GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 19

GIMBIYA SA’ADIYA 






CHAPTER 19



Murmushi Salbiyya ta sakar musu, sannan ta basu izinin zama. “K0 baki fada ba da ma zama za muyi.” Kursiyya ta furta cike da izza da takama. Salbiyya tayi dariya, ta dafa kan Hafsa tana fadin “Gimbiya Hafsa an girma. Ya kuke ya bayan rabuwa?” “Komai lafiya.” Hafsa ta fada babu annuri a fuskarta. Kun dawo Iafiya? “Alhamdulillah, Fulani. Na gode da kulawa.” 
Tana gama fadin haka Kursiyya ta mike, hakan yasa ita ma Hafsar ta mike suka ma Salbiyya sallama tare da fita daga dakin. A ran Salbiyya tace ‘Mai hali dai baya barin halinsa.’ 
Wuraren goma na dare Salbiyya ta amsa kiran mai martaba Sarki Sani. Sai data sake wadata jikinta da kamshi sannan ta nufi farfajiyarsa. A falo ta same shi zaune shi da Sa’adiyya. Cikin girmamawa Sa’adiyya ta mata barka da zuwa, ta amsa ba yabo ba fallasa. Mai martaba yace, 
“Gimbiya Sa’adiyya amarya.” Cikin mamaki Salbiyya tace, “Aure za tayi?Ashe tana da masoyi?” 
Daga mai martaba har Sa,adiyyar shiru suka yi kamar ruwa ya cinye su. Dukkaninsu ba suji dadin maganar ba. Ita kuwa babu alamun damuwa a fuskarta. 
“Saura kwanaki goma sha uku bikinta.” “Allah mai iko.’ Ashe da bamu dawo ba da baza muji ba.” “Dale za kuji mana, Uwargida. Ko kin manta cewa ku ne iyayen nata mahaifiyarta ta rasu?” Murmushi ta yi 
“Haka ne kuma. Tattaunawa ake game da bikin ke nan? Ke kuwa Halimatu ai da sai kiyi hakuri ki bar mana.” Murmushin yake Sa’adiyya tayi “Bama wannan maganar ce muke yiba .” 
“To batun me ake? Ko kuwa dai batu ne na tsakanin uba da ’ya? To an gama. Zaki iya tafiya?” 
Gyada kai Halimatu tayi tamkar ruwan hawaye zai fito mata. lta kam tana ganin jarrabta a rayuwarta. lta ma kanta Salbiyyar ta tsane ta, sai dai akwai bambanci tsakanin tsanar da Salbiyya ta mata, da kuma ta Kursiyya. Daidai da rana daya Salbiyya bata taba yunkurin 
azabtar da ita ba, a bar ta dai da dankara mata bakar magana ba wai tun yanzu ba. lta kuwa Kursiyya azaba kala-kala take gana mata. 
Washegari da safe Kursiyya ta shiga gaishe da mai martaba. Bayan ya amsa ta kankance 
murya tace, “Mai martaba dama akwai maganar da nake so muyi da kai.” Bayan ya dago kanshi ya amsa da, “Ina sauraren ki Fulani.” Ta sauke ajiyar zuciya. “Game da shirye-shiryen auren Halimatu ne. ” 
Ta dakata daga nan tana karantar yanayinsa, yadda fuskarsa ta nuna alamunjin dadi daga fara yin maganar. “Ranka ya dade, bai kamata a zauna ba a ma yarinyar wani shiri ba. Naso a ce an saka bikin da tsayi, ta yadda za,a mata gyara yadda ya kamata, akalla na wata guda. To amma tun da abin ya zama a kurarren Iokaci, sai nake ganin ya kamata a fara daga yau k0?” Sarki Saniya fadada murmushinsa. “Ehh tabbas haka ne. Kin yi tunani mai kyau Fulani.” 
A daidai nan saiga Salbiyya ta iso falon, sanye da maroon din alkyabba wacce aka kawata 
da kalar golden. Daga dayan gefen mai martaba ta zauna, ta kalli Kursiyya da murmushi, “Sannu Fulani. An tashi Iafiya?” 
Kursiyya ta dan tabe baki, cikin izza ta amsa da, 
“Lafiya. Ya gajiyarku?” “Tabi lafiya.” Kursiyya ta mayar da kallon ta ga Sarki Sani, “Ina son mu tafi tare da ita ne. Daga can sai muyi duk abubuwan da suka dace.” 
“Amma kamar zaifi dacewa a nemi duk masuyi su mata a gida ko? Naga suna da tela a nan wanda zai mata dinkuna. Haka kuma suna da mai lalle da kitso, ga kuma mai gyara musu jiki duk akwai a nan. Ko kuwa dai kina ganin dole sai kun fita din?” 
Murmushi Kursiyya tayi, tana maikokarin tabbatar da karyarta ta zauna daram a matsayin gaskiya. 
“Akwai program wanda muka tsara dani da ita da Hafsa. Program ne wanda ya amsa sunansa, na kuma tabbatar da zai tara manya-manyan mutane. To ganin haka yasa naga ya dace mu tafi da ita a zabi suturar data kamace da ita, wacce zata zauna mata, kowa ya tabbatar cewa Gimbiya Sa’adiyya diyar Sarki Sani ce ake aurarwa.” ‘ 
Lumshe idanuwa Mai martaba yayi, yana mai tsananinjin dadin kalaman Kursiyya. A zuciyarsa dada godiya yake yiga Allah, don a ganin shi aurar da Sa’adiyya da zaiyi ne yasa zuciyar Kursiyya ta fara yin taushi game da ita. 
“Amma ranka ya dade, idan kana ganin kamar bai dace mu fita ba sai a bari kawai.” Da sauri ya hau gyada kansa, 
A,a Fulani. Yadda kuka tsara din dai yayi. Na bayar da goyon bayana dari bisa dari kuje din.” 
“To shi ke nan, mun gode sosai da goyon baya. Bari in tura a kira mini Halimatun mu karisa 
maganar a gabanta. ” 
Tana kaiwa nan ta kira daya daga cikin masu gadin kofar. Tun daga nesa ya rusuna yana jiran umurninta. 
“Ka kira mini Halimatu yanzu. Kace ta same ni a farfajiyar mai martaba.” 
Da hanzarinsa ya bardakin ya isa inda Sa’adiyya,take ya sanar da ita kamar yadda Kursiyya ta fada masa. 
Bata bar dakinta ba sai da duk ta gama kimtsawa, a Iokacin Kursiyya ta mata aike na uku. 
Da sallamarta ta shiga dakin, ta rusuna ta gaishe da Sarki sai ta gaishe da Kursiyya da kuma Salbiyya. 
“An aiko kira na Abba, lokacin fitowa na kenan daga wanka. A yi mini afwa Umma.” Tajuyar da kallon taga Kursiyya. Dariyar yake Kursiyya tayi hade da fadin, “Babu komai Yata. An gama Iafiya dai k0?” “Alhamdulillah.” 
Ta fada kanta sunkuye a kasa. 
Gyaran murya mai martaba ya yi sannan ya ce, 
“Anjima zaku fita da Fulani ko?Akwai kudi zan bayar, da wanda za a siyo tufafin, sai kuma ki rike a hannunki ko da abin da kike so. Ni nan nine matsayin uban ango, duk wata hidima da anguna keyi ni zan yi. Kar kuji kyashin fada mini. Da karfe nawa ne zaku fita din?” 
Sa’adiyya ta dago kanta ta kalli Kursiyya tana mai neman karin bayani, saboda ita kam bata san komai a kan maganar ba. Da sauri Kursiyya tace
“Kamar da azahar aiya miki ko?A Iokacin nima bana kamai sai muje kizaba.” 
Wata zuciyar ke fada mata kan ta nemi karin bayani a kan maganganun nasu, sai dai mafi rinjaye na zuciyarta na dakatar da ita, hakan yasa kawai ta daga kanta fuskarta ba yaba ba fallasa. 
Daga nan ta mike ta nufi dakinta, zuciyarta cike da sake-sake. In baccin cewa maganar nan daga mai martaba take, da babu abin da zai hana ta kin zuwa. Sai dai ita bata kasance mai ja-in-ja da cewar sarki ba. Don haka dole zata daure ta fita din. 
Tana zaune taji motsin shigowar Hafsa, ta daga kanta ta kalIi’yadda Hafsar ke sakar mata murmushi. ’ 
“Kanwata ta kaina, amaryar Yerima Abu Sufyan.” Ta zauna a kusa da Sa,adiyyar. 
“Ke tun ma kafin a fara gyara ki har kin fara kyalli. Bakidaya idan aka kalli fuskarki an san ke amarya ce. ” 
Shiru dai Sa’adiyya tayi tana nazarfar yanayin na Hafsa. 
“Kin san me? Wallahi duk banji dadi ba. Na saka ma tare zamu fita tare anjima saboda in taya ki zaben kaya, to kuma wata hidimar ta taso mini, zanyi baki, Yanzu haka na baro ana kan aikin hidimar tarar su. Kin ga babu yadda za ayi kuma in tafi” in bar bakin da zan yi. Amma babu komai, tun da dai da Umma zaku tafi na tabbata zaku zabi mai kyau, kema 
kuma kin san kayayyakin kirki ai.” Har tayi ta kare k0 uffan Sa’adiyya bata ceda ita ba. Sai a karshe tace, “Babu komai’ ai.” 
Bayan Hafsa ta mike, ta Iura dakyau Sa’adiyya bata kallon ta, ta mata gwalo tana tuna yadda sukayi yanzun nan da Kursiyya, cewa tasan yadda zata yi don ganin ta tsara ma 
Sa’adiyya cewa banda ita za a yi tafiyar. “Bari in koma in Iura da masu aikin can. ” “To.” 
Kawai Sa’adiyya ta furta. 
Karfe daya na rana Kursiyya ta zo dakin Sa’adiyya cewa ta fito su tafi’. Cewa tayi gata nan zuwa, sai tayi sallah sannan. Bayan ta gama dinma tajima kafin ta mike. Gabanta takejin yana duka sosai, zuciyarta na nusar da ita kar tayi tafiyar, sai dai kuma wani bari na zuciyar nace mata taje, babu abin da zai faru face abin da Allah ya rubuta. 
Cike da kwarin guiwa ta mike, taja kofar dakin nata bayan ta fita, sannan ta nufi waje. Ta samu Kursiyya da Zabbau tsaye bakin mota sunajiran ta. Babu tunanin komai ta shiga motar, sannan su ma suka shiga, dreba yaja motar suka tafi. 

Tofa! Kome zai faru daga nan.shin zasu samu nasarar wannan mugum kudurin nasu? Idan har suka yi nasara me zasu fada wa al’ummar masarautar bayan a gaban idanuwan kowa suka tafi da gimbiya Sa,adiyya.’ Wane irin mataki ne Boka Fansi zai daukar mata.Hmm
Bamu shiga ko ‘ina ba, yanzu shirin zai fara.muje zuwa


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *