HASKE CHAPTER 10

HASKE






CHAPTER 10




Ba mai shago ba harta Napep dinda ta hau ta koma gida saida suka kaura dashi. Baida canji yace taje ta samo nan ta zage ubansa kuma tace taci banza karfin sa ya kwace mai, sai tayi tafiyar ta, Allah ya isa ya bita dashi yana gunguni. Lantana ta gani a bakin kofa tana gogewa. Babu abinda ya dameta tasa takalmi tayi wucewarta duk ta bata. Daki ta je tayi zaman dirshan bakin kofa. Anan ta bude sabon babin kuka.
Yi takeyi tana shesheka. Har muryanta yana son dishewa ‘na bani na lalace’ ta rinka maimaitawa. Tana yi tana tafa hannunta tareda dafa kanta. Tashin hankali take gani, gatada ciki kuma Isi ya gudu. Tabbas abinda ya faru da Haske zai faru da ita. Yanzu tayi dana sanin da batayi saurin cewa a kore Haske bA kila itama da an yafe mata. Ammi ce taga shiganta kuma tabbas abu na damunta.
Ammi mace mai san yaranta sosai bata san taga bacin ransu. Musamman ma Fijr duk tafi
shiga ranta. Fijr na kama da kakansu na Misra sosai dan duk family din dakyar a samu
wanda ya dareta ta fannin kyan fuska. Kawai dai tanada uban girma ne kamar mutanen farko. Gashi muryanta a sama yake kamar an kunna injin markade, ba’a iya sirri da ita
yanzu zata tona tanayi tana kallon wanda ake maganar sa. Gashi bata kama jikinta tayita
sabar sabarjiki yana rawa. Sannan ko bra mai kyau masu karfi bata sawa tunda tanada dukiyar Fulani mai yawa. Haka zakaga kirjinta kamar an rungumo agwagi.Tura kofar Ammi tayi sai taji kamar da mutum bakin kofan, nan ta sake yi wanda saida Fijr ta motsa. Ita kuma saita juya domin taga waye kafin ta watsa ashar. Ammi ta gani saita mike tsaye domin ta shiga. Gaban Ammi yayi mummunan faduwa saboda bazata tuna randa
taga hawayen Fijr ba. Sai dai ta saka ka kuka amma wane mutum. Wannan shi ne abin mamaki wai ciyawa da cin doki. “Fijr dear! Meya faru halan? Wani ya mutu ne?” ta watso mata. Karkata baki Fijr tayi ba tace komai ba. Yadda ta tona ma Ammi asiri akan Haske tana tsoron karta tona mata yanzu. Gwara tayi gum da bakinta. “Lafiya lau Ammi kaina ke ciwo” “Ke kam wani irin ciwo ne wannan harda kuka?” “nidai nace ki kyale ni kaina ke ciwo” ta fada “Allah ya kiyaye, bari Lantana ta kawo maki abinci da panadol”
“Uhmm hmmm” Ranar gabadaya Ammi batada walwala, yadda taga Fijr cikin damuwa duk taji babu dadi. Tabbas Fijr tana cikin matsala amma ai ita ce mum dinta. Zata iya mata komai a duniya. a
Kashegari Fijr kafin 8 tabar gida. Maternity clinic taje inda ta saba zuwa. Nan ta rinka rokan Doctor da Allah da Annabi ya cire mata cikin ko nawa ne zata bashi. Shi kam yace bazai iya ba tunda dai yasan zata iya mutuwa kuma bai so tayi hannunsa. Daga nan ya tambaya cikin wata nawa ne? Narai narai tayi saboda bata sani ba.
Ta riga ta saba daukar ciki alamu taji kawai kuma kwanan nan. Anan ya gwadata sai aka ga watan cikin biyar. Dayake tanada jiki baya nunawa kamar tumbi yake. Tabbas bataga 
bakonta na wata ba amma kuma tunda taga suna amfani da kwaroran roba wanda bokan bature ya kera bata kawo wani tunani ba. Dama chan basa amfani dashi sai yanzu. Anan taci kwalarsa tana jijiga shi tana cewa ‘Karya ne! Karya ne! Karya ne dan bakwal uba!‘ sai kuma ta sake shi tareda zubewa kasa tana kuka, saida ta kusan lankwasa masa kujera tana bori. security ya kira domin su taya shi rakata waje kuma karsu kara bari ta 
shiga mashi asibiti. Haka ta fita tanata zage zage kamar sabon hauka. 
Ammi Hadiza bata gida sanda ta koma, Lantana daga nesa ‘ta hangeta ta boye saboda ta lura kanta yana touching. Daki taje tayita kuka, a ranar tayi kukan da bata taba irinsa ba. Gashi sai ke war Isi takeyi. Hotonsa tasa a gaba tana kallo tana shafawa tareda sumbatan screen din Wayan. “Come to me my darling, I promise to behave” tace. Sanda Ammi ta Dawo Lantana ta sheda mata Fijr na gidan, a wannan yanayin ta riske ta.
“Wallahi sai kin gaya min meke damun ki” tace a haslace. Kuka Fijr ta cigaba dashi, tasan ta kusan girban abinda ta shuka. Daddy ma yafi bata tausayi zata bata mashi suna a gari. “Ammi ki yafe min… Dan Allah” tace cikin kuka. Dama Ammi tanata neman fada, da sauri ta rungume Fijrtana shafa mata kai tareda buga mata baya cikin kulawa.”Shhhh my baby, ki fada min koma menene nayi maki maganin sa” “Ammi ciki gareni” abu Ammi taji kamar saukar mashi. Gwara ma a harbe kunneta da takobi mai tsini da sanarda ita mummunan abu kamar haka. Dan kuka maijawo ma uwarsa jifa, wannan wani irin debo ruwa ne. Sandarewa tayi ta daina motsi, numfashi take kokarin saisaita wa. Ko kiftawa dakyar take yi. Ta kame Kamas kamar bango. Fijr taga bata kula ba duktana tunanin bataji bane. Ammi nace ciki gareni na wata 5…..”da sauri Ammi ta tsinke ta.” Naji please basai kin sake maimaitawa ba ” bayan Ammi ta saisaita kanta saita mike tsaye tareda finciko Fijr,” Tashi muje asibiti a cire ” Kwace kanta tayi daga rikon da Ammi tayi,” Babu inda zani ” ” Wallahi babu inda zani” ta sake maimaita wa. “Ba shawara nake nema ba, bazamu haifa shege ba inji kunya” “Nifa Ammi bazani ba, ina tsoron karna mutu” saita fashe da kuka. Ammi tana kallonta sai taji tausayinta ainun. Kila ma fyade akayi mata yasa take tsoro haka. Runguman ta tayi ta soma shafa mata baya, “karki damu ki dena tsoro, cire ciki baida wahala. Sabida baki taba yi bane amma muna cirewa zaki warke” Daba Ammi Hadiza ta haife taba data kaureta da 
mari saboda takaici. “Ciki na shida kenan, kuma ance idan na cire zan mutu. Koko kina tunani da zan iya bazan cire abina bane” Da sauri Ammi ta ture Fijr tareda ja da baya. Tasan bataji amma tana tunanin rashin kunya ne kawai. Ashe harda asalin iskanci ta iya kuma ta kware akai. Tabbas tayi 
kaurin suna a bariki. Hawaye yayita mata gudun famfo. Rawajikinta yakeyi wanda saida kafarta yayi mata nauyi. Da sauri ta kwance kallabin ta tana fifita dukda AC din daki. Tsoro fal ranta tayi zaman dirshan hannu a kumatu. “Wayyo ni Dijangala jikar Fatima da Abubakar ina zan saka raina! Yau nice za’a haifa min shege a matsayinjika. Dankari makari salatin maguzawa” Wannan kenan! 
Da yake Saifyasan Laila batada maraba da Fly over bai yi wani mamaki ba. Sai dai ya nuna mata fushin sa karara. Nan tayita rantsuwa tana cewa a lambu dake kasan layinsu akayi mata fyade. Tabbas akwai lambu amma shi kuma yaga irin text din da sukayi da khadija. Anan ya kawo mata zancen. Gabanta yayi mummunan faduwa saboda ya nuna shi namijin duniya ne. Dukda yasan da zancen bai hanashi aurenta ba. 
Toh yanzu wani zama zasuyi kenan? Narai narai tayi da idanu ta soma sabon kuka. Anan 
tace masa tabbas taje hotel amma babu wanda ya kwana da ita. An gayyace ta ne bayan an bata kudin kafin su soma harka tace tana bakonta na wata. Dama plan dinta kenan tun 
farko saboda ta saka pad a jikinta. Sam zance baya shigan Saif. Rantsuwa take yi da wallahi tallahi, kwarankwatsa duk ta hada tana kuka.
Wani tunani ya fado mashi kila kuma da gaske ne, balle yasan ba zatayi ganganci satin 
bikinta tayi haka ba. Bai dai ce mata komai ba yana kallonta. Tabbas yayi nadamar aurenta. 
A komai Sameera tafita amma bahaushe yace dukwanda aka hadashi da kazar wahala 
bazai huta ba saiya yanka. Baida niyyar sakinta kodan kudin daya kashe mata. Amma 
Kuma zata gurzu har saiya huce. 
Jikinta yanata rawa, hankali yayi bala‘in tashi duk tana tunanin zata koma gidan ubanta ne. Yanzu me zata ce ma Baaba? Haske ? Da Duk kawayenta. Gashi ita dadi miji tabar aiki yadda aiki ke wahala amma tayi watsi da nata. Sannan ita kuma bata iya wani sana’ar hannu ba‘ A sittin taje gefen mirror dinta domin ta dauki Quran kila idan yaga tana rantsuwa ya yarda da ita. Yana ganin yadda ta dauka qur,ani shima a sittin ya bita tareda karbewa. Ajiyewa yayi yana juyawa ya fuskance ta, baiyi wata wata ba ya sharara mata mari. Tana dagowa ya haska mata wani. “Ke dabbar ina ne?” yace a fusace. lta kuma rudewa ta sake yi saboda ta tsorata dashi. Tinda take dashi bai taba daga mata murya ba ko yaji haushinta. Kullum yana cikin tarairayan ta yana bata dariya. Shi kam tsorata yayi ainun kafin taje tayi rantsuwa da qur,ani da karya su kone cikin dakin. Data bari yabar gidan tukun kam tayi ganganci. A duniya 
yana bala’in tsoron mutuwa baya masan zancen. Ko kabari baya zuwa balle yayi sallan gawa. Ko sanda babansa ya rasu gudu yayi da za’a tafi Neman sa akayi ko sama ko kasa amma ba‘a gansa ba. Haka aka hakura aka tafi banda shi. “Ki rufe min baki kafin matana taji inji kunya” yace mata cikin tsawa. Kodan karya kunyatu wajen Sameera bayan yace zai aure yar fara yar shila bazai ma iya sakin Laila ba. A yau taci albarkacin matarsa. lta kuma da hannu tasa ta rufe bakinta Saboda bata iya tsaida kukan da kanta. A hankali ta soma kallon sa tareda magana, “Ka yarda dani kenan? Girgiza mata kai yayi alamar eh. Ta wani wajen a nasa tunanin yana bama kansa laifil. Da yana sake ma Laila kudi kila da batabi maza ba. Balle dole ya nuna mata babu komai kafin ta dauko Qur,ani tajawo masu. Wannan kenan! 
Kashegari kamar babu abinda ya faru. Sai dai idonta yayi kanana saboda kuka. Amma tayi wanka ta zambada make-up kamarzata biki. Sannan ta saka riga off shoulder tareda bra acuci wanda ya kara mata dari. Abin ya burge Saif dan kam saida sukayi ta barkwanci. Nan tayi murna sabida ga dukkan alamu Saif gara ne. Kitchen taje ta soya masu dankali da kwai. Dama ya siyo kayan shayi. Dab da Dankali zai sauka saiyaje dakin
 Sameera. Kamshi ya fara tarban sa na abinci, anan yaga ta soya masu doughnut dajam da tea suna sha. Ga doughnut yayi kashar kashar amma babu halin ci tunda bashi ya siya ba. Ransa ya 
biya ainun sai hadiye yawu yake amma Kota kalle shi ta wannan fannin. Ita ma taci kwalliya tasa atamfa dinkin boubou. A ladabce ta gaida shi tareda tambayan lafiyan Laila. Shi kam gogan da kyar ya amsa yana shan Kamshi. Balle ya saka sabon kaya wai shi ango. Su Abul 
khair suka je wajensa suna wasa tareda tambaya inda ya kwana. 
Haryanzu haushin ta yake akan Dankali, gashi kuma yanzu tayi doughnut kuma daga 
dukkan alamu bazata bashi ba. “Yanzu kizo dakin yar lele inajiran ki” sai ya fice.Takaici taji sosai wai ita zatabi amarya daki. Dama miji ke siyan maka mutunciwajen kishiya kuma 
bata tsammani Saif zaiyi haka. Koda ya Koma Laila ta gama soyawa ta saka a wasu kwanan tangaran fari da lemon mai kyau. Ta hakince tana kallon hausa fllm tunda batada decoder. 
Mikewa tayi cikin rausaya taje ta rungume shi, shima ya ware hannu sosai harda dagata sama.”My Destiny nayi kewarka daga mar ka” Shi kuma ya sumbaceta a baki. Yasan babu mamaki Sameera ta ganshi kuma tunda ta hana shi doughnuts saiya kunsa mata bakin ciki. Ita kuma Sameera mamaki take yanada yara uku kuma yanada kamfanin ruwa amma 
baya kula dasu. Ba tace ya ciyar da ita ba amma atleast yayi ma yaran sa. Tunda shi yanzu 
ya nuna kamar kwalta yake ba’a banbaransa. “ 
A makale da juna ta riske su, murmushi tayi wanda ya bayyana wushiryanta saita ce, “Amaryar mu gaskiya kina rikita Babansu Abul” abin yabama Laila haushi wai baban Abul. Sai dai ta kanne, “uhmm ya zanyi” tace sai suka shiga ciki duka. A lokacin Sameera taga dakin da kyau. 
Baida kala daya da zakace ko purple ko blue ko brown. Duka komai akwai kamar rainbow. Purple kujeru, jan labule, centre rug almy green. Gashi Saifyayi fenti orange Dukda tace yayi mata purple ko milk. Ganin dankali da madaran gwangwani da tayi akan centre table yadan taba ta. Kujera ta samu one seater ta zauna. Su kuma suna kan two seater inda centre table yake. Anan ya rinka hada masu shayin yana yi yana dariya. Bata ce uffan ba banda mayar da hankalin ta kan TV dake aiki. 
Saida suka ci yaf’l rabi ko tayi basu yi mata ba. Abin yayi ma Laila dadi saboda yadda Sameera ta kwashe mata lefe. Sunaci suna iya shege mutum daya yakai dankali bakin dan uwansa kamar zai bashi sai kuma a dauke ana dariya. Daga bisani Saif ya Kalle ta yace, “Sameera kiyi hakuri fah, bari na gama karyawa da mai daki na ….. Bismillah” Ai ba damuwa ni dankali ya fita kaina kojiya da daddare shi mukaci, kwanan nan cin hauka mu ke masa. Balle kuma bana cin dankali tsura garau garau babu sauce k0 ketchup. Yanzu hankali na zai tashi” tace tareda yatsina baki. Ba Laila ba har shi Saifyaji haushi. Magana ta gaya masu. Gashi tana yi kadan kadan kamar babu lakajikinta. 
Bayan sun gama ci saiya soma magana, yana yi yana sakuce kamar yaci kaji. “Yanzu nayi amarya. Bakin alkami ya bushe kuma yan bakin ciki sai dai su mutu” Mamaki fal fuskan Sameera dan bata san wake masa bakin ciki ba. Sai dai kuma tayi shiru kamin ya dizga ta gaban Laila. 
“Nifa bazaku maida ni mutumin banza a gari ba kuce zakuyi dambace dambace akai na…. Eh duk da nasan nayi haduwarda mata zasu rinka rubibina amma kune kukaci gasar samuna… Mata gasu bila adadin sunyi kwantai amma kun samu ina rike ku cikin mutunci na ciyarwa da shayarwa. Ga kuma tufafl sannan muhalli mai kyau. So better behave yourself banda kishi mai zurfi” ya karasa yana mazurai. Dariya Sameera tayi saboda sai dai ya gayama Laila ba ita ba, tasan halin sa kamartafin hannunta. Laila kam murmushi takeyi tayi dace da mijin kwarai. Anan ya cigaba da magana, “Ke Sameera kece babba, kija girman ki karki raina kanki. Dan idan baki kama kanki ba babu abinda ya shafeni idan amarya ta nakada maki duka. Kinga anyi babban banza kenan” ya gama magana cikin izgili yana dariya wanda itama Laila ta dara. Sameera kam shan kunu tayi. Sai ya kalle Laila dake cika tana batsewa “Ke kuma Amarya bakya laifI, Allah ya hada kanku” 
Zungurinsa Laila tayi da kafa tana magana kasa kasa, “Destiny fridge dinfa .Shiru yayi gabansa yayi mummunan fadi saboda ba Fridge dinsa bane, Yanada fridge dan karami na gefen gado sai ya lalace. Sameera takai aka cika shine aka bata Samsung babba. Duk ya rude ya soma rawar baki kafin Laila ta gane makaryaci ne ta raina shi. Yasan bazata dauka abinda yake ma Sameera ba. 
“Dama Amarya zata rinka saka kaya ne a fridge idan ta bukaci haka” ya fada cikin gadara kamar nasa. “Babu damuwa ai, an zama daya” tace cikin raha. Laila kam haushi taji amma ta hakura kafin ya disga ta akan abin jiya. Kallon Sameera takeyi atampha jikinta yayi mata kyau, “Ba mamaki nawa ne” ta ayyana a ranta tareda watsa mata harara. Sannan kuma tabi jikinta da kallo daga sama zuwa kasa. Babu haufi duk abinda Saifyake fadi gaskiya ne. Yana rike gidansa yadda ya dace saboda fatar Sameera abin kallo ne dukda tana bakar mace. a 
Abin yayi mata dadi ta samu miJi gangariya ajin farko, dukda yanada mata baida maraba da saurayi, sune sukazo duniya da kafa! dama. Babu ruwanta ita dai kawai a kawo mata, 
taci ta koshi ta kuskure baki da Fanta. Yanzu zataci karenta babu babbaka. Sameera ta tashi tayi masu sallama saita tafi Koda ta koma daki gado tahau ta kwanta. Hawaye ke malala mata daga idanu. Saif baida mutunci na karshe. Gashi bata mashi komai ba balle yace laif’lnta ne. Yan Lalle ne suka zo wanda yasa ta daina kuka domin tayi masu. Dashi take rufawa kanta asiri wanda Saif ke kokarin tona mata. Wannan kenan! u 
Wajen 12 na rana Haske ta samu hutawa, yanzu babu Laila aiki yayi mata yawa kafin a samu wanda zai maye gurbin ta. A lokacin ta raba kilishi domin ta kai ma Haisam. Tana kallon abin sai taga yayi simple dayawa. Shago na wajen taje domin ta siya lemu, chi exotic ta siya ta hada mashi dashi. Kirkinsa yayi yawa yasa take so ta saka mashi. Bama wannan ba tanaso ta kwanltanta yin haka ita ma. Koda taje baya ofishin da aka ware mashi, saita ajiye masa zata fita Tana saka hannu akan mabudin kyaure kenan ashe Shima zai shiga sai suka ci karo. Zakaga jin dadi karara a fuskansa. “Sister kece a nan?”
“Eh na kawo maka abinda Mommy ta bamu ne” kallon kan tabur dinsa yayi tareda kallonta itama. “Okay mu zauna muci tare zaifi albarka“ ya fada baiko kalleta ba. Wucewa yayi cikin ofishin tareda ajiye kayan hannunsa. Ba kayan daya sanya dazu bane, yanzu riga da wando ne blue iri daya irin na Doctors, sai kuma Labcoat akai. Sannan ga stethoscope a wuyasan. Juyawa tayi tana kallonsa sai tayi murmushi, Kayi hakuri Haisam babu kowa kan tabur dina maybe wata rana“ Tunda yake ba’a taba kiran sunarsa haka ba. Salonta daban yake 
ba irin na sauran jama‘a ba. He could feel the respect sanda ta kira sunarsa. Gashi kamar 
da forne tayi abin. Yaji dadi sosai ko wannan ya isa ya saka shi murmushi gabadaya ranar. Bai iya magana ba saiya girgiza mata kai alamar ya gane. Murmushi ta bisa dashi wanda baka rabata dashi saita fice. “Yesssss” yace tareda naushin iska. Saiya zauna akan kujera kuma ya daura kafa sa kan tebur. Yanayi yana karkada kafa yana raha saiya dauka kilishi ya soma ci yana kurban lemu. a 
“Haiiiisam” “Haisammmm” haka yayita yi yanaso ya tantance wanne harafi m ja da yayi mashi dadi haka. lta kuma Haske koda ta Koma Bilal yayi mata 3 missed calls. Gabanta ya fadi duk 
tsammanin ta yayi hatsari ne ake neman ta. Lafian Bilal kalau bazai kirata sau biyu ba. Sai dai idan network yayi haka wayar ya shiga amma bai sani ba yanata trying. 
Da azama tayi redialing kuma cikin bugu daya ya dauka. “Sweet ina kika shiga, kinsan bani 
san kiyi nesa dani” ya fada cikin wani siga. lta kuma lumshe idanu tayi “Afuwa sweet gani yanzu koh” “Ina zaune naji kamar za’a kwace min ke yasa kikaga na rude, please sweetie idan na kiraki 
ki rinka dauka nan take” Dariya tayi mai sauti kamin tayi magana. 
“Karka damu Sweetie dina, ni taka ce to love and cherish, all that I am and all that l have is yours”
shiru yayi jikinsa yayi sanyi. Lashe bakinsa ya soma saiya share fuskansa duk da babu gumi kuma yabi yatsunsa cikin dogon gashin kansa tareda lumshe ido. Duka kalaman data fada saida yabi duk wani bargo najikinsa. Zuciyar sa ya soma harbawa yana amsa sonta. “Nima naki ne, I am you and you are me. Mun zama daya tamkar tsoka dajini. In dai Badman Bilal ne karki damu Haske kin sameni. Kawai ki sakejiki dani muji dadin soyayya na nuna maki how much I love you“ 
“Uhmm” tace kawai sabida bazata iya kara wani magana ba. San shi ya sake mata wani ruri kamar garwashin wuta. Harbawa kawai zuciyarta yakeyi. Bata gane ma’anar ta bashi dama 
ya nuna mata son saba. lta dai kawai abinda ta fuskanta shine ko wani irin so yake mata Dan Allah ne bawai da kyau ba ko abinda zai samu. San tsakani da Allah yake yin mata yasa ita ma bata tunanin zata iya rayuwa ba tare da shi ba. Idan bata samu Bad a matsayin miji ba duniya zaiyi mata kunci da baki. 
Wajen biyar daidai Haisam ya kwashe komai nasa, sauri yake domin kar Haske ta gaji da jiransa dukda bawai sunyi zasu gida tare bane. Yana isa itama ta mike kenan. “Muje koh” 
Binsa tayi suka jera tare, saida suka kai wajen parking lot saita tsaya, “Okay sai anjima bari naje” ta fada sabida Bilal yayi mata text yana jiranta. “Ana jiranki koh?” yace cikin takaici. Girgiza kai tayi tana murmushi. Shima sai ya mayar mata. Ashe duk abinda akeyi Badman yana kallon su daga cikin mota. 
Haushi ya kama shi wanda saida ya fita yaje wajensu ya tsaya. Kawai a kansu sukaga mutum yana haki. Kallon Haske yakeyi cikin bacin rai wanda saida ta tsorata. Sai kuma ya kalli Haisam ya watsa masa harara. Yana bala’in kishin ta Kuma bayaso yana raba yarinya da mutum. Balle yadda yaga Haisam sai duk yaji wani iri. 
“Sweet ka bani tsoro… Anyway ga cousin dina Haisam” kallon Haisam yayi na hadarin kaji shi kuma ya mika masa hannu suyi musabaha. Baiko amsa ba banda kallon Haske da yayi cikin fushi, “Cousin kuma? Yaushe kuma wannan ya fara?” ’ 
Murmushi tayi mai ban takaici, Bilal akwai rashin mutunci amma bataso yadda yake tsareta haka ba kamar mara gaskiya. Idan da Haisam dukda bata wanisanshi ba bazai yi abinda Bilal keyi ba. “Dazu Mommy take gaya min” 
“I see…” Bad yace ko magana da Haisam din baiyi ba. Tafiya yayi abinsa yana shan kamshi. Haske ta Kalle Haisam saita daga kafada, “Sorry… Zan masa magana” “Trouble in paradise, injin dai banja maki matsala ba” “Karka damu zan mashi magana kuma zai sauko…. Ba haka yake ba” 
Harta tafi ta shiga motar Bad Haisam bai bar inda yake ba. Binta yayi da ido wanda kake ma abinda kake so. Bad yana kallon sa ta tint zuciyar sa yana tafasa‘ Koda ta shiga da sallama bai amsa mata ba. “Bana san kina kula samari, kinsani kuma amma kike so kiga ina hauka. Abin yana burge ki koh?” “He is my cousin, da gaske nake magana” 
“Aure kike so koh Haske? Toh kin samu sai muga dan iskan cousin dazai kalle ki kuma” yace cikin fushi saiya tada mota kamar zasu tashi sama. Haske ta tsorata saboda har ta runtse idonta. Baya san competition kuma Haisam bai isa su fafata ba. Gwara tun wuri yaci gasar tun abin baiyi nisa ba. 

Wannan kenan! 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *