HASKE
CHAPTER 11
Bayan wasu kwanaki
Haske tayi wuyan gani a wajen Haisam, duk yanda yaso ya ganta su kebe koda na minti biyar ne abin ya faskara. Idan yaje tabur dinta baya rasata tana rubuce rubuce. Gaisawa kawai sukeyi saita sha kunu ta cigaba da abinda take yi. Ko gidansu yaje baya ganinta a falo. Dama bata iya abin ba tun farko.
Idan kuma da safe ya tsaya a bakin gate domin suje motar Bad yake gani yana jiran ta duk yayi babakere dole ya hakura ya tafi shi kadai. Wannan shine yaga samu yaga rashi. Ya lura tun randa suka hadu da Bilal ta dauke mashi wuta. Wutar da tun kafin su san su yan uwane. Dan kam da chan tafi sakar masa fuska akan yanzu. Kuma wajen 4:30pm Bilal ke zuwa haraban asibiti yajirata. Sam yanzu baya barinta tasha iska taji dadi. Bai taba ganin tayi ma wani murmushi irin wanda yaga tayi ma Haisam ba shi, yasa yake killace abinsa.
Ita kuma Haske Badman ya sheda mata ba’a raba mace dashi. Baya neman yarinya kuma wasu samarin suna neman ta. Idan yaje waje dole a buda mashi a bashi hanya. Gamji mazajen dawa, dodo kowa yana tsoron ka. Irin kashe din daya bata yasa ta shafa ma kanta da Haisam lafiya. Tasan baya sonta amma tunda Bilal yace baiso kawai a barshi haka. Bad zata aura dole ta koya ma zuciyarta son abinda yake so tun kafin ta shiga saboda daga nan idan anyi auren zata saba.
Sai dai kuma duk ziryan da Haisam ke mata akai tana ankare dashi, abin ya soma wuce yan uwantaka, daya matso dab da ita saita soma rubutu. Abin dariya yake bata yadda duk ya damu. Zakaga fuskan sa da damuwa fal ga kuma dukjikin sa yayi sanyi. Tasan menene so, tasan zafin sa, tasan yadda yake dawainiya da mutum. Zafinsa yafi zafin harbin mashi a kirji, kokuma a watsa ma mutum garwashi. Idan zuciya ta karkata tace ga abinda takeso to rashin samunsa zai iya zama baraza ga wanda ya hanata. Komai tsaya maka yake idan kana san mutum, tasan duk wannan sanda take tareda Bllal wanda sai kwanan nan ta soma samun kansa yadda ya dace inda zuciyarta ya sanyaya. Kuma fuskan Haisam tsantsan soyayya yake nunawa. Sai dai abin da bata sani ba shine tun yaushe yake fama da wannan abu? Kwanan nan da suka san juna na hakika kokuma tun da chan yana dauke da abinsa. Wannan tambaya ne da tasan bazata samu amsar ba saboda tayi alkawarin fita harkan sa balle suyi wani dogon zance.
Wajen 12 lokacin tana hutawa saboda mutane sun ragu, text message ta gani ya shigo daga wajen Bad. “Kizo ta wajen parking lot inajiran ki”
Murmushi ya mamaye mata fuska, Bad is romantic babu karya. Anan ta mike da azama taje inda ya bukata. Dube dube ta soma amma bataga Bad ba balle kuma motarsa. Tana cikin wannan yanayin sai taji mutum a bayama, duk daukarta shi din ne. Lumshe ido (ayi wani san shi ya kara mamaye ta. Magana ta soma tareda juyawa cikin natsuwa, “Sweet ka bani tsoro” ta fada a shagwabance tareda rnakale kafada. ‘
“Ba sweet dinki bane face dan uwanki” ya fada cikin sautin dariya. Daga nan sai ya cigaba, “Yanzu Shamsss guduna kike?”ya fada cikin wani siga mai sanyi tareda lumshe ido. ba tace komai ba illa duba wayanta. Idan ba hauka take yi ba tabbas ‘Sweet‘ yayi mata ‘ext kamaryadda tayi saving.
Hannunsa yana cikin aljihun wandonsa. Yana tsaye yana kallonta gashi dama da kwarjini mai cika ido. “Karki bata lokaci kina dubawa, idonki bai maki gizo ba. Sai dai ba Sweet dinki da kikayi saving bane. Wannan dan uwanki ne. MTN ofis naje sukayi customising suna irin na bulk SMS sai na saka Sweet a matsayin mai tura sako. lrin yadda su bankuna da sauran masu talla keyi. Sau da dama Naga kina waya da Sweet wanda ya taimaka min waien iawo hankalin ki, bature yace ifthe mountain can’t go to Mohammad. then
Mohammad should go to the Mountain” !
Duk abinda yake cewa kawai kallonsa takeyi, wannan neman suna da daukar ma kai wahala na menene? Tunani kala kala suka rikito mata. Batasan Kotaji dadi ba kokuma taji haushi. Sai dai kuma babu haufi tun da take ba‘a taba nuna ana san ayi mu’amala da ita ba haka. Ya nuna mata tabbas yanaso su rinka mu’amala. Amma kuma wani irin mu’amala yake so? Ita bazata iya bari wani abu ya shiga tsakanin su ba banda yan uwantaka. Me kake yi haka Haisam?” ta fada fuska babu yabo babu fallasa. “Let’s go to the movies?” yace mata. Runtse ido tayi bataso ta yarda da abinda zuciyarta ke raya mata. Ta riga ta sallama ma Bad zuciyarta da komai nata. Haisam ya bala’in makara yanzu. “Please Haisam ka bari, banso kaja ma kanka matsala k0 ni. Balle muna wajen aiki yanzu” tace cikin damuwa
“Toh sai muje idan an tashi, kallo kawai zamuyi, idan kuma yayi tsauri sai muje muci abinci. Why can’t we hang out? Kefa yar uwata ce? Me yasa kike guduna? Idan laifi nayi maki meyasa baki fada min ba? Koko shiya hanaki magana dani?” ‘
Dab da ita ya soma matsawa ita kuma tayi tafiya biyu baya, kwarjinin sa kawai takeji. Runste ido tayi, ta lura Haisam bazai gane ba. Baya maso ya fahimce ta ya kyale ta. Hawaye siriri ya soma ziraro mata daga idanu, kadan kadan sai kuma da gudun famfo. “kayi hakuri ka kyale ni, bansan ka wahala saboda ni” “Too late” Dariya tayi mai ban takaici, saita soma goge fuskanta da ta. Haisam yayi nisa da dukkan alamu. Amma bazata bari ya ruguza mata rayuwa ba. Yanzu ta samu Bilal zai aureta. Dole ta kiyaye ta bi dukkan dokokin daya gindiya mata. In fact Haisam karamin yaro ne. Bata tsammani k0 zai girmeta. Ko zasu zo tsara kokuma zatama girme shi. Bazata iya barin Bilal ba wanda al’ada ya nuna dole saika aura wanda ya girme ka da shekaru aru aru idan ba haka ba zaka tsufa da wuri yayi maka kishiya. ‘ Zancen kishiya baya ma wani damunta, idan zata iya zama da Ammi to fa zata iya zama da kowane mahaluki a duniyar nan. Wannan ba dokokin ta bane, al’ada yazo da haka. Bata taba jin wanda ya aura age mate dinsa be a Kasar Hausa. Ba garin turawa bane balle ayi haka wannan Arewacin Nigeria ne. ‘
Haisam yanada hankali flye da shekarunsa, k0 cikin sa‘o‘insa a asibiti ya fita daban, magana yake yi cikin hikima da basira. Tsab idan ba’a fada maka ba zaka sha yakai 27yrs amma kam baifi 23. Itama haka take saura sati biyu ta shiga. Amma batasan kwanan watan sa ba. Zai iya yiwuwa ta flshi ko ya fita, sanda yazo farko yana cika form duk ta gani a wani ofishin dataje abu.
“Kayi hakuri, karka bata zumunci saboda san kai da san Zuciya… Please… Haisam banso kaja min matsala…” saita fashe da kuka. Bai hanata ba Shima da zai samu zaiyi. Salon maganar ta da kuma yadda take kiran sunansa kamar ingiza shi takeyi. Bugun kirjinsa sai ya kara tsananta, numfashi kam ha a daidai yake yi ba. Bayaso yaga kukan nan, baiso kwata kwata. Dama sharara mashi mari akayi zaifi samun sauki akan dirar hawaye daga idonta. She is too precious to him. Nazarinta yayi yana kokarin tantance abu. Daga dukkan alamu kamar tana tsoron saurayinta. Wannan wani irin soyayya ne dayake firgita ta haka? Me yasa take zaunedashi? Na gaya maki it’s too late, yanzu ina cikin rayuwar ki… Banyi kuma tsammani zan iya bari ba” Abunsa ya daina bata mamaki illa haushi yanzu, wai ya tafi mana. Sai wani zuciya yace mata gudun me take? Ai bai ce yana santa ba. Alamu kawai take gani. Kuma maganar shiga rayuwar ta ai shi dan uwanta ne dole su rinka haduwa jefi jefi. Saisaita kanta tayi ta kalle cikin idon sa, “Me kake so daga gare ni?”
“Yanzu!!!! Uhmmm!!! Muje movies, ko restaurant… Kawai mu fita… Ni da ke ina son sanin ki, labarin ki, me kike so… Duk dai abinda ya shafe ki… Daga nan kuma zan fada maki abinda nake asalin so
“Okay…. Ka bari weekends zan samo mana time” “Uhmmm Uhmmm” cikin shagwaba yace “toh me kake so”
“Muje yanzu, mu dauki excuse family emergency Sai mu tafi. Nayi maki alkawari kafin 4:30pm zan dawo dake nan kafin najawo maki matsala. Bazan taba bari wani cutarwa yazo gareki ba muddin muna raye” “Okay naji, daga yau ba zamu kara fita ba. Kazo ka sameni bayan azahar”
Naushin iska yayi sau uku yana jin dadi. A hankali zai samu ‘Hasken Annurinsa
Abin duniya yayima Ammi cinkoso, batada aiki sai sumbatu.‘ Bazan kunyatu ba’ take ta nanatawa. Daga takai mari sai takai gauro duk ta soma flta hayincinta. Bataso kowa yasan zancen kafm ace mata ‘alhaki kwikwiyo’ kokuma ‘kaikayi ya koma kan mashekiya’ a
Gashi Fijr ta rantse bazata zubar ba, Doctor yace zata mutu kuma akan kunyar duniya bazata salwantar da rayuwar ta ba. Anan Ammi ta tuna da wata kawarta wanda suka yi ABU a Maiduguri mai suna Hajia Yagana. Nan ta kirata ta sheda mata dukkan abinda ke damunta. “Kukan ki yazo karshe Hadiza, kedai kawai kizo wajena. Ina da wani malami chan gaba da Mandara inda zan kai ki” Sosai Ammi taji dadin wannan shawara kawai yanzu ita da Fijr zasu tat1.$annan kuma zata tambaya Daddy akan zata bikin yar Hajia Yagana ya matso. Da kyar ta iya shawo kan Fijr akan ta yarda suje. Ita tace duk zancen cire ciki beta so. A yau Fijr ta samu abu daya wanda take tsoro tunda tazo duniya. Wajen boka Ammi tace zasu inda Fijrtace ta samu damar neman Isi a madubin dubarudu. a
Karyan da Ammi tace zatayi shi ta labta mashi, banda bata kudi na gudunmawa baiyi komai sai kuma addu’a. Yaji dadi sosai saboda Haske zata koma wajen sa da zama har Ammi su dawo. Sai dai yaga sati biyu abin yayi yawa. Nan tace tanaso ta koya ma Fijr sana’a na turaren wuta dasu dilke tunda boko ya kita. Hadima sosai yayi ma Haske na kayan sawa da kayan abinci. Vasan zata lura dashi kamar yadda shi ma zaiyi. Koda yake tunda yayi kudi Hadiza tana kokari wajen masa hidima babu laifl. Ranar tafiya baya sukayi, sun soma shiga train ya maida su Abuja kafin suka shiga jirgi inda yakai su Maiduguri. Hajia Yagana hamshakiyaryar siyasa ne wanda idonta ya fedare da rashin tsoron Allah. Ko Sanda suke school lokacin ana SUG tayi naflonal treasurer. Driver dinta yaje har airport ya dauke su. Wani arniyar mota ne wanda zai tafi da imanin ka. Dama gata kin yadda association(kaudi). Ammi itama taji dadi yadda taje da manyan lesussuka da super ita ma baza’a raina ta ba. Gidan Hajia Yagana abin kallo ne tunda dan jam’iyan su yaci gwamna. ltama ta ‘saya takarar yar mijalisa ta kasa amma bataci ba. Yanzu kawai tana facaka da kudi abinta. Ammi
tako raina kanta tayi niyyar tayi mata kaudi amma wannan tafl karfln tunanin ta. Haka tayita bin gidan da kallo tana tunanin yadda zata cema Daddy suma ya canza masu.
An sauke su a dakin baki inda zasu huta kadan kafin su fito suci abinci. Wannan daki inda ake kira na baki yafi dakin kwanarAmmi. Anan kam tayi kishi da ita harda watsa kananan magana, ‘Mutum yanada yan uwa a kauye amma shine yake zaune a irin wannan babbar gida, wasu duniya kawai suka saka a gaba‘ Wajen dinner akayi buffet din abinci kala kala, daga Arabian cuisine, Italian Sai Kuma Nigeria duk wanda ka zaba. A lokacin Hajia yagana ta fito cikin wani arniyar leshi. Fatarta yayi luhu luhu kamar zai fashe dan kyau. Tana tafe tana takama baka ganin komai sai hakorin Makka guda 4. Biyu a sama biyu a kasa. Sosai ta burge Fijrsaboda itama tanadajiki kamar ta. Ammi kam yake takeyi saboda a duniya bataso ka fita. Sun rungumejuna tareda gaisuwa na yaushe rabo, anan Hajia Yagana ta kalle Fijr taji batayi mata ba. Duk gashin kanti da kuma mugayen kaya ga kirji kamar an rungume agwagi. Fijr bata kara gashi sai bata gaban Daddy, yana tafiya ko awa bata karawa zata kasuwa suyi mata kitso. Anan aka zauna ana cin abinci, yaran Hajia Yagana uku sai sauran yaran mijinta ne wanda tayi sanadin korar uwarsu. Akwai Falmata, Hauwa da yaronta Ghali wanda shi ne babba. Sune zaune sai gashi yazo Shima zaici abinci. Dawowarsa kenan daga Australia ya gama masters dinsa. Dayake Hajia Yagana ta riga su Hafsa aure Ghazali ya girme Haske. Aikam ya tafl da imani Fijr nan ta sake baki tanata kallon sa. Gaida Ammi yayi har kasa a mutunce saiya zauna. Yana cin abinci sannu a hankali da earphone a kunnen sa. Su Hajia Yagana da Hajia Hadiza anata kwasar hira. Fijrtayita so su hada ido da Ghali amma yaki kallonta. Yana ankare da irin kallon datake binsa dashi. A duniya kuma baya san kallo, wai ka saka shi a gaba kamar hoto. Abin yana takura mashi lamura. A sanyaye yayi magana yadda zataji “Kejuyar da fuskan ki” saiya dake. Duk falon kowa kuma yaji shi. Hajia Yagana taji haushi saboda sam bazata hada dangi da Hadiza ba, daga ita har yaranta watsartsu ne. Haka Fijr tayi abinda yace wanda batada kunya balle taji, amma kuma taji nauyin sa wanda ya kara burgeta. Wannan shine ribar kafa wai kura tayi tuntube da kwadoA Gashi zata zubarda ciki ta hanya mai kyau kuma ta samu miji tsalele wanda yafi Isi komai zata aura. [
Dayaga kallon bazai kare ba sai yayi kwafa ya dauki plate dinsa da robar ruwa ya ‘afi. Hajia Yagana ne cikin raha tayi magana, “Kinga kin takura ma yayanki harya tafi, baya san kallo wallahi” “Ai gayen ya hadu ne babu karya yasa na shagala” tace tana dariya. “Dankari” Hajia Yagana tace cikin ranta. Kashe gari Fijrsun shirya za’a gidan boka, taso ganin Ghali amma abin ya faskara. Masu aiki suka ce da azahar yake fitowa tunda ya dawo Naija. Abun bai mata dadi ba amma kuma ai suna tare ko cikin dare zata dakinsa ta bashi hakuri ‘unda an zama yan uwa. Fijr da Driver 3 gaba, sai Yagana da Hadiza a baya anata hira ana cin tufa da inibi ga AC na watso su. Sannu a hankali har suka kai chan wani kurmusun daji ne inda zasu karasa da kafa. Ammi gabanta yayi mugun faduwa saboda kana ganin wannan bokar hatsabibi ne. Ashe kam sunar sa ma kenan.
“Hatsabibi dan gidan kandanbolo, shugaba kaba kaba wanda gidan su babu mai hankali sai wawa. Na kawo kaina gareka neman taimako” Hajia Yagana tace gwiwa biyu a kasa.
Suma tun kafin su isa tayi masu sheda haka zasu yi. Dariya ya rinka yi sai ya soma sumbatu daga nan yace, “Kejiki shiga cikin tukunyar chan” ya Kalle Fijrtareda nuna mata wani tulelen tukunya akan murhu. Ammi murmushi tayi saboda tun kafin ayi magana yasan da zance. “Jar uba! Nine zan shiga wancan kazamin abun” Boka kayi hakuri wallahi zata shiga” Ammi tace tareda finciko Fijr. “Ke dan ubanki girka ki za’ayi. Bayan nan cikin zai kwanta bazai sake girma ba. K0 nanda shekaru ne. Idan yaso kin samu miji sai a tada, Kinga za’a haifa gidan uban sa” “lsi ne fa uban sa” tace tareda tura baki “Jiminja’irci irin naki” Ammi tace cikin takaici. Anan Fijrta hakura, dakyar ta samu ta shiga Sabida girma. Anan Ammi ta rufe sai ta koma tayi kneel down. Nan boka ya rinka sumbatu hayaki yana fita daga cikin tukunyar. Anyi kusan awa sai yace Ammi ta bude ta.
Tsamo tsamo kamar kazar mayu ta flto duk ta flta hayacinta. Anan Ammi tace ta tambaya inda Isi yake, “Karki damu Ammi na samu wani” “Kika samu uban wa? lnjin dai ba Ghali dina ba” Yagana tace. Murmushi tayi alamar eh. Nan ta Kalle boka tace masa kada ya bari wani alaka ya hada su. Ammi taji haushi amma babu yadda zatayi tunda ko ita ne bazata bari ba. Fijr tana gunguni tabar wajen amma ta dauki alwashi saita samu Ghali. Koda boka koda mallam, ko yana 50 kc baya so saiya aureta. An basu maganin da Fijr zatayi amfani dashi na sati daya. Koda suka koma gida Hajia Yagana tace su tattara kayansu su tafl tunda dai sunyi abinda ya kawosu. Da kanta ta biya masu kudin jirgi kam su jawo mata jangwam. Suna cikin mota zasu fita Gate sai Fijr taga Ghali yana zaune a wajen Mai gadi yana hutawa. Daga mashi hannu tayi amma ya watso mata harara. Ko ajikinta saita hura mashi kiss tana dariya. Koda boka koda mallam, ko kana so ko baka so saika aureni Sweetie ” tace da karfin tsiya wanda dole yajita. Wannan kenan!
Saifya lura Laila batada hankali ko kadan, irin dabaran nan wai na mace bata iya ba. Kudin daya bada cefane iya girkin take masa. Babu kari ko kadan. Haka zata kawo mashi abinci garau garau babu armashi. Tun yana dannewa harya somawa cijewa.
Ita kuma ragowar kwan da kuma kayan miya ta kai dakin Sameera. ta saka nightgown ko mayafi babu ta wuce dakin. Batayi sallama ba illa daga labule ta fara zare ido, dakyar ta iya cewa ‘sannu‘ dadin abin Fridge din baida nisa da kofa. Kanta tsaye babu abinda ya shafe ta taje ta bude. Nan ta shiga matsar ma Sameera kayanta. Duk abinda take yi Sameera tana tsaye tana kallon ikon Allah, Dama ta fito ne daga kitchen domin ta dauki tafasarshen nama cikin fridge wanda ta ajiye.
Mubina tazo wajen Laila domin tayi wasa da ita, yar shekara uku da doriya amma ta ingije ta. Dayake yaro baida wayo bata damu ba. Sameera ta karasa wajen ta janye ta, “Zo muje kitchen Mubina ki tayani daka” “Zan bita dakinta ne” yarinyar tace kamar zatayi kuka. lta kama Sameera batasan abinda Laila zatayi mata ba idan sun hadu su biyu.
Daukar ta tayi ta saba a baya, anan Laila tayi gaba itama Sameera tayi abinda ya kaita fridge. Abinci takeso tayi tana marmarin dambun shinkafa. Ta tsinci zogale sannan ta
sassama nama mai uban yawa domin daga ita sai yaranta. Saif saura kwana 1 ya dawo
dakinta inda zasu rinka raba kwana dai dai.
Laila ranar macaroni tayi mashi da miyan kwai. Yasha uban barkono wanda sai kayi amfani da ruwa kayita korawa. Gashi tayi mashi magana ya siya siga saboda tayi masu zo’oo amma yaki. Duk zatonsa zata kwance asusu ta dauki kudima ta siya amma batayi ba. Dayaga ta kawo mashi ruwa tsura bakin ciki kamarya turnuke shi. Ko babu dadi basa kwana biyu Sameera bata barin su babu kodajollyjuice ne. Zuwa yayi dakin Sameera domin ya dauki wani shadda dinsa. Koda yake da biyu yayi, yaje yaga ko tayi abinci ne yaci. A falo yaga sun zauna suna cin [aflyaryan dambu mai uban nama da kayan hadi. Ga kuma ginger gefe suna korawa. Har zai wuce haka sai yace bari yayi mata magana. “Ke kam Sameera bansan inda kika koya mugun hali ba, tunda nake dake baki taba irin
wannan dambu mai kyan gani ba” yace yana mata raha. Dakewa tayi sosai. “Ai Kaine baka bada kudin cefane isarshe, iya kudinka iya shagalin ka” “Karfa ki gaya min magana dan ina wasa dake, yanzu zan saba maki ainun” saiya soma taf’lya. Harya kai bakin kofa tayi magana, “Na zuba maka dambun ne?” murmushi karara fuskansa. Bai waigo ba ya amsa, “Ki saka a cooler kiba Abul Khair ya kawo min” Ciki ciki ta amsa yadda bazai jiba, “Ai bance dayawa zan baka ba” Kitchen ta wuce ta dauko cooler mai uban kyau tasa masu harda Laila. Sannan ta zuba Gingera gora ta bada akai mashi. Yana zaune da boxers a falo yanata jira. Abul Khair ya gani tuni ya soma murmushi. Baisan sanda yace, “Allah sarki yar albarka kin cika alkawari” Laila tana daki taji yayi magana. Duk zaton ta da ita yake yi.
“Me nayi Destiny?” ta fada fuskanta zallan annuri. Tana ganin cooler ta dake, “Meye wannan kake ci” baiko tanka ba ya wuce kitchen ya dauko cokali. Itama Laila abin ya biya mata rai, nan ta sake fuska sosai. My Destiny ina ka samo mana dambu?” MANA da tace ya bala’in bata mashi rai. Tanada bala’in kwadayi banda zubar da kai ina ita ina cin abincin kishiya. “Ke yanzu da rashin kintsi abincin kishiya zakici salan ta raina ki”yace cikin takaici. Kallon kofa tayi bataga kowa ba sai tace, “Ai bazata sani ba” saita wuce kitchen dan ta dauko cokali. Loma biyu biyu Saif yayi kafin ta dawo. Kadan ya rage mata saiya basar.Kashe gari tana ninke mashi kayan sawa dinsa. Sai taga dubu goma. Anan ta dauki dubu hudu domin tayi masu cefane. Bai lura ha ya saka kaya ya flta abinsa. Haka tayi mashi text akan ta taf’l kasuwa. Duk zatonsa kudinta ne harda shi mata albarka cikin ransa. Ita kuma ta je Abubakar Gumi central market wajen layin yan nama. Bindin shanu ta siya 2k. Sai ta siya sauran abubuwa datake bukata wanda har saida ta cika 500 dinta. Yan Lalle sunzo ana yin masu, gashi yanzu ta soma saida su turaren wuta, kasko, sagem, mahallabiya da kuma turaruka. Kudi take caska abinta purse dinta sai girma yake yi. Laila kuma tasa riga English wear Off shoulder da pencil skin. Sai shige ta flce take yi tana rawar kai. Wata mai Lalle tace “Maman Abul Khairan maki Amarya ne?” “Eh wallahi” “Aikarn yar gayu” “Uhmm”
Shi kuma Saif mai yakai shi dirga kudinsa sai yaga bai cika ba. A lokacin ya lura da kudinsa
taje cefane. Wannan asalin ja’ira ce kuma yau saita yaba ma aya zaki. Idan yaso ya kunyatu wajen Sameera duka ya hada yayita duka. ‘
Tana waje ta flto da shara, gida makil yake da yan lalle. Sai gashi ya shiga. Cikin rawar kai ta ajiye Parker da tsintsiya ta nufa wajen sa cikin. Ware hannu tayi zata rungume shi. Daga murya yayi ya daka mata tsawa. “Ubanki yaci uwatai! Waye ce ki daukan min kudi?” a hankali ta soma siyasa yayi shiru ga mutane hankali yana kansu. Shi kam ya rufe ido bala’i yana cinsa. ‘ “Wallahi ko ki biyani kudina kokuma yau na shiga fatarki da duka saina fansa adadin asarar da kike min” Kunya taji sosai babu kama hannun yaro. A hankali ta koma dakinta domin ta samo mafita. Wani zuciya yace ta kira Haske ta ara mata kudin. Wannan kenan!
Haisam yace mata su tm wani sabon Chinese restaurant a Waff road. Taji dadin wajen sosai saboda ba wajen zuwan Bilal bane. Baya ta’ammali da Chinese. Sunje sunata raha inda suketa dariya. Ta mance yaushe rabon datayi dariya haka. Ashe Haisam idan ya samu waje akwai barkwanci. Sai tsokanar yake yana mata dariya. Daga nan suka fadi labarin kansu sama sama. Ashe shima yana san poetry kamar ita har yayi mata alkawari zai rubuta mata wani. Sannan suna san animation na Boondocks. Waka kuma suna san Simi, Jonny Drille da J Cole. Haka dai abubuwa da yawa suna so iri daya wanda duka batada wannan like din da Bilal. Basuda abinda suke so tare sai turare wanda shima Haisam nasan abin. Bilal yayi sabbin customers wanda zasu canza naira zuwa Yen kudin China. Sai suka ce yaje Chinese Restaurant na waff Road domin su hadu. Yana kallon time yace bayan nan zai wuce Barau Dikko wajen dauko Sweet dinsa. Har ya basu ya kusan fita sai yaga kamar Haske daga chan kurya. Karasawa yayi kuma babu haw itace tana dariyarta mai flrgita samari. Haki yakeyi yana numfashi sama sama ya masu saukar ruwan sama. Daga Haisam har Haske suka tsorota. Tsaye ta mike ta Soma rawar baki. .
Da kafa ya tokare tabur din wanda komai saida ya tamatse Shima Haisam ya mike tsaye. Kallon kallo suka soma suna mazurai abinda Haisam bai taba yiba. Haske ta shiga tsakanin su tana kuka. Kallon Bad tayi “Dan Allah Sweet kayi hakuri, wallahi nine banajin magana. Please kar Kuyi fada” bai ko Kalle ta ba balle ya kulata. Yanata watsa ma Haisam mugun kallo. Juyawa tayi ta kalle Haisam. “Haisam ka Kalle ni” WHY” yace amma bai Kalle taba
“Please Haisam, do this for me” a hankali ya saukar da kwayar idonsa ya daura nata. “Please calm down and go home” tace mashi. Haske ce! Duk abinda tace dole yayi mata. Babu abinda tafi karfi wajen 5a. Hura iska yayi na bacin rai saiya dauki makullin motarsa ya wuce. Shi kuma Bilal ya bishi da harara. Saida ya tafl saiya soma kallon ta.
“Sweet kunnen kashi koh? Kin fiso kiga ina hauka koh? Meye kike name a wajen da namiji da banida shi sai kin kalle wani? Toh kinjawo ma yaron mutane. lcan kill sabida ke kuma kin sani amma kike turani bango” ciro kudade yayi wanda baisan adadin suba. Nan ya watsa ma waiterajiki saboda barnar da yayi masu. Saiyajanye hannun Haske domin su tafl. Wannan kenan.