GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 12
Zabbau dake Iabe bakin kofa ta zaro dukkan idanuwanta, a kidime take magana da zuciyarta ‘Karfa abin da bamu tsammani ba ya kasance.’A hankali cikin sanda ta gaggauta barin wurin, zuciyarta na azalzala mata yadda zata tinkari Kursiyya da wannan maganar.
Mai marraba ya dan murmusa, tukunna ya fadada dariyarsa.
“Ehh tabbas su biyu ne. Akwai Yar uwarta Gimbiya Saadiyya, sai dai ita ba takai Haka shekaru ba. Duka shekararta goma sha bakwai ne yanzu. Sabanin Hafsa dake da sha
takwas tana dafda shiga sha tara. Kamar Gimbiya Saadiyya za tayi maka yarinta.” “Babu komai in don wannan mai martaba. Da dai an turo ta din, watakila ta fiyi mini ma.” Tamkar an daba ma Hafsa mashi a kirji haka taji. Zuciyarta ta shiga kunci mara adadi a yan dakikun da basu wuce biyar ba. kalaman mai martaba kuwa su suka fi komai bakanta mata rai. Idan bata manta ba, ko jiya sai data tambayi Fulani Kursiyya kan yadda suka yi da mai martaba idan aka nemi ganin Halimatu. Mai martaba yajaddada mata da cewa bama za a yi haka ba. Saboda Halimatu ita ce karama, ba ita ta cancanta da zama matar Yerima Abu sufyan ba, saboda ba zai aurar da ita ba bayan ga yayarta zaune babu aure. Amma ya zai mata haka? Me yasa zai canza magana? Wasu irin hawaye taji suna shirin zubo mata. Ta gaggauta tsayar da su,
amma duk da haka sake saukowa suke yi, “Bari in je. Yanzu za a turo maka Gimbiya Saadiyya in sha Allahu.”
Mai martaba ya fada yana kokarin mikewa. Da hanzari fadawansa na bakin kofa suka isa gare shi, suka kare shi da manyan rigunansu sannan ya mike. Cikin takun shi ya bardakin, shi kanshi yanaji babu dadi, saboda ya saba zancen Kursiyya. Amma ya zaiyi? Bai san abin da zai fada ma Yeriman ba. Kuskuren nashi ne tun asali da ya shaida wa Sarki Abdurrahman cewa yan matan guda biyu ne.
Bayan mai martaba ya koma farfajiyarsa, ya umurci waziri kan ya turo masa Gimbiya Sa’adiyya idan ya fita. Kamar koyaushe, shi kanshi waziri ba son a ambaci yarinyar a gabansa yake yiba. Kawai don bai da yadda zaiyi ne, ba zai iya musa wa mai martaba ba.
A gaban dakinta ya isa. Yana jin gumjin kukanta, wanda yaki ci yaki cinyewa. Ya kwankwasa kofar da karfi ta yadda za ta iyaji. Ta dakata da kukan nata tana saita
kunnuwanta a karar kwankwasa kofar. Haka kawai ta samu kanta da faduwar gaba. Tsoron ta biyu ne, kar ace Kursiyya ce ta dawo da wani makircin. Na biyu kuma, kar mai martaba
ne ke son ganawa da ita kamar yadda ya saba a kowacce rana. “Ki bude mini kofa Halimatu. Sakone daga mai martaba. ”
Dajin muryar waziri ta hanzarta ta bude mishi kofarjiki na rawa. Ta dube shi ya dube ta. Duk ta zama wata iri. Idanuwanta sun kumbura sosai. Kyakkyawar farar fatar fuskarta ta koma jajur tsabar kukan da ta sha. “Mai martaba na son ganinki. ” Ya fada hade dajuyawa ya bar ta sake da baki. “Kawu…!” Ta fada da dan karfi yadda zaiji. Ya waigo ya kalle ta. “Lafiya?” “Kawu bazan iya zuwa wurin mai martaba ba yanzu, bani da Iafiya…” Waziri ya katse ta. “Ko baki da lafiya ai kina iya tafiya k0? Maza ki tafi wurinsa, yana son ganin ki da gaggawa.”
Hannuwanta duka biyun ta dora bisa kai. Sosai take tunawa da umurnin da Kursiyya ta ba ta. Ta sake fashewa da wani kukan, tana fadin
“Na shiga uku ni Sa’adiyya! Wallahi bansan me zan fada mata ba. Ban san me zan ce da ita ba idan ta kama ni da take umurninta. ”
“Ruwanki.” Waziriya fada hade da dage kafadarsa.
“Ki kuma wuce ki tafiyanzun nan, bana so kibata mini Iokaci. Na ‘ma fasa tafiyar sai tare dake.”
Duk da halinta na hakuri, a yanzu sai take tsananinjin haushin Waziri. ldanma ba ita da take shiru shiru ba, ta yaya waziri zai rinka yi mata irin wannan tsawar? Duk abin shi ai baya ma Hafsa. Haka kuma ba yayi ma sauran yayyenta maza guda biyu haka. K0 da dai su ba mazauna bane ba saboda azabar da Kursiyya ta gana musu tun suna yara.
“Ki tafi kiyafa mayafi ki fito kona tattaka ki a nan.”
Sosai tsawar tashi ta firgita ta. Da hanzari ta shige ciki ta yafa mayafinta, sannan ta bi bayan waziri domin zuwa farfajiyar mai martaba.
Sintiri Kursiyya keyi daga wannan bango zuwa wancan bango. Hannunta na hagu ta dunkule ta buga shi da karfi? a cikin tafin hannun dama. Ta runtse idanuwanta cike da takaici sannan ta gyada kai.
“Wannan wane irin wa wan yaro ne? Da alama so yake ya bata mana baki daya tsarinmu. Idan ba haka ba, uban me ya sa zai ce wai saiyayi zabi? Duk adon da ,yarlelena ta sha har yana da damar da zai ce saiya zaba tsakaninta da wata kucakar banza wai ita Halimatu? Wallahi ba zata sabu ba! Koya zabe ta da sake don Duk yadda za a yi dole sai an yi don a raba su. ldan ma kashe yarinyarza a yi ban damu ba, matukar dai bazata aure shi ba. Yo to ko da Hafsa bata son shi, ta yaya ina da raina da Iafiya zan bari mai bakinjinin can ta auri Yerima Abu Sufyan dan sarkin Kubaisu? Ina! lna”
Ta sake gyada kanta. Cikin makirci Zabbau tace, Babu ko tantama abin da kunnuwana sukajiye mini kenan. Kuma yanzu haka yaron yana can yanajiran zuwan Halima mai bakinjini.” Ta wani karkace kanta irin na tsoffin munafukan nan. Guntun murmushi Kursiyya ta saki. Ta datse hakoranta, “Ba za taje wurinsa ba, na tabbata.“ Zabbau ta tallabe habarta, ta yikasa-kasa da murya. “Me yasa kika fadi haka, ranki shi dade?”
“Mun yi magana da ita, kamar na san hakan zata faru kuwa. Ai tana da tsoro yarinyar. Koba tsoro bama, tana da Iadabi sosai. Duk abin da aka hane ta tana dainawa, haka kuma abin da aka umurce ta tana gaggauta binsa. Na san Halimatu, na san wace ce ita. Duk dabararsu ba zata taba fitowa daga dakinta ba.”
Hannu Zabbau tajinjina, alamar Iambar yabo. “Kina da kwanya sosai ranki shi dade.” Kursiyya ta daure fuska. “Ni kike fada wa haka? Sa,arki ce niko me?””Tuba nake, da girman kujerarki. ”Sosai jikin Gimbiya Sa’adiyya ke kyarma, tsabar tsoro da fargabar abin da zata tarar. Ita babban abin da take ma gudu karta yi kicbis da Fulani Kursiyya, ta tabbata saita yaba wa aya zakinta. Da isar su farfajiyar mai martaba, ta cire takalmanta hade dajawo marufin kanta ta rufe gefen fuskarta. Suka shiga dakin Waziri gaba tana biye da shi, tana yi tana share hawayen da ke sake zo mata. Sunkuyawa tayi a gabansa, baki na rawa ta furra, “Ga…gani mai martaba.” ”Lafiya dai kike kuka?” Ya gaggauta tambayarta. “Babu komai Abba, ciwon kai ne amma da sauki.” Ta furta hade da kirkiro murmushi. Kansa ya gyada. Tabbas ya san tana da damuwa. K0 bai tambaye ta ba ya riya a ransa akwai abin da yake damun ta, wanda harya saka damuwarta bayyana. Yana da wuya a gane halin da take ciki. Saboda a kodayaushe fuskarta cikin annuri take. Duk iya bacin ran da za a saka ta bata nunarwa a idanuwan mutane, sai dai ta shanye abin ta ita kadai ba tare da kowa ya sani ba. “Shiga bandakin can ki wanke fuskarki ki fito. Dakin baki za kije ki samu Yerima Abu Sufyan da Hafsa yarlele. “Kirjinta ta dafe da yayi wata irin razananniyar bugawa. Ta kwalalo idanuwa tana sake bin mai martaba da kallo. K0 kadan ba halin Saadiyyarsa bane hada idanuwa dashi haka gatsau babu kunya. Ya tabbata dalili ne ya saka ta yin hakan. Ba zaya ce da ita komai ba, saboda Yerima Abu Sufyan na can yanajira, kuma baya son bata masa Iokaci.
“Tashi maza kije, mayi magana daga baya.”
Ba zata Iya musa masa ba, hakan yasa ta mike jiki babu kwari ta nufi bandakin. Bayan ta wanko fuskarta ta dawa, waziriya mata jagora har suka isa dakin bakin. Kanshi sunkuye yake har ta kariso bakin kofa. Tun a nan yaga bambanci, saboda bata shigo ba har saida Shaheed ya amsa mata sallama sannan ta karisa isowa daga ciki. Ta
nemi wuri bisa kafet daga can nesa dasu ta zauna, har a Iokacin bata bari fuskarta ta fito ba.
“Barka da zuwa. ” Ta furta cikin muryarta kasa-kasa, tamkar bata son fitowar maganar. Shaheed yayi murmushi ya dan saci kallon Yerima Abu Sufyan, “Yauwa yace Gimbiya Sa’adiyya. Fatan mun same ku Iafiya hamdulillah.”
Tace da Shaheed haryanzu kanta a sunkuye. Sai a Iokacin Yerima Abu Sufyan ya samu damar dago kansa ya kalle ta. Da haka kadai mutum zai tabbatar da tarbiyyar yarinyar. Tun baiga fuskarta ba zuciyarsa ta aminta da ita. Ya raya a ransa itace zabinsa, ita ce daidai da halayyarsa.
Hmm Lallai shin ko mai zai faru