gimbiya Zulaha ta shigo bayan sun gama gaisawa su ka fara magana..
“Kin san mai ya kawo ni Kilishi? “Aa Gimbiya, “yauwa nazo naji ina aka tsaya wajen aikin Maimartaba tunda naga duk aikin da muke kanshi ba ta siri shima”..
“Ai wannan aiki ne mai sauki, dan ban dauki kashe Maimartaba wani aiki ba”..
“To shikenan, Amman duk da haka sai mun gyara shirin mu, “to Gimbiya insha Allah, “ni na wuce, sai sa safe”..
To fa kunji wata sabuwa kuma, Ashe harda maimartaba ake shirin aikawa barzahu, Allah ya kare zuciyoyinmu daga aikata aikin da na sani ko wani kallar ne Amin😞🙏🏻
_By Jameelah Jameey✍🏻_
*Share*
*Comment*
*Vote*
*Like*
*pls*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
+
17&18
Yau karfe biyu Gimbiya Hakima take da lectures sai da su Lantana suka ji kamar su fasa ihu…
“Lantana baki da hankali? Wai dan Allah har sai yaushe zakiyi hankali?ke duk yanda aka nuna maki baki gane sai kace mai kwakwalwar kifi”..
“Allah ya huci zuciyarki, wallahi akasi ne aka samu”..
“Akasi! Akasi kikace Lantan? to yau zan nuna maki ni Hakima ban yarda da wannan kalma mai suna akashi ba”..
“Allah ya taimakeki, Ina neman sausauci, insha Allah banzan sa….. Tas!! Kake ji Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana nuna ta da yatsa sannan ta fara cewa, “ke wata kallar kidahuma ce? Inba kina kidahuma ba daga goge riga saboda sakarci irin naki kinbi ki toya, ni dallah can tashi kibani waje tsohuwar banza”…
“Godiya nike Allah yaja da tsawanci kwana uwar marayu, nan Inna Lantana taja yan kafafunta ta tafi, tana hawaye saboda tunda take da Gimbiya Hakima bata taba yi mata wani abu da taji haushi kalar wanna, dan ko ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha Mari a wajen Gimbiya Hakima Amman yau taji haushin abun sosai..
“Azima, “Naam Allah ya taimakeki, “tashi ki sake goge man takalmin nan, dan nasan wacer mahaukaciyar hauka kawai tayi man”..
“Angama ranki yadaɗ’e, nan Azima ta sake goge ma Gimbiya Hakima takalmi, duk ba abunda takalmin yayi, Amman haka ta sake goge mata shi..
Gimbiya Hakima ba ta tashi tafiya makaranta ba sai karfe daya dai-dai gashi tana da dan nisa tsaka ninta da makaranta gashi lecture din karfe biyu gareta..
“Bala kayi sauri bansan na makara, “angama Gimbiya, haka Gimbiya haka ta kama azalzalar Bala yayi sauri, haka suka samu suka isa, karfe biyu saura suka yi parking a bakin depertiment dinsu..
Sauri sauri Gimbiya Hakima take saboda hango Yarima Hakim da tayi yana tafiya cikin natsuwa yana shirin shiga lecture..
Duk da tasan yana ganinta hakan bai yana Gimbiya Hakima sauri ba, ita acewarta sauri take, Amman Yarima Hakim gani yake kamar bata san taka kasa, dan da nan ranshi ya baci sosai Amman zai barta ta shiga dan shi kad’a yasan abunda zaiyi mata..
Gimbiya Hakima na shiga taje wajen Maryam ta zauna, gaisawa kawai suka yi Yarima Hakim ya shigo..
Kowa ya natsu ya maida hankalinshi waje Hakim, dan suna jin dadin koyawarshi, dan prof Hakim ba daga baya ba wajen iya lesson, dan haka shiyasa kowa ya kama kanshi ya naba’a dan ya samu abunda ya samu..
STORY CONTINUES BELOW

Baki daya hankalin Gimbiya Hakima yana kan lesson din da Hakim yake dan harga Allah taji dadin koyawarshi dan ba karamin ganewa take ba..
“Hey stand up yayi pointing ɗin Gimbiya Hakima, Amman sai tayi kamar ba da ita yake ba, dan ta lura Malamin nan yana da san raini ita kuma ba daukar raini zata yi ba…
“Ke! Ke wata kallar kidahuma ce? KO baki jin turanci? Babanki yayi asarar kudin registration, dallah can stand up idiot nonsense stupid girl”Mtssss! Ya tsaki tana mata kallar ƙama..
Haka Gimbiya Hakima ta mike ji take kamar ta tsiga kasa ta nitse dan kunya, dan ba karamin kunya taji ba ta yanda taga kowa a ajin ita yake kallo kamar wanda tayi sata…
Sai da Hakim yayi kusan minti ashirin sanan yayi time ɗin Hakima…
Duk tayi laushi ta gaji, Amman ta daure dan bata san yan ajin suga gazawarta..
Questions masu wahala Hakim ya fara jefo ma Gimbiya Hakima, Amman ga mamakinshi yaga tana bashi amsa, sai kawai yayi mata wani question nan ta kasa bashi nan yace mata…
“Get out of my class, nan Hakima ta tashi ta wuce tazo dai dai fita Hakim yace meet me in my office, classrest ka anshin man matrix number dinta ka kawo man office dina”.
“Ok sir, class captain yace, sannan ya cigaba da yi masu lecture, bayan ya gama ya Kama gabanshi..
Ita ko Gimbiya Hakima direct gida ta wuce ranta bace..
“Allah ya taimakeki, Allah yasa lafiya dan ban saba ganin uwargijiyata cikin
Wannan yana yin ba?”..
“Azima so nike na san waye shi, waye ubanshi a cikin Nigeria, da har zai ci man mutunci a cikin mutane Azima?”..
“Tabbas ya tabka babban kuskure, dan bai san dawa yake magana ba shiyasa da baiyi maki abunda ya san ranki zai baci ba ranki ya daɗ’e”….
“Kyale shi Azima, yanda yasa na zubda hawaye ta dalilin shi, shima sai na sashi zubda hawaye da idonshi, sai ya san ni *GIMBIYA HAKIMA* duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha”…
Haka dai su Lantana suka Kama fadanci sannan suka samu Gimbiya Hakima ta sauko daga dokin fushi, sannan suma hankalinshu ya kwanta haka har tayi bacci..
_________________________________
Hakim bayan ya koma gida wanka yayi yasa kayan shan iska ya tafi bayan gida domin shakatawa..
“Fulani,wai kinji abunda naji su Gimbiya Kilishi suna cewa, wai ko da bala’i sai sun kashe yaya Hakim”…
“Laaa nima Maryama wallahi nima naje rannan suna maganar randa na tafi shan iska ni daya banda ke Maryama, har Mino tace man wancen satin har magani Lanto ta kawo asa mashi abinci, wai yana ci zai mutu, ke wani abunma bai faduwa makircin da asirin da suke yi ma Yaya Hakim”…
“Kunga duk kuyi man shuru da wannan surutun naku na banza, koma maiye mufi karfinsu da Ayar Allah dan haka ku cigaba da neman tsarin Allah ba na mutun ba”..
“To shikenan Fulani Allah ya tsaremu, “Amin Maryama”..
“Dan Allah Kilishi dubarshi sai kace wani sarki, wannan idan aka bashi sarki shida uwarshi banzaye zasu maidamu cikin gidan nan, tun yanzun yana wannan mulkin Ina ga ya zama sarkin?”..
“Kyaleshi Gimbiya lokaci kawai nike jira, wallahi indan har lokaci yayi Hakim jama’ar zaria baki daya mantawa zasuyi da anyi wani mutun Hakim, duk san da suke yi mashi ko, ke harta wanann munafukan yan biyun kannan nashi sai na shafe da babun su, balle uwar tasu”…
“To wai yaushe wannan lokacin zaiyi Kilishi?”..
“Nan ba da dadewa ba, kedai kisa ido kiyi kallo, “shikenan Kilishi”..
Nan suka gama meeting dinsu na kullun, sannan suka tafi..
*Sudai su Gimbiya Kilishi basu da magana sai ta Hakim💁🏻♀️, laile ko suna da aiki wanann shi ake kira aikin burus inji tusa🙅🏻♀️..*
________________________
“Allah yaja da ran uwar marayu ga abinci nan yana jiranki”…
Kallon Bilkisu kawai tayi, sai ta shiga toilet ta zubo ruwa a roba ta kawo mata ta wanke hannunta..
Hakan na nufin yau bata san zuw parlour yin dinner dan haka shiyasa ta wanke hannunta, bayan ta gama wanke hannu, suka hada kayan suka kawo mata..
Ana cikin zuba mata Azima taji tace, “tsaya! Azima waya ce ku dafa man kus-kus?”..
“Allah ya ja da ra’n Gimbiya Hakima ai ba kus-kus kawai muka dafa maki ba, harda macaroni, sannan kuma ga coffee nan duk munyi maki”..
“Uhmmm!
Nan Azima ta zuba ma Gimbiya Hakima macaroni, nan suka zauna suna bata labari taci har ta gama ci, sanan suka kwashe kayan suka je suka wanke, sannan suka dawo Lantana da Bilkisu suna tausa, ita kuma Azima tana karanta mata novel har tayi bacci sannan suka wuce suma suka kwanta..
Yan wattpad bakuyi COMMENT why? 😢😢😢😢😢😢😢
_By Jameelah Jameey✍🏻_
*Share*
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Please*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
19&20
Washe gari bayan Lantana ta gama shiryawama Hakima littafan ta, saboda karatun da Gimbiyar ta fara na dare dan cikin week din nan zasu fara tests din su dan haka shiyasa ta fara karatun ta..
“Lantana! “Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki”..
“Maza kije kice ma Bala, ya fiddo mota yanzun dan ayi fixing din lecture yanzun nan, dan haka yayi maza ya fiddo mota, gani nan fitowa”…
“Allah ya kara maki jaraja angama, “Amin, nan Lantana ta tafi wajen Bala…
“Malam Bala, ka tashi lafiya? “Lafiya lau Lantana, ya aiki? ”Aiki da godiya, “To Allah ya bamu ladar, “amin”..
“Sako daga Gimbiya Hakima, “mai kuma nayi Lantana?”.
“Kwantar da hankalinka, ba abunda kayi, “Alhmdulh, kin san wallahi Lantana ban san abunda zai hadani da Gimbiya Hakima da girmanka da mutuncinka, amman Gimbiya Hakima sai ta taci maka mutunci cikin mutane”..
“Hakane gaskiya, Allah ya kara tsaremu daga cin mutuncin ta, “Amin Lantana, mai ita Gimbiya Hakima tace maki?”.
“Cewa tayi ka fiddo mota yanzun dan an maido masu da koyarwa yanzun da safen nan, shine tace ki fiddo mota ga tanan fitowa”..
“To shikenan, ai yanzun kuwa zan fiddo ta, “ni na wuce Bala na barma lafiya”..
Nan Lantana taje ta gayama Gimbiya Hakima an fiddo mota..
“To ni zan wuce Bilkisu yau ki san kuyi man dambun masara, ku samu zagole kusa a cikin dan yau da bakuwa zamu dawo kuma tana san dambu”…
“Angama uwargijiyarmu, Allah yabada sa’a, “Uhmmm, sannan ta gama gaban tana saurin dan yanzun seven thirty tayi gashi lecture din eight yayi fixed dinta, bayan basu da wata lecture sai two amman dan mugunta ya maidota eight…
“Bala kayi sauri, ban san na makara ka sani, dan haka kasan yanda zakayi kafin eight na ganin acikin lecture hall”..
“To Gimbiya uwar marayu, Gimbiya diyar sarki uwar sarki insha Allah”..
Nan Bala ya kama bankama mota wuta, Gimbiya Hakima sai da taji tsoron kalar gudun da Bala yake da ita cikin mota, to amman bata da choice ɗin hana shi, dan idan sukayi wasa kan titin to zatayi lating ne, kuma bata san wani abu yake hadata da Yarima Hakim, shiyasa tayi hakuri tana ganin rayuwarta a iska..
(Lol sun Gimbiya Hakima ashe dai ana tsoro, kike iskanci🙃)
Cikin ikon Allah, karfe eight dai-dai tayi ma Gimbiya Hakima cikin makaranta tana hango Yarima Hakim shima lokacin ya fito office din shi, dan haka tayi sauri ta shige warta ta zauna nan Maryam itama lokacin ta shigo ta zauna kusa da kawarta…
STORY CONTINUES BELOW

“Morning class,”Morning sir, “ok class listings attention, keep quite everbody, and get of a sit and sitdown pls, I said all of you keep quite”…
Yarima Hakim ya fada cikin fada, sakamokon hango Hakima da Maryam da yayi suna ta surutu hankalinsu kwace..
Ba su san da shigowarshi ba sai da suka ji yayi tsawa sannan suka juyo lokaci guda, nan take Gimbiya Hakima taji bata , jidadi ba, dan tasan yanzun zai wulakantasu..
“Maryam,wannana idiot ɗin kin san yanzun zai fidda mu waje dan kinsan bai da wayau, baki ga irin kallon da yake mana ba?”..
Ta fada ma Maryam a hankali dan bata yarda lips dinta suka motsaba ma ba, balle yace tayi laifi dan Hakima tana san chemistry bata san ta ringa losing ɗin lecture din shi, gashi ya iya koyarwa tana gane wa sosai..
“Mu boni Hakima gashi nan ya taho, “Uhmmm, abinda tace ma Maryam kenan, Ni kuwa nace yan mulkin sun taso kenan tun kan ya iso🥺.
“Hey you again? And you also? Kin biye ma wanann yarinyar zaki fara wasa da karatunki ko?”..
Yace ma Maryam daya ke ba anan ba ya santa, ya santa kawarsu Gimbiya Maryama ce..
“Yaya Hakim dan Allah kayi hakuri, wallahi bamuji shigowarka ba”..
“Saboda an koya maki jikkanci shiyasa baki ji shigowata ba”..
Ita dai Hakima inda suke bata kalla ba, tana dai jin cin kashin da Hakim yake yi mata cikin class kowa na jinsu amman bata kyalesu ba har ya fidda Maryam waje sai ji tayi yace, “lock at you, stupid girl kawai, kina jiran nace maki get out ne? Oyaaa get out of my class idiot..
Gimbiya Hakima tsayawa tayi kallonshi, tana mamakin yanda yake san wulakanta ta cikin mutane, amman daga yau ba zai sake ba tace cikin zuciyarta, ta hada bag dinta ta fita ta baimar class dinshi, ga shi harda Maryam yau ya kora balle tayi mata tutorials ɗin abinda ya kowa ya…
Bayan ya yi waje dasu Hakima ya cigaba da lecture din shi hankali kwance, dan shi ma kanshi yana mamakin yanda ya tsani yarinyar ce sosai, tunda yake bai taba tsanar wani mutun ba kamar ta, dan baya santa baya kaunarta ya tsaneta sosai…
“Hakima kin fito kenan? “Eh Maryam ba dole ba na fito, wallahi na tsani Hakim bani kaunar mai kaunarshi, ya gode ma Allah ni dalibarshi ce, shiyasa nike jure duk wani wulakancinshi amman wallahi Maryam banda na yau sai na rama”..
“Haba Hakima sau nawa zan gaya maki mai hakuri yana da riba? Kuma malaminkine duk kowa yasan yana wulakantaki amman hakuri zaki yi tunda keke nema wajenshi kinga dole mu ringa hakuri da malamanmu komai kuwa suka yi mana”..
“Maryam kinga ina sauraran wa’azinki ko? “Eh gaskiya kuma ina jin dadin ka, “to dan haka tashi mu tafi samu abunda zamuci dan ni ko breakfast banyi ba na fito”..
“Ok mu tafi nidai naci cake cikin mota, kafin na iso, “ai ni banyi wanna hausar ba ai da nasa Azima tayi mani cake, amman zansa tayi mani cake ko dan saboda da kallar wanann bakar lecture din tashi na kamaka rabona da bacci wallahi tun karfe biyun dare Maryam”..
“Gaskiya kina kokari Hakima, nan dai suka shiga restaurant suka samu abinci suka ci, bayan sun gama, Hakima tace aka wo mata chip exotic chivita na watermelon..
“Hakima mai zakiyi da chivita bayan nasan baki shan exotic ke kika fadamn da bakin ki kin fi san ayi maki juice nan take dan baki shan chemical?”.
“To yau ina bukatar sha, ji nayi kawai ya burgeni da naga wannan guy din yana sha, “to ai sai ki sha mu tashi mu tafi wata lecture din”..
“Aa ba yanzun zan sha shi ba, kiyi gaba gani nan tafe zan biya wajen Bala na bashi kudi ya samu abunda zaici dan shima baiyi breakfast ba muka taho”..
“Ok sai kin iso, ni na wuce amman dan Allah kiyi sauri kinsan bansan zama ni daya sai naji duk ba dadi”..
“Ok yanzun ko zan taho ai ba wani ajima zanyi ba”..
Nan Maryam ta wuce lecture hall, ita kuma Gimbiya Hakima ta kama hanyar office ɗin Yarima Hakim, tana zuwa tayi nocking..
“Yes, ya cigaba da aikin papers din gabanshi dan yayi ma level 2 test, kuma yasa ma Aliyu ne yazo..
Nan Gimbiya Hakima ta shiga office din cikin takama da nuna ita watace dan harda taunar chigum take, bata san shi Hakim baya san yaga mace na tauna chigum sai yaji ya shiga cikin wani hali mai wuyar fassara..
Tashi yayi ya nuna mata kofar dan ko magana kasawa yayi tunda yaga tana cin chigum take felling dinshi ya taso more felling ma, shiyasa ya kasa magana dan idan yace zaiyi magana numfashinshi na iya daukewa shidai kawai ya narka mata narkarkun idanunan nashi da suka tashi daga fari suka koma ja dan tsananin azaba…
Sai da tayi kusan three minutes tana mashi kallon tsana dan ji take kamar ta zunduma mashi wuka a ciki ya mutu ta huta da ganinshi..
Kawai Hakim ji yayi an watsa mashi abu mai sanyi ai take ya dawo cikin natsuwarshi, tsaya wa yayi yana kallon abunda Hakima tayi mashi, new gizina shaddarshi da yafara sawa yau itace tayi ma haka gata fara ce sosai amman ta watsa mashi Jan abu a jikinta..
“This is a last warnings ɗin da zai sake yi maka Hakim, ka fita a rayuwa hakanan karka sake shigarman rayuwa ni na fi karfin a wulakantani cikin mutane, kuma nace maka da man duk wanda yaci tuwo da Hakima miya yasha useless kawai ta kai”mtssssss! .
Nan Gimbiya Hakima tayi tafiyarta class bayan ta gama yin abunda tayi niya…
😱😱😱😱😱Anya Team Hakima ta ɗauko hanyar fullewa kuwa bata ɗauko wutar dafa kaitaba🤭🥺.
Yarima Hakim kasa komai yayi, “wannan idiot girl ɗin wai yar gidan uban wa ye, waye ubanta cikin zaria bama zaria ba duka kaduna da kewayanta, da ko zanga ubanki a gaban idonki zansa a yanke mai yatsan hannu dan dole na hukuntasu saboda basu baki tarbiya ba Hakima”..
Abunda Hakim yace kenan ya tuna da papers ɗin students ɗinshi Allah ma yaso basu jike ba, nan ya tartarasu a jiye ya kira Aliyu waya yazo ya daukeshi ya taho mashi da wasu kaya…
“Hakima ina kika je? “Lafiya wanann question ɗin ka bayan kinsan nace maki zan ba ma Bala kudin abinci”..
“Hakima ba wajen Bala kika je ba, dan yanzun na ba Bala kudin abinci dan yazo neman ki bashi izini yana san ya koma gida yace abinci har ya kowa maki naki inkina bukata”..
“To uwata naji ba wajen Bala naje ba, shi kenan ko? “Wajen prof Hakim kika je ko Hakima? “Eh wajenshi naje wani abu?”.
“Haba Hakima maiyasa kika biyema zuciya eyeh? Hakima ya kamata ki sani ba komai ake biyema zuciya ba dan sai kazo kayi da na sani daga baya, kin ko san ki waye Hakim a garin nan ba kuwa Hakima? “…
“Da kata dallah Maryam bani bukatar nasan waye wani Hakim can, NI KINSAN KO WACECE HAKIMA A GARIN KANO?..
“Duk da haka ya kamata kiringa ragi ko yaya ne Hakima, ina san mutun mai sausauci da ragi Hakima, yanzun wanann Balan baki daya baki raga mashi ko kadan kuma shima mutun ne kamar ke yana bukatar hutu, haba Kawayata pls ki dan ringa rige”..
“Naji, amman indan Hakim yayi mani wallahi sai na rama, “to wai maikika yi ma Hakim din? “..
“Maifa zanyi mashi tunda ban iya dambe zanyi dashi ba? Kawai chivita naje na watsa mashi a jikin wannan tsunman shaddar tashi daya sa yau”..
“Yanzun gizinarshi kika watsama chivita Hakima? “Kwarai kuwa Maryam take dubu dari shidda? Ni shadda inba ta kai one million ba ban dauke ta shadda ba ke harda atamfa dasu laces dan haka take note”..
“Uhmm gaskiya ne Hakima Allah yasa mudace, “Amin dai Maryam, ya naga har yanzun bai zo ba? “Eh ba wani abu yayi ba area of concentrate ya bada kawai”..
“Ok shikenan, tashi mu tafi gida, dan nasa su Lantana sunyi maki dambu fa, “woow like uh Hakima gaskiya naji dadi sosai”..
Yan wattpad na fara ganin comment naji dadi kuma
_By jameelah jameey ✍🏻_
#JameelarhSadiq@wattpad
Share#
comment#
Vote#
Like#
Please#👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
+
21&22
“Hakim mai yasa mai kayan haka?”.
“Hmmm! Aliyu kai dai kawai ni ban ma san ya zance maka ba, amman wallahi Aliyu na tsaneta”..
“Ka tsaneta? Wacece mai kuma ya hadaku? Kai da baka damu da mutane ba”..
“Ban qaunarta I hate her wallahi, Hmmm Ammn, “gaya man wai wacece Hakim?”.
“Hakima wai ita sunan ta, bani san ta wallahi Aliyu, ko ganinta bani san yi”..
Nan dai Hakim ya gaya ma Aliyu yanda sukayi da Hakima..
“Bala’i ko wacece wannan bata san ko kai waye ba shiya take yi maka haka, dan haka ka nuna mata kawace ajinta ta ko ina”…
“Kyaleta Aliyu zanyi maganinta ai tace duk wanda yaci tuwo da ita miya ya sha, to zata gane kurenta bani rigar nan nasa”..
Nan Hakim ya sa rigar da Aliyu ya kawo mashi sannan suka wuce gida…
“Sannu da zuwa Maryam yau dai gaki temporary house ɗin Hakima”..
“Gaskiya ko gani gidan Hakima, amman ita Hakima ko maganar zuwa namu gidan bata yi”..
“Karki damu kisa a ranki Hakima tazo gidanku har angama, “to Allah yasa ita Hakima da gaske take, “da ma gaske take”..
“Lantana! “Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki, “sai nace kuke wo ma bakuwata abin sha da abinci?”.
“Muna neman sausaucin uwargijiyarmu , “mtsss! Wai ku dan Allah wasu kalar jahilai ne mararsa gwalkwalwa baki daya har yanzun baku da lissafi, komai sai kunsa mutun magana”..
“Allah ya huci zuciyarki Gimbiya Hakima yar’sarkin kano jikar sarkin yola, muna neman sausaucin Gimbiya Hakima uwar adalci, uwar marayun kano baki dayan ta”..
“Inba kuna banzaye ba… “Ya isa haka Hakima dan Allah, Maryam ta fada ta mai daga ma Hakima hannu ranta a bace dan taji haushin abunda Hakima tayi masu Lantana gasu sun fara manyanta.
“Mama tashi ki dauko mana abinci ki kawo mana cikin daki, “to godiya nike ranki yadaɗ’e”..
“Hakima mu shiga ciki mana, “maiyasa kika yi man haka a gaban bayi na? ”.
“Shi ne nace mu shiga daga ciki magana zamuyi, “Uhmmm”..
Nan su Lantana suka kawo ma Gimbiya Hakima abinci..
STORY CONTINUES BELOW

“Allah ya taimakeki, aci lafiya uwargijiyarmu Gimbiya Hakima uwar masu adalci”..
“Dillah can tashi ki ban waje, zaki cika man kunne da surutun banza, kuma wa kika ajiye ya zuba abinci?”.
“Ina neman afuwarki, nan Lantana ta zuba masu abinci sannan ta wuce jiki ba dadi ..
“Hakima daman ke yar Sarki ce? Shiyasa kike yima prof Hakim abunda kika gadama, “Uhmmm! Ai ba sai na gaya maki ba Maryam, ni ban damu da ansa ko ni yar gidan waye ba”..
“To shi Hakim din kin san ko waye? “Dakata Maryam indan muna tare ban san kina yi man maganar wannan useless boy din, dan na tsaneshi ban kaunarshi balle har na tsaya naji shi dan gidan uban waye bani bukatar wannnan”..
“To shikenan Hakima, amman dan Allah ki daure ki ringa hakuri da wanann bayin Allah, wallahi Hakima su biyun sun haifi kamar mu har uku may be, gudarce dai bata isa haihuwar ki ba”..
“Kinga bai kamata ba ace kina yi masu kallar wannan zagin ba, tunda iyayen wasu ne, kinga bai dace ba ina neman masu alfarma kawata”..
“Ai laifin su ne Maryam, kinga ina yi ma Bala drive na haka? “Aa gaskiya ba kamar su ba, “yauwa kingansu nan baki ɗaya basu da tunani balle hankali kuma, komai sai ance masu yi sannan zasu yi wallahi na gaji kawai zan ma Baffah magana a chanza man wasu bayin dan ni su kayi man sai nayi masu”..
“Nidai bance kice a chanza maki wasu ba, a shawara ta amman kidai rage yi masu wani abun please mana”..
“Tom naji, yanzun dai kici abinci, “tom mudai ci tare, “Uhmmmm”..
Nan dai suka ci abinci, nan Maryam tayi ma Gimbiya Hakima wuni sannan ta wuce gida, itama tana jirin zuwan Hakima gidan su..
_______________________________
“Ranki yadaɗ’e, Gimbiya Kilishi ga wannan maganin nan inji Boko yace a tabbatar da an barbadashi bisa gadon Yarima Hakim yana kwanciya zai samu ciwon mutuwar rabin jiki, kinga dole ya rage wanann bakar sallahr da yake yi har cikin dare sai a turo aljanu su ida nasu aikin”…
Hahhahhahahaha! “Mariya gaskiya aikin ki yana kyau sosai, yanzun wacece ki gyara shashen Hakim? Dan wanann aiki ne mai sauki boka ya bada”…
“Eh Hasiya tana cikin masu gyara ma Hakim shashe, “Hasiya? da kyau kice tamu mace take mashi, “eh ranki yadaɗ’e”..
“To Mariya yanzun aiki ya rage naki, “angama Amaryar Sarki kuma uwar sarkin gaba, na barki lafiya”…
“Fulani sannu da hutawa, “yauwa Hakim har an dawo kenan? “Allah ya yarda, “Sadiya tashi ki dauko mashi abinci, “to Fulani”..
“Fulani nifa a koshe nike, “ai nasani Hakim, ai kai kullun a koshe kake, kai dai har yanzun baka san cin abinci ko Hakim?”.
“Aa Fulani ina cin abinci sosai ma, “Allah yasa da gaske kake, “yaya Hakim ga abincin nan”..
Kallonta kawai Hakim yayi Gimbiya Sadiya ta tashi ta barma masu waje, dan daman ita Gimbiya Maryama bata fito ba tana dakin ta..
“Kaci abincin ko sai raina ya ɓaci? “to Fulani yanzun zanci, nidai Fulani ina mamakin a ina Hamad ya koya wanann hali”..
“Mai kuma Hamad din ya sake yi? “Wallahi ina hanyar dawowa naganshi shida wata yarinya cikin mota sun shiga wani hotel”..
“Allah ya shirya shi, sai ka cigaba da neman ma dan’uwanka shiryar Allah, kuma ina sake maimai ta maka dole sai kayi hakuri dan kaine Babba, duk da dan watan nine tsakaninku ya zam dole kayi hakuri da yan’uwanka tunda jininka ne”..
“Insha Allah Fulani, nan Hakim ya cigaba da cin abincin shi yana mamakin halin kanin nashi, dan daman tuni ya lura da Hamad yana neman mata…
“Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, “Lanto da magana a bikin ki, gaya man ko Hakim ya mutu ne?”.
“Ko ɗaya Gimbiya,Hakim ba mutuwa yayi ba, amman kinga wanann magani to shine ajalin Hakim, dan yanzun daga Niger nike wajen boka yanka ɗaya”..
“Maiyace ayi dashi maganin? “Eh cewa yayi kisa ma Hakim shi cikin shayi da hannunki sannan sai kije ki bashi yasha to yana sha zai mutu”…
“Taya haka zata faru Lanto, bayan kinsan Hakim bai yarda dani ba, balle na bashi abu ya sha?”.
“Abu mai sauki ne Gimbiya, sai ki hada mashi ki kai mai, kice kinji ance bai lafiya kwana biyu, daman kinga ya bar zuwa gaisheki, kinga ba yanda za’ayi yake shan shayin da kika kawo mashi da hannunki”…
“Hakane fa Lanto bari na tashi naje na hada mashi kinga dare nayi”..
“Na manta yace sai kin baryin sallahr asuba kuma, “na baryin sallahr asuba Lanto? bayan ya hanani yin sallahr la’asar yanzun ya dawo yace ta asuba”…
“To ranki yadaɗ’e duka na sati nawane? ai kedai ba bukatarki kike san ta biya ba? ai nasa komai zaki iya yi Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha”..
“Hakane Lanto, tashi muje muyi mashi sanyin nan, dan da zafi-zafi kan buga karfe”…
“Kina jina ko Hasiya? “Eh Mariya, “anshi wannan maganin inji Gimbiya Kilishi ki tabbarta da kin barba ba ɗashi a bisa gadon Yarima Hakim”..
“Wanann ai kinsan aiki ne mai sauki a wajena, “ai shiyasa Gimbiya Kilishi tace ke take so kiyi mata wannan aikin dan tasan baki da wasa wajen kallar wanann aikin”..
“To kije kice mata ni Hasiya nace aikin ta anyi angama, to ni na wuce ki huta lafiya”..
Nan take Hasiya ta barbadema Yarima Hakim magani bisa gado sannan ta cigaba da hidimar gabanta..
Gimbiya Zulaha ta gama hada ma Hakim shayi ta juye magani, sannan itama ta dauki hanyar shashen Yarima Hakim..
*ASSALAMA ALAIKUN MASOYANA INA GODIYA DA KULAWARKU GARENI DUKA KWANA BIYU NAYI BAN HAU ONLINE BA AMMAN NAGA MESSAGE DA KIRA NAJI DADI SOSAI😍*
*ZANYI MAKU POSTING YAU INSHA ALLAH, DAGA YAU ZAMU HUTA TSAWON SATI ƊAYA NI KUMA ZANYI KOKARI KAFIN SATI NA GAMA TYPING DIN GIMBIYA HAKIMA BAKI DAYA. DA MUN DAWO HUTU SAI KAWAI POSTING KUNGA BAMU DA WATA DAMUWA TA TYPING 😍*
*fatan kun fahimceni my fans😍, inayinku over and over❤️💯*
_By jameelah jameey ✍🏻_
*#JameelarhSadiq*@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’+
*ALHMDULH AM BACK, NAGODE SOSAI DA SOSAI MASOYANA NAGA ADDU’OI DA KUKAYI MAN ALHMDULH JIKI YAYI SAUKI SOSAI, DAN MU CIGABA DA GASHI SUYA SAI RANAR SALLAH💃🏼💃🏼🥰*
23&24
“Ranka yadaɗ’e Gimbiya Zulaha ta kawo maka ziyara, “ziyara yanzun cikin daren nan? “Eh tana bakin kofa ma tana jiran ayi mata iso, “je kice mata ta shigo”…
“Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, Yarima Hakim yace ki shigo”..
Nan Gimbiya Zulaha ta shigo, Lanto na biye da butun shayi a bayanta..
“Allah ya kara maki lafiya yau kice da kanki wajen ɗa’nki? “Ba dole ba Hakim nayi kusan sati uku ban saka a idona ba, ko gaisuwarma mu bar cin arzikinta”..
“Ba haka bane Gimbiya, aiki ne yayi man yawa, kin san zaman banza ba aikin yi bane sai sakaran namiji shine zai kwanta yace komai sai dai ayi mashi, dan yana ɗan wani she kiga basu komai sai bin matan banza da sheye sheye”…
Gimbiya Zulaha taji haushin maganar da Hakim ya gaya mata, dan tasan da Hamad Hakim yake, magana ce ya gaya mata a takaice, Amman sai ta nuna bata gane da ita yake ba, ita dai burin ta yasha tea, dan yana sha ya gama aiki..
“Aiko dai Hakim ai kasan babu maraya sai raigo, Allah dai yayi maku albarka baki dayanku kai da kannanka”..
“Amin Gimbiya”…
“Da man Hakim jina nayi ance baka ji dadi ba kwana biyu shiyasa nace bari dai nima nazo duba lafiyar sarki mai jiran gado”..
“Godiya nike Gimbiya, Amman ni lafiya ta lau gaskiya, Wanda suka gaya maki basu fadi maki dai-dai ba”..
“Tabbas, dan gashi na gani da idona, ga shayi nan nayi maka da hannuna dan nasan kana san shayi sosai”..
“Nagode, nan Hakim ya ansa shayi ya aje gefe, ya cigaba da marking din papers dinshi, Gimbiya Zulaha na san tace mashi ya zuba yasha Amman bataga fuskar haka ba sai da tayi ta maza sannan tace..
“Hakim ai ya kamata kasha ka jike makoshinka, da man naga duk ka gaji da alamu”..
“Zansha Gimbiya amman sai zan kwanta bacci, dan bani shan wani Abu in ina aiki”..
“To shikenan na barka lafiya Hakim, “toh Gimbiya nagode sosai sai da safe”..
Haka Gimbiya Zulaha ta fito wajen Hakim ranta bace dan ya bata mata aiki, tunda boka cewa yayi ya sha gabanta sannan maganin zaiyi aiki..
Shiko Hakim Gimbiya Zulaha na fita ya tashi yayi wanka yasa aka fitar mashi da Tea din da Gimbiya Zulaha ta kawo mashi,sannan yasa aka chanza mashi new bedsheet yayi addu’a ya kwantaciyarshi, cikin dare zai tashi yayi sallahr shi..
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari da wuri Hakim ya shirya ya wucewarshi fada, dan yau weekend…
”Allah ya ja da ran maimartaba”..
“maimartaba sarki yana ansawa Yarima mai jiran gado”..
“Allah ya karamaka lafiya na samaika lafiya? “Lafiya lau Hakim ya aiki? “Alhmdulh, “Allah yayi maku albarka baki daya “Amin ya haiyu”..
Nan ya zauna, su kuma fadawa suka cigaba da fadancinsu, Hakim bai bar fada ba sai karfe hudu, dan zasu dan fita shida Aliyu…
Nan ya shirya suka wuce warsu wani join inda ake sha iska..
__________________________________
Masha Allah wata fine girl ce nagani tana shiryawa, fara ce tas masha Allah, ga dara-daren idanunta wanda lashes tayi lub bisa rufar idanun sai kayi tunanin fixed dinsu tayi, girarta tasha gyara kamar anzanata saboda yawanta ga kuma shape da tayi ga kuma uwa uba brownrish ne a girar ita ba baki kiranba ita ba brown ba, shiyasa indan ka kyaleta sai kayi tunani jagira tayi, hancinta yana da tsawo amman ba sosai ba sai dai ace medium shi ba karami ba kuma shi ba mai tsawo da yawa ba, bakin ta dai dai dashi shine Wanda ake kira round mouth ga pinklips dinta masha Allah dai-dai kiss, fuskarta round face ce Amman ba sosai ba round din..
Tana da breast sosai dan idan kaga breast dinta bazakayi tunanin na yar ‘shekara 19 bace, ga uwa uba hips dinta ga shape coca-cola shape gareta, masha Allah gaskiya *GIMBIYA HAKIMA* ba daga baya ba wajen kyau ba..
Bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa, ta dauke post dinta da wayarta kirar IPHONE, iphone 11 pro ce, nan ta dauko agogonta ta manna a hannu, yau Gimbiya wane dan bala’in lace tasa black color ba karamin kyau yayi mata ba, sannan ta dauko gyale da takalmi purple colar ta daurama laces din, sannan ta jefa sweet a bakinta ta sannan ta fito parlour…
“Allah ya kiyaye hanya uwargijiyarmu, hannu kawai Gimbiya Hakima ta daga masu sannan ta fita waje wajen Bala ta amshi key din mota da hannunta dan yau Gimbiya Hakima da kanta dake bukatar yin drive dan sha’katawa zataje..
Nan ta dauki hanyar join itama..
______________________________
“Hakim kasan abunda ke ban mamaki a cikin gida?”.
“Aa Aliyu sai ka fada, “Hmm! Lamarin Hamad wallahi Hakim ya fara bani tsoro wallahi baki daya Hamad ya bata rayuwarshi da kanshi”…
“Kaga shine neman mata, shine shaye-shaye, baki daya yanzun baida aiki sai na neman mata”..
“Uhmm, Aliyu ya zanyi mashi? Nace ya daina? yaron da baki daya baya matuntani, how comes zani cema shi ya daina ya daina Aliyu?”.
“No way gaskiya Hakim ni shiyasa na fi shiri da Humad shi ba ruwanshi, bai yarda ya baiyema Gimbiya Kilishi ba”..
“Eh ai daman Humad da Hamad ba halinsu daya ba, shi Hamad baida hankali shiyasa nike yi mashi uzuri, kuma ina guje mashi ranar da Maimartaba zai gane yana wanna harka wallahi daga shi har Gimbiya Zulaha tausayi suke ba, Allah dai ya kauda tsotsayi, “Amin ya Allah”…
“Masha Allah, Hakim kalli wata beb nan na tana tahowa wallahi ta hadu, “kai dai ka bani da kallon matan tsiya, dan haka kyaleni ba wata macen da zani kalla, yana fada yana yarda bawon ayaba, nan ko Gimbiya Hakima ta taka bawon bananar nan take sintsi ya kwashe ta ta fadi kasa…
“Inalillahi na boni, “sannu baiwar Allah inji Aliyu, dan shi Hakim tun faduwarta tana juyowa da shirin bata hakuri yaga Hakima ce ya kyale ta ya cigaba da cin ayabarshi hankali kwance..
“Sannu yi hakuri”.
“Dallah can malan matsa kabani guri tunda ba kai kayi man ba, zaka tsaya yi man wata maganar gulma”..
“Aa Allah ya huci zuciyarki, dole mu baki hakuri tunda mumaka yi maki laifi”..
Tun ihun da Hakima tayi ma Aliyu ta zanyo attention din mutanan wajen sun tsaya suna kallon ikon mai sama Allah…
“Kai har ka isa ka jefoman banana ka kadani cikin mutune how dare you? Ko dan kace kana sona last week nace nafi karfinka shiyasa kace bari kazo nan tunda kasan nan ne wajen zuwa ka bani kunya cikin mutane to karya ne, ka sani dai Hakima na fi karfenka banza stupid man kawai dakai…
Aiko nan mutane Suka kama yan maganganu suna mamaki kamar yarima Hakim wanann yarinyar take yi ma wanna abun cikin mutane..
Yarima Hakim rasa abunda zai cema Hakima yayi, dan haka ya mike ya wucewarshi ranshi bace, nan fa yaƙara sama mutane confused dan wasu sun yarda wasu ko suna confused sosai..
Nan itama Hakima ta juyowarta ta koma gida…
_By jameelah jameey✍🏻_
#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
+
25&26
“Hakim gaskiya wannan Yarinya ta cika marar kunya, amman abun Mamaki shine baka yi mata komai ba”..
Uhmmm! “Aliyu itace wanda na gaya maka ta watsaman chivita a office”..
“Da man wannan yarinyar kake gaya man? Gaskiya batada mutunci ko daya bata san rajarar mutane ba”.
“Hakima kenan, Aliyu wallahi yarinyar na tsane ta sosai, “Aa Hakim ka daina cewa ka tsane ta, domin karda tsanar ta juya soyayya”..
“What? Aliyu maikake cewa? Kana nufin ni Hakim zani so Hakima? To har abada wallahi ko bcox I hate her, baki daya behavior and character ɗunta bai yi ma ni ba, kai idan zanga wani yace yana son Hakima sai nayi iyakar koƙarina na gaya man bata da hali”..
“Haba Hakim! Ya kake yin haka ne dan baka santa sai ka hana kowa aurenta? “Eh domin ban san tayi farin ciki a rayuwarta..
“That Mean! Kaine kenan zaka zama mijin ta kenan? “Wallahi Aliyu da ba dan kai bane da bansan abun zanyi maka ba, taya zanso Hakima”.?
“Amman Hakim! “Dallah Aliyu, please! can’t uh keep quite or No”.?
“Shikenan nayi shiru kamar yanda ka bukata, Allah ya bamu sa’a Hakim, amman wallahi ka rage tsanar Hakima a zuciyarka, in my advance kenan”.
“ok i’ll try my best “.
_____________________________
Tunda Hakima ta fito daga Join bata tsaya ko ina ba sai gidan su Maryam nan take gaya mata yanda su kayi da Hakim..
“Wai Hakima gaskiya baki da sauki, amman kiyayi prof Hakim fa, kinga gobe zamuyi test din shi, ga kuma next week exams dan haka ki ajiye makamanki Gimbiya Hakima yar sarkin Kano, ai haka naji bayinki suna cewa ko”.?
“Mtssssssss!!! Wallahi keki ka damu da test dinshi nidai iyaka mutun ya kadani indai nasan nace banyi failure ba, wallahi sai na shiga na fita cikin ABU Zaria an fiddo man hakina”..
“Hakane kuma, balle ma nasan baya kadaki, saboda yanada kirki”..
“Wai ke Maryam mai yasa kullun maganarki bata wuce, Hakim yana da mutunci? “To dan yana dashi ai shiyasa na fadi, dan wallahi ya fiki mutunci da tausayi ma, nan ne kawai bakuyi marching ba wallahi Hakima”..
“Godema Allah a cikin gidan ku kika yi man wanann maganar, “inba cikin gidan mu nayi maki ba mai zaki yi man”.?
“Wallahi sai nasa anyi maki hukunci mai tsanani, sai kinyi wata goma gidan horo, horon ma mai tsanani, dan naga baki d’aya baki sona, Hakim kike so ai sai kije ki gaya mashi bai sai kin dunga man haka ba”.
“Hmm! Shikenan nayi shiru, wannan tsanar is too much gaskiya Hakima very much ma, taya zakiyi ma dan uwanki musulmi irin wanann tsanar”.?
“Nidai!! I tell you, dan haka No Need to touch my friend, “ok as with wish Hakima” ..
“Ni zan wuce gida mangrid tayi, sai mu hadu test tomorrow by the graces of God, “ok byee thank for visit me, “don’t wrong, thank uh too”..
Nan Hakima ta wuce gida, wanka kawai tayi da sallah ta zauna ta cigaba da karatunta, dan yanzun bata da lokacin kowa sai na karatunta tayi missing din gida, amman tayi promise bata ko mawa wani weekend sai dai taje holiday..
Bayan ta gama karatu tayi alwallahr bacci da addu’a ta kwanta bacci da wuri dan eight suke da test din gobe ..
_______________________________
“Gaskiya Kilishi Ina mamakin yanda Hakim yake bata mana aikin mu, ko wane aiki mukayi mashi bai kamashi abun da Mamaki”..
“Ni abunda nace Gimbiya mai zai hana mu sake boka, “mu sake boka fa Kilishi? “Eh mana, tunda shi yanka daya aikinshi yaki yi sai mu sake wani mu gamu, ba mu san ida za’a dace ba”..
“Kin kawo shawara mai kyau kuwa Kilishi, amman wani hanzari ba gudu ba, “maikenan”.?
“Ni ina gani harta bayi wanda muke ba aiki sai mun sake wasu amman ya kika ce? “Eh to hakane mu fara chanza boka dai”..
“To zanyi ma Lanto magana sai ta chanza mana sabon boka, dan Lanto ba bakon da bata sani ba”..
“To hakan ma yayi, ni zan wuce na barki lafiya, “mun kwana lafiya”..
“Kaga Aliyu nifa na fara jin bacci, tunda muka dawo duk ka bi ka damai ni da shurutunka, har yanzun ban saurari mai amfani ba”..
“Yanzun maganar Hakimar ce bata da amfani? Wallahi serious Hakim inasan naga ka auri Hakima dan kunyi marching”..
“Kaga ai shiyasa nace maka baka da abun fadi mai amfani dan haka sai da safe, karda nasa ayi man waje da kai”..
“Mai yayi zafi Allah ya tashe mu lafiya, “Uhmmm, Hakim yace sannan ya shiga toilet yayi alwallah ya fara sallolinshi da duk abunda ya saba yi kafin ya kwanta bacci…
washe gari bayan ya dawo daga massallaci wanka yayi ya shirya cikin shampoo shadda brown ba Karamin kyau Hakim yayi ba, sannan ya dauki hanyar makaranta saboda test..
______________________________
“Gaskiya Hakima kin burgeni yau da kika shigo da wuri, “kinji ki da wata kallar magana daman can da wuri nike zuwa school, wancan marar mutuncin ne shine yake ganin bani zuwa cikin lokaci”…
“Hmmm!! Nidai Hakima kina bani Mamaki wallahi kedai Hakim bai yin dai dai a wajen ki, “Hmm”..
Nan Hakim ya shigo yayi masu test sannan ya kama gabanshi…
_Dan Allah kuyi manage da wanann har yanzun banji dadin jikinta wallahi hakuri kawai Nike nake yi maku typing 😰_
_By Jameelah Jameey✍🏻_
share and comment and vote and Like please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
27&28
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ba bu wata jutuwa a tsakanin Hakima da Hakim, dan baki dayansu sunyima juna tsana maitsanani wanda suna iya kashe junansu idan suka biye ma zuciyoyinsu..
”'(Allah ya rabamu da akin da nasani Amin)
”’
Yau su Gimbiya Hakima zasu fara exams, dan haka tunda safe ta shiriya duk da ba eight garasu ba Amman tana san fita da wuri dan ta kara duba inda take confused din bai zauna ba sosai, shiyasa..
“Lantana! Kinsan bansan kuna bataman lokaci Amman gashi har bakwai ta wuce baku gama yin wani breakfast ba, dan haka ni na wuce kunci abunku”..
“Allah ya taimakeki, ko akawo maki a makarantar indan sun gama? kinsan abasan mutun ya fita bai karya kumullo ba”.
“Aa Lantana karku damu ba sai kun wahalar da kankuba, zani samu abunda naci, kudai kusamu kaci ni na wuce kinyi man add’ua”..
“Ubangiji Allah ya baki nasarar wannan jarabawa uwargijiyarmu, “Amin Lantana nagode”..
Nan Gimbiya Hakima ta tafi tabar Lantana da mamakin da kusan kwana biyu suke ganin chanjin Halin Gimbiyar tasu..
“Saurin maikuke Bilkisu? “Harkin tambayimu saurin mai muke Lantana, bayan kinsan Gimbiya Hakima muke hadama abinci karya kumollo”..
“To ai ita uwarjiyarmu ta wuce boko yanzun-yanzun man”..
“Kai haba Dan Allah Inna Lantana da gaske kike? “Azima kintaba jin anyi wasa da sunan Gimbiya Hakima”.?
“Aa gaskiya, Amman abun ne yana bani tsoro fa”..
“Tsoro! “
Su’duka biyu suka hada baki wajen yin maganar at wants, dan sun tsorata da suka ji Azima tace tana jin tsoro bama mamaki ba..
“Wani kalar tsoro Azima? “Eh Ba’ba Bilkisu tsoro, gudu nike karda musake jiki muna murna Gimbiya Hakima ta chanza Hali baki ɗay, tana gama jarabawa tadawo mana da halinta na farko”..
“Maiyasa kika ce haka”.?
“Inna Lantana kin fini sanin halin Gimbiya Hakima nisa ba kusa ba, saboda tun tana yarinya kuke yi mata bauta,Amman ni daga baya nazo”…
“Dan haka ba Gimbiya Hakima kawai ba mutane da dama suna chanza hali saboda zasu fara jarabawa Dan Allah ya basu nasara, wani da bai sallah kan lokaci da zaran zaya fara jarabawa daga ladan sai shi a jam’in sallah, abubuwa da dama ma wanda dan Ina jin yaunwa da sai na tsaya na gaya maku shi”.
STORY CONTINUES BELOW

“Tab! Mudai insha Allah ta chanza kenan, dan har munfara kumatu da Gimbiya Hakima ta chanza kwana biyu”..
“Kai Ba’ba Bilkisu abun harda zagi kuma? wai mun fara kumatu”..
“Uhmm! Nima haka na lura Allah Bilkisu munfara kiba ba kamar da ba kamar a hure”..
“Kudai ku taho muje muba cikin mu hakinshi,mu dawo mufara girkin rana kuma, “to mu tafi”…
___________________________________
“Hakima gaskiya exams din Dr Moha tayi masifar dadi Allah yasa shima ta prof Hakim tayi dadi kamar ta Dr Moha ko ma tafishi tashi dadi”..
Mtsssssss! “Kinji matsalarki wallahi Maryam ina ruwanki dadi tunda kiyi karatu, ko ta Dr Moha bata yi ma wanda basuyi karatu dadi ba, kuma tayi ma wanda sukayi karatu dadi, ai haka abun yake uwar yantsoro, je kiyi karatu sosai sannan ki fidda ma ranki tsoron course din Hakim ina kana tsoron abun baka cin nasara kanshi dan haka TAKE NOTE kawata”.
“Hakane gaskiya Gimbiya kawata, ni na wuce gida zan shiga gidan sarkin zauzau gun kawayena, ko zaki ki taho mu wuce”.?
“Aa bani wani zuwa inda ba’asan ni ba, “ai sai ingaya masu kema yar’sarkin Kano ce, “dakata dan Allah Maryam bani san asan koni wacece dan haka sai kin dawo kuma kawayen har biyu gareki”.?
“Eh ai twins ne shiyasa Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya, nan suma suke karatu sai dai ba department dinmu daya ba, kuma yayansu nan yake yin lecturer”..
“Haba wallahi kin cika surutu watarana, yaushe na tambayeki labarin gidansu? “Ai wai ina san kinsan waye pro.. “Dakata haka dan Allah ni kinga wucewata, “to Hakima bye”..
Nan Hakima ta wuce gida, itama Maryam ta wuce gida su Hakim.
Bayan Hakima taci abinci ta huta ta fara karatun tunta Dan gobe suke da exams ɗin Hakim…
_______________________________
“Haba Maryam ya naganki ke daya bada Gimbiya Hakima ba”.?
“Sadiya har yanzun na fahimci baku fahimci halin Hakima ba yanda nike gaya maku”..
“Wai ita wannan wani kallar haline da ita Maryam”.?
“Maryama Hakima tanada murderden hali, yar’sarkice mai nuna mulki da isa, bata daukar raini amman kuma indan ka zauna da ita tanada dadin zama”..
“Ko kin manta na gaya maki kullun sai sunyi fada da yaya Hakim”.?
“Niko ina so naga wannan Hakimar da har ta iya kallon idon yaya Hakim ta gaya mai magana aiko da gani ta wuce tunaninmu”.
“Kuma wallahi Sadiya sunyi bala’in marching sai dai matsalar su duka basu san juna”.
“Kash!! Wannan ko itace matsala dan wallahi bakiji yanda nike sonta ba duk da bansanta ba labarinta kawai nike ji a bakinki”.
“Karki damu zaki santa very soon, dan duk sallahr da zanyi sai nayi addu’ar Allah yasa Hakim ya zama miji ga Hakima”.
“Amin Maryam, muma daga yau zamu fara insha Allah, “Allah ya sa ni zan wuce gida nayi karatu gobe zamu yi exams din yaya Hakim”.
“Gaskiya ne tashi ki tafi, dan kinsan kika yi failure keda shi ne dan yanda yake mana da muna secondary school haka naga alamun zai cigaba da yi mana shiyasa yanzun bani bacci dan idan na kuskure na faɗi exams ɗin Yaya Hakim kasheni ne kawai bazaiyi ba”.
“Aiko dai ni na wuce byeee”.
“Kilishi! Wannan karan indan har ba’ayi nasara ba da kafafuna zani waje boka gaskiya dan na fara gajiya da asarar kudin da muke a banza”..
“Aa Gimbiya Zulaha, ke kara basu lokaci mana, ni sai naga indan muka basu lokaci indan aiki baiyiba sai mu tashi muyi aikinmu da kafafunmu”.
“To shikenan na basu lokaci Kilishi, amman ina gudu karda lokacin da muka basu cikin lokacin Hakim yace yana bukatar aure ai kinga mun makara”.
“Haba ina shi ɗin banza ai Hakim bashi ba aure, wanda zamu kasha har lahira kike ma maganar aure dai na dan Allah Gimbiya karda an Amin su ansa”..
“To nadaina Kilishi na basu lokacin kamar yanda kike bukata”..
“Yauwa Gimbiya yanzun naji dadi, ni nawuce sai da safe dare yayi, “mukwana lafiya”..
________________________________
Washe gari tunda safe Hakima ta tafi makaranta dan eight take da exam ɗin Hakim..
Sun shiga exams sun fito tayi ma wanda sukayi karatu dadi, wanda basuyi ba kuma bamu cewa komai..
Haka Su Hakima suka Kama zuwa exams har Allah yasa yau suka gama exams..
“Hakima zo muyi selfi ko? “AI ko dai Maryam ko nima yau wani kallar farinciki nike yau zanga Yakumbo da Fulani da Maimartaba”..
“Eyehh! Yau fa Hakima za’a koma gida a cigaba da mulki da wulakanta bayan Allah”.
“Haba wallahi ba ruwana da su, amman insuka kaini karshe sai na hukuntasu, “to nidai ina neman masu alfarma dan Allah, “karki damu mufara picture ɗin mana time yana wucewa dan su Lantana nasan sungama parking ni suke jira…
“Tom chease, nan suka gama daukar selfi dinsu sanann suka yi sallama kowace ta wuce gida…
“Ranki yadad’e mun gama harda komai muna jiran umirninki”..
“Kun kai kayan a boot ko? “Eh munkai komai duk abunda kika ce dashi za’a tafi gida”..
“To mimuke jira ku taso mu tafi gida kawai, “to Allah taimakeki”..
Nan su Gimbiya Hakima suka dauki hanyar birnin Kano, Kano ta dabo tinbin giwa koda mai kazo anfika☺️
_By Jameelah Jameey✍🏻_
Share
Comment
Vote
Like
Please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
29&30
“Oyoyo! Oyoyo!! Oyoyo!!! Daughter sannu da dawowa”…
“Yauwa Momy, wallahi Momy duk nayi missing dinku, “ai muma munyi missing dinki Daughter, “Amman shine ko ziyara baku kawo man ba”.?
+
“Ai Maimartaba yace karda aje, a barki kiyi karatu sosai, yanzun tashi kice abinci sai kije ku gaisa da Fulani”.
“Uhmmm! Mai aka dafa man? “Sinasir mana shi nayi maki da kai na ma, “Yauwa thnk you Momy”.
Nan Gimbiya Hakima taci Sinasir din sosai sannan ta nufi shashen Fulani….
“Fulani sannu da hutawa, “Yauwa Hakima ya karatun? “Alhmdulh, “Allah ya baki sa’a, “Amin ya Allah”.
“Kinje kin gaisa da Maimartaba ko? “A’a sai gobe zani, na dai aika am maman ison ganinshi”.
“To Allah yayi maki albarka, “Amin ya Allah, ni zan wuce, “To Hakima dan Allah kiyi hakuri da wannan bayin Allah da suke a karkashinki”..
“To insha Allah zanyi iyakar kokarina Fulani, na barki lafiya”..
Bayan Hakima ta koma shashen ta, waya tayi da Maryam sun jima suna wayarsu sannan sukayi sallama..
“Bilkisu, “Allah ya taimaki Gimbiya Hakima gani gabanki ina jiran umirninki”..
“Ki dauko takalma nan akaima Barau ya gogeman su, dan inasan gobe naje gidan marayu”..
“Angama ranki yadad’e yanzun zani cika umirninki “..
“Uhmmm, abunda Gimbiya Hakima tace Kenan , sannan tace, “kice ma Azima ta ansoman ɗinkina gidan waziri, Lantana kuma ta gogeman kayan baki dayan su”..
”To angama yar’sarki jikar’sarki, “bayan nan ki gayama masu aiki nan shashen gobe da safe bayan kungama aiki ina san ganinku baki daya”…
“Insha Allah uwargijiyarmu na barki lafiya “…
Nan Bilkisu ta tafi ta gayama Barau sakon Gimbiya Hakima..
“Malan Barau sannu da hutu, “Yauwa Bilkisu yan zauzau ansha zauzau, “Aiko dai Malan Barau ya muka samaiku? “Alhmdulh “..
“Ai mu tunda kuka tafi , muka fara ƙiba da kumari, dan rabon da aima wani bawa a masarautarnan hukunci ko yatsa tun tafiyarku ba’a nuna mana ba, daman Gimbiya Hakima itace marar tausayin da mutunci, to kuma tayi mana nisa”…
“Muma ai tunda muka tafi muke jindadinmu, da man kune kuke jamana, tunda bakusan halin Gimbiya Hakima ba shiyasa kuke bata mata rai”..
”Ai baku ganeba Bilkisu Amman.. “Da kata dan Allah, haba ya isa haka Malan Barau , ko baka san baki shi ke yanka wuya ba? Yanzun idan wani yazo wucewa ya jika kana ai banta Gimbiya Hakima kaga kashiga uku kenan, harda ma ni, dan haka ga wanann takalman nan na Gimbiya Hakima ka gogesu kafin gobe”…
STORY CONTINUES BELOW

“Yanzun duka uban takalman nan zan goge? Kuma kafin gobe? “Eh ashe ma tambayata kake? Kayi yanda ka gadama ni kaga tafiya ta”..
“Gaskiya sunyi yawa dan na Gimbiya Yakumbo nike gogewa tun jiya har yanzun ban gamaba, kuma ni Gimbiya Hakima daga gani sunfi na Gimbiya Yakumbo yawa”..
Nan Bilkisu ta tafi tabar Barau da salati, dan ya rasa yanda zaiyi ya gama kafin gobe da yaga tunanin ba mai fishewa bane ya tashi ya cigaba y da aikinshi ya samu ya gama kafin gobe..
“Ku Gimbiya Hakima tace gobe bayan kungama aiki tana san ganinku”..
“Munbani Ba’ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya? Daga dawowarta ko sati biyu batayi ba”…
“Taya zan sani Larai? Nima ai yar sakoce, ke kuma Azima tace kije gidan Waziri ki anso mata dinki, Lantana kuma ki goge mata su”…
“Mun shiga ukunmu Allah yasa dai ba wani abu mukayi mata ba, “Amin Ladi nima abunda nike tunani kenan, dan wallahi bansan kiran Gimbiya Hakima dan ba alheri bane”…
“To Ab’u ya zamuyi inba hakuri ba, dan ni wallahi ban so suka dawo hutu ba, muna zaman-zaman mu ta dawo zata matsa mana “…
“Murja wallahi ku iya bakinku, nidai gaskiya nagaya maku, nidai kunga kwanciyata sai da safenku dan yau da wuri zanyi bacci, “to Ba’ba Bilkisu mu kwana lafiya”…
__________________________________
“Gimbiya Zulaha nifa nafara gajiya gaskiya, “Kilishi kwantar da hankalinki dan boka yace nan da wata hudu Hakim ya zama labari, dan yace mutuwa zaiyi cikin ruwan sanyi irin mutuwar da ba wanda zaiyi zargin kashe shi akayi ba”…
“Yauwa Gimbiya Zulaha, gaskiya naji dadin wannan labari naki”..
“Au ai yanzun gashi kingani da naje da kafafuna, ansamu aiki maisauki da kyau, dan Million da’ya na ba boka yayi abunda ya kamata ayi “..
“Da yace na samo bakar Akuya da bakin Zakara da Kaza mai wake-wake da Bunsuru dan shekara goma sha biyar”..
“Dan shekara goma sha biyar fa Gimbiya”.?
“Ki tayi gani Namiji da suna Hajara, shiyasa nace ni ina zan samu wannan abubuwan ina gidan sarauta fita sai kabi dare”.
“Gaskiya ko Gimbiya,”ai shiyasa na bashi million daya yayi duk abunda ya dace ayi, da man ni bani san aikin da za’abamu mu zuba ma Hakim a abinci ko abun sha”…
“Nima gaskiya bani san kallar wannan aiki, gwanma kaba da kudi suyi aikinsu da kansu, kai kuma kayi baccinka, ni zan wuce mu kwana lafiya muna zuba ido muga wata hudu yayi zamuyi shagali dan har rawa ma sai nayi “…
“Wai Allah waya ga Kilishi da rawa? ai yana mutuwa zamuyi lokacin ubanshi dan shima na gaji da ganinshi a doran kasa”…
“Au hakane fa, amman ni ban dauki ubanshi matsala ba shiyasa nike mantawa dashi, amman zamuyi lokacinshi mu kwana lafiya”..
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Gimbiya Zulaha da Gimbiya Kilishi sun kasa zaune sun kasa tsaye wajen neman Bokaye..
Basu wurin Boka basu wurin Malan Boka, dan ko wace so take ace nata ya zama Sarki, amman duk tungun da Gimbiya Kilishi take yima Yarima Hamad Gimbiya Zulaha bata gane ba…
Ita dai tasan bata da masoyiya kamar Gimbiya Kilishi, kuma bata da makiya kamar Gimbiya Fulani, dan gani take da Sarki bai aureta ba da Hamad ya zama Yarima mai jiran gado, amman Sarki yayi gajin hakuri yayo mata kishiya ga shinan tana haihuwa da wata biyar itama ta haifi Hamad, dan haka ta uzurtama kanta sai Hamad ya zama sarkin Zaria, dole ta zama uwar sarki dan haka sai inda karfinta ta kare…
Ita kuma Gimbiya Fulani baiwar Allah bata damu da hidimarsu ba, Ita dai tasan rai da lafiya suna wajen ubangiji mu dan haka idan Hakim ya rasu lokacinshi ne yayi, ba dai asiri ba.
Shiyasa bata tada hankalinta ba tasa hidimar gabanta a gaba tana kula da mijinta da yaranta..
Itako Gimbiya Kilishi tana ganin yanda take yar’sarki jikar sarki matar sarki dan haka ya zama dole ta zama uwar sarki bata damu da Humad ba shi bane Babba tunda nan da wata hudu Hakim zai mutu, sauran ta ida dasu Hamad shida uwarshi..
Dan haka sai inda karfinta ya kare, mundun tana da rai da lafiya sai Humad ya zama Sarkin Zaria, shiyasa ta bazama neman bokaye da Malan Boka…
________________________________
Bayan ko wace ta gama aikinta suka hadu a kofar shashen Gimbiya Hakima suna jiran fitowar ta..
Sai da Gimbiya Hakima ta gama shiryawarta sanann ta fito..
“Kuna jina? “Eh Ranki yadad’e, “naji dadin yanda yanzun kuka maida hankali wajen aikinku, wannan ya nunaman kun fara sanin abunda ke maku ciwo, dan haka sai ku Kara maida hankali sosai, da mai magana? “…
“Aa babu, Allah yaja da tsawancin kwana, “Uhmmm! Kun iya tafiya ku bani waje”…
Nan suka tafi suna mamaki da jindadin chanjin da suke samu wajen Gimbiya Hakima dan tun dawowarta suke ganin chanjin sosai a wajen Gimbiya Hakima ..
“Lantana wuce kicema Bilkisu ta anso man takalman nan wajen Barau, sannan ku tabbatar da kun shirya dan fita zamuyi”…
“Angama ranki yadad’e, nan lantana ta gayama Bilkisu sakon Gimbiya Hakima, sannan suka fara shiryawa itada Azima..
Bayan sun gama shiryawa suka tafi shashen Gimbiya Hakima, ita ma Bilkisu ta anso takalmi har shiryawa tayi suna jiran fitowar Gimbiya Hakima su wuce gidan marayu..
Bayan ta fito suka wuce gidan marayu tayi masu abunda ta saba yi sanann suka wuce kasuwa nan tayi provision dan gobe take koma wa school sun gama hutu, zasu dasa second semester…
Washe gari Gimbiya Hakima ta shirya tayi bankwana da kowa sanann suka dauki hanya Zaria..
_ByJameelah jameey ✍🏻_
Share
Comments
Vote
Like
Please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
+
31&32
Washe gari da wuri Gimbiya Hakima ta shirya ta wuce school dan ko breakfast bata tsaya tayi ba saboda tanada pratical…
“Lantana!ki tabbarta da kungama komai dan bansan na ɓata maku rai”..
“Allah yataimakeki,Ranki yadad’e insha Allah zaki samaimu masu bin umirninki”..
“Uhmmm”..
Nan Gimbiya Hakima tafi tana sauri dan bata san ta makara dan ta lura lokacin gudu yake ga prof Hakim ne zai shigo masu..
“Bala”..
“Allah ya ji da tsawancin kwana, “idan ka kaini ka juyowarka gida zan kiraka indan mun tashi”..
“Godiya nike uwar marayu Allah ya ƙara maki lafiya da daukaka”..
“Uhmm! Yi sauri Bala bansan na makara lokaci na tafiya”…
Nan Bala ya ƙara bama mota wuta dan shima ya fahimci Gimbiya Hakima batasan tana makara dan taba bokonta Fahinmanci sosai…
Haka suka isa ta fita ta wuce class shi kuma ya wucewarshi gida yana murnar yanda Gimbiya Hakima ta barshi ya wuce gida ba tare da tace ya jira har sai ta gama lectures ba..
“Maryam kinga yanda kika ka ƙara kyau da haske kamar ba keba kinga yanda kika koma kuwa? “Hmm! Na kaiki Hakima baki ga yanda kika yi kyau ba, wannan ai sai kisa Hakim ya kasa gane ki kisa yayi mana lectures bugaga”..
“Kinji matsalarki ko? Har zaki fara ɓata man rai ko”.?
“Hakuri Gimbiya yanzun dai ya kika baro su Fulani da Yakumbo”.?
“Lafiya lau wallahi suna gaisheki ma, “ina ansawa, mundawo kenan sai hutu kuma tunda second semester ba wani daɗawa akeyi ba”…
“Ni daman ba wani weekend din da zani sai hutu, yanzun dai muna zuba ido muga anfiddo mana da result”…
“Allah yasa dai muga alkhari”Amin ya Allah “..
Nan dai suka cigaba da maganarsu, nan sai ga Hakim ya shigo…
“Morning class,”morning sir, ba tare da ɓata lokaci ba Hakim ya cigaba da yi masu lecture, lecture ta dauko dadi dan class din yayi shiru ba kajin motsin komai sai maganar Hakim..
A na cikin lecture Gimbiya Hakima taji wani irin fitsari ya matso ta, dan tayi iya bakin koƙarin ta na ta matsa fitsarin amman abun ya faskara dan ya ma kusa kufce mata…
“Excuss me Sir”…
Hakim yana jinta amman yayi banza da ita, dan tunda ya kalleta ya fahimcin fitsari ne ya kamata dan haka ya kudircin ma kanshi bai barinta fita sai dai tayi a wando, dan yanda ta cimai mutunci cikin mutu a join itama sai taga wulakanci yau din nan…
STORY CONTINUES BELOW

“Please Sir i beg Excuss me, “can you sit down or no”.?
“Sir i want to i.. “Shutup idiot i said sit down or cary your materials get out of my class”…
“Plea..se”…
Abunda Hakima tace kenan taji ruwan fitsari na bi mata kafafu, ba tasan lokacin da ta duƙe ba tana kukan bakin ciki dan tunda take ba’a taɓa ci mata mutunci ba kamar yau..
Ita dai Maryam da Yan class suna kallon ikon Allah, amman basu ji dadin abunda Hakim yayi ma Hakima ba dan cin fuskar yayi yawa ya wuce misali sosai…
Ko shi kanshi Hakim baiji dadin abunda yayi mata ba, dan tunda yake bai taɓa jin tausayinta ba kamar yau, amman dole ya rama abunda tayi mashi itama taji yanda yaji…
“Selient Class give me yours attension”..
Nan dai suka cigaba da lecture dinsu amman ba dadi dan gani suke yau cin mutunci Hakim yayi yawa dan ya cuce Hakima…
Itako Hakima tunda ta duƙe bata sake dago kanta ba, tana aikin kuka dan bata san wani kallar mataki zata ɗauka tsakaninta da Hakim, dan wata kallar wutar tsanarshi ke ruruwa a cikin zuciyarta…
Hakim bai fita ba sai da ya gama abunda ya kawo shi sannna fita amman duk jikinshi a sanyaye yake, da yake Hakim jarumine bai yarda aka gane mashi ba..
“Yi Hakuri Hakima tashi mu tafi ki chanza kaya dan Allah ma yaso na taho da wasu ɗinki da na anso wajen tarler na”..
“Na tsaneshi wallahi Maryam banda maƙiyi kamar Hakim insha Allah sai nayi mashi abunda bai mantawa dani”…
“Haba Hakima wai har sai yaushe zaku daina yar ramuwarnan? Nasan wallahi wani abu kika yi mashi shiyasa shima yayi maki haka”..
“Dan Allah kiyi hakuri ki ƙyaleshi ba dan ni ba, na roƙi wannan alfarma nidai yau a wajenki dan wallahi banjin dadin wanann faɗan da kuke yi, kudai baku taɓa haduwa waje ɗaya kamar annabi da kafiri”.?
“Wallahi sai na rama Final na gama magana, ni gida zani muje kiƙa ni na chanza kaya kafin Dr Moha ya shigo”…
“Ok less go”..
_____________________________
Wanene Hakim..
Masarautar Zaria, Masarautace wanda tana ɗaya daga cikin Masarautun da ke babban a Nigeria..
Sarki Sulaiman Abdulmalak shine ya Haifi Sarki Abdulmalak Sulaiman, Sarki Abdulmalak Sulaiman shine ya Haifi Yarima Hakim, Yarima Hamad da Yarima Humad da Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya su biyar ne Allah ya bashi a duniya…
Sarki Abdulmalak Sulaiman Gimbiya Zulaha ya fara aure ita yar’Sarkin Daura ce a kasar Katsina…
Allah ya daɗe bai ba Gimbiya Zulaha haihuwa ba, Gimbiya Zulaha ba karamin tashi hankalinta yayi ba, dan taga har sunyi shekara biyar da yin aure ita da Sarki Abdulmalak amman haihuwa shiru kake ji..
Ban inda Gimbiya Zulaha bata shiga ba dan ta samu taga ta haihu amman ba wani bayani tun tana zuwa asibiti har ta fara biye-biyen Malamai da bokaye itada baiwarta Lanto amman duk inda suke je kudin su ake ci a banza ba, dan ba wani chanji da Gimbiya Zulaha take gani..
Ana cikin haka Sarki Abdulmalak Sulaiman yazo mata da zancen ƙarin aure, zai auri yar’sarkin Yola..
Tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki Abdulmalak yayi mata maganar zai ƙara aure nan ta ƙara tashin hankalinta dan ba asirin da batayi ba dan karda Sarki yayi mata kishiya amman ina Allah ya kaddara sai anyi wannan aure, bayan sarki ya gaya mata bikin da wata ɗaya aka ɗaura mashi aure da Gimbiya Kubrah, suna kiranta da Fulani..
STORY CONTINUES BELOW

Bayan auren ba wahalar da Fulani Kubrah bata sha ba wajen Gimbiya Zulaha, dan magungunan hana haihuwa aka kama sa mata cikin abinci amman bata yarda tasha koda ruwa ba da ya fito daga shashen Gimbiya Zulaha ba..
Ana cikin wanann hali tsakanin Fulani Kubrah da Gimbiya Zulaha sai ga ciki a jikin Fulani Kubrah, tunda Gimbiya Zulaha ta lura da Fulani Kubrah tana dauke da ƙaramin ciki ba ƙaramin shiga tashin hankali tayi ba..
Dan batasan iya adadin kudin da ta kashe ba, wajen neman Malamai da Bokaye amman a banza dan bakin duk Zakaran da Allah ya nufa da cera kona mazuru a na shaho sai yayi shi..
Gimbiya Zulaha tana cikin neman Malamai sai itama ga ciki ya fito a jikinta, ba ƙaramin murna tayi ba, dan harta Sarki Abdulmalak Sulaiman sai da yayi murna yana godema Allah da ya bashi kyauta biyu cikin shekara guda..
Haka suka cigaba da rainon cikin su, amman duk da haka Gimbiya Zulaha bata ƙyale Fulani Kubrah da cikin ta ba, dan tayi alwashin bata haihoshi duniya sai ta kaudasu..
Haka dai Fulani Kubrah tai ta hakuri tana neman tsarin Allah daga sharin Gimbiya Zulaha dan tunda take ko sau ɗaya bata taɓa gayama sarki irin zaman da suke da Gimbiya Zulaha ba..
Duk da yana sane da duk abunda ke faruwa tsakanin iyalinshi amman ya samusu ido, dan yasan gidan sarauta ya gaji haka…
Cikin Fulani Kubrah ya isa haihuwa dan ta haiho santalelen ɗanta Namiji mai kama da ubanshi aka sama yaro suna *HAKIM*..
Da Gimbiya Zulaha taji labarin haihuwar Fulani Kubrah kuma ɗa Namiji ta haifa ba dan ƙaramin yaki tayi cikin ɗakinta ba ita ɗaya, haka ta baza amintatun bayin ta bin Bokaye dan ganin mutuwar ɗan da Fulani Kubrah ta haifa amman asiri bai tashiri kanshi tunda Allah ya tsareshi..
Bayan haihuwar Fulani Kubrah *da wata biyar* itama Gimbiya Zulaha ta haifi ɗanta Namiji shima yana kama da ubanshi dan shi yana da duhu ba kamar Hakim ba…
Ranar suna yaro yaci suna *HAMAD*, bayan Gimbiya Zulaha ta gama wanka ta cigaba da neman sa’a dan taci alwashin sai Hamad ya zama sarkin zauzau, ko ta wani hali..
Tare suke yin komai Hamad shida Hakim, ba ƙaramin kaunar juna suke ba haka suka taso komai nasu iri ɗaya ne…
Suna da shekara biyar Sarki Muhammd ya auro Gimbiya Kilishi yar’Sarkin Gumal..
Ba yanda Gimbiya Zulaha batayi ba dan karda Sarki yayi mata kishiya ta biyu amman ba yanda ta iya sai dai tasa ido yayi aurenshi..
Ita ko Gimbiya Fulani bata wani damuba ita dai tasa Allah gaba tana neman tsari daga masu sheri dan ba dare ba rana haka take wuni ibada da roƙan Allah..
Gimbiya Kilishi daga auren ta da shekara ɗaya itama ta haiho ɗanta Namiji mai bala’in kyau dashi masha Allah, yaro yaci sunan *HUMAD*..
Tunda Gimbiya Zulaha ta lura da Gimbiya Kilishi itama ba daga baya ba wajen bin Bokaye da Malamai dan sau biyu suna haɗuwa wajen Boka daban-daban shiyasa suka kulla Aminta ba dan ransu yaso ba..
Gimbiya Kilishi ta sama ranta ko ta halin ƙaƙa sai Humad yayi sarkin zaria, shiyasa itama ta hana kanta bacci take bin Bokaye..
Amman a gaban Gimbiya Zulaha nunawa take Humad bai isa ya riƙe mulkin zauzau ba tunda ga Hamad..
Soyayya sosai ke tsakanin Hakim da Hamad da kuma ƙaninsu Humad dan basu yarda ko ƙuda ya taɓa shi ba..
Tunda su Gimbiya Zulaha suka lura da shakuwa na shiga tsakanin yaransu sai suka kama hure ma yaransu ƙunne..
Haka Gimbiya Zulaha ta kama cusa ma Hamad san mulki, a hankali Hamad shima yaji yana san mulki tun yana yaro dan shekara goma.
Shi ko Yarima Humad bai yarda ya biye ma hudubar Mamanshi ba dan bai yarda ya dai na hudɗa da Yarima Hakim ba..
Humad yana da shekara goma a duniya Fulani Kubrah ta haifi yaranta yan biyu duka mata, ranar suna yara sukaci sunan Maryama da Sadiya , lokacin Hakim yana da shekara goma sha biyar a duniya..
Gimbiya Kilishi da ta lura Hamad yana san mulki sai tayi mashi asiri tasa aka tusa mashi ƙiyaiyar Hakim cikin zuciyarshi sannan aka sa mashi shiririta da rashin san yin ibada..
Amman Bokan yace duk randa Hamad ya ɗauki buta da sunan zaiyi alwallah yayi sallah wannan sihirin ya kare..
Wanann shine dalilin da baki ɗaya Hamad baya san Hakim dan ko ganinshi bai san yi..
Aliyu shi dan gidan Waziri ne dan sa’annin junane shida Hakim, Hakim wata biyu ya ba Aliyu a duniya duk tare suka taso..
Wannam kenan ☺️
Back to the story kundai ji summary din labarin Hakim shida yan uwanshi..
_By Jameelah Jameey✍🏻_
Share
Comment
Vote
Like
Please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
33&34
“Hakim lafiya naga duk ka wani zama silent maike damunka.”?
“Hmmm! Aliyu kai dai bari wallahi yau nayi ma Hakima abunda banji dadi ba ko da sau daya ne.”
“Mai kuma ya sake haɗaku da ita.”?
“Kawai dai kasan abunda tayi man a join, to shine nima na rama amman at the end banji dadin abunda nayi mata ba wallahi totaly.”
“Wata sabuwa inji yan-caca, mai kuma kayi mata.”?
“Kawai dai ta tambaye ni zata fita na hanata daman already na fahimceta fitsari xatayi, wallahi banyi tunanin fitsarin ya matseta sosai ba kawai naga yarinya na fitsari a tsaye, baka ji yanda nike ji ba kamar mai.”
“Ayya! Maganar gaskiya Hakim baka kyauta ba, ai koda zaka rama abunda Hakima tayi maka bai kamata kayi mata haka ba.”
“Ko baka san ba’asan mata na tara fitsari ba? Balle ita ta tambaye ka ka hanata gaskiya baka kyauta ba.”
“Uhmmm! Naje nayi ita bata ga abunda tayi man ba, dan haka ni nama kyauta, na lura kifi son Hakima a kaina komai akayi nine banda gaskiya.”
“Yes of course! Nidai naga kai ka wurga mata ɓawon ayaba, maimakon ka bata hakuri sai MULKI DA SARAUTA suka hanaka dan gani kake ka fi karfin da zaka bata hakuri, ita kuma taga bata iya kyaleka har ta rama.”
“To na Hakima naji sai akayi ƙaƙa? Dan haka ba ruwanka faɗana da Hakima kasa ido kayi kyalo shine naga OK.”?
“Ni kuma bani yin shiru mudin nagani sai nayi magana, kawai ina ganin gaskiya a hana ni magana gaskiya sai nayi.”
“To parrot! Ai sai kai tai tayi, tunda bakasan kaga bakinka yana shiru ni tashi ka ban waje zani gaida Fulani.”
“Ai bakai ɗaya keda Fulanin ba, dan haka tashi mu tafi daga nan naga Sahibata.”
“Baka da kunya a gabana? Kayi addu’a Allah yasa Maimartaba indan ya tashi badasu ya sa sunanka.”
“Amin ya Allah, Nifa Hakim duk wanda aka bani inaso dan ai duk kamarsu ɗaya dan har yanzun bani gane Maryama balle Sadiya.”
“Hakane kake wahalar banza baka ganesu kenan? “Wallahi ko”to Allah ya kyauta niko dai ba gaya maka zanyi ba.”
“Naji tashi mu tafi, Nan gaba dole na ganesu insha Allah tunda ɗaya zata zama halak malak ɗina.”
STORY CONTINUES BELOW

Haka suka tafi shashen FULANI shidai Hakim yana mamakin yanda Aliyu yake kare Hakima bayan duk rashin kunyar da take yi mashi..
Shidai baya iya ƙyaleta yaga tana yi mashi rashin kunya dan ko su Maryama sun girmi Hakima da shekara ɗaya ko biyu shiko maganar gaskiya baya iya daukar rainin wayau Hakima..
“Fulani barka da hutawa, “Yauwa Aliyu! Yau kenan a gidan namu.”?
“Laaaa! Ina neman afuwa Fulani amman ina shigowa sosai.”
“Eh ba laifi, dan nasan kafi wancan ɗan neman, dan na lura baki ɗaya Hakim baya san zuminci.”
“Aa Fulani ki bar cewa haka, wallahi kullun sai naje na gaida Mama ko Aliyu.”?
“Eh gaskiya kana zuwa, nine dai bani shigowa sosai, ina neman afuwa kuma.”
“Ai Aliyu nasan yana zuwa shashen ku sosai, ina nufin baya zuwa shashen Su Gimbiya Zulaha da Kilishi kaga banjin daɗin haka gaskiya Hakim.”
“Allah ya taimakeki yar’sarki matar sarki kuma jikar sarki, amman ba uwar sarki ba dan ni bani san sarauta na barma Hamad yaje ya riƙe.”
“Aa Hakim inkai baka so mu mana so a baka ko Fulani.”?
“Kudai kuyi fatan Allah ya tabbatar maku da alkhari cikin rayuwarku, mu kullun shine fatan mu dan haka idan ba Mulkin bane alkharinka Hakim Allah ya taya Hamad riƙo, in kuma shine alkharinka Allah ya tayaka riƙo.”
“Kuma ba wannan ba Hakim! Ya kamata ka fiddo mata hakanan dan na gaji da ganinka haka babu mata, ina amfani ku dukanku babu aure bakai babban ba ba ƙannanka ba.”
“Insha Allah Fulani zanyi koƙari naga na fidda mata dan bansan Maimartaba ya fara yi man maganar fiddo mata.”
“Aiko yana hanya dan har ya fara yi man magana kawai dai kaine bai kai dayi mawa ba.”
“Ai Fulani kafin ma yayi ma Hakim zai fiddo mata, dan yana nan yana neman wata… “Dakata haka dan Allah parrot uban yan’surutu.”
“Ya ka buge mashi baki? Bangane yayi shiru ba Hakim? Bakasan ya gayaman inda sirikar tawa take dan daman nasan Aliyu yasan inkanada Budurwa ko ma baka da ita dan shine kawai abokinka.”
“Wallahi Fulani banda ko kiyashi amman insha Allah zan fara neman budurwa verysoon insha Allah.”
“To Allah yasa! Inata addu’a dai Allah ya haɗaku da nagari, “Amin ya Allah.”
“Wai Fulani ina su Maryama suke? “Basunan sun tafi gidan su Maryam amman nasan suna hanya yanzun haka.”
“To Allah ya maidosu lafiya, “Amin, “Fulani maiyasa ake barin su Sadiya suna fita wai.”?
“taya zan hanasu zuwa gidan su Maryam bayan kasan wacece a wajensu.”?
“Hakane mu zamu wuce Fulani mun barki lafiya, “uhmm.”
___________________________
“Gaskiya Maryama abunda Yaya Hakim yayi ma Hakima bai kyauta ba baki ɗaya.”
“Dan Allah mai yayi mata.”?
Nan Maryam ta gayama su Sadiya abunda Hakim yayi ma Hakima..
“Wallahi da kun ganta a lokacin sai ta baku tausayi dan kuka ta kama yi ni na kaita gida da kaina.”
“Gaskiya Yaya Hakim bai kyauta ba, muda muke san su auri juna taya haka zata kasance yana yima ta kallar wannan cin mutuncin.”?
“Aa ai ko baya taɓa yuyuwa dan ko ni bani auren wanda ya tsaneni, to wani kallar rayuwa zasuyi bayan nasan baya sona ya tsaneni nida nike son nayi auren soyayya.”
“Kamar kin sani karkiso kiji yanda Hakima ta tsani Yaya Hakim, dan yau ta faɗi kalmar tsana bansan iyakaba.”
“Banga laifinta ba gaskiya ai abun yayi yawa, Fissabililah ai cin fuska baida dadi, sai kace ba yan’uwanjuna ba.”
“Yan’uwanjuna kuma.”?
“Ehman Sadiya yan’uwanjuna tunda su dukansu muslmai ne suna sallah kinga ko sun zaman yan’uwa.”
“Hakane kuma ai nasa mu yan’uwa ne, “Aa ko ɗaya kawai dai jininmu ne ya hadu da nata tun bamu ganta ba.”
“Wallahi ko, Jinike kamar naje na ganta amman ba dama, “aiko dai, dan Allah Maryam ki ƙara bata hakuri sosai please.”
“Ok insha Allah, “mu zamu wuce gida kinga dare ya fara karda mu kashema kanmu kasuwar gobe.”
“Gaskiya ku tashi ku tafi karda ma ku kashe harda ta jibi, “Byeee ki gaida Hakima, “ok zataji byee.”
_By Jameelah Jameey✍🏻_
Share
comments
Vote
Like
Please👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. 🤙🏻”’
________________________________
_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._+
”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍”’
35&36
Washe gari bayan Hakima ta gama yin breakfast ta shirya ta wuce school..
“Hakima! ina kwana.”?
“Yau kuma da wannan kika zo.”? Hakima tayi ma Maryam question dan ita dai tasan Maryam bata gaidata.
“Laifine dan na gaida kawata, kuma Gimbiya yar’sarkin Kano.”?
“Aa baki yi laifi ba, yasu Momy?, “suna lafiya Hakima, kawayena yan gidan sarki suna gaisheki.”
“Uhmmm, “haba Hakima ya zani ce maki friends ɗina suna gaisheki amman Uhmm kawai zaki ceman.”
“Kedai baki gajiya da complain uwar yan complain imeans ina ansawa haba, dole sai kinsa mutun magana koda baiso.”
“Allah ya baki hakuri kenan yau yan mulkin suna bisa kai, Allah ya kyauta, “Uhmmm.”
Nan Maryam itama ta kama ƙanta tunda ta lura da Gimbiya Hakima batasan yin magana itama sai tayi shiru dan bata san suyi faɗa da ƙawar tata..
Nan suna zauna sai ga Hakim ya shigo lecture, ba ƙaramin kyau yayi ba daman abunka da farin mutun ya ɗauko wani baƙin bowel mai bala’in kyau da tsada ya sanya sai ya fito jinin sarautar sak da shi dan yau shima sarautar ta mutso mai shiyasa class din basuga fuskar yin noise ba kowa ya kama girmanshi sun naba’a kamar anyi mutuwa..
Koyawa yake cikin natsuwa da jan-class dan ko shi kanshi yana mamakin yanda yake jin bayasan magana, duk da haka halin shi yake amman yasan na yau yafi na kullun..
”’Niko Jameey nace jinin sarautar kenan🤣☺️”’
Suna cikin yin lecture nan Hakim yayi pointing ɗin Hakima ta fito ta zana mashi wani compoud aiko ba karamin dadi Hakima tayi ba dan har ta shirya irin abunda zata yi ma Hakim, balle da ta lura yau wani mulki yake ji sai kace ɗan sarkin zaria..
”’Hahahahaha! TEAM Hakim kunji Hakima da wata magana wai Hakim take cema sai kace wani ɗan sarki kuji fa, koda yake tace shi ɗan gidan uban waye😚”’
Tafiya take cikin isa da nuna ita ɗin watace, dan tafiya take amman kamar mai tausayin ƙasa dan bata san taka ƙasar sosai…
Ba Hakim ba harda yan class suna mamakin yanda Hakima take tafiya duk da sun saba da halin Hakima ba sabo bane a wajensu amman suna mamakin izzarta, kamar wata yar’sarki…
”’Tofa! Team Hakima kunji fa abunda yan class da Hakim suke cema Hakima wai kamar wata yar’sarki☹️🙃”’
Tana zuwa gaban Hakim ta miƙe hannu ta amshi maker ɗin da zatayi using da ita, daman takalmin Hakima ba flat bane, masu tsinine dan haka tana sane ta takema Hakim ƙafa, dan sai da yace, “wash.”
Amman Hakima ko a jikinta dan nunawa tayi kamar bata taka komai ba, ta cigaba da abunda ya sata, baki ɗaya class din sai da suka tsorata…
Hakim ba ƙaramin zafi yake ji ba, dan yana ma tunanin yatsan ƙafarshi ya cire yanda Hakima ta take mashi su, kuma ta saki ƙarfinta baki ɗaya bisa ƙafar…
Amman da yake Hakim jarumin Namijine sai ya dake bai nuna yasan da wani hallita a ƙafarshi ba, duk da jinin da yaga ya fara fitarmai a ƙafa amman ya dake yanuna ma students dinshi bai damuba..
Hakima bata gamaba sai da ta tabbatar da Hakim yaji jiki sanann ta juyo ta miƙe mashi maker, suna haɗa ido ta kashe mashi ido ɗaya tayi mashi nuni da ita Hakima tafi ƙarfinshi dan ta wuce duk wani tunaninshi..
Hakim bai nuna ya ganta ba, haka ya cigaba da lecture ɗinshi har ya samu ya gama sanann ya fita..
Tafiya yake yana mamakin yanda Hakima ta raina mashi wayau, ta maidashi wani abokinta..
“Tabbas indan na biyema Hakima ina iya lahantata, harni Hakim, Hakima zata fiddama jini? Tabbas nayi sake da na bari Hakima ta rainani har haka.”
Hakim ne ke wannan maganar yana ɗaukar hanyar komawa gida yana mamakin rainin da ke tsakaninshi da Hakima…
“Haba Hakima wai bakiga abunda kikayi ma prof Hakim ba.”?
“Maryam na fahimci baki san Allah, ni bakiga abunda yayi man jiya ba? Dan na rama sai ya zama laifi.”?
“Ya kamata kubar yar’ramuwarnan keda prof Hakim, sai kace ƙananun yara, sai kace ba jinin sarauta ba.”
“Wannan matsalarkice, dan ina jinin sarauta sai akace karna rama abunda akayi man ko.”?
“Baki fahimceni ba, bake ɗaya bace jinin,”enough please Maryam ni kinga tafiyata gida dan inada abun yi, kuma wallahi Maryam ki kiyaye ni na gaya maki gaskiya ki zaɓi cikin biyu ni ko Hakim byee.”
“Allah ya baki hakuri ke na zaɓe ma ba sai gobe ba, byee.”
______________________________
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya rashin ganin mutuncin juna sai karuwa yake tsakanin Hakim da Hakima..
Dan ba wata jutuwa suke ba har yanzun, Hakima bata da wanda ta tsana kamar Hakim..
Haka shima Hakim bayan kaunar Hakima, dan baya san mutun marar kunya da rashin ganin girman na gaba da shi..
Kuma ya fahimci baki ɗaya Hakima yarinya ce wanda batasan ta girmama na gaba da ita ba..
”’Ni kuma nace kuji man Hakim yasan da haka yake biyema Hakima suna kallar wannan bed habib ɗin☹️ kash Allah dai ya shiryasu baki ɗayansu”’
Hakima tasa karatunta gaba dan har sun fara exams ɗin second semester kuma daman an fiddo masu result itace over rolla, tayi mamaki da Hakim bai kadata ba a course din shi..
Haka dai suka gama yin exmas dinsu har Gimbiya Hakima ta koma gida hutun season…
Su Gimbiya Zulaha kuwa suna nan sun zuba ido suna jiran wata hudu yayi suga gawar Hakim.. (Lol😜)
”’My guys kudai ku cigaba da biyoni kuga kallar cakwakwakiyar da za’ayi tsakanin wannan mutunan guda hudu☺️💞”’
*Gimbiya Hakima da Yarima Hakim*
*Gimbiya Zulaha da Yarima Hakim*
*Gimbiya Kilishi da Yarima Hakim*
*Yarima Hamad da Yarima Hakim*
_Wai Allah na, kai dai Hakim kaga ikon Allah kowa da akai yake faɗa ayya Hakim bakai ne baka da gaskiya ba🤔_
*Team Hakim ina jiran Answers ɗinku wai shi Hakim ba shi bane baida gaskiya ba☺️*
*please my guy kuyi manage da wannan pls yau aiki yayi man yawa☺️*
_By Jameelah Jameey✍🏻_
Share
comments
Vote
Like
pls