GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 23
A gabansu Boka Fartsiya bayyana. ldanuwanshi jajur ya kalli Kursiyya yaga yadda ta sunkuyar da kanta kasa. Cikin dakakkiyar muryarshi yace
“Kursiyya karki taba gigin kawo min wargi a cikin shaani na. Ta yaya ina fada miki abu ba zai yiwu ba amma kina sake tuhumata? Kursiyya ki tashi ku tafi ku bar wurin nan yau. Aljannu sunyi tsananin fushi daku, basa son ganin ku. Zasu iya aikata komai a kanku a yanzu matukar baku tashi kun tafi ba.”
Sosai jikin Kursiyya yake rawa. Dakyar ta iya bude bakinnta ta ce,
“Me yayi zafi haka ya Bokana? Ka sani cewa nayi imani da kai. Na yarda da kai. Babu abinda za ka fada mini na iya ketare shi. Amma ka sani alfarma ce nake nema a wannan karon.don kawari ne na daukar ma ’yata kan cewa duk yadda zanyi zanyi don ganin ta mallaki Yerima Abu sufyan a matsayin mijinta. Ba don komai ba sai don sanin ina da kai. Na tabbata kai din mai cika mini duk wani aiki da nake sone. Amma ka gafarta mini. Dan ban zaci abun zai bata ranka ba.” “Kursiyya! ”
Ya ambata da karfi. Ta daga kanta ta kalle shi sannan ta duke gabanta na cigaba da faduwa.
“Ba gagararmu wannan aikin zaiyi ba. Yaron ne zai gagare mu. Bakidaya ban ga hanya mai bulewa ba. Tsananta abun yasa aljannu sukayi fushi dake, domin kuwa ba karamin raunata za suyi ba matukar suka dage game da alamarin wannan Yeriman. Saboda haka ku tashi ku tafi tun ba suyi muku feshin wuta duk ku tattalbe ba. Ku tashi ku tafi? kwa dawo
wani lokacin! ” ‘
Da hanzarijiki a mace Kursiyya da Zabbau suka mike. Bayan ta ajje mishi kudinshi suka nufi barin wurin, ko waccensu sai sake sake take yi a cikin zuciyarta. Basu fasa zancen ba har sai bayan sun isa gida. Kursiyya ta fara ce ma Zabbau
“Wai Zabbau yanzu miye abun yi? Ni fai kam yanzu ban san kuma abin da zan fada wa Hafsa ba. Ga shi na mata alkawarin cika mata akawarinta ta hanyar mallakar zuciyar Yerima Abu Sufyan. Yanzu kuma sai ince mata wai ba zaiyiwu ba? Gaskiya da sake Zabbau ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, fuskar nan tata sum-sum tana kanne ido bayan ta
dubi hanyarkofa. Ta dawo da dubinta ga Kursiyya,
“Ranki shi dade, bana so muyi abin da zai iya jawo mana matsala. Ni ina ganin tun da har
Boka Fartsi ya ambaci abun ba zaiyiwu ba, me zai hana kawai mu hakura? Ki san yadda zaki kwakkwafi Hafsa ‘yarlele, na tabbata zata fahimce ki. Ki mata wayo ranki shi dade. Duk yadda za kiyi kiyi don ganin ta manta da duniyar Yerima Abu Sufyan. Ko ya kika gani?”
Shiru jim, tayi, kafin tace,
“Kin kawo shawara mai kyau Zabbau. A cikin shawararki nima sai wata shawarar tazo mini. Kawai zan koma wurin Boka Fartsi gobe, ya san duk yadda zaiyi domin ganin ya fitar ma Hafsa da soyayyar wanann tsinannen Yeriman daga zuciyarta. Kin ga idan aka fitar kowa ma ya huta.”
Murmushi zabbau tayi, “Hakan shi ne daidaida girman kujerar Fulani Kursiyya. Ko mu tashi mu tafi yanzu ne?”
“Ba zaiyiwu ba yanzu Zabbau. Kin manta a yadda muka baro Boka Fartsi cikin fushi .Mu bari dai har goben. ”
Da wannan shawarar Zabbau ta mike hade da nufar bangarensu. Hannunshi ya dora a bisa kafadar Yerima Abu Sufyan. A hankali Yeriman ya zare hannun daga bisa kafadarshi, yana furta,
“Ka bar ni kawai Shaheed. Ni kadai na san radadin da zuciyata keyi mini haryanzu. Ni kadai na san irin azabar da take ciki a halin yanzu. Ban taba gasgata cewa tausayi kan zama soyayya ba sai a wannan karon. Ban taba yarda so cuta ba ne saida cutarshi ta kama ni. Ban taba dandana dacin mutuwa mai tsananin wannan ba. Rayuwa tayi minikunci a lokaci guda. Ban san wane hali zuciyata zata shiga ciki ba idan har ta cigaba da shanye wannan damuwar. Wallahi Shaheed ina kaunarta, ina kaunarta da dukkanin zuciyata. Ina son Halima so na gaskiya. Ban san me yasa ta tafi ta barni ba. Ban san me yasa bata nemi mu tafi tare ba…”
Da sauru Shaheed ya saka tafin hannunshi ya toshe ma Yerima Abu Sufyan baki.
”Haba Yerima.’ Kar damuwa ta saka fadar maganganun da basu cancanta su fito daga bakinka ba. Kar ka bari shaidan yayi nasara a kanka. Mutuwar ta wajibi ce. Da ni da kai nan duk zamanjiran ta muke yi. lta ma Halima ba gaggawar tafiya tayi ba. Lokacinta ne yayi. Don haka don Allah ka cure wa kanka damuwa. Kayi mata addua ita tafi bukata, ita ce kadai soyayya gare ta a daidai wannan lokacin.”
Babbar yatsarshi data kusa da ita yasa ya gage guntuwar kwallar data fito a idanuwanshi duka biyun. Yace,
“Ba zaka gane ba Shaheed. Ba zaka gane irin tururin da zuciyata keyi mini ba. Haryanzu na kasa aminta da mutuwar Gimbiya Saadiyya.bane Gani nakeyi kamar ba gaske bane. ldan ma
da gaske ne kamar dai akwai makarkashiya.” Cikin sauri Shaheed yace,
”Ka daina duk wani tunani yerima, lokacinta ne yayi kuma ta amsa kiran mahaliccin ta. ”
“Haka ne Shaheed. Amma fa da ace zan fada maka wasu “yan abubuwa da suka faru a daren da zata rasu kai kanka sai ka shiga shakku. Shaheed tamkar fa yarinyar tasan dama zata rasu. ”
“Wannan kuma wani iko ne daga Allah. Wasu fa kamar suna ganin alama. ” Shaheed ya fada yana kokarin ganin ya kwantar ma Yerima Abu Suryan da hankali.
“Shaheed, am sorry to say, gaskiya ina zargin wannan Fulani Kursiyyar ita da ’yarta. Sosai jikina ke bani tabbacin suna da sa hannu a cikin mutuwar Halimatu. Saboda daren da zata rasu ta ce mini wai sunje wani wuri ita da Umma, sai dai ba zata iya shaida komai game da wurin da sukaje din ba. Kuma a cikin maganar da takeyi mini din ne take sako alamomin mutuwa. Daga cikinsu har tana ce mini kar in yarda da duk wani abu da zasu fada mini. To me take nufi? Su waye? Sannan mini duk wani tunani da zanyi a kanta ko mafarkinta zai iya zama gaskiya. In yarda da abin data fada mini, watakila zaiyi amfani. Shaheed ka fada mini, duk hakan ba yana nuni da akwai wata illa da ta hango suna gina mata ta karkashin kasa bane?”
“Ka fada mini, shin ba zasu iya iIIata Halimatu ba ko don ganin Hafsa ta mallake ni a matsayin mijinta ba?”
Shaheed yayi shiru yana jinjina lamarin. A wannan gabar kam ya fara gasgata maganar Yerima. Yana cikin wannan tunanin yaji Yerima Abu Sufyan ya cigaba da cewa
“Kuma wallahi ba zan taba auren Hafsa ba. Hafsa bata cikin irin matan da suke burge ni. Yarinyar da bata da tarbiyya ma me zanyi da ita? Me ake ci da mace marar aji maiyi ma saurayi kuka, saurayin ma wanda baya kaunarta? ldan kuwa harzatona ya tabbata ba zan barsu ba. Zan yi duk iya kokarina don ganin na kwatar wa gambiya Saadiyya fansa. Wallahi ba zan kyale ba!”
Ya fada cike dajarumta, idonshi kafe yana kallon wuri daya.
Shaheed ya gyada kanshiyana tunanin tsananin kaunar da Yerima Abu Sufyan yake ma Gimbiya Sa’adiyya a lokaci guda. Mutumin da k0 kadan mata basa gabanshi, amma yau shi ne ke neman zaucewa akan soyayya.
“Ka san me.Akwai abu guda daya wanda zai iya tabbatar mana da zarginmu.” Cikin sauri Yerima Abu Sufyan ya ce,
“Na san ko mene ne Shaheed. Kana nufin idan aka kawo zancen in koma wa Hafsa?”
Daga kai Shaheed din yayi yana kallon shi.
“Na tabbata zasu kawo din kuwa. ldan kuwa har suka kawo zasu tafka babban dana sani,
domin kuwa duk iya mulki da sarautar da Kursiyya ke takama da shi saina yaga su. Sai na
cire kunyar Maimartaba Sarkin Bilba na wulakanta Kursiyya da wannan munafukarkawar
munafurcin tata. Sannan akarshe ita Hafsa in nuna mata ita ba komai bace. In nuna mata cewa ba koyaushe bane asiru‘ yake tasiri a kan mutum ba.”
Hmmm