HARSASHEN SO CHAPTER 4

HARSASHEN SO
CHAPTER 4
A lokacin har shalele ya sauko daga saman dokinsa, sojan yana kokarin fita shalele kuma yana kokarin shiga cikin gidan, a bakin kofa sukayi kicibis, Da sauri sojan ya rike shalele, cikin tsananin bacin rai shalele ya kalli sojan sannan kuma ya dawo da kallonsa daidai inda ya rike masa hannu, wannan abu ya bala”in babbakawa 
shalele zuciya sosai, Cikin fushi yace cire hannunka a wurin, anki a cire kai dan iska ne ko? Waye kake da suna ma? Gyara tsayuwa shalele yayi tare da sake cewa cire hannunka a wurin nace! Cikin mulki sojan yace idan kuma ban cire ba ………… kafin ya karasa tuni shalele yayi juyin waina yayi tsalle ya caka masa akaifunsa a cikin idonsa, da sauri sojan ya saki shalele ya saki wani irin ihu a daidai lokacin da aka saki wata irin firgitacciyar kara, wato cidar hadari, 
Falau falau farfar walkiya taci gaba da tashi cike da izza ya shiga cikin gidan, a daidai lokacin da Mubarak ya fito daga cikin dakin mahaiflnsa dan ansa waya! 
Walkiya ta sake haska wurin sosai wanda kowa zai iya hango kowa amma a cikinsu babu mai iya tantance kamannun kowa saboda suna da nisa sosai, lokaci guda kuma haske ya dauke duhun damina ya sake bayyana sosai a wurin sai cida data sake tashi mai flrgita duk wanda yajita, 
Da sauri shalele ya rufe idonsa saida yadan murza shi dan wata “yar guntuwar kura data shigar masa a cikin ido, dagowar da zaiyi aka sake walkiya a inda yake hango tsayuwar mutumin yaga wani abu ya taho mai kama da ‘HARSASHE‘ da sauri ya hada hannayensa biyu cikin tsoro yace karka harbeni, ya karasa maganar tare da rumtse idanuwansa da sauri, 
Uhmm yace tare da bude idonsa da sauri danjin abun bai shigajikinsa ba, bude idonsa yayi sosai sannan ya fara dube dube, ganin baiga abunba yasa shi kallon kansa, hannunsa yasa ya fara shafa jikinsa yana lalubawa dan yaji inda abun ya shiga ajikinsa babu komai yaji, Kara daga kansa yayi ya kalli inda yake hango inuwar mutumin, abun ya kara gani ya taho amma wannan karon da gudu ya taho sosai, da sauri shalele yajuya amma kafin ya juya tuni abun ya soki zuciyarsa harsai daya fadi kasa, wannan karon yaji sukar abun a zuciyarsa duka yakai daidai saitin zuciyar sannan ya mike tsaye Cike da jarumta amma yana mikewa sai yaji yanayinsa kamar yasha kwaya, Tangal tangal shalele yake tare da kara faduwa kasa cikin tsoro ya sake kallon wurin a lokacin Mubarak ya juya dan komawa ciki shalele baiga fuskarsa ba sai bayansa ya gani wanda ganin bayansa yasa kyarma ta kwace ma shalele, Cike da tsoro hadi da mutuwar jiki shalele ya mike tsaye, cikin “yan dabaru yajuya dan komawa waje, a inda yabar wannan sojan yana wurin har yanzun kuma hannunsa yana kan idonsa, ko inda yake shalele bai kallaba dakyar ya iya hawa saman dokinsa cike da tsoro jikinsa sai kyarma yakeyi hannunsa daya yasa ya dafe daidai saitin zuciyarsa dan ciwo yakeji sosai abunda yaji ya shiga cikin zuciyarsa, Bashir daya fito daga ciki ya kalli Mubarak da sauri yace me kajeyi waje ne? Girgiza kansa yayi alamar babu komai sai kuma hannayensa daya bude duka wayarsa ce kadai a hannunsa, cike da damuwa Bashir yace wuce maza wuce ku tafl na fada maka, babu abinda ya dameka a cikin wannan fitina baka san lokacin da akayi ba baka nan aka fara ta dan haka maza kama gabanka na fada maka, 
Mubarak baiyi magana ba ya juya, da sauri kowa ya tashi ya biyo bayansa amma banda babanshi, zasu fita ne yaci tuntube da wani abu, da sauri ya cire wayarsa ya haska wanda tsayuwarsa yasa dukan yaransa dake bin bayansa suma suka tsaya! Tsaki Mubarak yayi ganin soja na kuka, tsallakeshi yayi ya wuce, daya daga cikin sojojin ya kamashi suka fita sai bare baki yakeyi yana kuka shege kamar mace mai nakuda, “ Lokacin da suka fita har an budewa Mubarak mota ya shiga, dan haka suma cikin sauri suka haye wuta balbal suke gudu dan fita daga cikin garin, 
A wahalce shalele ya isa gida, dakyar ya sauko daga saman doki ya lallaba ya sulale zuwa dakinsa ba tare da kowa yagansa ba,jin haniniyar doki ya tabbatarwa da mai gida shalele ya dawo dan haka yace ma balaga maza yaje yaga shalele laflya? Bayan balaga ya fitO doki kadai ya gani amma babu shalele, cike da tashin hankali ya nufi wurin dokin sosai ya duba dokin dan ganin ko zai samu wata alama wanda yasa shalele bai dawo gida ba, dubawa yayi yaga babu wani alama wanda zai tabbatar anyi dukawa shalele 
ko kuma anji masa ciwo, dan haka ya nufo dakin shalele cikin fargaba, A hankali ya fara dukan kofar dakinki, shalele dake kwance cikin wahala dakel ya iyayin magana cikin yanayi na mutum yana shan wahala cewa waye? Cikin girmamawa Balaga yace nine, mai gida yace ko lafiya? 
Lafiya qalau shalele ya fada, Balaga yace to mai gida yace saina tabbatar da hakan sannan na tafl, bai wani tsaya bata lokaci ba ya mike dan zuwa ya bude kofa yasan idan har bai bude ba Balaga bazai tafl ba, dan haka yaje ya bude kofar. Cike da tashin hankali Balaga yake kallon shalele cikin sarkakiyar murya yace hawaye? Me yasa kakeyin kuka shalele? Murmushin karfin hali shalele yayi sannan yace miye kuka? Kuma miye hawaye? Kuka alamace ta damuwa tashin hankali ko tsoro firgici yana sa kuka yayin da zuciya taji tsoro, 
Ajiyar zuciya shalele yayi sannan yace ni wanne nakeyi? Balaga yace a zahirance hawaye kakeyi, amma a badini bansan abinda kakeyi ba, a hankali shaleleya sadda kansa kasa yabi hawayen daya diga kasa da kallo sannan yace wannan shine ake ce ma hawaye? 
Balaga yace sosai ma kuwa dan tunda nake ban taba ganin haka daga gareka ba, kallon balaga Shalele yayi sosai sannan yace mi yake kawo kuka a rayuwa? Balaga yace abubuwa da dama suke sa ayi kuka, kuma suke sa a ayi hawaye, mutuwa, ciwo, rabuwa, haduwa, tausayi, tashin hankali, tsoro, damuwa, fargaba, bakin ciki, farin ciki, hassada, kiyayya, wahala,jin dadi masoya kuma sunayin kuka ne guda biyu, na farko sunayin kukan farin ciki yayin da suka hadu da junansu bayan sun dauki lokaci mai tsawo basu hadu dajunansu ba, masoya sunayin kuka yayin da zuciyoyinsu suke dakon soyayya idan har aka rabasu ta karfin tsiya, mutum yanayin kuka yayin daya ga abinda ya shi yaji tsoro ko kuma ya firgitashi! To idan yaji tsoro sai duk jijiyonjikinsa su daina aiki, wannan dalili yake sa jijiyoyin da suke rike da ido suma zasu tsuke yayinda suke cude a wuri daya sai hawaye ya fara gangarowa alamun ka tsorata ke nan! Shalele yace to miye tsoro? Murmushi balaga yayi sannan yace ban tunanin zaka san tsoro dan duk yanda zan kwatanta maka shi baza ka gane ba domin kai kaine tsoro, Jinjina kai Shalele yayi sannan yace ngode zaka iya tafIya, ba tare da balaga ya sake cewa komai ba ya juya ya tafi cikin natsuwa shalele ya kulle kofarsa ya koma ciki, A gaban madubi ya tsaya tare da sauke rawanin da yake nannade gashin kansa dashi ya ijiye a gefe, hannunsa yakai daidai satin idonsa ya tabo hawayen dake digowa masa daga cikin idonsa, kallon hannunsa yayi wanda ya tabo hawayen dashi sannan ya mika hannunsa gefen madubi, Wani dan karamin akwati ne ya bude ya dauko wata takarda, diga hawayensa yayi a saman takarda sannan ya dauki abun rubutu yayi rubutu ajikin takardar kamar yanda yaga 
mahaifinsa yanayi, Bayan ya gama ya cire kayan jikinsa ya saka na bacci,jikin window ya matsa danjib karar ruwan sama, tsaye yayi yana kallon yanda ruwa yake saukowa daga saman sararin samani, murmushi yayi tare da matsowa daga wurin ya tattara gashin kansa ya daure sa, Saman gado ya koma ya kwanta bargo yaja ya lullube kansa, amma daya rufe idonsa inuwar mutumin dabai san ko waye ba yake gani, tare da wannan abun daya soki zuciyarsa, da sauri ya tashi zaune yana mai fitar da lumfashi sosai akai akai da sauri yakai hannunsa ya taba wurin, ajiyar zuciya yayi sannan ya koma ya kwanta, 
A daddafe dai gari ya waye, yana saukowa daga saman gado takardar daya diga hawayensa akai ya dauka dan a lokacin ya bushe, rubutu ya karayi akai sannan ya mayar da ita a inda ya dauko, Bayan ya gama abinda yakeyi ya fito palo danyin kalaci, dashi da mama da mai gida zaune a saman tebirin cin abinci, kowa yanayin kalaci amma banda shalele dan haka mai gida ya kalleshi yace lafiya dai? Ajiyar zuciya yayi cikin irin muryar mata yace mai gida akwai damuwa fa, Idanuwa mai gida ya zaro sosai cikin masifa yakai dukawa dirning table in harsai da glass din ya watse na gabansa, sannan yace miye damuwa kuma? Cikin ladabi Shalele yace Allah ya huci zuciyar mai gida, ruwan zafin gabansa ya dauka ya rike a hannu sannan yace idan na sakejin kalmar damuwa a bakinka saina babbaka da ruwan zafl na fada maka, Jinjina kai shalele yayi cikin girmamawa yace insha Allah zan kiyaye, tsaki mai gida yayi sannan ya mike cike da bacin rai, shalele yabi bayan mahaiflnsa da kallo yana tafiya yana masifa sai kace kura ta kama mutum ya gudu, Bayan mai gida ya bace shalele ya gyara bakinsa amma baiyi magana ba, wani irin dunkulelen abu yaji ya hadiye kamar dutsi kuma dutsin wanda ya shekara cikin wuta, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli mama, cikin tausayawa itama mama ta kalli jikarta da aka mayarda ita namiji saboda fitinar duniya, murmushin karfin hali shalele ya yi ma mama sannan ya tashi a wurin, cike da damuwa mama tabi bayan ummu suleim da kallo, A bakin kofa shalele ya tsaya ya fara kiran sunan balaga, da sauri balaga yazo cikin girmamawa yace karamin mai gida barka da fitowa, hannu shalele ya daga masa dan yaga yazo da sigar wasa, dole balaga ya tattaro natsuwarsa ya kalli shalele cikin girmamawa, shalele yace mai zane nake so ka samo min a cikin gari, 
Ranka ya dade me za”a zana maka ne? Kallo sosai shalele yayi masa sannan yace akwai abinda nake so na gano ne, amma abun a cikin duhu na ganshi, ka samo min dai wanda ya iya zane sosai nasan idan na fada masa zai zana min fiye da yanda nake tunani,jinjina kai balaga yayi yace karka damu, har shalele ya juya ya fara tafiya kuma ya tsaya, ba tare daya juyo ba yace karka fadawa mai gida na fada maka, balaga yace an gama ranka ya dade, sauri shalele ya fada tare da ci gaba da tafiya! 
Da sauri Balaga yaje yahau doki ya fita daga gidan ………………….. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *