GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 10
A hankali Kursiyya ta fara jiyo wannan sautin wakar nasu irin wanda suka rinka yi jiya. Sai dai akwai bambanci, domin kuwa na yau ya yawaita, alamun sun kara yawa ke nan.
“Shakeke bulabi, honole hu, hu hu hul hu hu hul Shekeke bulabi, honole hu, hu hu hul Hu hu hul” ‘
Da sauri ta zabura ta tashi zaune. Tana jin gabanta na tsananta duka. Fargabar abin da za suyi mata idan sunzo kawai take yi. Tun tana jiyo sautin nasu daga nesa harya fara kusantowa gare ta. Ko da ta daga idonta sai hango su tayi su da yawa sosai, idan za a bata aikin kirgarsu to lallai ba za ta iya ba. “Allah ka fitarda ni…Ta fada, a daidai lokacin kuma wani tunani yazo mata. Ashe fa tun da suka shiga cikin wannan halin ko sau daya bata taba ambaton sunan Allah ba sai yanzu. Ta sauke ajiyar zuciya, tana jin yadda bakidayan jikinta ke karkarwa.
Dukar da kanta tayi a lokacin da suka iso gare ta. Tanajin yadda motsinsu ke kusantowa daf da ita, ta dan daga idonta kadan ta kalli yadda suka zagaye ta, suna sake rero wakarsu. ‘ Muryar Roshi tajiyo ya ce,
“Fardi shobini sakitiyo mujallikuryum bisuk. Ladarhu karhidgaltu mijhu. (Yanzu na tabbata abin bauta ya gama yanke mana shawarar abin da za muyi. Mu isa gare shi tare da ita.)” Da karfi taji an jawo ta, ta saki kara tana mai yamutsa fuskarta. Kallon halittun kanshi wani tashin hankali ne, bare kuma yadda suke da yawa a yanzu tamkar kuda. A tunaninta dai duniyarsu ce boka Fartsi ya jeho ta. Amma dai bai kyauta mata ba, sam bai mata adalci ba. Cira ta sama suka yi suna ci gaba da wake-wakensu, har suka isa wurin abin bautarsu Talmijo. Mutum goma daga cikinsu ne suka tasa Kursiyya gaba, sauran kuma suka dakata daga bakin kofa, suna masu ci gaba da wannan wakartasu.
Idanuwan Kursiyya a rufe suke tsabartsoro, har suka isa gaban abun bautar
nasu bata bude ba, har sai da ta farajiyo sautinsu cikin mamaki suna magana.
“Shawaleleyanku kalsumbiya tattesu wal huhuwa. Kalmasusawijhu galjisu Talmijo (Abun mamaki ga shi kalar kyalle ba ta sauya ba. Ke nan babu nasara tunda har Talmijo bai bada goyon baya ba.)” ‘
Fuska murtuk wani daga cikinsu yake yin maganar, yana sake kallon Kursiyya.
Maganganu suka ci gaba da yi a tsakaninsu na tsawon lokaci, kam taji an fesa mata wani irin abu mai matukar sanyi. A hankali ta fara jin gangarjikinta tamkar ba nata ba. Tana zamewa daga inda take har ta gama sulalewa kasa.
Kamar an ce mata ta kyafta idonta, tana budewa ta gan ta a wani irin daji, wanda ya fi wancan da Saadiyya ta kawo su tsanani. Matse jikinta tayi a lokacin da taji wani irin sanyi na ratsa ta, jikinta na karkarwa sosai har tsigarjikinta na tashi.
Ta daga hannunta na dama ta kalla, taga yadda kananan kuraje suka jeru birjik ajiki, a take ta fasa kuka mai karfi.
“Mutum ko aljani Don Allah a taimaka mini. Ataimaka a fitar dani daga wannan mugun dajin. Ku mayarda ni masarautarmu.” Sautin maganar da take yi ne ke sake dawo mata. Hakan yasa ta tsorata sosai, ta rinka darara idanuwanta ko da wani wanda zata gani dake maimaita maganartata.Jin shiru ya sa ta sake maimaitawa, a wannan lokacin sai taji dariya da karfin
gaske tana kusantowa inda take. Sautin dariyar hade yake isowa da wani iska mai haske. Da karfi ya diro gare ta, ta firgita a tsorace hade da sake kadaddabe jikinta.
Cibrarren iska ne mai zubi da halittar mutum, har da kwayar idanuwa. “Na roke ku da Allah kar ku cutarda ni. Ku taimaka ku barni da wannan azabar da nakeji ma ta ishe ni. Don Allah ku mayar dani gida.”
Dariya sosai halittar keyi, kafin a hankali ta warware ta dawo halittar Sa’adiyya. ‘ “Sosai kika bani wahala. Kin san azabarda na sha wurin neman ki? Kin san yadda na yawace duniyar nan wurin neman ki? Duk ke kika ja mini komai, ke kika fusata boka fartsi harya yi miki wanan jifar.” Ta yi shiru daga nan, hakoran bakinta na kara yin tsini sosai, tamkar na zaki. A yau din nan zan yi magana ta karshe da ke, amma idan kin so. Ki fada mini inda kika ajje mahaifiyata, sannan kuma ki labarta mini kalar mugun tsafin da kika mata, wanda har Boka Fartsi ya kasa gano inda take. Idan har kika
fada mini gaskiya, nayi alkawarin zaki huta da azabar nan, zaki samu sassauci. Amma idan kika yi mini karya ko kuma kika ki fada mini, ina mai tabbatar miki da cewa azaba baki sha komai ba yanzu zaki fara.” Ido Kursiyya ta runtse, ta matso wasu irin zafafan hawaye. Ya aka yi Gimbiya Sa’adiyya ta gane cewa ita tama mahaifiyarta wani abu? Ya aka yi ta gane cewa tana raye har yanzu? Ya za tayi da wancan asirin kuma? Gaskiya Boka Fartsi bai kyauta mata ba, bai mata adalci ba. Ta tabbata duk shi ne ya fada mata wannan sirrin, sai dai taji dadi da ya kasance ya kasa warware aikin da Uwar biyu ta mata, wanda shi ne silar samun sabaninta da Boka Fartsi tun asali.
“Ba zaki fada mini ba ko? Ashe baki gaji da shan azaba ba. Lallai zan koya miki darasi. Zaki gane cewa ni ba mutum ba ce a yanzu, zan yi abin da har ki mutu ba zaki taba yin shi ba. Muje zuwa!”
A fusace Sa’adiyya tayi wannan maganar, hade da fesa wata irin wuta mai
fartsatsi a saitin Kursiyya. A tare suka bace daga wurin.
A gaban boka Fartsi suka bullo. Ganin yadda fuskar Sa’adiyya take a fusace ya sa ya sunkuyarda kansa kasa, yanajiran abin da zai fito daga bakinta. Cikin wata irin murya mai nunar da zallar bacin ran da take cikinsa ta fara magana, “Nace maka ka fita harkar Kursiyya, ka bar ni da ita. Ni ta azabtar, ina so ka zare hannuwanka daga duk wani sha’ani nata. Yanzu ka san irin wahalar dana sha wurin neman ta? Ka san a inda na ganta?”
Ta dakata daga nan, zuciyarta na tsananin zafi, sai huci take fitarwa. Gabansa ne ke duka a lokacin da Sa’adiyya ke magana. Bashi da yadda zai yi, domin kuwa duk wani karfi nashi ya tattare shi ya mayar dashi ga Sa’adiyya. Wanda ya yi saura ba wani mai yawa ba ne, ba zai wuce iya wullawar da yama Kursiyya har ta bulla a kasan ruwa cikin waYancan mutanen ba. Dole ne a gare shi yabi maganar Sa’adiyya, domin kuwa a yanzu ita ke iko dashi. Yalwatacciyar sumar gemensa ta kama da yan yatsunta biyu, ta hau
wani irin bakin jini ya rinka fitowa, da zararya digo, kafin yabi iska zai daskare.
Sosai Kursiyya ke mamakin karfi irin na Sa’adiyya. Take tuna baya. Wato yadda boka Fartsi yake da karfin iko da takama. Wai yau shi ne Sa’adiyya ke Runtse idanuwa Sa’adiyya tayi, da karfi ta saki wani irin gumji mai tafiya da wani salon sautin da duk wanda yaji shi dole sai ya tsorata. Kamar an ce Kursiyya ta runtse idanuwanta, kafin ta bude ta ga babu Sa’adiyya ko kadan babu alamunta. Ta gaggauta sauke ajiyarzuciya. Sai dai ba ta ankara ba taji ta bullo kusa da ita. Ta tallabo wuyanta da karfi ta matse. Tana jin yadda Kursiyya ke kakari amma ta ki sakinta. Har sai da ta tabbatar ta jigata sosai sannan ta sake ta. Ta fesa mata haske daga tafin hannunta ya iya saitin makogoronta. A take ta koma yadda take, bakinta ya karkace, wannan yawun ya ci gaba da dalala mai matukarwari.
Da yatsar hannunta ta mayar da Kursiyya kadangare, irin daka-daka din nan mai dogon bindi.
Sa’adiyya ta kyalkyace da dariya, ta watsa hasken hannunta jikin kadangaren, sai gashi suf-suf-suf ya wuce daga wurin ya tafl.
A wata ‘yar karamar huda ya bi ya kurda sai ga shi tsamo-tsamo cikin dakin Kursiyya. Abin mamaki, ko da ya iso ya tarar Sa’adiyya zaune bakin gadon, tana sakin wata irin dariyar keta, tana ta famar wuwwulla idanuwa. Sake yarfa hannun nata tayi sai ga Kursiyya ta dawo yadda take, yawun kazantar nan na fita. ‘
“Hahahahahaha! Tun da har kika yi alwashin kin fada mini boyayyen sirrin nan, nima na yi alwashin azabtar dake fiye da yadda nayi niyya a baya. Zabbau na dakin horo ana bata horo mai tsanani saboda rashin ganin ki. Idan sunzo sun same ki, sai ki san yadda za kiyi dasu.” Tana gama fadar haka ta sake kecewa da wata irin dariyar, wacce ginin dakin ya rinka amsawa ta ko’ina. Ta bace bat daga dakin ta bar Kursiyya da hawaye. ‘
Hmm