GIMBIYA SA,ADIYYAH
CHAPTER 41
Da karfi Kursiyya ta mike tsaye, tamkar wadda aka kwalla ma kira take neman hanyar fita.
Mallam Khamis ya kalle ta hade da zare mata idanuwa. Ya nuna mata wurin data mike yace
“Koma ki zauna!” Ba shiri ta koma ta zauna, sai wuwwulla idanuwa takeyi. Zabbau kam in banda kuka babu abin da take yi. Ta tabbata a yanzu kam tasu ta kare. Ba makawa komai nasu ya gama lalacewa, jiran sakamakonta kawai take yi.
Mallam Khamis ya kalli Khalili yace, “Ka taimaka ka miko mini jakar can tawa. Don mu gaggauta rabuwa da gawar wannan matsafin.” Khalili da hanzari ya mika wa Mallam Khamis jakarsa, sannan ya zura ido yana kallon sarautar Allah.
Ya bude jakar, saiga wani littafl dan karami ya fiddo. Ya bude littafin, dauke yake da adduoi masu kaifi, wadanda ba ma a ko’ina ne aka sansu ba. Ya duba wadda yake nema din hade da rufe littafln, ya ce i was contemplating ne ko sau uku ne ko sau biyar ake karanta ta? Ban taba amfani da ita ba.” yayi murrnushi. “Kun san komai kamawa take yi.” Ya hau karanta adduar, sai da yayi sau biyar kaman yadda ya karanta, sannan ya guntsi ruwa a bakinshi, ya fesa a fuskar boka Fartsi.
Babban abin daya ba mutanen wurin mamaki shi ne yadda ruwan ya sauka a fuskarshi, tamkar an dora tukunya a wuta babu komai a cikinta, kun san idan ta dauki lokaci sannan aka zuba ruwa, za kuji tana wani cinnnn! Har yana tafasa gefe da gefenshi. To tamkar haka ne fuskan Boka Fartsi ta yi a lokacin da ruwan bakin Mallam Khamis ya sauka a kai. Yana gama cinininini din kuma sai ta hau tattalbewa, wani irin gari na murzowa daga kai, yana sauka a kasa. Sai da kaf fatarfuskan ta daye sannan ta yi baki-kirin tamkar gawayi. Sai zagayen idanuwanshi kuma ya yi jajur. Wani irin muni dai ta yi mara fasaltuwa. Mai ban tsoro da ban mamaki. Sai suka rinkajin wata irin kara tana kusanto dakin, duk sun tsorata amma banda Mallam Khamis da ya dukufa addu’o’i,jikinshi har rawa yake yi. Ya dora idanuwanshi a saitin inda ya hango wani bakin kare, wanda ya tabbatar da cewa aljani ne. Idamuwanshi jajur, bakinshi yafi na sauran kare tsayi. Ga shi wani irin kato da basu taba ganin kare mai girmanshi ba.
Bayan karen ya iso gaban gawar boka Fartsi ya dakata. Ya daga kanshi ya kalli Mallam Khamis da har yanzu bai dakata da addua ba. Sannan ya sunkuyar da kanshi, alamun Ladabi.
A lokacin da karen ya fara magana duk sai suka karisa tsorata. Khalili da waziri suka mike tsaye suna neman hanyar guduwa. “Ban zo da nufin cutar da kowa ba. Kayi mini gafara ya mallam, ka dakata da karatun nan har sai na dauki gawarshi mun tafi. Abin da ya kawo ni kenan. Matukar ba ka tsaya da adduar nan ba to ba zan iya aikata komai ba, hasalima sai illata ni da zaka yi.”
Mallam Khamis yayi shiru yana kallon shi. “Me ya sa kazo daukan gawarshi?” Karen yace “Saboda gawar kasurgumin boka kaman boka Fartsi ba karamin amfani take yi mana ba. Bare ni da ya kasance amini a gare ni kuma makusanci. Zanje in ci gaba da kallon shi ina kuka har ranan da tawa mutuwar zata dauke ni. Kuma na tabbata idan na bar muku gawan a nan babu abin da za kuyi mata. Bai halatta ku sallaci gawar mushriki ba. Gwara ni da zata amfana in dauka.”
Mallam Khamis yace “dalilin da yasa nake kan addua kenan, na tabbata da ma mafita z tazo mana. ldan har ba tazo ba din kuma ina da niyyar mu dauki gawan aje a tona rami kawai a binne ta. Amma tun da kazo, falillahil hamdu. Ni bazan hana ka k0 kuma neman yi maka nasiha ba. Kaga dai yadda karshen shi ya yi. Ka dubi yadda fuskarshi tayi dameji, bayan ya cika da munanan kalamai a bakinshi. Wannan kadai wani babban sako ne ga mai hankali.” Ya dube shi, “Ku tafi!“
Daga haka bakin karen nan ya dauki gawan boka Fartsi suka bace daga dakin.
Mallam Khamis yace “Alhamdulillah! Hakika babu karf’l babu dabara face a wurin Allah madaukakin sarki. Tsira da aminsu su kara tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammadu SAW.
Yanzu mai martaba aiki ya rage naka. Ka daukan musu hukunci ko ka kyale su, ni dai na gama nawa. Wa’yannan bayin Allah’n dake a kwance kuma zasu tashi da iznin Allah. Barcin wahala ne suke yi, da zarar ya sake su za su dawo tamkar ba ayi ba. Sai mu dage, mu tashi tsaye sosai mu yi riko da adhkar dinmu. Matukar muka yi sake to irin abubuwan da zasu ci gaba da faruwa damu ke nan. Hailala da istighfari mu damke su. Salatin manzo SAW, karatun littafi mai tsarki, yawan zama da alwalla da duk wani nau’i na ibada. Kar muyi sake. Kun daiji abin da boka Fartsi ya fada da bakinshi, sake da adhkar shi ya jawo suka ci nasara ga lndo tun tashin farko, suka yi galaba a kanta. Ga wannan garin maganin, ajika shi da zam~zam kullum Safiya a rinka ba Sa,adiyya da lndo suna sha, harna tsawon mako guda. Ni zan tafi ranka ya dade.” Ya mike bayan ya mika wa Waziri garin maganin dake kulle a leda.
Mai martaba ya mike shi ma hade da mika wa Mallam Khamis Ciro hannu suka yi musabaha. Yace, “Na gode sosai Allah gafarta mallam. Hakika samun irinku yana da matukar wahala. Kuma kuna da amfani mai tarin yawa. Lallai babu tabewa ga duk wanda ya riki Allah, ya bi dokokin Allah.
Bani da abin da zan iya biyanka da shi, Allah ne kadai zai biya ka. Sai dai ka yi hakuri, in ba damuwa Mallam zan dan dora wani nauyi a kanka.” Mallam Khamis ya yi murmushi yace “Ka wuce komai a wurina ranka ya dade.‘
Sarki Sani ya ce “Duk Juma’a nake rokon alfarma ka rinka zuwa masallacin masarautar nan kana yin wa’azi, kana dada jawo hankulan mutane a kan su ji tsoron Allah. Na lura har da sharrin jahilci ne yake bibiyar al’ummar masarautar.” Mallam ya ce “In don wannan ne babu matsala. In shaa Allahu za muyi bakin karfinmu, aikinmu ne wannan. Sai fatan Allah yasamu dace, yasa a amfana da iliminmu.’ Ameen suka fada su duka, sannan ya fice daga dakin rike da yarjakarshi. Yana fita Hafsa na shigowa. Da gudunta ta iso tana ta faman kuka tana fadin “Abba wai da gaske Ummana bata da laflya?” Hangen Kursiyya da ta yi hannunta jina-jina yasata yi gaggawar isa gare ta. Tace, ‘Ummana me ya same ki? Sako bai riske ni ba sai yau din nan. Hankalina a tashe yake sosai. Ga mutuwar uwar kishiyata, Jiddah, ga kuma rashin lafiyarki. Ashe ciwon har ya tsananta haka?” Har tayi ta kare babu wanda ya ce mata uffan. Sai kuma ta kai kallon ta ga mutum biyu da ke kwance ajere dajuna. Ba taga fuskokinsu ba, sai dai tun a yanayin kwanciyar taga ta san mai ita. Don haka ta matsa wurin ta tattaba ta, tajanye hannunta da ya dan rufe fuskarta.
Da sauri ta zabura taja da baya. Ganin ‘yar uwarta data mutu shekara goma sha biyar da suka gabata, a kwance kuma tana numfashi. ‘
‘Umma, Abba don Allah ku fada mini abin da yake faruwa. Wata nake ganin kamar marigayiya Halimatu.‘ Khalili dake daga gefe ya ce, “bame kama, ita bace ita ce fa da kanta gata nan. Kuma ba gawa bace ba, da ranta.” Hafsa ta zaro idanuwa cike da mamaki da tsoro, she couldn’t say anything sai rawar labba da take yi. Ta kalli inda lndo take ta kalle ta. Bata san taba ita kam.
”Don Allah ku fito ku min bayani sosai yadda zan fahimta. Kunce Halimatu ce wai da ranta, to ita kuma wannan din wace ce?” A nan ma Khalili ne yace ‘Sunanta lndo, mahaifiyar Gimbiya Saadiyya, data rasu tsawon shekaru talatin da daya da suka gabata.‘ Tamkar mahaukaciya haka Hafsa ta koma. Sai rarraba idanuwa take yi tana kallon sarautar Allah. “Gaskiya mafarki ne wannan nake yi. Don idan ba a mafarki ba babu inda hakan zata kasance da gaske. Ban tabajin inda mutum ya mutu ya dawo ba.‘ Sai a sannan ne mai martaba yace, “Ba mafarki kike yi ba Hafsa. Dukkanin abubuwan da kike gani a yanzu da gaske ne. Da gaske Gimbiya Saadiyya bata mutu ba. Ta dai yi rayuwa a cikin kwalbar shiri na tsayin shekarun da aka ce ta mutu. Ga kuma Indo nan, ita ma ashe duk shekarun nan tana nan, tana a cikin bandakin mahaifiyarki, wanda bata bari kowa ya shiga cikinsa.” Hafsa ta zaro idanuwa. Sai ta hau tunanin abubuwan da suke faruwa a duk ranan data yi attempting shiga bandakin Kursiyya. Harma ta gaji ta hakura. Lallai biri ya yi kama da mutum.
“Abba don Allah kayi mini bayanin dukkanin abubuwan da suke faruwa. Wallahi ba Hafsar da ka sani da bace. Wannan wata Hafsa ce data bidu da rayuwar duniya, tayi nadama sosai. Ka fada mini Abbana.”
Ta fashe da kuka hade da fadawa a jikinsa. Mai martaba ya hau dan bubbuga bayanta a hankali. Duk da cewa yana cikin tashin hankali shi ma, yana cikin tsananin tsanar mahaifiyarta, hakan ba zai hana shi kaunar ‘yarshi ba. Yana son ta duk da haka. Sosai kuma ya ji dadin sauyuwalta. K0 ha a fade mishi ba ya san ta yi nadama, ta gane komai da take yi a baya ba daidai ba ne.
“Ki nutsu sosai ‘yata, zan yi miki bayanin komai daga baya. Amma ina so ki kwantar da hankalinki, ki saka a ranki cewa komai kaddata ce daga Allah. Kuma babu ta inda Allah baYa jarrabtar bayinSa. ‘
Ki matsa wurin ‘yar uwarki, kuji gumin juna. Tabbas Halimatus-Saadiyya dinki ce, ‘yar uwarki ta jini, ba ta mutu ba da ranta, da kuma lafiyarta sosai.‘Da sauri Hafsa ta sake shi, ta koma inda Saadiyya take ta rike mata tafin hannunta na dama, a hankali tana fadin,
“Ki tashi ki kalle ni Halimatu. Ki tashi ki kalli ‘yar uwarki da fuskar aminci. Ba Hafsan da kika sani ba ce, ba Hafsan nan da ta tsane ki bace ba. Wannan wata Hafsa ce dake maraba da dawowarki a duniyarta. Take burin kuci gaba da yin rayuwa mai aminci a cikin duniyarku.
Don Allah ki tashi Saadiyya. Ki tashi in shelanta wa kaf duniyar nan cewa ‘yar uwata ta dawo gare ni. Nima din inyi alfahari da jinina.” A hankali Gimbiya Saadiyya ta hau bude idanuwanta, harta sauke su a bisa jikakkiyar fuskan Hafsa dake kunshe da murmushi hade da kuka. Murmushi ta saki ita ma Saadiyyar, ta kara kankame hannun Hafsa da ke cikin nata. ”Alhamdulillah!” shi ne abin da Hafsa ta fada, tana mai kokarin tallabo jikin Saadiyya, ta manna da nata. “Finally, gani ga Halimatuna. Gimbiya Saadiyya ta dawo gare ni a daidai lokacin da nake da bukatarta. Ki yafe mini ‘yar uwata. Ki yafe mini dukkanin abubuwan da suka faru. Wallahi ina kaunar ki Halimatu. Sharrin shaidan ne da rashin tarbiyya da na samu a wurin uwa. Amma har cikin zuciyata ina son ki ina kaunarki. Fatan za ki…” Da sauri Gimbiya Saadiyya ta dora yatsunta biyu a kan labbanta alamun Hafsa tayi shiru da maganan da take yi. “Ki daina tashin abin da ya wuce Yaya Hafsa. Gani na dawo gare ki, gani na dawo a duniyarki, kuma in shaa Allahu babu abin da zai sake raba kanmu. Ni ma ina kaunarki sosai.“ Ta sakan mata murmushi. Mai martaba sai ma ya rasa abin da zai yi. Wata irin faraa yake yi da yajima bai yi irinta ba. Ya dora idanuwanshi ga yaranshi da suke kusan kai daya, yana sakin lallausan murmushi. A zuciyarshi yana cewa ‘Saura Adnan da Anwar.’ ‘
Hmm