GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 23

GIMBIYA SA’ADIYA 






CHAPTER 22



Haka aka cigaba da zaman gaisuwar Gimbiya Saadiyya bayan an binne ta. 
Sai da mai martaba ya shiga dakiyaji wasu irin zafafan hawaye na zuwa mishi. Ya koma ya tura kofar hankali ya rinka kuka, yana yi yana tuna mahaifiyar Sa’adiyya da ita kanta Saadiyyar. Irin gubar data hadiya tun tana yarinya Kenan
“Kiyafe mini Halimatu. Hakika na tafka babban kuskure zuba idanuwa da nayi ana muzguna wa rayuwarki. Kinga jarrabtar rayuwa tun kina kankanuwarki har kika girma. Sharri da makirci kaIa-kala kuma duk na san gaskiya amma gudun bacin ran wasu inaji ina gani nake kware miki baya. A yau ga shi na rasa ki, rashi na har abada. Kin tafi kin barni, kin 
bar masarautar nan, kin bar duniyar ma baki daya. Allah gani gare ka ya Allah. Allah ka saka ma wannan baiwa taka ga duk wanda take da hakki akanshi Allah yaji kanki Halima yasa 
mutuwa hutu ce a gare ki.” 
Yayi kwanciyar rufda ciki yana kuka sosai tamkar ba shahararren sarki Sani ba. Yanaji ana 
kwankwasa kofar amma yaki cewa ko da uffan. Muryar Kursiyya yaji tana fadin, 
“Mai martaba magana nake so muyi dakai. Yau fa mako guda ke nan da rasuwar yarinyar nan amma haryanzu ka hana ma kanka walwala. Haba mana, kar kaba mu kunya. Kamar dai ba sarki ba? Yo k0 dai ni na mutu ai ba zaka yi irin wannan damuwar ba. Ni dai don Allah ka bude mini magana nake so muyi da kai. ” 
Duk da yadda yakejin zuciyarsa na masa zafi amma baya da zabin da ya wuce yabi 
umumin Kursiyya. Ya mikejiki ba kwariya bude mata kofar ta shigo sannan yaja ta ya rufe. 
Bayan ta zauna a kusa da shi ta dubi yadda idanuwansa suka kada tamkar ba shi ba. Ta dan 
yi kasa da murya sannan cikin kisisina tace “Ranka ya dade waiya ake cikigame da bawan Allahn nan?” Bai dago kanshiya kalle taba yace, “Waye kenan?” 
Mai martaba ina nufin Yerima Abu Sufyam. Tun da dai AIlah bai kaddara Sa’adiyya zata zama tashi ba sai nake ga ai bai kamata a bar shi a haka ba.” 
Bai ko tanka mata ba, saboda a ganinshi bai kamata a tado wannan maganar a yanzu ba, duka duka sati daya ne da rasuwar Halimatu, amma ga shi Kursiyya na kawo mishi wata 
maganar da sam bai tsammaci zuwanta a daidai wannan Iokacin ba. “Mai martaba magana fa nake maka. Na tabbata yanzu mahaifinshi ya fara tunanin nema masa wata ‘yar. A gani na dasu tafi bare su nema ai gwara a hada shi da Gimbiya Hafsa, tun da tajima da nuna raayinta gare shi. Na tabbata ba zai butulce ba, saboda da Sa’adiyya da Hafsa duk daya ne, jininka ne su duka biyun.” 
ldanuwanshi yaji sun cika tafda kwalla, ya dafe kanshi da yajima yana sara mishi. A hankaliya fara magana, 
”Fulani Kursiyya ina so ki fahimci wani abu guda. Halimatu fa yata ce ta cikina wacce ta rasu a Iokacin da nake tsananin kauna da tausayinta. A ganin ki mutuwarta bata sosai mini rai ba? Kina ganin kamar mutuwar Halimatu zata iya  daga zuciyata? Na tabbata har abada ba zata tice ba. Ba zan taba daina rokon Allah gafara a kan halin ko’inkula dana 
nuna mata ba. A yanzu ne nakejin kaunarta na dada shiga dukkanin zuciyata. A tunaninki a 
cikin mako guda kawai zan Iya mantawa da ita? Kina ganin kamar ban yi abin kunya ba 
idan na kira Sarkin Kubaisu a kan maganar auren Abu Sufyan tsohon wanda marigayiya 
Sa’adiyya zata aura ba? Haba Kursiyya! Ban zaci kalamin nan zasu fito daga bakinki ba. Ashe ma dai murna kike da tafiyarta?” 
Tuni hankalin Kursiyya ya tashi. Duk sai ta tsargu, taga kamar asirinta na dafda tonuwa. Cikin rawar murya tace, 
“Kayi hakuri mai martaba ni ba nan na dosa ba Dama gani na yi kar muna nan zaune sai dai muji Iabarin auren yaron. Kuma ga shi yana da hankali na yaba da kyawawan dabiunshi. K0 kadan ba zan so ya kufce daga zuriar masaraurar nan ba.” 
Yayi shiru daga nan bai kuma ce mata komai ba. 
Tajawo shi jikinta amma ya kufce. Ta sake jawo shi, cikin marairaicewa ta ce 
“Ka gafarta mini mai martaba. Wallahi ban yi don in bata ranka ba. Kayi hakuri, ba zan sake tayar da maganar ba.” 
Ajiyarzuciya ya rinka saukewa ajikin nata, hakan ya bata tabbacin ba yadda ta zargi abun ba ne ya kasance. Sunjima a haka kafin ta zare jikinta daga nashi. Ta mike bisa 
kafafuwanta ta doshi barin dakin. Cikin sanyin murya taji yace, “Fulani Kursiyya!” Ta dakata hade dajuyowa ta kalle shi. “Dawo kizauna.” 
Babu musu kuwa ta dawo ta zauna kanta a sunkuye kasa tana wasa da zoben zinaren dake yatsarta. 
“Fulani Kursiyya hakan bashi yake nunar dana ki amince wa maganarki bane. Abin da yake zuciyarki tabbas hakan ne ya dace a yi, sai dai kuma babbar matsalar bai kamata a tayar da maganara yanzu ba. Bani kadai ke da tabon mutuwar Gimbiya Sa’adiyya ba. Ba a iya masarautar nan ne abun ya tsaya ba. Ina da yakinin al’ummar Kubaisu ma abin ya girgiza su. Saboda mutuwar Halimatu abu ne mai zama rai, irin mutuwar gaggawace keda wuyar a manta da ita. Su kansu idan sukaji na tada maganar auren a yanzu za su iya kokonto a kan anya kuwa na damu da rashin Halimatu?A saboda haka na yanke nan da mako guda, kin ga a daidai Iokacin Halimatu tayi sati biyu da rasuwa kenan’, sai in tinkari 
Sarkin Kubaisu da maganar. Kamar hakan zaifi ai k0?” 
A cikin zuciyar Kursiyya murna ce fal da farin ciki. A zahiri kuma ta bata fuskarta gami da cewa, 
“Sati guda yayi kadan mai martaba. Ni ma sai da kayi maganar naga rashin dacewar hakan. Bai kamata ba tun yanzu a tada batun auren Gimbiya Hafsa da Yerima Abu Sufyan.” 
Mai manaba yayi murmushin karfinn hali, 
“Rashm Gimbiya Sa’adiyya ai ba shi zai sa mu zira ma Hafsa idanuwa muna kallo ba tare da an aurar da ita ba, Dole za mu so a kai ta dakin mijinta. Don haka ki fada mata ta zauna a cikin shiri, In sha Allahu aurenta da Yerima Abu Sufyan ba zai wuce wata guda mai zuwa ba.” 
Kursiyya kasa boye farin cikinta ta yi. Ta dago kanta da murmushi kunshe a fuskarta. Ta 
dubi maimartaba tace, “Har ma ka ari bakinsa kenan ranka ya dade?” Sarki Sani ya dube ta a tsanake, 
“Sarkin Kubaisu bazai taba ketare duk maganar da zance mishi ba. Idan gobe nace a daura auren Abu Sufyan da Hafsa to hakan za a yi. Kawai dai na duba ne naga bai dace a gaggauta ba. Kamar yadda na miki alkawari in sha Allahu nan da mako guda zan tinkare shi 
da maganar. Saimu yi fatan Allah ya sa alkhairiya kuma nuna mana Iokacin lafiya. ” “To ameen maimartaba. Bari in tashi in tafi, ina da baki.” 
Daga haka suka yi sallama. Cike da doki Kursiyya ta aika sako a kira mata Zabbau domin tana so duk dare yau sai sun ziyarci Boka Fartsi. Tana so a gane mata ko akwai aure tsakanin Hafsa da Yerima Abu Sufyan. 
To jama a ku dakace ni. 

Long time bamu hade baWai tun da muka dauko wannan taliyar kun taba tunanin Amrah ba ta taba dauko muku abin da ya faru bayan haihuwar Gimbiya Saadiyya ba.’ Shin ta yaya aka yi (a tashi babu uwa.’ Me ya 5.: Fatawalwar nan ke yawaita cewa tun tana cikin ciki Kursiyya ke azabtar da itaIA wanna hali mahaifiyar Saadiyya take? Wane irin tin amana ne Kursiyya ta yi ma boka Fartsi wand: harya karya dadadden sihirin da ya ma Saadiyya.’ 

A yanzu da Kursiyya ta ta tafi wurin Boka Fartsi ko za 3 date? Men :19 makomar aljana ko fatalwa? 

Akwai fa sauran labari, don zan iya cewa ko rabi ba mu yi ba bar yanzu. 


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *