GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 29
Ajiyar zuciya Zabbau ta sauke. “Kiyi mingafara uwargijiyata. Kiyi hakuri da maganar da zan fadi. Yanzu idan har aka samu maimartaban yazo yana da wani abu da zai iya yi ne? Aure ne an riga an daura shi, bana tunanin saki k0 wani bayanin rabuwa zai halatta ga sarakunan biyu. Kiyi hakuri Fulani. ” Tajinjna hannunta.
Dukewa Kursiyya tayi ita da Hafsa, ta zaunar da ita a bisa sofa. Ta san gaskiya Zabbau ta fada mata. Ko Sarki Sani yazo babu abin da zai iyayi yanzu. Bakin alkalami yariga ya bushe.
JI’ tayi tamkar ta dora hannunta aka ta fasa ihu. Saukin ma daya shima Yerima Bukar din dan Sarki Abdurrahmanu ne.
“Ya isa haka ki daina kukan Hafsa. ”
Hafsa ta dago rinannun idanuwanta ta kalli Kursiyya. “Umma har kina da bakin rarrasata? Kina tunanin kuma zan yi shiru? An zalunce ni Umma. An bata min Iissafina.”
Ta sake fashewa da wani kukan.
Duk yadda Kursiyya taso ta dakatar da Hafsa daga kukan da takeyi kasawa tayi. Suna cikin hakan maimartaba ya shigo cikin karfin hali. Basu ko amsa sallamarshi ba sai Zabbau ce data yi suf-suf ta fice daga dakin. ‘
“Maimartaba me yasa ka mana haka? Me yasa zaka Iullube mana zance ka barmu a duhu?”
Ya sassauta muryarshi, cikin rarrashi yace “Ban san yadda zan yi bane. Bani da wani zabin da ya wuce aura wa Hafsa Yerima Bukar. Inda a tun farko baki tilasta da lallai sai Abu Sufyan ya auri Hafsa ba da duk haka bata taso ba. Abun ne yafi karfina, sam bazan iya butulce wa Sarki Abdurrahmanu ba. Nace masa da nufin a hada auren Hafsa da Yerima Abu Sufyan amma saiyaron bai amince ba. Shi kuma sarki gudun kar inga an min ba daidai ba yasa yace Idan har na amince sai a hada auren da Yerima Bukar. Ni kuma ganin wannan gwaninta da yayi min yasa sam naji ba zan iyace masa ban amince ba. Kawai na amince a daura din.” Clke da takaici Kursiyya tace “To amma meya sa ka boye mana?”
Ya yi murmushi yana mata kallon kauna. ”Ranki shi dade ai baki tambaye niba. Baki k0 tsaya kin saurari sauran maganar ba kika hau murna. K0 kin manta?”
Shiru tayi sai sauke ajiyarzuciya takeyi. “Yanzu dai mai faruwa ta faru. Aure an riga an daura shi. Yanzu haka amarya kawai akejira a tafi da ita. Ku gaggauta basa so suyi dare.”
Kuka Hafsa ta kuma saki mai karfi. Maimartaba bai k0 tsaya yayi magana da ita ba ya mike ya bar dakin yana jajjada ma Kursiyya yanzu ake son amarya da yan rakiyarta su fita.
Cikin Iokaci kadan idanuwan Hafsa suka gama rinewa. A haka aka fito da ita, cikin rantsattsuyar sabuwar motar da maimartaba ya mallaka mata aka saka ta. Kuka kawai take yi wanda yake da ma ‘anoni daban~daban. Kursiyya ta sunno kanta cikin motar, ta kama hannun Hafsa tana mata adduar sauka lafuya. Hafsa ta kuma sakin wani kukan, tanajin ina
ma dai ace a bubbuge ta ta tashi daga mummunan barcin da takeyi.
Kamar daga sama taji an bude gefen motar an shigo. Kamshin turare taji, ta daga kanta ta
kalli fuskar Yerima Bukar dake ta sakar mata murmushi. Tsaki tayi mai kara hade da dauke kallon ta daga gare shi. “Ranki shi dade amarya Gimbiya Hafsa matar Yerima Bukar.” Ya kyalkyace da dariya.
“Mtsw! ” ta sakejan wani tsakin. Ko ajikinshi ya daga kafadarshi. Ya san duk salon shegantakarta ba zata kai Jiddah uwargidanshi ba. A ranshi yana tunanin kalar badakalar da za,a sha a gidan. Ya sake sakin dariya.
Har motar ta tashi bata dago kanta ba. Jin tafiyar ba mai karewa bace ya sata dago kan nata tana kallon waje ta gilashi. “Aina zaci a haka zaki dauwama. ” Yerima Bukarya fada
yana kallonta. “Kaga, kayi min shiru Mallam. Babu abin daya dame ka dani da in dago da kar in dago. Ah to! ”
Ya tabe bakinshi. “Wannan rashin kunya da fitsarar gwara ma tun wuri ki daina su, don babu inda zasu kai ki. Lallai ina ga baki san ko wa kika aura ba tun da har kike tunanin zaki iya
ja dani, ni din nan Yerima Bukar da kowa ke shakku.”
Bata kuma cewa k0 uffan ba ta cigaba da Iatsar wayarta. Shi ma ya fiddo tashi wayar yana latsawa. Kira ya shigo a wayarya gagauta dauka. ‘jiddah Ke da Alla malama ki rufa min baki. Kin san bana son shashanci fa. ” a dayan bangaren Jiddah tace, “Wallahi ka shirya hadiyar masifa da bala ‘i, matukar ka kawo amarya a cikin gidan nan ina mai tabbatar maka da sai nishadi yayi kaura a nan. Gwara ma tun wuri ka
san inda zaka kai ta, ba dai a cikin gidana ba.”
Tsaki ya saki hade da cewa “A nan din zan kawo ta, in yaso ku kashe kanku. Ke din waye da
ba zan hada ki da wata ba?”
“Zaka sani ne Yerima. Ina nan zamanjiran isowarku. Kayi mata albishir da rashin hankalin
da zata taras. Sai ta san cewa ni Jiddah diyar Sarauniya Maimounatu ce abokiyar kishinta. ”
Tana kaiwa nan ta tsinke wayar. Duk abin data fada Hafsa taji. A hands-free Yerima Bukar ya saka wayar. A take tajigabanta ya fadi. Duk rashin kunya da tsagerancinta bata iya fada ba. Bata iya kwatar wa kanta fansa ba. Ko a gida Kursiyya ce gatanta in dai ta fannin daukar fansa ne. Bata san sadda hawaye ya sauko mata ba. lta dai kam wannan kaddara ba taji dadinta ba. A tunaninta muradin zuciyarta ne aka aura mata, ashe sam ba haka bane. An cuce ta Ta riya a ranta.
Hmm