HAKURI HASKE NE COMPLETE

 HAKURI HASKE NE COMPLETE 

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

A tsaye take a gefen titi rana ta dake ta, banda wari ba abunda take,gefe guda ga yayanta nan akwance, kowa yazo wuce wa kyankyamin su yake yi, ga yara kana na a tare da ita, danger ce ta bada hannu,motoci suka tsaitsaya,duk wajen motar da taje sai su kore ta, wasu ma su zuge glass din koda ko a sauke yake, taje jikin wata mota da gudu har tana faduwa, amma ta mike ta kade jikin ta ta karasa jikin motar, da hausar ta bata fita sosai.
“Ka temaka mun dan Allah katemake ni, ka bani abunda zamuci nida yayana” wani mugun kallo yai mata, matashin saurayi ne ya watso mata yawo a fuska, matsa ki bani wuri kazaman banza bararoji kawai, sadakar yalla kawai kun baro kasar ku kunzo kun dame mu a kasa mtsww,” dai dai lokacin da aka Basu hannu ya figi motarsa.


Kadan ya rage ya take ta, ta saki marayan kuka ta koma kan yayan ta, da gudu ta kara rungume su, ga yarinyar macen babbar kwance sharban, itace me dan girman ba lafiya, ga wata macen da namiji karami, gashi ta rasa yadda za tai dasu, kuka kawai suke dukan su basu da girman da zasu jure yunwa. Koga babba ya ya kare bare yaro, ta rasa ina zata sa kanta, kawai itama ta rushe da kuka. Cike da karfin hali babbar tace “adda kiyi hakuri zamu samu mafita insha Allah, komai na Allah ne, Alaife ce ta karaso wajen maman itama, ita ke bin Sheri,  adda yunwa zan mutu, kuka tasa ta rungume su, ta jawo Karamin ta rungume shi shi bama ya magana.
Suna wannan halin wata jibgegiyar Jeep tai parking dai dai su, daga mota ya kare musu kallo wow very nice, burina ya cika lallai dawa zatai nama, wannan dabge haka ga alamu ba wani tare dasu, ya daga waya ya kira wata number, “hello oga wallahi wasu buzaye nagani irin yan Nijar din nan, amma a wahale suke idan suka ji kiwo ba karamin kudi zamu karba dasu ba, dan iri ne me masu daraja” daga chan bangaren aka sheke da dariya, “shiyasa bana jinka na gida na, indai kaya ne masu kyau da inganci kasan su, maza maza ka tahon dasu” yai murmushi angama oga ya kashe wayar ya fito.
Cike da tausayawa a fuskar sa ya kara sa wajen su, “hajiya lafiya  nagan ku anan a gefen hanya”, cike da kuka adda tace “almajirai ne mu sadaka muke nema, diyata bata da lafiya karta mutu ka temake ni” yai murmushi a ransa murmushin mugunta a zuciyarsa, cike da tausayawa a fuska, hajiya bakusan cewa kama mabarata ake a kano ba? suka kara fashewa da kuka, ya kalleta ya hadiye yawu, gaba daya yarinyar da aka kira Sheri ta tafi da imaninsa, “yi shirun ki insha Allah yanzu zan temake ku, idan kunyar da zan kai ta asibiti, daga nan ku bini gidan mu wajen mamata, zaku samu masauki me kyau. Wat yarinya ce ta karaso da gudu tana haki, ta fada jikin uwar adda ga wannan kuci wata busashshiyar gurasa ce rabi, nan uwar ta karbe ta gutsutstsura musu.
STORY CONTINUES BELOW

Shi kansa da yake tsaye sai da ya tausaya musu, saboda yadda suke cin gurasar yar mini mini, yaron karamin ma Tai masa kadan, amma an kasa ta gida hudu, ita kuma kallon su kawai take tana hawaye ya kalle ta “adda idan kin amince dani muje gidan mu ko” ranta be kwanta da shi ba haka kawai, tai murmushi “mu musulmai ne, duk halin da muka tsinci kanmu muna godiya ga Allah, saboda haka kabar temakon ka, indai kasan cutar damu zakai gwara kabar mu a halin daka ganmu.” Jikin sa yai sanyi lakwas gaba daya jiyai kunya ta lullube shi. Muryarsa a shake ko fita bata yi, “nayi alkawari zan temake ku saboda Allah, bazan cutar da rayuwar ku ba, amma nima kuyi min alkawarin fada mun labarin ku.
Murmushi tayi! “zan baka labarin mu, amma sai munga yadda zaman mu a wajen ka ze kaya. Kuma baza mu zauna a wajen ka din din ba, abunda yasa zan bika saboda muna bukatar temako ne yanzu, amma da Sheri ta samu lafiya zamu kara gaba, insha Allah munfi so mu nemi komai namu dakan mu.” Jikin sa yai sanyi ganin halin da suke ciki, “nayarda indai kuka ga ina cutar daku ku tafi.” “Shike nan na yarda” ta kalli yaran “kuyi hakuri mu bishi, duk da nace mundena bin kowa, amma (hakuri haskene) kuyi hakuri muje.”
“Idan kaga kabar gidan nan wallahi kaban kudin dana lissafa ma”. “Kiyi hakuri ki sake ni, ki sakar mun rigata.” Hhhhhh! “wa  wallahi idan kaga na sake ka ka lale mun dubu ashirin da takwas kudin ankon nan” haba hajara “yanzu ina naga wannan kudin? abunda zamuci ma wani lokacin gagara yake, bare kuma kice sai na baki wannan kudin, kiyi hakuri duk abunda na samu yau insha Allah zan baki.” “Wallahi karya kake ka fita baka ban kudin dake jikin kaba” nan ta shiga chaje shi, dari uku da ashirin ta samu a jikin sa, “matsiyaci fakiri jeka.” Ta koma daki, kalmar tai masa ciwo dakyar ya iya fita.
Tafiya kawai yake besan inda yake jefa kafar sa ba. Idan da sabo yaci ace ya Saba da halin matar tasa, kullum ca ake masa yayi hakuri da ita, yayi hakurin ya gaji, kuma yana santa, ko ganin san da yake mata ne yasa take wulakanta shi haka? kullum yana rokon Allah ya bashi hasken hakurin da yake yi. Allah ya kawo haske rayuwarsa, ko shi ma ya zama cikaken mutum kamar kowa, yana wannan tunanin ana tai masa horn be jiba, kawai ji yai anyi sama dashi ya fado kasa tim, be kara sanin inda kansa yake ba, motar ce tai wani irin kugi ta tsaya.
makeken gida ne gari guda, motocin da suke harabar gidan ma bazasu lissafu ba, tsayawa lissafa su bata baki ne, dan wasu har sun gaji da kura kura har ta kamasu. Gida ne gidan alfarma, gidan da idan kazo shiga wani abu ne kamar miciji ze leko da kansa ya fesama turare. Gida ne da duk wani abun more rayuwa ba wanda babu a cikin sa, lambu ne, swiming pool, har da bangaren namun daji dana gida. Ko wanne da daban daban, gida ne iya kallon ka bazaka gano karshen sa ba, dan bazaka iya zagaye shi ba sai a mota, duk wani abu da ka sani a duniya na jin dadi akwai shi a wannan gidan.
Wata mata ce a wani daki a daddaure da sarkoki, kai daga gani kasan tana cikin halin hauka, tayi kashin ta da fitsarin ta duk a wajen, banda ihu ba abunda take. Wata yarinya matashiyar budurwa wadda bazata wuce shekara sha tara ba, naga tana ta faman aikace aikace, kai daga ganin ta kasan wahala da rashin hutu sun samu mazauni a jikin ta. Wasu hamshakan mata ne zaune a parlour, kai daga ganin su kasan cewa nera ta zauna a jikin su tayi kaka gida. Ba abunda suke sai ciye ciyen kayan fruit, wanda duk wani fruit suna da shi a lambu, a hankali take tafiya ta taho daga kitchen rike da manyan warmers ta nufi bangaren dining. “Ke yar mahaukaciya cewar uwar gidan a tsorace ta juyo kawo mun abincin nan” kije barin masu aiki ki dauko na sojoji ki aki musu, duk ma’aikataki kaiwa kowa nasa.” to Momy, ta wuce ta kai mata gashi
Momy, tana mikewa ta zabga mata mari.
“Hala baki da hankali ne?  To juye mun a kaina juye mun shi kinji ko” shiru tayi tace “kiyi hakuri” “hakurin uwarki” ta  daki bakin ta sai da yai jini, haka ta zauna sai da ta mula dan kanta ta bude tace “bude muga” sai sannan daya hamshakiyar tai magana, “niko hajiya Hafsa meze hana yarinyar nan ki bawa me gadi sadakar ta, ko ma huta da wannan mayyar yarinyar, duk fa abunda muke wallahi tana ran alhaji” mtsww ita da aure ai sai dai taga anayi, na gama yanke shawara zan kai ta gidan hajiya Halima, ta horar da ita horo me tsanani, nasan a chan ne kadai zata shiga hankalin ta.” Suka sheke da dariya ta kara gaura mata mari, “uban kine ze zuba mana abincin koko mahaukaciyar uwarki, kin bude ya sandare dan bakin ciki.
A hankali ta fara share kwallar idonta, idan da sabo yaci ace ta saba da wannan rayuwar ta gidan mahaifinta. kullum a wahale take, bata da sauran hutu duk da tarin yan aikin gidan. ta jawo warmers din ta bude ta zuzzuba musu a plates guda, dama farfesu ne na kifin gida, sai me suna kaiwa baki suka firzo cike da kyankyami. Hajiya Habiba ce ta mike ta dauki gaba daya farfesun na cikin warmers din ta juye mata. Tun daga tsakar kanta har jikin ta, wani wahallalen kuka ta saka saboda masifar yajin da take ji har cikin pant din ta, ihu take gaba daya ta haukace. Sai da suka yi dariya ta ishe su sannan suka dakata. Momy ce tace “kin mun dai dai antyn yara, gwara da kikai mata haka gobe ma ta sake, yar iskar yarinya jarababbu mayu, yar mahaukaciya kawai .” Ta sakar mata rankwashi wanda tsabar azaba ta saki fitsari a wajen, anty ce tace “haba hajiya banda mugunta ta dafo mana farfesu ta zubo uban gishiri, ga karni shedar ko kayan kamshi bata saba, saboda mugunta da mugun hali.”
“Kai kai kai! kan uban nan kai, wallahi yadda kikai mun fitsari a rug wallahi sai kin shanye shi. Kin kuma wanken rug din tas, yanzun nan kuma wallahi bayan kin ci duka.” Idon ta yayi jajur banda digar hawaye ba abunda take, banda mahaifiyarta da tuni tabar gidan ta shiga duniya, ta huta wa rayuwar ta dan tabbas sune ajalinta. “Ina miki magana kina jina haka, kin tsare ni da idanuwa to wallahi sai kinci ubanki” gaba daya suka mike suka fara dimar ta. Alhaji ne ya shigo da hanzari jin ihu da sautin duka, hankalinsa a tashe ya karaso dan yasan hanan ake jibga haka. “Hajjaju makkatu allah yaja da ranki, waya taba mun kene haka har yasa ki duka keda madam.” Sam ji yai baze iya tambayar meya faru ba, bare ya tsawatar musu, yasan dai abun yana taba ransa amma yazeyi.
Hmmm “kyaleta haka Habiba”, suka tsaya da dukan ta sun mata lilis, har targade tayi a hannu, “wallahi nida wannan shegiyar yarinyar ne fitsari tai mun a rug.” “Fitsari sai kace yarinyar goye ,to ko dan goye a gidana ana ganin fitsarin sane, wallahi ni nasan izayar da zan mata, bani ita nan na nakasa ta.” Cike da jin dadi suka damkata a hannunsa, ji yai sam baze iya dukanta ba, duk da wani sashe na zuciyarsa na ingiza shi. “Sojojin gate din farko zan kaiwa suyi mata bulala hamsin”  “Dan Allah Daddy da Momy kuyi mun alfarma zan kaiwa umma ta abinci, wallahi zan dawo ko kashe ni sai kuyi,” “baki isaba yau lefin ki ya shafeta itama bazata ciba.” Alhaji ya rausayar da kai “hajjaju makkatu, ai mata alfarma dan bariki zansa su kaita ta jigata sannan ta dawo.” ransu kal tace na barta dan kasa baki Alhajina, Habiba sai banka mata harara take a fakaice, zuciyarta fal tsanarta dan dai tasan Hajiya tasha gabanta ne.  ta mike hannu a sintime tace “nagode” ta nufi barin yan aiki, banda kuka ba abunda take, tana shiga ta fada jikin Inna marka tana kuka. kuka tasa itama ganin ta a wannan halin.
“Idan da sabo yaci ki saba da wannan rayuwar, hanan kiyi hakuri, haka allah ya kaddara miki taki rayuwar a gidan duniya. Kiyi hakuri da rayuwa hakuri haskene, maza ki kaiwa ummanki abinci ki dawo, ki wanka ki huta kici abinci kema nasna baki karya ba. “Bazan dawo ba inna, barikin sojoji daddy yace ze kaini ai mun hukunci,banda kowa banda ne sona,daddy ne yake dan rarrashina a bayan fage,shima yanzu ya dena bama na ganinsa tsoron su yake inna.” kuka inna tasa, ba komai akwai allah yanaji yana gani shize muku sakayya, Me kikai musu? “fitsari nai musu a kafet bansani ba, saboda azabar duka dana ke sha shiyasa. Haka suka hadu suna ta kuka, ta dauki abincin ummanta ta nufi dakin ta, dakyar take takawa hannunta harya fara kumbura yatsu biyu, haka take daurewa saboda barin da take da inda aka daure mahaifiyar ta tafiya ce ta tashin hankali. A mota ake zuwa, amma haka ta daba da kafar ta, amma me tana bude dakin a hankali, ta saki wani ihu ta zube a wajen, saboda ganin abun da bata taba tunani ba.

*To fans bari indaka anan. Allah yasa labarin yai muku, labari ne me taba zuciya, kubini a hankali danjin gundarin labarin. Yawan comment din ku shi ze bani damar yi muku shi yadda ya kamata*
            *Feedyn Bash*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

*Wannan book din tun daga farkon shi kar karshe sadaukarwane agareki, mamana takaina (MAMA JINJIN). Allah ya kara lafiya da nisan kwana, ki dade ki lasting ki shekaru irin na dabino. Fans kuyiwa mamana addu’a, Allah ya kara mata lafiya, ya bata lafiyan kafar ta.*

_*Jinjina agareki kawata takaina fatyma matar sardauna, amana takai miki kawata, ki huta kiji dadinki, kiyi yadda kike so daga ke ba kari a gidan sardauna. Wannan page din naki ne, kiji dadin ki ta gidana kiyi yadda kike so, more kudi a account ga sabuwar iphone a gefe.🤣🤣🤣🤣*_
              *5-10*

Hankalin ta a masifar tashe, ta bude motar ta fito a gigice, jinine kawai ke zuba a jikinsa, ta baki ta hancin sa. “Ya mutu! ya mutu!” haka kawai take furtawa, ta saki wata kara ta zube a wajen. Dai dai lokacin Allah ya kawo wani, shi ma yana tafiya a kasa, daga ganinsa kasan kinko yai masa katutu(talauci) yagan su a wannan halin, dai dai lokacin da ta zube a kasa, yaja wani mugun salati ya karaso da gudu. Ganin gawa da yai shimfide shi  ya kara daga hankalin sa, da hanzari yai kanta yana taba ta shiru, yai sauri ya tafi neman agajin jama’a, ba kowa a layin hanya ce shiru  cikin sa’a ya samu number Yan sanda a wani symbol dai dai kan kwana, ya zaro wayar sa da taci uban kyauro, naira goma ya rage masa a ciki, ya kira Yan sanda minti goma suka karaso, suka fara yi masa tambayoyi? Ogansu ne ya fara magana.

+
“Garin yaya haka ta faru?” “Wallahi yallabai nataho kawai sai naga wannan yarinyar ta zube a wajen nan, shine na taba ta naji tana numfashi, amma ban karasa kan wanchan din ba.” “Kai ya Isa haka, karya kake kai ka kashe su, shine kake so ka fitar da kanka, ta hanyar kiran mu, kun saba zuke jinin mutane a wannan hanyar, to wallahi sai ka girbi abunda ka shuka, wato zakai tsafi dasu ko shine kai me wayo ka kira mu a waya, to muje chan kayi bayani. Ku kwashe su muje a asibiti, shi kuma kai inspector hayatu ku wuce dashi station.” suka dauke su sukai asibiti dasu, shi kuma yana ji yana gani suka sa masa ankwa, suka wulla shi a motar ta, dake ko key din bata zare ba, inspector hayatu yaja, su kuma su d.p.o sukai asibiti dasu a motar su ta yan sanda me jiniya. hawaye ne me zafi da kuna ya fara silmiyo masa, a hankali ya furta “daga temako sai hakan ya zama lefi, ba binkice ba komai kun zartar mun da hukuncin da ban aikata ba.”

Tas kake ji dan sandan  ya wanka masa mari, zakaci ubanka ne idan munje station kayi bayani, irin kune kuke tsafi da mutane, ku sasu suyi hatsari ku zuke jininsu ku gudu, jibe ka sai kace almajiri duk mun san irin ku, to wallahi zakayi bayani ne, kwanaki the same wannan case din mukai mugaye.” ya hadiye kwallar sa. Ya kalleshi, “yallabai ka dakeni ba’akan hakkina, ba ka zageni ka jefeni da mummunar kalma duk akan abunda ban aikata ba. Ina rokon Allah yai gaggawar yi mun sakayya akan abunda ka aikata mun, nasan baya bacci shi kadai ze futar dani daga halin da nake ciki, daga temako ya zama sharri.” “munafiki zakai bayani idan munje station.” yana ji yana gani suka kai shi station, suka watsa shi a cell. Banda addu’a ba komai a bakinsa, haka suka kai shi cikin wari, da datti da kazanta suka ajiye.sukai parking din motar basu kuma bi ta kanta ba, ko tunanin su duba su Sami wani evidence basi ba hukumar wannan zamani sai hakuri.
Asibiti aka nufa das,u da sauri likitoci suka amshe su akai emergency dasu. Banda jini ba abunda ke fita a jikinsa, sabanin ita da tas take kawai dai bata motsi ne, amma tana numfashi, nan da nan likitoci suka fara basu temakon gaggawa, cikin ikon Allah sun tsaida zubar jinin jikinsa, amma sai dai hakuri dan duk yadda suka so ya farfado abun ya faskara, amma yana numfashi, basu san kuma takamai mai lokacin daze farfado ba. Ita macen sunyi nasara ta farfado, amma Allah cikin ikonsa ta rasa hankalin ta gaba daya, ba abunda take furtawa sai ya mutu ya mutu, nina kashe shi bani bace hhhhhh!. Abunda kawai take furtawa kenan sun tabbatar da kwakwalwar ta ta tabu.

Cikin tashin hankali Yan sanda suke, ganin ba kowa nasu shi namijin baya hayyacin sa, ita kuma macen ta samu tabuwar kwakwalwa, nan da nan suka yanke shawarar baza hotunan su a gidan TV da kuma social media, cikin sa’a ummin ta na zaune tana kallo, gaba daya hankalinta baya kan TV din, karfe goma ta wuce ba sajida ba alamun ta, daga zuwa shopping ga shi babanta baya gari, hankalin ta ya gama tashi, ta kira wayarta tana ta ringing amma shiru kake ji, ta aika a duba mata amma shima habu driver shiru. Cikin ikon Allah kamar an jeho shi ya shigo, hankalin sa a tashe “hajiya wallahi banga sajida ba, ba ita ba alamarta, bama wanda kawai ya ganta, tun fitar ta a mota da mutanen layi suka gani, shawara mukai cigiya gidan radio da TV da Yan sanda.” Jikin ta yai sanyi kawai jitai ance an tsince su a yashe a bakin titi, wani na yunkurin kashe su, daga kan da zatai taga kamar sajida ce amma hoton ya dauke, sakin ihu tayi wayyo sajida ta Allah ya tsaremu ke, wallahi jikina yana bani ba lafiya ba, maza habu dakko mota mu fita bamu ga ta zama ba.” Banda kuka ba abunda take suka fita suka nufi police station mafi kusa dasu.

Hankalin ta kwance tana zaune a rumfa, Banda tunanin inda zata samu kudin anko ba abunda take. kawarta me suna zubaida ta shigo, tana wani kyan kyamin gidan kamar Kashi ne a jiki, ta shigo ba ko sallama, matar gidan bata nan ne? “hajara! hajara!” mikewa tai zaune, “ina nan kawata karaso, ta shiga dakin haba hajara gaskiya ya kamata ki mike tsaye wallahi, wannan rubabben gida haka, wannan ai sai ya ruf toma a ka, gaskiya ki kwaci yancin kanki, da kyan ki da komai amma ace kin zama wata tantal batete, gaskiya da sake.” “To kawata yazanyi, meye shawara?” “shawara kona baki bakya dauka, idan nace ki kashe auren sai kice bazaki iya ba, ke kina sansa, so ba ko kwabo meze amfane ki da shi, gaskiya kawai kisan me zaki.” hmmmmm! “kawata kenan, ni kaina na fara wannan tunanin, dan nagaji da zama haka.”

“Yanzu mike ki shirya mu tafi, gidan wata hamshakiyar hajiya, irin wayanda suka ci suka tada kai, irin yan Kano to jeddah. “haba dan Allah kawata? Ina kika samo irin wayan nan hajiyoyin kawata?” Hhhhhh! “ke ba kin tsaya hauka ba, to wallahi idan mafarki kike ma gwanda ki farka, maza ki tashi mu tafi kafin anacen mijinki ya dawo.” Mtsww bar tuna min dan rainin wayo, kin san kudin anko ma kadai ya gagara ya bani, wallahi jiran shi nake ya dawo koni ko shi.” Haka ta shirya tasa kodaddiyar atamfar ta, duk cikin kayan ta sune na fita baban taro.mtsww wallahi nagaji da ganin ki da wannan shegiyar atamfar, kayan ki duka basu fi bakwai ba,lokaci yayi da zaki san me kike.” “Hmmm! muje kawai kawata, suka fice ba tare da ko dar ba.

*To fans anan zan dakata, idan naji comment in typing, idan ba comment ba typing, more comments more typing, yanayin comment yanayin typing.*

          *Feedyn bash*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________
*Dedicated to: Hassan ATK ina godiya kwarai Allah yabar zumunci nagode sosai🤝🏻*

                 10-15

Ya kwashe su a mota ba inda ya zame dasu sai wani haddaden asibiti me tsadar gaske me suna Providian. Nan ya kaisu suna zuwa aka karbi Sherie, saboda da kudi ba’a tsaya tambaye tambaye ba, ya ajiye musu ATM kawai yace su zara. Nan da nan akai emergency da ita, abu na farko da’aka gano shine yunwa tai mata mugun kamu, ga zuciyarta ta dan kumbura, nan da nan aka fara bata temakon gaggawa, aka saka mata dirp da magunguna sannan doctor ya fito neman wanda ya kawota. Yana neman wanda ya kawo ta amma be gan shi ba, abun yaba shi mamaki ganin almajirai a cikin asibitin suna zaune kan kijeru, sunyi jigum jigum cikin harabar ajiye mutane ta asibitin.

+
Ransa a matukar bace yake kwalawa security kira, ya zo jiki na rawa cikin bacin rai ya fara magana “wane wulakanci ne wannan zaku bari almajirai su shigo har cikin asibiti, asibitin ma cikin inda mutane ke zama su sha iska da jiran marasa lafiya.” da turanci yake maganar shima yake bashi amsa da turanci “kayi hakuri sun kawo patient ne da wani mutum dogo haka, da wata yarinya tafara galabaita” what! wace yarinya? Ya fada da karfi “yarinya wadda aka kawo yanzu Yar budurwa haka” zaro ido yai “wanda ya ajiye ATM dinsa yace kawai mu cira” “eh shine Oga.” Mamaki ya kama doctor din, meye hadin wannan gayen haddaden matashi da wannan kazaman, “yana ina yanzu? “naga ya fita a mota tun da kuka shiga.”

Adda da yaranta duk wannan hirar tanajin me suke fada, musamman Gobinya dake ta fisu girma daga Sherie sai Gobinya sai Ailaife sai karaminsu Yusuf. Hawayene ya zubowa Adda ta share abun ta, addu’ar ta daya Allah ya tashi kafadun Sherie, ita ba abunda ya dameta dama chan tasan su almajirai ne, agun Allah suke nema ba wajen wani ba. doctor yace da security “koma bakin aikin ka, daya shigo kace ya sameni a office” ya wuce office ransa a bace meye hadin wannan gayen da  mutanen da dukansu suna bukatar gado, yana ta mamaki ya shige office, minti goma tsakani ya dawo security ya isar masa da sakon doctor, to yace yayi wajen su Adda ya ajiye ledojin dake hannunsa, ya wuce wajen doctor zuciyarsa fal fargaba ko wani abun ne.

Bayan sun kara gaisawa doctor yake sanarwa dashi abunda yake damunta, jiyai ya kara narkewa a kogin tausayin su da begen ta, doctor ya gyara zama “niko meye sunan ka idan bazaka damu ba” murmushi yayi ” Umar Faruk” “masha Allah dama tambayarka zanyi? amma dan Allah karkaji haushi.” ok “ba matsala ina jinka yi tambayarka” ya gyara zama “game da mutanen da kuka zo tare, shin tare kuke kome? nagansu kamar almajirai” murmushi yayi “daga kauye suke chan Nijar mahifiyata ce da kannena, shiyasa amma akwai matsala ne?” “eh akwai gaskiya suna bukatar abasu gado da kulawa na tsawon sati guda, su sha drip da magunguna tunda da hali.” murmushi
yayi ba matsala nagode doctor da kulawa, nima nayi tunanin hakan, amma ban furta bane nagode sosai naji dadi, yanzu abamu daki me kyau da gadaje, su Fara cin abinci sai ai maganar, dan nasan Basu ci komai ba” murmushi yayi “Naga alama wallahi.”

STORY CONTINUES BELOW

Amma kunada masu jinya ko? eh ba matsala nan da nan suka gama magana suka fito daga office din, doctor yasa abasu daki dukansu me gado biyar, aka kaisu ya bude musu abinci ne me rai da motsi, ga kaji guda hudu a gefe nan da nan suka daka masa wawa, kawai kallonsu yake cike da mamaki, kananan hannu bibbiyu suke ci, ga kaji da lemu ka sukaci sukai kat, amma Adda ta kasa ci sai sa suka koshi suka ture. Tace “nagode sosai Allah yasaka, amma kadena wahala haka dan Allah” basar da zancen yai sannan tadanci itama, yace “Adda baki tambayi suna naba? tai murmushi najin kunya “to kayi hakuri dana, meye sunan ka? wani kallo ya bita dashi na mamki dajin dadi, “danki Adda yau an kirani da d’a nagode nagode, ya dinga godiya rabon da akirani da wannan sunan tun rasuwar mahaifiyata.” nan da nan idonsa ya kada yai jajur a hankali Adda ta dinga bashi baki, ya sanar da ita abunda za’ai musu ita da Yara, saboda sudan murmure su samu lafiya fafur taki.

Shima ko ya hade rai, “tabbas baki daukeni da ba Adda, yanzu kin kirani danki amma kin sanja, kin kasa yadda dani ba cutar daku zanba.” shiru tayi ,ba haka bane, wahalar tayi yawa.” dakyar suka hadu da doctor sukayi mata dalla, ta yarda kodan lafiyar yaranta, amma ita taki tace tayi jinyar yaranta, a hade mata su dukansu, haka akai aka dinga basu temakon gaggawa, suna samun kulawa, ga cima me kyau ga sittira duk yase musu, satin su guda aka sallamesu, tun daga ranar da ya kira Oga ya gaya masa ba nasara, yadinga fada ransa ya  baci ya nuna yayi fushi, ya kashe wayarsa be kunna ba saboda besan mezece da Oga ba tukun, sai ya kaisu ya boye ze samu bakin daze tunkari Oga, ya nuna shima fushi yai Amma ya huce, shima izuwa yanzu yasan yana ta neman sa, dan yasan halinsa mugun mutum ne maketaci, amma baya jurar fushi da faruk dan shike jan ragamar aikin nasu. A zaman su na asibiti yai mugun shakuwa da dukkansu, musamman Gobinya, ita Sheri bata damu da magana ba, an sallamesu duk sun warke garas abunsu, dama wahala ce da yunwa da datti ke damunsu sun samu kulawa kuma.
Suka fito daga asibitin, suka shiga motar tasa gaba daya tausayin yaran  yake, ga dukkan alamu sunga rayuwa, wayan nan bayin Allahn tausayi su ya shiga zuciyarsa, shi tunda Allah ya halicce shi besan komai ba sai zalunci, besan wani abu ba wai shi tausayi amma haka kawai yake tausaya musu, tabbas baze bari Oga yasan da zaman su ba, be taba alkawari ya cika ba amma a jikinsa yana ji ze cikawa wayan nan bayin Allahn, duk tausayin su ya cika shi, a hankali yake tuki zuciyarsa cike da tunani kala kala. ya gama yanke hukunci gidan sa na lamido cresent ya yanke ze kaisu, baze bari kowa yasan da zaman suba, saboda Oga da Abokansa ba wanda yasan yana da wannan gidan, idan ba yasan a dame shi nan yake tahowa ko idan yai karyar baya gari, duk ragowar gidajen su kowa bayai wa kowa gate da shiga, shiyasa yaji dadi ashe wannan dabarar zata amfane shi a gaba yai godiya ga Allah.

A hankali ya juyo ya kalleta hajiya zan kai ku gidana dake Lamido Crecent, ba wanda zesan da zamanku a gidan daga ku sai megadi, banaso koda wasa ku fito, nima bazan dinga zuwa sosai ba saboda tsaro, duk abunda kuke bukata akwai me gadi. Zan samar muku me wanki da me aikin cikin gida, shiru tayi ta numfasa “Da kace gidanku zaka kaini, nadauka kanada mata zaka kaimu wajen ta, shiru yayi a hankali ya kalleta gaskiya hajiya banida mahaifiya, mamata ta mutu banda kowa banda mata, banda kowa ni kadai nake rayuwa sai Ogana, da abokaina bandasu bana kula kowa, su kuma Basu da kirki basu da Amana.” shiru tayi kawai “Shikenan nayarda muje amma idan naga da cutarwa zamu tafi.” “Nayarda Adda insha Allah zaku manta da kuncin da wahalar da kuka shiga, insha Allah haske ya shigo rayuwar ku, nima inaji a jikina haske ya shigo rayuwata, nagode sosai Adda ta.”

Sherie ce ta kalle ta adda “kiyi hakuri Adda yanada kirki baze cutar damu ba, ki diba irin temakon da yai mana, amma kike tunanin ze cucemu,meyasa basu hada baki da likitoci ba sun cucemu, tunda yasan bamu da kowa akasar nan, babanmu wane irin tozarci ne bamu sha ba ta bangarensa, kowa kyamarmu yake gudunmu yake amma shi ya dauke mu Dan Allah ki kyutata masa zato koyayi niyyar cutarmu Allah ya sauya Masa zuciyarsa.” A hankali ya juyo yazo kalleta gabansa na faduwa, tun a asibiti idan tai magana hankalinsa tashi yake ina kuma ga ta kalleshi, ya rasa meyasa yake shakkar yarinyar, yarinya karama haka amma akwai baiwa ga nutsuwa da tsara zance, yanasan jin muryarta gwanin dadi. “Nagode kanwata da yadda Kika fahimceni”ta sakar masa wani murmushi daya gigita shi, wannan wace irin yarinya ce karya jefa ko gamo yayi, wannan tashin hankali har ina dakyar yake tukin, dan ta gama kashe masa jiki wani layi ya shiga an rubuta lamido cresent ajiki, sukayi tafiya kadan suka je bakin wani tangamemen gida.

Ba sabon abu bane a wajensu shiga makeken gida, shiyasa basuyi kauyanci ba. Horn ya dinga bugawa, da hanzari ne gadin ya taho yana zage wando daga gani daga bayi yake, ya bude masa gate yana daga masa hannu nan da nan ya karasa wajen motar, yaba bude masa ya fito suma suka firfito. Megadi ya fara kwalalo ido cike da mamaki yana kallonsu, kamar larabawa idan ka kallesu ya hadiye mamakinsa, suka gaisa a tsorace ya dauka basajin hausa. “kai iro” yace “na’am ranka ya dade” “wannan babatace da kannena, ka kula dasu sosai da sosai, daga kai sai su zan bari a gidan nan, ban yarda ka matsa ko nan da chan ba idan ba ni nazo ba, ban yarda ka budewa kowa kofa ba.”

“Za’ai yadda kace ranka ya dade girmanka ne ai, Allah yaja da girma sannunku hajiya sannu.” ya watsa masa harara koma bakin aikin ka sai na fito, ita ko sam sun kasa sakewa ko magana ta kasa, ganin wannan kayataccen gidan da sunan anan zasu zauna, “muje Adda ta kiyi hakuri ki saki jiki dani,’ ya kama hannun Alaife gobinya ta dau kaninsu Yusuf ita kuma adda tana rike da hannun Sherie saboda yadda jikin ta ba kwari har yanzu, da ledojin magani a hannunta suka shiga gidan bakinsu dauke da bissimallah da ambaton Allah.

Ficewa yai da gudu ya tsallake ta, ba komai tagani bq sai wani katon namiji, jikinsa da jajeyen kaya, yazo yana yankar gashin kan mahaifiyar ta, yai mata aski sol yanzu kuma ya cire mata wando, yana askar gashin gabanta, ga mahaifiyar ta cikin halin jinin al’ada, ga jinin ya diba a gefe shima. Tsallake ta yai yai tafiyarsa, be damu da ya gyara uwar ba tunda bukatarsa ta biya. Ita kuma bata san halin duniyar da take ba, ita ko wannan mahaukaciya tunda ya shigo ya watsa mata wani ruwa bata kara motsi ba. Yayin da budurwar take a sume a wajen, ba wanda yasan halin da suke ciki basu da matemaki sai Allah.

Suna zaune a parlour din da suke, Hajiya tace “Alhaji kaga yar’iskar yarinyar nan ko, maza bita nasan tana sashin su, kaje ka dam keta abincin ma bazata bawa wannan mahaukaciyar ba. Banda asara alhaji ina kai ina cida mahaukaciya” “kwarai ko hakane Hajiya” ba musu ya mike yai hanyar barin yan aiki. Yana fita Mommy ta sheke da dariya, “banza gaula” suka tafa ita da Anty, “amma meyasa kika kora shi?” mtsww! “kin manta da aikin mu? kinsan lawan mukasa yayo aikin ciro gashi da jinin jikin mahaukaciyar nan, ya debo yadda zata mutu gaba daya mu huta da wannan maitar tata. Tunda yaki sakin ta yaki bari tabar gidan, nifa ba abunda bazan iya yiwa kishiya ba a duniya.

Kinsan ke kanki Antyn yara kinsan meyasa nake daga miki kafa, saboda nasan cewa ke babyna ce, kina bani kayana a lokacin da nakeso, amma ban hada san Alhaji dana kowa ba araina.” Ran Anty ya baci amma ta dake tai murmushi “ni kaina a wajena hakan take,idan banda inasanki hajiya harkallar mu daya,da tuni an manta da zamaninki.” Ke dakata karki gayan maganar banza da wofi,kinsan na fiki komai na fiki malamai,na fiki bokaye, na fiki kudi, na fiki manyan Mata,” hhhhhhh! “Hajiya Mommy kenan, wallahi kinban dariya,me laya ka kiyayi me zamani ko kin manta?

Da Mata na kika ganni, da harkallata kika ganni, haka zalika bake kika kaini India gurin dodon tsafi ba. Ganinki nai a chan ganina kikai, saboda haka mubar wannan maganar, saboda cigaba dayin ta zesa mu ruguza alakarmu,wanda kinfi kowa sanin me hakan ze haifar.” Dariya Mommy tai “zolayarki nake tawan, yanzu haka ma kin tayar mun da sha’awata, ki daure muje kidan sauken marata ko naji dai-dai.” Hhhhhh! “Wallahi Mommy bakya gajiya ke, yanzu ki bari Lawan ya kawo mana sakon, sai mi shiga daga ciki, tunda kinga wan chan solobiyon mun korashi.”

A hankali Daddy yake tafe yana ta tunani, yazo barin yan aiki suka hadu da Inna. Yake tambayarta bayan sun gaisa, ta gaishe shi har kasa ya amsa, yana baya so tana dukawa ta tashi.”Inna ina Yasmeen?” Shiru tayi dan tasan idan za’a yankashi besan inda uwar gidan nashi take ba. Tasan dai ya hana a fitar da ita daga gidan,amma sam inda yasa a ware mata sashe guda,sam bashi bane inda take a yanzu. “Yallabai tana wajen uwar dakina uwargidan ka” hankalinsa ya tashi yama manta da ita sam, “kaini wajensu kai ni dan Allah haka kawai yaji bakinsa ya furta.

*Yawan comment dinku yawan typing my idan kuna comment da dogon sharhi kuga dogon typing idan babu na kame hannuwana😂😂😂*

           *Feedyn Bash*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

*WANNAN PAGE DIN SADAUKAR WANE AGAREKU ALL FEEDYN BASH REAL FANS GASKIYA NAJI DADI YADDA KUKA TAYAMU ALHININ RASHIN DIYARMU (FAREESA) ALHAMDULILLAH  ALLAH YA BAYYANA MUNGODE DA ADDU’AR KU GAREMU ALLAH YA BAR KAUNA ALLAH YA KARA TSARE MANA ZURI’A ALLAH YA BAR KAUNA YA BARMU TARE*
             15-20

Suka fara zuwa police station din kusa dasu suka bada sanarwa na batan yarinyar ta me suna sajida yar Alhaji Atiku suka bada hoton ta da komai
+
DPO din ya kwantar musu da hankali yace ta koma gida
Habu direba ya dakko ta suka koma gida
Ta kira Alhaji Atiku ta sanar da shi labarin batan Sajida
Duk inda tashin hankali yake ya shige shi
Yace ta kwantar da hankalin ta yana nan tafe gobe da safe jirgin karfe bakwai ze hawo ya dawo
Kwana tai tana kuka shi kansa mahaifinta be rintsa ba

Kanwar mahaifinta ce tana zaune suna kallo da mijinta

Sai ta samu a  TV ana ana haska Labaran karfe daya
Kwatsam suka ga hoton sajida duk inda tashin hankali yake ta shige shi
Ta dinga kiran Hajiya number din ta a kashe

Dama Alhaji Atiku baya gari wayarsa bata tafiya bata san baya nan ba
Ta dagawa mijinta hankali shi kansa ya tausaya mata yadinga  lallabata yai mata alkawarin da asuba zasu fita yanzu dare yayi tunda tana hannun Yan sanda suna asibiti ana basu kulawa basu da wata matsala
Kuka take kamar karamar yarinya saboda tana San sajida yarinya me hakuri ga ladabi da biyayya
Dakyar ya samu tai bacci saboda yadda ta kafa masa darun sai sun fita a daren

A kunnen ta akai sallar asuba

Duk yadda yaso tayi hakuri gari yai haske taki

Haka suka fito ya goyata a bayan machine dinsa ko iskar asuba bata ji burin ta taga Sajida kawai

Asibiti sukaje amma fafur likitoci suka hana ganinta duk da sunce yan uwanta ne amma sun hana dole sai sun je station sunzo da Yan sanda

Tana kiran Hajiya ta shiga muryarta ko fita ba tayi ga dukkan alamu taci kuka ta gode Allah tana dagawa ko ta rushe da kuka

Katime sajida ta sajida banganta ba ba ita ba alamrta ta share tata kwallar Hajiya gamu a asibiti munzo wajen ta jiya muka samu Labarin sanarwa a tvy shine tun asuba mukazo wajen ta amma likitoci sun hanamu ganinta wai sai Yansanda sunzo ko dan sunga mu bamasu karfi bane ta rushe da kuka
STORY CONTINUES BELOW

A kidime Hajiya ta tashi wane asibiti ne murtala what gani nan zuwa da gudu ta fita ta dinga bugawa habu direba daki a firgice ya fito dan bacci yace
Maza ka fito ba lafiya

Hankalin sa a tashe meya faru Hajiya anga Sajidan ne ko gawarta aka tsinta
Wata tsawa ta daka masa bansan iskanci da zancen banza kazo mu wuce malam asibitin murtala
Da hanzari ya shiga gidan dan yaga bata hayyacinta ya dakko mata takalmi ya dakko mukullin motar ya fito
Ta karbi takalmin tasa da hanzari yaja motar megadi ya bude musu cike da tausayin su da alhinin bacewar sajida suka nufi asibitin murtala
Gudu ya dinga shararawa saboda safiya ce ba kowa a hanya har suka isa asibitin
Ko parking bata bari ya gama ba ta fita da hanzari ta nufi emergency room
Tana shiga ciki ta tarar da Katime a zaune ita da mijinta sun hada uban tagumi
Da hanzari ta tare ta yauwa Hajiya ai tsantsar kamar ku tasa ke subar ki kiga yarki
Suka shiga office din doctor gaba daya Hajiya a kidime take doctor katemake ni  naga yata banda kowa sai ta
Ajiyar zuciya ya sauke tabbas Hajiya na yarda yarki ce amma case din nata babba ne bari in kira dpo din daya kawo ta
Haba doctor baka da imani ne yata ce nina haifeta ka gwada jinina da nata ka gani mana ta kara rushe masa da kuka dama a kusa take
Kiyi hakuri hajiya abunda yasa bani na karbesu ba nima dutyn dare na karba shiyasa amma bari na kira dpo amban lambarsa
Da kyar ya daga kiran dan yana jin dadin barcinsa hello waye ne yauwa yallabai doctor ne mahaifiyar yarinyar nan ce tazo kuma kunce kar kowa ya ganta sai kunzo
Cikin bacci barsu kawai zanzo anjima ya kashe wayar
Yauwa Hajiya kinga na fita yanzu yace ku ganta ba matsala suka shiga dakin da take ita kadai abun tausayi ta takure waje daya
Hajiya ta karasa kanta ta fashe da kuka meya sameki sajida me akai miki
Ta janye jikinta ta sheke da dariya meya sameki sajida me akai miki sai ta bushe da dariya ta kuma fashe da kuka nice nan da hannuna na kashe shi hhhhhhh
Kuka Hajiya ta fashe dashi ita da Katime doctor meye haka mezan gani Sajida tace fa
Yayi gyaran murya sai dai kiyo hakuri Hajiya ta riga ta samu tabun kwakwalwa dan yanzu haka asibitin masu tabin kwakwalwa zamu maida ta
Ihu Hajiya tasa ta tafi luuu ta zube a kasa nurses doctor ya fara kwalawa kira katime ta kara rushewa da kuka mijinta ne ya rungumeta shi kansa dauriya yake amma abun ya taba zuciyarsa

Suna fita daga gidan zubaida ta tare musu napep malam shagari quarters sukai ciniki suka hau suka tafi
Hajara tace keko zubaida ina kika samo ita kuma wannan hajiyar
Hhhhhhh kema dai hajara toni din ta wasa ce ko kin mantani a kasuwa muka hadu wani shago taje siyan kaya kinga kayan data siya sun haura dubu dari uku kuma duk nata ne nan da nan na shige mata
Hhhhhh kai zubaida baki da dama ko wulakanci bakya gudu
Yo wulakancin me ai indai da cittar muna jurewa ai bare ni kinsan ba kalar wadda za’a wulakanta bace
Shiru tayi dan tasan magana ta gwaba mata a hankali take nuna masa layin shedar tasan gidan yayi malam
Yai parking ya ajiyesu ta biya shi suka yi nocking gidan me gadi ya leko yana ganinta ya sheda ta
Yako tsuke fuska lafiya ko yauma kinzo maular ne koko tijarar zaki mun
Tako hade rai kai megadi ka kiyayeni wallahi ka fita idona idan ba haka ba wallahi aikin da kake takama dashi sai na sa an koreka
Ya kalleta ya bushe da dariya banza sauna ai gwara ni halak nake nema ba maula ba Hajiya kuma bata nan sai a juya
Ta galla masa harara wallahi ba inda zani sai na jirata ta dawo dan bakin ciki annamimi
Banza yai mata ya rufe gate garam
Bakin ciki ya gama cika zubaida ga kunya ta rufe ta batai tunanin ze yarfa taba haka
Jikin hajara yai sanyi ta kalli zubaida anya ko ba zamu hakura mu tafi ba
Cikin bacin rai tace bansan haka dan kin samu zan rufa miki asiri ki tsaya mana kiga bata rufe bakin taba motar hajiya ta sawo kai
Da hanzari ta mike yauwa gata nan ma suna tsaye tazo bakin gate ta danna horn ditt dit
Da sauri zubaida ta karasa a’a Hajiya sannu da zuwa
Ta zuge glass cike da fara’a a’a yana ganki anan meyasa baki shiga kin jirani ba
Ranta bace ta zayyano mata yadda sukai dame gadi
Idi idi da sauri ya fito Allah ya temakeki Hajjaju Allah ya kiyaye ki nan ya hau yi mata kirari
Ya isa haka  meyasa kake haka bance karka kara hanata shiga ba nasan da zuwan ta ai
Ayi hakuri Hajiya bata da kirki gadara take mun ne tana nuna mun kyankyami alhali na fita kyan gani
Ya isheni haka bansan ka kara shiga sabgar ta idan tazo ka bude mata kawai
Muje ciki ta wuce da motar ta cikin gidan
Zubaida ta kalleshi shekeke wallahi ka kiyayeni kaga dai matsayina ko ina gab da sawa a koreka kwata kwata daga gidan nan
Mtsww wannan ne kuma kinyi kadan nan gani nan bari tsakakanin mu da Hajiya wuce Yar maula
Ranta ya baci matuka itako Hajara dariya ce ta subuce mata
Zubaida ta watsa mata harara me kikewa dariya ta gimtse bada ku nake ba
Wuce muje ke kuma wallahi kawata banda kece sai munyi rashin mutunci kinsan bansan dariya
Hajiya na tsaye na jiranta sam bata lura hajara dake tsugune ba sai yanzu
Suman tsaye tai ganin wannan zankadediyar yarinyar me kyau haka ga diri sai hadiyar yawu take
Suka karasa Hajara ta gaishe ta ta kasa amsawa kawai kallonta take tana mata screening

*Bari indaka anan sai naji comment dinku ina godiya masoyana👏🏻👏🏻*

                 *Feedyn Bash*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________
           *SAKON TA’AZIYYA*

*(RABI’AT S.B.S) INA MIKO SAKON TA’AZIYYA TA AGAREKI ALLAH YA JIKAN YAYANKI YAI MASA RAHMA YASA YA HUTA ANNABI YASAN DA ZUWASA ALLAH YA GAFARTA MASA ALLAH YA BAKU HAKURIN RASHIN SA*

*MARUBUCIYAR BURIN MAHAIFIYATA (ANLAN NISA)INA MIKI TA’AZIYYA R RASHIN YARKI ALLAH YA JIKANTA YAI MATA RAHMA YASA ME CETO CE ALLAH YA BAKI HAKURI DA JURIYAR RASHINTA ALLAH YA GAFARTA MATA*
*Wannan page din sadaukarwane a gareki sudy beauty kalar kyau my blood sister Allah ya dafa miki kawata kuma yar uwata Allah ya kawo miji nagari cikin gaggawa kafin azumi mu cillaki gidanki mu rakashe mu jajige ki huta kiji dadin ki Yar uwa page din naki ne ina yinki irin sosai dinnan my sister Haleema madakee me kaunata yace ameen*
+
               *20-25*

Tsayawa fasalta girman gidan da kyansa da akwatuwar sa bata baki ne
Amma duk wannan tsantar kyan gidan be sasu sun razana ba ko su shiga halin dimuwa ko su gwada kauyanci
Shi kansa Umar Faruk yasha mamaki ganin yadda sam basu da nuna damuwarsu da shiga wannan hadadden gidan ba jikinsa yai sanyi kalau
Tabbas jikinsa yana bashi akwai lauje cikin nadi game da rayuwar wayannan bayin Allahn
Suna shiga suka nemi waje suka zauna akan kujeru kowa da abunda yake sakawa a ransa
Yusuf dake jikin alaife kwance yace Adda gida muka sanja namu gidan yafi wannan
Murmushi tayi tace a’a Yusuf ba zamu dade ba shima zamu barshi kaji
Yako fashe da wani gunjin kuka wallahi Adda bazan koma inda ake dukanmu ba ana koromu
A hankali ta mike ta karbe shi daga hannun alife
Kayi hakuri kaji babana rayuwa haka ta gada kudinga hakuri zaku ga hasken hakurin daza kuyi kunji
Haba Adda kidena yawan tuna abunda ya faru mun dogara da Allah na tabbata shize iya mana kiyi hakuri Adda cewar Sheri
Gaba daya yaran suka rungumeta suna hawaye saboda tunawa da tsananin wahalar da suka sha bayan shafe shekaru suna jin dadin rayuwarsu
Ba komai Sheri nagode miki ko bayan raina ki rike kannen ki ki dinga yiwa mahaifin ku uzuri dan Allah
Gaba daya sun daurewa Faruk kai yama rasa me zece musu gashi tace bata san tambaya
Sheri zo muje  na nuna miki tsarin gidan ni zan tafi ne yanzu
Murmushi tayi tom yayana muje nagani Gobinya tace nima zan biku
Suka fara zaga gidan yana nuna musu dakin adda ba abunda babu dana Sheri dana Gobinya da Alaife tunda dai yasan da Yusuf zata kwanta
STORY CONTINUES BELOW

Gidan yayi musu dakuna ne birjik ba abunda babu harda kitchen ko wanne da bandaki a cikinsa
Yara sai murna suke sun fita daga wahala Faruk yace bara yaje yayo musu siyayya suka dawo parlour yaiwa Adda sallama yace kozaki rakani Sheri ta girgiza kai ya fita yana murmushi
Ya karayi wa me gadi takara akan kula dasu ya amsa cike da biyayya
Ashe haka yake da kanne masu kyau shiyasa shima yake da kyau ashe  matsalar dai shi baki ne
Ya fice da mota abun tsautsayi yana fita daga kan kwana Ashe Oga ya biyo hanyar shima yaga fitowar motarsa
Yayi mamaki matuka beyi tunanin yana Nigeria ba saboda duka layikansa a kashe suke yana doubting koba shi bane sai yaga tabbas shine
Dan ga venz dinsa nan shine tabbas to meya kawo shi nan har yake cikin farinciki haka me yake boye masa haka
Nan da nan ya bishi a baya yaga yayi hanyar tarauni ya dinga binsa a hankali saboda a sabuwar mota yake baze taba gane shi ba
Yazo wajen wani sabon abokin harkallar sune yace ya jira shi a wajen yai ta neman Faruk din be same shi ba shi yasa yazo da kansa
Kasuwar tarauni ya shiga ya nemi waje yai parking kusan minti talatin yaga ya fito bayansa yara ne dauke da kaya niki niki aka dinga lodawa a mota
Sai da suka gama ya juya ya wuce ya kara koma lamido cresent din abun ya bawa Oga mamaki saboda ko tantama bayayi shine
To meyake boye masa ya dauke shi uwar shi ubansa a duniya baya boye masa komai dole sai ya lalubo meyake aikatawa
A hankali yake bin bayansa har sukazo kofar gate din ya danna horn shi kuma ya fara slow a hankali me gadi ya hangame masa gate din
Yusuf ne da Gobinya suke wasa a harabar gefe Alaife ce da Sheri keta hira hankalinsa ya tashi ganin su a harabar
Oga suman tsaye yai ganin wayannan luntsuma luntsuman matan wanda daga gani suka ji kiwo za’ai mata
Ta mirror yaga wata mota na slow a bayansa da sauri ya bude ya fito ganin haka oga ya shiga layin dake hannunsa
Dama wanda zasu hadu yana ta kiransa yai masa kwatance yana layin dama mace ze turo masa

Gaba daya jiyai be yarda da motar ba yana tsaye yasa an rufe gate din yaga wata tsaleliyar budurwa ta bude gaban motar ta shige ya saki ajiyar zuciya

        *************

Inna ce tai masa jagaba suka fito ranka ya dade wajen da take baze zuwu da kafa ba
Nan da nan ya kura driver aka dauke su aka kai su har bakin wajen da take gab da barin namomin daji
Ya kalli Inna yanzu sadiya ce take rayuwa a wannan wajen a Wannan halin kawai ya fara hawaye
Banda murna ba abunda Inna take dan jiya tasa akai musu saukar alkur’ani saboda yaranta kolawa ne na kauye
Ita take karbowa Yasmeen rubutu da magnunguna shi yasa bata sake da bata magani ko kadan
Shiyasa sam bata so ta matsa daga kusa da ita tsafi yana da tasiri ita kuma addu’a sai a hankali tunda Allah ake gayawa ba gaggawa ake ba
Saboda irin zaman da sukai da Haleema mace me karamci da alkhairi me maida kowa nata shiyasa take temaka musu da temakon magani
Tana yawan kaiwa Haleema rubutu kuma bata musu take sha tasan dai Allah ne be kawo karshen lamarin ba
Suna shiga tai masa jagora hankalin sa a masifar tashe

Yaushe rabon sa da Haleema yake wa kansa tambayar a kalla shekara goma sha biyar
Shi dai tun da ta fara hauka aka nemi Usman aka rasa be kara waiwayar taba sai yau
Ji yai kuka na shirin subuce masa amma ya dake Inna na gaba suna bin wani bangare
Wanda ake kiwon kaji a wajen ya gama shiga tashin hankali
Suna zuwa bakin dakin suka ci karo da Yasmeen Inna tai kanta da gudu
Yasmeen meya sameki Alhaji ya bangaje Inna yai kan matarsa
Kuka ya fashe da shi ganin wai wannan ita ce Haleema yar uwarsa jininsa matar ladan nomansa
Kuka ya fashe dashi wiwi ya rungumeta tsirara take numfashi kawai take amma ba motsi
Ga jini yana fita daga gabanta na al’ada da kuma yayyanke ta da yayi
A hankali Yasmeen ta farka saboda ruwan da Inna ta kwara mata
Duk wani ruwa da Inna ta kwara wa Haleema bata farfado ba
Sungumarta kawai suka ga yayi yai waje da ita da gudu jikin ta jina jina
Kan nan yasha aski sol tun daga ciki yake kiran driver yana juya mota maza maza
Da hanzari ko ya juya ta duk ya gigice yana zuwa ya bude ya fada muje maza Providian
Duk da jikin ta ba kwari amma itama gudu take tana kiran ummata karka tafar mun da ita
Tana fitowa suna jan motar ta saki ihu da kuka tana kiran ummata ze karasa kashe mun ita
Inna ce ta fito ta rike ta ki nutsu mijinta ne me Santa baze cuce taba ina har ta fara fita hayyacinta

*Bari na dakata anan Allah ya bamu hasken hakuri my fans nice taku a kullum a koda yaushe*

          *Feedyn Bash*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________
_*Wannan page din sadaukarwane agareku kuyi yadda kukeso da shi Fateema U Adams da Jadeera ba abunda zance daku gaskiya bakina baze iya furta adadin godiya ta da jin dadin yadda kuke mun comment ba gaskiya ina godiya Allah ya bar kauna kuyi yadda kukeso dashi my Fans*_
             *25-30*
Nan da nan aka fara bawa hajiya temakon gaggawa dan ta dawo hayyacinta
Katime kuka kawai take tana tausayawa Hanan ganin yadda take ta sheka dariya ganin hajiya ta fadi
Cikin ikon Allah Hajiya ta farfado amma jinin ta yai mugun hawa ga zallar damuwa data ke ciki
Karfe goma Alhaji ya sauka a Nigeria garin kano yana zuwa gida megadi ya sanar masa basa nan
Ya kira wayarta Katime ta daga tana kuka ta gaya masa suna asibitin murtala
Motar data kawo shi ta airport ita ya juya suka koma asibitin
Suna zuwa ya shiga emergency dai dai lokacin DPO suka shigo asibitin
Kicibus sukai da juna sun san juna sosai tare sukai secondary suka gaisa a gaggauce
Lafiya Alhaji naga kana sauri haka kanada patient ne naganka a firgice haka
Eh wlh yata ce ba’a gani ba to kuma na dawo na kira me dakin nawa akace tana nan
+
To muje nagansu ai da ka sanar Allah yasa lafiya dai suka shiga ya kira Katime ta fito suka shiga wajen likita suka je har da DPO
Nan ya tarar ai wadda ake case akan ta ne itace yarinyar tasa ashe
Ai Alhaji yarka kashe su akaso yi ita da wani warwas muka samesu wani ya kiramu to yana hannu dan sai munyi shari’a dashi
Ya kwashe komai ya sanarwa da alhaji har haukan da Hanan ta samu tashin hankali mara misali Alhaji ya shige shi
Nan da nan yasa a shirya musu Visa zuwa Egypt suka fito ya nufi dakin da sajida take duk ta fita hayyacin ta
Alhaji ne yace shima Namijin besan shiba besan waye shiba dan haka shima a bada tasa sanarwar ko a samu yan uwansa
Suna wannan maganar da doctor din da DPO nurse ta taho da gudu tace ya farka doctor
Da hanzari sukai kansa amma magana ma ya kasa likitoci suka fara bashi temakon gaggawa aka karai masa allurori bacci me nauyi ya kara daukansa
An dauki hotunan sa an sa a tv da gidan radio
Hajiya ta fara watstsakewa hankalin ta ya fara kwanciya saboda ansamu Visa gobe zasu wuce garin nan ba kyau komai na kudi ne
Shi ko bawan Allah daga temako yana Police station yana jibguwa dan ba karamin izaya ake masa ba
Bashi da kowa beda gata gashi sun matsa masa akan lallai sai ya amsa lefin dabe aikata ba
Shi kuma ya rantse akan baze amsa lefin dabe aikata ba Allah shine shedar sa shize fitar dashi a halin daya ke ciki
Ranar Monday zasu kai ahi kotu gaba daya ya fita daga hayyacinsa
   *************

Muje ciki Zubaida wannan ce kawar taki kenan
Murmushi tayi eh itace hajiya hajara ba muje tom suka wuce zuwa ciki
Hajiya ta kawo musu ruwa da lemo da abinci me rai da lafiya wanda Hajara bata taba cin irinsa ba a rayuwarta abinci ne na yan labenon
Hajiya ta kalli Zubaida wannan kawar taki tayi sosai da sosai gaskiya zata samu duniya zata samu kudi fiye da tunanin ki
Matsalar talauci da yai mata yawa jibi kayan jikinta duk sun sha faci saboda haka yanzu zata sanja kayan jikinta
Saboda a yanzu haka zan kira Alhaji Warbeshi yazo ya fara ganinta dan zamu samu kudi da wannan yarinyar
Cikin tsoro Hajara ta kallesu dan sam ta gaza fuskantar me suke nufi da maganganun su diban girki kawai take tana mamakin haduwa da tsaruwar Hajiya da gidanta
Niko Hajiya ke kadai ce a gidan nan cewar Hajara
Ta saki murmushi eh ni kadai ce a gidan nan kuma idan kika bada hadin kai abunda zaki mallaka sai yafi haka dan kin hadu ke kyakykyawa ce
Hajara kina da kyau me daukar hankali talauci da rashin gyara yasa kike neman lalacewa amma a yau zaki fuskanci wacece ke
Zan sanjaki zaki gane ainihin kyanki ayau yanzu bada dadewa ba zan hadaki da Alhaji Warbeshi nasan zaki godemun
Zaro ido tai zubaida karuwanci da aurena tun ina budurwa banba sai yanzu bazan iya ba ta mike tsaye

*Kuyi manage da wannan bana samun time ne wlh nayi busy amma insha Allah dana gama abunda nake zaku dinga jina akan kari insha Allah*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________
*DEDICATED TO:HASSAN ATK&HUSSAN 80K*

_~*MY FANS ƊINA BA ABUNDA ZANCE DAKU SAI GODIYA, ALLAH YABAR ZUMUNCI DA KAUNA, NAGODE DA YADDA KUKE ƘAUNATA. BA RUWANKU DA NOVEL ƊINA, KO NAI POSTING KO BANBA MUNA TARE, GASKIYA NAJI DAƊIN YADDA KUKE MUN COMMENT IDAN NAI POSTING. INSHA ALLAH KODAN YADDA KUKE FARANTAN, DANA GAMA WANNAN ZAN MUKU (DAN ISKAN NAMIJI BOOK 2).NAGODE SOSAI MY FANS WANNAN PAGE DIN NAKU NE, KUJI DAƊIN KU KU HUTA, KUYI YADDA KUKESO DASHI, (FEEDYN BASH) TAKUCE A KODA YAUSHE.👯🏻👯🏻👯🏻*~_
+
              *30-35*
Wasu daga cikin manyan yaransa ya kira, ransa a matuƙar ɓace ganin irin cin amanar da Faruk yai masa.
“Hello Virus kana ina?

“Oga gani a sabon gari na zaga akwai wasu yara da zan ɗebo,munyi dasu zasiyi wannan aikin.

“Duk abunda kuke ku juyo kuzo nan Lamido cresent,akwai matsala zan turo ma location din gidan,ka nemo manyan terros da virus irinka akama kowa da komai na gidan.
Kit ya kashe wayar ransa a matuƙar ɓace ya kunna motar suka bar wajen,tsula gudu kawai yake a titi, ya karya kwana zuwa Taheer guess palace.
Suna shiga aka bashi card dinsa, dama shi parmanent daki ne dashi, ya bude sai sannan ya kamo yarinyar ya rungumeta.
Suna shiga ya buɗe fridge ya dakko kwalbar giya, ya sha yai tatul sannan ya kunna sigari ya dinga daddakawa cikinsa hayaki.
Sai sannan ya samu nutsuwa ya fara magana “kankana tabbas bana san yaudara,cin amana na riki Faruk tamkar ciki daya muka fito,tabbas zan nuna masa cewa ba’aiwa Boss karya a kwana lafiya,ko suwaye wayannan yaran yabar ganin su har abada.
Zasu zama ɗaya daga cikin waƴanda zaki wa training na karuwanci,akwai matan daza’a kawo,su kuma su za’aiwa operation asa musu cocein a cikin su,idan kikai aiki me kyau hhhhhhhhh! ya sheke da dariya.
Tai wata shu’umar dariya, hhhhhhhh!Boss karka manta kankana ka ɗakko uwar ruwa,baka da matsala da ni ta wannan fannin,bari ma in fara gwada ma kagani.
Ta faɗa jikinsa suka afka duniyarsu ta masha’a, wanda ba komai ciki sai lalacewa da tsantar taɓewa.(Allah ka shiryi wayanda suka ɓata)
Faruk ya shiga gida ransa a bace,”ke Alaife me kuke anan wajen?”
A firgice suka juyo, Gobinya ta rushe da kuka saboda tsoro.
Ya ƙaraso fuska a hade”ba kuka nace kimun ba,duk fadin gidan nan cikar sa da batsewarsa amma sai kunzo nan zakuyi wasa?haba Alaife kin fa fada girma be kamata kina boyewa Gobinya ba kinsan yarinyace.
“Kayi hakuri yayan mu,mun dade bamu samu sakewa haka ba,Gobinya nasan yin wasa amma ba dama,saboda bamu da wannan lokacin,tausayinta yasa na biye mata,amma naima alƙawari bazamu kara ba yayana,zamu din gayi a ciki.
Gaba ɗaya jiyai tausayin yaran da kunyarsu ta rufe shi,be kamata yai musu tsawa haka ba,yarane su da suke bukatar kulawa.
Kiyi haƙuri Alaife, banyi haka dan ma bata muku ba nayi ne dan kareku daga kowace barazana.
Na fuskance ka yayana muje na tayaka ɗebo kayan mukai ciki.
    *************

Antyn yara kinga Alhaji shiru ba shi ba bayaninsa.
“Haba Hajiya kin cika ƙwalafici wallahi,to yanzu banda abinki me Alhaji ze miki kuma a tsakar ranar nan,kinsan da saninki kin aike shi aje a hora waccen koɗaɗɗiyar yarinyar.
Af nafa manta tawan, kinsan meyasa nai miki maganar?saboda inaso mudan huta dake mu kyankyashe rayuwar mu.
Mtsww!wallahi ke matsalace dake sam baki da hakuri,bakya barin mutum ya huta, nagaya miki Lawan muke jira ko kin manta.”
Bata gama rufe bakin taba sai ga Lawan ya shigo kamar an hankado shi.
“Hajjaju makkatu uwargida rangida,Antyn yara ki dade ki lasting amarya bakya lefi,ko kin kashe dan masu gida.”

“Dakata Lawan sarkin kinibibo, wallahi sai dai bata kashe ba,ai har uwar amarya ta shiga uku.”
“Kedai wallahi Hajiya kin cika kishin masifa,ga rashin hakuri,kaga Lawan dan iskan duniya ina sakon?
Hhhhhhhh! Antyn dan iskan namiji nake,ga sako inji dumus.
Y mika musu wata leda,ga gashin kanta tumus,ga kuma na gaban nata shima daban,gefe ga wata ƴar roba da jinin al’adarta a ciki.
Lokaci guda suka bushe da dariya, Hajiya ta fara magana”Haleema kin kade har ganyenki,duk yadda nai kokarin Alhaji ya sake ki ya faskara,lokaci yayi da zaki bar wannan gidan bari na har’aba.”
Hhhhhhhh!”Hajiya kenan,ba kyason kishiya ko kadan,nasanki tun sanda aka auroki,amma abunda ke ban mamaki ya akai kuka hade da Antyn yara.”
“Kai Lawan jin kwakwaf,to  bari kaji nagayama,Hajiya bata da yadda zatai danine, kamar yadda ba yadda zan da ita,saboda haka muna nan mu biyu zama daram, duk wadda Alhaji ya aura haka zami mata, yadda mukaiwa waccen mahaukaciyar da mayyar nan.”
“Kaga ungo jeka zan nemeka,kasan gobe zamu wuce india, sai munyi wata zamu dawo, muna dawowa zan nemeka kaji dan hannuna.” ta kashe masa ido.
“Shike nan Hajiyata.”Ya fice zuciyara fal zargin akwai wata ɓoyayyiyar alaƙa tsakanin Hajiya da Antyn yara.Tabbas idan zargina ya zama gaskiya wallahi duk sai na musu akuyanci.
Yana futa Hajiya tai kan Antyn yara, har ta shawo kanta suka fada duniyar su ta masha’a.
Gudu suke a mota yana kwararar hawaye,”dan Allah kai sauri karta mutu,kiyi hakuri matata tun ta ladan noma, wallahi inasanki namanta dake ne lokaci me tsawo sannu Sadiya.”
A haka suka karasa asibitin cikin gidan, suna zuwa likitoci suka amshe ta, nan da nan akai emergency da ita.
Doctor Hannat abun ya daga mata hankali, ganin yadda akai mata, ga dukkan alamu kasheta akai niyya,domin hodar iblis aka watsa mata wadda tafi karfin ta,gata dama ba hankali,duk yadda suka so temaka mata matan Alhaji sunki.
A karshe suka dena ganinta, dan da suna zuwa a sace,duk da barazanar da suka samu daga wajen matan na Alhaji,amma suna kaunar matar, Allah yai mata fara’a, ga kyauta, ga sanin darajar dan adam.
Sunyi kokarinsu sun shawo kan matsalar,amma tai mamakin ganinta a wannan halin, jage-jage da jinin al-ada an yayyanke ta a gabanta, an mata kwal kwal, amma ba hurumunta bane ta basar.
“Yasmeen nutsu! kinsan da saninki cewa suna asibitin cikin gidan nan,dole can zasu a wannan halin,bamu da zabi sai bin bayansu.”
Haka suka daba da kafa suka je asibitin,wanda yai dai-dai da fitowar doctor Hannat daga emergency,”Alhaji inasan ganinka a office” itama bin bayansa tai dan bema san ta shigo ba, itama bata kulashi ba dan tafi tsanarsa akan kowa.

_*TO FANS KUYI MUN HAKURI FA DAMA NACE BA KULLUM ZAKU DINGA JINA BA SABODA WALLAHI INADA BUSY DA YAWA NAGODE MASOYANA MASU HAKURIN BIBIYATA NICE TAKU A KULLUM A KODA YAUSHE*_
              *FEEDYN BASH*

[1/29, 9:48 PM] 💃💃 Feedyn Bash Cele👯🏻👯🏻: ☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

*DEDICATED TO: ALL HAKURI HASKENE FANS*
               *35-40*

Angama komai na shirin fita da Hanan waje, da sassafe suka daga zuwa kasar Germany dan nema mata lafiya, Mahifinta jakadan ƙasar ne dama, shi kuma wanchan din ko oho, ba kara ba komai suka barshi cikin halin jinyar mutuwa da rayuwa.
_(Wannan rashin imani yayi yawa, kunada kudin da zaku fitar da diyarku kasar waje, amma wanda aka gansu tare wanda ya fita jikkata, bazaku iya temakawa a gano meke damunsa ba, tunda ko farfadowa beba tayaya muke tunanin zamu ga ci gaba a rayuwar mu, zalunci yai yawa a duniya Allah kasa mudace.)_
+
Suna dira a ƙasar motar asibiti ce ta ɗaukesu zuwa asibitin, suna zuwa a kai wani daki da ita wasu na’urori aka fara jona mata, dukkan kanta har gangar jikin ta.
Sun mata checking din kwakwalwar ta sosai, inda karshe suka gano cewa kwakwalwar ta ta juye ne, saboda tsananin tashin hankali data shiga.
Doctor ɗin ya fito yazo wajensu a wani katon daki kamar ba’a asibiti ba, yai nocking suka bude sannan ya shiga, ya zauna ya farai musu bayani cikin harshen nasara.
“Abunda yake damun yarinyar ku shine tana da ƙaramar kwakwalwa, akwai abunda ta gani ya ruɗa ta ya ɗaga hankalinta, wannan shi ya janyo kwakwalwarta ta motsu, amma zami iya kacin kokarin mu ta dawo hayyacin ta.”
Hankalin su ya kwanta dukkan su ganin an samo karshen matsalar, sai dai fatan samun lafiya daga diyar tasu, sunji daɗi sunyi hamdala ga Allah, sukai wa doctor godiya saboda nan ne masaukin su, ya fice suka  ci gaba da jimamin abunda ya firgita Hanan.
Alhaji ne ya gyara zama “tabbas hajiya nifa ina zargin cewa tabbas yarinyar nan ganin za’a hallaka daya yaron nan yasa ta samu motsuwar kwakwalwa, wai shin an dakko motarma kuwa?
A’a Alhaji “amma ni shi kansa yaron da kake magana a kansa ban yarda da shi ba, so nake ta warke tai bayani tabbas ni ban yarda firgita bace, kawai nadai bi kune a haka.”
“Koma dai menene ya kusan zuwa ƙarshe tunda gamu muna hanyar nema mata magani, komai zezo karshe da ikon Allah koma waye sai mun dau mummunan mataki akansa”.

       ***************

Wata nurse ce ta taho a guje tana kiran “Doctor! Doctor! Doctor! ta shiga office dinsa tana haki.Patient din nan ya farka”.
Wanne daga ciki? “ki nutsu kimun bayani mana kamar ba nurse ba, tearter zamu shiga a halin yanzu, wanne daga ciki ne ya farka masu accident din nan ko masu gobarar nan?
“A’a Doctor waƴanda ake case din wannan mahaukaciyar,wadda suka wuce Germany dazu da safe, to shine ya farka yana ta salati”.
Ok,”kai alhamdulillah amma naji daɗi,maza muje kafin mu tafi tearter  sai na gan shi, musamu ko zeyi magana sai mu kirawo Police din, ko zasu samu wani impormation din daga gareshi”.
STORY CONTINUES BELOW

Suna zuwa suka tarar da shi yana ta hawaye,yana kwance kamar gunki.
Doctor ya karasa ya taɓa shi yaga idonsa biyu,ya daga hannunsa yaga ya koma yaraf.
Hankalinsa ya tashi, nan da nan yace wa nurse su turo shi zuwa tearter, saboda akwai manyan Doctors da zasi tearter su duba shi, saboda ba wanda yazo daga bangarensa yana masifar tausayinsa.
Su Alhaji sun ɗauke ƴarsu sun tafi wata ƙasar dan duba lafiyarta, shi kuma ko oho sun bar shi ko kudin magani ba wanda ya biya, kawai bashi suke loda masa idan ƴan’uwansa sunzo ko ya farka ya biya.
Suka tura shi zuwa tearter, nan da nan likitoci suka rufu akansa suka fara duba shi, sunyo iya binkicen au a kansa,amma a ƙarshe suka gano Spinal Code dinsa ya tabu.
   ****************
A yau ta kama monday, yau aka gurfanar da wannan bawan Allahn wanda ya kira Police, suka kama shi a zuwan shi yai yunkurin kashe su, be kara magana ba a station tun daga ranar, an kai shi kotu dai yau gaban alkali.
Bayan me karanta ƙara ya karanta ƙara, aka farai masa tambayoyi,”da fari zamu so jin cikakken sunanka?
A hankali ya dago idonsa da sukai jajur, ya kalli alkalin”sunana bawan Allah”
“Bawan Allah ai ba suna bane, cikaken sunanka muke san sani, da kuma dalilinka na yunkurin hallaka wasu mutane, daka ga hakan be samu ba shine ka yanke hukuncin haukata Hanan, ƴa ga babban attariji Alhaji Jamilu, wanda jakadan Nigeria ne da kasar Germany. “

“Kamar yadda na gayama ranka ya dade sunana Bawan Allah, haka na taso naji ana kirana, banda kowa a halin yanzu banda komai, banda wanda ze tsaya mun.
Amma nasan cewa akwai Allah, nayi Haƙuri da jarabawar da yai mun a rayuwata dan nasan cewa hakuri haskene,nasan cewa Allah shi kadai ne ze warware mun matsalata”.
Zuciyoyin mutane da yawa ta raunana, musamman yadda yake magana,cike da kyautayi da tsoron Allah ƙarara a idanunsa.
Ganin haka yaja hankalin mutanen Kotu da shi kansa Alkalin, yasa lawyer din da suka ɗauka ya mike yafara magana.
“Yame girma me shari’a, karkuyi la’akari da maganar wannan mutumin, yana san wasa da hankalin kotu ne,ganin asirin sa ya tonu yake so yayi wasa da hankalin kotu,wajen nuna shi me gaskiya ne.

Inaso wannan kotu me adalci data tsananta binkice akan wannan mutumin, saboda ya bayyana waye shugabansu dan har yanzu yaki yin magana, nagode yame girma me shari’a”.

Alkali yace “to kaji Bawan Allah mezaka ce game da wannan maganganun, ko kanada hujjar da zaka kare kanka a kan zargin da akema”.
“Banda ita Allah ne sheda ta, nasan yana jina yana kallona dan haka nabar masa komai, nayi hakuri bisa jarabawar data sameni, ina rokon ya bani ikon cin wannan jarabawar.
Mutane sun shiga tausayi da halin dimuwa na wannan shari’a, nan aka fara hatsaniya aka fara kace nace masu kuka nayi masu alhini nayi,masu cewa makirci ne nayi, amma a kaso uku kaso biyu da rabi tausayinsa yafi ratsa ransu.
Alkali ne ya buga guduma kotun tai tsit kamar ruwa yacinye su, “abisa rashin gamsassun hujjoji daga bangarori guda biyu, kotu ta dage sauraron wannan ƙarar zuwa wata biyu masu zuwa,wanda ko wanne ɓangare muke bukatar ƙwararan hujjoji na kare kai daga gare shi,kai kuma Bawan Allah ka nemi Lawyer ɗin daze tsayama”.
Aka fice dashi zuwa cell ɗin kotu, kafin a gama sauraron ragowar karar, a   tasa keyarsu zuwa gidan ɗan kande.
    *************

STORY CONTINUES BELOW

Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un, “Zubaida kinsan waye wannan? Mijina ne wallahi, shine a gadon asibiti, kingan shi ana neman ƴan uwansa, beda kowa a garin nan sai ni, iyayensa sun rasu” ta fashe da kuka.
Mtswww!”wallahi na dauka wani abunne har gabana ya fadi, dan wannan yana asibiti sai me to, dakike wannan zancen kina zuwa asibiti batun kudi ne, shin ke kina dasu koko shi yana da shi?
    “Kinga Zubaida bita a hankali, matso kiji ki share hawayen ki, a daren yau  zaki samu manyan kudin da baki taɓa rikewa ba a rayuwarki,fatana kiyi biyayya ga Alhaji warbeshi”.
Haduwa sukai suka dinga yi mata munanan huɗubobi, shedan ya kawata mata lamarin ta yarda ta amince zata yi, kodan ta fita daga kuncin talaucin data ke ciki, tunda ance mata na rana daya ne.
Tana zaune aka kirawo wata hajiya ta fara gyarata loko da sako har wanka ita tai mata, kaya ne na alfarma masu bayyana ainihin surar mutum aka bata tasaka, aka tsantsara mata kwalliya abunka game kyau yarda kasan ƴar tsana haka ta koma, ga shape ga ƙira ga kyau banda zuzuta kyan da tai ba abunda suke.
Banda hassada ba komai a zuciyar Zubaida, ganin yadda Hajara tai kyau na mamaki ta zama kamar fure, gashi Hajiya sai waya take da manyan Alhazawa tana gaya musu tai musu babban kamu kaya ne masu kyau.
Ƙarfe goma na dare a lokacin ne taga wata tazo itama ga dukkan alamu matar aurece, tayi kyau itama na mamaki dan dole kai sha’awar ta, suka taba hira tana ta jan  Hajara da hira har ta fara sakewa.
Sha ɗaya dai dai sai ga Hajiya “yauwa ƴan albarka ku taho Alhaji warbeshi yazo, ke Lubna ki nunawa Hajara harkar nan kinga ita sabuwa ce a harkar, keko an daɗe ana harkalla” suka sheƙe da dariya suka fice.
Wata mahaukaciyar mota ta hango a harabar gidan kamar jirgi, suna dumfarar ta wani masifaffen ƙamshi ne ya fara ratsa ta, suman tsate tayi ganin suna zuwa kofofin motar sun bude, abunda ba’a saba gani ba, Hajara saura kadan ta zura da gudu.

*_TO FANS WALLAHI BAKWA MUN COMMENT YADDA YA KAMATA SHI YASA NIMA SAI SANDA NASO NAGA BANDA ABUNYI ZAN TYPING YAWAN COMMENT YAWAN TYPING IDAN KUN GYARA NA GYARA IDAN NAGA AKASIN HAKA NA DIRE ALKALAMINA🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀_*

          *FEEDYN BASH*
[2/2, 8:35 PM] 💃💃 Feedyn Bash Cele👯🏻👯🏻: ☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

*DEDICATED TO:ALL HAKURI HASKENE REALLY FANS*

               *40-45*

Hanan jiki ya rikice sauki sai a wajen Allah, dan me makon sauki abun nata sai gaba yake yi.
Hankalin Hajiya da Alhaji ya gama tashi ko baccin kirki basayi, musamman Hajiya duk ta fita hayyacin ta.
Ko abinci bata ci, duk yadda Alhaji yake lallabata amma abun ya gagara, su kansu sunyi tunanin matsalar karama ce sai suka ga abun ya zama babba,sai da suka kira babban likitansu.
STORY CONTINUES BELOW

A yau ne suke sa ran zuwan baban likitan asibitin daga kasar jamus, shi yasa Alhaji yake ta lallaba Hajiya.
Cikin ikon Allah likita yazo a yau ya fara duba Hanan, ya gano cewa magungunan sun mata karfi shiyasa suke kara tuburata.
Duk da kwarewa irin ta kasar waje amma Allah ya nuna ikonsa, sai da suma suka kuskure, karshe tafiyar tasu da suka yi ta da niyyar sati biyu gasu sunyi wata guda.
(Duk inda kake a duniya Allah shine me dora cuta kuma me maganinta, sunbar kasar su saboda suna ganin suna zuwa kasar wajen zata
samu lafiya, saboda suna ganin su masu kudi ne, amma hakan bata samu ba Allah ya nuna ikonsa, Allah kasa mudace.)
Sati biyu da fara karbar maganin ta alhamdulillah jikin nata ya fara dama dama, dan yanzu ta dena dariyar sam sai dai ba umm ba umm umm sai dai kallo, hankalinsu ya fara kwanciya yanzu.

        **************

Suka shiga da kayan cikin farin ciki, Yusuf ko ba’a cewa komai saboda ganin irin siyayyar da akai musu shi da Gobinya, tunda sune yara kanana.
Bayan ya ajiye musu duk abunda zasu bukata yai sallama da Adda, ya bar musu duk wani abu da zasu bukata, ya roke ta akan dan Allah karta bari koda wasa yaran su kara fita harabar gidan, akwai komai ciki na wasa.
Idan ma basuyi musu ba suje bayan gidan ta ciki suyi wasan su, tace insha Allah zata kiyaye, yai musu sallama ya ajiye mata waya koda matsala ta taso ta kira shi.
Ya kira Sheri waje, ta bishi bakin motarsa cikin takunta na nutsuwa me daukar hankali, ta karasa kusa da shi.” gani yayana”
Gaba daya jikinsa sai da yai shock, ganin yadda gaba daya ta gama tafiya da imaninsa, sai da ya nemo nutsuwa ya sawa ransa, sannan ya fara magana.
“Sherri dan Allah kinga kece babba, ki kulamin da kanki da kannenki, inaso ki rikeni tamkar yayanki, kisani a ranki kamar yadda nasaki, idan kunada wata damuwa ki sanar dani.
Ga wannan” ya mika mata wata hadaddiyar waya da wata jaka, “karki bude ki bari sai kinje ciki” dakyar ta amsa sai da ya nuna ransa ya baci, sannan ta karba tai godiya.
Haka suka wuni cikin farinciki, ta ajiye wayar da jakar cikin wardrobe, ba abunda ta taba suka ci gaba da hirarsu.
Har lokacin bacci yayi sallah kadai ke tada su suna ta kallo abunsu, a daki daya yaran suka kwanta gaba dayansu, Yusuf da Gobinya da Sherri.
Alaife ce kawai tace ita daban zata kwanta, sai sai Adda itama tana dakin cikin yaranta suna hirarsu gwanin sha’awa, ba yadda basi ba amma Alaife tace ita kadai zata kwana tana tuna baya ne.
Alaife ce ta tafi chan karshe ta nemi wani daki ta kwanta abunta.
Karfe daya na dare a dai-dai lokacin su Boss sukai wa gidan tsinke, suka daure me gadi suka tara masa gajiya suka harbe shi a kafa.
Suka shiga gidan suna zuwa suka fara binkice gidan har suka samu dakin da suke, Adda ta shiga bandaki kama ruwa.
Jin motsi Adda ta fito su kuma sun fito da yaran dukansu, harda Yusuf karamin yaro dabesan komai ba sai Adda da yan uwansa, ga tsaleliyar budurwa sherri da Gobinya wadda batama san meye duniyar ba.
Dukansu har Sherrie ba wata wadda ta san me take a cikinsu, kawai kyau ne zallarsa irin na buzaye da baragen girma, dan nono sun fara fitowa Sherri amma ba wasu manya ba.
Nan da nan Adda tai kukan kura tai kansu tana ihu, tana jan Yusuf suna ja, baras kake ji hannunsa ya karye.
Kuka kawai suke da addu’o’i, suna neman tsarin Allah.

Duk wannan abun da ake alaife na chan taji ac tana baccin ta tayi dai-dai akan gado.
Ganin Adda zata bata musu lokaci gashi sunci nasarar aikinsu, sun duba gidan kaf ba wanda yai saura, dakin alaife ne kawai Allah be basu ikon budewa ba, saboda watsuwa sukai suna duba gidan,har wani ya murda Boss ya kira shi  yace angansu.
Ji kake dau sun sakarwa Adda harbi, ta baje a wajen wannan harbin shiya farkar da Alaife, ta kwalla wata razananniyar kara.
Wadda tai dai-dai da lokacin da Sherri tai karar itama ta sume a wajen, shi yasa basuji karar alaife ba, wani daga ciki yaso ji amma Boss ya daka musu tsawa, sungume ta suka fice daga gidan.
Lokacin Alaife ta fito daga dakin jikin tana rawa, ganin an fita da Yan uwanta ta kara labewa ta toshe bakinta, tana kallo suka wuce dasu.
Da gudu tayo kan Adda da gawarta take yashe a kasa, ta kwalla kara ta zube a wajen itama a sume.

    **************
Suna zuwa doctor tace “Alhaji wannan wane rashin kulawa ne haka, harda aka bar Hajiya taiwa kanta wannan raunin haka.
Koma dai ince an mata, sam bata samun kulawa ko kadan ba, hakan ya kara tuburata, saboda haka zamu rike ta a wajen mu zamu dinga bata kulawa ta musamman, zamu ware mata babban sashi anan zata zauna.”
“Zan zauna da ita indinga kula da ita” ta fashe da kuka cewar Yasmeen da basu san ta shigo ba.
“Baze yiwu ba Yasmeen, kema kinada lefi meyasa bakya kula da ita, tunda kina tare da ita sai yanzu da abu ya kwabe zaki zo kina kuka” cewar Alhaji kamar ze rufeta da duka.
“Daddy kafi kowa sanin cewa banda lokacin zuwa wajen mamana, Hajiya da antyn yara basa barina na huta.”
“Ya isa Yasmeen! kije gida kawai kinji kya dinga zuwa ganinta, ki tai mata addu’a kawai shine abunda take bukata.
Alhaji kuje na sallame ku Allah ya bata lafiya, shiyasa tun farko mukaso kubarta a wajen mu kuka ki.”
Jikinsa a sanyaye ya kamo hannun Yasmeen tana kuka tana komai suka fito, yace da Inna su koma kawai, suka shiga motar kawai rungume Yasmeen yai yana kuka.
Itama kuka take na tausayin babanta, da mamanta, da ita kanta, suka je gidan ya riko hannunta ya nufi sashin sa da ita, ya bata abinci taci ta koshi.
Sun gama badalarsu da kokensu saboda yadda suke gamsar da junansu, suka fito rungume da juna sun kissing juna suna dariya abunsu.
_(Ya ilahi way wayannan kishiyoyi ne, matan mutum daya duniya ina zaki damu, duk saboda neman duniya da san abun duniya, sun manta da auren su, mijinsu ya zama hoto junansu suke aure kawai, Allah kasa mudace. )_
“Baby bara naje naga Alhaji nasan ya dawo, maganar bizar mu kinsan jibi ne tafiyar saboda zamu huta sosai, dan a wannan karon zan iya bada jinin mutum bana shanu bama.”
Hhhhhhh! “Hajiya kenan, kedai baki da tsoro ko kadan, kuma nasan jinin mahaukaciya zaki bayar, gashi ba’a tsafi da jinin mahaukata.”
“Au namanta Antyn yara sai na bada na waccen mayyar yar tata.” hhhhhhh! suka sheke da dariya ta wuce.
Hajiya ce ta shigo dakin, wani ashar ta saka “kan bura uban nan. Alhaji! nizaka munafinta yau, wallahi sai ka gane kuskuren, ka ke kuma yau wallahi sai na kusa kashe ki.”
Ta fara dukanta kamar ta samu jaka, jikin Daddy rawa kawai yake bashi da ikon magana, masifar tsoronta yake kamar mutuwarsa, rabonsa da kula Yasmeen yafi shekara biyu sai yau, bare matarsa daya manta da ita,ashe tsautsayi ya kai shi, dan yasan yau ta Allah,in ta farai masa bala’i sai Allah, jikinsa kawai rawa yake saboda tsoro.
Nan ta wurgata gefe,wayar Daddy ta dauka ta kira waya, “maza ku turon soja daya mara imani zemun wani aiki yanzun nan” ta katse kiran.
Minti goma be cika taji ringing din wayar, “yauwa gani nan” ta fara jan Yasmeen da take ta sheka amai, ko ajikinta kamar kayan wanki har zuwa bakin parlour.
Ta wurga masa ita ta sauka saman kirjinsa, “gata nan ka kaita guardroom kai mata dukan mutuwa” ta maida kofa ta rufe.
Gaba daya ransa ya gama baci, ya gama fita hayyacinsa saboda bacin rai,jijiyoyin jikinsa duk sun tashi, tsam ya rungumeta a kirjinsa ya dauketa chak yasa ta a mota ya fice.

*To fans shin waye wannan sojan? meke faruwa ne? kudai ku biyoni a next page, comment dinku shi ke kara mana kwarin gwiywar yi muku typing.*

      *Feedyn bash*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________
*DEDICATED TO:AMIRA NIGER, NAGODE SIS YADDA KIKE MUN COMMENT ALLAH YABAD ƘAUNA.*
    
                  *45-50*

Hanan taji sauƙi sosai yanzu tana karɓar abinci taci da kanta, amma har yanzu bata magana.
Doctor yace za tai maganar ma sai a hankali, amma kotai magana kar wanda ya tuna mata abunda ya faru.
+
Saboda ita abun ya wuce a wajen ta, idan suka tuna mata zata iya birkicewa, amma tunaninta a yanzu normal yake.
Sunji daɗi hankalinsu ya kwanta, musamman Momy dan ba ƙaramin ƙaunar Hanan take ba, ita kaɗai Allah ya bata a duniya, shi ya sa suke mugun ji da ita.
Sunyi waya hankalinsu ya kwanta, game da yadda zaman kotu ya kasance sunyi farin ciki.

     *********************
Jin lalurar data ke damun sa ta ɗimauta shi sosai, a wajen ya ƙara sumewa ya shiga wanj mawuyacin hali, hankalin likitocin ya gama tashi.
Saboda har yanzu basu samu impormation akan sa ba da danginsa, wannan shine abunda yake ɗagawa doctor hankali.
Saboda anyi shela an sanar a radio ansanar a tv amma shiru, ba ƴan uwansa ba alamunsu, ga dukkan alamu mutumin ƙauyene, tom gashi yaji abunda ya same shi ya shi ga wani hali basu samu bayani daga gare shi ba.
Gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, nan da nan manyan Doctor suka duƙufa akansa.
Abun yaci tura dole aka kai sho ICU, bashi da kowa bame kula dashi, abunda ya ƙara ɗaga hankalin Nurse Fatima kenan da Doctor.
Nurse Fatima ce ta samu Doctor idonta fal ƙwalla, saboda ganin halin da bawan Allahn yake ciki.
“Doctor ni na yarda zan tsayawa wannan bawan Allahn, idan yaso kome ya kama zan cire a salary ɗina ina biya a hankali, kariga kasan gwamnati bata tallafawa kowa a wannan lokacin.
Komai sai da kuɗi, ba wani abu da yake kyauta a asibiti, wanda ma aka kawo kyautar ba’a bari a bayar.” Ta  faɗa tana matse hawaye cike da tausayawa.
Jikin Doctor yai sanyi, “tabbas maganar ki haka take, kuma nima akwai tausayin wannan bawan Allahn fal raina, saboda haka nima na ɗauki nauyin sa, zan masa komai saboda Allah kibar naki tunda kema kina buƙatar temakon.”
Farin ciki ya gama cika ta, Alhamdulillah! naji daɗi sosai Doctor, Allah ya ƙara dafa ma saboda temakon da kake, Allah shize duba ka, mungode sosai sosai yallaɓai.
Ita ko Nurse Fateema mugun son wannan mara lafiyar ne ya kamata, duk da bata san daga ina ya fito ba,amma shi ya sa kullum baya yarda tai nesa da shi.

STORY CONTINUES BELOW

      ****************

An kai su Bawan Allah prison ta kurmawa, cikin manya-manyan masu lefi na kisan kai, da kuma ƴan fashi, suna zuwa suka wurga shi ɗakin duk duhu.
Wani bahagon duka yaji an sakar masa, “kai hattara kasan inda ka shigo, ni zaka taka ?hmm! to wallahi yau na lahira sai ya fika jin daɗi a gidan nan, kai gaka sabon ɗan iska ko? to wallaho sai na sanja ma kamanni, kai laya Me laya.”

“Na’am Oga” “ku lallasa mun shi yasan ya shigo fadata, yasan cewa cewa prison ba gidan rago bace, kuyi masa dukan mutuwa.”
Yuuu suka yo kansa kamar sun samu nama, suka din ga jibgar sa sai da suka tara masa gajiya, sannan yace su bar shi haka sannh da zuwa sukai masa, na ya shigo gidansu, saboda sun san yazo kenan baze fita ba.

Ko motsi baya yi haka yake a kwance kamar gawa, Oga ne yace “ku watsa shi kusa da wancen dattijon, ga ɗan uwa nan ya samu.”
Hhhhhhhhhh! suka bushe da dariya, “angama Oga” suka kwashe shi kamar tsumma suka watsa shi kusa da wani ya musashshen dattijo.
     ****************
Suna shiga cikin motar suman zaune tayi, saboda muguwar ac ɗin data ke dukanta ta ko ina, ƙafa da hannu har tsakar kanta.
Suna shiga aka ja motar, ita a tunanin ta Alhaji Warbeshi ne, bata san cewa driver ya aiko ba.
Direct wani haɗaɗɗen wajen cin abinci suka je.
Sai da suka cika tumbinsu, sannan ne Nancy tace “magaji Alhajin yana ina ne?” “yace mu wuce yana garin Kaduna a yanzu haka, Kaduna zamu wuce direct.”
Hajara fitsari ne kawai batai ba saboda tsoro, ta zaro ido yanzu ke baki ji me yake faɗa bane? Kaduna fa yace Kaduna dai wadda nasani me nisa?”
Hhhhhhhhh! “haba Hajara karki ban kunya mana, meye a Kadunan, Magaji ya iya tuƙi awa biyu yai yawa mun isa, kuma Alhaji beda matsala gobe zamu juyo.”
“Gaskiya nifa Nancy sai dai mu juya, kuna kallo mijina na gadon asibiti amma kuce naje Kaduna, ni tunda nake ban taɓa barin Kano ba.”
Mtsww! haba Hajara karki bada mata mana, mace har mace amma sam ba wayewa a tattare da ke, shi mijin naki kinsan wainar daya ke toyawa a waje? ko ko ba kuɗi zaki asibitin?
Wallahi ki farka daga nannauyan baccin da kike, dan wallahi in dai kika riƙe Hajiya kwanan nan zaki jiki a sawun mata masu kuɗi na garin nan, kwanan nan zaki fara keta hazo.”
“Dan girman Allah Nancy da gaske kike?” hhhhhh! “wallahi nima matar aure ce, amma mijina beda shi ɓigewa nake da business ina sheƙa aya ta, ke dai ki bari kawai, kwanan nan zaki fara zuwa Lagos, Abuja, Bauchi ke duk wani gari da kika sani.
Saboda da manyan mutane muke harka, musamman masu mulki a hannu, da manyan masu kuɗi, saboda haka ki kwantar da hankalin ki.”
Famfon ya gama hawa jikin ta har hango ta take da manyan wayoyi, gata a ƙasar waje, sai ta bushe da dariya “gaskiya wannan sabga tayi, dole nima na laƙe da neman kuɗi mu wataya.”
Hhhhhhhh! suka sheƙe da dariya suka tafa, suka ci gaba da hirar su.
Basi aune ba suka ji mota ta tsaya, “A’a Magaji lafiya ka tsaya?”
“Hajiya Nancy ai har mun iso, Alhajin na ciki yace ku shiga, yanzu za’a zo a shiga daku.”
Suna fita suka ga wani yazo tafiya dasu, “ku biyoni” haka kawai yace
Wani hamshakin gidane wanda tsayawa fasalta shi sai na cika page ɗin ban gama ba, Hajara ta zama ƴar ƙauye dama ita ce tunda ba’a saba gani ba babu a House.
Har tsayawa take, ganin zata ɓata musu lokaci Nancy ta figi hannunta suka wuce, suka isa parlour ɗin da yake zaune, tsayawa bayyana tsarin parlour ɗin da ƙayatuwar sa ɓata baki ne.
“Lale marhabun da manyan baƙi na na wannan dare.”
Murmushi sukai duka, “Nancy tace godiya muke Alhaji, ga sabuwar yankan raken naka, tunda mu ka watsar damu, yanzu Hajiya ce ta gayya to ni da ba zaka neme niba.
Hhhhhhh! “kin ban dariya, bana gari ne wallahi yanzu na dawo daga Dubai, so ya kuke? ƴammata ke bakya magana ne gaki me kyau.”
Ita ko Hajara abun tagani bambara kwai, ganin yayi sa’a da mahaifin ta, shi ne duk kunya ta kamata, ga shi dai fari ƙal da shi, daga ganinsa kinga bafulatani na asali, bashi da wani jiki.
Ita yadda taji sunan sa ta ɗauka wani wargajeje ne, ashe firit yake dama ta tsani lafcecen namiji, matsalar dai yai girma dayawa a shekaru ace yana iskanci, ya fara tsufa.
Bakya magana ne Baby na, ki kwantar da hankalinki kin mun sosai, kin riga kin gama samuna a hannunki, yanzu ziciyar taki ce sai yadda kika juyani, gaskiya Hajara kin mun zan kuma bawa Hajiya tukwici me tsoka, dan tabbas ina sanki daga kallo ɗaya.”
Wani kututun baƙin ciki ya tsayawa Nancy a ranta, ko kunyar ganin ta ba yayi yake gayawa wannan bagidajiyar wai yana santa, tunda suke sai dai ya biya buƙata da ita kawai an wuce wajen,be taɓa cewa ta burgeshi ba bare so.
“Nancy ku muje ku fara, kinga dare yayi kinsan ni ban takurawa mutum, kuyi sai nayi mu kwanta naji ɗuminku.”
Tako bushe da dariya, dan tasan ba lallai Hajara ta yarda ba, tunda bata san dawar garin ba, shi ko Alhaji be taɓa cin mace ba sai sunyi less, take ze warɓeshi ya sallame ku da manyan kuɗaɗe masu kauri.
“Alhaji bata san dawar garin ba, amma a gaban ka zan mata jawabi, Hajara zamu fara less dake, sannan sai Alhaji yai sex damu shi ke nan.”
Gabanta ne yai muguwar faɗuwa, “bangane nufun ki ba?” Ina nufin zamu ci juna ni da ke, ma’ana maɗigo.”

~*TO FANS MU TARA A NEXT PAGE, LABARIN BA WANI DOGO BANE ZAN YANKE SHI SABODA UZURIRRUKA DA SUKAI MUN YAWA. NAGODE SOSAI, NICE TAKU A KULLUM A KOWANE LOKACI.*~

                 *FEEDYN BASH*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

*Dedicated to: My kawata takaina aminiyata Fadeela (ummu mufaddal)*
_*ASSALAMU ALAIKUM, DAN ALLAH FANS KUYI HAKURI SABODA CHANJIN SUNA DA AKA SAMU, SAJIDA ITACE TA KOMA HANAN, SAJIDA NE SUNANTA, HANAN AMMA AKE CE MATA SABODA TACI SUNAN MAMAN BABANTA, YASMEEN KUMA DA NASA MATA HANAN, AMMA A GU ƊAYA YA FITO, MISTAKE NE DAMA, DAMA HANAN NICK NAME NE, SHIYASA NA SANJA MATA TA KOMA YASMEEN, INA FATAN KUNGANE?*_

+
                *50-55*

Hanan jiki yayi sauki alhamdulillah, ta fara magana yanzu sosai suna hira da mahaifanta, sunji dadin yadd ta dawo hayyacinta, lallabata suke kamar kwai, dama can Yar gata ce, amma abun ya kara karuwa fiye da da.
Tana yawan tambayarsu meya same ta aka kawota nan? amsar daya ce suke bata a kullum, ciwon kanta ne ya tashi suka kawo ta nan, saboda tana fama da ciwon kai me zafi sosai.
A ranta sam bata yarda, amma ganin bata da wanda ze gaya mata gaskiyar me ya faru da ita yasa ta hakura, badan ta yarda ciwon kai bane kawai ya kawo ta kasar waje, har da kwanciya a asibiti.
Bayan wata ɗaya yau aka sallamo Hanan daga asibiti, saboda yadda jikinta yayi sauki ba abunda ke damunta, suka shigo jirgi suka dawo gida Nigeria.
Saura wata guda a koma zaman kotu, wanda duk wata sheda da suke nema na bogi sun hadasu, saboda samun goyon bayan dpo, da kuma lawyer din da suka samu, yasan aikinsa sosai, shine ya basu damar samun shedu na bogi.
_(Kawai saboda san zuciya, lallai a ɗorawa mutumin da be jiba be gani ba, wannan duniya Allah kasa mudace kawai, amma zalunci yayi yawa a wannan rayuwar.)_
Sun gama haɗa komai rana kawai suke jira tazo, saboda su ɗaukarwa ƴarsu fansar abunda akai mata, saboda taƙamar suna da kuɗi.

_(Talaka bawan Allah! ba komai rayuwace, haka masu kudi suke cutar da talakawa, saboda takamar suna da arziki, a buga shedu na bogi duk dan a cutar da bawan Allah, ba komai Allah na kallo, kuma shize sakawa wanda aka zalunta.)_

     *******************

Karar harbi shiya farko ga makota hankalinsu yai mummunan tashi, tabbas daga layin ne nan da nan dake layin manyan mutane ne aka kira yan sanda.
Cikin minti ashirin suka zo layin, kowa ya fito banda mutanen gidan, kuma mutane sunce daga gidan suka dinga jin harbi.
Da sauri Yan sanda suka shiga gidan, suka fara cin karo da me gadi a daure tamau, kafarsa na fitar da jini saboda harbinsa da sukai.
Ko magana baya yi, ya fara fita hayyacin sa nan da nan suka tura da shi asibiti, saboda karya rasa rayuwarsa, yana daga cikin evidence, suka shiga gidan.
Suna shiga parlour suka tarar da gawar Adda yashe a kasa, ga Alaife wadda basu sani ba ta mutu ko tana raye, tunda da alamun ita ba harbi bane a jikinta.
Ba wanda suka taba a cikinsu, hotuna kawai aka dinga dauka, nan da nan akaiwa jami’an lafiya waya suka zo gidan, nan da nan Yan sanda suka fara binkice a gidan.
Cikin sa’a suka ci karo da wayar da Faruk ya baiwa Adda a dakinta da aka ware mata, da sauri suka dauka suka kunna, ba number din kowa sai son kawai suka gani.
Da hanzari sukai dialing number dinsa, sai da suka kira so uku ya daga cikin magagin bacci, ya daga “hello Adda lafiya a daren nan, ko jikin Sherrie ne ya matsa?”
Muryar namiji da yaji shi ya daga hankalinsa, “waye kai? me kake nema da iyalaina?” “calm down, muna gidanku yanzu haka barayi sun shigo gidan, saboda haka kai hanzari kazo.”
Ihu ya saki “wayyo Allah na Adda ta Sherrie” yai wulli da wayar yadau key din motar sa ya fice, Allah ne kadai ya kai shi gidan, saboda masifar gudun da yai, ma’aikatan lafiyan ma basu karaso ba shi har yazo.
Da gudu ya shiga suna rike shi, “suna ina? suna ina? haka kawai yake cewa, suka dinga rarrashin sa ya samu nutsuwa ya zauna, a hankali yakai idonsa inda Adda da Alaife ke kwance.
Ihu ya runtuma yai kan gawar Adda, yanaso ya rungumeta suka hana shi, a daidai lokacin ya sulale kasa shima a sume saboda tsananin tashin hankali.
         **************
Suna fita dasu suka kai su dan bare, anan gidan nasu yake da suke tara mata, yara da manya, suna zuwa suka watsa su wani daki daban, saboda ance su na dabanne kar hada su da kowa ba.
Haka suka hada kai suka dinga kuka, gashi Yusuf hannu a karye yama kasa kukan saboda azaba, suma kawai yake, hannun nasa yai tsami sosai.
Haka suka kwana ba wanda ya rintsa, kuka suke na rashin mahaifiyar su, musamman Sherrie da take da hankali, duk sun firgita basu taba ganin harbi da bindiga ba, hadasu tai ta rungume tana tunanin Alaife, da safe aka fito dasu gaban Oga, ya kallesu ya sheke da wata muguwar dariya.
“Ni Faruk ze munafinta, nadauke shi tamkar dana, shine babban yaro na, amma shine ze kamaku yaje ya boye saboda karmu karu daku, tabbas kune buzayen da ya gayan ya gani a bakin titi.
Amma daga karshe yace ba’ai nasara ba, ashe yayi nasarar boyeku, besan cewa duk abunda ze a idona yake ba, saboda haka gaku yanzu a hannuna, kuma burina ze cika akanku.” Hhhhhhhhh! ya dinga sheka dariya.
“Kunemo doctor a waya yanzu a dora wanda ya karye, su kuma matan a fara treatment dinsu, amma aiwa babbar kawai karamar base an mata ba.
Iya babbar ma kadai zata kawo kudin mutum ashirin, saboda suna da kyau da diri me kyau, wannan tayi karama da yawa a fara sa musu cocaine, nan da shekara uku sai a fara sata sawun mata.”
Doctor da nurses sukazo, Yusuf suka fara dorawa yadinga ihu yana kuka kamar ze mutu, duk cikin su ba wanda be kuka ba, suko dariya kawai suke shekawa.
Ana dorashi ya sume, sai da aka gama suka kwantar dashi, an masa allurai na dauke zugi da radadi.
Nan aka dinga hada wasu allurai kala kala iri iri, aka ce Sherrie ta gyara ai mata amma fafur taki, ganin zata bata musu lokaci yasa Oga yai nuni da a danneta ai mata.

_*Nima bakwa mun comment, saboda haka nima dan guntun typing zan dinga muku, idan kun gyara na gyara, idan baku gyara ba na ajiye alkalamina nima na huta.*_

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

_*Dedicated to: Feedyn Bash Exco committee*_

_*Special gift to: G.G.S.S Yakasai 2015 candy*_

 
               *55-60*

Alhamdulillah sun samu nasarar daidai tuwar numfashin nasa gaba daya, Nurse Fatima hankalinta yai matukar tashi sai da taga komai ya daidai ta sannan hankalin ta ya kwanta.
Kwana biyu a tsakani ya farfaɗo, alhamdulillah an samu ci gaba sosai, ya dawo cikin nutsuwar sa da hankalin sa, yai salati ya sanar da ubangiji yai godiya ga Allah a bisa jarrabawar da yai masa.
+
Doctor ne a kansa saboda Nurse Fatima har ta kira shi yanzu, bata da wani aiki sai kula da wannan mara lafiyar da har yanzu bata san meye sunan saba.
Doctor yace “sannu bawan Allah kaji, ya jikin naka? Allah ya kara sauƙi, kayi haƙuri kaji da ƙaddarar data same ka, domin shi haƙuri haskene zaka same shi a gaba.
Ka daure ka dena shiga mummunan yanayi da yake barazana ga rayuwarka, cutar da take damun ka ana warke sarai lamar ba’ai ba kaji.”
“Naji Likita nagode da kulawar ka agareni, nagode kema Nurse duk farkawar dazan naga ke ke kula dani.”
Murmushi tayi na jin daɗi, “haba dai karka damu wallahi, ai aiki nane kula da mara lafiya, musamman me buƙatar temako irin ka.”
Doctor ne yace “meye sunan ka ne? saboda har yanzu bamu samu wani naka ba, muna ta cigiya shiru har gidan radio da tv amma ba labari.”
Hawaye ya silmiyo masa yace “ai ko radio babu a gidana bare tv, banda kowa banda komai sai matata Hajara, kuma nasan yanzu hankalin ta a tashe yake matuƙa saboda rashin gani na, ko wuni ban taɓa yi ba a waje, in dai naje nai dako na samo abunda zamu ci gida nake komawa, wajen ta a hanyata ta tafiya tsautsayin ya sameni.”
Ƙirjin Nurse Hajara ne yai mugun bugawa, innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un! wannan wace rayuwace haka dako, da mugun tsoro a ƙirjin, da tsananin tausayinsa, bata san sanda bakin ta ya suɓuce ba tace “dam…ma kana da aure?”
“Eh ina da Mata, dan Allah ki temaka ga kwatancen gidan kije ki sanar da ita halim da nake ciki, ko ta samu nutsuwa ta samu tazo inda nake ta ganni, banda kowa sai ita itama bata da kowa sai ni.”
Zuciyarta cike da ƙunci da tsananin kishi, tace “to ba matsala” aranta tana tausayawa rayuwarta da shi kansa, dan tana mugun sansa amma bazata iya auren me mata ba, ga ƙarin tausayi ko radio babu bare tv  yai mata kwatance tana rubutawa a takadda dan kar ta manta ta fito tana sharar hawaye.

        *****************

Bawan Allah suna shan wahala sosai a prison ɗin nan, ga wahalar aiki gata mugayen ƴan ɗakin su.
STORY CONTINUES BELOW

Shi tun da Allah ya halicce shi be taɓa ganin mutune marasa imani kamar su ba, basu da imani ko kaɗan bare tausayi.
A zaman da yai ya kasance yana koyawa ƴan gidan karatu, sai da ya zama shi ne limami a masallacin cikin prison ɗin saboda, yawan iliminsa da haƙurinsa, da yadda yake tausayawa kowa da kulawa.
Suna zaune da wannan Dattijon me Suna Tanga, yana bashi labarin su Boss yadda suke zalunci da mulki a prison ɗin kafin zuwansa, amma yanzu duk sun sanja, ya ga wata azurfa ta leƙo daga wuyansa, da baƙin zare me kauri azurfar danƴwaleliya.
Karaf a idon Tanga, wata irin firgita yai, duk inda tashin hankali yake ya gama shigarsa, “kai ne? kai ne? kai me dama?”
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah kai ne abun godiya, Allah nagode ma, yau baƙin ciki na ya yanke, damuwata ta ƙare, Alhamdulillah!.
Bawan Allah ya cika da mamaki, “wai lafiya Baba naga hankalin ka ya tashi haka? muna zaune naga kuma kana ta hamdala  da tambayar nine?”
“Ƙwarai ko dole nai hamdala, na kuma tambaye ka kai ne? saboda nasanka nasan waye kai, duk duniya ba wanda ya kai ni sanin ka a halin yanzu sai iyayenka, saboda nine wanda na rabo ka da gidan ku da dangin ka da kowa naka.
            
Kai ɗan gidan sarkin santabul ne, haka ake kiran mahaifinka dashi, saboda mugun kuɗin da kuke dashi, shi kansa mahaifin ka besan adadin dukiyar sa ba, ainihin sunansa Alhaji Sani ne, mutumin ƙauyen bichi wani ƙauye ana ce masa Saye.
Kakan ka shi ne Sarkin Noma na garin, rumbun kuɗi ne dashi a ƙauyen mu, ba wanda ya kai shi tarin dukiya da yawan noma tun a lokacin, mahaifinka shi kaɗai ne ɗansa a duniya, mahaifiyar ka ƴar Amininsa ce ana ce mata Haleema, baban ta me
Masifar kuɗi ne shi ma a ƙauyen, su biyu suke tashen kuɗi a lokacin amma kakan ka yafi babanmu, tana da ƴan uwa maza da mata ciki ko har da ni, dan ita ce ƙarama a cikin mu, mahaifiyar ta ce amarya a gidan mu, tun daga haihuwar ta ta rasu ita kaɗai ta haifa.
Ta taso cikin wahala da ƙunci na rayuwa, duk da wadatar mahaifin mu abinci ma bata samu so uku wata ran so ɗaya ake bata, haka ta taso yarinya ce me tsananin haƙuri, haka ta dinga haƙuri tana  yi mana biyayya, duka zagi hantara ba abunda bata sha ba a wajen mu, wanki wanke-wanke ba abunda bata yi mun tsaneta tsana me tsanani, saboda yadda Babanmu ke santa shi ya sa iyayem mu suka sa mana ƙiyayyarta a zuciyar mu.
Mahaifin ka yayi makarantar boko har zuwa secondry anan ya tsaya, dan mahaifinsa yace sai dai yai noma shi ma ba dai boko ba, duk yadda yake masifar san boko haka ya haƙura da ita, mahaifinka mutum ne me ƙwazo sosai da sosai, nan da nan yai noma me mugun yawa da albarka, farin cikin wannan noma da yai kakan ka ya nema masa auren mahaifiyar ka.
Ba tare da wata wahala ba kuwa mahaifina ya amince masa, sam mahaifin ka baya san auren, saboda yace batai boko ba bata waye ba, amma ba yarda ya iya saboda babansa yana san babansa da biayyya a gare shi, ita ko murna take zata yi aure tabar zaman uƙuba da muke sata a ciki kullum.
Ba daɗewa aka ɗaura auren, wanda dukkan mu bamu so ba daga mu har iyayen mu, munso ƙannen mu mata aka bashi amma fafur baban mu yaƙi, duk da ita ce ƙarama ga yayyen ta a zaune, amma sam yace gwara tai auren ta huta da wahalat da muke bata.
Duk malamai da ƴan tsubbu da muka bi sai da aka ɗaura wannan auren, aka kai ta gidan ta shi kuma yana da wadda suke soyayya sosai da ita, dalilin haka ya din ga wulaƙan tata yana kiranta (Matar Ladan Noma), ita kuma bata taɓa nuna masa ta damu ba, haka zatai masa wanki tai na iyayensa, saboda gida ɗaya suke tana mugum samun kulawa daga garesu.

Saukar bulala suka ji da gudu suka miƙe, suka nufi wajen da zasu yi aiki, kowa wajen da yake daban.

    ****************

“Allah ya sawaƙe wallahi bazan aikata ba, ai ba haka mukai da ku ba, gwara na haƙura na tafi kawai na haƙura.” Ta miƙe tsaye ta fara tafiya.
Suka bushe da dariya gaba ɗayan su, Alhaji warbeshi ne ya fara magana “ai bazaka ki taɓa iya fita daga gidan nan ba tunda kika shigo.” Saboda bama zaki gane hanya ba, ba wanda ze barki ma ki fita gwara ki zauna ki nutsu.”
Jagwab ta koma ta zauna idon ta ya ciko da kwalla, rafar dubu ɗari biyu ya watsa mata, nan da nan jikin ta ya hau rawa yana karkarwa, “na meye wannan duk kuɗi ne wannan?”
Yai murmushi “nasan su kika fito nema, to gasu nan na baki wannan kyauta ne kafin na sallame ku, saboda haka ku mu shiga ku fara dare nayi mi bacci nagaji.”
Jikin ta na rawa ta miƙe “ko me kake so nayi ma zan ma a duniya Alhaji, muje ƙawata Nancy.’ Suka sheƙe da dariya a tare, duk da ƙasan ran Nancy baƙin ciki ne tsantsa da hassada a ranta.
Suka shiga ɗaki Nancy ta din ga yiwa Hajara maɗigo, sai da ta koya mata sosai ita ma taji daɗin abun, Nancy taji daɗin Hajara sosai tasa a ranta bazata taɓa barin ta ba, ita ma ta gamsu sosai hajaran.
Nan Alhaji Warbeshi ya fara warbeshi hankali kwance, da Nancy ya fara ya gama ya koma Hajara, zoka ga ihun kuka gun warbeshi, tunda yake be taɓa gamsuwa kamar yau ba.
Kira  yake “kin zama tawa banni barin ki har abada, ki kaso auren ki kizo na aure ki.” baƙin ciki ya cika Nancy ga kishin Hajara dake cin ta a rai, ga yadda Alhaji ya haukace a kanta yana warbeshi, be taɓa komawa mace a lokacin ba sai ita in yai so ɗaya sai wani karon kuma.
Dubu ɗari biyar biyar ya basu, ya ƙarawa Hajara ɗari uku wai saboda yafi morarta, million guda kenan ya bata, gaba ɗaya ta haukace tama rasa ina zata sa rayuwar ta dan murna  da farin ciki, haka yasa direba ya maida su zuwa Kano, da manyan Alƙawari da yai wa Hajara bayan danƙareriyar wayar daya sa asai mata, amma yace sai bayan an kai ta gida dan kar Nancy ta gani, ya bada umarnin a haɗa mata haɗaɗɗun kayayyaki a babban super market ɗin sa na kano.
Sukai sallama suka tafi, ran Nancy duk a jagule ko hira da ƙyar take iyawa, suna zuwa Kano gidan Hajiya sukai wa tsinke, Zubaida na nan nan suka gayawa Hajiya yadda akai, Hajiya tai ta murna dan ita kanta ba ƙana nan kuɗi ta samu ba, su kai sallama da Nancy ranta a ɓace da ƙyar ta bawa hajiya dubu Hamsin, wai Hajara ta haɗa ta sallame ta.
Hajara ko dubu ɗari biyu ta bata, tabawa Zubaida dubu hamsin ranta ya ɓaci matuƙa, ganin yadda rana ɗaya Hajara tai arziƙi haka, har ta nai mata kyautar dubu hamsin.
Kije driver ze mai daki gidan ki yanzu, “bara na bita mu tafi Hajiya” cewar Zubaida “A’a zauna ban sallame ki ba, ita da mijin ta ba lafiya zata wajensa.” Sukai sallama ta tafi cike da murna, yau ta zama Hajiya dare ɗaya Allah kanyi bature.

Ta fita ta shiga driver motar yaja suka ɗau hanya, wani katafaren super market ya kai ta kafin suje an zuba komai a leda, aka dinga lodawa a boot yaja suka tafi, ta din ga nuna masa hanya har zuwa ƙofar gidanta.
Suna zuwa taga mace a ƙofar gidan a zaune tai mamaki, wannan daga ina daga ganin ta bata san ta ba ma.
Ta sauka ta tsaya a ƙofar gidan, direba ya din ga fito da kaya, tace “kayan wenene wannan kuma?” “Alhaji yace a baki, ga waya ma yace ze kiraki anjima ze shigo gari.” Ya juya ya tafi bayan tai masa ihsani.
Mamaki kawai Fatima take, wace kuma wannan?  taƙara sa tace “baiwar Allah lafiya?” “lafiya ƙalau wallahi, matar gidan nake nema.”  “nice matar gidan lafiya?”
Kece kece? “eh meye kike mamaki, ban dace da gidan ba ko? mtsww! ni kai  na ina baƙin ciki in nuna wannan a matsayin gidana.” “dakata! ba wannan ya kawo ni ba, mijin ki bashi da lafiya yana kwance a gadon asibiti, a asibitin murtala baban ɗaki na maza.” Ta wuce ta barta a wajen sororo tana mamaki.

*SAI NAJI COMMENT ƊIN KU MY REAL FANS, INA GODIYA SOSAI ALLAH YA BAR ƘAUNA.*

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

_*ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA, KUYI HAKURI NA JINA DA KU KAI SHIRU KWANA BIYU, HAKAN YA FARU SAKAMAKON RASHIN LAFIYAR DA NAI TA FAMA DA ITA, AMMA ALHAMDULILLAH! NAJI SAUKI SOSAI, MASU KIRANA A WAYA DA MASU YI MUN TEXT DA MASU YIMUN MAGANA TA PC NAGODE SOSAI, WAYANDA BAN SAMU NAIWA REPLY BA KO DAGA WAYARSU DAN ALLAH SUYI HAKURI, BA  WULAKANCI BANE WANI LOKACIN BAN IYA DAGAWA, AMMA ALHAMDULILLAH! KOMAI YAI DAIDAI YANZU ZAMI DORA DAGA INDA MUKA TSAYA, AKAFTA MY FANS*_

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

                 *60-65*
Gaba dayan su aka kwashe su aka nufi asibiti dasu cikin tashin hankali likitoci suka dukufa akan su, anyi nasarar shawo kan Faruk ya dawo hayyacinsa Alaife ce shiru ba bayani sai da ta kwana ta wuni, amma Adda tuni rasu rai yayi halinsa.
Sai da ta kwana ta wuni tukun ta dawo hayyacinta,  anyi jana’izar Adda ta samu jama’a duk wanda yaji wannan rashin imanin sai ya zo don ai jana’izar da shi, a nan Lamido cresent ake zaman makokin nata.
Duk da ba wanda ya san su amma abun ya dagawa mutane hankali, saboda ance a ranar suka tare iyayen me gidan ne, dan ana gaisawa da shi Faruk mutum ne na mutane, daga zuwansu amma akai  musu wannan ta’asar.
Abokan Faruk duk ya sanar dasu amma ya ce kar su shedawa Oga, sun tabbatar masa da ba wanda ze gaya masa, sam baya iya magana sosai saboda tashin hankali da zulumi, babban abun da ya bashi mamaki zuwan Oga wajen rasuwar, amma ya basar kawai ya dora alamun tambaya akan sa?.
Bayan anyi sadakar uku gaba daya Alaife ta fice a hayyacinta bata ci bata sha kullum kuka, tunaninta waye yai wannan aikin waye shi bata da me amsa mata sai Yaya Faruk, kuka tasa mecin rai daidai lokacin da Faruk ya shi go gidan.
“Alaife shirya mu tafi ki debo kayan ku duka mubar gidan nan tun da anyi sadaka, makota ne dama sukai mana kara dama daga ni har ku bamu da kowa, kuma yanzu an gama zaman mokoki kowa ya watse, kuka ta cigaba dayi “ka gaya mun gaskiya me ya samu yan’uwana? suna ina? su waye su? wayasan muna nan banda kai? tabbas kai ne! kai ne!.”
Ta saki kuka me tsuma zuciya, “mugune kai azzalumi, tun farko Adda bata yarda da kai ba amma muka matsa mata muka biyoka muka zauna tare da kai, mun dauke ka yayan mu amma kai ne ka kashe mana Adda. kai ne!
Daidai lokacin yan sanda suka shigo parlour din, duk hirar da suke a kunnensu suke, saboda suna yawan zarya dan samun information akan kisan da batan yaran, amma sam basu ji shigowar su ba.
“Ki saurareni Alaife! nafi kowa sanku, nafi kowa tausayin ku, akan me zan maidaku dangina kuma na cutar daku? kin san yadda nakesan Sherri a raina kuwa? ina santa! bazan taba bari wanda ya kashe Adda ya huta ba a duniya ko da ko abun da na mallaka ze kare.
STORY CONTINUES BELOW

Kanwata ki mun alfarma ki min adalci, ki yarda dani karki bari wannan yardar da ki kai dani tai rauni a ran ki, zan binciko gaskiya insha Allah case din na hannun police.
Tafi suka ji a bayan su, “yayi actor good, suka watsa masa wasu hotuna, hotonsa ne da yara da yawa yana tsaye yana dariya, “wannan fa me zaka ce? Maza kace akan su!’ya daka masa tsawa, shiru yai jikinsa na rawa kamar mazari.
“You are under arrest! mugu maci amana, masu cin amanar kasa da ta bayin Allah, muna da video din harkallar da kuke ta safarar mata, mun samu sakon ne yau da safe shi ya sa muka kawo ma ziyarar bazata.”
Kuka yake da hawayensa “tabbas na gano komai amma wannan abun kowa zata shafa, bani ka dai ba lokaci ne na tonon asiri, zan biku ku kai ni inda zaku kai ni, amma kafin nan ina so ku sani ni dan halak ne ina zaune dasu Adda da zuciya daya.
Tun da Allah ya hadani da Adda rayuwata ta sanja, dama rashin mahaifiya ne yasa na fada halin dana ke ciki, Adda ta zame mun uwa ko yaranta basu fini jin dacin rabuwa da ita ba, saboda nagartar ta kuma na tabbatar Allah ze bayyana gaskiya.
Amma inaso kasani na tuba saboda Allah! kuma Adda tasan halina kafin ta bar duniya, tasan sana’ata ban boye mata komai daya dangance ni ba, kuma ita ta dorani a hanya madaidaiciya, kuma Sherri sheda ce akan komai idan Allah ya bayyanata, a gabanta a kai komi amma ba komai na barwa Allah!.
Amma ina rokon alfarma yallabai ga amanar Alaife, har izuwa san da gaskiya za tai halinta ni ban taba kisa ba, ban taba zina ba, aikina na tafi da matan da suka yarda suka amince suna so, bana safarar mata kanana amma ba komi akwai Allah wannan shiri ne tabbas.”
Duk gurin jikinsu yai sanyi, da gudu Alaife ta rungume shi “ina kaunarka yayana, na yarda da kai da soyayyarka agaremu, tabbas bazaka cutar damu ba.”
Tana kuka tana komai aka bambareta daga jikinsa aka tasa keyarsa zuwa Police station, ita kuma wanda aka bawa  amanar ta dpo ne ya tafi da ita gidansa cike da nazarin maganganun Faruk.

**********************

“A’a Oga kar ai mata.” Cewar kankana da take dumfaro wajen ta karaso jikin Sherri, “wannan kayan bata bukatar allura saboda da daraja, kalli fa Oga karka bata aikin mana.
Kawai kiwo take bukata na dan lokaci kankani da gyara, na tabbata ko kai bazaka ganeta ba ka bani ita ta koma dakina kaban wata biyu oga, ta saki wata shegiyar dariya.
Wani murmushi yake, “na sallama miki kankana uwar ruwa nasan zaki iya, duk abun da kika furta wannan kadan ne daga aikin ki, kin mun kankana uwar ruwa nagani na yaba.”
Ta sheke da wata shu’umar dariya ta tantiran yan bariki, “Oga nawa ni ka dai” ta kashe masa ido, nan da nan jikin sa ya fara rawa, “shirya kankana mu tafi shirya yanzu, gata nan na baki ta biki dakin ki, idan kina bukatar kari a kara miki wasu.”
Ta sheke da dariya, “bana bukata ta isa wannan ma ita ma kai zan gyarawa, ta kamata tana kuka ta kiran kannenta tana rusgar kuka, nan fa kannen nata suka din ga ihu suna kuka suna kiran ta amma haka kankana taja ta zuwa dakin ta suma aka mai dasu dakin da su ke.
Suna shi ga ta rufe ta kofa ta sheke da dariya, “kin san meyasa na ceceki? saboda kin yi mun, biyan bukatar kai na tasa na karboki, saboda ina fatan mu dore har abada tare dake, kallo daya nai miki na kamu da tsananin sanki da shaukin begen ki.
Ihu ta sa na firgici “ki nutsu kin ga bame kwatarki a gidan nan ni yar lesbian ce,” hankalin ta ya tashi dan tasan meye lesbian, tunda tayi school ba jahila bace ta keta kasashen duniya ita ma, “na cece ki ne saboda biyan bukatar kai na, da na bari an miki allurar cikin sati biyu zaki zama katuwa.
STORY CONTINUES BELOW

Amma cikin shekara kalilan zata lalata ki ta lalata miki jini da komi naki, karshe ta kashe ki har lahira, allurar tana da matukar hatsari ga tarin poison a cikin ta, abun da nake so da ke kibi umarnina ki zauna lafiya.”
Idan kuma ba haka ba zan mai daki wajen Oga ai miki allura a fitar dake kasar waje ai ta passing passing da ke, zaki kare rayuwarki cikin rashin yanci kin ji nagaya miki zamu fita da Oga me zan siyo miki?”
Shiru tai cike da tsoro “ki magana mana” ba baki girgiza kai kawai tai, “ok” ta tabe baki “kiyi tunani ki yanke shawara kafin na dawo, idan ba haka ba shawara ta rage game shi ga rijiya ni na tafi.”

********************

Gudu yake shararawa a motar fuskar sa tai ja abun ka da farin mutum, wani hadden estate ta ga sun nufa tsayawa fadar tsaruwar sa bata baki ne duk da be kai gidan su tsaruwa ba.
Suna shi ga ya kamo hannunta tana kuka tana ihu amma be saurareta ba ya shi ga da ita wani side, wani tankamemen parlour suka shi ga ya zaunar da ita a akan kujera, ya bude wani hadadden fridge ya dakko ruwa me masifar sanyi ya sha ya mika mata.
Sannan ya zauna “why? meyasa? meyasa za tai miki haka? wacece ita za tai miki haka? tasan matsayin ki a wajena? Sajida!” ya kira sunan ta na gaskiya waro ido tayi dan tayi mamaki! ya akai ya san sunanta da ba kowa ya sani ba  sai yan gidan su kowa Yasmeen yake kiranta.
“Yanzu da ba dan ni nazo ba kowane kare da doki haka zata watsoki jikinsa? shin tama san wanene soja da zata bashi mace? ba’a bawa Soja amanar mace Sajida, musamman mace me kyau kamar ke, Sajida zuciya ta ta ginu da soyayyar ki da kaunar ki.
Dan tana matar mahaifinku ba ita ke iko da rayuwar ku ba, nasan komai akan gidan ku Sajida ke yarinya ce ki ta shi kiyi sallah yanzu nasan baki ba, a hankali zaki tuna waye Yaya Aminullah din ki.”
A hankali ta kalleshi” Yaya Aminullah kai ne? Kai ne haka yayana?” Tuni ta fara hawaye, shiru yai mata yana jin kuna a ransa, ta taso da gudu ta rungume shi, ‘meyasa ka gujemu? muna cikin damuwa sosai na rashin ka, tun ina shekara goma rabona da kai maganganun ka su suka na tuna ka, bazan taba mantawa da yayana ba.
Ina yawan tuna ka amma kamannin ka sun sanja yayana, ina kaje dan Allah!” hawaye fal idonsa “Daddy ne ya kai ni Spain nai degree na gama na dora da master har Phd nayi, yanzu haka ina da mukamin General a hannuna ban fi wata uku da dawowa ba.
Duk wata hanya da zan ganku na rasa ance bame shi ga gidan, Daddy yasan na dawo Nigeria amma yana boyen komai game da Mama, meya ke faruwa ne?” wani kuka ta fashe da shi ta kara rungume shi gaba daya ta gama daga masa haka hankali.
To fa muje zuwa waye kuma Aminullah? wane matsayi yake da shi a wannan gida? wace irin rawa ze taka a rayuwar Sajida? kubiyoni dan jin karshen labarin.

*****************

Momy ta koma ciki tana sheka dariya suka tafa da Antyn yara, “hehehehe! ai damu take zancen nasan yau sunan ta matacciya.
Dan bayan tarin dukan da zata sha nasan sai sun tara mata gajiya, Allah ka dai yasan mazan da zasuyi amfani da ita, karshe sai dai mushen ta kin ga shi ke nan mun gama da Sadiya ba ita ba ahalinta” suka sheke da dariya kamar kafirai.
Kwana uku tsakani ba Sajida ba labarin ta amma basu damu ba, Alhaji ma be tambaye su ba suma basi masa magana ba, suka shirya a zuwan zasu check up India daga nan su wuce London ganin yaran su dake karatu, amma ga Sajida a gida na bauta Allah ya kyauta.
Karfe 2 na rana jirginsu ya daga zuwa India domin karasa ganin bayan Hajiya Sadiya, amma sun manta Allah na barawo ne kuma na me kaya kullum ba suke da nasara ba, Allah ka shiryar da wayanda suka bata.

Sai naji daga gare ku my fans ku sa mamana a addu’ar ku Allah ya bata lafiya ya kuma biya mata bukatunta na alkhairi, Allah ya dafa mata a lamuranta ya dorata a kan masu shi gar da promotion su shigar mata 3 years ana abu daya shiru, ina yin ku my fans iya wuya ana mugun manne ni ce taku a koda yaushe.

              *Feedyn Bash*

☄HAKURI HASKE NE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_2

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

*FEEDYN BASH ITEMS ONLINE BUSINESS*

*MUNA DA LESS*
*MUNA DA ATAMFOFI*
*AKWAI JAKUNKUNA*
*AKWAI FASHIONS*
*AKWAI HIJAB*
*AKWAI ORIGINAL MAGANIN BREAST*
*ORIGINAL MAGANIN HIPS*
*AKWAI NA MALLAKA*
*AKWAI NA MATSI*
*AKWAI NA SA KIBA*
*AKWAI NA RAGEWA*
*AKWAI NA RAGE TUMBI*
*AKWAI NA KARA NI’IMA*
*AKWAI HADADDUN TSIMI NA JARABA*
*AKWAI TSUMIN TABAJE*
*AKWAI GUMBA*
*WANDA NI FEEDYN BASH NAKE SIYAWAR WA SERIOUS BUYER PLS CONTACT ME ZAN TURA MA KAGANSU TA PC 08106795647 SERIOUS BUYER PLS AKWAI ABUBUWA DA DAMA DA BANSA A CIKI BA BA ABUN DA BANA SIYARWA NA KAYAN MATA SAI NA JIKU👯🏻👯🏻*

*MAGUNGUNA NA NA GARGAJIYA NE, WANDA ZAN HADA MA MAGANIN NE  NAI MA BAYANIN YADDA ZAKA HADA KAYAN KA DA KAN KA, MAGANINE WANDA BA CUTARWA A CIKIN SA, KAR KU MANTA SIYAN DAYA KO SARI, MAGANINA BE DA SIDE EFFECT NATURALLY NE, ME BUKATA SERIOUS BUYERS YAI MUN MAGANA TA PC KO YA KIRANI, INA ZAUNE A LAGOS AMMA DAGA KANO NAKE TURA MAGANIN DUK IN DA KAKE INA TURAWA, IDAN KUMA A KANO KAKE ZAKAJE KA AMSHI KAYAN KA DA KAN KA, SAI NAJI KU SERIOUS BUYER PLS SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*

+
                    *65-70*

Wani tsaki Hajara taja  “mtsww! kin ga wata banza kuma wacece wannan? yar wahalar kawai mtsww! Ko meye nata oho wata kodaddiya da ita” ta kuma jan tsaki ta bude gidan.
Tana shi ga ta fara ya tsine fuska tana tabe baki duk abun da ta samu ball ta ke da shi tana tsine wa halliru da gidan duka.
Haka ta sheka wanka ta bude take away taci ta ko shi, sannan ta dakko wata tsaleliyar doguwar riga wadda kudin ta ya haura 25k kai daga gani base ka tmby ba.
Ta dakko wani uban takalmi ta dora a kafarta, tai rolling mayafin akan ta wata dariya tai ta kara kallon kan ta, “wow! gaskiya kudi sunyi waze ce hajara ce matar fakiri halliru mtsww!” taja tsaki.
Ta zuba kudi a jaka tasa wayar dan idan za’a kashe ta bazata iya kunna wayar ba, haka ta dibi kudi ta rufe gidan ta fito ta tsai da adaidai ta ta gaya masa asibitin murtala ze kai ta.
Suna zuwa ta bashi dubu guda ze bata canji tace yaje ta bar masa yai mata godiya ya tafi, da tambaya ta karasa babban daki gadon sa yana daga farko bakin taga, hakan yasa bata sha wata wahala ba wajen ganin sa yace ta zaga.
Tana shi ga ba sallama sai da yai mata magana sannan tai masa sallama ya amsa, daba dan matarsa bace yai mata farin sani ba abun da zesa ya gane ta, ko da take tambaya muryarta yasa ya gane ta, tayi kyau na tashin hankali duk hassadar ka ka kalleta sai ka kara kalla.
STORY CONTINUES BELOW

Mamaki ne ya nemi kashe shi ganin ta a wannan yanayin a wannan sittirar da be saba ganin ta ba, tsoro ne da mamaki ya kama shi Hajara ce wannan matar tasa?.
Murmushi yayi mata me ciwo daga gani kasan na dole ne, dauke kai tayi “halliru meya sameka haka kuma naga ka kasa motsi?”
Murmushi yai “ba gaisuwa ba nuna tashin hankalin ki na rashin ganina? ba  alamun fargaba a tare dake? sai nutsuwa da kwanciyar hankali, hmmm! hatsari nai wallahi na samu mutuwar laka.”
Wani mugun ihu tai da yaja hankalin yan dakin, laka? laka fa kace? Taya kake tunanin yadda na faso gari ake yayina ynz zanyi jinyar ka?” Sam kar kasa haka a ranka. Mutane suka taso suna bata hakuri amma ina taki sauraron su kamar ma turi sai bakaken maganganu da ta ke gaya musu.
“Haba Hajara kiyi a hankali mana bakya ganin mutane na ta baki hakuri, ki bari mana, ina kika samo wannan kayan masu kyau haka? meyasa zaki taho haka ba mayafi wace rayuwa ce wannan kuma?”
“Dakata Halliru! kana so kace mun ciwon da uba yai a kauyen mu wanda baya iya motsi sai magana shi ne ya sameka? Kana nufin komai sai anma kenan?”
“Eh Hajara kaddarar data sameni kenan” ya fada yana share kwallar da ta cika idonsa, “a’a dakata Halliru wallahi wallahi bazan zauna da kai ba bazan iya ba.”
Ihu take duk ta hada mutane suna ta kallo, daidai lokacin nurse Fatima ta shi go taji ana ta masifa ta karaso wajen ta zuba mata ido tana mamakin tantiranci irin nata a asibiti mijinki bayan cin amanarsa da take.
“Wallahi Halliru bazan zauna da kai ba, nasan waceceni nasan yancin kai na da kyauna da komai ka mai dani tsohuwa wallahi bazan iya ba.”
“Kiyi hakuri Hajara bamu da kowa dagani har ke sai kan mu, tun da Boko Haram suka kone kauyenmu bamu kara jin duriyar kowa ba wa muke da shi wanda zeyi jinyata bayan ke?”
“Ka ne ma amma ba ni ba, ni! ni Hajara ai nagama auren ka wallahi, dole ka sawwake mun wahalallen auren ka, zan dai iya temaka ma da wannan.” Ta ajiye masa dubu dari ido ya zaro cike da razana gaba daya tsoro ya gama rufe shi.
“Ga shi nan kuma zan dawo karbar takarda ta ina da uzuri yanzu” ta juya ta fara tafiya .
Cikin zafin nama Fatima ta damkota fuskarta yabe yabe da hawaye, ta dakko kudin ta watsa mata, “debi kayan dattin ki dattin duniya bama bukata.”
“Ke ni kika rike haka? wacece ke? meye hadin ki da mijina?” “ki tambaye shi zefi baki amsar tambayar ki daidai.”

“Kai kuma shawarata agareka kayi hakuri da wannan matar taka, domin hakuri haskene baya faduwa kasa banza, ka hakura da wannan ba mace ba ce ta gari tun da har ta iya tarama jama’a a asibiti kowa na mata magana taki saurarar kowa.”
“Ta cika ta ta juya ta fara tafiya tana share hawayenta, “ke jaka mahaukaciya, naga alama san sa kike to na bar miki, idan kin isa yar halak ce ke idan ya sake ni ke ki aure shi kiyi jinyar sa.”
“Da hanzari ta dawo ni kuma zan nuna miki na cika yar halak dan Allah ka saketa yanzu a dauran aure da kai a nan wajen, banza ballagaza wadda bata san wacece ita ba jahila dakikiya.”
Wani kukan kura Hajara tai tayo kanta nan da nan mutane suka tare akai waje da Hajara, gaba daya sun gama sa Halliru a rudani ita ko Fatima sai kuka ta ke kowa na tausaya musu ana ta Allah wadai da halin Hajara.
Bala’i ta kafa a waje akan bazata bar asibitin ba sai ya sake ta, tonon asiri kala-kala ta din ga yi masa abun da ya daga hankalinsa kenan, kuka yake kamar karamin yaro yasa aka kirata aka kira nurse Fatima.
“Hajara na tabbatar bakya kaunata ko kadan, dama abun duniyata kike wa kuma yanzu babu ya kare, saboda haka zan jure komai ban da zagin iyayena, me kike so yanzu zan miki shi?”
Tana hura hanci “ka sakeni kawai dan wallahi bazan jinyar kaba da kuruciya ta na tsofe a banza a wofi, baze yiwu ba ita karuwar taka ta aure ka idan zata iya, fakiri ne dai kai baka da komai.
Ran sa ya gama baci ya kalli Nurse Fatima “kin amince zaki aureni?” ta daga kan ta “zan aure ka kuma a yanzu bana bukatar komai daga gareka na yafe.”
Nan wani a dakin yace sam shi ze bada sadaki, tuni wani yace bari ya kawo goro da alawa da dabino dama gasu ga rimi minti ashirin yai yawa ya kawo, nan aka fara hada  sadakin aka harhada a dakin abun mamaki dubu hamsin cas har da dori aka ware dubu hamsin din na sadaki.
Aka nemi waliyyi tace ta wakilata wani tsoho me musu share-share, nan Halliru ya wakilta wani dattijo, take aka daura auren sa da Fatima akan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba.
A take kuma ya saki Hajara ta saki wata buda ta farin ciki, ta ajiye masa dubu dari uku “ga wannan gudunmawa ta” Fatima ko kuka take tana mamakin tarar aradun da tai da ka.
Nan ta damko Hajara a karo na biyu ta wanka mata mari ta dauki kudin tasa mata a jaka, “kin san nasan wace ke daga ganin farko, saboda haka kar ki kuskura ki kara yiwa mijina banzar magana.”
Ihu yan dakin suka saki musamman samari na murna, “sake ta Fatima saketa” cewar Halliru “Allah yai miki albarka, insha Allah zan zame miki dan halak a rayuwar ki.
Ke kuma kije duniya ce wanda bezo bama jiransa take, Allah ya shirye ki Hajara idan zaki yana shiryu.” Ya fada yana matse kwalla abun yai wa Fatima ciwo ta bar wajen da gudu tana kuka, karo tai da mutane suka rike ta, ita ko Hajara tuni ta fice tana masifa da alkawarin ganin bayan Fatima.
Gaba daya staff din asibitin ne suka zo mazan su da matansu, rike ta su kai nan metrom din dakin su ta fara magana “Fatima baki da hankali koko asiri akai miki? aure a asibiti da me jinya haba Fatima.”
Mutane kowa na fadin albarkacin bakin sa tai musu banza, kuka kawai take tana tuno rayuwarta da kuma wacece ita din kan ta kuka kawai take.
“Ya isa haka! kun san wacece ni din? na samu me aurena zan zauna har yanzu haka? yanzu kuma na samu kuna wata magana, ku bar ni! ku bar ni haka ina san mijina.”
Ganin haka kowa kama fadar albarkacin bakin sa, tai musu banza suka gaji suka watse, ana ta tsegumi a asibitin ta hada kayan ta koma bakin gadon sa ta zauna, “zan gaya ma waceceni a yau ina fatan bazaka gujeni ba.”

*********************

Hanan ce zaune gaban tv ita da Momy suna kallon wani film a Mbc Bollywood suna hira abun su ta kalli Momy.
“Gaskiya Momy na gaji! ace ko ina kamar wata me lefi sai da driver, kuma shi dan kauyene gashi ina san zuwa gidan su kawayena, banaso si mun dariya idan sun ganni da driver big girl like me.”
“Sorry my daughter ki bari zaki driving da kan ki, amma sai kin kara warwarewa kin ji yar autata.”
Buga kafa ta fara tana kuka kamar yarinya kukan shagwaba na yaran gata, “gaskiya Momy ina so naje gidan su Deejah, amma na rasa me ya sa  sam bakwa son na matsa ko ina ko nan da can?”
“Hmm! bazaki gane bane, tun lokacin da ki kai rashin lafiyar nan Daddy din ki ya hana ki driving.” Daddy ne ya shi go parlour din “a’a Mamana lafiya?”
“Daddy ina so na din ga driving da kai na gaskiya” ta fada a shagwabe “sorry Mamana ki bari muje London ki huta sosai idan mun dawo sai ki ci gaba da kayan ki.”
Yehhhhh! ta saki kara da murna tana rungume shi yai kissing din ta suna ta hira abun su suna shan fruit, Daddy ne ya mayar CTV saboda ze kalli labarai.
Yana mayarwa befi five minutes ba sun tafi hutun rabin lokaci sai ga hotonsa tangararan, ana cigiyar yan uwansa komai da ya faru tiryan tiryan ya shi ga dawo mata.
Wata zabura tai ta mike “shi ne! Daddy wallahi shi ne! dama be mutu? ba ni ce nan ni na kade shi, ji kake yif ta yanke jiki ta fadi da gudu su kai kanta amma ina ta sume.
Sungumar ta daddy yai yana kwalawa idi driver wani mahaukacin kira su kai asibiti da ita Momy kuka take kamar zautacciya.

To fans bari in dakata anan labari ya kusa karewa fa, dama nace muku bazan ja shi yai tsawo ba ga azumi yana kara sawo kai, ban karasa Dan iskan namiji ba ina so na gama su all kafin azumi, nice taku a kullum a ko da yaushe.

            *Feedyn Bash*

☄HAKURI HASKE NE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

_*Wishe you happy birthday Yaya Hayat! Admin of Admins, wishe you long life and prosperity, more money in your account and beautiful wife.*_

*Dedicated to: Yaya Hayat Admin of Admins.*

                   *70-75*

Bayan sun gama ayyukansu suka koma daki sai dare kowa ya kwanta, wannan dattijon na zaune bawan Allah ya ce “dan Allah kayi kokari ka karasa mun labarina.”
Ya gyara zamansa ya mike zaune “zan baka labarin ka yanzu har karshe insha Allah” nan mutanen dakin suma duk suka mike zaune suka zuba musu ido dan jin labarin.

+
“Bayan wata bakwai da auren mahaifiyar ka kakan ka ya rasu, kuma a lokacin mahaifiyar ka ba ta taba ko batan wata ba.
Lokacin da kakan ka ya rasu mutuwarsa ta girgiza mutanen gari da dama, musamman talakawa dan kakan mutum ne me matukar tausayi da temako.
Bayan an gama zaman makoki  kowa ya watse bayan kwana Arba’in akai rabon gado, irin dukiyar da aka din ga fitowa da ita ta kakan ka sai ka rike baki, har rumbun kudi ne da shi a wannan lokacin.
Mahaifinka ka dai ya haifa yayi kudi na ban mamaki, hakan yasa wani abokinsa da su kai karatu ya ba shi shawarar ya koma makaranta hakan shi ze bashi damar bunkasa dukiyar sa, haka ko a kai da ke dama mayen karatun ne be wani sha wahalaba wajen komawa.
Matsin duniya da takura mahaifiyar ka tana ganinsa daga wajen baban ka, amma tun da mahifinsa ya mutu ya dan daga mata kafa saboda ya ce me kashin arzikice ita.
Dan tun da ya aureta yake ganin cigaba a rayuwar sa duk abun da ya taba kudi ya ke zama, sunan ta da ya ke kiranta matar ladan noma har yanzu be sanja sunan ba da shi ya ke kiranta.
Ya samu damar shi ga birni in da ya samu gurbi a Bayero University Allah yai masa kwakwalwa, a wannan lokacin ne ya samu ya hada degree ya fito da first class, wannan dalili yasa gwamnati ta biya masa schorlarship.
Kasar China suka turasu me mata shi da matarsa, yaje kauye ya ke sanarwa da Innar sa amma fafur taki ta ce ko in dai ze je sai dai ya tafi da matarsa, dan sam baya bata lokaci sam saboda haka baze barta ba.
Duk in da tashin hankali ya ke mahaifinka ya shige shi a lokacin saboda wannan maganar, haka dole ba dan yaso ba ya amince tun da dama me iyali ance ya tafi da matarsa amma kunyar nuna matar ladan noma yake a matsayin matarsa.
Zuwan su China ya kara takura mata saboda rashin wayewa a haka tana dan fitowa shan iska idan ya fita dan ya hanata fita ko nan da can, kar tsautsayi ya sa abokansa su ganta ya ce musu me matarsa ce wannan wannan bagidajiyar Allah ya sawake.
STORY CONTINUES BELOW

A haka ta hadu da wata bahaushiya yar uwarta itama sun zo da mijin ta ne suna yawan haduwa a compoud din  gidan, wayayyiyar macece ta lura da matsalarta ta din ga koya mata dabarun zaman aure da kula da miji.
Alhamdulillah! tana daukan komai a kan ta cikin wata shi da mahaifiyar ka ta sanja sai dan kadan na kauyancin kasa mutumin kauye, yako ji dadi sosai da hakan saboda haka sai ya yanke shawarar sa ta a makaranta ta goge sosai.
Ya daukar mata me lesson cikin wata shida ta koyi abubuwa da dama aka sata a secondary school tun da dama bata da wani girman jiki.
A lokacin ne mahaifinka ya je ganin gida ya kun zugo makudan kudi ya fara sarin kaya yana turawa Nigeria, a cikin shekara biyu sunansa ya shahara a Kano.
Ganin haka sai ya kara samun dama bayan yayi course a business yayi degree sai ya koma karatun Soja kuma saboda yana masifar kaunar aikin soja.
A lokacin mahaifiyar ka ta kusa kammala secondary a lokacin ta samu cikin ka me wahalar laulayi, ta Sha wahala da kyar ta samu ta gama makaranta saboda yadda cikin yai nauyi.
Wata daya da gamawa ta haifeka a lokacin da aka haife ka a lokacin sunan mahaifinka ya fantsama duniya, kasancewar sa attajiri kuma General a Soja wannan ya kara masa kai mi a idon duniya.
Akwai wani abokinsa da suka hadu a School me suna Abdulwahab shi ya din ga nanika masa kanwar sa tun suna karatu ganinsa shahararren me dukiya.
Bayan haihuwar ka su kai nasara a kansa ga giyar kudi na dibansa ga asiri, ba me gaya masa yaji a lokacin ne ya tamfatsa wani uban gida a Sokoto road.
Sun je saudiyya sun yi Hajj  lokacin kana jariri a lokacin suka je gida kauye, duk basu gama karatun ba ganin gida a wannan zuwa a ka shirya kitimurmurar a kai auren matar mahaifin ka ta biyu Hajiya sha’awa da mahaifinka.
A lokacin ta kafe sai dai a tafi da ita dan fitinanniya ce sun koma shekarar su uku suka dawo, lokacin kana yawon ka ko ina ita kuma da tsohon ciki tayi bakin ciki da ita ma bata haihu a waje ba.
Gallazawar duniya mahaifiyar ka ta sha ta a lokacin a kai wa mahaifinka wata sarauta wai sarkin santanbul, ma’ana; sarkin masu kudi, saboda kudi gidan sa idan zaka shi ga sai wani maciji ya fesa ma turare.
Kai ba abun da babu a wannan gidan wannan zuwan ne na makalewa mahaifinka na biyo su birni, saboda na tsani kanwata ni da yan uwana muka shirya ganin bayanta ko ta halin yaya.
Zuwa na gidan muka hade da Momy sunan da ake kiran ta ganin itama bata kaunar mahaifiyar ka, a lokacin mahaifiyar ka ta kara samun wani cikin tashin hankali a wajen Momy ba’a sa masa suna.
Ganin haka ta nemi shawarata akan zubar da cikin dan kar ta haifi namiji kai kan ka ta tsane ka, ita ya macece da ita kuma ga shi planning ta ke taje ta cire amma shiru ba bayanin haihuwa gashi anyi anyi a kashe ka abu ya gagara.
Nan muka fara yunkurin zubar da cikin amma ko gezau Allah be bamu sa’a ba, ganin wankin hula ze kai mu ga dare na bada shawarar a wullar da kai a lokacin masu gadi ne a gidan ku dana ga sun samu bacci tsakar dare na taso Momy.
Muka tashi ni da ita muka daukeka na fitar da kai na kai dan wani kauye na wullar, a lokacin wannan azurfar ta wuyanka tana wuyanka babana ne ya daura ma tun haihuwar ka wannan shi ne sanadin barin ka gida.
Bayan gari ya waye aka nemeka aka rasa amma shiru ba labari a lokacin ne na fara rakata wajen bokaye dan mallake mahaifinka, duk da ya na mijin kanwata amma na tsani zaman su tare saboda cigaban da take samu dan yanzu yana mugun san ta ya damu da ita.
Gashi ta samu wani almajiri Aminullah wanda ya ke debe mata kewa sosai yana da nustsuwa da hankali, shi ya ke mata rubuta yana bata tana sha yana baka kai ma shi ya sa duk asirin da ta ke mata baya tasiri har mahifin naka yakan yi masa lokaci zuwa lokaci.
Mun yi nasara dan sam hankalin sa ya koma kan ta ya manta da mahaifiyar ka bare batun ka, bayan wata uku da bacewar ka mahaifiyar ka ta rame Aminullah ke kwantar mata da hankali jin sa ta ke kamar dan ta dan yana masifar kaunar ka kai da ita.
Hawan jini ya kamata haikan a lokacin saboda bacewar ka ga tsohon ciki, a lokacin Aminullah ya dage da bawa mahaifinka rubutu abun ya warware ya sake shi, ga mahaifiyar ka kullum addu’o’i ta ke duk ta rame ta lalace.
Saboda yadda mahaifiyar ka ke addu’a a lokacin aka din ga neman ka amma ko me kama da kai shiru, dan anyi sake tun farko ba’a bi lamarin ka ba dama Aminullah ke zagawa ya bada sanarwa amma shiru, lokacin ne mahaifin ka ya kawo sojoji gidan a lokacin ne mahaifiyar ka ta haifi ya mace kanwar ka kenan.
Bayan haihuwar ta shiru Momy ba labari ganin haka Momy ta kara komawa asibiti suka tabbatar bazata kara haihuwa ba, saboda ta sha magunguna ba bisa ka’ida ba sun lalata mata mahaifa.
A wannan lokacin sunan Sarkin santanbul ya kara fantsama a duniya a lokacin ne idon Momy ya kara budewa ni kai na ta fara juyan baya, a taron matan manya da suka je wani biki tai wata kawa da ta bude mata ido suka tafi India tsafi.
Anan ne bokan ya gaya mata cewa lallai sai an hana Hajiya mahaifiyar ka haihuwa sannan zata mallake Alhaji ita daya, dan yana da san yara anan ya sheda mata abun da Aminullah yake wanda in dai yana nan ze din ga warware komai.
Lokacin da suka dawo da kawarta a lokacin ne suka fara kulla kullar korar Aminullah, amma abu yaci tura a gefe guda kuma ashe soyayya ake sha da mahaifin ka da aminiyarta.
Wanda lokacin mun fara neman juna ni da Momy saboda yadda muke kasancewa tare da ita, kawarta ita tai asirin da ta raba ita kan ta da Alhaji lokacin ne ta haukace ta koma India in da dodon tsafi ya bukaci shanu ta tanka masa.
Ta ke Alhaji ya koma hannunta sai suka fara gwara kansa kamar kwallo, bayan shekara biyar a lokacin ne Momy taci nasarar kullawa Aminullah sharrin satar gwalagwalai, wanda ita ta boye nata ta sa Alhaji ya kore shi daga gidan.
Mahaiyarka tai kukan rashin sa tare da ita, a lokacin shekarar kanwar ka shekarar ta goma a lokacin Antyn yara tai nasarar auren Alhaji in da suke buga bala’i a junansu.
A hankali suka hade suka fara kokarin ganin bayan yar uwata a lokacin mahaifin mu ya rasu yai mana nasiha me tsuma jiki na koma bayan kanwata har nai aure mun tare da matata a gidan.
Mun haifi yara biyu ganin na gujeta na shiryu na koma ga Allah a lokacin suka shirya haukatar da mahaifiyar ka, wanda sun yi nasarar haka kuka take kamar karamin yaro.
Nazo shi ga naji suna zancen na gaya mata amma sam taki yarda sai wayar gari mu kai ta haukace, nima ko na dira musu hauka dan Alhaji baya gari a lokacin nace sai na tona.
Nace yana dawowa zan gaya masa a lokacin su ka shiryan makirci a daren ranar suka aiko aka kashe matata aka samun wukar a hannuna sai farkawa nai naga yan sanda sun zagaye ni wai dan kungiyar asiri ne ni.
Ina kallo aka dinga zakulo kayan tsubbu akace dan kungiyar asiri ne ni haka aka kawoni kotu, rashin gamsassun hujjoji aka yanken hukuncin rai da rai a gidan yari yarana iyayen matata suka dauka.”
Ya rushe da kuka kowa kuka yake a dakin na tausayin sa, “matata abun sona yar uwata sun gama dasu wannan bakin cikin ya kashe kakar ka Babar baban ka, amma be damu har yau yana rayuwane amma shi ba mutum bane a waje ne kawai yake namiji amma a gidansa be da maraba da gunki.
Daya koma gida sunan sa mace su suke mulkar gidan, ita amaryar yaranta uku duk mata ana ce ma ta antyn yara, ita kuma Momy da ga ya daya bata kara ba wannan ne labarin ka.”
Kowa kuka yake a dakin a lokacin nan gandirobobi suka hasko su suka kwanta kowa yai shiru.

To fans comment  din ku shi ke karan karfin gwiywa sai naji daga gareku ni ce taku a kullum a koda yaushe.

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

                    *75-80*
DPO ya tafi da Alaife gidansa ya bawa matarsa amanar ta ya roki alfarmar ta rike ta amana saboda amanace a wajen sa.
Tana ganin yarinyar taji ta shi ga ranta matuka daga ganin buzuwace ita irin yan Niger din nan taji ta kwanta mata a ranta sosai.
An kai Faruk Police station tambayar duniya ya ce bai da masaniya amma yasan gidan da suke ajiye yaran shi da Oga, aka dibi bataliya aka tafi amma Yan sanda suka ce su sam basu ga komai ba sai fili, shi kuma ga gidan yana gani har da masu gadin amma fafur sun ce ba komai abun ya daga hankalinsa.
Amma sam su basu gani ba karshe aka maida shi, duk wani evidence da ya ke san bayarwa babu saboda anje gidansa ba komai sun kwashe duk wasu shedu na gidansa, ganin yana wasa da hankalin hukuma aka dauke shi aka kai shi kotu.
Da ke yana da lawyers aka dage sauraron karar zuwa wata biyu masu zuwa aka hana belinsa saboda case ne na kisa ga batan yara aka tura shi prison.
Bayan sati biyu lawyers din sa sun rasa hujjoji ganin wankin hula zai kai su ga dare suka nemi dop, suka ce ya kawo yarinyar prison din gwauron dutse zasu yi musu tambayoyi ita da Faruk ba bata lokaci ya kai ta.
Bayan sun je a ka basu daki guda suka zauna lawyer ya fara tambayar Alaife? “muna so ki bamu tarihin rayuwarki dana mahaifiyar ku dan muna so mu gano ainihin wake bibiyar rayuwarku.”
Ta sharce hawaye duk da karancin shekarun ta amma wasu abubuwan na nan daram a kanta ta fara magana kamar haka.

“Mahaifiyata cikakkiyar buzuwace yar agadez irin talakawan nan futuk sun taso su biyu a hannun matar babansu, a yadda take bamu labari ita da yayar ta Sherri ita kuma Afsi sun taso cikin wahalar rayuwa da kangin talauci mahaifiyar su ta rasu bayan ta haifi Afsi.
Sherri tana da shekara goma a lokacin akwai ratar shekaru tsakanin su mahaifinsu ya bawa wata makociyar mu yafindon Afsi saboda ta nemi haka, ta cigaba da kula da Afsi har aka yayeta a lokacin ba shi da niyyar aure, saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki na rasuwar matarsa.
Bayan an yaye Afsi ga shi yafindo ita ma bata da karfi ga girma dole aka matsa masa ya auro Ramai! dan kula da yaransa tun da duk mata ne tun da aka dawo da Afsi Sherri ce ke kula da ita ta ko ina.
Saboda tsananin kaunar ta da take mata, zuwan Ramai ya tarwatsa farin cikin su dan bala’i da masifar ta kadai sun isheka ka koshi a gidan, bata basu abinci sai dai suci kanzo dan ma Sherri ta dan girman ta haka take daka da wankau taci dasu, dan mahaifinsu shi ma sai a hankali Ramai tafi karfinsa shi dasu sai kallo.
A haka sai Afsi tai kashi a kasa idan Sherri bata nan haka Ramai zata daureta ta dinga duka ba wanda baya zubarwa da yaran kwalla a makota, amma kowa tsoron Ramai ya ke bame iya tanka mata, haka zatasa ta cinye kashin nan bazan iya lissafa muku kalar azabar da mahaifiyata ta sha ba.
STORY CONTINUES BELOW

Idan suna cuta baza kai tunanin zasu rayu ba a turken dabbobi suke kwana tare da dabbobi, duk ruwa sai dai su koma gefe su rabe Sherri ta rungume Afsi suna kuka, haka zasu zauna a wajen ko mai ruwa dan mahaifinsu ba shi da ta cewa, daki daya ne a gidan ta rantse kuma bazasu kwana tare ba shi ma dakin duk ya lalace saboda rashin kula.
A haka afsi ta kai shekara bakwai Sherri na da 17 wanda a kauyen garin nasu yarinya sha uku tayi aure, amma saboda talauci ba abun da za’a kai Sherri da shi yasa take zaune tana kula da kanwarta suna shan wahala tare, haka suka taso ba arabi ba boko sai dai idan sun ji yara na karatu su labe.
Lokacin ne wani wai shi Alhaji Buba yana kawo hatsi daga Nigeria yake bin mahaifinsu tarin bashi, ganin beda hanyar biya ya yanke shawarar ba shi Sherri kawai ya aura saboda rufin asirin sa, ba dan ransa yaso ba sai dan tsananin talaucin sa ya gwammace yi maga auren biyan bashi.
Ga shi dangin mahaifiyarsu yan damagaran ne iyayenta sun rasu, kuma zumuncin yanzu sai a hankali bata da yan uwa da suke ciki daya, shi ko babansu bema san kowa nasa ba a haka sukai aure na rashin gata, ga yara sun tashi cikin kuncin rayuwa da rashin gata.
Alhaji Buba yaji dadi dan dama ya dade yana kaunar yarinyar rashin fuska da bata bawa kowa yasa ya hakura kawai, kamar daga sama mahaifin ta yake gaya mata gobe auren ta da Alhaji Buba auren da bata san da shi ba ga kanwarta me shekaru bakwai tunaninta kanwarta kawai.
Kuka haka ta dinga yi kamar ranta ze fita kwana tai ba tai bacci ba tana rungume da kanwarta me karancin shekaru daba ta san me ake ba, ita ko Ramai bakin ciki kamar ze kashe ta saboda Sherri zata auri me kudi ba yadda batai a bar auren ba amma ya gaya mata ba fashi da asuba ta bazama wajen bokanta.
Amma ya sanar da ita dole ayi idan ta matsa zata rasa rayuwarta dan auren ba fashi akwai rabo, amma zata wahala a auren wannan wahalar yasa ta hakura ta yarda a ranar aka daura auren a ranar aka tafi da ita, ba yadda ba tai ba a bata kanwarta ba amma Ramai ta hana baban ya bayar, shi mijin ya amince amma Ramai ta kekashe kasa taki tana kuka aka rabasu rabuwa ta har abada, tun da ga Adda ta rasu bata ga yar uwar ta ba” ta dinga wani irin kuka kamar zata shide.
Ganin haka aka bata ruwa aka ce ta huta suyi sallah suma ta karasa gaba daya, kowa tausaya musu yake jikin Faruk yai sanyi kalau kawai kallon ta yake yana so ya tuno wani abu ya gaza.

**********************

“Kankana uwar ruwa” cewar Oga suka sheke da dariya suka tafa ya kamota suka fito da sauri masu gadi suka sanar musu zuwan Faruk da Yan sanda a kofar gida.
Wata dariya Oga yai “yaron nan bashi da hankali kankana! wai dani zeja? karku damu in dai mutum ba gidan nan ya bari ba da kewayen gida wahalar banza zasuyi ba wanda ze gan ku, ku kwantar da hankalin ku Kankana mu koma ciki.”
Ta turo baki “gaskiya ni” ta fara bubbuga kafa “sorry my beb ki kwantar da hankalinki ba abun da ze faru, abun da nakeso dake shi ne kiyi hakuri mu koma ciki nayi shi dan ban iya hakuri” suka sheke da dariya suka kashewa juna ido.
Su ka koma side din sa suka nufa sai da ya sha giya yai tatul sannan ya far mata wai tafi kara kuzari, sai dare ta baro side din nasa ta tarar da Sherri a kwance tana ta hawaye.
Ji tai wata muguwar sha’awa ta birkito mata kamar ba wuni sukai abu guda ba ta karasa kusa da ita ta birkitota jikin ta, ta fashe da kuka me tsuma rai sai da jikin kankana yai sanyi lakwas amma shedan ya buga mata gangi.
Ta din ga shafa bayan ta tana hura mata iska a kunne gaba daya sai tai sanyi tai lakwas, duk wata jijiya dake aiki ta jikin ta ta saki ganin ta samu haka gata yarinya karama kawai ta janye ta ta murzawa dakin key.
Ta dakko lemo ta faki idonta dan tai luf tama fara bacci ta watsa musu kwaya a Shani ta tsiyaya musu a cup, ya dau raba ta mika mata a hankali ta karba ta sha ta gama sha kenan taji wani yanayi na gushewar tunani.
Gaba dayansu suka haukace suka fita hayyacinsu ta fara murza Sherri san ran ta, wayarta ta tsaida ta inda ake ta kiran ta ganin me kiran baze saurara mata ba yasa ta daga.
Da hanzari ta ta mike tsaye what? Ta furta da karfi da sauri ta zura kayan ta ta fice ta bar Sheri na kuka da ihu saboda sha’awa, kiranta take amma tai gaba kuma ta rufe dakin.
Sheri ta koma ta kwanta ta dinga zunduma ihu kamar wadda ranta ze bar gangar jikinta, jikinta kawai rawa yake abu ne daba ta taba tsintar kanta a ciki ba bama tasan menene feeling din ba so biyu ta taba al’ada ma.
Zubewa tai a wajen tana kuka me tsuma zuciya a haka bacci ya dauketa tana hada wani uban gumi duk da ac din dake cikin dakin.
A matukar tashin hankali ta shi ga asibitin ta tarar da kanwarta tana rusa kuka da hanzari ta karasa ta rungume ta lafiya? Meya sameta ne? Cikin kuka tace kije Mamaa sunan ki kawai take kira.
Da hanzari ta shi ga dakin da take da ke asibiti ne me zaman kansa ta karasa bakin gadon da gudu tana kuka, “Ummi ki tashi dan Allah gani nazo na miki alkawarin bazan kuma bata miki ba.”
Tai wani murmushi me ciwo “Mamaa bakya ji kinyi nisan da bakya jin kira, kullum nai sallah ina miki addu’a makarantu ina bi malamai ina bi, Mamaa har dawafi ina yi saboda ke har umara ina miki Mamaa meyasa bakya ji? kina yar babban gida amma kin dauki zina ado abun ya wuce nan ya koma safarar yara.
Yanzu Mamaa a ce safarar yara kika koma ta ya ya kike tunanin hankali na ze kwanta, tunda kika sa kafa kika bar gida bake ba labarin ki Mamaa wai safarar yara?” nan ta shi ga wani mawuyacin hali ta fara wani irin tari me sarke numfashi.
Hankalin Mamaa ya kara tashi “Ummi na miki alkawari na bar halayena dukansu Ummi zan nutsu dan fari  cikin ki, kiyi hakuri” Ummi tana tari ya dan lafa “idan har kina so na yafe miki Mamaa ki ceci yaran da kuke safarar su ku maidasu gaban iyayensu.”
Abun yai mata girma dan Oga ya wuce tunanin ta amma haka ta hadiye tashin hankalinta saboda mahaifiyar ta, “na amince Ummi” ta kamo hannunta ta rike “ki rike girmanki dan Allah! kiji tsoron Allah ga kannenki nan kece babba ki kula dasu, yadda mahaifinku ya barni daku kema zan bar ki dasu, gasu nan ki rike su amana ki kula da rayuwarsu ki zama gatansu.
Kuka kawai sukaji kannenta ne suka shigo suke ta kuka gaba dayan su suka rungumeta nan tarin nata ya kara tsanani, abun da ya daga hankalinsu kenan suka kira likita, yace su fita amma fafur Mamaa taki da kyar ta yarda ta fita.

*******************

Hajiya Sadiya ce kwance a dakin da aka bata kwanciya tana kwance cikin tsafta, abun da sauki sosai saboda kulawa da take samu yanzu, bata doke doke kawao gata nan kwata-kwata bata magana yanzu.
Alhaji ne ya shi go ya kalleta fes gwanin sha’awa ta kara komawa danya sharaf abun gwanin sha’awa kallonta yake kamar wani wawa wai sadiyan sa ce.
A hankali ya matsa jikin ta yana tai mata magana ba magana sai ido kawai take binsa da shi, ganin haka ya fara shafata ta ko ina nan ya ga bata nuna alamun ki ba, ganin haka ya fara juyata san ransa ya biya bukatar kansa.
Tun daga wannan ranar ya samu nayi saboda yadda yake samun nutsuwa har wata kiba ya fara, musamman da jarababbun su kai tafiya tarewa yai a can ba um dai ba um um, sai dai yai ta kallon ta wasu lokutan kuma sai tai ta kuka.

To fans sai naji comment din ku mu hadu a next page insha allah.

               *Feedyn Bash Cele*

HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________

Bissmillahirrahmanir rahim
                   80-85
Kallon ta kawai ya ke ya na tsananin tausaya mata ,tare da tsantsar soyayyar ta a ransa, ina jinki Fateema ta gyara zama hankalin kowa yayo kan ta musamman masu san jin kwaf.
Asalin suna na Fateema yar mahaukaciya ake kira na ,wasu bayin Allah ne su ka  rada mun suna Fateema, wanda su suka dauki nauyi na da rayuwa ta gaba daya a wannan lokacin!.
Sun ban labarin kawai mahaifiyata ta na yawan zama a bolar bayan gidansu ta na tsince tsince ance, ba ta duka bata komai sai dai surutai, ba ta umm bata umm umm sai dai kallo, idan taga zaka takura mata za ta sanja waje bayan ka ta fi ta dawo gurin ta ci gaba da yin tsince tsincenta.
+
Watan ta uku da fara zama a wannan bolar aka lura da bullowar ciki daga gareta .
Abun ya daga hankalin mutanen unguwa sosai da sosai, sai aka fara zargin Alhaji Habibu da yiwa mahaifiyata fyade.
Saboda ya na yawan zuwa ya bata abinci musamman da ya fuskanci ciki ne da ita. yana ajiye mata kuma ta na dauka sosai cikin ke girma wanda mutane suka fara zuga matarsa mama nafi akan shi yai mata cikin.
Mama Nafi mace me yakana da fahimta da tsananin tsoron Allah, ganin haka ta sa aka dakko mahaifiyata ta dawo da ita gidan ta, lokacin cikin ta ya yi nauyi sosai .

Mijinta ya dawo yai mamaki dan hankalinsa ba karamin tashi yai ba da ya duba inda ta ke bata nan.
Yaji dadi kuma yai hamdala ga Allah ya sawa matarsa albarka sosai da wannan abun alkhairin da tayi, da yadda ta fahimce shi bayan wata biyu mahaifiyata ta haifeni tasha bakar wahala tun daga lokacin kulawata ta koma karkashin Mama Nafi.
Mahaifiyata wadda har yau ban san sunan ta ba, ta na masifar sona duk da tana halin hauka tun da ta haihu ta warware sai ta dauke ni ta gudu zuwa wannan bolar.

Ganin haka hankalin su ya tashi da kyar suke karbata su ganni sai sun mata dabara fafur ta ki zaman gida kullum magani suke amma abun shiru .
Bayan na kai shekara goma a lokacin tuni Alhaji Habibu ya sewa Umma wannan bolar an gina mata daki guda kuma tana zamanta a ciki, ga makeken tsakar gida haka za ta hada bolar ta tai ta wasa, niko idan taga na fara kuka za ta fara kukan itama tai ta rungumeni.
Ganin haka sai nadena yawan kuka a  gabanta, A lokacin Alhaji Habibu ya sani a makarantar boko da ta islamiyya.
Alhamdulillah ina da tsananin kokari ,hakan ya ja mun farin jini wajen malaman mu sabanin yan ajin da suke kirana yar mahaukaciya” ba na wasa da kowa banda kawa ba na kula kowa haka rayuwata ta kasance.
STORY CONTINUES BELOW

Har zuwa san da na mallaki hankalin kai na .
A lokacin Mama da Alhaji sun yi tafiya sukai hatsari suka rasu, a lokacin na zana jarabbawar gama secondary ,tashin hankalin na shige shi musamman da ya zamana bangon da muke jingine da shi ya fadi.
Gashi yaran su sun tsanemu ganin yadda iyayen su ke kula damu, musamman ni yaran su duk sun girmeni ,matan duk suna daki amma sun tsani su bude ido su ganni ,gidan da muke suka fara sawa kahon zuka, cikin ikon Allah babansu yayi abun a gaban shedu a gaban mai unguwa da manyan unguwa, wannan shi ya karya lagonsu suka hakura ba dan suna so ba.
Tashin hankali na shige shi saboda rasa abun da zamu ci ,ni da mahaifiyata gata ita ba hankali ba ,ba wani namiji da yake sona ko kace kana sona za’a gayama shegiya ce ni” kuma yar mahaukaciya wannan abun yana taba ni sosai ,yana sani a damuwa ganin haka na yanke shawarar aikatau.
Na sha wahala sosai kafin na samu gidan me sai da abinci ina mata wanke wanke ,nan maza sukai mun ca ganin haka sai ta nemi ta fara neman kudi dani ,amma sai naki karshe dai ta koreni a haka jarrabawata ta fito.
Inda na samu nine credit abun da ya farantawa principal din mu ta shiga ta fita na samu scholarship na gwamnati: na samu suka samar mun admission a school of nursing su suka dauki nauyi na a haka  suna temakan musamman dana bata labarin rayuwata, duk inda taji tallafin gwamnati tana karbamun .
A haka na gama su ka samar mun aiki da  gwamnati na zauna a Jakara kafin na dawo nan ,ba wanda yake sona ko kaunata ban da kowa ban da komai ban da wata kawa a duniya yanzu munyi aure da kai bansan a wane matsayi auren ya ke ba, ta rushe da kuka me tsuma rai!
Duk wanda ke dakin ya tausaya mata harda masu sheshsheka saboda tausaya mata.

Hawaye yake ya kalleta kawai wani mahaukacin so ya ke mata me barazanar tarwatsa mata zuciya.
Yanzu ina mahaifiyar taki ta warke ko har yanzu bata warke ba ?
Ta share kwallar da ta zubo mata har yanzu magani nake mata amma shiru har yanzu !.
Kuna gidan da kuke har yanzu ko kun tashi daga gidan ?
Muna can taki yarda mu tashi bata motsawa ko ina har yanzu ga shi har ta fara manyanta ,  har yanzu bamu dame temaka mana ,duk inda mukaje sai ace sai munyi ido biyu da wadda tai mata wannan asirin sannan komai ze tarwatse.
Duk ranar da ta ganni ko mahaifiyata a ranar zata fadi da tai komai ze bayyana kansa a ranar zata nuna inda tasa wannan asirin, ranar za’a warware amma har yau Allah be hadamu da ita ba.
Shiru ya yi cike da tausaya mata yana share kwallar idonsa tabbas akwai tausayawa a cikin labarin ki ,bari nima zan baki nawa takaitaccen labarin.
Asalinmu mutanen Maiduguri garin Goza, wani kauye ne wanda muke rayuwa cikin rufin asiri da wadatar zuci ga karamci irin na mutan Maiduguri .
Ni Halliru na taso cikin gata da wadata saboda mahaifina Allah yai masa arziki sosai ,hakan yasa muka tashi da wadata nayi karatuna tun daga matakin primary har masters ina aikin banki.
Lokacin nai aure na auri matata Hajara ,aure mukai na soyayya an kashe dukiya nera tayi kuka a wannan ranar, bayan auren mu da shekara uku shiru ba haihuwa hankali Hajara ya tashi amma na kwantar mata da hankali na nuna mata komai na Allah ne ,ban damu ba kuma ba batun kara aure a rai na.
Shekarar mu biyar da aure aka fara Boko Haram a Maiduguri, saboda kashe malam Yusuf tun daga wannan lokaci gari yaki dadi, saboda yadda sojoji suke bi gida gida suna kashe duk wanda ya taba cewa shi dan Boko Haram ne, koda ko da wasa yake.
Wannan ta’asa ta kara fusata yan Boko Haram ashe suma da shirin su, dan da abun nasu kamar wasa ashe gaske ne ,nan su ka fara tada bomb, ranar da ba zan taba mantawa da ita ba, ranar da aka dasa bomb a kasuwa wanda ya ritsa da mahaifina da karamin kanina.
Suka shiga kauyen mu sukai muguwar ta’asa a lokacin ne muka taho ni da Hajara dan zuwa gidan mu, kafin mu isa sojoji sun je kauyen suka dinga shiga gidaje akwai kofa ta bayan gidan mu ta nan muka shiga inda muka tarar sun rufe ta gaban.
Babban abun da ya dagan hankali” ya rushe da kuka me tsuma rai! ganin sojoji sun hallaka mahaifiyata sun yiwa kanne na mata hudu fyade ,sun kashe mazan guda biyu ,yara suna fita muna shiga kanwata ta ke sanar da ni ta na halin mutuwa da rayuwa sai jin motsin su mukai .
Muka boye ni da Hajara a wani daki ,dake sun duba gidan basuyi tunanin da wata hanyar ba munaji suka dinga murkushe kanne na ,bayan wayan can sun gama sun fita,sai wasu suka shigo a haka sai da mutum sha uku sukai wa kan wata falmata fyade dan ragowar duk sun rasu.
A wannan halin ita ma ta rasa rayuwarta , mu na ji su na zasu kone gidan saboda ace yan Boko Haram ne sukai wannan aikin ,suna fita na kamo Hajara tana kuka ina kuka muka dinga gudu haka sojojin nan suka nike gidan mu .
A bakin wani naji sunce wai yan Boko Haram ne mu shi ya sa suka nike gidan da mutan gidan, mun sha azaba a hanya wanda muka dinga tafiya da kafa daga wannan dajin zuwa wannan, mun wahala sannan muka iso Potiskum muka ya da zango.
Mu na nan zaune cikin ikon Allah na samu wani uban gida na gari, yai mun ciku ciku aka karbomun takadduna na karatuna dana gama a jami’ar Maiduguri.

matarsa ta tsanemu ni da matata muna nan zaune haka muna buga buga muna samun na rufawa kai asiri, sai labari ya sameni boko haram sun gama da garin mu.
Wannan shi ya dagan hankali wani dare muka silale nida matata muka biyo duhun dare ba inda nai sha’awar zuwa sai garin Kano ,mutane masu karamci da yaka na ,anan muka hadu da wani mutum na bashi labari na ,shi ne ya kai mu wajen me unguwa aka saukemu aka tausaya ma na aka hada mana goma ta arziki.
Kama daga kan suttura abinci ,wani Alhaji ya ba ni gidan da muke zaune muddin rai, tun da wannan abincin ya kare mu ka shiga halin tashin hankali ,mara misali na rasa abunyi sai buga buga ,tun daga wannan lokacin da iftila’i ya fadan Hajara ta juyan baya gori kala kala da wulakanci .
Musamman da tai wata kawa dake hure mata kunne da muna zaune lafiya, amma tun da su ka hadu da zubaida komai ya lalace, wannan shi ne mafarin rikici na da ita bacin ran da ta kunsa mun shi ya sa ban san ana mun horn ba har wannan iftila’in ya sameni ,amma alhamdulillah ba abunda zance da Allah sai godiya.
Kuka mutanen dakin suke har da sheshsheka saboda tausayin sa shima kuka yake na tuna abun da ya faru.
Ka na so ka ce mun sojojine sukai wa yan uwanka fyade har suka kashe maka kanne da yan uwa ;ta na wani irin kuka ta ke wannan tambayar.
Murmushi yai me cin rai ya ce” tabbas su ne su ka yi musu fyade suka kashe su saboda gudun tonuwar asirin su shiyasa suka yanke wannan hukuncin .
Abun da baki sani ba shi ne “duk wani fyade da akai sojoji ne saboda yan Boko Haram basu ma da nutsuwar da zasu tsaya har suyi fyade ,sai dai su dibi matan su gudu wannan shi ne gaskiya suyi fyade su kashe mutan gidan shi ya sa na tsani sojoji bana kaunarsu.
A da na kaunaci soja sosai amma sam yanzu na tsane su ,haka suka dinga kuka mutane nata mamaki suna yi musu fatan alkhairi. ya ce” ya ji ya gani kuma baze taba wulakanta ta ba ,tai masa ranar da matarsa ta kasai masa duk tarin wahalar da suka sha tare.
Ya na san Hajara ya na tausaya mata dan tare suka wahala amma yaze yi ita ce ta nuna bata kaunarsa.
Hanan ce ta farfado bayan tasha drip duk wani tunaninta na baya ya dawo ,ta fashe da kuka Daddy wallahi ni ce na kade shi da kai na da mota ,ku kai ni wajen sa ta fashe da kuka ta fara bige bige ganin haka suka nufi asibitin murtala da ita cikin gaggawa.
Ba su sha wata wahala ba wajan nemansa,aka kai su dakin da aka kwantar dashi,tun da suka durfafi dakin gaban Momy ke faduwa amma ba ta kawo komai ba, haka ta ci gaba da bin hanyar dakin da aka nuna musu.
Su na shiga haka kawai Fateema ta zubawa budurwar yarinyar ido ta hango tsantsar kamar da sukeyi ,matsowa ta yi kusa da gadon ta na lekensa ,lokaci daya ta fara fadin ,wallahi Daddy shi ne nice na kade shi ,ni ce na kade shi da mota ta fashe da kuka .
Da hanzari Momy ta kallesu caraf idon ta ya sauka akan Fateema, wani irin ihu ta saka Wanda sai da ya tashi hankalin mutanan gurin,ta fadi a wajen ta na wasu abubuwa kamar tababbiya tana wa su surutai.

To fans mu tara gobe book ya kusa karewa idan ku ka yi sanya da comment na ajiye shi sai bayan sallah

HAKURI HASKE NE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

.🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Bissimllahir rahmanir raheem*

*Dedicated to: ATK  PALACE*
               *85-90*

Wani ihu ta ke tana zillo “ni ce na haukata Sherri, na koreta da ciki saboda bana so ta kara haihuwa da kai, ni nai maka asiri na rabaka da danka ka koreshi daga gidan ka na shafe maka shi a kwakwalwarka.
Ni ce! ni ce nan na sa shi a mummunan hali, ni nai masa asiri ya lalace, ni ce na raba shi da mahaifinsa ya tsane shi ya tsani ambatonsa” ta din ga ihu tana tumami.
+
Gaba daya a firgice suke musamman Daddy da komai ya din ga dawo masa tiryan tiryan kamar a mafarki lokaci daya ya saki kara ya zube kasa a sume.
Hanan kuka tasa tana ihu “Momy kin cuceni kin cuci rayuwata kin rabani da yan uwana, mai su kai miki a rayuwa haka da ki kai musu wannan hukuncin? kin gama da ni Momy da wane ido zan kallesu?”
Kuka ta ke mutane sun cika dakin suna kallon ikon Allah wannan abu kamar a mafarki kamar a kiyama tana fadin abun da ta shuka tun a duniya, kafin ka ce wannan dakin ya cika dan kam sai da akai kora a ka rufe kofa.
Kuka ta ke kamar ranta ze fita Fateema kuka ta ke tama rasa me zatai hamdala kawai ta ke a zuciyarta, saboda tasan karshen abun da akai wa mahaifiyarta ne yazo, babban abun da ya sata kuka da taji cewa tana da yaya amma yayi musu nisa sai ta kara fashewa da kuka.
Likitoci ne suka bawa Daddy temakon gaggawa minti talatin ya dawo hayyacinsa, ranar dai yan babban daki na asibitin murtala sun yi kallon ikon Allah sun yi mamakin wannan abu tun safe su ke ganin abun al’ajabi.
Yana farfadowa ba sunan kowa a bakin sa sai Farouk “kana ina dana? kazo gareni ka yafemun, ina kike Sherri naci amarki na cutar da ke mace tagari salaha Allah ka gafarta mun.
Wannan yarinyar dana gani ku nunan ita ko kaffara bazan ba jini na ce, yar gidan Sherri ce dan idan akwai abun da ya bambanta ta da Sherri be wuce bakar fata ta da ta debo tawa ba.”
Kuka Fateema ta ke sosai ta ruko hannun Hanan da ke rusar kuka, ta karasa gadon wata runguma yai mata yana kuka shi ma “kuyi hakuri diyata, ina mahaifiyar ki ta ke na cutar da ita na zalunce ta.”
Toshe masa baki tayi “kayi shiru babana tabbas nasan ba yin kan ka ba ne Allah ne ya tsara haka zata faru bamu da tsumi ko dabara akan haka kayi shiru.”
Ita ko Momy an yi waje da ita an kai ta wani daki an daddaure ta saboda yadda ta ke bige bige tana cije cije duk ta yakushe jikin ta duk wanda ya ganta sai yai mata kuka ya tausayawa rayuwarta.
Anan ya tambayi Fateema labarin mahaifiyarta ta sanar masa komai ya tambaye ta unguwar da suke anan ta sanar masa suna zaune a wani kauye Makole gaban mariri.
STORY CONTINUES BELOW

Hankalinsa yai masifar tashi ya sakko daga gadon ya hannunta ya kamo hannun Hanan suka karasa gaban gadon Halliru “sannu sirikina ka kwantar da hankalin ka insha Allah wahalar ka zata zo karshe ka kwantar da hankalin ka.
Yanzu zamuje police station saboda mu fitar da bawan Allah wanda be ji ba be gani ba muka sa shi a cikin wahala, kai kuma insha Allah a satin nan zamu fita waje a dubaka nagode kwarai da yadda ka karbi yata, nagode da alkhairin ka a gareni”  “ba komai Daddy kubar ni ma anan zan warke” “bana san musu dana” haka kawai ya ce ya kama hannun Hanan da Fateema suka fita.
Gidan sa ya kai su nan da nan ya kira DPO ya ce ya same shi a gidan sa yana zuwa ya kai shi babban parlour din sa ya ce yana so a saki yaran da aka kama, saboda yar sa da kanta ta amsa ita ta kade mutumin a hanya, ganin halin da ya ke ciki ne tayi tunanin ya mutu ta shi ga wannan halin.
Ya fahimta har ze fita sai ya tuna “yauwa yallabai idan bazaka damu ba ina so ka cigita mun yarona” “yaro kuma Alhaji? dama kana da wani da ne bayan Hanan?” “eh ina da shi ya bata shekaru ashirin baya” “to yallabai meye sunan sa da hotonsa? amma kayi sake sosai wallahi shekara a shirin.”
“Gaskiya ban da hotonsa amma dai Umar sunan sa ina kiransa da Farouk” “to fa Alhaji ai Farouk da yawa da dai da hoto shi ne komai zai zo da sauki” “gaskiya babu” “tuna dai Alhaji tuna pls” can ya tuna “na tuna akwai wani da nai masa Switzerland yana nan cikin documents dina.”
Da sauri ya mike ya dakko document din ya binciko sai ga hoton ya mika masa, wata zabura yai duk da wannan yana yaro ne amma tabbas kamaninsa basu sanja ba “Farouk wanda muka rufe a prison?
“Yanzu haka ina wajen sa munje da wata yarinya muna musu interview ka kirani na taho saboda muhimmancin ka, kai maza mu tafi yanzu ka duba Alhaji ka gani ko shi ne sai mu biya ta wajen yaron shi ma.”
Da sauri ya mike ya zari key yana kiran su Hanan su fito da Fateema suka fito Fateema ta ce “inaso naje gida naga Umma ta saboda tun safe na fito bata ganni ba” jikinsa ya kara sanyi dan har ga Allah ya kara mantawa da ita ta yayansa kawai ya ke.
“Kiyi hakuri za muje har ni yanzu wajen yayanki zamu je yanzu mu gan shi” jin haka zuciyarta tai sanyi “to” ta ce kawai suka fito suka shi ga mota suka nufi prison ta gwauron dutse in da Farouk ya ke.
A prison kuwa Farouk kuka ya ke kamar karamin yaro yana rungume da Alaife “tabbas jini ba wasa ba jini ba karya ba shi ya sa ganin farko kuka shi ga raina, ashe yan uwana ne ku gaskiya ba abun da zan ce da Allah sai godiya.
Duk da baki karasa ban labarin ki ba hakan ya tabbatar mun da cewa Mama na ita ce yayar Adda, saboda ita ce Sherri da kike magana kullum maganar ta kanwarta Afsi duk da na rasata itama ance ta mutu” ya kuma fashewa da kuka “ban da kowa a yanzu ban da komai.”
Shi dai lawyer abun ya daure masa kai jin wannan chakawakiya da ake zabgawa a wajen, me suke nufi wasan kwaikwayo zasu yi masa ko me? ga shi dpo ya fita saura shi da gandiroba suna kallon ikon Allah.
“Ki karasa bamu labarin dan muna tsintar abun da nake so mu samu daga labarin naki” taci gaba da magana.
Afsi ta sha kuka haka taci gaba da shan bakar wahala a rayuwarta in da Ramai ke gana mata kalolin azaba kala kala a wannan halin har ta isa shekaru goma sha biyu talla ta ke kusufa kusufa ba dare ba rana.
Hankalin Ramai a kwance babban farin cikin ta yadda ta mallake mijinta sai abun da ta ce a gidan, bashi da iko akan komai da kowa na gidan wannan bakin cikin yasa masa hawan jini me tsanani, ga tashin hankali tun da ya aura wa Alhaji buba Sherri be kara jin duriyar sa ba.
Har ta kai amma dena boyewa gar da gar za’a nuna shi a ce ga wanda ya seda yarinyarsa nan saboda bashi, abun yana damunsa ga Afsi kullum sai tayi kuka na rashin yayarta me share mata hawayen ta ta kasa sabawa, ciwon ya kwantar da shi ga rashin kulawa daga matarsa ga tsananin tashin hankali hakan yasa ya fadi.
STORY CONTINUES BELOW

Wanda sanadiyyar hakan ya ke kwance cikin halin mutuwar barin jiki, watansa bakwai a kwance ba kulawa saboda sam Ramai bata bari Afsi ta kula da shi hake ze kashi ya wuni da shi sai san da ta gama yi mata ayyukan ta zata gyara shi, kuma abinci sai dai taci kanzo dan ma tana wanki da surfe dasu ta ke samu tana ciyar da mahaifinta tana dan sai masa magani.
Duk yadda Ramai taso tai karuwanci Allah bai bata sa’a ba ita ko maza take kawo wa kala-kala, watan sa bakwai yana jinya a wannan halin ya rasu tun daga lokacin rayuwa ta kara juyawa mahaifiyar mu baya,Ramai ta koreta daga gidan tai asirin da ba mai tausaya mata a garin sai da ta kai sai dai ta bi bololi ko kango ta kwana abun da zata ci sai dai idan an zubar ta tsinta taci.
A haka wasu sojoji yan kwantar da tarzoma suka kawo dauki garin su saboda tashin hankalin da ake, anan suka tsince ta da daddare tana gararam ba sun so siyi mata fyade ogansu ya gansu wanda ya kasance mahaifi a garemu a yanzu.
Ya karbe ta su kuma yasa aka hukuntasu anan ta bashi labarin ta da komai na rayuwarta ya tausaya mata inda be kasa a gwiywa ba ya kai ta wajen sarkin garin ya nemi auren ta aka aura masa saboda bata da gata.
Bai zame ko ina da ita ba sai kasar Spain anan ya ajiye ta saboda yana da wasu hatsabiban mata amma ya boye mata, Daddyn mu sunan sa Sarkin Santabul, gaba dayan su sai da jikin su yai shock saboda mamaki.
Eh da gaske nake muku dani da yayata Sherri a Spain aka haife mu can ya ke zuwa ya samu Adda, haihuwarta ta farko ta haifi mace ta roki alfarmar yasa mata sunan yayarta shi ne taci sunan Sherri.
Bayan nan sai ni naci sunan mahaifiyarta Alaife sai Gobinya sunan tsohuwar data shayar da ita sai Yusuf autan mu, bayan an haife mu sai suka dawo Nigeria a nan aka haifi Gobinya da Yusuf makaranta muke me tsada ta yayan manya ita kan ta Adda degree gareta.
Bayan haihuwar Yusuf da shekara biyu sai ga wasu mata sun zo gidan mu lokacin Daddy na nan duk muna gida a parlour, a nan suka samemu suka lakadawa Adda duka muma suka jibge mu san ransu, sannan suka sa Daddy yai wa Adda saki uku ko tsinke basu bari ba suka kora mu.
Haka muka fito dan kunnen kunen Adda aka siyar dana kunnen mu muka kama gidan haya muka sai kayan abinci, to zama haka hakan yasa watan mu uku komai ya fara karewa dama ba wadatar suttura haka Adda ta din ga buga buga gidan masu kudi tana aikatau da ta ci damu, kuka ta kuma fashewa da shi.
Sai da muka shekara a wannan halin sai ta yanke Shawarar gwara mu koma kasar ta, haka muka koma Niger amma sai da mukai dana sanin zuwan mu saboda gidan su Adda ya zama matattarar karuwai ya zama gidan gala.
Wulakanci kala-kala haka muka sha shi wannan bakin jinin na Adda sai da ya shafe mu, da dutsuna aka koro mu daga garin duk an farfashe mana jiki mace a yawon dandi ta samo mu, haka muka kuma dawowa Nigeria muka din ga gara ramba da barace barace har Allah ya hadamu da Yaya Farouk.”
Kuka ta ke su kansu duk kwalla suke saboda tausaya musu barrister ne ya ce “bayan tafiyarku mahaifinku be nemeku ba?”
“Sam ko da wasa mun sha ganin motocinsa na wucewa ana jiniya a gefen titi sai dai mu kalla mu koma gefe muyi kuka.”
“Bakwaya tunanin akwai sa hannun wayannan matan na Alhaji a batan yan uwanki da rasuwar mahaifiyar ki?”
“Eh nima yanzu ina zargin haka amma ban da hujja dan tun daga ranar ban kara ganin su ba.”
“To shi ke nan Alaife kiyi hakuri ki dena kuka tun da har Farouk ya tabbatar da shi dan uwanki ne insha Allah gaskiya za tai halinta.”
Suna wannan maganar Daddy suka shi go da hanzari yana ina Farouk din take?”
Kan Farouk yai yana “dana kayi hakuri ka yafemun” ya fashe da kuka Farouk ma ya sa kuka “haba Daddy dan na daukar ma kudi ka koreni daga gidan ka saboda mahaifiyata bata nan” ya kuma rushewa da kuka.
“Ina da karancin shekaru shekara goma sha biyu daba dan Oga na ba duk da cutar da rayuwata yai amma ya fika.”
“Ya isa Farouk kayi hakuri ka saurari mahaifinka” cewar dpo.
“Shi ke nan na yafe masa amma ya sa rayuwata a wani hali ina ganinsa kuma ban mantawa da shi ba amma yadda Momy tasa ya Kore ni yasa bana sha’awar rabar su na yafe masa ko dan ganin jinin Mama ta da nai.”
Da sauri ya tambaye shi ya nuna masa Alaife “tabbas wannan Afsi ce ko kaffara bazan ba” nan ya bashi labarin yadda ya aura mahaifiyarsa da yadda Momy ta din ga gana mata azaba saboda ita bata haihu ba har asirin da tai mata ya nuna masa kanwarsa.
Yayi farin ciki ya rungume kanwarsa suka rungume Alaife suna addu’ar bayyanar ragowar Hanan kuka ta ke da kyar tai shuru.
Nan ya bashi labarin irin yadda suke safarar yara da sawa yara kanana cocaine a ciki ana shi go dasu Nigeria da ita.
Ya shi ga tashin hankali mara misali daidai lokacin time din da aka basu na ganawa da shi ya cika, yana kuka suna kuka yana komai haka suka rabu da mahaifinsa  da kannensa sun masa alkawarin kawo masa mahaifiyarsa su gana dan wajen ta sukai yanzu.
Suka ja mota sukai wa Kurmawa tsinke su Bawan Allah na zaune da yan dakin su yana koya musu karatu dan tun daga ranar suka nutsu suka koma ga Allah suma tun da ya basu wannan labarin nasa.
Suna zaune aka ce ya fito yayi free nan fa aka fara koke koke musamman kawunsa nan suka yo zuga suka rako shi har bakin gate suna tsaye su kuma yana ta sallama da jama’a sunata kiran sa da Ustaz Bawan Allah sunata hawaye.
Anan kawun sa ya bude murya “na roke ku sada shi da iyayensa dan nasan baze iya kai kansa garesu ba, dan gidan General Suleiman ne Sarkin Santabul” caraf a kunnen Alaife wata muguwar juyowa tai ta zuba masa ido tabbas ba inda ya bar babanta wani ihu ta saka ta tunkaro shi da gudu bayan ya fito tana “yayanaa.”

Wash Allah wallahi nagaji typing akwai wahala amma kayi ka gama comment da vote ya gagara, gaskiya idan bansamu yadda nake so ba zan ajiye shi duk da yazo gangara bayan sallah na karasa ni ce taku a kullum a koda yaushe.

          *Feedyn bash*

HAKURI HASKE NE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

.🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Bissimllahir rahmanir raheem*
*Second to the last page*
                      *90-95*

Hajara na fita daga asibitin bata zame ko ina ba sai gidan Hajiya kuka ta ke tana tumami “Hajiya na cuci kai na mijina ya sake ni a gaban idona ya auri wata.”
Hhhhhhh! “haba Hajara meze dameki dan wannan nakasashshen yai aure ai ina ganin ba abun damuwa bane, ke dai ba kin tsinke igiyar auren ki ba na tabbatar anan gaba duk wannan daular da na ke ciki sai kin fini shi garta.”
+
Hajiya ta din ga yiwa Hajara famfo da hau kai ta zauna ta dauketa a motar ta sukaje gidan ta dakko duk wani abu da ta ke bukata nata ta koma gidan Hajiya da zama.
Hajara duniya sabuwa ba ruwanta da wani damuwa barikinta ta ke bugawa san ranta yadda ranta yaga dama watan ta hudu a gidan Hajiya masoya sai kara bulbulowa suke.
A lokacin Alhaji warbeshi ya bijiro mata da maganar aure kwadayin abun duniya da irin daular da ya ke kashe mata yasa ta yarda ta aure shi.
Zubaida ko bakin ciki kamar zatai hauka wai yau Hajara ce a cikin wannan daular irin ta Alhaji warbeshi ta sha alwashin ganin bayan Hajara sai ta malllake warbeshi ya zama nata.
Ana yin auren be yarda sun tare ba ya kai ta asibiti ya ce baya bukatar mahaifarta a cire gaba daya badan ranta yanaso ba ta danne saboda tsananin soyayyar  da ta kewa kudin  dan ba’a ce shi ba.
Sun tare a Kaduna unguwar Sarki watan ta uku suna cin amarci sosai ya ke jin dadin gamsuwa da ita tana wadatar da shi sai dai mai kawai jini ya balle mata ta rasa ta ina yake zuwa sun yi yawon asibiti amma an rasa gane meke damunta.
A wannan halin Alhaji warbeshi dama ba fasa barikinsa yai ba dan siyasa ne babban ma’aikaci to meze dame shi ya tattara ta ya watsar da lamarinta ya ci gaba da sabgarsa sai ga shi sun din ke da Zubaida.
Sosai ta mallake shi ta makalkale shi baya ji baya gani dama uwar gidansa Hajiya Talatu da ita da babu daya ya daukesu mace me mutunci da karamci ba ruwanta da shi ga abun da be shafe ta ba.
Daidai da abun da zasuci ita da yayanta ita ke nema musu gidan da suke ciki idan aka baki kur’ani dafawa zaki kice ba iyalan Alhaji warbeshi bane saboda wani kucakin gida ne suke zaune a unguwar rimi.
Ginin bilo ne amma dakuna hudu ne kwata kwata a dakin gidan, daya kuma na shi ne ya ke zaune ainihin gidan da ya ke da shi ne tun kafin yai arziki anan su ke zaune, yaransa takwas biyu mata shi da maza kuma dukkan su ba manya ba ne ba wanda ya aurar.
STORY CONTINUES BELOW

Matan duk sun isa aure amma mugunta da zalunci irin nasa ya sa ya kasa yi musu saboda bakin cikin kar yai musu kayan dak,i ya ce karatu zasi amma shiru har yanzu sai yai wata shi da beje gidan ba saboda karma ya basu sisin sa, suna kallon yadda ake wucewa da maka makan motocin sa ana masa jiniya amma ba wanda ya taba lura da halin da iyalansa ke ciki.
Babban abun bakin cikin dukansu ba wanda ya ke da takaimammar madafa haka suke zube manyan matan ne ke sana’ar kunshi da kitso ragowar duk maza ne da suke bukatar temako
Haka Hajara ta din ga hakuri tana lallabawa ranar da ya kawo Zubaida gidan gadon barcin ta, a ranar tai masa hauka ranar ya nada mata duka ya tattara ta ya kai shi gidan sa ainihin inda iyalansa su ke.
Yana shi ga ya ajiye ta a tsakar gida “Talatu! Talatu! kina ina?” gabanta na dukan uku uku cikin tashin hankali ta fito “gani Alhaji.”
“Yauwa ga mata ta nan amarya ta a bata daki ta zauna ta dawo cikin ku saboda naga samun ido ta ke da gulma, saboda haka matsayinku daya yanzu ta dawo ta zauna daku idan ta samu lafiya na din ga maleji tun da tana da dadi kuma ita bata haihuwa.”
Yaran duk suka fito suka jere suka zuba masa ido rabon da sugan shi wata takwas kenan sai yau da ta shi ta kawo shi, a hankali suka din ga gaishe shi ya hade rai “lafiya” ya juya ya shi ga dakinsa ya debo wasu takardu ya fito.
“To Talatu gata nan sai ki gaya mata dokokina bana san yawo bama a fita a gidana sam saboda haka sai ta kiyaye” ya juya ya fara tafiya “to Alhaji ka manta ne daki hudu ne kacal a gidan nan daya nawa daya na yara maza daya na mata daya naka a ina zata zauna?”
“Ke Talatu ni kike gayawa yayanki ne a daki saboda raini to su koma daki guda su gwamutsa kaza uwar yaya” ya fada ya juya ya bar gidan.
Tsananin mamaki da tashin hankali ya hana Hajara magana sam wani kuka ta ke me taba rai, “mtswww!” babbar me suna Ilham taja tsaki “shegen kwadayi irin naku ai ga shi nan haka zeta wulakanta ku a banza gwara ma ke auren ki yai ba lalataki ya gama ba ya watsar.”
Tas kake ji Talatu ta wanka mata mari “dama baki da hankali haka Ilham i nai miki kallon me hankali wadda ko bayan raina zaki kula da tarbiyyar kannen ki, ashe ba haka bane mahaifinki kike jifa da wannan mummunar maganar da matarsa, a matsayin Uwa ta ke a wajenki tsuguna ki bata hakuri.”
Jikinta yai sanyi ta tsuguna “kiyi hakuri dan Allah” ta fada tana doka nata harara “ba komai ya wuce” ta fada tana shekar kuka tashin hankali ta gama shigarsa a wannan gidan za tai rayuwa bayan ta baro daula, ba wanda ya fado mata arai sai Halliru wani kuka ne ya subuce mata tabbas hakkin sa ke bibiyar ta.
Aka bata dakin yaran mata ta share ta ba ta tabarma dan itama dakin nata wata yololuwar katifa ce tun ta aure ta haka Hajara ta lallaba ta kwanta, tabbas ko gidan Halliru da ta ke rainawa yafi wannan dakin daraja da komai kwadayi ya kai ta ya baro ta kuma rushewa da kuka tana tunanin makomar rayuwarta.
Bayan kwana uku Talatu tana bawa Hajara abinci so uku a rana wulakanci kam tana shan sa idan ba Talatu ce a tsakar gida ba bata iya fita saboda yadda suka gallaza mata ruwa ma da kyar ta ke hadiya.
Talatu ce ta shi ga dakin Hajara tai mata sallama ta amsa “dama Hajara magana nazo miyi, magana ta gaskiya sai dai ki mike ki nema kema saboda gaskiya bazan iya ci da ke ba, wahala tai mun yawa daka na ke da surfe sai yarana yammata da suke kitso da kunshi.
To kinga yadda rayuwar gidan ta ke a matsayinki na bakuwa nai miki abun da manzon Allah ya umarci kaiwa bakonka na karrama ki saboda haka sai ki fito kema ki nemi sana’a dan ci da kan ki.”
Kuka Hajara ta fashe da shi musamman da ta ga tun da tazo gidan yadda Talatu ke wahala tun da ta ke a duniya bata taba ganin wannan irin rayuwa ba, kamar Alhaji a ce iyalansa na cikin irin wannan rayuwar ga shi ko wayarta be bari ta dakko ba.
STORY CONTINUES BELOW

Tun da ta ke a gidan Halliru bata taba nemawa kanta abinci ba, duk babunsa ze san yadda ze yi ya ci da ita amma yau Allah ya kawota gidan attajiri kamar Alhaji warbeshi amma ita zata nemawa kanta abinci.
“Shi ke nan Anty nagode da kulawarki a gareni Allah ya biyaki, gaskiya samun mace me karamci da yakana kamar kk akwai wahala, zan din ga irin sana’ar da kike sai mu rufa wa kai asiri.” Tai murmushi “zaki iya kuwa?” “zan iya Anty insha Allah” “to shi ke nan ba matsala Allah ya sa ki fara a sa’a” tai mata sallama ta koma tsakar gida ta barta da sake sake a ranta.
Ranar da ta fara surfe kwana tai ba tai bacci ba saboda ciwon jiki da hannu, kuka haka ta din ga yi gaba daya tayi nadama ta koma ga Allah, tun ranar da ta zo ta nemi wannan jinin ta rasa abun da ya dada daga mata hankali ke nan.
Washe gari dabara tazo mata ta tuna ta iya kitso da lalle irin na yan Maiduguri, ta sanarwa Talatu ta ce ba matsala amma yaran fafur suka ki suka ce gasa ta ke dasu musamman Ilham, sai da Talatu tai mata jan ido sannan suka yarda sun sha mamakin yadda ta ke kitso da kunshi sosai.
Kuma Hajara tayi nadama ta domin Allah amma babban tashin hankalin ta rashin mahaifarta daya cuce ta yasa aka cire mata, saboda tana masifar san yara a yanzu saboda yadda su Ilham ke taimakawa mahaifiyarsu abun na burgeta.
A yau Alhaji yai wa gidan zuwan bazata ya kira Hajara dakin sa gaba daya ta tsane shi ta tsani duk wani abu da ze hadasu, babban abun da ta ke bukata shi ne Allah ya yafemata ta nemi yafiyar tsohon mijinta dan ta koma ga Allah, ya yanzu ta tsani Zubaida tsana me yawa dan ita ta sata a cikin wannan halin tayi nadamar sanin ta a rayuwa, duk yadda Halliru yaso nuna mata illar mu’amala da iya sam bata gano ba sai yanzu.
Ba dan ranta yaso ba ta tafi dakin saboda ta samo musu mafita ita da Talatu, sai mai tana shiga dakin sai jini kuma ya shi go ya tarar da ita tana sallah ransa yai masifar baci cikin fushi ya rufeta da duka, yai mata lilis san ransa ya tsallaketa ya fice ko kallon inda Talatu ta ke beba bare yaransa ya sa kai ya fice.
Da sauri Talatu ta shi ga taga jini malala amma me tana shi ga ya tsaya cak abun da ya daga mata hankali ke nan ta kamota suka fito, sai ga shi ya aiko a rufe dakin ya bada umarnin a gyara dakin Talatu ce ta gyara ta koma wajen Hajara ta tambaye ta komai ke faruwa haka.
Bata boye mata komai ba ta sanar mata halin da ta ke tsintar kanta idan tana tare da Alhaji, tai salati ta sanar da ubangiji ta sanar da ita cewa asiri ne akwai wan babanta yana bada magani insha Allah zata kai ta kwana uku tsakani suka rankaya su kai gidansa.

*******************

Tashin hankali Kankana tana cikin sa minti goma mahaifiyarta bata kara ba ta ce ga garunku nan kuka suka din ga yi ita da kannenta haka aka basu gawar bayan cike-cike suka tafi da ita gida was he gari akai mata sallah aka kaita.
Bayan an kai ta Oga ya din ga kiranta kanwarta ce ta daga ta sheda masa mahaifiyarsu ce ta rasu suna gida ana zaman makoki Oga yaji ba dadi dan yana san Kankana ya yarda da ita.
Yaje mata gaisuwa ji tai ta tsane shi saboda alkawarin da taiwan mahaifiyarta na rabuwa da shi ta sanar da shi sai bayan arba’in zata koma ya kula da yarinyar nan Sherri.
Yaji ba dadi ya koma yasa aka dinga bawa Sherri kulawa ta musamman sati biyu a tsakani bizar su Gobinya da Yusuf ta fito zuwa America, amma ban da Sherri bata ma san sun tafi ba saboda basa ganin juna sati biyu zasi su dawo.
Sati daya a tsakani Kankana ta dawo ta dawo da shirin ganin bayan Oga da tona masa asiri wa duniya dan ta hada hannu da state cid, amma me sai ta samu labarin an fitar da yara dayawa America wasu India amma rana daya zasu dawo.
Ta samu Sherri ta kwantar mata da hankali ta nemi yafiyar ta bisa hanyar da taso dorata hankalinta ya ta shi tayi kuka da taji anfitar dasu Yusuf waje tunanin ta ko hannunsa ya warke bata sani ba, a hankali ta yarda da Kankana ta dauke ta matsayin yayarta musamman da ya zama ba wanda ta ke gani sai ita.
Yau ta kama su Gobinya zasu dawo an musu operation an sassaka musu cocaine a ciki an din ke, ba’a kwance dinkin sai sunzo wanda inda karar kwana yaran su rasa rayuwarsu.
Kankana ta sanarwa da yan sanda duk wasu abubuwa da suke faruwa aiki ta ke tukuru duk wasu hirar su ta makala camera a cikin gashin ta tana nadar maganganunsu tana turawa Head quarter, sun fito sun bar gidan sai sannan Police suka samu damar ganinsu suka tabbatar da cewa a kwai gida a wajen.
Tabbas Farouk ba karya ya ke ba ikon Allah suka din ga binsu cikin shigar basaja har suka isa airport din Malam Aminu Kano daidai lokacin da suka shi ga daidai lokacin da jirgi ya sauka.

*******************

Lokacin da ta rungume Bawan Allah abun ya bashi mamaki ya tambayeta kota san shi nan Daddy ya ce suyi hakuri su tafi sayi maganar saboda mutane sun zubo musu ido da sauri suka shi ga mota tana jikinsa tana ta kuka.
Makole su kai wa tsinke lokacin magariba tayi kuka Daddy ya fashe da shi ganin inda iyalansa suke rayuwa wanda ko karen gidan sa yafi karfin yai rayuwa a wajen, suka kutsa kansu cikin gidan a takure a gefe suka hangota jikinta na ta rawa duk ta fita hayyacinta zazzabi ta ke idanuwanta har wani kafewa suke.
Da hanzari su kai kanta Daddy ya cincibota ya sata a bayan motar suka bi bayansa suka shi ga motar ya bata wuta sai private hospital, suna zuwa aka karbeta aka fara bata temakon gaggawa Daddy kawai zagaye ya ke yana zufa ashe ze kara ganinta? zasu kara haduwa a duniya? tambayar da yake taiwa kansa ke nan kamar a mafarki.
An shawo kanta zazzabi ne me zafi ya sauka tana hutawa, anan suka zauna a dakin Alaife ta kara basu labarinta, Daddy kuka ya ke da tausayin su kowa kuka ya ke, ta sheda musu Daddy din ta ya nuna mata hoton Bawan Allah ya ce ya bata ne ba’a ganshi ba.
Anan ya basu labarin wahalar da ya sha ta rayuwa hannun iyayensa da ya ta shi malamai ne daga mijin har matar kuma sun koma ga Allah basu haihu ba sai shi kadai, a haka suka zauna har ta fara motsawa lokacin sha biyu da rabi na dare amma idon su kir suna hira har yar rige rigen fita su ke kiran doctor.

*******************
Momy da Antyn yara ne durkushe a gaban bokansu inda ya juya baya har yanzu yaki juyowa ya kallesu sai da suka din ga wasu sambatu suna kirari sannan ya juyo, ya farai musu turanci saboda basa jin indiyanci ya fara magana kamar haka.
_”Ku gafallalu tsinannu inaso kusani cewa karshen ku ya kusa zuwa, mun ce kar kowa yaga sanda za a debo kayan aikin amma kunyi sake yarta ta gani bazata mutu yanzu ba, saboda aiki ya lalace sakamakon addu’o’in da ake mata aljanin da ke jikinta baya samun damar rabarta, sihirin ne kawai ke tasiri a cikin ta, abu na biyu idan har kuka bari mahaukaciyar nan tai ciki a ranar data haihu a ranar daya a cikin ku zata haukace daya zata mutu, a ranar dukkan yaransa zasu bayyana agareshi saboda haka ina so ku sani lokaci ya kusa kure muku asirin ku na gab da tonuwa, damin wanda ya ke temaka musu da addu’a ya dawo kuma sun kara samun wasu da zasu temaka musu wajen cetonsu.”_
Jiki na rawa ta suke tambayarsa meye mafita? ya sheke da dariya “mafita guda daya ce duk yadda za’ai kar tai ciki bare ta haihu, sannan kuma kun nemi duniya kun samu saboda haka kowaccen ku zata bamu jinin dan ta guda daya.”
Wani ihu Momy ta saki tana tumami yarinyarta daya kacal a duniya ko sun kai dubu yadda ta ke da san Yaya bazata iya ba “bazan iya ba boka ko jinin mutum nawa ne zan bayar banda na yata.”
Wata tsawa ya daka mata “ba agun wasa kike ba saboda haka abun da nakeso da ke ki sani ba fashi, kun nemi duniya kun samu kuma munyi da wajewa cewa idan bukata ta biya komai muka bukata zaku bamu” Antyn yara ko duk ta gama fita hayyacinta saboda yaranta uku duk mata ba wadda bata kauna a cikin su musamman autarta, “ku ta shi ku ban waje shawara ta gama gareku”
Da gudu suka mike suka fito suna kuka direct airport suka wuce suka yanki ticket zuwa Nigeria.

HAKURI HASKE NE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

.🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Bissimllahir rahmanir raheem*

*Alhamdulillah dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah! yadda ya bani ikon kammala wannan book din yadda na fara alhamdulillah! na gama lafiya banci karo da kalubale ba ko wani abu daya sabawa shari’a sai yabo da na ke samu daga mutane da dama, gaskiya ba abun da zan ce da Allah sai godiya yau ga shi na kawo karshen wannan book din me suna Hakuri Haske Ne! duk wanda ya ce yayi hakuri be ci riba ba to tabbas wannan hakurin kadan yayi, Allah ya bamu hakuri ya kuma bamu ribar hakurin.*

+
* Last page*

                  *95-100*

Aminullah ne ke tuka motar Yasmeen na gefensa gaban wani gida yai parking wanda almajirai sun cika kofar gidan suna ta karatu wani tsoho ne tukuf zaune a gaban su suka sakko suka karasa gabansa.
Bayan sun gaisa Malam ya’u yai mamaki da yaga Aminullah gani daya ya gane shi nan ya fara yi masa fada, ya din ga bashi hakuri suka zauna suka din ga yi masa bayani dalla-dalla ya dinga jin jina kai.
“Tabbas wannan aikin sihiri ne ina zuwa” ya dakko musu turare ya ce su je su yi shi a cikin gidan gaba daya duk wani sihiri ko wani aljani da ke gidan sai sun kone kurmus, ya basu wani hayaki ya ce a din ga yiwa mahaifiyarta ba aljanin da ze kuma rabarta.
Anan Malam ya ke sanar masa kwanaki da dadewa wani yazo nemansa amma be kara zuwa ba, yai ta kuka saboda rashin ganin danginsa amma ba komai yasan hakuri haske ne ga shi silar hakurin da yai ga abun da ya same shi na cigaba, su kai wa Malam sallama ya ce su dawo karbar mata rubutu bayan kwana biyu.
Haka suka samu damar shi ga gidan suka bawa Inna turaren sun tarar basa nan su Momy, anan suka samu dama likitar da kyar ta kai su suka ga Umman ta kuma alhamdulillah tana samun kulawa sosai, anan suka samu suka shaka mata turaren dama na shaka ne ta din ga attishawa tana wani abu amma cikin ikon Allah sai bacci.
Ganin haka Doctor ta karba ta ce zata din ga yi mata, suka rabu a haka suka koma gidan Aminullah dan ya samo mata wadda zata din ga taya ta zama dan ya ce ta bar zaman gidan zaman ukuba, lokacin hutun ta yayi tana daga kwance komai ta keso yi mata ake har tayi wani ja ya maida ta makaranta s.s 2 suka kai ta saboda kokarinta.

*******************

Sherri ta dawo hayyacinta sai dai jikinta ba kwari ga lalurai saboda ta dade cikin halin hauka ko Fateema bata sani ba amma sarai ta gane mijinta.
Ya zauna yai mata bayani duk abun da ya faru, ta fashe da kuka nan ya nuna mata Alaife ya sanar da ita ya ce ga kanwarta Afsi, wata zabura tai ta mike ta rungumeta ta fashe da kuka me tsuma rai wanda duk dakin ba wanda beyi kuka ba.
STORY CONTINUES BELOW

Bata kara shi ga tashin hankali ba sai da ta samu labarin mutuwar Afsi sumewa tai a wajen, sai da tai sati biyu a asibiti sannan aka sallamesu gidan sa suka nufa suka huta a ranar suka dunguma zuwa asibitin murtala wajen Halliru.
Duk da kullum suna zuwa wajensa an sanja masa daki an maida shi bangaren sarakai kullum Bawan Allah ke kwana da shi abun nasu alhamdulillah!.
Ita ko Momy an kai ta dawanau saboda abun nata hauka ta ke tuburan duk kayan da aka sa mata sai ta yaga su taci kashinta da din ga yagar jikinta ta zama abun tausayi.
Kwana uku da fitowar su daga asibiti suka daga zuwa Spain gaba dayansu Daddy ya rabawa Malamai kudi suna ta addu’a Allah ya kawo karshen lamarin gidan Sarkin Santanbul kamar yadda ya kawo karshen nasa lamarin.
Sherri za’ai mata wankin hakora dana kafa za’ai mata wankin inji a kara duba lafiyarta general check off za ai mata, shi kuma Halliru za ai masa surgery na spinal code din sa idan aikin yai kyau insha Allah zasu wuce suyi umara dukansu sannan su dawo gida.
Amma ban da Daddy shi ze barsu ya dawo gida Nigeria saboda dan sa Farouk da ke prison, so ya ke a gama shari’ar gaba daya sai su tafi dukansu yana kai su kwana uku yai ya juyo Nigeria.

*******************
Suna zaune aka din ga fito da yaran daga jirgi abun mamaki sai ga Yusuf da Gobinya sun fito suma, yara takwas ne suka fara dawowa cike da murna suka karasa wajensu suna zuwa aka ritsa su da bindigu har Kankana.
Ihu Oga ya ke yana zage-zage yafi karfin tozarci ya zaro waya aka kwace, ya fara zage-zage da zaginsu cikin kankanin lokaci suka tara masa gajiya suka sauya masa kamanni suka watsa su a mota sukai SAS da su.
An kai su an musu tambayoyi yaki amsawa duk wasu shedu amma yaki amsawa, sai da sukai masa raga-raga suka balla shi baras, yaran tuni anyi asibiti dasu kuka haka mutane keyi saboda tsananin tashin hankali, wai wannan mummunan labarin a kasar su a kasar ta suma garinsu labarin da suke ji a wasu kasashen.
Haka akai wa yaran wata tearter din aka ciro cocaine din inda yara biyu suka rasa rayuwarsu a cikin takwas ga cocaine nan an firfito dasu aka kai su SAS.
Yan sanda sun dibi manyan Malamai saboda su ko sunje basa ganin gidan sai da aka karya asirin da akai wa gidan suka shi ga, suka tattare kowa Sherri kuka ta ke tana godiya ga Allah da ya kubutar da ita tana kukan neman kannenta.
Sati daya aka gama binkice da shedu aka shi ga Kotu inda aka gano da sa hannun manyan kasa tare suke harkallar su, saboda jibgar da yasha da yadda suke ballashi su dora su kara ballawa suma ya ke saboda azaba, ashe suka daure masa gindi a lokacin kowanne yaro aka nemi iyayensa aka damka shi a hannunsu.
Sherri ko Daddy ne ya karbesu yana kuka na tausayin rayuwarsu musamman Yusuf da hannunsa ya ballake a haka ya warke saboda rashin kulawa.
An zauna a kotu duk shedu daga bakin mutane da yaransa ya tabbata jiga jigai ansamu mutum goma sha biyar ciki har da wanda suka kashe Adda da ke Sherri ta ganesu, an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi ihu Oga ya ke yana tsinewa Kankana da Farouk ya sha alwashin ganin bayan su idan ya fito a fadarsa.
Farouk anyi binkice akansa shi aikinsa nemo yammata ko iyayen da suka yarda  su bada yayansu a zuwan aikatau, duk da haka Kotu bata barshi ba duk da ya tuba sai da aka yanka masa tara me yawa da zaman gidan kaso na shekaru biyu, an biya tarar nan ta ke aka fito dasu zuwa prison.
Kun san lamarin kasar waka sani waya sanka suna fita za’a tafi dasu a hanya aka sauke shi, Daddy ya dauke shi suka wuce gida kwana uku tsakani suka samu visa suka wuce Spain wajen su Umman sa dan su gana dan ya tuba tuba na gaskiya dama sihiri ke dawainiya da shi.
STORY CONTINUES BELOW

An harbe su Oga sun girbi abun da suka shuka tun a duniya ya dandani zafin mutuwar da ya ke dandanawa jama’a.

Shi ke nan karshen Oga da jama’arsa duk abun da ya tara aka din ga rabawa iyayen yaran da suka zalunta, yaran da suka tura waje karuwanci da ke akwai takardu da komai aka dinga turawa jakadan kasar da suke aka din ga dawowa dasu, kalilan ne ba’a samesu ba dan wasu sun ma mutu tun da ba’a bari a kwashe duka, wasu kuma sun yi nisa bazama a gansu ba, karshen Oga yazo wanda beyi karshe me kyau ba.
Kankana ta shi ga hankalin ta ta tuba ta koma ga Allah, anan commissioner of police ya nemi auren ta ya kuma kwashe kannenta suka zauna a gidansa dama matarsa ta rasu ta shiryu tana taka tsantsan da kannenta da yaran mijinta.

*******************

Aminullah ne da Yasmeen suke tafe zasu isa wajen Malam suka tarar yana da baki, Hajara ce da Talatu a gaban sa Hajara tai masa bayanin komai tanayi tana kuka.
Ya tausaya mata ya bata addu’o’i ya bata rubutu da turare ya shaida mata insha Allah komai zai warware sihiri ne akai mata, shi ma mijin nasu su kara hakuri tun da ya san halinsa ya ce “ku kara hakuri Talatu.
Na sanki da hakuri ki kara akan nada, tabbas hakuri haske ne, zaku ci ribarsa halinsa ne a haka idan kuka dage da gayawa Allah sai Allah ya shirya shi komai ya wuce kamar ba’ai ba.
Ke kuma kamar yadda kika fada harda hakkin tsohon mijinki yadda kika din ga gallaza masa, kije ki roki gafararsa akan abun da ki kai masa sai ki samu saukin komai naki” tana kuka suka shi go kirjinta ne yai wani mugun bugawa.
Tabbas wannan yayanta ne Aminu ko kaffara baza tai ba, “Aminu!” ta furta da karfi wani kallo ya bita da shi na mamaki wace ce wannan kuma? “Aminu wallahi kai ne kai ne jini ai ba karya bane kamar ka kamar mahaifinmu.”
Tasa kuka ganin haka Malam ya ce su nutsu su zauna, bayan sun zauna ya ce “Aminu tabbas wannan jinin ka ce daga kallo daya ta kira sunanka, baiwar Allah ko zaki gaya mana asalinki?”
“Asalina Yar Maiduguri ce kauyen Goza a nan muke, yayana ne wannan Aminu wanda nake bi an taho dasu karatu ne, akwai wanda ya ke kawosu a hanyar shi ta komawa yai hatsari anyi neman duniya bamu same shi ba har muka hakura.”
Wata zabura Malam yai “meye sunan sa?” “Malam Dalha” Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allah babban Sarki! tabbas wannan shi ne Aminullah dan uwanki, Aminullah ga yar uwark.” Habawa tuni ya rushe da kuka “duk da kananun shekaruna bana manta kanwata Hajara abokiyar wasana da Baffana da Inna ta.
Suna ina? na manta garinmu da komai nawa shi ya sa, banda wayon da zan rike kauyen mu shekarata bakwai nazo nan, dama Goza garin mune ina iyayenmu?” ta rushe da kuka “duk sun rasu tun kafin yakin boko haram Baffa ya rasu saboda rasaka, daga baya Inna ta bishi” nan ta bashi labari tun daga auren da tai da komai ya tausaya mata.
Ya kuma nuna mata kuskurensa ya nuna mata Yasmeen ya ce iyayenta suka rike shi ita kuma zai aura, kunya ce ta kamata ta fice Malam yai murmushi “ka bata kunya” nan Malam ya basu nasu rubutun ya sallamesu suka fito.
Yana taiwa Talatu godiya yadda ta rike kanwarsa ya ce su shi ga ya kai su gida, ya fara zuwa supermarket ya siya musu kayan abinci dana shayi siyayya yai musu kamar hauka aka loda a mota, yaja ya kai su gida har sun saba da Yasmeen hira suke sosai abun su.
Ya kai su har kofar  gida yara suka din ga shigar da kayan cikin gida yai mata alkawarin binciko labarin Halliru dan ya taimaka masa, musamman yadda ya rike ta itama ta nemi yafiyarsa ya ce zeje asibitin ya duba su kai sallama suka shi ga gida.
Ya kai wa Doctor rubutun da turaren ta ke shaida musu ciki ne fa da Umman nasu, habawa farin ciki kamar sa zuba ruwa a kasa su sha musamman Hanan wani tsalle tai ta shi ga dakin tana kwance ba um ba umum sai dai kallo Daddy ne a gaban ta kamar zai lashe ta.
STORY CONTINUES BELOW

Su Momy da Antyn yara sun dawo a haukace musamman Momy maganar jinin yaransu yasa suka shagala da batun cikin Hajiya Haleema.

*******************

Su Daddy sun isa anan aka din ga kula da Yusuf da Gobinya, anwa Halliru surgery watan sa shida ya warke sarai yaran ma duk sun warke hankalinsu ya kwanta.
Tabbas hakuri haske ne gashi sun gani kullum Adda abun da ta ke gaya musu ke nan, hakuri haske ne gashi sun ga ribarsa tun ba’aje ko ina ba, a wannan zaman Fateema ta kara course na 6 month ta kara gogewa ta samu result me kyau.
Hanan soyayya ce me karfi ta kullu tsakaninta da Bawan Allah haka bangaren Farouk da Sherri duk da karancin shekarun ta, a yau suka bar Spain suka je Saudi watan su biyu suka koma gida Nigeria.
Hanan kullum ta tuna Momy sai tayi kukan tausaya mata ta roki Allah ya yafe mata ya sassauta mata, ta nema mata yafiyar Umma kuma ta yafe mata duniya da lahira ta kuma yi alkawarin zasu ziyarceta idan sun koma.
Dan yanzu haka Umma na da karamin ciki na wata uku wanda duk basu sani ba Fateema ce kawai ta gane ta tsurkun ta musu suke ta murna a junansu.
Zama ake na jin dadi duk wanda ka kalla a wannan ahalin kasan cikin farin ciki su ke, suna zaune wayar Daddy tai kara ya daga suka gaisa ya ce “muna tare ma dawowar mu ke nan daga Saudi, to ba matsala kafin magriba dai, zuwa bayan magriba ba zaka sameni ba dan akwai inda zamu.”
Aminullah ne ya je asibiti da yai binkice aka bashi number din Daddy aka ce shi ya dauke shi daga asibitin shi ne ya kira shi, ya shaida masa suna gida ya je ya dakko Hajara har da Talatu dan ta zame mata Yaya yanzu suka nufi gidan Daddy.
Suna parlour dukansu ya kira shi ya ce sun iso ya aika aka shi go dasu dukkansu, suna zaune ana ta hira ya kori matan mazan ne kawai a zaune, bayan sun shi go an gaisa da kyar Hajara ta gane shi kuka ta fasa ta nemi yafiyarsa ya yafe mata.
Ba’a tsaya tashin tashina ba tun da suka shi go ya ke kallon Bawan Allah, ya ce “wallahi Alhaji kallon sani nake wa wancen yadda kasan banana” yai dariya “waye baban naka?” “Sarkin Santanbul.”
“Alhamdulillah! tabbas dan uwanka ne yanzu haka gidan ku zamu ai” da murna ya mike “Mohd kai ne? alhamdulillah Allah! ina zan sa kai na da wannan farin cikin” suka zauna ya fara basu labarin su da dangantakarsu komai ya warware.
Mohd na kuka ya sanar masa haduwarsu da wan mahaifiyarsa a kotu, ya gaya masa komai shi ma sukai ta kuka aka kira su Sherri ya kallesu tabbas nasan su amma tun suna kana na babansu baya boyen komai na rayuwarsa.
Nan sukai sallar magriba suka fito suka fita a motoci suka nufi gidan Sarkin Santanbul domin warware wannan kullin.

*******************

Sai da suka nutsu suka tuna dokar boka suka bazama nemanta amma ba ita ba alamun ta, dakin ma da ta ke a rufe ya ke duk wanda suka tambaya sai ya ce bai san inda ta ke ba.
Gashi yanzu tun da suka dawo ba Alhaji ba alamunsa koya shi go baya dadewa, watan su biyar da dawowa suna zaune Alhaji ya shi go a rikice kuje asibitin cikin gida Haleema ba lafiya nakuda ta ke.
Wata zabura sukai wanda kashi ya kufcewa Momy da sauri tai bayi gaba daya sun rikice dan ya fice ya barsu a wajen, ganin ba mafita Antyn yara ta ce “kizo muje ai komai a gaban mu wallahi munyi sake tun farko.”
Momy ta ce “zuwa zami miyi lumbu lumbu mu kashe ta kafin ta haihu” suka bazama ko takalama babu suka nufi asibiti da kafa kamar mahaukata kowa kallonsu ya ke ma’aikatan gidan suna mamaki.
Suna zaune a bakin dakin Hanan ce da Daddy daidai lokacin suka shi go suna kokarin shi ga dakin likitoci suka hanasu, aka tare kofar amma sun ki gaba daya sun haukace suna sambatu sai ka rantse kaunarta su ke sai lallabasu ake, daidai lokacin ta sullubo sambalelen dan ta, daidai lokacin aka kira Daddy aka sanar masa mutuwar Afra autar Antyn yara da rasuwar Amra diyar Momy, salati ya ke yana karasawa zubewa yai a wajen yana hawaye.
STORY CONTINUES BELOW

Yana kuka anan ya sanar musu rasuwar, daidai lokacin da aka fito da yaron a showel, zunduma ihu suka fara suka din ga tonawa kansu asiri suna tsinewa junan su duk abun da sukai kamar a kiyama su ke fada.
A lokacin Daddy yaji kamar ana warware masa wani kulli a kansa, ji yai allurar ta motsa wani nishi kawai ya ke, ya mike ze yi kansu Yasmeen ta rike shi tana kuka, a lokacin Daddy dasu Fateema da su Sherri ranka ta kaf din su suka shi go suka tsinci wannan tashin hankalin kuka kowa ya ke yana la’anarsu.
Anan Momy ta fara dukan Antyn yara ta na tsine mata tana ita ta janyo mata, suka kaure da fada Antyn yara ta dakko wani karfe ta makawa Momy a ka, ta zube matacciya ita kuma ta bazama da gudu ta yage kayan ta bat ta bace ba wanda yaga inda tai.
Anan aka shiga tashin hankali sai da Daddy ya kamo Daddy sannan dan kuka ya ke yana tsine musu, “relax abokina, kayi hakuri domin shi haske ne, me kake nema a duniya duk iyalanka sun kammala muje gida mu zauna ai magana.”
Lokacin likitoci suka sanar musu Hajiya ta warke garas zasu iya tafiya da ita suka dunguma zuwa gidan anan aka warware komai.
Daddy yai farin ciki ya godewa Allah Haleema har suma tai saboda ganin gudan jinin ta, tayi farin ciki sosai na ganin yaronta anan ya nemi yafiyar yar sa da matarsa suka yafe masa ya rungume yaransa sai wajen sha biyu na dare su Daddy suka tafi.
Bayan kwana uku komai yai normal kowa na gidan su, anan Halliru ya bukaci zasu koma gidan sa shi da matarsa Daddy ya ce sam bai yarda ba akwai gidan da ya ke gina musu ya ce shi kuma bazai zauna ba gaskiya.
Ya dogara ga Allah zai rayuwarsa yadda Allah ya tsara masa ita ma ta amince amma ya nemi alfarmar ai biki ta ce bata so haka suka kai su, kuka suka din ga yi na tausayin su amma daga gani talaka ne shi mai takawa da gudun duniya, dan bayasan kyale kyale Farouk ne ya bawa Daddy shawarar nema masa aiki tun da akwai takardu.
Yau ne ranar suna su Sherri sun yi kyau gaba dayansu Umma ta hada ta rike ta kankame, shi ko Mohd karatu zai tafi waje anyi suna lafiya yara sun koma makaranta.
Halliru haka ya ke fita yai fafutuka yai buga-buga yaci da iyalinsa bai kuma hanata aikin ta ba, amma kwandala baya karba a hannunta, Aminullah ne yai wa Daddy shigar sauri da ke shima ya san manya nan da nan aka bashi offer ya fara aiki a guarantee trust bank GT.
Shekarar sa daya yana aiki ya samu ya mallaki gidansa daidai na rufin asiri, yana tsara rayuwar su a hankali yana taimako sosai, biyu ya ke kasa albashin sa rabi na hidimarsu rabi na hidimar jama’a, yana masifar kaunar matarsa ba abun da ba yai mata, rayuwa suke cikin kwanciyar hankali da amana har sun samu karuwa da ya mace.
An hada auren Farouk da Sherri, Mohd da Hanan, Yasmeen da Aminullah, anyi aure lafiya ansha shagali dukkan su sun samu cigaba dama an ce hakuri haske ne sun ga ribar hakuri a rayuwarsu gashi duk sun ga bayan makiyansu.
Alhaji warbeshi yana kwance da Zubaida jini ya balle mata nan ta din ga ihu ta din ga fadar abun da taiwa Hajara dama an ce indai asirin ya karye kan ta zai koma, ya lakada mata duka ya koreta.
Yayi nadama yayi tuba na domin Allah ya nemi gafarar iyalansa ya debesu ya maida su Abuja yaran duk ya kai su waje karatu.
Ita kuma Hajara sai ciki ashe doctor din juya mata mahaifar yai ya taimaketa yanzu kuma ta juyo da kanta, farin ciki kamar mai dama yanzu ya nutsu san yara ya ke kamar mai ya dena komai sai dai dan tsalle tsalle wannan kuma sai a hankali.
Hajiya Haleema rayuwa tayi inganci tana zaune ita kadai da yaranta Alaife, da Gobinya, da Yusuf, da yaronta Sauban, sai yaran Antyn yara guda biyu suma sun dawo ta hada ta rike ta mallake mijinta duniya ta samu.
Momy anyi mutuwar wulakanci dan kabarinta maciji ne ya ke fitowa duk inda aka tona haka a turmutsa ta aka barta da halinta Antyn yara ko ba wanda ya kara jin labarin ta.
Hajara rayuwa tayi kyau ta haifi yarinyar ta kyakyakyawa mai kama da ita suna zaune lafiya da kishiyarta Talatu anwa Ilham aure suna zamansu a Abuja lafiya.
Umman Fateema rayuwa tayi inganci ta haifi tagwaye inda tasa mu mace da namiji macen tasa mata Afsi namijin sunan mahaifinta, rayuwarsu tayi inganci sun kulla zumunci da Hajiya Haleema tana kula da yaran kanwarta sosai.
Momyn Hanan tana cikin halin hauka amma abun da sauki ta dena cin jikinta sai dai kashin har yanzu suna zuwa ganinta amma Daddy sam yaki zuwa dan ya tsani ganinta ko jin sunanta.
Yara kuma suna zaune lafiya da matayensu rayuwar kowa tayi inganci kowa ya girbi abun da ya shuka, wayanda sukai hakuri sun ga ribar hakuri tun a duniya rayuwarsu tayi inganci wayanda suka yi sabanin haka sun ga yadda makomar su ta kasance.

Karshen labarin hakuri haske ne kenan.

Alhamdulillah nagodewa Allah daya bani ikon kammala wannan novel nawa Allah ya bamu ikon amfani da darasin da ke ciki, mu watsar da sharrin da ke cikin sa               *Feedyn bash*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *