GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 30

GIMBIYA SA’ADIYA




CHAPTER 30






Daidai sallar magriba suka dira masarautar Kubalsu. Sosai Hafsa ta sha jinin jikinta, ganin girman masarautar, ta zarce tasu nesa ba kusa ba. Da gudu fadawa da kuyangu suka iso bakin motar, sai da aka fara bude wa Yerima Bukar ya fita sannan Hafsa ma ta fito sai faman shan kamshi take. Amma fa adonta ya fizgi jama,a, da an ganta an san yar gayu ce wacce ta amsa sunanta. Wasu kuyangu guda biyu suka kamo kasan alkyabbarta da keja kasa sosai suka rike. Sai wasu guda biyu kuma suka shiga gabansu, sune za su musu jagoranci zuwa bangaren su Hafsa. Da kuyangun da aka hada Hafsa dasu daga Bilbah suka mara musu baya. 
Kanta sunkuye suka isa daidai bakin kofa. Da karfi taji an fizgo fuskarta an dago sama. Tana daga kanta taga kyakkyawar mace mai zubin Larabawa‘ Tayi ado Clkin jan Ieshi mai matukar tsada da daukar ido, Ga wani tafkeken mayafi da ya hau daidai da kayan‘jikinta. Fuskar nan tata a tamke, babu ko alamun murmushi tace, “Ba kina murna bake amarya? Zaki gwammaci kida da karatu. Tun wuri ki nemi alfarmar a kaiki wani bangaren daban. 
Don zama tare dani sai kin kusa hauka. Kinji na fada miki. ” 
Sosai kalaman Jiddah suka tsorata Hafsa. Sai dai ta dake, a ganin ta zata ga wallenta idan har ta kyale ta‘ “Bana gudun duk wata masifa k0 tashin hankali. A shirye nake kyam, don naji Iabarinki ba tun yanzu ba. Don haka ga fili ga mai doki, saura sukuwa kawai ta rage.” 
Dariya Jiddah tayi sosai sannan ta tsagaita dayin ta. “Ban taba tunanin akwai wacce zata iya karawa dani Gimbiya Maijiddah ba, ko a mafarki. ldan ma zuciyarki ta riya miki haka kiyi gaggawar karyata tata, domin kuwa ba gaskiya bane.” Su dai kuyangu sun zura na mujiya suna kallon sarautar AIlah. Dukkaninsu na Kubaisu sun san halin Jiddah. Bata da mutunci k0 kadan. Kuma da alama ita ma amaryar haka take. Lallai akwai kaIlo a wannan zama. Su saima abun ya burge su, fadan ‘ya ‘yan sarakuna, kuma dukkaninsu masujiji da kansu. Masu takama da sarauta. 
“Bana tsoron duk wani abu da zai faru. Muje zuwa. Kuma ki bamu hanya mu shiga.” 
Babu musu Jiddah ta matsa musu hanyar wucewa, sai dai fuskarta kunshe da murmushin 
da ita kadai ta san ma,anarshi. 
Kuyangun ne suka kai ta har dakinta, inda yaji ado kayatacce, kalar siminti. Har kurya suka raka ta sannan suka gabatar musu da kansu, cewa su zasu cigaba dayi mata hidima. Babu dariya babu murmushi ta fatattake su. Saboda ba tajin ta a mood mai dadi. A wannan Iokacin ma zata iya marin wata idan ta zake mata. 
Suna tafiya ta fashe da kuka. Babu wanda ya cuce ta face kanta da kanta. Inda tun farko bata nace sai ta auri Yerima Abu Sufyan ba da duk haka bata tasa ba. Gashi nan abin daya 
kasance gare ta. Ta hada kanta da guiwa sai rusar kuka take. 
Da dare bayan isha,i sai ga Yerima Bukar ya iso. Yanayin tafiyarshi kadai idan ka kalla zaka fahimci akwai matsala. Ya iso gare ta yana Iayi. Kamar’ Ya fado bisa gado ta tattakura ta zame gefe don karya fado mata. Bin shi take da kallo, tana mamakin yanayinshi. Kamar dai a buge yake. Ta ayyana a kasan ruhinta. A hankali ya fara kokarin kusanto ta. Idanuwanshi ta kara kallo, ta tabbarar mankas yake. Ga wani irin wari da yake yi, wanda ta zargi cewa na giya ne, duk da dai bata da tabbas, don bata tabajin shi ba. Ta gaggauta daukar filo ta musu iyaka, sannan ta tashi da sauri tabar wurin. “Wai me kike nufi ne?” Ya fada cikin muryar mashaya. 
”Wallahl baka Isa ka afko min a Cikin maye ba. Kowacce mace
burinta mijin aurenta ya kusanceta a cikin hankalinshi. Sai nice nawa mijn zaizo mini cikin maye?AIIah ya isa daka aure ni. Munafuki katon banza.” 
Da gudunta ta fice daga dakin ta koma wancan dayan, sannan ta datse don karya dawo 
Tagumi ta zabga hawaye na zuba bisa kumcinta. Yau watanta biyu ke nan amma haryanzu bata san mene ne dadin aure ba. Bata rasa ci da sha ba. Sai dai kuma farin ciki ya mata kaura. Yerima Bukar sam bai san darajar aure ba. Idan aka cire miyagun kwayoyin da yake sha, bai san mene ne sauke hakkin aure ba. Idan zaije wa matarshi tamkar bunsuru yakeje mata. Da alama uwargidanshi Jiddah har ta saba da haka. Ita din dai ce abun yake ma radadi, don bata taba sanin cewa akwai maza irin haka da gaske ba. Tana cikin wannan tunanin taji takun amintacciyar kuyangarta Dije. “Ranki shi dade…”
Hafsa tayi saurin share kwallarta. “Dije, yaushe kika shigo.” “Tun dazu nake sallama shiru ba a amsa ba. Lafiya dai ko Aunty?” 
Kaman tanajiranta ta fashe da kuka hade da afkawa ajikinta. ’Subhanallahi! Ranki shi
dade Iafiya? Me ya faru?” 
“Dije mene ne ma bai faru ba. Da ace nasan a matsayin da nake yanzu zan shigo gidan nan da tun ana daura aure nai guduwata. Babu wanda ya cuce ni sai maimartaba.
“Ki daina fadan haka Aunty. Kaddara ta rigayi fata. In shaa Allahu komai zai daidaita.” 
“Dije… Ina cikin damuwa. Ga dakon son wanda sam bai damu da niba. Na kasa cire Yerima Abu Sutfyan daga raina. Wallahi hargobe ina kaunarshi, ina burin hada ido dashi. Na tsani Yerima Bukar. Na tsani zama tare da shi.” Dukkan maganganun da Hafsa keyi kafa cikin kunnen Yerima Bukar, yayi bakam yana sauraren ta harta kai aya. Ya zaro idanuwanshi cike da mamaki. A wani bangaren na zuciyarshi kuma yaji dadi kwarai tun da harya san wani weak nata. Dan haka zai cigaba da gara ta, yana cin zarafinta tun da dai ya gano bata kaunarshi. Fasa shiga dakin yayi yayi yawarshi ya tafi. 
Dije ta cigaba da rarrasar Hafsa, sai dai k0 kadan bata yi nasara ba. Domin kuwa Hafsa karajin tukuki kawai take yi a kasan ruhinta. 
‘Ina tsananm son ganin Ummana. Ina son inji duminta. Ina son gumin hawayena ya sauka a 
kafadarta, ta karanci tsan tsar damuwar da nake cikinta. ” 
Cikin tausayi Dije tace, “Hakuri za kiyi ranki shi dade. Tabbas ke da barin masarautar nan da sunan zuwa ganin gida sai kin haihu kinyi arba’in, haka al’adar masarautar take.” 
Dago kai Hafsa tayi ta kalli Dije. “Dije da gaske kike ko wasa?” 
Dije ta sauke aiyarzuciya. “Ranki shi dade k0 ina wasa dake ba zan miki irin wannan wasan ba, ballantana ma ba nayi. Gaskiya nake fada miki. Haka al’adar masarautar Kubaisu take.” 
Hafsa ta kara karfin kukanta, tanajin yadda zuciyarta ke dad’a zafi. Damuwa na kara dabaibaye ta. Tsanar Yerima Bukar da duka masarautar na kara ta’azzara a kasan ruhinta. 
Washe gari da sassafe Jiddah ta shigo. Babu ko sallama sai karar haurin duk abun daya tari gabanta take Hafsa taji. Ta bude idanuwanta da suka gama kumburewa. Ba tayi mamakin ganin Jiddah cikin kuryar dakinta babu ko sallama ba. Saboda ba yau aka fara ba. 
“Ke! ” Ta fada cikin raini da gadara. Hafsa ta sauke kanta bata tanka mata ba. Ta sake kiran ke amma ko kaIIo bata ishi Hafsa ba. Ta matsa dafda ita ta zunguro ta. A kufule Hafsa ta rike mata hannu sannan ta mike tsaye. “Shirye nake da dukkanin abin da kikeji. Daidai nake dake. Yadda kike ‘yar sarauta jikar sarauta nima haka nake. Baki fini da komai ba. 
Don haka ki farfado tun wuri ki san me kike. Ruwa ba sa’an kwando bane.” 
Cikin mamaki Jiddah take kallon Hafsa. “Lallai bakauya ta fara wayewa. Ke! Yaushe kika yi bakin mayar da magana? Yaushe ma duk kika san wayan nan kalaman? Lallai nayi sake. Nayi sake da karamar kwaruwa ke neman raina ni. Tun wuri ki gane, kigane cewa ni gimbiya Jiddah na wuce da ajinki. In banda tsautsauyi ma, me zaija mini hada miji da bakauya irinki? Dayake dai ni ba hada mu aka yi da Yerima ba. Shi da kanshiya ganni yace yana so. Ba wai auren huce takaici ba ne irin naki ba. ” 
Har tayi ta gama Hafsa ba tace mata komai ba, don sam bata iya fada ba. Duk iya rashin mutuncinta bata iya masifa ba. Jin Jiddah dai kawai take yi, ranta na tsanann baci. Zuciyarta na zafi Tama rasa abin da zatayi. 
“Abu biyu ne ya kawo ni wurinki. Na farko, an jima za muje. farfajiyar mai martaba zamu gaishe shi. Hafsa k0 kadan kar kiyigigin fadar wani abu wanda bai dace ba. Idan ba haka ba, wallahi za kigane kurenki. Don sai zama cikin gidan nan ya gagare ki. 
Abu na biyu, ban yarje miki saka hadimaina aikiba. Dazu na nemi Safare aka ce wai kin saka ta aiki, to ban amince ba. Kin ga dai ai an bawa kowa hadimanta k0? Ki kiyayi nawa. Ban sani ba ko dai hada baki kike sonyi dasu a cutar dani ba. To ahir dinki! Kurwata ta fi karfinki.” 
Tana gama fadin haka ta tsirtar da yawu ta fice daga dakin. 
Da karfi Hafsa ta fashe da kuka. Babu mai rarrasarta. Da a gida ne da yanzu Ummanta tayo kanta. Da yanzu ta hada kirazansu sunajin bugun najunansu. A nan kam bata da gata sai Allah. Kuma babu wanda zata fada wa damuwarta ya mata magani. lta ta kawo kanta. Sai yanzu ta yarda cewa ba Iaifin mai martaba bane, nata laifin ne. Da tun asali bata tirsasa sai an aura mata Yerima Abu Sufyan ba da duk haka bata taso ba. Shi kuwa Mai martaba yayi haka ne don bai da yadda zaiyi, tsabaryana son faranta mata. 
“Har abada ina kaunarka Yerima Abu Sufyan. Ba zan taba daina son ka ba har karshen 
numfashina.” Ta murmusa, hango hoton fuskarshi da tayi a cikin zuciyarta. Komai nashi burgeta yake. Har isasshiyar maganar nan tashi. Tana hango yadda yake ajje kalamanshi. Matsin bakinshi, idanuwanshi dake kara narkar da zuciyarta. Haka kawai saita tsinci kanta a shauki. 
Clkin kankanin Iokaci kuma sai farin cikin nata ya gushe. Tuna cewa ba zata taba zama matar Abu Sufyan ba har abada. Mata take ga Yerima Bukar, yayan Yerima Abu Sufyan. Kuma babu saki. Sai dai ko mutuwa. Tsanar da Yerima Abu Sufyan ya mata kuwa bata tunanin k0 Yerima Bukar ya mutu zai aure ta. Bai aure ta sadda take budurwa ba sai data zama ne zai aure ta? Ta share hawayenta. Ba ta da magani‘ Bata da mafita. Don haka ta koma ta kwanta, zuciyarta sai sake-sake take mata. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *