GIMBIYA SA,ADIYA CHAPTER 34

GIMBIYA SA,ADIYA




CHAPTER 34





Sarauniya Malmounatu tace aikin da nayi a mahaifar diyarki Gimbiya Hafsa, ciki bazai taba zama da jikinta ba hargaban abada. Sannan a yanzu babu wani aiki da zai iya gyara shi. ”
Runtse ido KurSiyya tayi, tanajin takaici cike da zuciyarta. Wani irin kunci da tururi takeji, tana ayyana girman tsanar Sarauniya Malmounatu a cikin zuciyarta.
“Yanzu kina nufin ba zan taba samunjika ba kenan?” Ta matso maganar daga kasan makoshinta.
Yalwatattun idanuwanta Sarauniyar tajuya. Ta hadiyi yawun daya dan makale a makoshinta, tana cewa abinda ta aikata bashi zai sata samujikan ba itama.
“Kinga ai anyi daidai kenan Ke ba zaki samu ba, ni ma kuma ba zan samu ba. K0 ya kika ce?” Sarauniya Malmounatu ta fada cikin annuri.
Uwar biyu data darara idanuwanta a kansu ta kyalkyace da dariya. Kursiyya da Zabbau suka kalle ta, sosai suke mamakin yadda take da yawan dariya. Gata ‘yarkarama da ita.
“Kuna shagalinku mutanena, Gwanin ma ban dariya diramar taku. Wato ke wannan kina son kiga jikanki, ke kuma wannan kina bukulun ta samu. Hahahahal Sannunku kunji. Bazan shiga wannan zancen naku ba‘ Kuje can ku karata.” Ta karisa maganar da wata irin dariya.
Cikin kuka Kursiyya ta tsugunna a gaban Saraunlya Maimounatu ta ce, “Ki rufa mini asiri rankiya dade. Duk duniyar nan Hafsa kadai gare ni. BanI’ da wam’ da k0 ’ya bayan ita. Ina son ganin nawajikokin ni ma. Ki rufa mini asiri ki warware wancan aikin. Ba don halina ba.” Kursiyya ke nan. A mummunar zuciyar nan taki na tabbata idan ke ce da tsafina sai kin yi wulakancin daya zarce nawa. Da ace kece da karfinn tsafina tabbas za ki iya kashe mini Gimbiya Jiddah har Iahira. Amma ni sai banyiba. Na rangwanta mata. Ina so ki sani, babu alkin da da Zan iya karyawa . Gwara ma tun wuri ki dangana. Ki koma ki shawarce su a cire mata mahaifarta tun kafin ta rube ta sakar mata wata cutan” ’
Tashi Kursiyya tayi ta koma inda take a farko, ta share hawayenta sannan tajuya ga Uwar biyu. ”Uwar biyu Ina so zamu koma. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Gaskiya ina shakkun boka Fartsi, saboda akwai tarin alkawurra a tsakaninmu. Ina gudun karya illata ni, don da kaina na nemi ya ilIata ni duk ranan dana butulce masa. Ban zaci akwai ranan bane yasa na daukar masa wannan alkawarin. To kuma saiga shi a yau din an samu. A yau nayi abin da ban taba mafarkin faruwarshi ba. Ki taimaka mini ki kare ni. Kar ki bariya cutar dani.”
Uwar biyu ta mike ta tako hargaban Kursiyya. Ta dafa kafadarta da murmushi kunshe a saman fuskarta. “Kursiyya, hala dai haryanzu ba kigama gasgata karfin tsafina ba? Idan har kin gasgata bai kamata ki kawo cewa wancan karamin kwaron zai iya aikata komai a kanki ba. Tun daga nan na zama garkuwarki. Babu wanda zai iya yi mikivkomai har sai Idan nice na bashi dama. Don haka ki cire tsoro. Ki raya a ranki kin zama ‘yargata. Babu ke babu sauran dire makudan kudi a miki aiki. Ni bana son kudi don babu abin da zan yi dasu. Taimakon nan daya da kika yi mini ya zarce komai a wurina. Durkushewar boka Fartsi ya fiye mini duk wata tarin dukiya, don kona same ta ba zan mora ba. Ni da nake zaune a kasurgumin daji daga ni sai namun dawa. Kawai ki kwnatar da hankalmki. Ina zuwa.”
Uwar biyu ta taka ta koma bakin gadan karanta ta zauna. Kanta ta dukar kasa, ta zaro idanuwa a take bakinta yayi tsawo sosai, ya cika da bakar . Idanuwan nan nata suka zazzalo waje bayan sun yijajur. Ta saka hannunta na haggu ta bibbigi goshinta, saiga shi yayi rami zurun zurun wani irin hayaki na fitawa daga ciki Ta dago kanta ta kalle su, sannan ta watsa yan yatsunta. A take saiga hayakin ya dawo fita daga tafin hannun nata, yana yin sama sosai. An dauki tsawon lokaci a haka kam ta sauke hannun. A kasa ta koma
yin zane, babu alamar komai amma saigajini na bulbulowa daga kasa. Yayi maIe-male a gabanta.
Harshenta ne ya zazzalo ya sauko har indajinin yake ta hau Iasa, har ta shanye shi tas. A dan lokaci kadan saiga ta ta dawo daidai tamkar komai bai faru ba. Tayi murmushi sannan ta mikar da hannayenta duka biyun, saiga kwarya ta bayyana a cikinsu. “
Mikewa tayi tsaye ta tako hargaban Kursiyya, ta dire kwaryar a gabanta sannan tace “Duba kiga nawa salon.”
K0 da Kursiyya da Zabbau suka saita magannansu ga kwaryar, saiga fuskar baka Fartsi ta bayyana aciki. Da mamakinsu suka kalli Uwar biyu sannan suka sake kallon Boka Faltsi.
Murza yan yatsunta biyu ta yi Uwar biyu, Saiga garin gishiriya bayyana a hannunta. Ta barbada shi a fuskar boka Farsi. Daga farko sadda ta kawo musu kwaryar idanuwanshi a bade suke, amma tana barbada mishigishiri saiya rufe Idanuwan, tamkar wanda barciya figa a Iokaciguda. A take kuma sai babu komai a kwaryar ta tsatssage tamkar ba ita ba.
Uwar biyu ta fashe da dariya taCe “Kursiyya, kina da bukatar in fassara miki duk abubuwan da suka faru ko in bar ki?”
Kursiyya tayi gaggawar daga kanta, “Ina sonji Uwar biyu. ”
Uwar biyu ta ce “Daga farko na yi amfani da tsafina na isar da sakona ga bandakinki inda Uwar Halima take. Na saki hayakin da duk ya mamaye wurin baki daya. Har duniya ta nade matsawar ba ni na cire wannan hayakin ba babu wanda zai taba gano inda take. Ina gama wancan aikin sai karfin Boka Fartsi ya ragu. Don haka nayi amfani da nawa karfin najawo shi da karfin tsiya. Na barbada mishigishirin daya kashe mishigangarjiki. A takaice dai boka Fartsi bai da wani karfi a yanzu. Babu abin da zai Iya yi. Na batar da shi, na kai shi inda babu wanda zai iya gano shi sai lani Maharazkhan, wato Aljanin nan nawa daya raba ni da shi. Ko shi kanshi Maharazkhan din ba karamin wahala zai sha ba kafin ya gano shi din. Dan haka ba na ma tsammanin zai iya. 
Na gama komaiyanzu. Ina fatan duk wani tsoro ya fita daga ranki Kursiyya.” 
Murmushin daya bayyana hakoranta tayi Kusiyya. Tace “Na gama gasgata komai naki Uwar biyu. Ki ba mu izinin tafiya kawai mu tafi. Sannan ina neman alfarmar ki kara kusanci tsakanina da mai martaba, da duk kowa ma na masarautar.” 
Uwar buyu ta amsa da ”An gama. Ku tafi kawai.” Kafin su tafi sarauniya Maimounatu ta ce “Harza mu tafi ban ga ‘yar uwata ba.” “Ba kigan ta ba a gidan kasa tana sana’ar tata” 
Da mamaki Sarauniya tace “Sana’arta? Kuma mene ne sanarta 
Uwar biyu ta tabe baki tare ”Tace ta kuka mana. Wai ita fa da tsiya aure take so yo to waye zai aure ta? Ita ba mutum bace ba kamar ke bare inta  koma cikin mutane ta nemi miji. Sannan ita ba aljana ba bare in hada ta da aljaniya aure ta. Toya zan yi da ita? In dai ba da 
zaki ko maciji zan hada su auren ba?” Ta fashe da dariya. Dukkansu dariyar suka yi su ma. Sannan Sarauniya ta kama hannun Kursiyya da Zabbau suka bace. Suna bullowa a dakin bakin da suka bari, Kursiyya ta dora idonta ga agogo. Abun mamaki sai ta ga wai duka-duka mintinsu biyu da tafiya. Cike da al’ajabi ta yi shiru, tana ganin komai tamkar a mafarki. 
“Kursiyya da Zabbau.”sarauniya Maimounatu ta fada tana kallon su. “A yau za ku tafi ko sai kun huta zuwa gabe sannan ku wuce?” Ita kam Kursiyya da gaske ta Bani Sarauniya Maimounatu. ta mata bukulun ganin jika bata da makiyya sama da ita. Cikin tsana taCe mata “Zamu wuce yau din nan.” 
Murmushi tayi sannan tace “za a kawo muku abinciyanzu. Sannan akwaiguzuri da tsaraba da za a hada muku duk a cikin dakiku kadan. ldan kun tashi wucewa ba sai kun min sallama ba. Zan koma cikin gida, na gaji sosai.” Ta mike sannan ta fara ajje takunta har ta isa bakin kofa. 
Da sauri maigadin ya busa usur, saiga hadimanta sun iso, wasu suka shiga gabanta wasu kuma bayanta. 
Kamaryadda ta alkawarta musun haka aka yi. Kyakkyawan abinci aka kawo musu, shinkafa da miya da naman kaza, Sai kuma farfesun naman kazar daban, ga pepper chicken ga kuma soyayye. Sai Iemuka fresh homemade da akajera a gabansu. Sosai suka ci abincin. Misalin biyar na yamma suka mike domin tafiya. 
Bayan sun isagaban motarsu suka tarar da buhu biyu na abubuwan arziki. Sannan ga wata karamarjaka da basu san k0 mene ne .a cikinta ba. Da saurin Kursiyya ta dauke ta ta duba. Abun mamaki cike take da duwatsu da coins din zinare. Ta zaro idanuwanta tana kallon Zabbau. Tun da take a rayuwarya bata taba ganin dukiya tsagaga kamar wannan ba. Su ma din suna da tasu bakin gwargwada, amma fa bata kai ko rabin ta masarautar Banii Hashim ba. 
”Ranki shi dade, an kawo min abinci mai rai da lafiya na ci. Gaskiya yan masarautar nan suna da karamci sosai. Ba zan taba mantawa da su ba.” 
Murmushin dole Kurslyya ta kirkira. Ta ce da shi “Ai haka ake so. Yanzu dai a shigar da 
buhunnan nan a booth. Muyi mu baryankin nan na kuma gaji da shi.” ”To. ” Ya furta hade da mikewa ya bude booth, sannan ya saka buhunnan ya rufe. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *