GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 31

GIMBIYA SA’ADIYA

CHAPTER 32

Tun bayan fitar Zabbau Kurstyya keta kai-komo a dakinta. Wasu Irin daskararrun hawaye takejisun yi tsaye cak a saman idonta. So takeyi su fito amma da alama basu da niyyar fitowa. Hakan ya sata koma bakin gado ta zauna. Zuciyarta cike da kuna. Ta dafe kanta, cikin bakin ciki to ashe dai da gaskiyar boka Fartsi‘. Da gaske Sarauniya Malmounatu tafi karfinmu. Da gaske bamu da karfin aikata komaiga Gimbiya Jiddah. Toni ya zanyi?A haka zan zura idanuwa ana zaluntar min ‘yarinya haka rayuwa zata cigaba ‘yata bata da wani ‘yanci a gidan aurenta?” 

Sai a wannan karon idanuwanta suka kyafta wanda suka ci karo da fitarguntun hawaye dake cikinsu. Rayuwa tayi wa Kursiyya kunci. Ita kanta ta sani tun da take a rayuwarta bata tabajin dacin rai irin na wannan lokacin ba. Bata taba cin karo da abinda ya dugunzuma zuciyarta ba irin wannan. 
Wayarta ta zare daga jikin chaji ta Iatsa kiran Hafsa. Bugu daya ta dauka. Da sauri ta zabura ta mike tsayejin yadda Hafsa ta karbi kiran, cikin muryar kuka. 
“Hafsana Iafiya? Meya faru dake naji muryanki wata iri?” 
Hafsa kara karfin kukan nata tayi. “Ummana banda lfy, yanzu haka ina dakin kula da marassa Iafiya na cikin masarautar Kubaisu. Umma…‘ 
Sai kuma tayi shim. Tana son fada mata halin da take ciki amma tana tsaro, ta tuna yadda Kursiyyar da Sarki Sani sukajaddada mata ta rike sirrin dakinta, don ko ta fada musu babu abin da zasu iya yi mata. 
“Hafsa bari kika yi? Na shiga ukuna ni Kursiyya.aikin wahala kikeyi ne a gidan?” 
Hafsa ta runtse idanuwanta cike da radadi da kunar zuciya tace, “Ko daya Umma. Bana aikata komai tun da nazo. Nima kaina ban san dalili ba.” Kursiyya ta gyada kanta. “Uwargidanki bata taba haihuwa ba k0?” 
Da sauri Hafsa ta bata amsa. Abun ku da mai irin halin juna, a take ta gane daga inda matsalar take. Ta fara sake-sake a cikin zuciyarta. 
“Kiyi hakuri ki daina kuka Hafsa. Zaki samu lafiya bada jimawa ba. Na tabbata za a baki kula sosai a Kubaisu, tamkar kina nan Bilbah. Na san ko nace muje mu duba ki mai martaba ba zai amince ba, saboda Sarkin Kubalsu zaiga kaman an raina nasu. Kiyi hakuri kinji?“ Sai data tabbatar ta rarrashi Hafsa sannan ta yanke wayar. Cike take da tausayin yarta, 
kawai bata da yadda za tayi ne da kamai gorin da za,a mata ta amince ta dawo da diyarta gabanta a matsayin karamar bazawara. 
A gaban boka Fartsi suka bayyana ita da Zabbau. A kagare take danjin yadda za suyi kuma. Babujimawa saiga shiya bullo a gabansu. Fuskar nan tashi kaman koyaushe babu annuri a cikinta. 
“Ina fatan a yanzu ba kya bukatan karin bayanigame da Sarauniya Maimunatu? ldan da! akwai to ina saurarenki. Menene baki fahimta ba a kaftarihinta da kika samu?” 
Cikin rawar labba Kursiyya tace, “Daidaikun abubuwa ne na fahimta ya bokana. Shin Ita 
Sarauniya Maimounatu bata da uwa?sannan wanne dajine sarki Jaheedu ke kaita? Me yasa yake kai ta? Naji ance kaf dabiunta irinna namun dawa ne, tajima kafin ta iya na mutane. Me yasa?” 
Boka Fartsiya gyada kanshi sannan ya runtse idanuwanshi a hankaliya bude. Ya hura hanci hade da taunar lebenshi na kasa. Yace, 
“Saraumya Maimounatu mutum ce sai dai ba kamar kowa ba, saboda akwai sirkin maita da mugun sihiri‘ da take dashi. Hakazalika tana da uwa kamar yadda kika sani ba a halhuwar mutum babu uwa. Na samu Iabari daga manyan aljannu cewa Sarki Jaheedu mutum ne mai tsananin kaunar matarshi kafin ta rasu. Hakan yasa tun bayan rasuwarta bai sakeyin wani auren ba. Sai dai abin da mutane basu sani ba shine, akwai Uwarbiyu da yake yawan kai mata ziyara a wani kurmuzun daji mai suna Dumburzu. Ya gano wannan dajin ne ta dalilin zuwar mishi da Uwar biyu keyi a cikin kownane barcinshi, ta nunar mishi da soyayya. a haka da haka har ta lubbace shi, taja shi har inda take rayuwa ita kadai a dokar daji. Uwar biyu ba mutum ba. Muguwar mayya ce mai tsananin asiri. ’ 
Sannu a hankali Sarki Jaheedu ya fara tarayya da Ita, har ta samu juna biyu, inda ta haifi yan biyu duka mata, kuma kamanninsu daya ko kadan basu da bambanci. Sai dai aka samu akaSI daya ta samu sirkin mutum, dayar kuma zallar mayya ce kaman mahaifiyarsu. A nan fa rikiciya fara shiga tsakaninta da Sarki Jaheedu. shi bai taba haihuwa ba, ita ma din bata taba haihuwa ba. Dukkansu sai suka dora soyayyarsu ga wannan ‘yan biyu. 
Bayan sunyi wayo ya nemi ta bashi yaranshi amma sam taki. Ta nuna ha tasan da wannan maganar ba. A karshe dai suka sasanta shiya karbi Hassanar mai suna Maimounatu, ya wa uwargidanshi data rasu takwara. Ita kuma ta dauki Usainar ta mata suna da Balkeesa. Kasantuwar da ma ita babu sirkin mutum ko kadan a jikinta. 
A inda uwar biyu ke rayuwa daga ita sai namun dawa. Ta zame musu tamkar uwa ko kuma shugabarsu. Duk abin data saka su sai sun yi. Abin data hana su kuwa basa tinkarar aikata shi. 
Tafiyar da Sarki Jaheedu yayi da Maimounatu sunyi yarjejeniya kan cewa zai rinka kai ta wurin uwar biyu ziyara, ya kuma amince da hakan. 
Wannan shi ne takaitaccen bayani game da abubuwan da baki fahimta ba a cikin rayuwar Sarauniya Maimaunatu.’ 
Nannauyar ajlyar zuciya Kursiyya ta sauke. Tanajin gabanta na tsananta bugawa. Boka Fartsi ya kara kallon Kursiyya a karo na biyu yace, “Sarauniya Maimounatu tafi’ karfina, tafi karfin duk wani tsafi nawa. Don haka ni ba zan iya yiwa diyarta komai ba. 
Amma ke Idan zaki Iya, ga fili ga mai doki Ku tashi ku tafi.” 
Cike da takaici Kursiyya ta mike, Zabbau ta mara mata baya. Shi kanshi Boka Fartsin ji take tayi mugun tsanarsa a daidai wannan Iakacin. Ga takaicin barin da Hafsa tayi. ga kuma takaicin babu wani mataki da zata iya dauka. 
Tun dawowan su gida ta kasa zaune ta kasa tsaye, a haka har mai martaba ya aiko kiranta. Sai data kikkimtsa kanta sannan ta tafi wurinshi. Gaishe shi tayi bayan ta zauna bisa. Sarki Sani ya karisa inda take. ya dube ta sosai hade da kamo habarta da hannun dama. 
“Kursiyya, ba tun yau na fuskanci sauyuwar yanayinki ba. Ba tun yau na gane kin ajje damuwa a cikin zuciyarki ba. Na fahimci tarin kunci a fuskarki, wanda na tabbata kai tsaye daga cikin zuciyarki suke.” Ya duka a gabanta. “Amma meya sa? Meya sa Kursiyya kika ajje damuwa a zuayarki bayan kin san kina dani? Ki fada mini kowacce irin matsala ce ni nan zan warware miki ita komai tsananinta. Na miki alkawari.” 
Duk yadda Kursiyya taso ta boye damuwar tata ta kasa. Bata san sadda ta fada a jikinshi ba, tana kokarin shanye kukan dake zo mata, amma ina, tuni mai martaba yajigumin hawayenta a kafadarshi. Da sauriya hau bubbuga bayanta tamkar wata karamaryarinya. 
“Ki daina kuka Kursiyya, don Allah. Ki daure ki fada mini matsalanki. Kuka bai da wani amfani face ya darsa miki wata cutar.” 
Sai a sannan Kursiyya tayi kokarin raba gangarjikinta data mai martaba. Ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Tana gudun hada ido da shi kuma ta masa karya, don ba wuya zai iya gane ta.” 
“Ranka ya dade, yau kimanin wata biyu kenan da auren Grmbiya Hafsa amma tun bayan nan na gaza samun nutsuwa, zuciyata a kullum fada mini take ‘yata Hafsa na cikin damuwa. Idan barci na kwanta kullum sai nayi mafarkinta wai tana neman taimakonmu. Nayi duk iya kakarina don ganin na fahimtar da zuciyata, na karyata ta, amma abun ya gagara. Kullum dada yawaita ma abun yakeyi. Wannan daIiIi ne yasa nake cikin damuwa. Na kasa kwantar da hankalina. Kuma ban fada maka ba don nasan babu abin da zaka iya yi min daya wuce ka bani hakuri.” Ta dakata daga nan tana karantar yanayinshi. Rasa ma abinda zai ce mata yayi. Bai san ta inda zai fara ba, sai dai k0ma ta hali kaka yana son ya kwantar ma Kursiyya hankali. 
Ya kama tafin hannunta na haggu ya saka a akin nashi na dama. Yace “Wannan kuma duk 
sharrin Shaidan ne Kursiyya. Kin san shi Shaidan yaki jinin yaga an zauna Iafiya. Ya tsani yaga anyi aure bai daura damuwa a zukatan mutane ba. Kinga aiyanzu idan kika nemi a raba auren shiya samu yadda yake so, yayi galaba a kanmu. Sannan a karshe ya raba zumunci, dadadden zumuncin dake tsakamna da Sarki Abdurrahmanu. Ya mayar da Hafsa bazawara wacce ba lallai ba ta auru. Kin san tsarin gidan sarauta, kinfi kowa sani. Abun zai zama abun gori garemu da ita kanta Hafsar. Don haka kiyi hakuri, na tabbata babu komai wallahi, Hafsa na samun kulawa sosai, tamkara nan take. Ki kwantar da hankalinki, idan ba kya tare da ita aivAllah na tare da ita. Kuma duk son da kike mata Yafiki, ke iyakacinki haifarta, shi kuma halittarta yayi. Kar in sakeji k0 ganin kina damuwa ko Kuka ki daina, walwalarki ta dawo, ki mayar da komai tamkar ba,a yi ba. Kinji ko?” Kaita daga tana share kwallarta. Ita tasan me yake damunta. Ita ta san a wanne hali diyarta take ciki. Kawai dai tana sauraren mai martaba ne.
Kwana uku Hafsa tayi a dakin kula da mara lafia aka sallame ta, tare da bata sharudda da dama a kan yadda zata kula da kanta. Tana kwance taji shigowar Jiddah, motsinta hade da kamshin turarenta ne ya sata gane ita ce, don dama can bayi mata sallama take yiba. 
Kara noke kanta tayi kamar bata san da shigowar Jiddan ba, Sannan Jiddah ta kariso gabanta. ‘ 
“Naji ance abinda kike kumensa ya bare. To Allah ya tsayar kanki. Shawara nazo na baki Hafsa. Tun wuri ki koma asibiti a juyar miki da mahaifa, sabada k0 ba a juyar da ita ba da kanta zata Ialace tsabarzubewar ciki. Kin rinka wahala kenan a duk sadda cikinki zai zube. Gwara kawai ki magance wahalar, tun wuri ki iyakance ta.” 
Ba tajin zata iya kyale Jiddah tana fada mata wannan maganganun. Cikin karfin hali tana cije lebo ta tashivzaune. Ta kalli Jiddah sama da kasa sannan tace, “Oh Ashe ma da sanin ki cikina ya bare. Ashe har kin san cewa cikina zai cigaba da barewa.to Koma mai kika taka zai karye. Kuma idan Allah yace sai dana ya shaki iskar duniya baki isa ki hana shi ba. Mugun abunki zai koma gare ki. Wato ke yadda kike juya shine kike hassada ni ma kar in samu haihuwa to Baki isa ba Allah yafiki.” Ahayye nanaye!” Jiddah ta fada da murmushi a fuskanta tana tafa hannaye. “Sai a yanzu ne kika san akwai Allah? Hafsa! Dukkanin sirrikanki cike suke a tafin hannuwana. Duk kalar makircinki ke da uwarki babu abin da ban sani ba. Ke, a takaice harsirrin yadda aka yi auren na sani. Da kuma yar uwarki da uwarki ta kashe duk don ki auri‘ Yerima Abu Sufyan, sai AlIah yasa ba zaki taba auren nashi ba. Idan kina tsammanin wa yannan sirrikan ba zasu zomin ba to kinyi banzan tunani. Na san komai. Na san zaluncin Kursiyya, na san tsafinta. Sai dai abin da bata sani ba, ke ma kuma baki sani ba, dukkan abin da take takama dashi to gidanshi tazo. 
Tanagama fadin haka tajuya ta bar dakin tana sakin murmushi. Tana tuna wayar da tayi da mahaifiyarta duk ta kitsa mata wannan maganganun. 
Tun data fita Hafsa ta fashe da kuka, yau taji sirrikan da ita kanta bata san da suba. Harga Allah bata san da hadin bakin Kursiyya a mutuwar Gimbiya Sa’adiyya ba. Sai dai kuma ba tayi mamaki ba. Don ita kanta tajima tana zama ta kissima mutuwar Sa’adiyya, da kuma kalar makircin da mahaifiyarta tayi kafin mutuwar yarinyar. Saita tabbatar da lallai haka 
ne. “Umma ashe za a iya hada baki da ita ayi kisan kai? Me yasa?Gashi nan tun a duniya ni 
kam na fara girbar abubuwan dana aikata. Kin cute ni Umma Fulani.” 
Ta kuma fashewa da wani kukan. Duk wani tunani da Kursiyya za tayi na neman mafita tayi, amma babu abin data tsinta a ciki. Ba tajin zata iya hakura, saboda a kaf tarihin rayuwarta bata san wani abu wai shi hakuri ko yafiya ba. Takan turje, ko da ace zata wahala, in daiza ta kwatar wa kanta fansa ne. A yanzu maji take duk wuya duk runtsi zata iyajurewa in dai hakan zai sa ta dauki fansa. Amma ta yaya? Amsar data gaza samu kenan. Ta canza hannun tagumi izuwa na dama, 
idanuwanta a kafe wuri daya, fuskar nan tata ko kadan babu alamun imani a ciki. ’ 
Zabbau ce ta shigo har ta nemi wuri ta zauna amma Kursiyya bata san da wanzuwanta a cikin dakin ba. Rankatakaf hankalinta ya dauke ta dafya kaita ga yadda zata samo wa kanta mafita. Shiru ya ratsa dakin, Zabbau na bin uwargijiyarta da kallo, Sunjima a haka kafin tace, 
“Ranki shi dade barka da yamma.” Shiru ya biyo baya. Ta sake maimaitawa nan ma shiru Sai data dan bubbuga ta kadan sannan ta zabura da sunan Sarauniya Malmounatu a bakinta. Cike da mamaki Zabbau ke kallon ta. 
”Zabbau yaushe kika shigo?” 
Ajiyar zuciya Zabbau ta sauke hade da fadin “Na dan jima zaune a nan ranki shi dade, duk baki sani ba. Hargaishe ki nayi, na miki magana amma shiru Na rasa gane daIIin da yasa zancen matar nan ya gagara fita daga ranki 
Kursiyya ta gyada kanta tace, ”Zabbau, duk wata hanya da zanbi don ganin nayi na samu mafita nayi amma na kasa. Duk da cewa boka Fartsi yajaddada min bazan iyaja da Sarauniya Malmounatu ba amma na kasa yarda in hakura. Hafsa tayi bari biyu kenan daga zuwanta gidan can, kuma duk kaidin Sarauniya Maimounatu ne. Da haka ne zan iya manta da waccan makirar matar? Da haka ne zan iya hakura in fita shirginta? Ba naji ko kadan zan 
iya daurewa Zabbau. Ya zama dole na kwaci fansa k0ma ta halin kaka ne.” Mamaki karara a fuskar Zabbau tace ~Ranki shi dade kar fa kiyi abin da zaijaza miki masifa. Ba a baki daya ba kikaji Iabarin Sarauniya Malmounatu ba.” 
“Zabbau kenan. Ina shakku, da hakan ba shi zai hanani daukar fansa ba. Wallahi sai inda karfina ya kare, k0 da ace hakan yana nufin zan rasa numfashina ne.” 
Zabbau ta zabura hade da mikewa tsaye. Ta fara tsorata da Kursiyya, tama rasa yadda akayi ta zabi daukan fansa ga matar da tafi karfin har uban dakinsu, boka Fartsi. 
Tace ranki shi dade ta ina zaki fara?” Dariyar gefen baki Kursiyya tayi, wanda ya tabbatar wa Zabbau cewa Iallai ta samo mafita. 
Duka ma wada ba gajiyawa bace. Zanje haryankin Bani Hashim. Zanje wurin Sarauniya Maimounatu, zamu daidaita kanmu. Da wayo da dabara zanje dajin Dumburzu, zanga uwar biyu mu daidaita kanmu.” Zaro idanuwa sosai Zabbau tayi. Tama kasa furta komai tsabar mamaki. 
“Zan lubbace ta, har sai ta aminta dani.” Da sauri Zabbau tamkar tanajiranta a wannan gabar tace ”Amma ta yaya zaki iya cin nasara ga mayyar macen da ba mutum ba? Ta yaya zaki iya shiga tsakaninta da ‘yarta gudanjininta?” 
Murmushi Kursiyya tayi. “Nima kaina ban sani ba. Ban san ta yaya hakan zata faru ba. Ina fatan samun nasara. Ina ji a jikina kuma zan yi nasarar. Goyon bayanki nake nema. Tafiyar tana da bukatar mataimaki. ldan har kika amince muyi aikin nan tare zaki samu kyauta mai tarin tsoka. Sosai Zabbau kejin tsora, sai dai sam bata gaji asara ba. Mene ne asara? Tanaji tana gani kyautar Kursiyya ta kubuce mata. Hakan yasa ta aminta da zancen tare da daukar alkawarin duk tsiya duk runtsi zasu gudu tare su tsira tare. 
A rayuwata ban taba yarda da kowa ba, ciki kuwa har kaina. Amma abun mamaki sai na dauki kafatanin yardata na dora a kanki. Na yarda dake Zabbau. Sosai kike son farin cikina. Sosai kike son ganin nasarata. ” Murmushi Zabbau tayi jin irin yabon da Kursiyya ta mata. Da gaske tana kaunar Kursiyya 
har cikin zuciyarta. “Daga ina zamu fara?” Kursiyya ta danyi shiru jim, sannan tace Mu fitar da ranan tafiya yankin Bani Hashim.” ‘Yaushe ke nan ranki shi dade?” Bana son abin ya dauki Iokaci. Zan san yadda zanyi da mai martaba.” Zabbau tace “To ya zamu yi da Boka Fartsi? Ko ba dole saiya sani ha?” 
Tabe baki Kursiyya tayi tace, “Shi da bakinshi kinji yace wannan matar tafi karfinshi, 
babu abin da zai Iya yi mana. Saima yayi mini gatse waiga fili mai doki. shine nake so na bashi mamaki. Ya ga nawa aikin ba tare da tsafi ko sihiri ba. A wannan karon da kaina zan yi, k0 kadan bana neman taimakonshi.” ”To amma…’ 
Ya isa haka Zabbau. Karki wani damu. Alkawari ne na daukar wa kaina ta cikar wannan alkin, zan kuma yishi. Don haka bana so ki saka tsoro ko wata fargaba a ciki.” Ta mike a bisa kafafuwanta. “Zan isa wurin mai martaba. Zan tsara shi game da tafiyar. Komai ke nan 
a yau din nan zaki sani. Idan ta yiwu to akwaiyiwuwarmu tafi gobe.” 
Tare suka fice daga dakin Ita da Zabbau. Kai tsaye ta wuce Iarfajiyar mai martaba. Kuma tayi sa,a dawowarshi kenan daga fada. 
Sumi-sumi Kursiyya ta zauna a kusa da shi. Ganin yadda take kasa kasa da ido ya sa ya fahimci akwai dalilin zuwanta‘ Ya dawo kusa da ita ya zauna hade da kama mata hannu ya rike. “Fulanina lafiya dai na ga ki a haka k0?” Daidaita muryarta tayi sosai ta yadda ba zai Iahimci akwai karya acikin maganarta ba. Tace, “Wata alfarrna nazo nema a wurinka ranka ya dade. Ina fatan zan samu. ” 
Da saurinshi haryana in-ina yace “Na miki alkawari zanyi komai koma miye‘ Ki fada kawai kanki tsaye.” 
Ta dan murji fuskanta da tafin hannun dama. “Wata tafiya nake so nayi mai dan tsayi, wacce zata iya daukanmu kila har kimanin kwana goma k0 sati biyu. Zata iya yiwuwa ma baza mu kai hakan ba. A kiyasce ne na Iissafa kwana goman ko sati biyu. Ina fatan kar ka tambaye ni inda zan tafi, kamar yadda nake tsammanin ba zaka nemi sanin dalilin tafiyar ba. Cike da mamaki yake kallon fuskanta, yama rasa abin da zaice Ta cigaba da cewa “Na maka alkawarin ba zanje inda bai dare ba. Ba zan alkata abin da bai dace ba. Sannan bani 
kadai ba zanyi tafiyan, ni da Zabbau ce sai kuma drebana.” 
Sai a sannan Sarki Sani ya iya hadiyaryawu. Bai ma san ta inda zai iya musa mata ba. K0 kadan ba kuma zai iya tambayanta komai game da tafiyan ba. Hakan yasa ya jinjina kanshi 
cike da gamsuwa da amincewa da magananta yace, 
“Babu komai Fulani. Fatana a kodayaushe shi ne in ganki a farin ciki. Na tsaniganin fushi ko bacin ranki. Duk wani farin ciki naki shi ne nawa. Ina fatan za kuje lafiya ku dawo lafiya. Na yarje, da amincewata ku tafi duk sanda kuka shirya.” 
Dagaggawa Kursiyya ta isa gare shi ta bashi kyakkyawan runguma, wata irin dariya take saki da ita kanta sai da tayi mamaki. Haryanzu hankalinta baigama kwanciya da tafiyar ba. Ita kanta ta san ta tafka babban kuskure na kirkirar wannan tafiya, ba tare da ta shirya wa komai ba. Sai dai kuma a wani bari na zuciyarta tanajin cewa dari bisa dari ta ammta da tafiyan. A ganin ta komai zai zo mata yadda take so
“Gobe da sassafe nake so muyi tafiyar ranka ya dade. Sai dai ban shaida ma abokan tafiyar tawa ba, dama Inaso harsai na fada maka ne idan ka ammce sannan na sanar da su.” 
Daga kanshiyayi Sarki Sani, yace, “A sanar dasu yanzu, ni Sarki Sani na amince. Allah yasa a tafi lafiya a dawo Iafiya
“Ameen hubbina. Gaskiya samun miji kamanka a daidai wannan Iokacin ba abu ne mai sauki ba ranka ya dade. Ina alfahari’ da kai sasai da sosai.” 
Ta mike hade da tafiya ta bar dakin, 
Bayan ta koma dakinta ta kira Zabbau a waya ta shaida mata yadda suka yi da mai martaba, sannan ta umurce ta kan cewa taje ta fada wa drebanta maganan tafiyar. Suna gama waya kuma ta latsa kiran Hafsa. Bayan ta dauka suka galsa sannan ta mata ya jiki. Jiki da sauki Umma har ma na dawo dakina.” Hafsa ta fada cikin karfin hali sosai. 
“Haka nake sonji Hafsa yar Ielena. Dama fada mikizanyi akwai tafiyarda zanyi gobe da 
safe, zan iya yin sati biyu kafin in dawo.” Da sauri Hafsa tace ”Umma har ina ne zaki tafi na sati biyu?” Kursiyya ta sassauta muryarta cikin rarrashi tace “Neman dacewa zan tafi Hafsa. Zan tafi nema miki warakan matsalolinki ne. Duk da cewa haryau baki taba fitowa fili kin fada mini halin da kike ciki ba amma na sani. Na san komai Hafsa. Hatta cikinki daya zube sau biyu duk makircin Jiddah da uwarta ne. Don haka nizan nuna musu na iya. Duk abin da sukeji da shizan iya dasu. Zan tafi gobe, k0 ni k0 su…” 
Ba ta rufe baki ba Hafsa ta fashe mata da kuka. ”Umma kar kije don Allah. Bana so kijefa rayuwanki a cikin hatsari’. Ba zaki iyaja da mahaifiyar Jiddah ba‘ Nina yarda zan cigaba da zama a haka, na dai tabbata ba zan taba dauwama cikin kunci ba. Akan in je in rasa ki gwara ni inta wahala.” 
Murmushi Kursiyya tayi tace “Hafsa kenan. Baki san kamai ba, haryanzu ke yarinya ce. Kina tunanin masifa da bala’i in Sarauniya Maimounatu zaisa ki samu ‘yancin kanki ne 
matsayinki na matar dan sarki? Ba zasu taba bari ba har sai idan an daukar musu mataki.” ‘ “To naji Umma. Amma yanzu ta ina za ki fara? Ina ma zaki ne?” 
Kursiyya ta tabe baki cikin halin ko’inkula tace, “Kai tsaye zan tinkari Sarauniya Maimounatu ne. Zan kankantar da kaina wurinta har in samu nasaran haduwa da uwar biyu. 
Nasan me zanyi.” 
Hafsa ta kara karfin kukanta. “Ni daigaskiya inajin tsoro Umma. Da dai zaki hakura ki bar maganan da naji dadi. Wallahi harga Allah na yafe miki.‘ 
Kursiyya ta dakatar da ita daga nan. “Kar ki nemi bata min rai Hafsa. Tafiya dai ba gudu baja da baya. Sai mun yi waya.” 
Daga nan ta Iatse wayarta tanajin haushin Hafsa. Sai dai zuciyarta na mata kuncin kukan da yarta keyi. Bata da zabin daya wuce daukar wannan fansan. 
Washegari tun wurin karfe shida na asubahi suka gama shiri“. Saida Kursiyya tayi bankwana da mai martaba sannan ta dawo bangarenta. Ta fesa turare hade da gyara tukku wargashinta data dan shige, ta fiddo ta waje. Ta daukijakanta da waya ta kama hanyar fit. K0 data fita ta samu Zabbau da dreba ita kadai sukejira. Ma’aikata na ta rusunawa suna kwasan gaisuwa amma babu wanda ta kalla. Ta shige cikin mota suka kama hanyan tafiya. 

Hmm ko me zai faru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *