HARSASHEN SO CHAPTER 7

HARSASHEN SO 
CHAPTER 7
A zuciye mai gida ya isa gaban shalele hannunsa ya dunkule tare da kaima shalele wani irin lafiyayyen duka a saman baki harsai da jini ya fita a bakinsa! 
Meye abun burgewa a duniya? Babu komai a cikin duniyar nan sai ‘KIYAYYA‘ babu burgewa a cikin duniya babu sha”awa sai bakin ciki, tashin hankali, babu so a duniya tsakaninka da mutum sai azaba duk abinda kake tunanin zaka gani a duniya ya burgeka kafin zuciyarka tayi maka wani dogon saddabaru maza ka cire wuka ka caccakawa wannan abun tun kam kai ya caccaki taka zuciyar! ldan na sakejin burgewa, sha”wa, tunani k0 mafarki a bakinka saina bare maka baki biyu na fada maka! Cikin girmamawa shalele yace insha Allah, Tsaki mai gida yayi sannan yace maza kaje bayan gari akwai bako na yana nan zuwa zai baka sako ka kawomin kayi hankali sosai hatsabibin boka ne, kuma yana da illa dan saddabarunsa sunfi naka tsauri maza kaje, Saida shalele ya sadda kansa kasa alamar girmamawa sannan ya dago yace mama saina 
dawo ba tare daya tsaya ba yayi gaba! Allah yasa ka dawo lafiya, mama ta fada, 
Ta bayan gidansu shalele ya fita, a kafa yake tafiyarsa cikin hanzari dan bayasan ya batawa mai gida rai ko kuma ya bata masa lokaci bai dawo da wuri ba yayi fada, 
Yana tafiya idonsa a lumshe yake yana tunanin Mubarak baima san inda yake saka kafarsa ba, murmushi yayi tare da bude hannayensa kamar zai rungumi wani yanajin dadin yanayin garin dan garin yayi irin yanayin damina sai iska dake tashi sosai har yana kada kayan jikin mutum, 
Murmushi yayi sannan ya bude idonsa, dan gudu gudu ya farayi dan ya kagara yaje ya dawo ya samu natsuwa dan yin tunaninsa cikin kwanciyar hankali, da gudu ya isa inda mai gida yace amma babu mutumin babu labarin sa kwata kwata, 
Yana tsaye a wurin harwani lokaci amma mutumin baizo ba, wannan dalili yasa shalele ya dan fara tafiya cikin jejin yana yawo sosai sai kalle kalle yakeyi cikin yanayin damuwa, Taflya yakeyi yana tafiya saman busashshen ganyen daya fado kasa ya bushe duk inda ya taka sai yayi motsi saboda bushewar ganyen alamar dai ana tafiya a sama, yayi taflya mai 
nisa sannan yajiyo alama ana tahowa ta bayanshi, Da sauri ya juya amma baiga komai, ba tsaki yayi sannan yaci gaba da tafiya ta bayanshi yaji anci gaba da tahowa, cikin rashin jin tsoro ya tsaya amma bai waigo ba, Tafiyar yaji anayi ba”a daina ba, dan haka juyowa yayi da sauri,wani irin isashshen maciji ya gani yana wata irin tafiya kamar ba saman kasa yake taflya ba! Cike da tsoro shalele ya fara ja baya, macijin kuma ya fara binsa kara ja yayi da baya har yanzun shima 
macijin binsa yayi, cikin tsoro shalele ya juya da gudu aiko maciji ya bishi da gudu sosai, Gudu sukeyi sosai a cikin dokar daji ba”ajin karar komai sai nishi irin na mata idan sukaga abun tsoro da dan guntun kuka, da shalele ya juya zaiga macijin nan ya kusa cinmasa, haka yayi ta kutsawa yana dukawa dan wuce itatuwan da suka tare masa gaba, Yana kurdawa wani wuri icce ya rike masa rawani ya tsaya cirewa yaga macijin nan ya KUSa Cim masa aikuwa daqar ya cire rawanin ya sake Iecewa sukayl ta guau nan shalele ya 
fita daga wannan dajin ya fada wani, 
Gudu yakeyi yana waiwayen bayansa sosai gashin kansa gaba daya ya watse ya sauka a gadon bayansa wani kuma ya bazo ya rufe masa fuska baya ko ganin gabansa, faduwa yayi saboda gajiya macijin kuma ya fasa kai dan kaiwa shalele sara da sauri shalele ya rufe 
idonsa tare dasa hannunsa saman fuskarsa yana jiran yaji sara
Shiru har wani lokaci baiji macijin yakai masa sara ba dan haka ya bude idonsa baiga macijin ba sai wani irin mutum mai munin gaske da firgitarwa, wata irin dariya mutumin yayi wanda duk girman dajin nan saida ya amsa, cikin tsoro shalele ya fara ja baya tare da cewa kai waye? 
Saida ya sake kecewa da dariya sannan ya wurgowa shalele wani abu, da farko shalele leda ya gani amma abun daya sauka kasa saiya koma wata kwalba, cikin tsoro shalele yace meye wannan kuma? A tabbatar dan Bashir an zuba masa wannan ruwan a cikin ruwan wanka, yana fadin haka ya farayin baya baya saida yayi nisa da shalele sannan ya koma macijin ya bace, Saida ya bace sannan shalele ya maido dubansa ga kwalbar, cike da tashin hankali yace to waye dan Bashir din? Mutumin ma da babu wanda yasan sa bare kuma asan sunansa? Daukar kwalbar shalele yayi da hannu ya daga ta sama yana kallo, ajiyar zuciya yayi sannan ya goge zufar goshin sa ya mike ya nuf’I gida a gajiye,
Sanye yake cikin kananun kaya wanda suka matukar dacewa da kyakkyawan jikinsa, gyara zaman hular kansa yayi wanda ake cema fesin cap ta matukar dacewa da kyakkyawar fuskarsa tayi kyau sosai a kansa, da murmushi ya daga kyawawan idanuwansa masu matukar burgewa da sha”awa, saida ya sakeyin murmushi da gefen sannan ya kalli daya 
daga ciki yaransa da suka zagaye shi yace bani ruwa, Da sauri ya dauko ruwa cikin girmamawa ya duka gaban Mubarak ya ijiye ruwan, kallonsa Mubarak yayi sannan yace shanyesu cikin dabircewa ya kalli Mubarak amma saiya basartare da daukar kafa daya ya dora saman daya yana kallon agogon hannunsa,Babu yanda ya iya dole ya dauki ruwan yasha, bayan ya shanye, Mubarak yace dauko wasu hankalinsa ya tashi sosai dan yasan khadija za”a dauko masa dan duk lokacin da 
za”a daukota saiya azabtar da mutum sosai yau abun ya zagayo kansa cikin girmamawa yace ranka ya dade tuba nakeyi don Allah zan daukota cikin girmamawa da bata kariya kayi hakuri ya fadi maganar tare da girmamawa, 
Ko kallonsa Mubarak baiyi ba, zai kara magana Mubarak ya murza “yan yatsun hannunsa tare da dan motsa bakinsa, a hanzarce ya koma bakin firij ya dauko robar ruwa biyar dan yasan wannan gejin zai sha, Cikin damuwa ya balle murfin robar ruwa yakai a bakinsa ya shanye ya daga ta ukku ya dora,ya bude ta hudun yace ranka ya dade kayi hakuri, cike da rainin hankali Mubarak yace ai ba laifi kamin ba kawai dai ina shawa”ar haka ne, tou kayi hakuri don Allah wallahi zan kawo maka ita cikin kulawa, Kallonsa Mubarak yayi sannan yace jirginsu zai sauka nan da 20minutes kar tayi jira kar tayi fushi cikin gamsuwa yayi waje, Hilux biyu na sojoji suka tafl, saishi driver da zai daukota ya shiga ciki wata mota mai kirar “Aston martin“ a ciki za”a dauko matar mai gida da ta dawo daga london, Babu wani dadewa suka isa, a daidai lokacin da jirginsu khadija ya sauka filin jirgin Abuja, kallo daya zakayi mata kasan ta huta, “yar gayu ta koke kanta ya fashe da yawa, cike 
da wulakanci ta fara musu magana, 
Sai yanzun kuka ga damarzuwa? Kuna kasan mijina kuna zuwa a daidai lokacin da nake sauka, ni banga amfanin talaka ba danni duk talakawa bayina na daukesu baku da wani amfani daku da dabbo banbanci daya ne kawai su ana yankasu aci namansu ku kuwa saidai a kasheku a zubar a rami dakikai ku wuce muje, 
Tayi gaba sunabin bayanta tana mai ci gaba da fada, matsiyaci kawai 
khadija ajin farko bata da mutunci kuma Allah ya kwarara mata ruwan kishi da masifa akan Mubarak har kisan kai tana iyayi, bata da wata damuwa dan tana samun yanda takeso sosai shi Mubarak baida damuwa da mata harkar gabansa kadai yakeyi danshi mace bata sha masa kai ba, itama khadijar itace ta nace ta kwakwafe saida ya aureta dan da kanta take zuwa zance ko yana nigeria ko baya nan duk kasar da yake saita bishi, ita ta manta da yanda aka aureta amma yanzun tanajin bakin cikin wata Hafsa dake nace da Mubarak itama duk inda yaje saita 
bishi amma ita ba “yarwulakanci bace ba, 
Haka taci gaba da masifa da wulakanci da rashin mutunci bace, cikin girmamawa yake bata hakuri dan yasan idan har sukaje gaban Mubarak a haka kashinsa ya bushe, sosai yake bata hakuri tare da daukar mata alkawari hakan bazai sake faruwa ba, dakel ya samu ya shawo kanta, sai kuma ta fara tambayarsa miya faru bayan bata nan,,, 
Shalele ne kwance a saman cinyar kaka Balaga ya shigo cikin dakin da sallama, mama ta ansa, barka da hutawa Balaga yayi ma Mama sannan yace karamin mai gida ga mai zanen nan yazo, 
Ba tare da shalele ya juyo ba yace ya jirani a dakina ina zuwa, tou ranka ya dade sannan ya juya ya fita daga cikin daki! 
Bayan fltar Balaga Shalele yace Mama don Allah tambaya daya kawai zan miki kiyi hakuri ki amsa min a karo na farko ki taimaka ki warwaremin abinda ban sani ba ki fitar dani daga cikin duhu, 
Cikin muryar tsufa tace inajinka dan nan, tashi shalele yayi zaune tare da tattaro dukan natsuwarsa ya kalli mama, tsareta yayi da idanuwa sannan yace waye dan Bashir? Kai tsaye mama tace baya da dan da,,,,,,, yasa kika ce bashi da da ne? 
Mama tayi shiru, Shalele ya kamo hannunwan mama ya rike a cikin nasa sannan yace nasan kinsan komai kuma duk abinda ya faru a gaban idonki ya faru ki daure a karo na farko ki fadamin waye dansa? Maganar mai gida sukajiyo daga waje dan haka da sauri shalele ya mike da niyar fita a bakin kofa suka hadu, cikin fada yace kasan kana da aiki a gaban ka sosai kazo ka zauna a wurin nan k0? 
Cikin sanyin murya Shalele yace me zanyi ne mai gida? Tafiya zuwa kasashen waje nemo yaron nan boka yace karna kuskura lokacin nan ya wuce banyi aikin nan ba, dan nayi alkawari kafin ka kashemin Bashir saiya samu labarin mutuwar dansa yaji bakin ciki kamar yanda naji a lokacin dana rasa nawa dan, Insha Allah Shalele ya fada sannan ya fice daga dakin, kai tsaye dakinsa ya nufa anan ya samu mai zane dan haka shalele a gefen gado ya zauna, yace fara, Me za”a zana maka ranka ya dade? Mai zanen ya tambaya, gyara zama Shalele yayi sannan ya dauki kafa daya ya kafe a daya yace, hadari ya taso sosai duhu ya bayyana a cikin garin nan, walkiya tana haskawa a lokutta kadan kadan , 
Cikin wani gida ne na shiga, yana da yalwar girma a gefe kuma akwai dakin dawakai sai daya gefen kuma an daure wani lafiyayyen doki wanda duhun hadari bazai iya bari na tantance wane kala bane, a can kuma kofar daki wani mutum ne tsaye Cikin kayan da suma bazan iya gane kalarsu ba, walkiya ta haska harso ukku sai kuma cidar hadari ta sauka mai flrgitarwa, Akwai abunda ban fada ba wannan sirri ne tsakanin ni da kuma zuciyata, har yanzun ban ga fuskarsa ba sosai, bayan hasken walikiya ya sake haskawa sa naga bayansa, yanda yaga 
bayan nasa ya fadawa mai zane’. 
Murmushi mai zanen yayi sannan yace to babu bukatarzana fusakar sa tunda kaima baka fada mana yanda take ba, yanda zane ya bada ya mikawa Shalele ya kalla, murmushi Shalele yayi sannan ya ajiye a gefe, Sake gyara zaman sa yayi sannan yaci gaba siffanto kamannin Mubarak mai zane ya dora, har Murmushin da Mubarak yayi saida ya fada aka zana da dariyar da yayi a lokacin daya dora hannunsa a saman bakinsa, lokacin saukowa daga saman benen palonsa da igiyar daya wurwura ya nadosa daga saman doki fadowarsa da komai saida aka zana, 
Bayan mai zane ya gama Shalele ya sallameshi tare da fada masa zai sake neman sa idan bukata ta taso, godiya mai zanen yayi sannan ya tafl, 
Bayan fitar mai zane Shalele yabi hotunan zanen da kallo yana mai jin farin ciki sosai a zuciyarsa gani yakeyi kamar Mubarak ne a gabansa, tunanin inda zai manna hotunan a dakinsa ya farayi dan duk lokacin da mai gida ya gano haka akwai babbar matsala, Ajiye hoton Mubarak yayi sannan ya dauki dayan zanen mutumin da ya gani a gidan Bashir amma ya kasa gano komai, ajiyewa yayi a gefe ya sake daukar hoton Mubarak yana mai binsa da kallo sosai, 
A guje yake taflya saman dokinsa yayi masa kyakkyawa riko dan dazo maza ya gani sosai a wani wuri can a gefe sun cika sosai har ya wuce kuma saiyajuya linzamin dokinsa dan komawa wurin yaga abunda ake kallo, Sauka yayi daga saman dokinsa a lokacin daya isa wurin, dan tuttura mutane ya farayi ya shiga wurin, wasu irin garada ne ya gani suna fada kowa ya cire rigarsa kamar dai “yan dambe, idanuwa Shalele ya zaro tare da kallon kansa daidai kirjisa ya kalla sannan ya maida dubansa ga mazan da mamaki yake kallonsu idanuwansa kamar zasu fado kasa, Lokaci guda kuma idanuwansa suka kawo hawaye kara kallon kansa yayi cikin yanayin mamaki da sauri ya fito daga wurin da gudu ya koma ya hau dokinsa ko gabansa baya gani ya nufi gida ……… 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *