GIMBIYA SA,ADIYYAH
CHAPTER 35
Bayan wasu shekaru
Abubuwa da dama sun faru a cikin wannan shudaddun shekarun. Daga cikinsu akwai shafewar babin boka Fartsi. Kwata kwata babu komai da ya dangance shi, tamkar ma ba,a taba halittashi a doron kasa ba.
Sau da dama yakan fado ma Kursiyya ko Zabbau a rai, sai dai su kawar da tunanin nashi, saboda a ganin su sun gama da shi. Sun yar da kwallon mangoro sun huta da kuda. Babu sauran moriya da zaiyi musu nan gaba.
Hakazalika ko kadan babu Iabarin Salbiyya da yaranta Adnan da Anwar . Mai martaba ya manta da su, ya manta cewa ya taba sanin su a duniyarsa. A nasu bangaren kuwa basu manta da shi ba. Sai dai sun dauki fushi’ mai tsanani a kanshi. A ganin su basu da babban makiyi sama da mai martaba. Ya yada su, ya mayar da su banzan bazara, da su da babu duk daya. Wata rana Adnan ya samu Salbiyya na kuka, ya zauna a gefenta. Da hannuwanshiya share mata kwalla sannan ya tambaye ta dalilin kukan da take yi. “Ban taba ganin rayuwa irin tamu ba Adnan. Ban taba ganin aure irin nawa ni da mai martaba ba. Ya mayar dani da aurena amma tamkar babu. Ya mayar da ni mara ’yancin kaina. Kimanin shekaru goma sha wani abu ke nan rabonmu da shi. Bai taba binaken halin da muke ciki ba bare musa ran zaija mu a jikinsa. Ni kam hargwara ya sawake min fiye da wannan zaman rashin yancin kan da nake yi.” Adnan ya share yar kwallar da ta taru masa a ido, Yace “Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki Goggoji. Allah yana ganin kowa da kuma komar‘. Allah ba azzalumin bayinsa bane. Sannan kuma Allah majin rokon bayinsa ne. Duk daren dadewa akwai ranan da gaskiya zata yi halinta. Akwai ranan da zaigane muna da amfani a gare shi, Abin da nake so dake kawai ki daina damuwa. Ki mayar da komai ba komai ba. Sannan ki saka a ranki cewa komai nisan jifa kasa zai fado.” “Wannan haka yake.”salbiyya ta furta bayan ta share hawayenta. “Yauwa Goggona. Ki cigaba da hakuri kamar yadda kike yi a baya. Addu,a bata taba faduwa kasa banza. Ko ma wane irin kaidi ne Fulani Kursiyya take da shi watarana zai karye. Gaskiya za tayi halinta.”
Hafsa kuwa sau biyar kenan tana yin bari, har da na yan biyu tayi. Wannan dalilin yasa akace a daure mahaifarta na shekara biyar, ana yi ana neman magani har a dace. lta kam harma ta cire rai da samun haihuwa. Ta mika Iamuraanta ga Allah.
Har ga wannan Iakacin Yerima Bukar baya kaunarta. Bai taba zuwa Aurtayya da ita ta fuskar data dace ba. Bai taba zuwa mata da koda digin tausayi k0 soyayya ba. Yana daije mata ne domin biyan bukatar kansa. Yana gamawa kuma bai damu da nata bukatar ba zai samfeya kyale ta. Tun tana damuwa har ma ta gaji ta daina. Ta kai korafin ga Kursiyya har sau ba adadi amma ta gaza yi mata komai‘ A karshe sai ma tace mata kawai ta cigaba da hakuri, sannu a hankall komai zai daidaita. ’
Tsakaninta da kishiyarta ma dai babu wani sauyi. Kiyayya kullum kara ta,azzara takeyi. Ta kai munzalin da har Sarki Abdurrahmanu ya gano halin da suke ciki. Ya tara su sau ba adadi ya musu nasiha amma sun kiji.
A jiya suka yi wani fada mai tashin hankali, wanda labarin ya riski kaf al’ummar masarautar, aka yi ta cece-kuce. Ran mai martaba ya baci sosai, ya kira su su biyun sai kuma shi Yerima Bukar din. Ya yi musu tatas, sannan a karshe yace “Yerima Bukar, indai ni na haife ka to na baka umurnin ka kara aure, watakila Idan ka aura wata zasu hade kansu kowa ma ya huta da bakincinsu.”Yerima Bukar bai musa ba, don dama akwai wata yarinya daya taba yi ma fyade yaji ta yadda yake so, sai ta shiga ranshi sosai. A take ya amsa wa mai martaba cewa ya amince zai kara auren, yana ma da wacce yake so. Su dukansu suka daga kai suka kalle shi cike da mamaki, sannan suka kalli juna.
“Ku tashi ku tafi ku bani wuri. Idan kun ga dama kuyi hankali ku hade kanku. Idan baza kuyi ba ina mai tabbatarmuku da cewa kuna zaune zan saka shi auren ta hudu ma.” Sumi-sumi suka mike kowacce bakinta na motsi, sai dai basu ga fuskan magana ba. Babu wacce ta cewa kowa uffan harsuka kai marabarsu, kowacce ta nufi nata sashen.
Bayan sati uku aka daura auren Yerima Bukar da Uwani, diyar wani talaka sosai a Kubaisu.
A maimakon Hafsa da Jiddah su hade ma Uwani kai, sai Jiddah da Uwani suka hade ma Hafsa kai. Suka cigaba da muzguna mata, suna Ci mata fuska, har ta gwammaci zamanta ita da Jiddah kadai banda Uwani. Dama ance yaran matsiyata basu iya wayewa ba. Uwani ta zarce duk tunaninta.
Da shigowar ta gidan da wata biyu ta samujuna biyu. Duk da takaicinta da Jiddah taji sai taji kuma ba zata iya yi mata kamaryadda ta ma Hafsa ba. Hakan yasa cikin Uwaniya tasa har lokacin halhuwarta yayi ta haifi da namiji.
A ranar al ‘ummar Kubaisu sun shiga farin ciki mara misaltuwa. Dukjikokin da aka haifa wa Sarki Abdurrahmanu babu namiji duk mata ne.
Wannan haihuwar ta karajawo ma Hafsa bakin ciki a cikin gidan. Kullum cikin goranta mata ake. Ita yanzu duk babu bakin, Jiddah kuwa radau, ita ke kara dora Uwani a hanya.
Wani irin tururi yakeji zuciyarsa nayi masa. Baki daya gangar jikinsa ta masa nauyi, ga gumi da yake ketowa ta ko’ina daga gabbansa. Yajawo numfashi da karfi, sannan ya sauke nannauyar ajiyarzudya.
’kiyi gaggawar sakin kurwar Boka Fartsi Uwar biyu. Ki sake shi nace, ki sake shi da gaggawa.”
A cikin wani irin yanayi da ta dade bata shiga irinshi ba tace “Ba zan sake shi ba Maharazkhan. Nace ba zan sake shi ba, kayi duk abin da kake ganin za ka iya.” Ya yi murmushi bayan ya tauni Iebansa. “Kin san ina da karfin da zan iya fatali da duk wani abu da kike takama da shi?”
“Baka da shi Maharazkhan. Ba zaka iyaja dani ba, tun wuri ma karka fara saka ma ranka
hakan. Domin kuwa karya ce bayyananna.” Ya daure fuskarsa tamau, daka kalle shi ka san rikakken mara imani ne. Ya gyada kanshi.
”Ban san abin da ya faru ba kenan. Ban san da cewa da bana nan abin da kika yiwa
boka Fartsi ba kenan. Munyi sallama ni dashi kan cewa zan tafi aure An aura mini muradin zuciyata. Ina can ina sheka soyayya, ashe abin da kika aikata ga aminina kenan. Ki sake shi Uwar biyu, kigaggauta sakinshi, kinji na maimaita mlki.” DuguI-dugul ta iso gare shi. K0 bakin gwuiwarsa tsawonta bai kai ba, ta daga kanta ta kalle shi. “Ba zaka iyaja dani ba, ka kiyayi kanka ka tafi ka cigaba da shan Soyayyarka.
Karka jawo ma kanka masifa da bala ‘i kana zaman zamanka.”
Guntun murmushinda ko yima fuskarsa kyau baiyi ba yayi, sannan ya sake daure fuskanshi alamun babu wargi ka kadan a maganarshi. Zoben hannunshiya nuna mata. “Kin san cewa da wannan kadaizan iya tashin baki daya dajin nan. Zan iya gamawa da duk wata halitta dake cikinsa, ciki kuwa har dake? Kin sani. Kin san komai Uwar biyu. Saboda haka ki sake shi. Komai zan iya yi don ganin Boka FarLsi ya tashi da kafafuwanshi. A cikin ruwan sanyi da lalama kiyi abin da ya dace in tafi. ldan ba haka ba kuma zan kofsa. Zan yi abin da zaki share shekaru kina dana sani a kanshi. Kina ganin wautar kanki. Uwar biyu! ” Da karfiya daga muryarshi madaukakiya ya kwala mata kira. A gigice ta zaro idanuwanta, bakinta ya zazzalo waje harshenta ya yi tsawo. Hannuwanta ta daga Sama saiga kwarya ta bayyana a cikinsu. Ta koma ta zauna a gaban Aljani Maharazkhan.
take boka Fartsiya bayyana a cikin kwaryar. “Kiyi maza ki sake shi, dashi nake son tafiya yanzun nan.” ‘ Cikin rawar jiki Uwar biyu tace”Gaskiya kana da matsala Maharazkhan. Kai kam butulu ne na gasken gaske. Ka tuna cewa asali tare kake dani. Amma a Iokaci daya ka butulce mini ka koma wurin mugun mutumin nan. Kuma wai a kanshiyau kake neman gamawa dani da wannan sihirtaccen zoben naka. Gaskiya baka min adalci ba. Ka cuce ni sosai gaskia. Amana bata ce haka ba Maharazkhan.”
“Amana?”
Ya fadi haka a bayyane fuskarshi babu annuri. Tayi shiru bata kuma cewa komai ba tsabar
Tsoro.
“Kinsan amana kuma kika yi mummunan aikiga matar data kasance katotuwar butulu? Baki san da cewa abin data biye miki kuka ma Boka Fartsi kema wata rana idan ta samu wanda ya fiki zata biye ne a miki Wanda ma yafi nashi Ba
Uwar biyu. Kiyi aikin da na umurce ki, da gaggawa.” A kidime ta zabura. “Gishiri.” Ta furta a bayyane Saiga gishiri‘ya bayyana a tafin hannunta. Ta barbada a fuskar Boka Fartsi da idanuwanshi suke rufe. A take saiga su sun bude, suna yayyawata ko’ina.
AIjani Maharazkhan ya mika yatsarshi ta hagu ta isa cikin kokon. Yace “Bansan komai ba Boka Fartsi. Na tafi hutun angwanci na tsawon shekarun , shiyasa duk abin nan da ake yi ban san ana yi ba. A yanzu haka ma ziyara naje kai maka, ban same ka ba. Shi ne nayi bincike na tabbatar Uwar biyu ce ta kira ka kiran tsiya kazo. Ta maka wannan aika-aikar.
Komaiya wuce daga yanzu. Zan iya yin komai a kanka.” Ya shige cikin kwaryarshima, a tare suka bace, saiga su sun bayyana a dakin boka Fartsi.
Baki daya ya canza. Idanuwanshi sunyi jajur, fatarshin nan fara ta koma baka. Kayan jikinshi duk sun yayyage. Sumar fuskarshi ta kara yawaita, ya kara tsufa sosai.
Maharazkhan ya zaro zoben hannunshi ya mika ma Boka Fartsi. Yace”sa wannan, ka fini bukatarshi. Ka rike a hannunka zuwa na wani Iokaci, wannan muguwar matar na tabbata
ba zata kyale kaba, Amma idan yana a hannunka ba zata iya yi maka komai ba.”
Uwar biyu dake Iabe cikin gugu wa tana kallon su ta kyalkyace da dariya. Basu san cewa a yanzu ta mafijin haushin shi Maharazkhan dinba. Hope din ta a kanshi yake yanzu. Babban burinta ta dauki fansan abinda ya mata. Sai taji dadi daya cire karfinshi ya mallaka ma boka Fartsi. Zata samu damar daukan fansa a saukake kuma yadda ya kama ta.