HADIN ALLAH CHAPTER B KARSHE
Cikin mamaki nura da mumy ke kallon driver da yake ta faman shigo da kayan nur a akwati,
” lalaima yarinyar nan watakan bata san gatse ba kenan” nur ya fda a ransa
” Hadi me zan gani haka wadannan kayan fah, kan yay magana Nur ta shigo mumy nawa, Nur wannan kayan ai sunyi yawa
” a’a mumy basuyi yawa ba, toh nur Allah ya tsare ” Amin mum”
.
Washe da asuba Nur bata koma bacci ba daman batai wani baccin kirki ba,
Kara shirya kayanta tayi sannan ta fito ta Dora girki
A bangaran Aisha kuwa kaguwa tayi nura ya dawo taji dalilin kwasar kayan, amma tin tana duba agogo har ta daina ganin bashi da niyyar dawowa a haka bacci ya kwasheta
Tin da tai sallar asuba ta shiga kitchen ta hadawa nura abinci kala kala, bayan ta gama girki tayi gyaran daki sannan tai wanka, dakin nura ta wuce kai tsaye, da sallama ta shiga dakin, ya amsa mata ba yabo ba fallasa, swt hrt ina zuwa haka naga kana shiri da wuri, unguwa zani, ya fda a takaice, wayarsa ya dauka da mokulli yabi ta gefenta zai wuce, swt hrt bafa ka ci abinci ba kuma na gama, ya juyo a fusace zaiyi magana, sai kuma ya fasa, muje na ci dan sauri nake, murmushi tayi ta rike hannunsa har dining, bayan sun fara cin abinci, Aisha ta dago ta kalleshi, swt hrt wai ina Nur ne naga bata kwana a gidan kwana biyu kuma sai naga jiya tazo ta dibi kaya,
Wani bakin ciki ne ya tokareshi shiyasa kenan yau har dayi masa girki ta zaci sakin nur din yayi kenan, nura ya fda a zuciyarsa, a fili kuwa yace ban sani ba nima jiyan ai da kin tsayar da ita kinji inda zata, ya fda rai a bace tare da daukan key dinsa yay waje daman ba jin dadin girkin yake ba,
Duk suna zaune a falo suna jiransa dan har kayanta ta fito dasu, da sallama ya shigo mumy ta amsa masa, nur kuwa ko kallansa batayi ba bare yaci arzikin gaisuwa, mumy kan kyalesu tai dan ta san da kansu zasu shirya,
Hadi ne ya zo ya debi kayan yasa su a mota sannan suka fice,
Nur ki gaishe da umma kafin nazo ga kuma wannan kya basu ita da Abban naki,
Mumy ta fda tana mika mata wata katuwar leda, toh mumy an gode ta karba tana sawa a motar, murfin motar baya ta bude zata shiga,
Cikin bacin rai nura ya daka mata tsawa ” uban waye drivern ki da zaki shiga baya,
” haba nura baka ga yarinya bace, da auta suna nan ma tare zasu tafi toh sun min yajin aiki nima, saura kana mata tsawa a hanya ma
” ke kuma ki fito ki koma gaba ban san rashin kunya, turo baki tayi sannan ta fito ta koma gaba yaja motar suka dau hanya
Tin da suka tafi ba wanda yay wa wani magana, ganin ta gaji da yin shiru yasa ta dakko wayarta da mumy ta siya mata jiya ta fara kallo da ita, a haka har suka karasa garin panisau mai albarka, gari mai niima garin da kowa yake son sa,
Yi hakuri sister Haima kar kiji ina koda garin mahaifata ce
Ihu nur ta Saki sanda ta ganta a kofa, wannan dalilin ne yasa nura sa burki bbu shiri
” ke meyasa baki da hankali nur sbda munzo zakinayi ma mutane ihu, turo baki tayi bata kulashi ba ganin bata da niyyar yin magana tasa shi jan motarsa sukai ciki,
” suna isa fada kowa ya bi su da kallo kuma ana yaba kyan yarinyar da ke gaban motar, a haka har suka shiga layin su, motar bata gama tsayawa ba nur ta fice da gudu
” ummana ummana ummana,
Kamar daga sama umma tajiyo muryar gudan jininta da sauri ta fito daga dakin dan ta tabbatar da ita dince ko gixon da ta sabayi mata nene
Allah ina rokonka da sunanyenka tsarkakaku guda dari bbu daya Allah ya bawa abul kair lpya Allah ya albarkaci rayuwarsa, Allah yasa ni auntynsa, mamansa da kuma duk wani alummar musulmai suyi alfahari da shi amin summa amin
.
Mutuwar tsaye umma tayi sanda taga yadda gudan jininta ta zama babba,
Rungumar da nur tayi wa umma ne ya katse mata tinaninta,
” ummana nayi misssin dinki alot,
Murmshi umma tayi dan ba sanin mene mssn tayi ba,
” nur kece kika girma haka,
” ummana nice ina Abba, kan umma tai magana nura ya shigo rike da karamar akwatin nura yara biyu kuma matasa na rike da sauran kayan
” yanxu nura da tare kuke kika kyaleshi da dibar kaya, sannu da zuwa nura umma ta fda fuskarta dauke da mirmushi kuma tana shimfida musu ta barma,
Bayan sun gagaisa umma ta gabatar musu da abinci da ruwa suka ci sannan suka dora hira sosai umma taji dadin yadda yarta ta ta koma
.
Bayan sallar laasar nur ta sake yin wanka ta shirya cikin wata dakakiyar doguwar riga ta shadda, tasa takalmi da jaka sai gyale kalar kayan, tsayawa fadar irin kyan da tayi bata lokaci, bayan ta gama shirinta ta fito ta tadda umma na shan inuwa,
Ummana bari na dan zaga zan iya kaiwa dare idan yayana ya dawo kice mashi na fita zaga gari,
” toh nur a dai kula, kai ummana yanzu fa na girma sosai, ” ai naga alama kan, dariya nur tayi tana ficewa
Ajiyar zuciya umma tace in banda *Hadin Allah* nur da ban san ya rayuwarta zata kasance ba, Allah ina godema, Allah kara hada kansu,
” nur na fita makotansu ta zazagaya duk inda taje sai tayi bayani ake gane ta
Wani gida ta shiga da ke gab da wakeken dutsen panisau yana kallon ramin da kuma masallaci a kofar gidan da sallama ta shiga,
Wata mata ta amsa mata tare da mata shimfida,
Bayan sun gaisa matar tace baiwar Allah ban gane ki ba fah,
Murmushi nur tayi,
” yanxu baba magajiya baki ganeni ba, daman zuwa nai ki kwatanta min gidan Asabe naje mu gaisa, cikin mamaki matar tace a ina kika santa, ” baba nur ce fah dazu nazo,
Sosai baba magajiya tai mamakinta,
Sannan ta kwatanta mata ta tafi,
Gidan dama ba boyayye bane a wajanta irin katan gidan nan ne da kowa da bangaransa,
Da sallama ta shiga ta kwa ci saa duk suna tsakar gida,
Wata kujera da ke gefe ta zauna tare da gaida su,
Sannunki asabe wallahi baki da kirki da auren ki ya tashi ko ki aika mini in ma fishi kike da ni ni yanxu nazo neman yafiya, cikin rashin fahimta matan gidan da kuma asabe ke kallonsu
” nifa baiwar Allah ban sanki ba, asabe ta fda cikin rashin fahimta
” mutum sai bakin jinin jaraba a kasa masa talla amma baa siya wlh in nice mai kasa miki tallan nan na dena kasa miki” amma ai baki manta mai fda miki wannan maganganun ba koh”
Nur ta fda tana kashe mata ido,
” in kinga na manta da mai fdan wadan nan zancen tah tabbas zan mata da zan mutu asabe ta fda tana kallon nur
” aikuwa rukayya (sunan asabe na gaskiya) kin manta kwa da zaki mutum dan kwa nur ce ni, ihu sosai asabe ta saki tana ruko nur yan gidan ma sakin baki sukai suna mamaki, dakin asabe suka nufa, sosai suka sha hira duk da mafi yawan maganar nur turanci ce yafiyar asabe ta nema sannan da zata tafi ta bata kyautar dubu goma, asabe sbda murna har kuka tayi, sukayi akan gobe da safe asabe zata xo gidan umma suje gidan ladidi sa sauran kawayensu,
Tana barin gidan asabe ba inda ta wuce sai gidan kaka,
Lkcin kaka na girkin abincin dare dan an kusa mangariba
” kaka wai umma tace ki bata dadawar hamsin da goran ashirin, nur ta fda tana turo baki a gaban kaka
Dariya kaka tayi ” jairar banza iskancin da kika tina kenan, murmushi nur tayi tare da rungumo kaka ta baya, a nan suka zauna suka fara hirar yaushe gamo har akai ishai ta ci abinci taiyiwa kaka sallama
Karon da nur taji tayi da mutum a sorone yasa kwala ihu
.
Tsawar da taji an daka mata shi ya dawo da ita daga hayyacinta, ke! Bakya ganine kina buge mutane?, jin muryar Nura yasa ta danyi ajiyar zuciya, kokarin janye jikinta takeyi ya kankame ta ajikinsa, suna tsaye ahaka cikin soron, takun tafiya suka ji yayi saurin saketa.
Ficewq tayi daga gidan, gidansu ta nufa, umma tana kwashe tuwo Nur ta shiga da sallama, ganin Nur yasa umma yin turus ke!,lfy kika dawo? Ina mijin naki?, turo baki Nur tayi tace yana gidan kaka, kan ta karasa magana tajiyo muryar abbanta, “maza ki kama hanya ki koma gun mijinki wannan ai sakarcin banxa ne, ” haba abba nifa hutu nazo, hutun uwarki bace mun dagani cewar abban, da hanzari ta fice, tana tafiya tana hawaye.
Sake karo tayi da mutum cikin hanzari ta dago jin kamshin turaren Nura ya tabbatar mata shine, toh ina zaije ta tambayi kanta, Kanwata ya ina kuma zaki?, ” abbane yace sai dai naxo gunka mu kwana tare bayan nikuma hutu naxo, taso bashi dariya amma ya gimtse dariyar yace”kanwata toh meyasa bakice musu ni nace ki kwana can ba, na fada musu abba yace ban isa ba, wani dadi yaji rike hanunta yayi suka juya gidan kaka.
.
Sai karfe goma Nur ta tashi daga inda suke hira ta nufi dakin kaka, ai kuwa kaka tayi maxa tace”maza fitomun zokibi mijinki dakin shi, turo baki tayi ta fara bubbuga kafa tana kunkuni ita ba inda xata, Nura kam ko ci kanki baice musu ba ya mike ma yayiwa kaka sai da safe ya tafi daki, kaka ma ta mike, tayi nata dakin, nur kuwa na tsaye abin duniya ya isheta, ta rssa nayi dankwalinta ta shimfida kan barandar inna ta kwanta, amma sam ta kasa bacci.
Nura yana daki shiru shiru ba Nur ba alamunta, har bacci ya fara daukansa, mikewa yayi ya fito hango Nur yayi kwance akan baranda cikin hanzari ya karasa, Nur ya fada, bata tashi ba bare ta amsa, idonta arufe kamar me bacci, ya sake kiranta Nur, nan ma shiru sai daya sake kiranta akaro na uku sannan ta bude ido, ransa ya gama baci, cikin bacin rai yace” tashi mu tafi daki, ganin yanayinsa yasa ta mike ba musu, dakin ta shiga kan kujera ta xauna, anan ya taradda ita ya haye gado abinsa, bai kara bi ta kanta ba.
Washegari tun kafin Nur ta tashi ya shirya yaje yayiwa su umma sallama ya bar garin, ransa duk a jagule.
Nur lokacin data farka ta ganta kwance kan kujera, ta mike tayi salla sannan ta fita dakin kaka ta wuce taje ta gaidata, bata tambayeta Nura ba, itama kakan bata ce gashi ba haka tayi wanka ta nufi gidansu.
.
Tun ransa nura yabar panisau bai kara waiwayar garin ba kimanin kwana ashirin da shida kenan, Nur kam duk tabi ta damu ta dena walwala kuma sam taki fadawa kowa halin datake ciki, haka abba yasa ta fara shirin komawa, tace ai sai yayanta yazo, nan abba ya rufe ta da fada akan maxa ta hada kayanta jibi xata bar gari.
Hakan kuwa akayi ranar da xata tafi sai kuka takeyi, suna zaune da iyayen suna mata fada, driver yaxo daukarta, nan ta fito suka dau hanya.
Direct gidan mummy aka wuce da ita, tarba kam tasha ta gun sirikanta.
.
Nur tana zaune falon mummy tana kallo Nura ya shigo da sallama, ta amsa mai juyawa yayi gun da take ya watsa mata harar yayi gaba abinsa, murmushi kawai tayi, dakin mummy ya nufa da sallama ya shiga, ina kwana mummy”lfy lau ya Aisha take, lfy lau tana gaisheki, mummykam tajine amma tasan sam Aisha bazata ce agaidata ba, nan suka tattauna abinda ya kawo shi sannan ya fito, daidai coridor suka hadu da Nur sannu kawai tace mai tayi dakin mummy, shiko ya kuma cika fam yayi waje.
Tunda ga ranar Nur bata sake sa Nura a idonta ba, haka ko yaushe xaixo bata sani sai dai taji yaxo, sosai abun ke damunta amma bata da wata mafita data wuce hakuri.
*bayan kwana biyar*
.
Nur tana son tafiya taje ta zaga gari, dakin mummy taje ta zauna, tayi shiru mummy tace”lfy kuwa yar mummy kikayi shiru koda damuwane?, kai Nur ta dagawa Mummy, sannan tace mummy dama ina so nadan fita na zaga garine, murmushi mummy tayi tace yo banda abinki ai mijinki xaki tambaya, inya barki shi kenan, maza kirasa awaya.
MiMikewa Nur tayi ta nufi dakinta, tagumi ta zuba, ta rasa ya zatayi tasan da kyar yayanta zai barta fitan nan, mika hanu tayi ta dauko wayarta akan bedsite, dialing number Nura tayi cikin sa’a kuwa ya shiga sai dai ba’a daga ba, ta kira kysan sau uku ba a dauka ba mayar da wayar tayi, can kusan minti talatin ta ji wayar na ruri, hanu takai ta dauko wayar, karawa tayi akunne tare dayin sallama.
Hello yayana antashi lfy, lfy lau ya kuke yasu mummy”kowa lfy, yayana dan Allah inaso ne in dan fita xaga gari shine mummy tace na fada maka, shiru yayi yana wani nazari, har Nur tace hello yayana ko baka jina ne, gyaran murya yayi yace ina jinki, ba yau ba sai wani lokaci kawai ya katse wayar, bin wayar Nur tayi da kallo tana mamakin Yayan nata, toh meta mishi haka da zafi daxai sa ya tsane ta haka, haka ta wuni adaki jiki duk ba kwari, taki fadawa mummy gaskiya yadda sukayi.
*3 weeks later*
Nur ce durkushe sai sheka amai rake, cikin hanxari mummy ta taimaka mata ta gyarata suka nufi asibiti, a mota ma sai aman takeyi, waya mummy ta dauka ta bugawa Nura, a rude yace gani nan xuwa.
Minti kusan talatin da isar su har anbasu gado Nura ya iso, gani mummy na safa da marwa yasa jikinsa yayi sanyi, ganin Nura yasa tayi gunsa da sauri, lfy mummy? Ya tambaya kwantae da hankalinka Nura xata warware laulayine, suna tsaye sai ga dr ya bukaci ganawa da mijin Nur cikin hanxari Nura ya bishi office.
Gaskiya tana tsananin bukatar kulawa, kuma ya kamata ta rage yawan damuwa don karya haifar mata da ciwon hawan jini domin yanxy ma jininta ya fara hawa kasan mai ciki, dafe kai Nura yayi yana sauraron likitan nan, godiya ya mai sannan ya fita.
Dakin da Nur take ya nufa, tana kwance tana bacci mummy na zaune kusa da gadon da Nur take, sosai tabashi tausayi guri ya nema ya zauna yana ta karanto addou i gareta.
.
Nur tana zaune falon mummy tana kallo Nura ya shigo da sallama, ta amsa mai juyawa yayi gun da take ya watsa mata harar yayi gaba abinsa, murmushi kawai tayi, dakin mummy ya nufa da sallama ya shiga, ina kwana mummy”lfy lau ya Aisha take, lfy lau tana gaisheki, mummykam tajine amma tasan sam Aisha bazata ce agaidata ba, nan suka tattauna abinda ya kawo shi sannan ya fito, daidai coridor suka hadu da Nur sannu kawai tace mai tayi dakin mummy, shiko ya kuma cika fam yayi waje.
Tunda ga ranar Nur bata sake sa Nura a idonta ba, haka ko yaushe xaixo bata sani sai dai taji yaxo, sosai abun ke damunta amma bata da wata mafita data wuce hakuri.
*bayan kwana biyar*
Nur tana son tafiya taje ta zaga gari, dakin mummy taje ta zauna, tayi shiru mummy tace”lfy kuwa yar mummy kikayi shiru koda damuwane?, kai Nur ta dagawa Mummy, sannan tace mummy dama ina so nadan fita na zaga garine, murmushi mummy tayi tace yo banda abinki ai mijinki xaki tambaya, inya barki shi kenan, maza kirasa awaya.
MiMikewa Nur tayi ta nufi dakinta, tagumi ta zuba, ta rasa ya zatayi tasan da kyar yayanta zai barta fitan nan, mika hanu tayi ta dauko wayarta akan bedsite, dialing number Nura tayi cikin sa’a kuwa ya shiga sai dai ba’a daga ba, ta kira kysan sau uku ba a dauka ba mayar da wayar tayi, can kusan minti talatin ta ji wayar na ruri, hanu takai ta dauko wayar, karawa tayi akunne tare dayin sallama.
Hello yayana antashi lfy, lfy lau ya kuke yasu mummy”kowa lfy, yayana dan Allah inaso ne in dan fita xaga gari shine mummy tace na fada maka, shiru yayi yana wani nazari, har Nur tace hello yayana ko baka jina ne, gyaran murya yayi yace ina jinki, ba yau ba sai wani lokaci kawai ya katse wayar, bin wayar Nur tayi da kallo tana mamakin Yayan nata, toh meta mishi haka da zafi daxai sa ya tsane ta haka, haka ta wuni adaki jiki duk ba kwari, taki fadawa mummy gaskiya yadda sukayi.
*3 weeks later*
Nur ce durkushe sai sheka amai rake, cikin hanxari mummy ta taimaka mata ta gyarata suka nufi asibiti, a mota ma sai aman takeyi, waya mummy ta dauka ta bugawa Nura, a rude yace gani nan xuwa.
Minti kusan talatin da isar su har anbasu gado Nura ya iso, gani mummy na safa da marwa yasa jikinsa yayi sanyi, ganin Nura yasa tayi gunsa da sauri, lfy mummy? Ya tambaya kwantae da hankalinka Nura xata warware laulayine, suna tsaye sai ga dr ya bukaci ganawa da mijin Nur cikin hanxari Nura ya bishi office.
Gaskiya tana tsananin bukatar kulawa, kuma ya kamata ta rage yawan damuwa don karya haifar mata da ciwon hawan jini domin yanxy ma jininta ya fara hawa kasan mai ciki, dafe kai Nura yayi yana sauraron likitan nan, godiya ya mai sannan ya fita.
Dakin da Nur take ya nufa, tana kwance tana bacci mummy na zaune kusa da gadon da Nur take, sosai tabashi tausayi guri ya nema ya zauna yana ta karanto addou i gareta.
.
Ku kasance tare damu anjima .
Allah ubangiji ka karawa sis na lfy, shamsiya abokiyar aikina(antyn abul), amin ya Allah.
Yau sati biyu nura bai je panisau sbda kar Aisha tai zargin wani abun yasa bays zuwa, yana kwance akan doguwar kujera idonsa a lumshe kamar mai bacci amma kuma ba bacci yake ba, tinanin nur kawai yake, kullum da ita yake kwana kuma da ita yake tashi bashi da wani tinani in ba nata ba,
” honey, honey, Aisha ta fada tana tabashi, kamar bazai bude idonsa ba kuma sai ya bude a hankali, sweat heart ya akayi, ina bacci kina tashina koh ya fda cikin shagwaba, ” kayi hakuri honey ko zamuje kaje kaga likitane dan naga kwanan kamar baka da lafiya, ” sweat heart lpya ta kalau, nura ya fada yana yana mikewa daga kan kujerar,
” yauwa honey daman hajiya ce tamin waya wai zamu tafi abuja zamuyi sati daya, maganar ba karamin batawa nura rai tayi ba abinda ya tsana kenan na halin mumyn su Aisha kawai saidai taima yayanta waya suxo suyi tafiya, Aisha ce ta katse masa tinaninsa, honey yanaji kayi shiru ba komai amma bn yarda da tafiyar nan ba amma fah in na isa, ya fda yana shigewa daki,
Da daddare nura na kwance a daki, shawara ta fado masa akan ya bar Aisha ta tafi shi kuma yay anfani da wannan damar yaje ya kara sabawa da nur tare da iyayenta, murmushin jin dadi yayi tare da mikewa yay falo, ganin tana zaune tana sharar hawaye yasa ya zauna kusa da ita sweat heart me aka miki kike kuka, haba honey kasan dai mumy kuma idan ka hanani zuwa Allah zata iya cewa na taho, ni kuma bazan so na tafi ba tare da ixininka ba, ajiyar zuciya ya sauke, ya isa sweat heart kije ki hada kayanki ku tafi amma fah nima bazan iya zama gidan nan baki nan gidan kaka Zan tafi na gwadayin sati koh zan iya, toh honey a gaida kakan
Tin safe nura ya sauke Aisha gidansu, ya kama hanyar panisau, cikin mintinan da ba su wuce 40 ba nura ya isa garin panisau da sallama ya isa gidan kaka bata nan, ganin bata nan ya taxi fada ko zai hadu da zabin ransa, haka ya gama zagayansa a fada amma bata nan *kofa* yaje ganin yana ta zagaye bbu ita bbu dalilinta, yasa ya tafi gidan kaka jikinsa a sabule,
Sanda yaje gidan kaka bata dawo ba, kusan mintinsa biyar ya gaji ya tashi da nufin yaje ya tambayi gidan su nur, har yazo zaure ya hadu da kaka tana shigowa, a’ a nura kaine a gidan, ” eh kaka nine amma kuma kin fiye yawo, waya fadama yawo nakeyi, lkcn ne suka karasa cikin daki,
” kaka ina kikaje na kusa awa a garin nan ba kya nan, bari kawai nura wallahi nur ce …… Kaka mai ya sameta nura ya tambaya cikin tashin hankali, wallahi yau kuaan satin ta daya bata fita toh yau jikin nata yayi tsanani sosai yanxu ma wani magani zanje karbo mata a gidan wani wanxami…… Kaka wani irin wanzami kuma baku kaita asibiti ba, aa ba a kaita ba a gida ake mata magani,
Kaka tashi ki rakani gidan muje naga jikinta,
Toh amma ka jirani tukunna bari na dawo ba yadda nura baiyi yabi kaka ba amma taki
Sanda ta isa gidan wanxamin ta karbo mata magani sannan ta wuce gidan su nur dan kwata kwata hankalinta baya jikinta tana shan tinanin matsanancin halin da ta bar nur a ciki
Ganin kusan minti 30 da tafiyar kaka kuma bata dawo ba yasa hankalinsa yaki kwanciya ya fito dan yay tambaya ko za a kaishi gidan su nur din
.
*1 *week* *later*
Nura yana ta shirin komawa kano, zuwa wannan lokaci ya saba da Nur sosai, yana tsaye jikin motarsa Nur ta fito daga gida, tayi haske ta rame sosai ahankali take tafiyar kamar bazata taka kasa ba, da sallama ta isa gurin motar, “yayana kardai har ka shirya? Ta tambaya tana rausayar dakai, sosai ta burge shi domin tana da sexy eyes, ya bude baki yace” kanwata karki damu xan dinga xuwa kowani karshen sati ina dubaki, kai kawai ta daga mai sannan sukayi sallama ya tafi.
Tunda Nura ya bar garin Nur ta sake dawowa gidan jiya, kazanta sai abinda ya karu domin tama daina wanka, wata ranar laraba Nur ta dawo daga tallan gyada, tana dire tiren ta shige bayan gida, tana fitowa ba wanke hanu ta dauko abinci ta fara ci.
Ke baki da hankaline zakici abinci da hanunki baki wanke ba kin fito bayi umma ke magana, Nur ta turo baki tace”haba umma wani wanke hanu xanyi bayan bada hanun zanci ba, a zuciye umma ta biyota aikuwa maza Nur ta mike tayi haryar fita, sai dataga umma ta koma sannan taxo tadau abincin tayi xaure acan ta karasa ci.
.
Yau jumaa yaune Nura xaixo amma aranar zai koma kasancewar Aisha ba lafiya tunda ta dawo daga tafiya, yanata shiri Aisha dake kwance kan gado tayi wuf ta mike tace, Honey ina xuwa haka? bayan kasan bani da lfy, ya dubeta sannan ya dauke kai batare dayace mata komai ba yace panisau zani.ta murtuke fuska wlh sai dai muje tare, da sauri ya juyo yace ina?” Tace gun kakar yace ina ai yau xandawo dan haka kawai ki zauna, tace gaskiya bazan xauna ba.ficewa yayi zuwa dakinsa ya barta tsaye bakin gado.
Nura yana tsaye afalo yana tunanin yadda zaiyi da Aisha can dai dabara ta fado mai ya nufi dakin nata, a kan bedsite yasameta ta zuba uban tagumi yacire hannun ta dago ta kallesa sannan yace ki shirya muje, tsabar murna bata san sanda ta rungumeshi ba, ya rada mata akunne amma fa sai sunday zamu dawo, ta daga mai kai sannan ta zare jikinta ta fada toilet.
Basu fi mintina talatin ba suka isa panisau, isar su keda wuya ko gidan kaka basu isa ba, Nur ya hango suna gada, ganin tare suke da Aisha karta xargi wani abu yasa ya canja hanya, ashe Nur ta hango motarsa, taga kuma ya juya ta kumbura suntum tiran tallan ta dauka tayi gida.
Kudin kawai ta mikawa ummanta ta wuce daki, batayiwa kowa magana ba, gadon ummanta ta hau ta kwanta sai bacci.
Misalin karfe hudu da rabi na yamma Nura yaceawa kaka xashi gidansu Nur, ya fito lokacin Aisha tana tsakar gida yace mata xaije gidan abokinsa tace adawo lfy, ya fice da sallama ya shiga gidansu Nur, ummace kadai azaune tana tankade garin tuwo, kujera yar tsuguno ya dauko ya zauna, ya gaishe da umma cike da ladabi, baba bayanannane, wlh ya fita amma ya kusa dawowa.
Umma taje ta kawo mai ruwa yasha yana ajiye kwanan shan yajiyo sallamar baba, ya amsa sanman ya karbi ledar ya kai kusa da umma, sosai suka gaisa da baba, “ina Nur ne ko taje miki aikane?baba ya tambaya nan umma ta fadamai yadda akayi, dakin umman ya nufa yana shiga ya ganta zaune bakin gado, karasawa yayi ya zauna yace yar baba lfy?tace abba sannu da dawowa ba komai, toh taso muje ga yayanki can yaxo ta nuke kafada abba baxani ba ai tun xuwansa na hango motarsa daya ganni sai ya juya da motarsa shine yanxu xaixo.dariya tabawa baban nata dakyar yasamu ta fito.
Muje xuwa in munyi caji domin wayata ba caji yanxu
.
” mumy naga kinyi murmushi, ” toh nura me kake so na maka,
” mumy kina ganin nur zata gafarta min abinda na mata, me zai hana, kaje ka gwada ka gani mana, kamar jira yake ya mike yay dakinta,
Jin alamar ruwa a bandaki ya tabbatar masa da bata fito daga wanka ba
” a bakin gadon ya zauna yana jiran fitowarta, baifi minti goma da zama ba nur ta fito daure da towel iya gwiwarta, ganin nura a dakin yasata tai kicin kicin kamar bata taba dariya ba,
Ko kallonsa bata kara yi ba tai gaban mudubi dan ta shirya, a hankali ya taso yazo inda take gaban sa na dukan uku uku
” kanwata” nura ya fda lkcn da yazo gab da ita, ko dagowa batayi ba bare yasa ran zata amsa
” tabbas na kasance mai laifi a wajanki, amma bazan gaza wajan baki hakuri ba, kiyi hakuri ki yafemun,kanwata wallahi bnda bakin baki hakuri dan tabbas na cutar dake keda yayana, idan baki yafen ba bazan taba samun nutsuwa,ki taimakawa rayu……. Harar da nur ta watsa mashi ya sashi kin karasa maganar da zaiyi,
” kaga malam ka tashi ka fita zansa kaya hanxu ai bani na biyoka ba bare ka kirani da karya, nur ta fda tana nuna mashi kofa alamar yay waje, jikinsa a sabule yqy waje
Mumy bata falon hakqn yasa shi kwanciya akqn doguwar kujerq yana sharar kwallah
.
Mumy ce ta fito rike da hannun twince zasu fita unguwa, ” mumy yanxu wai zaku tafi nur ta fda tana fitowa daga daki, ” eh dota so nake mu dawo da wuri, Mummy unguwa zasu, nura ya fda yana tashi daga kwanciyar yake, karar kofar da yadda aka turo kofar yasa mumy kin bada amsa gaba daya suka mai da duban su ga Wadda ke shigowa
” sbda tsabar ka mai dani yar iska ina tambayarka ina zaka shine zaka share ni koh, najika shiru baka dawo ba driver yace nan ka taho toh da izinin wa ka fito, Aisha ta fda tana huci fuskarta a murtuke, shidai nura mamaki ya hanashi cewa komai daman haka take mashi kamarshi Aisha ta zauna tana juyawa lalai zai koya mata hankali zabin da take ta zabgawa na rashin mutunci ne ya katse mashi tunaninsa,
” ke dallah malama ki fice mana daga gda kafin ranki ya baci banza jaka dabba, banda ke jahilace kyazo ki sami saar uwarki kice zakina fda mata magana, ai koh bata haifeki ba kya mutunta ta dan dan da ta haifo kika aureshi, nur ta fda cikin matsifa
” ni zaki fdawa magana mara dadi Aisha ta fda zata mareta, gam nura ya rike mata hannu, kyawawan mari yayi mata guda hudu a fuskarta, ke dan iskanci nur din zaki mara, sbda baki da mutunci uwata zaki nama rashin kunya, toh kije na sake ki saki biyu dan uwarki, kuma wallahi idan kika kuskura na dawo na sami ko tsinke naki a cikin gdana sai ranki yayi mumunan baci kuma kin rasa komai, dan dai ba a so ai saki uku a take da ba abinda zai hanani yimiki ukun kije ki auri fasikin bokan ki banza karya me bin maza,
Aisha da tai mutuwar tsaye tin da ya saketa ta fara kuka, ” mumy dan Allah ki bashi hakuri wallahi Allah ina sanshi sosai,
Mtswwwwwww, tsaki mumy tayi taja twince dinta tai waje, kuka sosai Aisha takeyi a gaban nura, ita kwa nur na zaune Akan kujera tana chrtn
” nur Dan Allah ki bashi hakuri, Aisha ta fda tana rike kafar nur, bugemata hannu tayi, dallah malama daina tabani da kazamtacen hanunki
Ganin nura bashi da niyyar hakura yasa ta ficewa tana rusa kuka kamar mahaukaciya
” kanwata kuna da tea a kitchen yinwa nake ji,zaka iya zuwa ka duba nikan bn sani ba nur ta fda batare da ta kalleshi ba jiki a sanyaye ya hado tea dan kadan yasha
.
.
Yau kwanan nura uku da dawowa gda amma har lkcn nur bata kula sosai ya shiga damuwar haka,
Da daddare nur da mumy na hira, nur tace, mumy ina san zuwa panisau gobe, je ki fdawa mijinki shi ke da ikon barinki ba ni ba,
” mumy dan Allah ki barni ba sai na tambayeshi ba sbda naga da kina barina, nur ta fda cikin shagwaba,
” lalai kan baki shirya zuwa panisau ba da kin shirya zuwa da kinje kin tambaya, ba yadda ta iya dole ta nufi dakinshi tana turo baki,
Yana kwance akan gadonsa ya lumshe idonsa kamar me bacci, a hankali ta turo kofar tare da shigowa, da sallama ta shiga tare da zama a gefen gadon, ” yayana, nu ta fda tana kallonsa, sosai ya bata tausayi Dan kana ganinsa zaka San yana cikin damuwa sbda yadda ya rame,
A hankali ya bude runanun idonsa da sukayi ja sbda kuka har wani kumbura sukai, ga wani azababab ciwon kai da yake damunsa,
” kanwata” ya fda da dashashiyar muryarsa, ” mumy tace nazo na tambayeka zani panisau gobe, shiru kawai yayi mata ya bita da kallo, ” yayana magana fah nake ma,
” nur kije Allah ya kaimu goben, ” Ameen” nur fa fda tana mikewa,
Hanunta ya ruko cak ta tsaya amma bata juyo ba a hankali ya taso da kyar ganin jiri na dibarsa zai fdi yasa nur zaunar dashi, itama ta zauna,
” nur ki duba girman Allah ki yafe mun, ki tina Allah ma muna masa laifi in munemi yafiya ya yafe mna bare kuma a tsakanin mu, kin dai san haka kawai bazan wulakanta ki ba aikin asiri, kuma kinsan asiri bbu wanda yafi karfin ya kama, toh ni meye laifina abinda na aikatashi ba a cikin hayyaci na ba, nur ki tina ku kuka dage da addua da karbar mun magani har na samu sauki, na sami sauki yanxu maimakon ki yafen muka rayuwarmu kamar da sai kuma ki juyan baya, da me zanji, bakin cikin da Aisha ta sani a ciki ko kuma azabar da kike min wadda zuciyata baza ta iya dauka ba, nur ya karashe maganar cikin kuka
Nur wadda tinda nura ya fara magana jikinta yay sanyi a hankli ta matsa kusa dashi tana share masa hawaye,
” yayana kayi hakuri ka yafe mun bazan karaba” ta fda cikin shagwaba, na yafe miki Nima ki yafen na yafema, ta fda tana rungumeshi,
Lumshe idonsa yayi, a hankali ta fara kisssing din sa, a take ya fara maida mata martani nan da nan suka bar hayyacinsu, ni dai auntyn abul dauko shi nayi nai waje na rufo musu kofa
A dakin nura ta kwana sai da asuba ta koma daki ko wannen su fuskarsa dauke da murmushi,
Wanka tayi sannan ta fara gyaran daki kamar yadda ta saba karfe bakwai ta gama komai ta ciga kitchen dan dora girki,
Jitai an rike mata kugu da sauri ta juyo sbda tsoro, ido daya ya manne mata, murmushi tayi masa
” ina kwana yayana” ” lpya lau kanwata, shi ya taimaka mata sukayi girki sunayi suna shan soyayyarsu,
Karfe tara dai dai suka gama shirya komai a dining,
Nur ce ta taimaka mashi yayi wanka, sannan itama tayi wanka,
A tare sukai break fast, bayan sun gama break fast nura yaje aka rage mashi suma, sosai nura yay kyau,
Karfe hudu suka fara shirin tafiya, doguwar riga pink ta saka tai roln da blue din gyale sai blue din jaka da takalmi, wayyo zokuga yadda nur tayi kyau kamar a saceta, sanda ta fito nura na mota na jiranta, mumy tayi ma sallama ta ruko hannun twince suka fito, tinda nur ta fito nura ya kafeta da idanunsa had suka karaso ajiyar zuciya ya sauke sanda ta hura masa iska a idonsa Tina nin me kake yayana,” ba komai. Kanwata kawai kinyi min kyaune nagode ta fda tana shiga motar yaja suka taxi
.
Sanda su nura suka isa panisau gdan su umma suka fara sauka sosai umma da Abba suka ji dadin ganin su kuma ko da yaushe suna wa Allah godia da wannan hadin tabbas wannan shi ake kira *HADIN ALLAH*
Basu bar gdan umma ba sai laasar a gdan kaka suka kwana, kwanansu biyu suka koma gda,
***********************************
Tinda Aysher ta fita daga gdan mumy a hargitse, gudu take sosai a titi ita kanta bata San inda take saka kafarta ba da temakon Allah ta karasa gda, kuka kan ta shashi kamar ranta zai fita,
Sai da Aysher ta kusan sati tana jinya har ta hakura ta fauwalawa Allah komai tai ta faman istigifari
.
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah su haneefah ana level 4 saura shekara daya ta gare mata ta gama b.u.k twince kuma na wajan mumy tin da aka yaye su basu komo ba, har lkcn nur bata kara samun wani cikin ba, soyayya suke mai tsafta tsakaninsu
” yayana wai me na maka ne tin dazu fa nake kiranka amma kaki ko dago kai ka kalleni sai faman danna laptop kake, Aisha ta fda tana tsugunnawa gaban nura,
Dago kansa yay ya kalleta, sannan ya cigaba da danna laptop dinsa, cikin fushi nur ta dauke laptop din ta dora a gado,
” wai nur me yasa zaki dame ni ne aiki fa nakeyi, nura ya fda fuska a tamke,
.
” wallahi yaya bazan bar ka ba sai ka fdan me nayi maka, haka kawai sai ka hau fishi da ni, nur ta fda tana mikewa
Janyota nura yayi ta fdo Kansa so kike kiji me kika min, nura ya fda yana shafata, daga masa kai tayi alamar eh
” suna nake so ki canza min bana son yayana din nan, amma kinki chanja min, nura ya fda a shagwabe,
Hmmmmm murmushi nur tayi kar ka damu yayana daga yau ka zama prince, 😳 zaro ido nura yayi,
” da gaske kike princess, daga mashi kai tayi, sosai yaji dadin sunan, nan danan ya rungumeta sosai a jikinsa ya fara kissing dinta ta ko ina,hannunsa ya zura cikin rigarta ya fara yawo dasu a ciki, ganin suna neman fita a hayyacinsu yasa na fita na janyo musu kofar
“A gurguje ta shiga wanka sbda lattin da tayi yau a makaranta gashi malamin da suke dashi bashi da kirki,
A falo ta tadda nura yana break fast, prince ina kwana, lpya lau princess, wannan saurin fa na meye, wlh prince na makara ne bnsan nayi latti shi yasa, toh muje na sauke ki sbda naga yadda kika makara din nan zaki iya tukin ganganci, nura ya fda yana mikewa,
.
Sosai yake gudu da ita akan titi har suka karasa cikin gate din makarantar motar doctor salim na tsayawa ta su nura na tsayawa,
Cikin hanzari nur ta bude murfin motar zata fita ya ruko hanunta, haba princess bbu ko sallama naga bai shiga ajin ba, prince ga motarsa nan fah ta fda tana ficewa,
Mamaki dauke a fuskar doctor salim yake kallon nur da ta fito daga motar abokinsa, cikin girmamawa ta gaidashi, ya amsa har lokacin fuskarsa dauke da mamaki
Kwankwasa masa windown da akayi ne ya sashi dago kanshi cikin mamaki ya fito daga motar salim, daman kana duniyar, dariya salim yayi toh ba gashiba ka ganni, ai anan nake aiki, salim ya fda, daman nur kanwar ka ce, dariya nura yayi a’a mata tace, sosai suka sha hira, yan ajin kuwa kowa sai yaba kyan nura suke suna dama ya sosu, sosai nur ta kulu ko me yasa ya fitoma,
Fatima plsss zo muje mu gaida doctor salim ko Allah zaisa abokin nasa yace yana sanmu, amma Maryam kar ya dizga mu fah insha Allahu bazai disgamu ba suka fada suna ficewa
Ran nur ba karamin baci yayi ba sanda su fatima suka fita
Malam ina kwana, su fatima suka gaida doc salim cikin sakin fuska, lpya ya fada a takaice,
Nura suka gaishar ya amsa musu cikin sakin fuska, ya karatu, Alhamdulilah, malam daman tambayarka zamuyi zamu karbo abu kar ka shiga ka hanamu shiga, toh kawai ya ce musu,
Gefen su can kadan suka zauna suna jiran nura,
Sai da suka kusa minti sha biyar sannan nura ya tafi saidashi sukai har lkcin idon nur na kansu,
Ba yadda basuyi ba ya basu number amma yaki, ya ce musu yana da aure dole suka hakura suka kyaleshi ya tafi
.
Suna shigowa aji ran nur ya kara baci, kusa da ita suka zauna,
Mtswwwww aikin banza mutum duk inda kuka ga namiji sai kun ce kuna sanshi, wallahi kunyi asara, nur ta fda cikin bacin rai,
.
Kiji mata ina ruwanki mu mukaga muna so, idan ma bakin ciki kike ya kashe ki kinga mutum ba irin mijinki ba,
Banza nur ta musu tq cigaba da saurarar karatunsa,
Karfe hudu dai dai suka gama lecture, su maryam na fitowa motar nura na tsayuwa, cikin sauri suka karaso wajansa a zatansu wajansu ya zo,
Sannu da zuwa, suka fda a tare, yauwa ya fda fuska a hade, kunga dan Allah ku fita harkata kan na gwabza muku rashin mutunci, salon matata ta ganni da ku ku samin zargi, zaro ido sukayi mata kuma, eh ko ban isa nayi matar Bane, ka isa mana Allah ya baka hakuri suka fda suna barin wajen, kusa da shi suka zauna suna kallonsa, ganin ya fara murmushi yana kallon wani guri yasa su saurin kallon wajan
Wayyo zo kuga yadda su fatima suka rude kaddai nur itace matar nura, indai kwa itace sun gama jin kunya,
A hankli take tafiya fuskarta a tamke, tinda nura yaga ta hade rai ya sa shi jin gabansa na faduwa, baya san fushin nur dinsa ko kadan,
Da sauri ya karaso inda take littatafan hanunta ya karba, princess ya karatun, naga kamar yau kunsha wuya sosai, hararar da ta watsa mashi ya sashi yin shiru, shi ya bude mata gaba ta shiga ya saka littafan a baya sannan ya shiga ya ja suka tafi
Maryam da fatima sosai suka ji kunya, kuma tin daga ranar suka dau alkawarin dena kula duk wanda suka gani in ba shi ya kula su ba
Da daddare nur tana zaune tana shan ice- cream nura ya shigo tare da sallama, ciki ciki ta amsa, kusa da ita ya zauna,
” kanwata ki gayan laifin da nayi plsss kai ki azabtar da ni da share ni, bbu abinda ka min, ta fda a takaice, ” wlh akwai amma ni bn san mene ba, ” kaje ka tambayi yan matan naka mana
Lumshe ido nura yayi sai a lokacin ya samu nutsuwa,
Princess wlh ba yan matana bane nan ya kwashe komai ya gaya mata, turo baki tayi gaba,
Toh kuma mene ko baki gamsu ba, na gamsu mana amma ni ka daina kaini makaranta daga yau ni zan na zuwa da kaina
” yadda kika ce haka zaa yi ranki ya dade, yadda yayi ya burgeta sosai hakan yasata yin murmushi, nan suka cigaba da hirarsu har lkcn bacci yayi suka tafi suka kwanta,
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah su nur a na semester karshe sosai ta maida hankalinta ga karatun ta bata wasa, ko abinci bata ci sosai, ta maida hankalinta ga boko, nura kansa baya samun kyakyawar kulawa
.
Kamar kullum nur na zaune a kan sallaya tana tq faman karatu nura ya turo kofar tare da sallama, ba tare da ta dago ba ta amsa sallamar,
Yan boko karatun ne, eh yayana, gaskiya na kagu ki gama dan nasamu cikakiyar kulawa kamar da, kar ka damu prince ai na kusa gqmawa, sun dan taba hira kadan sannan ya fice dan ta samu damar karatun ta
Kwanaki haka suka dinga shudewa, twince sun girma sosai dan sun fara makaranta
**************************************
Aisha ba irin naci da batayiwa nura akan ya maida ta ba amma yaki, haka suka hakura ta fammalawa Allah komai sosai ta ke istigifari ta kuma koma makarantar islamiyyya,
A haka har wani ya ganta shima ba wani babba bane amma yana da yara biyu matarsa ta mutu wajan haihuwa,
Da kyar Aisha ta yarda ta aureshi, sosai take bawa yaran kulawa, kuma suma suka dauketa tamkar ita ta haifesu, nasir mijin Aisha na santa kuma yana bata kulawa soaai, da kyar ta yakashe son nura ta fara yiwa nasir shi
*Allah sarki duniya makaranta Aisha dai anyi ilimi a gidan duniya*
Kwanci tashi ba wuya wajan Allah su nur an kammala jarabawa kuma cikin ikon Allah tana daga cikin wanda suka fito da first klax an bata koyarwa anan jamiar bayero, murna wajan nur ba a cewa komai
Ranar da ta karbo takaddunta da daddare nura na kallo ta shigo falon a kasa ta zauna kusa da kafafunsa
” yayana na gode hakika bani da bakin godia a gareka dole na godewa Allah da ya hadani da kai badan taiman Allah sannan da taimakonka ba da banxo matsayin da nake ba, ta karashe maganar cikin kuka
Dagota tayi ya rungumeta,kanwata karki min godia, ngde da like bani cikakiyar kulawa fatana a koda yaushe ki cigaba da sona har karshen rayuwar mu
Insha Allahu yayana ni takace har karshen rayuwata
Kisss ya manna mata sannan suka cigaba da kallonsu cikin so da kaunar junansu