HASKE CHAPTER 1

HASKE




CHAPTER 1




Kaduna 

Haisam ne ke tafe bayan ya mika sakon da Mummyn sa ta aike shi dashi a tashar KSTA dake Unguwan Sarki, yana tafe cikin natsuwa wanda dama halinsa kenan. Bayada garaje ko rawar kai a cikin al’amuran sa. Komai nasa das das abin sha‘awa. Ba abinda ke nunawa a fuskarsa banda murmushi da nuna rashin damuwa saboda shi mutum ne mai yawan fara’a da maida komai ba komai ba. Da kyar Kaga bacin ransa ko kaji ance yayi sa’insa da wani. Shi a nashi tunanin duniyar kwara nawa ne idan akayi hak’uri za’a barta, kuma abinda hakuri baiyi magani ba tashin hankali bazai gyara ba. Tafe yake yana sauraron program din ‘Oga Driver’ a Motarsa kirar Honda EOD. Ba kasafai zakaga yara matasa wanda suka kai a cikin wannan ba. Ko wani namiji musamman dan Kaduna yafisan ace yana tuka Benz wanda shine motar da yan matan sukayi na’am wajen sauraron mai hawanta. 
Yan mata biyu ne suka shiga Napep a wajen bus stop din Unguwan shanu. “Barau Dikko” dayan tace a sanyaye. Daga nan bata sake cewa komai ba, dama haka suke abinsu. Barci tare, ci tare amma idan yan kan sun motsa sai kowa ya saka earpiece ya gimste fuska, balle kuma yau tanada dalilin shiga wannan yanayin tashin hankali. 
Kafin mai napep ya burga sai wasu samari su biyu suka tsaida suka shiga, daya ya zauna a baya dayan a gaba. Yan matan nan suka buga tsaki suka sake kanne fuska tamau. “Ina zan kaiku?” Mai napep ya tambaya mazan. “Muje kawai karka damu” An soma tafiya sai na bayan ya juya ya kalle yan matan yana washe hakorar sa kamar gonar auduga. dayaga bazai fisshe shi ba saiya gyara murya da kwabdeden tabaransa ya soma magana. “Afuwan na mance bamu gaisa ba, barka da asuba” Wanda tayi magana da farko ta sakeyi yanzu, “Yauwa” saita juya. Taso ma da wayanta ta canza wakar dake yi amma ta tuna ana kwacen waya a napep. Gwara ta taimaka ma kanta ta hakura. 
Sai wannan ya soma sosa keya, ya karkata ya kalle ta dayan gefen wanda batace komai ba. “Ke baki amsa gaisuwa ne?” 
Ido rufe tace masa ana dole. Nan yayi shiru gwiwar sa yayi sanyi bai sake magana ba. Sai daga bisani ya soma waka mai ban takaici, “Doguwa fara kinfi baka gajera, k0 baki dariya kinfl baka mummuna” muryansa irin shakakke ne mara dadin sauraro musamman idan ana waka da ita. 
Ba Yan matan ba har mai napep wakar yanata bakanta mashi rai. Amma babu yanda zaiyi yana hulda da jama’a. 
Kafin a kai kwanar Barau Dikko wanda batayi magana da chan ba ta soma, “Mallam sauke mu nan kawai ya ishe mu” ba itada kawarta ba harta samarin suka sauka suma. Dari biyu zasu mika sai samarin suka saurin mika dari biyar wai a cire nasu duka. 
“Ji mana” sarkin waka yace masu, wanda ta gwasale gaisuwar shi tace wai meye haka mallam ka wani takura mana tun dazu. Shi kuma yayi mata kallon hadarin kaji kana yace, kwantar da hankalin ki mummuna badake nake ba, da kawarki nake magana” 
Kowa a wajen yayi mamakin wannan batun nasa, saboda yadda ya debo ta da zafi. “Idan 
ba’a kasa dake ba karki diba. Kinata wani kumburi kina huci bayan ko kallo baki isheni ba. Halan bakin ciki kike ma kawarki dan ba’ayi dake” 
“Jar uba! Karka kuskura ka zageni Mallam saboda bakayi kamada kalan samarin da zanyi tarayya dasu ba” sannan ta wuce saboda tana dabda zabga mashi mari.
Dayar itama tabi sahunta suka barshi a wajen, sai a lokacin tayi magana mai zurfi. “Yi hakuri yau banajin garin ne dasai ya yaba ma aya zaki” wanda tayi fada batace komai ba illa huci tana mayar da numfashi sama sama. Banda raini ya za’a ce tanama na gefenta bakin ciki. 
“Mazaa ba haka akeyi ba!” Mai napep yace mashi. “Wannan kai ya shafa, babu ruwanka bani canji ka kara gaba” nan yayi zugum ya basu ya wuce kafin a zagi ubanshi. 
Haka suka soma shafa titi babu wanda tace uffan ma yar uwarta, Haisam ne ya karyo kwana ya wuce su. Wanda tafi natsuwa tace, “Laila ga mutumin ki dan ra’ayi” Laila ita banza jibe irin motar dayake hawa kamar za’a kai dabbobi kasuwa. A tare suka tintsire da dariya sannan suka tafa hannayen su. 
Shikan ta side mirror yagan su, jan birki yayi saiya soma reverse. Bai tsaya ba her saida ya kai inda suke. Cikin fara’a ya soma murmushi, “Assalamu alaikum” sakeke suka tsaya suna mashi dariyar izgilanci. Bai damu ba illa cigaba da maganarda yakeyi, “Ku shiga mu karasa ciki mana” kallon hadarin kaji Laila tayi sai tace mashi ya tafi zasu iya karasawa. Bai takura masu ba yaja motarsa yayi gaba. Ya riga yasan halinsu kuma dama da kyar su shiga motarsa amma ganin sun kusa latti yasa yayi masu tayi. 
“Sannun ku” suka ce a tare yayin da suka karasa wajen masu gadi. “Yauwa Barka da asuba” Mallam Dauda ya gaida  “Uhmmm Hum” suka amsa a miskile suka wuce suna yauki. 
Registry suka wuce inda suka rubuta sunar su da lokacin da suka isa. Sai kowace ta wuce taburin ta na aiki. Cashiers ne a Asibitin watau masu karban kudi. 
Sunata aiki gadan gadan ga mutane sun zo sosai harwajen 10am. “Dan Allah nawa ne bude kati?” Haisam ya tambaya a mutunce 
Basu tanka ba saida ya sake magana a karo na biyu, “Laila dake fa nake magana nace nawa ne bude kati” cikin tsawa tace ban sani ba halan yau ka fara aiki a wajen nan? Koko kai ka ajiye ni? Kallonta yayi yaga meyasa take ihu kamar karya, “Allah ya baki hak’uri” yace saiya kalle dayan. 
“Ji mana, nawa ne bude kati?” nan ta tashi ta fada mashi tareda bashi. “Meye matsalar ta?” yace a sanyaye. Bata amsa ba kuma batada niyyar amsawa banda binsa da murmushin izgilinci. Idan daya sani daya don 
Basu sanshi kuma basu san hulda dashi, yaro ne karami wanda yagama medical school yana houseman ship. Ana bala’in sanshi a wajen saboda ya iya turanci sosai gashi kuma yasan aikin sa. Sannan bashida raini ko wulakanci. 
Idan ka duba tsanar rashin dalili suka mashi, amma kamar baisan sunayi ba. Musamman 
Laila, kullum saita mashi rashin mutunci. Dama ance duk yadda ka kai ga Iya abu, ko kuma kyawawan halayyan ka dole akwai wanda zai tsane ka a kansa. 
Da la’asar sakaliya sun gama shift dinsu zasu wuce gida. “Ki cire girman kai ki kira shi” Laila tace mata. Dama duk wani zafin kai da kawarta keyi yau bai wuce sabani data samu da saurayinta ba. 
“Bafa zan kirashi ba, wallahi na hakura dashi. Bashi bane autan maza kuma bazan mutu ba” Tace tareda matsa kwalla. “Rainin wayo ne baniso, a duniya na tsana abin amma ya gama kure hakuri na” rike mata hannu Laila tayi tana murzawa a hankali, cikin natsuwa tace mata “Karki damu, hakuri zakiyi haka soyayya ya gada, dole akwai bacin rai, duk wanda kikaga basa fada akwai zaman munafurci. Ko harshe da hakori akan saba balle mutane” saita numfasa tace, “Balle Allah ya kara ma ayar ki zaki kin samu yaro matashi mai kudi da asali, matsalar meye yanzu kike dashi? 
Shi kam Bilal haka yayita bin agogo da kallo yana zabga tsaki, bai iya bin mace haka wai dan tayi zuciya dashi ya damu ba. Amma tun sanda ta shiga rayuwar sa ya koya, watau gadan gadan ba sanin dayayi mata a baya ba, yanzu soyayyar da sukeyi wanda tun yana tirgewa da kuma nokewa har ya yarda eh santa yakeyi. Saidai kuma ya kasa tantance k0 tausayinta, ko sha’awanta ko shi asalin madaran santa yakeyi na jini da ruhi. Babu haufi ta zame mashi wani magani wanda idan baiji muryanta a rana ba bazai iya tabuka wani abin kirki ba. Sai dai kamaryadda mosoya ke soyayya suna kokarin faranta ma juna rai, shi kam asalin akuyanci yake mata diban albarka, sai dai daga baya ya bata hakuri. Ya kasa gane meyasa baya iya faranta mata rai yayi abinda ya dace kamar kowa. Koko dai dama hake ake soyayyar? 
Basu gama maganar ba sai wayanta ya soma ruri, “Sweet” ya nuna dara dara akan screen din. Da zata ki dauka sai Laila tayi mata magana, “Meye haka ? Kinsan baya kiran waya sau biyu. Ki rufa ma kanki asiri tunda shi ya bibiye ki” 
Nan ta dauki wayar ta kara a kunne, “Inaji” tace. Shi kam dariya yayi mai sauti sannan yace “Hasken L ina bakin Gate inajiranki, idan kin karaso sai kiyi min fadan koh?” yace cikin izgili. Bata ce komai ba ta kashe wayan. Nan ta dauki hoda ta murza a fuska sannan ta dauko jambaki mai ruwan hoda tasa a bakinta. Kana tayi daurinta na tambari watau ture Kaga tsiya.
Tafiya suke kamar reshen bishiya harsuka kai bakin Gate, “Sai anjima“ suka cema Malam Dauda. 
Tsaye suka gansa gefen motar sa kirar marasandi, fara sol kamar kayanjikinsa. Riga ne doguwa iya gwiwa dinkin simple babu aiki ko wani style barkatai. Ya murza hula tangaran a kansa. Agogonsa da takalmin sa mai rufewa ma abin kallo ne,yana bala’in san gayu a matsayin sa na da namiji. 
Dogo ne sambal bayadajiki amma kuma babu rama a tareda shi, yanada tarin gashi sosai a kansa kamar Malam Aminu Kano. Sai kuma sajensa yaje daidai da kyakkyawan fuskan sa. Kana ganinsa kaga dirarran namiji san kowa kin wanda ya rasa. Duk inda ya wuce sai an kalle shi saboda ya kai ne. 
“Badman Bilal, angon Haske wallahi kun dace dajuna” Laila tayi mashi kirarin data saba binsa dashi saboda yana bala’in burgeta komai nashi. Murmushi yayi tareda kallon Haske wanda ita kam kunu ta sha. Laila kam sai washe baki takeyi sannan ta gaida shi. Bayan sun shiga motar wanda babu abinda ke tashi sai kamshi da sanyi. 
A hankali ya soma magana cikin tausayi, “Dan Allah sweet kiyi hakuri wallahi nasan na bata maki rai, kiji tausayi na mana” batace mashi komai ba illa fashewa da kuka. Tsaki ya doka saiya dafa kanshi, “Ki dena kuka nace bazan kara ba, komai kike so daga yanzu shi zan rinka maki wallahi na tuba” ya fada cikin nadama. Ko dayake ba yau ta farajin wannan kalaman ba, kullum zai canza amma shiru kakeji. Da canjin shi da zuwan J ba’a san 
wanne zai fara bayyana ba. 
A sanyaye ta soma magana tana shesheka, “Halan so hauka ne Bilal? Dan ina sanka? Ya za’ayi kace kana sona kuma kayita wulakanta ni? Dan Adam abin wulakantawa ne?” ta sake fashewa da kuka. Duk abinda sukeyi Laila na baya tana jinsu. 
“You don’t hurt someone you love” Haske ta furta. “Naji kuma na dauki laifina” Yace. Kakalo Murmushi tayi sannan tace “Babu komai Allah ya daidaita tsakanin mu” murmushi yayi tareda naushin iska alamun yaji dadi. ‘ “Haske kinyi a rayuwa” ya sake fadi, basu bar wajen ba saida ya bita da kalamai masu shigajiki. “Nidai mu wuce Havilla mu sha ice cream kafin mu wuce gida” Laila tace cikin basarwa. “Angama” ya amsa tareda kunna motar. Wannan kenan! 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *