HASKE CHAPTER 15

HASKE






CHAPTER 15



Ganin yadda Mum ta zube a kasa ya bama Ladidi damargudu. Su kuma su Adala da Salma karar sukaji inda suka f‘lrgita suka tashi. Anan suka flta waje a sittin domin suga meke wakana. Daidai lokacin sukayi karo da Ladidi.”Ladidi laflya dai koh”
Bata amsa suba kawai ta wuce dakin da aka ware mata. Nan ta soma hada kayanta cikin sauri sauri. Salma tabi hanyarda Ladidi ta fito, anan taga Mum kwance kamar babu rai a jikinta. “Adalaaaa… Kinyi sauri Mum ta suma” Innalillahi” Adala tace sanda ta karasa. Basu ma lura da yanayin Haisam ba. Sai daga bisani suka gani, tsandara ihu sukayi kuma yayi daidai lokacin Ladldi zata fita ta kofarfalo.
“Allah ya isa tsakanin mu dake” Adala tace, dama basu shiri. Suturta Haisam sukayi sai suka watsa mashi ruwan dake dakin, itama Mum haka. Sai dai Haisam bai farka ba, Mum ne ta tashi tana kuka. Anan tayi kokarin tashi taje wajen sa, da tangal tangal ta karasa tareda tallabo shi. “Ta cuce ni, wallahi Ladidi ta cuce ni…. Allah ya isa ban yafe ba” Bata taba jin anyi ma yaro namiji fyade ba, da bai faru da ita ba kuma bata gani da idonta bazata taba yarda ba. Sai kuma ta tuna Haisam ya taba korafin Ladidi. Taji haushin yadda bata kore Ladidi ba tun sanda yace bai san ganinta a gidan. Yaronta daya tilo an bata mashi rayuwa. Yanzu wani irin rayuwa zaiyi bayan wannan. Ta riga ta cin mashi fuska a matsayin sa na da namiji. Yanzu zai rinka tunawa kuma ya rike tabon har muddin rayuwar sa. Tayi mashi mugun cuta wanda warkewa sai dai da ikon Allah. Yau dataga Ladidi da tayi mata dukan kawo ceto. Haushin kanta tayi data suma maimakon daukar mataki. Acikin hakane sai yayi tari tareda magana chan kasa, “Ladidi dan Allah ki rabu dani” “Dan lele karka damu, Ladidi ta gudu you’re safe” Hawaye mai dumi ya soma kwararo masa, yanzu shikenan sun san abinda ya faru dashi. Zai rage kima a idon duniya. Mum ta taimaka mashi saka kaya daga nan suka wuce asibiti. Anan akayi running mashi test kala kala tareda flushing system dinsa, kuma anyi masa gwajin ciwon zamani da sauran cututtuka. Daga kuma haka aka kara mashi ruwa tareda bashi gado. Dama yana zazzabi saidai abin bai sauka ba, magani yaki masa aiki jikinsa yayi zafl kamar yana makera. Cikin daren tashin hankali kawai suke dawainiya dashi. Adala take tareda Hajia Jamila sai Salma babba tana gida domin lura da yaran. Gashi yanzu Ladidi ta gudu babu inda za’a kamata a hukunta ta. Wata kila ko zata koma Gabon wajen yan uwanta ne.
Haisam saida yayi sati biyu kafin aka sallame shi,jikinsa ya warke duk tabon dukan ya soma ‘afiya. Sai dai bashida sana’a sai kuka. Tun ana mashi nasiha akan rungumar kaddara har aka Soma zuba mashi ido.
A daddafe yake zuwa makaranta boko, ya zama shiru shiru Komai nasa a hankali, yanzu zaka tsinta sau nawa zaiyi magana a make bayan sallama. Ko dariya duk abinka baka isa yayi ba, A kwana a tashi…
Haka Haisam ya cigaba da rayuwa cikin kunci, abin yana bala’in damunsa. Tun daga ranar barci yakeyi yana firgici, baya iya zaman daki saiya saka makulli. Ji yakeyi kamar Ladidi zata fantsama tayi rab dashi. Gashi Kunya yakeji sosai domin Ladidi taci mashi fuska, yayi losing self esteem da kuma self confidence dinsa. Panic attacks yake samu kala kala saboda Ladidi ta shayar dashi tashin hankali lifetime, baisan masu aiki kuma tun lokacin Mum bata sake hayan suba. Koh gidan mutane
yaje ko yan uwa idan akace wane yar aiki ce jikin sa zai soma tsuma yana rawa, haka zakaga hannun sa yana karkarwa a hankali har sai ya barwajen. Shekaru sun tafi zai zana SSCE, yanada kokari daidai gwargwado tunda koda yaushe yana karatu ne maimakon hira.
A haka aka samo mashi Lesson teacher domin ya taimaka mashi wajen fahimtar tambaya irin na WAEC ko NECO. Dama al’adar gidan kenan saboda Abbansu bai san ka sake zana jarabawa.
Mallam Ibrahim yana koyarwa a Kaduna Capital School, wata rana Haisam ya biya ya kai mashi kudinsa na wata sai yaga Haske a Office din. Daga wannan ranarya soma ganinta kuma a hankali ta kafu cikin zuciyar sa. Akai akai yana zuwa sabida ya ganta, zaije da tambaya wanda ya shige mashi gaba, daga nan zai kashe tsuntsu biyu da dutse daya. Wata sa’in yana ganin ta wata rana kuma baya ganinta, shi dai bai taba mata magana ba kuma baya tsammani ta taba lura dashi. Murmushin ta yana saka shi nishadi sosai. Ita ta zama farin cikin sa, yanayin maganarta da natsuwa shiya kara attracting dinsa. Komai nata yayi masa babu ragi babu kari.
Bayan WAEC ya kuma koma Zaria wajen Gwaggo Marka, anan ya fl samun kwanciyar hankali We da gidansu. Anan baya firgice ko tunanin Ladidi zata far masa cikin dare. Ko dayake yanzu ya zama saurayi zata ci dan banza duka Kota karasa lahira gabadaya. 
Mommy tana zaune a Newyork da iyalanta, sai tace Haisam ya dawo wajenta da zama. Daga nan zai rinka zuwa wajen Doctor tana mashi therapy, a haka zai samu ya mayar da komai ba komai ba. Kuma US yafi saukin karatu zai zama Doctor kamaryadda yake buri. 
Mommy bata tsaya anan wajen ba, kullum saita bishi da nasiha akan tawakkali. Bawa yanada kyau ya rungumi kaddara mai kyau da mara kyau shine cikon imani, Allah bazai bama bawa abinda bazai iya handling ba. Jarrabawa ne kuma tanaso yaci nasa da flying colors. 
Murmushi yana cukin sunnah, ko bazaka iya ma mutum komai ba yanada kyau ka murmusa masa saboda yaji dadi. Kuma zafin rai da fadi bazaiyi cire maka damuwarka ba. Ya zama mai mayar da komai kamar bai faru ba. 
Kuma ya yafe ma Ladidi, idan ya rike ta acikin ransa kamarya bata haya ne ciki rayuwar sa. Forgiveness is the first stage of moving on, dole ka yafe ma wanda suka ci zalin ka domin ka samu kaji dadin kaima. Ta Hakan ne zaka iya mancewa dasu, idan kuma ka mance dasu bazata tuna ba balle kaji haushin abinda suke maka. 
Daga nan tana hadashi da MP3 dinsu Sheik Jafar, Daurawa dasu Albani. A hankali cikin ikon Allah ta samu aka shawo kansa. Ya daina wannan mugun tunani inda yanzu yana zama cikin dangi a yi hira. Yazo yanzu ya kasance mai bala’in saukin kai da dadin sha’ani. Kowa yana alfahari dashi daga dangi harwanda basu san shi bal Yanada kyauta da taimaka ma na kasa dashi. 
Bayan ya dawo Nigeria sanda ya gama karatu ya soma internship (finsa a Barau Dikko. Yanayin karatun sa gashi rainon turai bazaka bambanta shi da kwararru ba, yanzu kusan wata hudu kenan da fara aiki a wajen. Randa ya fara zuwa yana registration yaga Haske, anan ne yasan cewa yana tareda sa’a. Dashi da Hasken Annuri sa tare waje daya, sannu a hankali zai koya mata yadda zata so shi. Bai taba soyayya ba, mata sun fitar mashi daga kai. Duk nacin ki zakiyi ki gama, mutunci kawai da girmamawa zai hada ku. Duk yadda yaso ya cire shamsiyya ya kasa. Haka ya hakura ya barta cikin birnin zuciyar sa. 
Dukda tsammani sa daya koma US ya rasata har abada, ashe sai yanzu ne tunda tayi aure. Fatan alheri zai bita dashi duk da bai so ba. Yaso ace shine mijinta, amma kuma rabo ya riga fata. Dole ya runguma nasa kaddarar. Sai dai abinda ya sani koda zaiyi aure nan gaba, kawai domin raya sunnan manzo ne amma bawai soyayya ba. kafin Haske baida wanda yake muradi daya wuce ta. She would always have a permanent spot in his heart, babu wata ‘ya mace wanda zata iya canjin ta koda ta rabi. Ya riga yayi zurfi a soyayyar ta kuma baya jin kira. Yah sati biyu da kashe wayansa, bayaso ma wani ya kirasa balle ya damesa, hejust wants to be on his own for now, Wannan kenanl Badman Bilal ya tsaya a Kanti Plus ya siya kayan shayi da makamancin haka, sannan a Havilla Ice cream ya tsaya ya siya. A wajen gidan su na Yahaya Road akwai wani mai tsire wanda ya shahara, anan ya siya da kuma fruits duk ya riko. Bai so yaje yaga babu wani abu saboda Haske tafi haka a wajen sa. Mace ce tamkar dubu, yayi mata diban albarka kala kala amma yanzu ya dauki alwashin daga kan Shamsiyya bazai sake kallon kowace ‘ya mace ba. He is a changed man yanzu and promised to do better. Yasan shi mai laih ne, ya bata mata rai lokuta da dama, bama ita ba ya san bashida dacHn mu’amala. Girman kansa ya rinjaye komai na rayuwarsa. Kowa bai isa bane a gaban sa. Bashida dadin sha’ani ga kuma kaskanci, amma yana so wannan saban babin dazai fara da Haske ya zame masa best time of his life. Zai maida ita Sarauniya cikin mata, zai zame mata abin alfahari. Kowace ‘ya mace zatayi kishi da ita. ldan za’a bada award din best husband of the year zai kasance shi ne zai ci gasar. 
Ya canza number dinsa, saboda tsaro yayi hakan ba tsoro ba. Yayi hakan ne dalilin yanka alaka da past dinsa. Baiso wata kadangaran bariki tace zata ruguza masa rayuwa, har Laila batada sabon number din balle ta kai gulma. Abbansa ya roke sa alfarma akan ya rike Haske tsakanin 53 da Allah. Aure ba abin wasa bane, cikon addini ne. Anyi masa nasiha mai yatsajiki, har Ummansa tayi kukan murna tareda mashi fatan alheri. 
Kowa yasan weakness dinsa bai wuce mata ba, kuma an rokesa akan ya bar wannan mugun dabi’a. Aure dayajibanci haka ba aure bane illa disappointment. Bazai ma Haske adalci ba suna tare kuma yana bin mata. Koba komai idan ya dauko Sida ya shafa mata bazai gama da duniya latiya ba. Yana kwanar layinsu yayi mata text, angon karni duk zumudi yake yi. Horn yayi sai maigadi ya bude masa gate, cikin kwarewa ya shiga ciki. 
“Barka da zuwa” mai gadi yace shi kuma da hannu ya amsa mashi. Maigadin ya tayashi kwasan kaya bayan ya rufe gate, a falo ya ajiye saiya tah abinsa. Shikuma Badman koda ya shiga dakin tsab yake a gyara. 
Sanyi mai dadi yakeyi na room freshener tangerine flavour, sannan kuma akwai turaren wuta shima yana konewa a burnerdake chan kurya wajen socket. Yanayin falo ya burge shi matuka, simple but very classy ya ayyana cikin ransa. Anan ya sake ganin mutuncin ta saboda ta san abinda yake dace. Fararen kujeru ne guntaye irin wanda turawa suka fl amfani dasu, sai akwai cushion kalar ja. Sannan ta gefe anyi kwalliya da silver. Labule kuma farare ne. Komai na ciki kashar kashar abin ban sha’awa. lta kuma bayan taga message dinsa, bata san me zatayi ba bayan wannan, kawai zama tayi cikin kayan jikinta. Bataso ta saka nightgown kafln ya nuna tanajiran wani abu daga gare shi. Dakin kwanarta shima fari ne tas, daga fenti, gadon da zanin gado shima fari ne. Sai throw pillows kusan goma masu laushin gaske kala daban daban. Ta riga tayi wanka tanajiransa cikin atamfa green sai mayafi mai kyan gaske ta rufa kanta dashi, zaman zauna kaci tuwo tayi tana jiran sa. Murda hannun kofaryayi saiya tura, anan ya yaye labule tareda tura kansa cikin dakin. 
“Assalamu alaikum Rabi’atul bait” “Wa’alaikumus salam Habibi” ta amsa a hankali tana murmushi ta cikin mayaE 
Tsayuwa yayi bakin gado, hannunsa ya saka a aljihu, kaftan yasa fari wanda ake kiran dinkin na Bankole. Kallonta yakeyi yana sake gode ma Allah da bai barma Haisam ita ba. Babu haufi today is the happiest day of his life. “Uhmm uhmm” yayi gyaran muryan. “Uhmm… Yanga ne kuma zaki min nida abina” “Haba amaryar da uwar gidan Bilal a duniya da aljanna baki daya” yake fadi cikin annashuwa. Ita kuma shiru tayi. “Dan bude min fuskan dayafl na kowa Haske a duniya” “Kuka kike so nayi maki tukun nan“ “Anyi aure kuma bazan Kalle matata ba” “Baby nifa bansan kunya haka“ “Hasken Lantarkina… Ni gaskiya bazan yarda ba” zance yakeda zubawa ita kuma tana dariya tareda kallon sa ta mayafi. Dayake na karshen nan salon shagwaba yayi harda buga kafarsa a kasa kamar karamin yaro. “Ni ban hanaka ganina ba… Kazo ka bude” tace chan kasan makoshin ta. A hankali ya taka saiyaje dab da ita ya zauna, numfashin su yana sarkewa dana juna. Baiyi saurin bude mayafin ba, hannunta ya rike ya soma murza wa cikin kulawa. Murmushi yayi wanda ya kayata mashi fuska. Idansa ya canza kala zuwa na madara sai sheki yakeyi, zallan soyayya yake dauke dashi. Bayan wasu lokuta saiya saketa ya bude mata fuska. Runtse ido tayi tana murmushi tareda sinna fuska kasa. 
Kunyar sa ke dawainiya da ita, amma kowa ya sheda mata cewa dole ta rage wannan idan suna tare domin farin cikin sa da ita baki daya. “An daura baby” “Uhmm” 
“Kalle ni cikin idona please” ta dago domin tabi umurnin sa amma cikin sakan uku ya narkar da ita. Da sauri ta sukuya ‘ana murmushin ta mai kashe mashi jiki. Cizan lebensa yayi tareda lashewa. Sannan ya girgiza kansa yana murmushi. 
“Baby bazan iya da kunyar nan ba, please look me in the eyes. Ina so kiga yadda sanki ke min ruri” kallonsa ta sake yi, amma wannan Karon ta daure. Magana yakeyi kamar na rada. “Baby mun zama daya, am you and you’re me” kawar da fuskanta tayi. Wani yanayi ta shiga wanda baya fallasuwa. A hankali ta ciza lebenta kadan. Bata ma san tayi ba reflex ne. 
Da sauri ya kai hannun sa wajen kumatun ta, shafawa yayi. Dumin hannunsa saida ya isar mata da sako cikin zuciyarta, harbawa ya soma. Bawai na tashin hankali ba, A’a zallan soyayyar sa ke bin duk ilahirin jikinta. “Babyyy” yaja sunar cikin wani siga 
“Karki ciza bakin ki haka, it’s affecting me” 
Ita bata gane me yake nufi ba, kawai saita bari. A hankali take satan kallonsa. Yayi ne iya yi. Shikuma bai sauke hannunsa daga fuskantar ba. Bi yakeyi da yatsun 5a kamar yana neman wani abu akai, ya shagala sosai cikin abinda yakeyi. Daga bisani yace tayi alwala su kabbara sallah. 
Abbansa yajaddada masa amfanin haka, kuma shima karin kansa an (ada masa a islamiya. A dakinta sukayi sallah inda yaja su, yanada ilimin islamiya mai zurfl wanda ‘a sake razana dashi. Mamaki takeyi akan dalilin sa nakin amfani dashi. “Allaahumma ‘innee ‘as’aluka khayrahaa wa khayra majabaltahaa ‘alayhi wa ‘a’oothu 
bika min sharrihaa wa sharri maajabaltahaa ’alayhi.” yayi masu a matsayin su na sabon ma’aurata. 
“Baby akwai abinci a falo nazo dashi, kije ki hada mana. Ni bari naje nayi wanka” 
“Uhmm hmm” Mikewa tayi taje falo, akan centre table taga kaya birjik. Leda daya bayana daya ta rinka budewa. Anan ta rinka kwasa sannu a hankali her kitchen. 
Naman ta saka a microwave domin ya dundumu, sai tayi slicing ayaba da kankana yan madaidaita. Kwano farare masu kyan gaske ta dauko ta saka, sai ta kwaba madara ta zuba kan fruits din. Naman Shima ta jera shi, Komai yayi kyau akan tray, sai ta daura su akan food trolley ta gungura zuwa daki. lsanta keda wuya sai taga wani kwali na kaya da kuma letter. Shi kuma baya dakin. “Ki saka wannan kizo dakina ki sameni” rubutun dake ciki kenan. Juya kwalin tayi taga wata baturiya sanye cikin arniyar kaya wanda take tsammani shi ke ciki. Saida dariya yan subuce mata saboda ta ina zata fara saka wa. Budewa tayi sai wani silk gown baki ya f’Ito, yanada laushin gaske ga santsi. Hannun ta tabi tana shafawa, a hankali ta warware shi domin ta sake gani da kyau, kallon kanta tayi sosai bayan ta saka, bata iya f‘Ita ba saida ta zura hijab taje dakinsa. 
Da trolley din ta tura kofar wanda ba’a wani rufe ba. Wutar ciki ba’a kashe yake ba amma babu wani haske. Saida ta shiga ta sake ganin mamaki. 
Ya yi decorating dakin da wuta kanana na decoration ta ko’ina. Sanna ga candles suma kanana masu kamshi ya kunna tareda jerawa a kasa. Gadon kuma yabi da roses sai yayi shape din love a tsakiya. Tunda take bata taba ganin abinda ya burgeta kamar haka ba, ashe Bilal is this romantic? Komai nashi yayi ne, sai sansa ya sake mamaye ta murmushi takeyi batasan me zata ce ba. Wani zuciyaryace taje tayi hugging d‘Insa amma kuma saita fasa. 
Yana murmushi ya karasa ya shiga da abincin, sannan ya koma cire mata hijab. Runtse idanu tayi saboda tsabaragen Kunya. Baiko damu ba yajanye mata hannu sannu a hankali suna taWa. 
Kan gado ya zaunar da ita saiya duka gabanta yana kalloma, murmushi suke ma juna babu wanda yayi magana. Sun kusa minti biyar zuciyar su yana isar ma juna sakonni wanda su kadai suke fahimta. 
Shine ya katse shirun, saiya soma magana cikin rada. “I want ourflrst day together to be memorable, yasa kikaga haka. Nayi kokari baby ?” “Uhmm” tace saita ciza lebenta. Rufe ido yayi yana magana “Baby na hanaki, rudani kikeyi idan baki sani ba” da sauri ‘a bari wanda saida ya tuntsire da dariya. Da kansa ya zuba masu abinci, shiya ciyarda ika kuma ya noke kafada saita bashi. Yanayi yana shagwaba kamar karamin yaro. Abin ya burgeta yadda ya sauke kansa kasa domin farin cikin ta. 
Bayan sun gama ci saiya kwashe kwanon ya mayar kitchen, bai so tayi wani aikin komai. Jinta yakeyi cikin kowane sansa na jikin sa. Daya dawo sai ya kashe masu wuta suka kwanta. 
Da Safe ita ta rigashi tashi, anan ta kafa mashi ido tana kare mashi kallo. Barci yake abinsa hankali kwance. Dadi daya takeji yadda takai budurcinta gidan mijinta. Bilal banda shi mata albarka baya komai. Daya samu akasin haka tabbas tasan zatayi kwanar tsakar gida. Tashi tayi ta shiga bayi tayi wanka tareda alwala. Koda ta dawo har lokacin yana barci. Zama gefen gadon tayi domin ta tada shi. A hankali taje gefen kunnen sa ta soma hura masa iska. Motsi ya soma yi wanda tayi saurin mikewa. Chapke ta yayi tareda mannata da jikinsa. Cikin shagwaba ‘ayi magana kamar me kuka, “Baby ni ka sake ni asuba yayi” “uhmm uhmm” “ka tashi kaima ka kimtsa asuba yayi” bai bude idonsa ba haryanzu saidai sunata motsi. “Allah ya soki” yace saiya saketa. Da gudun vespa tabar dakin wanda taji sauti dariyar sa. Ta idarda rakatanil f’Ijr sai taji marsa, komawa dakin tayi domin gyara masa gadon, wani bedsheet blue ta saka tareda pillow case. Anan ta kawar dasu candle din komai yayi tsabtsab. Sai ta koma ta tada nata kabbarar, bashi ya dawo ba sai da gari ya soma Haske. A lokacin har ta gama azkar tabi Iatiyan gado. Shima shiga bargon yayi inda ta muskuta zatayi magana, “Shhh nine” yace inda bata sake cewa komai ba. Barci sukayi har goma inda aka tadasu, Umman sa ne ta kai masa abinci kuma haka zata rinka yi har bayan sati daya. Wannan kenan! a Bayan kwana biyar… “ Newyork City. 
Wata doguwa mara jiki mai bakin fata ke zaune akan kujera, kyakkyawa ce ajin farko amma yanayin kwalliyar ta bazai nuna hakan ba. fuskanta shake yake da make up mai uban yawa. Purplejambaki ne dampare a bakinta sai idon ta baki simk da eyeshadow da kuma eye liner ga zabga zabgan eye lashes ta saka. Tasha contour hancin nan ya fito kamar Karas. Kunnuwanta yan kunne ne shake guda shida, sai kuma hancinta yasha huji biyu. Jan kunba ne green a yatsun kafa dana hannu. Sai kuma kashin kanti blonde style din fringe wasu kuma suna alakan ta shi da style din Rihanna. 
Gajeran wando kejikinta irin bumshort sai ta saka riga crop top, anan ne ya bayyana tattoo kaca kaca a cikin ta. Kidan dake tashi a dakin zai iya dode maka dodon kunne dan kara, amma daga dukkan alamu wannan ita ta saka abinta. Wani Leda ta dauki cikin jakar‘ta dake gefenta, daga dukkan alamu yanzu ta dawo daga inda taje. Wakar ‘Radioactive’ na imagine dragons ke tashi. Ledar ta bude ta zuba akan center table data daura kafanta. Hodar ibliss ne ta saka, a hankali cikin kwarewa ta durkusa ta soma sinsina. Tanayi tana rufe idon shedan na mata bayani. Saida ta shaka dayawa sannan ta bari, zama tayi saita jingina bayan ta. Daga nan ta rufe ido, ba barci takeyi ba illa tunani yadda zata shayo matsalar ta. 
Wata ta murda kofa ta shiga, tsaki tayi saita wuce hanyar home theater ta kashe, Wanda ta gama shakar Hodar ibliss ta bushe da dariya. “Dija sarkin zuciya, meye matsalar ki dani…. Karki damu gobe zan tafl na bar maki garin” Harara Dija ta watsa mata sai taje gabanta ta tsaya sekeke, kallon kawarta takeyi wanda yanzu tayi bala’in nisa. “BANAN Yanzu ace idan bakya Tausayin kanki, at least kiyi tausayin iyayen ki mana.” 
“kin maida bakin ki salansa babu abinda bakya sha, kece wiwi, sigari, shisha yanzu kuma dan abu kin koma Cocaine” “Cocaine for heaven sake, cocaine fah…. Hodar ibliss… Bakida tausayi kwata kwata” 
Kwafa tayi saita so ma rage kayan jikinta, Banan tana bakanta mata rai sosai. Kamar ba yar musulma ba. Maganar gane ita bahaushiya ce baima taso ba saboda babu alama. Ko kallabi bata sakawa balle kayan mutunci. Sannan sai tayi hausa zakayi ta mamaki. “Shhhhh… Dija kin fiye takura, don’t worry babu abinda zai faru dani” 
“Idan mutuwa kike tunani dama dole abu ya kashe ka one way or the other, so gwara dadi ya kashe ni wallahi” 
“A Hakan zaki koma Nigeria? A hakan kike so ya aure ki? Bakida hankali ne? Wani da nagari zaiyi tarayya dake?” “Bakida sana’a sai zama cikin maye, shine kike so ki aure shi” dariya Dija tayi na isgilanci “Think again, iska yana wahalarda me kayan kara” 
Runtse Ido tayi wasu hawayen takaici suka bin mata fuska, Tasan abinda Dija ta fada gaskiya ne. Saidai bazata iya bari ba. Idan batayi shaye Shaye baji take kamar ana tsikarin ta kuma zata haukace. Tun tana Najeriya take ta’ammali da codéine, coflin da sauran su, cikin roban coke take sawa tayi ta shan abinta. Yanzu kuma datake zaune ita kadai sai abin ya karu sosai. 
Gashi taf’l sati tana kiransa a waya amma kuma a kashe, ta gwada yafl sau dari biyu abu daya wai switch of, kamar zata zauce takeji dole ta tattara taje gidansu taji lanya. Shirun yayi yawa haka. Wannan kenanl 

~~~~~~~~~~ 

WAVE BANAN? gurin wa zata 3 Nigeria? BILAL K0 HAISAM? 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *