GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 8
Sai da tayi dariya mai isarta, sannan ta dago kan Hafsa da ta dukar a bisa cinyarta. Ta saita idanuwanta a cikin na Hafsa, irin kallon dake nunar da magana mai muhimrnanci ce
“Tun da kike a rayuwarki kin taba ganin mutum mai bakinjini kamar Halimatu? Ehh ko a ‘a?” Kai ta gada alamara ‘a.a
“Da kyau. Kin manta cewa har kuyangu da bayi na masarautar nan sun tsane ta? Idan har mutanen da suke a karkashinta za suki ta. me zai sa dan sarki kamar Yerima Abu Sufyan ya sota? Hakan ba zai taba yiwuwa ba Hafsa. Ki ma cire wannan daga rayuwarki. Kin san akwai mafarki nasa ma rai abu. Inaji don kina tsananin kaunar Yeriman ne yasa har kika saka shi a ranki kika yi wannan mafarkin wanda ba zai taba zama gaskiya ba.” Zabbau ta amshe da fadin, “Mujiya face Halimatu. Da Bakin jininta waye zaisa ya sota? Mahaifin nata ne kawai, shima kuma don shiya haife tane. Kar ki damu ‘yarlelen uwa da uba. Ki kudurta a ranki cewa kin riga da kin auri Yeriman Kubaisu kin gama. Kin kusa zama Gimbiyar Kubaisu.” Lallausan murmushi Hafsa ta saki, tana mai tsananin jin dadin kalaman da suke fitowa tsakanin Fulani Kursiyya da kuma Zabbau.
”Umma, ni kaina na yi mamakin yadda soyayyar bawan Allahn nan ta shige ni a ‘yan Iokuta. Duka-duka kwana nawa ne da Abba ya bani takardunnan wai daga ganin hotonsa duk nabi na haukace da soyayyarsa. Wallahi Umma da zuciya daya nake son shi. Ban san ya rayuwata zata kasance idan na rasa yerirna Abu sufyan ba.”
Ido Kursiyya ta fidda waje. Tsananin mamakin kalaman ‘yarta rakeyi. Wannan wace irin soyayya ce ta kama Hafsa harhaka? “Karki damu. Ki saka a ranki cewa kin auri’ Yerima kin gama. Aure tsakaninki da shi babu fashi, sai dai kuma wani al’amarin na daban. Gobe zan yi magana da maimartaba, azo a fara maganar auren naku. Kwace jikinta ta yi dagajikin Kursiyya, ta buga tsalle da karfi tana murna. “Umma zanje dakina na fara shiri. Kin gama mini komai yau kam. ” Hararar wasa Kursiyya ta mata, “Yau kadai?” “Kullum ma.” Ta fada hade da barin dakin cike da farin ciki. Kursiyya ta juya ta fuskanci Zabbau. Tace
“Nan da kwana biyu ya kamata mu ziyarci boka Fartsi. Ya mana aiki dangane da wannan
mafarkin na Hafsa. ldan ma akwai wani abu da zai iya faruwa ya gaggauta mayar da shi tun wuri. Zabbau ta gyada kanta, fuskarta kunshe da murmushi. Tace Ranki yadade ke nan. Har kina tsammanin wai akwai wanda zai kaunaci Halimatu ne? Nifa gani nake yi a haka rayuwanta zata qare da bakinjini.babu wanda zai aureta sai dai a mata auren hadi da wanda zai wahalantar da rayuwarta.” Suka tulle da dariyar keta. “Wannan ma kuma magana ce. Babu yadda za ayi Yerima Abu sufyan ya kaunaci Halima Suka cigaba da hira sosai, hirarsu ta makirci da suka saba.
A gabanta Sadiyya ta bullo. Yatsarta ta saita bisa tsakiyar kan Zabbau, a take suka bace tare. Idanuwan Zabbau a bude suke tana kallon ikon Allah. Iska suke bi da tsananin gudu, wanda ba karamin azaba takeji ba, kasantuwar radadi da takeji fatar jikinta nayi mata. Basu wani jima sosai ba saiga su a babban dakin nan na Kursiyya sun bullo. ‘Dakin kace
kace yake, komai an masa dai-dai, alamun anzo neman su Kursiyya ba a gansu ba.
Cikin muryarta madaukakiya ta ce. “Sarki yazo neman ku sadda ba kwa nan. Sai ki san kalar karyar da zaki yi masa ta inda kukaje. da kuma inda kika kai masa mata.‘
Tana gama fadar haka ta bace daga dakin. ‘ Kursiyya kuwa tana can cikin kasan ruwa, tun wata jifa da boka Fartsi yayi da ita, a wata duniyarta daban, lnda ta hadu da wasu lrin halittu sun zagaye wuta, sun saka ta a tsakiya kusa da wutar, suna wani irin yare sannan suna zagaye ta. Ihu take mai tsanani, saboda yadda wutar ke laso ta. Amma ba ma ta ita suke ba, bama su san me take cewa ba.
“Ku taimaka mini ku fitar dani. ku mayar dani duniyarmu.” Wata irin waka suke yi,
“Shakeke bulabi, honole hu, hu hu hu! hu hu hu! Shekeke bulabi, honole hu. hu hu hu! Huhu hu!”
Haka Suke fadi suna maimaitawa. Tun Kursiyya na musu magiya harta gaji tayi shiru tana sauraren su. Sun zagayeta akalla sau biyar. sannan suka dakata, suna ci gaba da magana da yarensu.
” Karku kashe ta a yanzu. Mu bari har abub bauta Talmijo ya bamu lzini.”
Talmijo wani abin bautarsu ne, wanda ya kasance gunki ne, sun masa tsafi mai tsanani, suna bin umurninsa. Aduk sadda suke son suyi abu, suna bar masa zabi ne, ta hanyar rataye masa wani farin kyalle. Washe gari zasu dawo gare shi, idan suka samu farin kyallen ya koma kalarja, to ya basu izinin suyi abin kenan. Idan kuma suka same shi bai canza kala ba, bai basu Izini ba kenan. Duk kaunarsu da abin ba zasu yi ba, dole zasu hakura. Wannan farin kyallen wani daga cikinsu ya yafa a wuyansa. Suka jera dogon layi ta tsaye, sannan suka tasa Kursiyya a gaba, suna biye da ita, sai wani katoto daga cikinsu daga can gaba yana musu jagoranci zuwa wurin bautartasu. Kuka sosai Kursiyya keyi. Komai jin sa take kamar a mafarki. Ta tabbata cewa kadan daga ayyukan sharrin da suka shuka ne ke bibiyarsu. Kallon wayannan halittun kansu wani nau’i ne na azaba. To bare kuma yaren da suke yi.
A bakin wani tafkeken gini suka dakata. Ginin da wata irin kasa aka yi shi, sannan ga wasu irin kyalli dake fitowa daga gare shi. Duk ta kowacce kusurwa ta jikin ginin akwai kwayar ido a akinsa, ruwan hawaye na fita daga cikin kwayar idon, suna sauka zuwa wani tafkeken rami mai kama da korama. Da Kallo sosai Kursiyya ke bin wurin da shi, daga bayanta taji wani na magana,
“Roshi kubartimjinkuzu kardus. Gozakurwula sanumshirdiko. (Idan taki tafiya kaja tada karfi Roshi. Da alama tana so ta bata mana lokaci ne.)”
Bata san me suka ceba bare ta gaggauta bin bayan Roshi din. Ji tayi da karfu anjata izuwa cikin gidan. Radadi sosai hannunta keyi, kasantuwar hannuwansu duk kayoyi ne ajiki. Ta fasa kara mai karfi, tana kokarin fizge hannunta tsabar azaba. Bai sake taba Roshi din har sai da suka isa a gaban abun bautar nasu. Halittarsa kamar ta mutum, yana da kafafuwa biyu, hannuwa biyu, sai dai kawunanshi sun kasu kashi uku, kowanne da ido guda daya a jiki. Daga tsakiyar hannunshi na haggu ke da wata yatsa wacce ya mikartsaye, rataye da zoben zinare. mai tsananin kyalli. Kursiyya na ganin haka ta gaggauta dukawa a gaban halittar, gudun karsu sake yi mata wata kalar ketar kuma. Da wannan farin kyalle suka dode mata idanuwa, har tsawon minti goma shabiyar sannan suka bude ta. Suka rataye kyalle a jikin yar yatsar gunkin nasu. Zoben hannunsa suka cire, suka saka ma Kursiyya shi, sai dai kuma duk yatsarda suka saka shi ya mata yawa. Wannan dalilin ne ya sa suka fara kallon-kallo a tsakaninsu, suna mamaki. Duk yadda yatsar mutum take idan har aka saka masa wannan zoben to dole sai ya masa daidai. Amma wannan karon ga shi sun gwada dukkanin yatsunta amma duk sunyi ma zoben karanta.
“Yalbijoriya shahalartu kalbinsho sunkum. La bisunji dunum bolarjuku. (Akwai gagarunar matsala nake gani Amma tukunna, mu bari har gobe mu samu izini daga abun bauta.)” Daga nan suka mikar da Kursiyya tsaye kyam, sai dai tsananin zafi da ciwon da kafarta ke mata yasa take jin kamar baza ta iya daukar gangar jikin nata ba. Tafiyar da suka yi daga wancan wurin wutar, zuwa wurin bautarsu ba ‘yar kadan bace. Ga kuma irin fizgar da Roshi yayi mata, dole ne ta jigata. Ganin tana laba-laba yasa Roshi ya sungume ta tsam a hannuwansa. Abin mamaki, duk girman Kursiyya sai ta zamto tamkar zobe a tafin hannu tsabar kankanta. Sokar da hannun Roshi ke mata sai ta gwammaci ace kasa take, duk da ciwon da kafar tata ke mata zata iya daurewa a hakan ta tafi. lsar su bakin wutar da karfi ya saketa ta fadi kasa, bisa wasu hakukuwa. lhu ta saki mai kara, ta saka hannuwanta tana dafe wurin da ya fashejini na zuba.
A Cikln wannan halin kuma ta rinka jin wuta na laso ta, hakan yasa ta gaggauta mirginawa bisa hakukuwan tana kuka sosai, kuka mai cin rai. mai tsuma zuciya. Ita kanta ta sani, tun da take a rayuwarta bata taba mafarkin wannan lokacin ba. Bata taba tunanin akwai ranar da rayuwarta za ta wulakanta har haka ba. Sai dai kuma idan tayi tunanin munanan ayyukan data shuka, to sai ta gane cewa alhaki ne ke bibiyarta. Dama duk abin da ka shuka shi zaka girba. Yau dai gata a cikin wata rayuwa, wacce ta gwammaci mutuwa a kanta. Duk da bata san abin da suke da kudurin yi mata ba, ta tabbatar cewa suna da mummunan kuduri a kanta. Don taga yanayin nasu, ta karanta komai tsaf, rashin sanin abin da suke fadi a yaren nasu dai ne matsala. A cikin wannan halin mugun barci ya dauke ta. Barci mai cike da mugayen mafarkai masu bantsoro, wanda suka karisa kidimar da ita, ta sake tabbatar da cewa ba lafiya ba. Tunda ta farka bata sake komawa barcin ba, sai zufa da take ta ketawa, ga tsananin zafin wuta dake Iaso ta.
Na tabbata wasu zasu ce wai me Kursiyya ta aika ne haka data cancanci wannan sakamakon? Karku damu, labarin namu yana da tsawo, sannu a hankali zamuje inda kuke son zuwa. Da sannu ku da kanku zaku ce lallai Kursiyya tayi deserving din wannan sakamakon