GIMBIYA SA,ADIYYA CHAPTER 43

GIMBIYA SA,ADIYYA






CHAPTER 43





Washe gari

Kamaryadda mai martaba Sarki Sani ya kwana bai rintsa ba tsabar takaicin Kursiyya, da kuma zakuwa da gari ya waye ya yanke mata hukunci, hakan yasa gari na wayewa da fushin abun ya tashi. Ya sa ayi sanarwa tun daga cikin masarautar Bilbah har zuwa tsakiyar garin Bilbah, cewa duk wanda yake da ikon zuwa yau yaje, domin kuwa za a yanke gagarumin hukunci ga Kursiyya bisa ga manyan ayyukan data aikata.
A cikin gida jikin kowa a mace yake,jin cewa a yau din nan ne za a yanke ma Kursiyya hukunci, kuma sun tabbata cewa na kisa ne za a yanke mata. Cikin sanyin murya Sa,adiyya ta kalli Hafsa tace,
“Yaya Hafsa ko dai zaki bar gidan nan ne ki tafi wani wuri har zuwa anjima sannan ki dawo‘! Uwa uwa ce. Na tabbata za ki shiga tashin hankali idan kika ga hukuncin da za a yanke ma Umma. Abun zai zauna miki a rai sosai.” Hafsa ta kirkiro murmushin da iyakacinshi bisa lebonta. Tace,
“Duk kalar hukuncin da za a yanke ma Umma ta cancanta ne Halimatu. Idan harna nuna rashin damuwata to tabbas na so kaina. Don haka babu inda zan tafl, zan tsaya in kalli komai, watakila ma hakan zai kara mini imani sosai.”
Hawayen da Halima ke makalewa ne ya karisa saukowa kasa. Ta dafa kafadar Hafsa, “Yaya
Hafsa, ni kam gaskiya ba zan iya gani ba. Ko ba komai na rayu a gaban Umma. Duk da babu kyautatawa a tsakaninmu amma duk da haka ina jin ta a cikin jikina. Wallahi zan kwana ina tunani idan aka yanke mata hukunci a gabana.” “Halimatu ke nan. Wai ke kam wace irin sassanyar zuciya ce gare ki haka? Ban taba ganin irinki ba, ba na jin zan taba ganin wata bayan ke kuwa har abada. Zuciya dai irin taki mai matukar taushi da sanyi, wadda ba ta rikon mugun abu ko kuma sharri, kullum burinta ta tuna alkhairin mutum, ko kuma ta saka mishi alkhairi a kan sharri.
Da wannan halin naki kadai za ki ci gaba da cin ribar rayuwa. Wallahi ina jin ki can kasan zuciyata. Ina kaunarki da dukkanin zuciyata.” Murmushi Gimbiya Saadiyya ta yi bayan ta rike hannun Hafsa. Ta ce,
“To tun da dai kina kaunata ki tashi mu tafi mu bar gidan nan a yanzu, zuwa can anjima bayan komai ya Iafa sai mu dawo. Don Allah Yaya Hafsa kar ki ce mini a’a.”
Hafsa ta dan yamutse fuska, sannan ta mike a bisa kafafuwanta. “To naji. Tashi mu tafl.” Gimbiya Saadiyya ta mike hade da yin gajeren tsalle, ta ce, “Yauwa ko kefa yar uwata. Mu hau doki ma mu tafi zagayar gari kawai, kin ga daga can har mu hango mabukata mu taimaka musu. Na yi kewar irin wannan zagayen.” Hafsa da take bakuwa a taimakon al’ummah ta ce, “Da kuwa naji dadi sosai.” Asalin dakin Gimbiya Saadiyya suka je, suka zakulo alkyabbunta manya masu kyau, dukkaninsu suka saka sannan suka fito.
Dawaki suka hau, dayake dukkaninsu gwanaye ne a hawan doki, hakan ba bakonsu bane ba. Waziri ya gan su daidai zasu fita ya ce, “Gimbiyoyi sai ina haka a daidai wannan lokaci?” Gimbiya Saadiyya tayi caraf tace,
“Kawu, kawai dai muna son doje ma ganin hukuncin Umma Kursiyya ne. Ba zamu so a yI’ ba a gabanmu.” Waziri da ya tsani jin sunan Kursiyya ko tsayawa gama jin zancen bai yi ba ya kama gabanshi. Su ma din suka fice, bayan matakan tsaro mutum biyu sun bi bayansu. Da misalin karfe sha biyu na rana ne masarautar Bilbah ta cika makil a fllin yanke hukunci, ana jiran isowa da Kursiyya, da kuma isowar mai martaba.
Sarki Sani ne ya fara isowa, bayan ya hau mazauninsa aka mika sifika gare shi. Ya yl’ gyaran murya hade da farawa da sallama.
“Kamar yadda kukaji sanarwa, na san dukkaninku nan kun san dalilin haduwarmu a nan. Fulani Kursiyya tsohuwar matata, ta aikata tarin laifuka, manyan zunubbai da ta cancanci hukunci mai tsauri.” A daidai nan aka iso da Kursiyya da aka daure hannunta da ankwa. Jikinta ko’ina jina jina duk ta raunata kanta da cizo da tsunguli. Duk idanuwa suka koma kanta. Ta gama fuffigewa tamkar ba ita ba. Da ma ga kanta babu gashi, sai abun ya karisa lalace mata. “Daga cikin manyan laifukan Kursiyya, sun hada da kisan kai, zalunci, shirka, cin amana, ha’inci, yaudara da sauransu. Kamar yadda yazo a ayar littafl mai tsarki, inda Allah madaukakin Sarki ya ce Annafsu binnafsi. Wato wanda ya kashe a kashe shi. Don haka, za a kashe Kursiyya. kisa ta hanyar rataya.” Dukkanin wurin sai aka dauki kabbara. Wasu na hawayen takaicin mugun halin Kursiyya. Wasu kuwa hawayen tsoron Allah ne da ya kama su. Sai kuma masu mamakin ashe wai da gaske akwai mutum irin Kursiyya. Har a wannan lokacin, a fuskar Kursiyya ko kadan babu alamun nadama ko da na sani. Da kaga fuskarta ka san babu imani a cikinta. Babu tausayi ko digon tsoron Allah. “Daga haka nake cewa, aiki ya rage gare ku masu tsaro. Ku kai ta can bayan masarauta ku rataye ta. Sannan masu hoto zasu biku su tabbata sun dauki dukkanin komai. Hakazalika ni da Waziri da wasu daga cikin fadawana ba za a bar mu a baya ba. Za mu je a rataye ta a gabanmu. Idan an gama a dawo da gawarta nan, wanda suka ji za su iya su sallace ta. Babu wanda za mu farlanta mawa.”
Wata irin kururuwa Kursiyya ta fasa mai matukar karfl. Kururuwar da ta tsorata da dama daga cikin mutanen wurin Sai kallo ya dawo kanta. Ana ganin yadda take kokarin cire ankwar da ke hannunta. Da kam ta buga hannuwanta duka biyun da ke hade a jikin wani gini, sai ga jini sosai yana zirara. Cikin wata irin murya madaukakiya tace, “Na rantse da wanda numfashina yake a hannunSa baku isa ba. Ni Kursiyya nafi karfin ku rataye ni. Nafi karfln ku zartarda hukuncinku a kaina. Na gwammaci in kashe kaina a kan ku din nan ku kashe ni. Idan har na bari kuka rataye ni, ba zan taba gafarta wa kaina ba. Ba zan taba yafe wa gawata ba. Sannan kuma ku sani, idan na kashe kaina ba na bukatar ku sallace ni. Nafiso ku bar gawar tawa a haka, in ya so ta addabe ku da wari. A karshe ta fashe, daga haka har ta rube ta zama tsutsotsi.” Ta kyalkyace da wata irin dariya mai tarin manufofl. Da sauri suka yi kanta amma mai martaba ya dakatar da su. A ganin shi Kursiyya kawai dai ta fada ne, a ganin shi sam ba za ta iya kashe kantan ba. Sai dai yaga sabanin haka. Da karfi ta hau buga kanta ajikin gini, duk wanda ya nufe ta ta tunkuye shi da kai, sannan ta sake buga kan nata a gini, tamkar mahaukacin kare. Hakajini ya ringa malala daga kama, bugawar karshe ta buga fuskanta duka a ginin, sai ga jini ta hanci da baki yana zirarowa. Cikin azama mai martaba ya ce,
“Ku yi maza ku rike ta mana, kar ku bari ta cika burinta.” Dama abin da ya sa suka kyale ta saboda shi da kanshi ya ce su barta. Don haka mutum hudu suka yo kanta, suka rirrike ta. Ta riga ta flta hayyacinta, ta galabaita sosai. “Ku rike ta sosai mu tafl a haka.”
Mai martaba ya fada, sosai yake mamakin Kursiyya. Shi kam a yanzu tunani ma yake yi ita din ba mutum ba ce. A ganin shi wata halitta ce da aka yanko daga jikin shaidan. Daga nan suka rankaya zuwa can bayan Masarauta. Rabon da a yanke hukuncin rataye wani tun kafin Sarki Sani ya hau karagar mulki. Don haka yau ga shi ya yanke wannan hukunci kuma ga tsohuwar matarshi. Ajikin wani katon icce ne maratayin yake. Sun matsa kusa da iccen ana neman dora ta bisa dogon
teburin, duk sun sakankance ai Kursiyya ba ta da wani karfi a yanzu, ba su ankara ba ta kufce musu da karfi, ta karisa buga kanta a jikin katon iccen, a take ta zube wurin, bakinta cike da jini tana fadin,
“Ku kabbata babu wanda ya sallace ni idan na mutu. Na san makomata wuta ce. Kuma babu nadama a tattare da ni. Ku bari in karisa mutuwa da kaina kar ku…”
Ba ta iya karisa maganar ba ta hau fizge-flzge. Cikakken minti biyar ba a yi ba rai ya yi halinshi. Sauke ajiyar zuciya da tayi na karshe ne ya tabbatar musu da mutuwarta. Banda salati da ambaton sunan Allah babu abin da ke tashi a wurin. Suka kara jin tsoron Allah tare da fatan nisanta daga hali irin na Kursiyya.
Mai martaba duk da bai so yin kuka a gaban mutanenshi ba dole ya yi kwalla. Ba wai kwallar rashin Kursiyya ba, kwalla ce mai tarin ma’anoni, kwallar tsoro da mamaki. Shi ke nan ai ta kashe kanta ranka ya dade. Yanzu ya za a yi da ita?“
Sarki Sani ya ce, “Ba za a biye mata ba. Babu yadda zamu bar gawa ta dame mu da wari. Dole za a binne ta k0 da haka nan ne ba tare da an sallace ta ba. Don gaskiga ni dai ba zan iya sallatar gawar wadda ta kashe kanta ba.” Dukkanin mutanen wurin ma suka ce ba za su iya ba. Don haka aka yanke hukuncin daga nan kawai a nufi makabarta da ita a binne.
“Ki daina kuka Yaya Hafsa. Komai ya yi tsanani maganinshi Allah. Afarko naga kaman kina da courage, amma yanzu me yasa zaki bani kunya? Addu,a kawai za ki mata, Allah ya kai rahama kabarinta ya gafarta mata kurakuranta.‘ Hafsa ta kara kukan da take yi ta ce, “Halima ba wai kukan rashin Umma nake ba, kawai ina tsoron makomarta ne.” Cikin kwantar da hankali Halimatu ta ce, “Duk da haka dai ki mata addua.” Hafsa ta jinjina kanta hade da tsagaitawa da kukan da take yi. “Yauwa ko ke fa Yaya Hafsa.” Haka ta ci gaba da tausar zuciyar yar uwarta har dai ta samu ta yi shim.
Salbiyya ta kalli lndo ta ce, “Ni kam mutum daya nake son daukar ma hukunci a masarautar nan, wallahi ba na jin zan iya yafe mata abin da ta min. Dolenta ta tafi k0 ba ‘a SO Indo ta yi murmushi, “Allah yana son mai yafiya Salbiyya. Kiyi hakuri koma wace ce, ko mene ne ta yi miki ki yafe meta.” “Ki yi hakuri Uwar fada, amma fa ba zan iya yafiyar nan ba. Tabawa taci amanata, ta ha’ince ni,ta sa na kunyata a bainar jama’a.” A take ta zayyane ma Indo kafa abin da Tabawa ta mata lokacin da har mai martaba ya kore su ita da yaranta. “Uwar fada ta yaya zan iya gafarta wa Tabawa? Dole ta shaki takaici kamar yanda ta shaka mini.“ lndo ta jinjina kai. “Ba zan tilasta ki sai kin hakura ba, domin kuwa ta zalunce ki gaskiya. Amma ina mai miki al ilbishir da cewa ita kanta yanzu ta tsorata, tun ma sadda kika dawo.” “Ba ma za ta gama tsorata ba sai na sa an fiddo ta daga masarautar nan, an mata rakiya ta tafi ko ma ina ne.”
A cikin wannan rana Salbiyya ta sa aka kori Tabawa, bayan ta sharbi kukanta, cike da dana sanin abin da son abun duniya ya jaza mata. “Ganin komai nake tamkar a mafarki Ranka ya dade. Ashe da gaske akwai ranan da wannan lokacin zai zo?”
Mai martaba sarki Abdurrahmanu ya yi murmushi.
“Ai dukkan abin da aka gina shi a bisa sharri ko mugun abu ba ya taba tabbata, dole akwai ranan da zai karye. Karya bata taba dorewa Abu Sufyanu. Yau ga shi nan gaskiya tayi halinta. Halima ta bayyana bayan shudadden lokacin da aka dauka kowa ya zaci ta bar duniyarta. Ashe za ta dawo tsamo-tsamo a ciki ta ci gaba da rayuwa.” Fulani Maryama ta amshe da cewa “Wannan gaskiya ne mai martaba. To yanzu me ya rage?” Da faraa a fuskanshi ya ce, “Muje kawai a daura auren Yerimana da muradin zuciyarsa.” Yerima Abu Sufyan sai ya sunkuyar da kanshi kasa, kunya sosai yaji, amma fa dadi ne mamaye a kasan zuciyarshi.
“Mun yi magana da Sarkin Bilbah din ai, ranan Sati idan Allah ya kai mu za mu je a daura aure.” “Ma shaa Allahu. Allah ya tabbatar mana da alkhairi mai martaba.” “Amin ya Allahu. Ita kuma Jiddah wai gobe za su dawo da ita, ta dan ji sauki, likitocin kwalwa sun duba matsalarta, sai dai sun ce a kwakwalwarta akwai inda jini ya kwanta ta sanadiyyar buga kanta da tayi a karfe da karfl. Harjini ya taru a cikin kwalwar. Sun mata CT scan, da an ce ma sai an mata aiki an kwashejinin, to kuma sai suka ce wai bai kai yawan da dole sai an yi aiki ba. Sannu a hankali idan tana shan magani zai tsotse. Sai dai kuma abun zai iya ya rinka kado mata lokaci zuwa lokaci.” Fulani Maryama ta gyada kai, “To Allah Ya bata lafiya da dukkan musulmai. Shi ma kuma Yerima Bukar gaskiya sai an ja mishi kunne game da Hafsar Bilbah. Na dade da jin Iabarin gasa mata ayar da yake yi. ldan har ba zai iya rike musu diya da gaskiya ba gwara ya sauwake mata ta huta.” Cikin takaici mai martaba yace “Za mu yi magana da shi. Kuma zan sa ya ja ma wannan fitsararriyar Uwanin kunne, matukar ba ta bar shakiyanci ba zai sauwake mata.” 


(Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wallahi  Hakika Kursiyya ta samu hukunci daidai da yadda ta aikata. Na san kila wasu daga cikin masu karatu za su ga hukuncin kaman bai yi musu ba. Toh ina so ku sani, babu hukunci mafi girma sama da wannan. Domin kuwa kowa ya san hukuncin wanda ya kashe kanshi.) 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *