HASKE CHAPTER 14

HASKE






CHAPTER 14




Tausayin Haisam ya mamaye ta sosai, wani zuciyar ya raya mata meyasa tayi saurin yanke hukunci haka ba tareda tayi dogon nazari ba. Tabbas Manzo SAW yace kaso ma dan uwanka abinda kake so ma kanka, kuma batayi tsammani tabi sunnan sa ta wannan fanni ba. Ranta bai mata dadi ba because she would nevel hurt a fly da gangan.
Magana taso furtawa amma ta nema shi ta rasa. Rausaya kai tayi tareda runtse ido, da akwai abinda zatayi da zai cire mashi bakin cikin nan zatayi, amma kuma koda ta furta mashi Hakan bazai yarda da ita ba. Besides meyasa zai yarda da ita bayan baro baro ta nuna bata san shi. wani zuciyarya tuna mata ita matar aure ce, tunani irin wa’annan basu kamace ta ba. Komai rabo ne kuma dashi rabon ta ne koda batasan shi saita aure shi. Da sauri Haisam yabar gabanta tana kallo harya bace daga idonta. Gate ya nufa bai koma cikin gidan ba. Gaba daya yinin bikin batada walwala, kowa ya lura amma ana alakanta shi da auren datayi. Ammi taje da nata ayarin, dakin Maimuna yarinyar Mommy aka bata. Duk yan oflshin su banda fatan alheri basa mata komai, ita kuma tayita cewa ba amin ba cikin ranta. Har wasu suka ce kamar bata murna da bikin, anan tayi saurin cewa kewar Shamsiyya keta damunta kwanakin nan. Wajen la’asar sakaliya dangin miji suka je daukan ta, Anty Jalila first born dinsu Bilal ce a gaba. Anbi da ita sako sako kowa yayi mata nasiha. A hankali take kuka kana jin shesheka da jan majina. Abinda yasa suka je dawuri sabida ana so kowa ya watse kafin sallar Isha. Duk mesan ganin dakin amarya tun yanzu yaje tunda Jabi Road baida nisa da Yahaya Road. Kowa yayi mata nasiha har Ammi, babu yadda taso a babban falo aka taru daya bayan daya ake ta magana. Daga nan Mommy da sauran yan uwa suka rakata gidanta. Kamar yadda aka ce kafln Isha kowa ya watse. An bar amarya da halin ta wanda zai kwace ta. Text ya shiga mata waya daga Sweet.
“An daura fah, me kika ajiye min?” wannan kenan!
Ranar Laila bata samu damar zuwa bikin ba. Mahaifiyar Saif zata gidan a karo na farko domin taga dakinta. Kwana sukayi suna tashin hankali akan sai ta je. Shikuma yace idan taje zata jibgu. Saif tun safe ya nema almajirai suka kwashe kwata na kofar gida sannan suka share cikin gida fes. Da kanshi yabi yana cire yanan gizo kafin yayi shara harda mopping. Sanin halin Laila sau daya take mopping a sati balle ya hanata biki bazata yiba ko dan bakanta mashi rai. Kanwar mamansa tana cikin wanda zata zo kuma dakyar abu ya burgeta, ldan taga wani abun aibu zatayi ta zaginsa cikin dangi. Cikin aikace aikace ne yaga kudin Laila a karkashin kafet din daki. ‘Maraba garsarshe, wai kura taga bakarjaka’ ya fada a fili bisa rashin sani, da sauri ya saka hannu ya toshe bakinsa tareda duba kofa ko tana hanya, murna ya mamaye shi duk hakoran sa a waje kamar gonar auduga, mamakin munafunci irin na Laila yakeyi. Da karen bana ake maganin zomon bana kuma ya isheta riga da wando. Tanada kudi sai take barin su suci Lami, idan batayi dan Allah ba zatayi dan azabarsa. Anan ya zara san ran shi ya gyara kamar bai taba ba. Ita kuma bata ga amfanin kaiwa banki ba, a hankali takeso ta rinka zara tana ma kanta hidima har Saif ya gama gina mata gidan Kajinta. Zatayi amfani da kudin ta siya Salwa ta rinka saida kwan tunda mutane na nema sosai, Shifa sanda yake gayama Laila Sameera bata iya rike miji ba, bawai yana nufin I love you ko I miss you ba. Idan ta wannan fannin ne Sameera ta kece mata. Da yayi NYSC a Oyo wani gari Shepeteri. Maman Tunde mai aikin trader a layin su ita take siyan abinci a gidan. Kuma Baban Tunde za‘a saka mashi, ganda, nama da kayan ciki. Ko sisi baya badawa kuma idan ta bata mashi rai ya saba mata. Gashi tanada biyayya gwiwa biyu a kasa tana ce masa SIR. Yasa suna bala’in burge shi matuka yaran Yarbawa. Ya lura yaran hausawa basuda da’a kwata kwata. Basu iya rike miji ba ko kadan. Sunada bala’in mako sai dai a fita a kawo masu kuma shi bazai lamunta lalaci ba. Sannan ga bala’in rashin kunya,jibe yadda Laila taso dambe dashi akan zai siyar da lefen daya siya da kudin sa. Basu san ma’anan aure ba, hanyar samun aljanna ne kuma suna sha zasu sameshi a sauki ne Yanzu ace cikin Laila da Sameera, bawai zaiyi bane. Amma idan aka ce ya daga ma daya kafa ta shiga aljanna zai bama Sameera wannan damar. Tausayin Laila yakeyi idan bata canza ba bai san inda zata shiga ba bayan aljanna. Duk hidindimon dayake a gidan, da mutumiyar arziki ne bayan kwana biyu ta rinka bashi koda 20k ne ya kashe tunda yaga kamar kudin nada yawa, amma dan zalunci ta boye. Aikam zata sha madaran mamaki. Wannan kenan!
Dogon jallabiya ya saka ya wuce kasuwa yayi siyayya, broilers ya siya manya guda biyu da kayan miya mai uban yawa, sannan su kayan kamshi da ginger, da kuma kayan salad wanda zatayi amfani dashi. Rabon daya siya irin cefane tun tana amarya kuma satin farko, mamaki takeyi ashe yasan yadda ake cefane iya shege ne kawai bazai bari yayi ba. Haka ta zauna tana aikin rai baiso ba. Kunci takeyi kamar an aiko mata da sakon mutuwa. Gidan duk kamshi gashi ta saka albasa da tafarnuwa, dama tana bala’in san abin saboda zama da Haske. Saifyana daga falo yana hadiye miyau duk ya kosa ta gama, gashi Laila bata dandana abinci idan tana girki, kome take dafawa saita gama. Bayan ta gama tafasa kazan ta soya, tayi miya komai ya kammalu, sai ya shiga cikin kitchen domin ya raba. Coolerya dauko guda biyu yana bama Laila umurni a matsayin nashi dana baki. “Ki saka min kirji daya, sai ki saka masu…, Yauwa ni cinya daya sai sauran nasu… Yauwa ina san flffike saka min biyu sai kuma ki saka masu sauran…” kallon sa take tana rabo bata gane me yakeyi ba. Ragowar daya rage kai da kafa ne sai baya wajen duwawun. Murmushi yayi yace” Yauwa Rabin raina, saiki… saka a baki kema naki kason kenan” yace cikin izgilan ci tareda hura mata kiss a iska. A haka ma saida ya ciro kafa daya ya fita yana ci tareda fito. Haka bakin suka zo sai faram faram yake dazu, dukjikinsa rawa yakeyi ya kasa natsuwa. Yanaso komai yaje mashi daidai. Sunci sun sha anyi masu nasiha. Daga nan akaje sashen Sameera itama. Nan aka sake hadasu akan suyi hakuri da juna duniyar kwara nawa ne. Wata rana idan akayi hak’uri kowa zai barta ya koma gidansa na gaskiya. Sameera ta basu tsaraba na turaren wuta da lalle. Laila kuma taba karamin yaron da akaje dashi dari biyar ya siya sweet. “
Duk suna waje zasu shiga mota ana bankwana, sai ya koma daki ya zaro 5k a kasan kafet yaba kanwar mamansa daya maida su gida. Tayi masa godiya tareda neman masa tsari akan mugun ji da gani.
Fijr a daren ta tafi tashar da ake tafiya Maiduguri, sunce ta koma gida ta dawo da asuba amma saita fara kuka wai yar uwanta tana cikin yan matan Chibok kuma kila anada labari a kanta. Sunyi mamaki amma kuma ba zancen wasa bane, sai suka bude mata Bus ta zauna idan garin Allah ya waye Dama wajen karfe shida na safe ake tashi. Ko,a jikinta tunda ance sakai yafl bauta ciwo.
Be safe mota ya cika suka tafi sannu a hankali har suka isa birnin. Hotel ta kama inda zata kwana ta huta kafln garin Allah ya waye. Cikinta yanzu yana wata shida da kwanaki amma kamar ba shiba. Bai sake girma ba bacin yadda aka kwantar dashi. Tanada abubuwa kala kala wanda zatayi ma boka bayani. Na farko Ammi ta flta harkan ta, abin yana mata ciwo idan Ammi tayi mata korafl akan ta roketa kudi, daga yanzu ask and collect kawai take so. Sannan kuma Hajia Yagana ta shiga taitayinta, karta takura mata saidai bada hadin kai akan auren. Na uku bala’in duniya ya je kan lsi. Dashi da farin ciki suyi hannun babbar riga. Sai na karshe kuma ta samu Ghali cikin kwanciyar hankali, a susuta mashi tunani yaji banda ita zai kashe kanshi.
bayan ta tashi, tunani ya fado mata ya kamata tayi sallah ranar koko? Batasan ko ana sallah kafIn aje wajen boka ba. Har ta tashi zatayi alwala sai wani zuciyaryace kada taje aikin yaki ci tayi taflyar banza. Gwara idan taje ta dawo sai ta hada dasu asuba duka tayi. Gaba daya tana kaffa kaffa kar tayita salati saboda boka da mallam basu shiri.
Taje banki inda ta zara makudan kudi saita wuce. Dakyar ta gane wurin dadin abin bayan Mandara mountain ne, saida ta hada da tambaya hanyar wajen Hatsabibi. Wata dattijuwa ta tambaya, taso ta kyale ta sai Fijr ta haska mata dari biyar. Anan tayi kwance ta caska kudinta. Taga Hatsabibi inda tayi mashi kirarin da Yagana tayi mashi, ta soma magana sai ya dakatar da ita yace ya sani. Shiru yayi yanata dube dube kamar yana jiran abu. Kusan awa daya sai ga Yagana, dama yasan da zuwan ta. “Wa nake gani kamar Fijr” tace cikin tashin hankali. Atsorace Fijr ta kalleta ta soma barin lebe. “Ina wuni Anty…. Dama… Dama… Dama” tana magana gumi yana karyo mata
“Daman mene? Almura! Ko ki fada min meya kawo ki kona miki rubiti na bibbigeki” tace tareda dungule hannu sama zata rabka mata. “Daman nazo naji inda lsi yake ko zai aureni”ne ta fada a tsorace. Bala’in shakkan yagana takeyi kam tasa boka ya maida ta angulu. Ajiyarzuciya tayi saita kalle boka “Da gaske ne?” ido Fijrtayi mashi alamarya rufa mata asiri. Girgiza kai yayi alamar eh sabida yaji tausayinta. Yagana muguwa ce sosai. Kallon Fijr tayi tana murmushi. “Ashe haka abin yake, gaskiya daga dukkan alamu soul mate dinki ne. Kin zubar mashi da ciki sau biyar ga kuma wani…. Sannan sai bibiyan sa kike kamar tsohuwar mayya” saita Kalle boka “Yi maza nemo mata shi, tada mashi husuma cikin gidan shi kuma kasa dole yazo ya aureta…. Yi maza kayi ina kallon ka” Bayan boka yayi sai hankalin Yagana ya kwanta, duk zaton ta akan Ghali tazo. Kallon Fijr tayi tace ta basu guri. Anan tayi abinda ya kawo ta ka‘in dana‘in. Mijinta ya fara tunanin amaryar sa wanda tasa aka kora tazo neman solution. Sannan ta sake kare Ghali daga Fijr, kuma bazai ma so mace ba sai wanda ta yarje mashi.
lta ta rage ma Fijr hanya, anan take tambaya ina Hadiza. Fijr tace ai ana bikin Shamsiyya. “Lallai Hadiza tayi saukin kai, yar kishiya take ma hidima haka“ ta fada tana dariya. Anty ba yar kishiya bace, Shamsiyya ita ce first born dinmu“ “Aiba yar Hadiza bace, yarinyar mai rasuwa Hafsat ne“ tace cikin gasgatawa saboda tasan me take fadi. lta Yagana batasan ana boyewa tunda har Sunar Haske taje. lta asalin yar
Maiduguri ce amma a Zaria aka haife ta. Yanzu kuma aure ya maida ta Maiduguri. Kuma asalin kawarta Hafsat ne tunda tafi fara’a. Sama sama sukeyi da Hadiza har Hafsat ta rasu kwn suka dinke. “Duk wani makirci na cin uban Shamsiyya nike bama Hadiza duk dai abin yayi kamar cin amana amma ita ke raye Kuma tana min kirki. Sai dai ya muka iya da abunda ya Gagari wuta, wai inji kishiyar konanna. Sai gaba takeyi abinta” tace tana dariya “Ai Hafsat akwai fara’a sosai ga dadin sha‘ani. Yadda kika ga Shamsiyya haka itama takeda natsuwa da kamun kai….” haka tayita bata labarin komai da banbancin su. Da”Hadiza fa har Hafsat ta rasu batada wani saurayi, kawai rabon ku fito ne. Amma da ina ganin haryau bazata auru ba” anan Fijrta gane cewa tayi gadon rashin mashinshini wajen uwarta ne. Kuma taji tausayin Haske sosai,saidai taga laifinta domin ta ita ce data dade da burma ma Ammi baki. Hotel ta kaita ta kwashe kayanta saita maida ta tasha domin ta tafi gida. Sam bazata barta cikin garin ba. lta kuma Fijr haushin kanta taji, rashin sallar asuba da batayi ba shiyajanyo mata wannan. Ta fita bata nema tsari ba gashi Yagana ta kwapsa mata. Yanzu kawai tunanin komawa Niger state zatayi tunda taji suma sun iya aiki Wannan kenan!
Haisam yana flta yace ma Driver din Abbansa ya maida shi gida idan yaso sai ya dawo bayan nan. Shi bazai iya zaman bikin ba. Komai a wajen bata mashi rai yakeyi kafin yaje yayi abinda zaiyi dana sanin. Gwara ya nisance wajen. ‘Daki ya shiga saiya kulle da makulli, kan kafet ya kwanta ya bude sabon babin kuka. Duk tsammanin sa idan yayi Kuka zaiji sauki amma kuma sai akasin haka. Radadin yafi yawa yanzu, kamar karamin yaro yake kuka wiwi. Ya kusan awa daya a haka. Duka abinda ya faru dashi a baya suka dawo mashi sabuwa. Yasa ya birkice haka. Hawaye ke mamalo mashi daga idanu daya bayan daya.
Alhaji Sulaiman Bambale yanada mata hudu, kowane a cikin su nada yara daidai gwargwado. Amaryar sa nada yara biyu. Da Muktar da Jamila watau mijin Mommy da Mum din Haisam. Sun tashi kansu a hade komai nasu kashar kashar. Yaransu na iya zuwa gidanjenjuna kuma ayi masu hidima. Jamila ta aura abokin Muktar inda zumunci ya dinku da kyau. Barrister Adam Mijinyawa tareda Hajia Jamila Bambale sune maihaifan Haisam. Yaransu takwas, mata bakwai namiji daya. Akwai Salma, Adala,Amina sai Haisam, Siyama, Maryam, Fatima da auta Aisha. Suna zaune a lnuwa Wada road cikin Kaduna. Hajia Jamila nurse ce a asibitin Yusuf dan tsoho teaching hospital. Yanayin aikinta ana masu shifting, wata rana zata da yamma ta dawo da asuba, wata rana kuma da safe ne zuwa yamma. Dalilin haka yasa tana ta‘ammali da masu aiki. Daga haihuwar yaranta guda biyar mai aiki daya tayi amfani da ita. lta ke lura da yaran tareda masu hidima idan bata nan. Anty Safia tanada mutunci sosai balle ta taba aure mijinta ya rasu yaranta na kauye, sanda Haisam ke shekara bakwai sai Anty Safiya ta sake aure Kasancewa Haisam ne kadai da namiji, kowa yana bala’in ji dashi. Daga iyaye, yayye da kanne. Anan akayi mashi lakabi da Dan Lele. Duk da haka bai sangarta ba. Yanada hikima da kaifln basira tun yana karami. Zaka zauna kayi shawara dashi mai ma’ana. 
Yanada bala’in kwazo, “Da daya tamkar dubu‘ ake ce masa saboda ya fanshe gurbin wasu yara mazan wanda maihaifan sa basuda shi. Yanada shekara tara yayi sauka Al’qurani mai 
girma a madadin sauran da suka sauke a sha biyu haka. Daga nan bai tsaya ba ya wuce secondary na islamiya Inda zai gane fassara da Kuma yadda zai hau kan mutum sosai. Yasan littatafai nasu Umdatul Ahkam, Risala, Hadisai kala kala na Bukhari, Muslim, Tirmidhi, Malik Muwatta etc. Sannan gasu tarihin annabawa komai dai yanada daidai gwargwado. K0 boko babu kama hannun yaro, firamare din Mary Travis na kusa dasu yayi inda yayi Zamani college. A tsakanin shekarar 7 zuwa 10 sunyi masu aiki uku, daga masu sata sai bata gari. A lokacin aka kawo mata wata Ladidi. Yar kimanin shekara talatin da bakwai. A cewarta ta taba aure mijinta shima ya rasu kuma yunwa ya korota daga Gabon. Mum jikinta bai wani yarda da ita ba amma Kuma babu yadda zatayi. 
Masu aiki sun soma scarce, Ladidi batada kintsi kwata kwata sai ta flto da under wear da rigar mama idan babu Abba, a cewarta wai duka mata ne kuma Haisam yaro ne, sannan ba ta sallah. Mum tace zata koreta idan bata canza hali ba. Lokacin sallah zatayi alwala ta yi shela saita koma daki tayi kwanciyarta. Sai dai kamala na Haisam yana burgeta, dan shekara goma saita tsinta kanta da tunanin sa. ldan yana abu tayita binsa da kallo. Abin bai tsaya iya nan ba idan yana zaune kan kujera, zataje ta bayansa tayita shafa mashi kirjin ta tana mashi magana, walau ko sako kokuma tana neman karin bayani wajen sa. 
Abin baya masa dadi da farko yasha rashin sani ne, daga baya ne yasan tsabaragen iya shege ne. Anan yaje yace ma Mum baisan zama gida daya da ita. Mum ta bukaci sanin dalili amma ya kasa magana. Baisan ta ina zai soma fadin irin mugun abun nan ba. Mum kawai ki barshi, babu damuwa” yace saiya bar dakinta. Yayi alkawari zan nisance ta kuma yayi haka. Ta lura ya flta harkan ta sosai. Duk yadda taso ta bishi da iskanci yana kaucewa. Sai kawai ta dauki alwashin daukar mataki a hannun ta. Duk randa Mum take aikin dare zata saka mashi kayan maye cikin abinci ta bada akai mashi daki tunda baya fita zaman falo. 
Anan zata faki idon kowa cikin dare taje tayi masa fyade, ya lura da canji cikin jikinsa, amma kuma baida wani da namiji dazai tambaya haka. Kuma sai baiyi tsammani Ladidi tayi rashin hankali da zatayi mashi haka ba. Gashi Ladidi zata mayar mashi da kaya yadda ta same shi. Dama ance akwai ranar kin dillanci. Wai ranar da babban rigar mai gari ta bace. Barrister ya tafi aiki Abuja kuma Mum nada aikin dare. Ta fita aiki harta kai goma sai kawarta tace ta Koma gida zata rufa mata baya Sabida Haisam yana malaria. Dalilin haka bai samu damar cin dinner ba. A ranar Siyama taci kason shi wanda tuni tayi barci. Ladidi wajen goma ta shirya zata soma aikata masha’a, murna take yi saboda yau Babu Abba zata rashe da bala’in kyau. Da breziya da skirt ta tafi tana tinkaho. Yana cikin barci yaji tana shafashi. Da sauri ya bude ido tareda doka salati. 
“Innalillahi, Ladidi me kike yi cikin dakina?” 
Taji tsoro saboda kusan wata shida ana abu daya bai taba farkawa ba sai yanzu. Danne mashi baki tayi tareda kashe mashi ido, ita a daukarta kowane namiji haka yake. Tuni ta mance shekarar sa goma a duniya bai cika 11 bama
 Shhhh karka tara min jama’a” tace cikin kissa. Kokarin tureta yayi amma tayi crossing jikinta akan nasa. Balle matan Gabon manya manya kamar samudawa. Kamin ta rinjaye shi. Anan suke kici kici amma tafi samun galaba akan sa. Tanayi tana lashe mashi fuska wai ya taimaka mata. Kuka yake sharba amma ina. “Dan Allah Ladidi, kiyiwa Allah da manzon sa, karki lalata ni. Bansan abinda kike nufi haramun ne” “Wallahi babu mai kwatarka a hannu na yau saina yi abinda nazo yi.” sangartacce kawai” tace tareda wani zuciya, anan ta sharara masa mari sau biyu. Wani riga ta gani kan gado ta soma kulle masa hannu. a 
“Yanzu Ladidi bakya tsoron idan na mutu a wannan yanayi” “Kaiya shafa wannan zani wani gidan ne masu maza birjik” idan ka mutu
“Ke yanzu bakya tsoron ki mutu a haka? Me zaki ce ma mahilicin ki? Kinzo duniya kina lalata yara maza. Bakya kunyar haduwar ki dashi? Dan Allah ki kyale ni, karki bata min rayuwa dan zalunci. Kije wajen masu bukatar ki mana. Kiji tausayi na kiyi min rai. Wallahi idan kika kyale ni zan rufa maki asiri bazan gaya ba” ya fada yana kuka mai tsuma rai, murya sa yana rawa sosai. Wannan wani irin bala’i ne yake shirin fada mashi. Yana matsayin da namiji kuma za’a mashi fyade. Ya zai cigaba da rayuwar shi? Bakin cikin kawai ke dawainiya dashi, Ladidi batada imani ko dis. “Nasan zamana ya kare, yasa gwara na gwangwaje kafin na tafi” tace tana dariyar keta. 
Fito da harshen ta tayi tana kokarin hadawa da nashi. Cizo ya sake kai mata. Sai kuma ta bishi da duka. Kamar ganga take dukan shi babu sausautawa. Abin bai mata ba belt dinsa ta cire daga kugunsa ta soma labta mashi, gashi ta toshe bakinsa da tsumma balle yayi ihu. 
Numfashi sama sama yakeyi sai hawaye dake gangaro masa, dama bashida lafiya jikinsa yayi bala’in zafi Bata damu ba yanzu ta samu ya natsu. Rufe ido yayi yana addu’a cikin ransa, Allah ya dogara dashi ya kawo mashi mai agaji. “Duniya akwai azzalumai” ya ayyana. Rufe idonsa gam yayi, yanaji tana raba shi da kayan sa, a haka ya sume amma ko gezau. Bude kofa sukaji akayi. Mum ta dawo daga aiki. “Dan Lele kayi barci ne?” tace saita kuma saki kwanan abinci data kawo mashi wanda tanada tabbacin bai ciba. Tas tas tas komai ya fashejikinta yana rawa. 

“lnnalillahi wa inna ilayhi rajiun” “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” “lnnalillahi wa inna ilayhi rajiun” 

Tayita maimaitawa, sannan ta zube a wajen sumammiya. Wannan kenan! 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *