GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 25

GIMBIYA SA’ADIYA 






CHAPTER 25






Sallamce sallarshi kenan ya dubi Shaheed da duk damuwa ta gama bayyanuwa a saman fuskarshi. 
“Shaheed na rasa me yasa duk kabi ka damu kanka. Ina so ka gane nifa ba wai  burin na na bakanta ran iyayena a kan rashin bayyanuwata a gabansu bane duk yinin yau. Zan tabbatar maka da hakan idan kaga yanzu na mike zan koma gida, ba tare dako shafa’i da wutri nayi ba.” Ajiyar zuciya Shaheed ya sauke yana duban Yerima Abu Sufyan, 
“Ranka shi dade a gabanka kiran da Fulani tayi mini ya zarce goma, duk tana sake tambayana k0 naji wani Iabari daga gareka. Wallahi Yerima suna cikin damuwa sosai. Shi yasa duk kaga nima na damu. “
“Ka kwantar da hankalinka to. Aiyanzu zan tashi in tafi. ” “Kai kadai?” 
”Ni kadai mana. Ko kana so mu tafi tare ne asirinka ya tonu a ce dama can kasan inda nake?” 
Murmushi Shaheed yayi ba tare da yace komai ba kawaiya mike. “Nima zan wuce gidanmu, suma ce musu nayi na tafi Birnin Banuut.” “To shi kenan Shaheed. Na gode sosai.” 
Daga haka suka rabu, kowannensu ya kama hanyarshi. Yerima Abu Syfyan bai waniyi nisa sosai ba yaci karo da fadawan gidansu kusan mutum bakwai sunyi lakwas. Har rige-rigen yi masa magana suke yi “Ranka ya dade ina ka shiga tun dazu sai nemanka akeyi? Bakidaya hankalin masarauta ya tashi? Fulani na can sai zubar da kwallanta takeyi. Mai martaba kuwa sakar zuciyake tayi. Rashin ganin kaba karamin tashin hankalin al’umma yayi ba. Allah daiya sa lafiiya.” 
Cikin halin ko’inkula yace, “To ba gani ba yanzu? Mai martaba Sarki Sani yazo ya tafi?” 
Caraf Zailani ya ce, 
“Yazo tabbas. Yazoda nufin a daura muku aure kai da ‘yarsa a yau din nan. To kuma amma yallabai baa naji an ce wacce zaka aura din ta rasu ba? Ko dai watace daban?” 
Harararshi Jazuli yayi, “Zailani ka cika fadi koba,a tambaye ka ba. Yanzu kai a ina ka san wannan zancen?” Zailaniya ya dafe bakinshi ba tare da ya kara cewa uffan ba. “Aure kamar yaya? Shi mai martaban ne ya fadi haka k0 kuwa sarkin Bilba dinne ya nema?” 
Zailaniya ya danyi kamar zaiyi magana sai kuma ya kalli Jazuliya yayi shiru. Murmushin gefen baki Yerima Abu Sufyan yayi. Ya san yadda zaiyi, in dai har Zailani ya san wani abu a kai to tabbas zai rattaba mishi komai idan sun koma gida. Biyu daga cikinsu ne suka yigaba domin isar da sakon ganin yarima. Yayin da sauran suka karisa tare da shi, babu mai magana a cikinsu. 
Kabbara Sarki Abdurrahmanu yayi a Iokacin da suka sanar mishiganin Yerima Abu Sufyan. Duk da dai dama jikinshi baya ba shi akwai damuwa, amma dai duk da haka ba zai samu kanshi da kwanciyar hankali ba. 
“Fulani Maryama da mana fada miki Yeriman kiyana cikin kwanciyar hankali. Domin kuwa 
Abu sufyan ba yaro bane ba bare ace ya bata. Kin ga kuwa zancena ya tabbata.” 
Bayan ta share kwallarta tace, 
“Mai martaba kasan zukatan maza da mata ba daya bane. Damuwa ba zata taba gushe mini ba har sai sadda na samu kyakkyawan bayanigame dashi. Yanzu da naji din ba gashi na share kwalla ba har ina murmushi?” Ta saki tattausan murmushi. Shima mai martaba murmushin yayi na kasaita yace, ”To madalla. Haka ake so ai.” 
Yana gama rufe bakinshi Yerima Abu Sufyan ya shigo fuskarshi ba yabo ba fallasa. Domin kuwa Zailaniya gama zayyane masa duk abin daya sani dangane da zuwan Sarkin Bilbah. 
Ya tsugunna a gaban iyayenshi ya gaishe su, cikin ladabi ya fara ajje daidaitattun kalamanshi, 
“Mai martaba da farko dai ina mai neman afwarka a kan fita da nayi ba tare dana sanar ma 
kowa ba. ” “Babu komai Yerima, an yafe maka.” Ya saki ajiyar zuciya sannan yajuya ga Fulani Maryama, “Umma Fulani…” Ta dakatar da shi, 
“Ya isa haka Yerima! Ni ba kayi mini laifin komai ba. Domin kuwa da namiji kake ba mace ba. Mace itace ‘yar kulle. Kawai dai bana so kana yin nisa da gida ba tare da dan rakiya ko yan rakiya bane Koda ace Shaheed ne ka nema ku fita tare. Domin kuwa wannan zamanin 
Ba a dauki farautar rayuwar mutum a bakin komai ba. Wasu mutanen abin da suke so kenan, sai su faka ido har su samu nasara a kanka.” 
Yajinjina kanshi Cikin ladabi ya amsa da, “In sha Allahu za a kiyaye. ” 
“Sannan abu na gaba, ka daina fita ka bar wayarka. Kaga yau hankalina ya kadu sosai. Da ace akwai waya a hannunka ina kira zaka dauka. Kaga kuwa hankalina zai kwanta.” 
Shima din za a kiyaye Umma.” Ta murmusa cike dajin dadi, 
“To masha Allah! Kaje ka samu kayi wanka kaci abinci. Sai kazo mahaifinka zaiyi magana da kai. ” 
Shiru yayi a wannan gabar bai ce uffan ba sai dan sosa kunnenshi na haggu da yayi 
sannan ya mike a bisa kafafuwanshi. 
“Akwai muhimmiyar maganar da nake son muyi da kai. Kayi komai a cikin Iokaci kafin na shiga turaka.” “To Abba. ” 
Ya furta hade da barin dakin yanajin tamkar tafiyan kafafuwanshi ba zasu iya daukar gangar jikinshi ba. Sai dai a yadda yakeji zuciyarsa na masa tururi, babu abin da zai kasa fada wa mai martaba. Ba yajin zai iya yin shiru ya cucizuciyarshi. Alkawarin nan dai daya dauka saiya cika shi. a 
Yana isa kofar dakinshi zai shiga ya rinkajin wata irin kara gadan-gadan mai kama da cidar hadari. A hankaliya taka ya shiga Cikin dakin, saiyaji tamkar a saitin kunnuwanshi ne karar take. Ya tsaya cak yana tunanin silarkarar, ba wai don ya tsorata ba. Da karfiyaji an banka kofardakin an rufe tamkar iska ne ya rufe kofar. Cikin Iokaci kadan kuma ya dainajin karar sai wani haske daya cibre wuri daya yana kokarin tinkaro shi. 
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” 
Ya ambata a bayyane. A take saiga wannan hasken ya zama wani irin tsuntsu maijajayen idanuwa. 
A hankali ya rinka saukowa harya iso gaban Yarima Abu Sufyan sannan ya tsaya cak. Duk iya dauriya da jarumtarshi sai daya dan tsorata a yanzu kam. Cikin karfin haliya ce, “Waye kai kuma me kazoyi wurina?” 
Shiru tsuntsun nan bai ko motsa ba, hakan yasa ya sake maimaita tambayarshi a karo na biyu. Sai a sannan ne tsuntsun yayi girgiza da karfi, sai ga wata takarda ta fado daga jikinshi. A hankali kuma ya cigaba da tafiya, sai da yaje daidaijikin bango sannan haske ya sake mamaye wurin 
A take kuma hasken ya gushe, tsuntsun ma sai babu ko alamarshi. 
Cike da mamaki Yerima ya tsugunna zai dauki takardar, duk kuma saiya tsorata, ya samu kanshi da kasa dauka. Gabanshi sai tsananta buga wa yakeyi ya nufi bandaki, yayi wanka sannan ya yi alwalla ya fito. Bayan ya gabatar da sallar shafa ‘i da wutri da bai samu yayi ba, yayi tasbihi sannan yayi addua sosai. 
Yana gamawa gaba-gadi ya tinkari takardar nan da bismillah kunshe a bakinshi ya bude. “ 
Rubutun ajami ne a cikin takardar sai zanen wani tsoho fuskarshi cike da suma. Ga kuma wasu mata guda biyu daga gefenshi an zana, kowaccensu fuskarta kunshe da murmushi sai dai babu wanda zai iya gane asaIin fuskokin su waye. 
Da mamaki sosaiyake sake duba zanen, daga can kasansu kuma ya ci karo da wata yarinya 
kwance an zana ta, ga wuta daga samanta kamarza ta zubo mata. Bayan ya gama duba zanunnukan ya koma kan rubutun dake jiki din, ya fara karantowa, 
“Ka bi duk abin da zuciyarka ta saka maka, domin kuwa gaskiya ne. Kayi amfani da iliminka domin tabbatar da gaskiya da kuma gusar da karya. Wannan wata dama ce a gare ka. Kar kayi sake Abu sufyanu. Kar kayi sake wannan damar ta wuce ka. Taimako ne, jihadi ne maigirman gaske. Zan kasance tare da kai a duk Iokacin da kake bukatar wani taimako daga gare ni. Kar kaji tsoro, shakku ko kuma kokonto a kaina. Ba zan cutar da kai ba, ba kuma zan taba bari a cutar da kai ba.” 
Kanshi ya dafe a daidai Iokacin da ya kaikarshe. Gabanshi na tsananta dokawa, yana al’ajabin wannan abu. A hankali ya tauni Iebonshi, ya dan lumshe idanuwanshi. Da rashin kuzariya samu dakyarya ninke takardar, yajawo Iokar madubinshi ya jefa, sannan ya mike cike da kasala ya nufi barin dakin, domin ya tabbata mai martaba na can na zamanjiran shi. 
Tun daga nesa mai martaba ya hango rashin kuzari a tattare da Yerima Abu sufyan. Bayan ya iso a gabanshiya rusuna ya gaisar da shi, sannan ya koma nesa kadan dashi bisa tumtum ya danjingina kadan, yace, 
”Na kammala komai mai martaba.” Sarki ya dago kanshiya dube shi, ”Har abinci kaci?” Sosa kanshiya yi, “Nasha kayan marmari dai Abba. Kafin in kwanta zan sha coffee.” “Toka tabbatar daka sha, kar ka kwana da yunwa.” “In sha AlIahu.“ Ya fada sannan ya sunkuyar da kanshi yana sauraren abin da zai fito daga bakin mahaifinshi nashi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *