HASKE CHAPTER 28 THEND QARSHE

HASKE 

CHAPTER 28 THEND QARSHE

Ta rasu tanada fata daya a cikin ranta, Allah ya hada Bilal da Haisam da mata nagari

wanda zasu rinka sauraran su, mata masu kaunar su masu tarbiya, wanda zasu zame masu
uwaye nagari ga yaransu. Matan da zasu kara karkata su wajen hanyar aikin kwarai yadda
zasu dace ranar kiyama. Mommy ita ma Allah ya bata yara masu jin magana, ba irin ta ba
mai taurin kai. Wanda zasu ji tausayin ta idan ta tsufa.
Nurse ta cire duka tube da wayan da aka makala a hannun Haske saita kashe na’urar.
Case din Haske is rare, ba kasafai bane za’a markada mutum da mota ya samu recovery
dinda tayi. Rufeta da bargon jikinta tayi saita fita ta cigaba da round dinda takeyi tun farko.
A bakin varenda Haisam ya zauna har asuba, sauro sunyi mashi kaca kaca amma baima
lura ba, kuka yakeyi sosai a wajen. Ya kasa gasgata abinda ya faru yanzu, waifa da gaske

Haske ta tafi? Seriously shikenan ta tafi in a middle of a sentence, rabuwa yazo har abada.
Babu wani sauran jira. Ta tafi ta barshi sanda yake bukatar ta the most, dashi da Ajwad.
Yanzu ya zasuyi rayuwa ba tare da ita a ciki ba?
Kullum yana addu’a shi ya fara tafiya, baiso ya bude ido in a world without her. Amma
kaddara ya riga fata, worst nightmare dinsa ya faru, ya riga ya saba da input dinta na yan
kwanakin nan, balle tunda yayi wayo yasan menene soyayya take makale a birnin zuciyar
sa. Ita kadai ce mecen da yake so, there is no love for him without her, ya riga ya gama gina
irin rayuwar da zasuyi da ita. Mutuwa bata kyauta mashi ba ainun.
Wani Doctor daya kwana a wajen ya tadashi akan su wuce suyi sallar asuba. Addu’a
Shamsiyya take bukata fiyeda kuka. Duk gabobinsa yana mashi ciwo, sai ya tsinta muryan
Shamsiyya da take magana dazu, “I feel so much pain, duka jikina yana ciwo” wani siririn
hawaye yabin masa fuska, saiya fara shesheka, duk moments dinda sukayi tare kawai yake
tunawa da muryanta mai dadin saurara yana dakan mashi dodon kunne. Daci ranshi ke
masa, ga wani zafi dayake ji a kirjinsa, sannan kansa yana masifan ciwo. Baya ma ganin
gabansa sosai kawai jefa kafa yakeyi cikin fog dinda yake baibaye ko ina.
Kallonsa Doctor din yayi sai ya dafa mashi kafada, “Addu’a zakayi mata, Allah ya jikinta”
“Amin… She is… Was my everything”
**
Kwanaki biyun nan cikin hira Abubakar ya karance cewa Fijr bata tashi sallar asuba. Yanzu
shike tada ta kafin ya shiga bayi, idan kuma zashi masjid zai kara kira ya tambata ta tashi.
Toh dayake abin ya hada da sabon saurayi anaso a burge shi, tana kokarin tashi taga tayi.
Yau tun kafin ta tada salla ta kunna heater, tun wuri take so taje domin taga Haske. Koda
ta idar taje ta sauke, Lantana ta gani zata dauki Ajwad. Murmushi sukayi ma juna, “Ina
kwana” Fijr tace.
“Lafiya Lau Babban Hajia, yasu Hafsee?”
Kallon gadon tayi inda take sharban barcinta, murmushi tayi sai tace “Lafiya lau” kallon
Lantana tayi wanda Ajwad ke makale a kafadar ta, “Me zaki mashi?”
“Zan canza mashi pampers ne… Wanka ma zan mashi gabadaya”
“Ashe kin gane yau da wuri zamu fita”
Koda shi da rabi yayi harta shirya, Anty Fadeela tana kokarin hada breakfast wanda zata
zo dashi idan zata. Kowa yana murnar farkawan Shamsiyya. Harta Daddy zashi da wuri ya
dubata wajen tara saiya wuce aiki. Bilal shi kuma bai so yaje wajen sai an garka ma Laila
ankwa tukun.
Abubakar yazo ya dauke Fijr shima yaga Shamsiyya saiya wuce aikinsa, Fijr tace su biya
gidan Haske domin ta daukan mata kaya. Anan ta shiga durowa dinta domin ta zaba, ta
rasa me zata dauka saboda kusan komai na wajen sabo ne. Wani French lace kalar
Burgundy ta dauka.
Bayan sunyi parking mota a haraban asibitin wajen 7:10. Haisam suka gani yayi tagumi a
gefen motarsa tsaye ya rufe iso, zakaga siririn hawaye a idonsa. Duk zaton Fijr ciwon ne ya
tashi, bata kawo mutuwa a ranta ba. Ita ba ta tsammani Shamsiyya da kuruciyar ta zata
mutu.
“Ya Haisam halan jikinta ne ya tashi?” tace cikin damuwa. Kallonta yayi da kyar, sai kuma
ya kauda fuskansa. Hawaye ne suka fara masa zirya.
“C’mon be a man, zata warke” Abubakar yace. Bai tanka suba illa Fijr data bar wajen taje
dakin. Tana zuwa ta fara masifa, “Dan wulakanci wayace a rufe mata fuska”
Saita karasa wajen da sauri, dama Ajwad yana wajen Anty Fadila zasu je tare. Hafsee
kuma tana tareda Abubakar. Budewa tayi dai taga Haske bata motsi, tabata tayi taji jikinta
babu dumi, ranta ya bata kila sanyi takeji yasa aka rufeta haka. Sai kuma ta lura kirjinta
baya motsi irin yadda ake numfashi sama da kasa.
“Why is she not breathing? Innalillahi! Doctor kuzo ku taimakeni sister dina bata motsi”
ta fada da karfin tsiya. A lokacin Abubakar yazo saboda Haisam ya gaya mashi. A bakin kofa
yayi karo da wani Doctor dan matashi. Karasa wa Doctor din yayi wajen Shamsiyya zai
rufeta sai yayi magana.
“Ki daina jijgata, Allah ya dauki abinsa”
Tas ta sharara mashi mari saita ci kwalarsa gam, “Ubanka ! Ubankal!! Ubanka nace!! Dan
Ubanka bata mutu ba” ta fada tana kuka. Da sauri Abubakar yazo ya kwace Doctor din
wanda jijigashi kawai Fijr takeyi saboda tashin hankali. Tsaki Doctor din yayi saiya fita, bai
ce komai ba kafin ta bisa ta tara mashi gajiya.
“Ba ta mutu ba” ta fada tana kuka sosai harta zauna a kasa, takura kanta tayi a bango tana
shessheka. A lokacin Haisam shima ya shiga dakin. Haki ta fara ta cigaba ta fadin bata mutu
ba. Saita zube gefe a sume. Anan Abubakar yaje wajenta da sauri sai Haisam yaje bayin
wajen ya debo ruwa. Kwantar da ita yayi ta bayanta saiya soma danna mata kirji. Haisam
kuma yana yayyafa mata ruwa. Tari tayi a firgice saita soma kokarin zama, kallon Abubakar
tayi “Tell me mafarki ne, Anty tana nan bata tafi ba” baice komai ba kawai kallonta yake.
Mommy ne ta shiga da Sallama a bakinta, tunda suka isa asibitin da direba gabanta ya
soma fadi. Ganinsu charko charko ya tabbatar mata da zarginta. Balle ga Fijr zaune kasa
dabas.
“Ta tafi koh? ‘yata ta tafi ta barni” tace cikin kuka, share hawayenta ta soma. Saita zaunaa
kujera. “Abubakar zoka kira Daddyn ku da sauran yan uwa saboda a birne ta” tace. Gaban
Haisam ne ya fadi dayaji wannan, saiya kalle Mommy datake hawaye kamar gudun famfo.
Bata kuka saidai zakaga bakinta yana motsi da alama addu’a takeyi. Zuwa yayi ya zauna
gefenta, hannunta ya soma murzawa, a hankali ya fara magana.
“Mommy Shamsiyya ta tafi ta barni” ya fada kasa kasa.
Kafin mintuna 30 duk yan uwa da abokan arziki an samu labarin mutuwar, banda binta
da addu’a da fatan dacewa basa mata komai. Ana neman mata gafara tareda fatan haske
yaje kabarinta. Su Anty Fadila basu samu damar zuwaba. Zailani da Engr Muktar sukazo da
Hilux inda aka sanya ta aka kaita gidansu Zailani.
Mutane uku suka kawo sadakan likafani, duk wanda yaji mutuwar ta yana girgiza. Yarinya
ce karama so full of life with potential. Kullum tana murmushi babu abinda ya taba hadata
da mutane. Koda kun samu sabani zata ce duniyar kwara nawa ne wata rana sai labari
bayan an mutu.
Mutane sun soma hallara a kofar gidan, tabarmu sun soma cika ana jiran a kaita. Amma
babu Bilal babu dalilinsa. Mommy ne ta tambaye Ummansa, anan tace ta gaya masa kafin
ta fita. Kiran wayansa ake amma bai dauka.
Imran aka ce yaje ya dubashi sai Haisam yace zashi shima. Haka suka tafi gidansu Bilal a
karo na farko. Da tambaya suka gane wajen, cewa mai gadi shine mijin Shamsiyya. Anan ya
soma mashi gaisuwa. Basu yarda an bude masu gate ba sai suka bi karamin kofar sukan
shiga. Sashen Bilal suka je, falonsa babu kowa sai suka wuce bedroom. Ya kashe Lantarkin
dakin, Haisam ne ya kunna. A kasa yaga Bilal yana zaune, daga shi sai wandon shadda da
singlet. Idansa yayi ja alamar kuka shima yaci.
“Kuka name kuma bayan ba matarka bace” Haisam yace sarcastically. Anan Bilal ya kifa
kansa a gwiwa, “Laila ta cuce ni” ya iya fadi. Sai a lokacin Haisam ya wani tuna da ita, wani
daci ya sake ji, ciza lebansa yayi wanda ya bushe kamar hura. Takawa yayi sannu a hankali
har gaban Bilal. Mika masa hannu yayi, shi kuma Bilal yana jin tafijya saiya dago kai.
“Muje muyi mata sallah, addu’a tafi bukata” Haisam yace.
“Bazan iyaba” Bilal yace cikin kuka. “Ta rasu tana tunanin na tsane ta.. La haula am so
stupid” ya sake fadi. Duk abinda suke yi Imran yana gefe. Shima yana kewar Shamsiyya,
yana bukatar ta amma dole ya dauki dangana. Dukawa Haisam yayi ya dafa Bilal, “At least
ta tafi ta bar maka wani abu… Kanada Ajwad… Nikam i only have her memories” yace,
idansa yanzu ya bushe. Banda daci babu abinda ranshi yake tunda kukan zuci ya koma
wanda yafi na waje zafi. Girgiza kai Bilal yayi saiya dafa Haisam ya mike, a ranshi tunani
daya yake, wai yau shine kusa da Haisam. Dama idan arziki bai hadaka da mutum ba
waninsa zai hadaku.
Kaftan dinsa yasa saiya dauko hula, dama zai fita kenan yaji sakon mutuwar. A motan su
Haisam suka tafi inda Imran ya tuka. Daga shi har Haisam bamai iya tuki kafin subi
Shamsiyya.
Koda suka isa har Mommy ta gama mata wanka tunda Haisam bai r
an. An suturta na an
saka mata turare. Tana kwance akan katan rug a falon Zailani. Yan uwa daya bayan daya
suketa zuwa ana mata addu’a ana bankwana. Fijr ta kulle kanta a daki bata fita ba. Babu
yadda Anty Fadila batayi ba amma taki budewa. Suma su Haisam sukaje domin su ganta.
Haske sukaga tayi abinta, anan suka mata addu’a suma.
Wajen 10 na safe aka kaita gidanta na gaskiya, gidan da kowani mutum yake jiran zuwa.
Fatan mu kawai mu cika da kyau da imani. Bayan nan aka soma karban gaisuwa gadan
gadan. Tayi mutane har mamaki akeyi tunda batada shige shige. Ita Laila ranar ba taje aiki
ba. Anyi salari watan dubu goma aka bata. Saita wuce kasuwa domin ta kashe, kuma last
week baban wani Adam ya bata 5k zata rinka mashi extra lessons.
Destiny dan jagaliya ya tashi cikinsa yana kiran ciroma, jira yake Sameera tayi abinci
amma batayi ba. Cornflakes ta saka ma yaranta na leda da madaran peak shima na leda da
suga suka tafi school dashi. Kara barci takeyi abinta balle cikinta yanzu ya fito sosai wata
biyar. Da Saif ya gama jiransa saiya fita.
Ita batada rowa, idan kana waje tana kuma cin abinci babu yadda zatayi dole ta baka koda
bata soba. Sai dai kuma Saif baya wuce tayi, kuma abin yanzu ya soma takura mara, dama
ace sanda yake da shi yana bata ne. Amma da samunsa da rashin sa duk daya ne wajenta.
Tashi tayi ta wuce kitchen, plantain ta dauko ta fare tana soyawa. Saita fashe kwai guda
uku ta yanka su albasa, green pepper, sausage, madara da butter. Tana kokarin hada ma
kanta plantain Fritata.
Saida yakai bus stop ya tuna baida kudin mota, gashi maman Bukola tace tanaso ta
ganshi. Yana kyautata zaton ko Bukola zata dawo ne. Anan ya juya ya koma domin ya roke
sameera kudi, yanzu haka tana binsa dubu hudu. Kullum dari biyu dari uku haka take bashi
Kota so ko bata soba.
Kamshi ya dokan mashi hanci, duk tsammaninsa makwabta ne. Aikam yana shiga falo ya
soma kwala kiran Sameera sai yaji kamshin abinci. Balle ta siya spices na abinci kala kala
idan tana girki kamar kana restaurants dan kamshi. Ranshi yayi mugun baci, a fusace yaje
kitchen ya tsaya, tsoro ma ya bata. Ya wani hada rai yana haki.
“Dan rainin wayo saida na fita zaki so ma girki?” yace a tsawace. Kallonsa tayi saita juya
tayi flipping Fritata daga kan tukunya non-stick. A miskilce ta soma magana.
“Ai ba kai ka siya ba, kuma sanda naga dama zanci”
“Bakida kudin da zaki wulakanta ni, wallahi saina sake ki”
“Bismillah ina jira” ta ce masa itama a fusace. Ta gaji da threatening dinta dayake yi.
Motsi bakinsa yakeyi amma babu kalmar saki balle wani abu. Yasan Sameera ce foundation
yanzu dake rike gidan sa. Balle ga yara kaca kaca, idan ta tafi ya Kade. Tsaki yayi saiya tafi,
kudin ma ya fasa tambaya. Zai fita zai nema na kansa, yana kudi kuma zai ci ubanta.
A tsakar gida ya gansu su shida, yan sanda masu kaya blue da baki. Sai wata kamar
shugaban su fara sol kyakkyawa sanye da tabaro. Duk daukarsa Maman Bukola ne ta gaji
da jira ta tura a dauke shi tunda kudinta na hannunsa.
“Wallahi yanzu zan ranta na mota na tafi” yace tsoro fal ransa. Mamaki yan sandar suke yi.
Shugaban ta karasa wajansa ta tsaya, tuni ya soma gumi, zare tabaran tayi sai tace
“Sunana Inspector Rumaisa Mohammad(Nimra) wa’annan colleagues dina ne” saita nuna
sauran. “Zaka hau mota kaje ina?”
“Gidan Hajia Mujiba mana”
“Ban gane me kake fadi ba” tace saita mika masa wani takarda.
“Laila muke nema, ina tunanin Kaine mijinta”
“Kome ake zarginta dashi, she did it, i know she did it… Karku raga mata” yace cikin fara’a
tunda ba wajensa aka zo ba.
“Ana zargin ta Kashe kawarta Shamsiyya” Nimra tace
Tunani ya soma saboda bai gane ba, itama ta lura da hakan. “Ana kiranta da Haske”
Ja da baya yayi sosai harda tuntube. A duniya yana tsoron mutuwa balle kuma na wanda
ya sani. “Annabi” yace cikin tashin hankali, ya kasa gasgata abinda yaji.
“Sallalahu alaihi wasallam” Nimra tace.
Kofan Laila a garke, shiya rakasu har makaranta aka ce tace batada lafiya bata zoba. Anan
su Nimra suka tafi suka bama Saif number din wayan dazai kira idan Laila ta dawo. Koda yaa
koma Sameera ta gama Fritata ta kusan cinyewa, balle tanajin yan sanda tasa sakata duk
ma daukarta wajen Sait a kazo.
Anan yake gaya mata Laila ta kashe Shamsiyya, itama taji mutuwar suna gaisuwar arziki
da ita kuma ta taba siyan turaren 1500, yan dari biyu ta bata saita ce ta rike canji ta basu
Abul.
***
Mallam Baban Laila yazo duba wani abokinsa a Malali, anan yaji anyi mutuwa. Da sukaje
sai yaga ana maganar Shamsiyya, sannan yaga Imran. Kamar su daya dan shi namiji ne.
Kiransa yayi yaji ko sunada alaka. Sai yace shine kaninta kawai namiji. Jaje ya masu yace
yanaso yaga Zailani. Har tabarman Zailani ya kai shi. Dayake babu wanda ya sanshi.
Bilal daya sanshi hankalin sa baya wajen, ya rufe ido yana tasbaha. Bayan sun gaisa sai
yace shine Baban Laila a gari yaiji, Daddy shiru yayi yana nazari. Kana ganinsa mutumin
arziki ya akayi ya haifa tsinanna. Haisam ne ya tashi da sauri, “Wace Lailan?”
A lokacin Bilal ya bude ido, anan ya rike Haisam dan daga dukkan alamu fitsara zaima
Mallam. “Ka barni, Laila tafa kashe ta” Haisam yace yana tirjewa.
“Exactly Laila tayi kisan ba shiba, koba komai yaci albarkacin manyanta” Bilal yace. Gefe
Haisam yayi yana numfashi sama sama, har yanzu kukan zuci yake. A cikin tashin hankali
Mallam ya tambayi meya faru.
Tiryan Tiryan kanin Daddy Zailani ya fada iya shi abinda ya sani, da kashe auren Haske
wajen Bilal da sauran makirci nasu sata sai kuma mutuwa. Kafin a gama har mallam
hawaye ya ciko mashi.
“Dan Allah kuyi hakuri, innalillahi wa inna ilayhi rajiun”
Babu wanda yace komai kawai ana jimami, shi kadai yasan abinda ke damunsa. Ga
bala’in talauci da ko haya basu biya ba. Dama yazo abokinsa ya ranta mashi wani abu ne
yaje ya siya masara su barza ko fate a rinka ci kafin wani hanya ta fita a samun cin tuwo.
Yanzu kuma Laila ta jawo mashi ruwan datafi karfin sa.
Bilal yayi waya da DP0 inda yake ce masa ba’a ga Laila ba, anan yake gaya masu. Mallam
ya sake basu hakuri sannan saiya tafi. Gidan Laila yaje direct, a bakin gate ya tsaya yana
jiran ta dawo daga inda taje. Ita kuma ta siya chiffon zata dinka kimono sannan tayi cefane
abinta hankali kwance.
Mallam ta gani a kofar gidan, gabanta yayi mugun fadi. Tasha wani abu ya faru da
Gwaggo, “Mallam wani ya mutu ne na ganka duk hankali a tashe” tace.
Kallonta yayi yana hawaye, “Allah ya isa tsakanina dake, Allah saiya bin min hakki na.
Ban tozarta kiba amma shine kika cin min fuska haka… Kisan kai Laila na kawarki… Me
shamsiyya ta maki da zaki kashe ta? Wannan wani irin kafirci ne? Bakida tausayi sai kace
yar ta’adda.. Allah ya tsine maki albarka, duk wani alherin duniya Allah ya rabaki dashi,
duk wani tashin hankali Allah ya hadaki dashi ” yace yana kuka saiya tafi. Itama kukan ta
soma tana rokonsa ya yafe mata amma baiji ba yayi tafiyar sa, napep ya tsaida ya shiga
Share hawayen tayi ta wuce ciki, ta dan jin dadi akan mutuwar. Koba komai zata rabu da
kaya, bazata rinka ganin how inlove Haske take da mijinta ba. Kokuma sabon atamfa data
saka, ko sabon gwal kokuma laushin fatan ta. Yanzu tana kwance kasan kasa sai kaka!
Sai dai gabanta ya fara fadi, tunda Mallam ya sani kafin ta sani gari zasu dauka. Saif ta
window ya lekata. Anan yayi ma Nimra flashing saita kira, a hankali yace saita bashi dubu
biyar kafin ya gaya mata information. Bayan sun daidaita sai yace yanzu Laila ta shigo suyi
sauri. Sameera na gefe tana Kallonsa tana jimami, tanaso taje famfon waje ta debo ruwa
amma tana tsoron kada Laila ta kasheta itama. Yanzu bala’in tsoronta take, ashe ba ita
kadai ba, a hankali Saif ya tashi yaje ya saka sakata. Saiya rage muryan TV kafin Laila taji
haushi tazo tayi ram dasu.
Bilal haka kurum jikinsa bai bashi, sai yayi ma Driver na gidan su text akan yaje. Da zuwan
sa saiya shiga motar yace su nufa gidan Laila, yanaso yaje ya jirata. Tana daki tana hade
kayan ta a babban jaka, naman data siya tana tafasawa zata saka a cooler ta tafi dashi.
Daga cikin kayan harda atamfa data sace na Haske da wanda ta bata kwanan nan. Bilal ta
gani a kanta babu tsammani.
Sai yanzu tsoro ya fara kamata, baya ta fara ja dashi, anan tasan kashin ya soma bushewa.
Da kafa ya tokare jakar data hada. Karfen labule ya ballo. Anan ya zabga mata guda daya,
tsandara ihu tayi tareda lankwashe baya. “Kadan kika gani, yanzu zan kaiki inda kika
kaita… Ina ce nace ki fita harkan ta amma kika ki ji saboda taurin kai” saiya sake zabga
mata.
“Dan Allah kayi hakuri”
“Hakuri kika ce! She’s dead… Gone bazan sake ganinta ba, ko tausayin yaronta bakya yi,
so kike abinda ya faru da ita tana karama ya farun mashi? meyasa bakida imani ne?” Sai ya
sake zabga mata. Anan ya finciko ta ya soma kila kamar ganga. Ihu takeyi tana kuka. Saif ya
rufe kofa kafin azo suma ayi masu nasu. Sameera dai tayi shiru tana tunani. Haisam yayi
masu Nimra Text idan zasu arrest su kirashi yaje, haka suka biya suka dauke shi.
Koda suka isa ihun Laila sukaji daga bakin Gate, da sauri suka shiga. Kayan Bilal yayi kaca
kaca da jini fari ne, yana kokarin kasheta. Haisam ne ya rike shi, “Please ka barta haka,
mutuwa hutu ne a gareta.. Gwara taje hukuma ya soma hukunta ta kafin mu hadu a lahira”
anan Bilal ya barta. Har Haisam ya fita ya bama yan sanda waje, saiya juya ya soma
tokarinta.
“This is for me and Ajwad, da kika rabamu da abinda muka fi so a rayuwar mu, kika kwace
mana farin cikin mu kuma Hasken Lantarkin mu” saiya janyo ta ya kakkale ta da mari.
Nimra ne tazo da Ankwa, tana saka mata tareda reading mata rights dinta.
“Laila Muhammad you’re under arrest for the murder of Shamsiyya Zailani Abubakar,
anything you say here would be used against you in the court of law, you have a right to an
attorney, if you can’t afford any one would be provided for you”
“Wallahi bani kadai bace, harda Hadiza… Ammi nake nufi” ta fada tana kuka. Girgiza kai
Haisam yayi cikin bacin rai, “Hadiza taji tsoron haduwan mu” yace. Wannan kenan!
Tafi bakin cikin yadda asirinta ya tonu akan mutuwar Shamsiyya, yanzu ta ina zata fara
zaman gidan yari? Wani rayuwa zatayi a chan? Tasan cewa zata bala’in raina kanta. Saita
soma nadamar biye ma Ammi akan kashe Haske, wannan ba komai bane illa gurguwar
shawara. Dama basuyi ba an barta tana mata bakin ciki tareda da kaita kuma ta baro. Ko
babu komai zata rinka samun duniya ta wajen ta.
Da sun saka kawai an mata fyade an kuma sace Ajwad kamar yadda taso, sai dai yanzu
kam yadda zata gidan yari haka dole Ammi zataje. Suna mota sargafe da ankwa za’a police
headquarters dake Independence way. Nimra ta riga ta kira partner dinta Abu Dhar kuma
kamar babban yaya yake a wajenta. Anan yaje da boys dinsa domin su damko Ammi.
Ita Hadiza ta aure mai kudi amma ko sau daya bata taba cewa a gyara gidan gadon su. Ko
fenti sai dai idan wani dan uwa ko Hajia binta. Ita ce ta saka masu borehole a gidan kuma
tunda ya lalace batada labari bata sani ba sai sanda Ammi zata koma. Anan taji labari kuma
tayi mirsisi.
Ammi na bakin rijiya tana janyo ruwa, tana yi tana tunani saita saki gugar ciki. Tsaki tayi
tabar wajen, ruwan ma ta fasa diba. Dama wanka zatayi yau kuma ta yafe. Daki ta shiga ta
zauna akan kujera karama. Sai taji karan siren, duk daukarta wucewa za ayi. Bata kawo
komai ranta ba tunda tasan cewa Haske bata gansu ba kafin su dauketa da mota.
Kwadan zogale tayi yana gefe wanda bata ciba, ta janyo kenan tana ci sai mutane suka
shiga gidan. Yan sanda guda uku da Abu Dhar.
“Lafiya kun saka bakaken kaya kuka shigan min gidan? Wannan ai shiga hakkin dan adam
ne!” tace masu a fusace. Kallonta Abu Dhar yayi yana murmushi, a natse ya soma magana.
“Hajia kiyi hakuri dan Allah”
“Toh menene kuka shigan min gida?”
“Dama muna neman wata Hadiza Abidina ne?”
“Ni ce wake nema na?”
“You’re under arrest for the murder of Shamsiyya Abubakar Zailani, you have a..” ya
gama karanta mata rights dinta. Anan gabanta yayi mummuna fadi.
Yau anata shiri za’a Kaduna ta’aziyya tayi karyan bayanta yana ciwo, gashi yanzu anzo an
damke ta. Toh waye yace ita ce? Anan ranta ya bata kila Laila ta kai kararta saboda cin
amana, da karfi ta soma magana.
“Wallahi baku isa ba, da tsufana zaku ce nayi kisa. Kalle nifa! Shin wai wama ya fada
maku”
“Hajia karki saka aikin mu ya bamu wuya, kawai kiyi shiru muje”
“Ai bani kadai ya kamata ku kama ba, harda Laila”
Basu tanka ba illa ankwa da suka makala mata a hannu aka soma janta. Ko rufe gidan
basu bari tayi ba aka sakata a bayan Hilux domin aje Kaduna. Suna tafe tunani takeyi kala
kala yadda zata zabga karya tace banda ita.
Koda suka isa Laila ta tsufa a bayan kanta, da Haisam Ammi ta soma karo. Mummunan
kallo ya watsa mata wanda tasha jinin jikinta, amma a haka ta dake ana ingizata ta fara
magana.
“Dan lele mutumina wallahi karya ake min, kayi kokari ka fito da mamanka daga wannan
sharri saboda nasan aikin makiya ne” saita tura bakinta tana nuna Bilal watau shi yayi
tunda ya rasa Haske.
“Kiyi mana Shiru nace” Sergeant Jummai ta daka mata tsawa. Ita kuma babu yadda
zatayi ta rufe baki. Ganin yanayin Laila yasa gabanta ya fadi. Duk da farko tana ganin kamar
wasa ne abin. Anan aka kwace mata kallabi da takalmi. Ashe rabonta da kisto kusan wata
uku. Duk gashin yayi chibir chibir kamar an gama gwagwiye masara. Kunya ya lullubeta
sosai ta kasa kallon Bilal da Haisam.
Bilal ne yace a barsu a cell tukun, kada a fara case din gadan gadan sai anyi sadakan uku.
Yanzu su soma hutawa bayan kanta.
Ba Fijr ta yadda ta fito ba saida Abubakar ya kirata a waya yayi mata nasiha. Ranar ko kan
Ajwad ba tabi ba balle wata Hafsee. SMA aka rinka basu. Zaman dirshan tayi akan kapet
tanata ruzga kuka. Ita bata taba tunanin Haske zata tafi ba musamman yadda takeda
kuruciya.
Ta saba ganin mutuwa yana faruwa da tsoffi ne kokuma wajen nakudan haihuwa. Amma
duk wani matashi data sani koda hatsari yayi yana warkewa ras ya cigaba da rayuwar sa.
Anan ta sake imani da Allah da manzan sa. Ta kara ganin wani fannin rayuwa wanda bata
sani ba.
Da azahar data fito bata ma ganin gabanta, tayi kuka ta koshi dishi dishi take gani. Ga
muryanta ya tafi saboda kuka, abinda yasa ta fito Abubakar ya roketa alfarma akan yaranta
suna bukatar ta kada suma a rasa su. Da dafa bango taje har dakin Anty Fadila, Ajwad
tagani hannun ta tana bashi ruwa da glucose. Saiya bata tausayi ainun, anan wani siririn
hawaye ya malalo mata.
“Antyy” tace da kyar, amma kuma maganar bai fita ba. Saida tayi gyaran murya inda
hankalin Anty Fadila yaje kanta. Tana daga idonta itama yayi jazur dashi. Ajwad yana
sagale a jikinta ta mike taje kofa wajen Fijr. Hannu ta rike mata saita kaita bakin gado
domin ta zauna.
Anan ta mika mata shi saita wuce ta dauko Flask, shayi ta hada mata da milo, coffee da
lipton kamar yadda Fijr ke yin abinta. Saita juye mata madaran gwangwani fiye da rabi. Fijr
batayi musu ba ta karba ta soma sha a hankali. Abinka da yunwa lokaci kadan take cirewa
a bakinta domin ta huta, kafin kace kwabo ta shanye.
Bayan nan saita soma bama Ajwad nono. A lokacin Anty Fadila ta shiga bayi tayi alwala
zata kabbara sallah. Sanda ta idar tana azkar sai Ajwad ya soma barci. Karbansa tayi saita
goya, dashi ta cigaba da addu’a abinta. Sosai tayi ma Shamsiyya fatan dacewa a gidanta na
gaskiya.
Hafsee ne ta shigo da doughnut a hannun ta, tana ganin Fijr ta ruga a guje domin ta
rungume ta. Ita ma tana bugun kofa amma bata tanka ba. Da kanta ta soma cire ma Fijr
riga domin itama tasha. Bayan nan sai ta sauka tayi gaba abinta. Taga gidan ya cika da
mutane ko’ina sai wasanta take babu abinda ya dameta.
Sai wajen la’asar Fijr ta samu karfin jikinta bayan taci abinci, anan ta saka hijab domin ta
gaida bakin da suka je masu. Yadda taga mutane sunyi masu kara abin ya burgeta. Lallai
mutane rahama ne, kuma mutum ya rinka kyautata mu’amalan shi koba komai idan ya
mutu za’a bishi da sheda na kwarai.
Yasmin ta gani a falo tana kawo ma mutane abinci, hidima takeyi sosai abinta. Mommy na
daga gefe ta rufe ido. Ita abu daya take kokarin ganewa. Wai menene Shamsiyya tayi masu
da suka mata wannan abu, ace fada ya wuce na fatar baki ya koma kisa? Tanaso taje police
station wajen Ammi amma Haisam yace a barsu sai anyi sadakan uku.
Yan uwa dai sai tsine ma Hadiza suke da albarka, mamaki suke kamar ba nono daya
tasha da Hafsat ba wannan bakin hali. Kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake yana fadin
mugun abinda tayi masa, yau da ace mutuwa tayi babu wanda zai bita da sheda na kwarai.
*
Bayan sadakan uku..
Gidan Alhaji Zailani baya rabuwa da mutane, kullum mutane sai karuwa suke ana tayashi
jimami. Musamman idan aka ji kanwar mahaifiyarta da kuma matar uba tayi kisan. Har a
jakar magori an saka abin inda Laila da Ammi suka sha zagi. Mallam Mohammadu baban
Laila yaje kasuwa wajen abokansa yaje abin a radio. Yadda ake zagin Laila da iyayenta
saida yaji babu dadi. Baiji ba bai gani ba anata watsa mashi ashar.
Zazzabi ya lallube shi nan take jininsa ya soma hawa, haka ya hakura ya koma gida da
kyar ya kwanta akan gado. Rabon da yayi kwanciyar rana ya mance amma yau shine
kwance a daki.
Su kuma su Laila a jail babu mai siyan masu abinci, dama a cell kai kake ta kanka idan
kanada yan uwa sai kaci. Tsakanin wanda aka kulle su tare daga barayin kudi, sai wanda
sukayi fada da mutane aka kulle. Su kadai ne yan kisan kai. Anko tsangwame su sosai.
Tsakanin su biyu Ammi ta soma zagin Laila akan menene zata ce harda ita.
Kallan hadarin kaji tayi mata saboda ai gaskiya ta fada, suna cikin sa’insa sai Laila ta kalle
Ammi da mari. Aikam dambe ya kaure tsakanin su. Babu wanda ya rabasu cikin cell din
suka goga hammata.
“Dan uwarki tsohuwar Banza yau saina maki laga laga bakisan kema haushi kike bani ba”
“Daga kaina bazaki sake rashin kunya ba” Ammi tace. Banda hambarin Ammi a ciki Laila
bata komai. Ammi tayi kokari ta kai mata naushi a hanci nan bakinta ya fashe. Wani Officer
ne yaji hayaniya ana masu waka ku casu arna ku casu.
“Kaiii meye haka?” ya daka masu tsawa inda suka bari suna hararar juna tareda numfashi
dan sun daku. Bude kofar yayi ya fito da Laila zai canza mata daki. Anan dabara ya fado
mata, tasan dai maza da bin mata idan ta bashi kanta saiya kyaleta ta tafi. Jini yana malala
a bakinta ta soma murmushi wanda ko hakorin ba’a gani. Gyara rigarta tayi ta soma sagalo
shi kasa.
“Officer tsaya muyi magana” ta fada cikin kissa tana kashe mashi ido. Asalin dan iska ne
kuma ya gane abinda take nufi. Kallonta yayi sama zuwa kasa. Ba kalar matan dayake so
bane amma tunda ta kawo kanta bari ya kwasa rabonsa.
“Menene ina jinki” ya fada fuska a daure.
“Dama… Dama… Ina so mu gyara zancen ne”
“Me kenan ban gane ba”
“Idan akwai abinda zan iya maka sai ka fitar da ni zan iya” saita cigaba da juya mashi
jikinta. Haushin ta yaji sosai saboda bata iya salon jawo da hankalin namiji ba. Amma zai
koya mata darasi.
Wani ofis taga ya nufa da ita, anan ta soma murna tarkonta ya kama kurciya zata fita.
Anan yayi abinda yaga dama da ita, duk zaton ta gida zata wuce sai ya mayar da ita wani
bakin daki da ko tafin hannun ka baka gani dan duhu ya rufe yayi tafiyar sa. Ashe an masa
transfer zuwa calabar kuma ranar karshe ne yazo sallama yaji suna dambe.
Bilal ya fara isa station din bayan an idar da addu’an. Haisam yana zaune yana tarban
baki. Duk yanajin wani iri tuntuni hakurin sa ya gaza baisan meyasa ya yarda aka ce sai anyi
uku da.
File dinsu Ammi da Laila aka fito dashi, suma sai aka fito dasu suka sake bada statement
dinsu. Anan wata Sergent Hauwa taga Laila, ta ganeta sosai saboda tana yawan zuwa
Barau Dikko kuma suna haduwa. Sergent Bello yace mata ai kawarta da suke aiki tare ta
kashe. Salati ta soma tana tafa hannu, ko sati uku zuwa hudu ba’a yi ba kuma taga Haske
inda tace mata zatayi aure.
Suna mutunci da Haske sun saba sosai, ita tana ce ma Haske farin takarda, ita kuma ta
kirata mai bakin riga. Saida taje ta kaure Laila da mari. Rashin imanin yayi yawa, wai
amininka kayi ma haka. Suna haka sai ga Haisam. Napep ya hau ya gudu saboda kar
agansa.
Ammi bata saduda ba ta soma mashi magana tunda tasan yanada bala’in saukin kai.
“Dan Lele kazo kayi masu bayani kace wannan algunguman ne tayi min sharri”
Baiko kalle ta ba yabama Bilal hannu da sauran mazan suka gaisa. Daya juya sai yace, “Da
motar wa akayi? Koko wancan kanwar shedan din tanada abin hawa ne”
Jikin Ammi yayi sanyi sai tayi shiru, “kunada lawyer ne ko za’a baku na gwamnati?”
Sergent Hauwa ta tambaye su. Girgiza kai sukayi sai aka hadasu da Barrister Abubakar
Sulaiman. Bilal yasan yadda za’a yi akayi cuku cuku gobe za’a fara case din gadan gadan.
Kashegari..
Da tambaya suka isa gidan. Sameera taji labarin mutuwar kuma a jakar magori. Anan ta
roke Saif alfarma akan suje suyi gaisuwa. Nokewa ya rinka yi shi baya san gawa, wayar
mashi dakai tayi tace ai an dade da birne Shamsiyya kuma mutuwa yana kan kowa shima
zai so idan ya mutu azo ayi mashi addu’a.
Kwana ukun nan mutane da yan jarida sai zuwa gidan sukeyi sun je gulma. Idan ka bashi
kudi ya baka labari amma bazaka ce ga sunar mijin ba a cikin news din. A haka yayi kusan
dubu arba’in. Napep Sameera tayi masu chata har Malali.
Shi a waje ya zauna kasan canopy wajen su Daddy, yayi masu gaisuwa amma baice ga
alakarsa da kowa ba. Yanzu yake murna Laila bata bar masa annoba irin ta ba. An kawo
mashi sinasir, waina, dambun nama da fanta. Ya lura wajen kadan kadan ake ci ba’a wani
ci. Shi kam ya saka mai yawa a gaba yaci sosai yayi gyatsa, anan ya gode ma Sameera akan
3
tilasta mashi da haka abinci zai wuce shi.
Bayan nan ya soma murmushi, “Allah sarki Haske ko kina raye ko bakya raye in dai abinda
ya jibance ki ne sai anci an koshi…Allah sarki ki huta lafiya” ya fada yana watsa dambu
cikin bakinsa.
Dadin abin Sameera taji a jakar magori maman Haske ta rasu kuma Hadiza twin din
mamanta ne. Bata sha wuya ba tace tana neman wanda ta riketa. Zuwa tayi wajen Mommy,
tun kafin ta karasa wajen taga kamanni. Gefen Mommy ta zauna inda ta soma gaida ta.
“Ina wuni ina gajiya, Allah ya jikanta da rahama yasa ta huta kuma aljanna ne makoma”
“Amin Amin, nagode sosai Allah ya saka da alheri” ta fada chan kasa. Wannan addu’an
saida sameera ta koya ma Saif a kaikaice kafin yaje yace masu Annabi kawai yana kallonsu
dan ta lura jahili ne.
A lokacin sai mommy ta tashi zata kotu, yau za’a fara karfe sha daya. Sameera ta mike wai
zata, kallonta mommy tayi tana nazari, “A ina kika san Shamsiyya? Kawarki ce?”
“Ni kishiyar Laila ne” tace a sanyaye. “Muje” mommy tace.
Ga tsohon ciki haka Sameera ta rinka sauri ta fita waje, anan taga Saif ya kishingida babu
abinda ya damesa. Kunya taji sosai tasan yadda yakeyi ba’a san waye shiba. Dari biyu ta
bashi tace ya sameta a NDA High Court Of Justice. Rai baiso ba amma babu yadda zaiyi. Ita
kuma mota daya ta shiga da Mommy.
Abubakar ne ya dauke Fijr da Yasmin. Daddy kuma da Anty Fadila. Daddyn Haisam shine
Lawyer wanda zai wakilci Shamsiyya.
Daga Yan jarida zuwa mutane duk sun hallara anaso aga abinda za’a yanke masu. Alkali
mai shari’a Justice Yusuf Ahmad Hadeja shine zaiyi. Adam Mijinyawa SAN da Barr Abubakar
Sulaiman sanye da suit da tie sai bakin kayan lauyoyi.
Anzo dasu Laila da Ammi daga Cell suna zaune a gefe. Bayan kotu ta fara inda Adam da
Abubakar suka gabatar da sunayen su. Case number 98746 tsakanin Shamsiyya Abubakar
Zailani da kuma Laila Mohammad da Hadiza Abidina.
“Ya Mai girma mai shari’a, idan wannan kotu mai alfarma zata bamu dama mu fito da
dukkan shedan mu munada tabbacin cewa Laila da Hadiza suka kashe Shamsiyya” Adam
yace
“Kotu ta baka” Justice ya amsa
“Ya mai girma mai shari’a Hadiza ta kasance daya daga cikin tagwayen malam Abidina,
dayan yar uwanta itace Hafsat wanda ta haifa Shamsiyya…” anan ya zayyana ma kotu tun
auren Zailani da yadda take musguna mata. Kafin ya gama cece kuce ya soma a kotu ana
tsine mata albarka. Anan alkali ya buga sandar sa wanda ya sake magana za’a cisa tara.
“Objection, this is pure speculation “Barr Abubakar yace. Murmushi Daddyn Haisam yayi.
Shi idan ta shine basai anzo kotu ba. Kawai Alkali ya yanke masu hukunci a ofis. Ammi ne
takeda taurin kai, itace tace a hada da yan jarida. Tanaso mutane suyi sympathizing da ita.
Ya zata rike Shamsiyya kusan shekara ashirin kuma ta kashe ta.
“Karka damu Barr zan waye ma kowa dake cikin kotun nan komai” anan ya kuma bada
labarin kawancen Laila da Shamsiyya, yadda Laila ta taimaka mata sanda Ammi ta koreta
yasa Shamsiyya take ganin dole ta rama ma kura aniyarta.
“Still speculation… Bashi bane za’a ce ita tayi kisan'” Barr Abubakar yace.
“Amma akwai motif ai, kuma Shamsiyya tace taga Laila” Adam yace.
“Mai Shari’a yanzu an daure wannan matar masu mutunci, saboda abinda Shamsiyya
tace… Sanda ta fada anyi psychological evaluation tunda ance ta buge kanta…Kila gizo ta
gani ranka ya dade” Barr Abubakar yace.
“Toh kai Barr Adam kanada wani hujja da zaka nuna mana akan cewa Laila da Hadiza ne
sukayi kisan kokuma kawai akan wannan abu ne” Justice yace
“Ranka ya dade bincike ya nuna cewa Shamsiyya batada wani abokin hamayya sai su,
kuma da motar Hadiza aka kade ta. Ita kanta Laila ta fada da bakinta ba ita kadai bane
harda Hadiza. Shamsiyya bataga Hadiza ba da idanta Laila kawai ta gani”
Kallon Barr Abubakar Justice yayi saiya soma magana, “Me zaka ce game da abin da aka
fada?”
Inda inda ya soma saiya mike tsaye, “Daman cikin tsoro ne ta fada… Kuma ita batada
mota, sannan Hadiza tana zaune yanzu a Zaria ne”
Haisam ne ya shigo ciki, sai lokacin aka lura ya fita. Mai gadin gidan da abin ya faru ashe
sunada CCTV, abinka da layin masu dashi. Gate din akwai camera kuma ya dauki motar
Ammi yana wucewa sannan ga dishi dishi na mata biyu a ciki.
“Mai girma mai shari’a ga wani sabon evidence an samu, bari mu kunna ma kotu domin
kowa ya gani” Adam yace.
Anan ya saka masu a katon Plasma, ga Haske tana tafiya da sauri da sauri sai taji karar
mota. Juyawar da zatayi sai mota ya dauke ta. Mommy da Anty Fadila saida suka rufe
idonsu. Abin yayi mugun gani ga tausayi. Bilal ya soma tafasa a wajen, Fijr ji take kamar taje
ta shake Laila. Gameda Ammi kuwa ta rasa me zatayi, wai ace mahaifiyarta keda wannan
mugun halin.
Tun sanda abin ya faru idan ta tuna sai tayi kuka, ance ka zaban ma yaranka uwa nagari
amma Daddy bai kyauta masu ba daya aure Ammi. Gashi yanzu duk inda suka je duniya
zatayi ta kallon su. Alkali ne ya soma magana.
“Gamida case lamba 98746, ni Alkali Yusuf Ahmad Hadeja na yanke ma Laila Mohammad
da Hadiza Abidina dauren muddin rayuwar su. Watau life imprisonment akan kashe
Shamsiyya Abubakar Zailani da sukayi..” haka dai ya gama.
Anan Ammi ta botsare ta soma ihu” Wallahi ba zai yiwu ba” sai masu camera suka soma
haskata. “Wai ya za’a yi ace na kashe yar da na rike da hannu na… Jama’a ku fito ayi zanga
zanga wannan kotu anyi san kai. Mata wanda mazajen su suka aure su bayan sun rabu da
matarsu na farko sannan kuka rike masu yara ku fito muyi zanga zanga har sai an fito dani,
wannan ya nuna duk aikin da mukeyi ba’a gan…Yau nine gobe wata ce… Ku fito… Ku fito”
take fadi tana tafiya, kana gani kasan ta soma hauka.
Laila tunda aka fara batace komai ba, Haske ke mata gizo tana kallonta tana mata
murmushi. Koda ta rufe ido ta sake bude wa zata ganta a zaune. Abin yana bala’in takura
mata. Ana tafiya za’a turata mota sai Saif ya tuna bai saketa ba. Da sauri yabi motar.
“Na sake ki saki uku” waigawa tayi duk jikinta yayi sanyi. Bata iya magana yanzu saboda
Haske data ke gani gefen ta. Kallon Saif datayi saiya ja da baya. Tsoronta yake duk da
ankwa karta zo ta kashe shi. Taga kowa su Sameera, Fijr, Haisam, Bilal taga duk mugun
kallon da suke binta dashi.
Su kuma sai suka koma gida domin su cigaba ma Shamsiyya addu’a. Bilal zai koma Abuja
1
kwata kwata, Haisam ma haka kafin ace ya aure Yasmin dan baya santa ko dis.
Ita kuma Laila da Hadiza an kaisu Prison, an basu uniform dinsu anyi masu rejista. Ba’a
basu daki daya ba daban daban ne. Har yanzu Laila bata bar ganin Haske ba. Abin sai juya
mata kai yakeyi yana takura mata. Kanta ya soma mata ciwo sosai da kyar take gani.
Da aka je cin abinci an bata ta zauna zata ci, Shamsiyya ta gani gefen ta tana mata
murmushi. Kuka ta soma wiwi, “Dan Allah ki yafe min. Wallahi banyi niyar kashe kiba… Ki
tafi ki kyale ni” still gizon yana mata. Cocalin ta ta dauka ta soma chaka ma idonta.
Kwakulewa take kokarin yi saboda gwara ta cire akan ta rinka ganin Haske. Kafin yan sanda
su kai mata agaji ta tsiyaya idon tas jini ko ina.
“Besty! Besty! Besty!!” ta soma ji ta muryan Haske yana dukan dodon kunnen ta. Ihu
takeyi tana birgima “Dan Allah ki kyale ni… Dan Allah ki kyale ni” taketa nanatawa. Wannan kenan!
Bayan wasu kwanaki ..
Kowa yanzu yayi dangana Haske ta tafi bazata dawo ba. Al’amarin gidan Alhaji Zailani ya
fara komawa yadda yake, matarsa kuma uwar yaransa ta kashe mashi yarsa na fari. Ko ina
ana ganin ya gipta zancen akeyi. Yasan wannan ne Kaddaran sa kamar yadda kowa yake da
nashi. Anty Fadila tayi zarra cikin mata, yadda Hadiza ta shayar dashi bakin ciki baiyi
tsammanin cewa zai samu natsuwa haka ba.
Sosai take kokarin kula da gidan daga shi har yaransa. Mamaki sukeyi yadda ta cire kishi
cikin ranta take abinta tsakani da Allah. Tabbas da na kowa ne bakasan wanne ne zaijikan
ka ba. Kuma bakasan tsawon kwanaki da zakayi a duniya ba.
Laila tana gidan yari ta makance bayan ta kwakule idanta. Har yanzu tana zabure zabure
tana jin Haske tana kiranta Besty. Shima sau da dama taso ta tsire kunnen dan yana bala’in
takura mata. Batayi nadamar cizge idanta ba ko dis, in dai bazata ga Haske ba ko abinda ya
jibance ta. Yanzu haka tana marii (Chains) a psych ward ta prison din. “Bestyn Uwarki”
taketa nanatawa daga safe har dare muddin idanta biyu.
Ammi dai tana chan sai tsangwamanta akeyi a ciki. Kowa ya rainata a wajen. Kullum sai
anyi mata duka, yara kananan yan shekara 20 su jibgi banza. Dukta canza fasali ta tsufa. Ga
hakora uku an cire mata. Tana cikin wanka za’a dauke tawul dinta. Idan ta fara nema a
harde mata kafa ta fadi cikin kazantan. Gashi basu bari taci abinci, tana cikin ci wata zata
zo kamar bata gani ta bigeta komai ya watse. Yanzu kam ta gwammace kida da karatu.
Gashi babu ko daya daga cikin yaranta ko Zailani da suka je.
Mommy taje har prison domin ta ganta, kunya Ammi taji sosai data ganta. Ana bada kudi
ta prison din sai inmates su rinka amfani dashi suna siyan su sabulun wanki, Maclean da
dai sauran su. Mommy tayi ma Ammi depositing dubu biyar. Anan Hadiza tayita godiya
tana murna.
Fijr tunani yadda za ayi da Ajwad takeyi. Tanaso ya tashi cikin kulawa fiye da yadda
shamsiyya tayi. Bataso ya fuskanci maraicin uwa ko kadan. Dabara ya fado mata akan
neman Bilal tayi a waya domin yazo. Baya Kaduna kuma zuwa garin yana tuna mashi da
rayuwar da sukayi da Shamsiyya yasa ma ya bari tun asali. Anan tace mashi ta kasa gane
kan Ajwad yazo please kila yana kewar Dad dinsa ne.
Yaron ya girma yayi wayo abinsa bazaka ce ba ita ta Haife shiba. Ta samu yar aiki wanda
take zuwa shago domin ta tayata rike shi idan tana ma customers makeup. Dole ta yayee
Hafsee saboda bazata iya hadawa ba. Ko ajinkin Hafsee tunda ta saba da Lantana, kiriniyar
kwana biyu tayi ta watsake. Balle kullum mommy saita aika an kai mata ita. Yarinyar tafi
yanayi da Shamsiyya akan Fijr, to tana debe mata kewa tunda bata aikin fari balle na baki.
Haisam bai tashi daga gidan aurensa ba, saboda bautar kasan ne daya tafi US abinsa.
Amma yana gamawa ko kwana daya bazai kara ba. Yasmin yanzu takurar datake masa yafi
nada. Ya gane tanaso ta lura dashi taga baya cikin damuwa amma Allah ya amfana bayaso
haka. Yana ganin kamar cin amana ne wajen shamsiyya tareda soyayyar da sukayi tareda
ita.
Baiga kyautuwa akan fara dasa soyayyar wata akan nata ba. Dama bai aureta bane amma
yanzu yasan zuman soyayyar ta kuma bayada niyyar replacing dinta. Bama da kowa ba da
Yasmin, kamar da haka ma yanzu babu abinda ya canza little sister dinsa ce, his Chiquita.
Kullum saita dafa mashi abinci ta tura mashi, da safe kafin ya fita da kuma dinner bata
fasawa. Amma a wajen sa iska ne ke wahalar da me kayan kara.
Ita kuma batayi tsammanin ya dauki wannan tsatsauran matakin ba kuma baya santa.
Kawai taga yana grieving ne bataso ta takura masa. Amma kadan kadan ta soma lura,
saidai mahakurci mawadaci.
Sanda Bilal yazo Fijr sabon kaya ta saka, Swiss lace ne pink Riga da Skirt fitted. Breast cut
din ya yanku, kuma peplum yayi round mai kyau. Dama skirt din pencil ne abin ya karba
jikinta. Smokey blue mascara tasa sai jambaki kalar Taupe. Bata ja gira ba kawai tayi daurin
turban. Shima Ajwad wanda ya soma jan ciki a kasa tayi mashi kwalliya.
T-shirt din Ben 10 ne tareda 3 quater. Koda tazo falo Bilal yana zaune duk hankali a tashe
yana jira. Ganin Fijr dayayi tana murmushi. Bai kawo komai ranshi ba duk daukar sa cewa
Ajwad ya soma samun sauki ne.
Lantana ta kai masa samosa, spring rolls da pepper soup din kayan ciki wanda Fijr tayi da
hannun ta. Ya soma tabawa kenan suka fito. Tun kafin su karasa ya mike domin ya dauki
Ajwad.
“Prince am sorry, nasan Kanata kewa na kamar yadda nake kewar ka” saiya dauke shi.
Shima Ajwad murmushi yakeyi yana jin dadin ganinsa.
Bayan ta zauna saita gaida shi a mutunce, tunda yake da ita bai taba ganin ta so calm and
serene ba. Babu birgi birgi ko hayagaga. Murmushi kawai takeyi tana wasa da yatsanta. Sak
kamar yadda Haske takeyi. Yana cikin ci saiya kware, da sauri ta mike domin ta zuba mashi
Chi Exotic domin ya sha. Data mika mashi saida hannunsa da nata ya harde waje daya, da
sauri ta dauke nata taje ta zauna.
Ta riga tayi rehearsal din abinda zata ce, amma ganinsa gabanta sai komai ya bace mata.
Kwarjinsa yake bala’in dawainiya da ita. Batasan ta inda zata fara masa bayani ba. Duk
wani guts dinta ta nema ta rasa. Idan akwai wanda zaice mata magana zai gagare ta zata
gaure shi da mari sai gata yau ta nema abin cewa ta rasa.
Ajwad yana nan yana gwalan gwalan da sabon motan da Bilal ya mika masa. Shima Bilal
din yaji cewa tana so tayi magana amma tana ganin nauyin sa. Zancen kudi ya kawo ransa,
mamaki yakeyi yadda bazata iya fada mashi nawa take soba. Shi mai bata ne ko nawa
takeso.
Kallonta yayi sai yaga shi take kallo amma tayi maza take dauke idonta, dana sanin
kiransa tayi sosai. Saida yasha pepper soup din fiye da rabi, ya mance rabon dayaci
homemade food saina restaurant, zuwan sa Kaduna kenan ya biya nan direct.
“You can tell me” yace kasa kasa. Murmushi tayi saita soma maganaa natse. Nastuwar da
batayi tsammanin zata iya ba.
“Dama batun raina Ajwad ne, kasan am not getting any younger.” bai bari ta karasa ba ya
tsinke ta.
“Dan Allah kiyi hakuri, nasan kina bala’in kokari. Maybe bana baki credit ma abinda kike
yi amma please ki dubeni ki duba yaron nan karki ce min na amshe shi… Bansan ya zanyi
dashi ba…Please banaso abinda ya faru da Haske ya faru dashi.. Ko nawa ne zan biya ki..
Dan Allah
” Calm down Ya Bilal… Ba abinda zance ba kenan”
“Na gane kinada kuruciya kuma kinaso kiyi living life dinki, but ki yanke min ko nawa ne
zan baki.. 1 million! 5 million!! 10 any amount please Fijr”
Yadda ya fada sunarta saida ta runtse idonta, ya fita daban da yadda sauran mutane ke
fadi gatsal. Sai kuma ta soma wasi wa si. Anya babu cin amana akan abinda takeyi, mijin
yar uwarta ne wannan. Amma wani zuciyar ya raya mata saida ya sake Haske sannan tayi
wani aure kuma yanzu haka ta rasu. Abin daga tausayi ya fara nashi dana Ajwad. Sai kuma
yayi defining kansa zuwa wani babban al’amari wanda ita kanta bata fahimta ba.
“Ba kudi nakeso ba” tace a sanyaye. Kallonta ya soma yi yana nazari. Idan tafi karfin
kudinsa yanzu me zai bata wanda zata saurare shi.
“Me kike so?”
“Aure”
Kalonta yayi inda shima tana kallo, kowa da abinda yake ayyanawa. Idan yace mata a’a ya
taka mata kimarta na ‘ya mace. Kila ma ta mike tayi mashi duka, sai kuma wani zuciya yace
Bilal ne. Yafi karfin cin mutunci wajen ta kome zaiyi mata. Shi kuma tunanin auren yakeyi,
harga Allah baiyi tsammanin shi takeso ta aura ba. Yana tunani yanzu idan mijin da zata
aura yace baisan Ajwad ya zaiyi. Saisaita kansa yayi ya soma magana.
“Auren wa? Ajwad fah. Please Fijr ki taimaka mana”
“Kai Bilal… Auren ka.. If you would have me of course”
Tsit falon yayi, mamaki take yadda ta iya furta maganar. Shima mamakin yakeyi. Bai kawo
ma kansa aure yanzu ba, koda Haske bata rasu ba balle kuma yanzu data mutu. Amma
kuma Ajwad fah? Baiso yaron sa yayi maraici, baiso a maimaita abinda ya faru da
Shamsiyya ya faru dashi. Hawansa Ajwad yayi yana kokarin cire masa hula, wasa yakeyi
yana dalalo masa miyau ko ajikinsa. Anan soyayyar sa ya sake shigan sa.
“zan iya zuwa nayi shawara?”
“Eh babu damuwa” tace. Ita taso zai yarda nan take amma baiyi ba. Asalima kamar baiso
ba, tabbas ita ba mace bace wanda da namiji ya gani zaiyi muradin mu’amala da ita.
Batada siranta kamar Haske, batada natsuwan ta, batada kyan halayyarta. Amma idan aka
fahimce ta bazaa rasa wani abin kirki tareda ita ba.
“Please ki fahimce ni, aure muke magana anan. Ina so nayi dogon nazari” yace kasa kasa.
“No karka damu fah”
Haka suka kafa ma TV ido, suna kallon African Magic Urban dake aiki. Gabadaya basa jin
dadin kallon amma suka daure, duk saboda Ajwad ne fah. Ajwad ya soma barci sai ta kai
shi daki ta kwantar, anan Bilal ya tashi akan zai tafi. Wrap din 500 ya ajiye mata. Da chan
tana gani idonta zai washe amma yanzu sam basu birge taba.
“Ka barshi fah, kudin daka barmin ko taba rabi banyi ba… jwad baya bukatar komai”
“Toh ai bana amfanin Ajwad bane… Wannan tadi allowance ko me yan matan zamani
suke kiran abin… Ko ance maki zanzo zance ne ban bada komai ba, kina bina Shawarma da
Farm Fresh afuwan ban kawo ba'”
Murmushi takeyi kawai, Bilal kamar hawainiya yake. Baka gane gabansa ko bayansa. Yace
zaiyi shawara amma harya fara bada kudin zance. Har motarsa ta rakasa, bata dai ce komai
ba shima haka. Gefe tayi ya shiga ya rufe, saida ya kunna ya sauke window, murmushi yayi,
“Zamuyi magana” kada mashi kai tayi sai ya fita.
***
Abin duniya yayi ma Yasmin cinkoso, Haisam yanzu ya daina daukar wayanta. Ko abinci
idan ta tura saiya mayar yace baya nan. Tun tana ganin wasa ne harta lura da gaske baya
yayin ta. Ko Mommy yana ofis saiya tabbata Yasmin bata gidan zaije ya gaida ta a gurguje
ya koma.
Taje wajen Mommy ta soma mata korafi, anan Mommy ta wanke ta tas. Ta cika gajen
hakuri ya za’a yi mutum matarsa ta rasu sannan ta soma damunsa babu ko dan tausayin
karya. Daukar kit karama tayi ta tafi wajen Fijr, ya fi mata kwanciyar hankali dan ta lura
kamar harda Mommy a cikin wanda basa san hadin.
Ita kuma Mommy tana ganin a bama Haisam lokaci, sanda ya shirya zaiyi abinsa. Sake
gode ma Allah tayi akan barin ta datayi akayi auren Shamsiyya dashi. Da yanzu ta mutu
ba’a yiba Haisam baida babban mikiya bayan su Laila sai ita.
Yasmin zayyana ma Fijr matsalar ta tayi, lokacin kwana daya bayan tafiyar Bilal. Anan ta
soma rangaji tana mata tsiya.
“Yasa ni bana dating yara, sun fiye rawar kai” tace tana dariya. Kallonta Yasmin tayi na
rashin fahimta. “Yaya Abubakar dinfa, ba yaro bane halan?”
“Ke dalla wake ta Abubakar ana maganar mazaje”
“Sister kin barni cikin suspense, kiyiwa Allah ki fada min wa kika samu. Atleast one of us
should have a happy love life”
Ninke kaya Fijr ta cigaba dayi tana murmushi taki magana, itama har yanzu ta kasa yarda
da abinda ya faru. Dundu taji an duma mata a baya.
“Wasshhhh Allah”
“Ko kiyi magana ko ki daku” Yasmin tace tana dariya. Wulla manya idanta Fijr tayi saita
soma magana, “Well Ya Bilal ne”
“Wani Bilal? ” tace tareda daura hannu kan kiji.
“Bilal nawa kika sani? Bansan iskanci!”
Zama Yasmin tayi gefenta ta zuba mata ido, “Bani labarin komai… Everything… Shi yace
yana sanki?”
“Well not really… Ni ce” saita labarta mata abinda ya faru jįiya. Rungumar ta tayi tana
ajiyar numfashi.
“Shikenan kuma mu gadon da mukayi kenan a family dinnan bin samari muce muna
sansu… Atleast ke kin samu mai saukin kai. Nikam nawa dan zafin kan.” saita fashe da
kuka. Bugguga mata kafada Fijr tayi na kusan minti biyar. Saita dauki wayanta. Yasmin bata
san wa ake kira ba sai da ya dauka taji muryan Haisam.
” Hello na hannun dama” tace tana dariya.
“Yayane! Ya garin? Meke tsalle?” yace cikin raha. Dariya ita ma tayi. Yasmin kam idanta ya
sake cika da kwalla. Watau ita kadai ne baya sake ma fuska yanzu.
“Lafiya lau ya aiki da komai?”
“Kalau fah kice ma Ajwad maybe anjima zanzo mashi tsaraba”
“Kardai ku bata shi please, bakai ba ba Ya Bilal ba”
“Babu ruwan ki, he’s my son”
“Toh naji.. Ba wannan ba dama akan Yasmin na kira ka”
Shiru yayi bai sake cewa komai ba, da tana ganinsa da zataga yadda ya hade rai, harya
somajin wani daci cikin ransa. “Hello kana jina”
“Eh meya faru da Yasmin din?”
“Dama tace kwana biyu ne bata samunka”
“Eh kice mata am busy”
“Kai Ya Haisam sister dinka ce fah.. We don’t do this to family”
“Ban mata komai ba fisabillah… Bata barina na sha iska… Eh Iget tana so na or
something haka but tasan wanda nakeso ai”
“Kuma ta rasu ba… Baka ganin it’s okay to move on”
“Boundaries Fijr, Shamsiyya can’t be replaced”
Shiru sukayi na wasu dakikai. Itace ta soma magana. “Eh nagane you miss her, muma we
all do… Amma Yasmin tana kokari, baka tausayin yadda takeji cikin ranta… Haba yaya”
“Kin gane koh, kisan yadda zaki ce ma Yasmin tayi hakuri… Wallahi duk yadda nakeso na
sakata cikin raina na kasa. Ni da ita bazai taba faruwa ba”
Anan Yasmin ta fashe da kuka mai sauti wanda har Haisam yaji. Da sauri Fijr ta kashe
wayan. Shi kam yaji dadi yanzu zata fita harkan sa sosai.
Anyi kusan sati daya babu Bilal babu alamar sa. Tun tana dannewa kamar abin baya
damunta har abin ya soma damunta. Tun kafin ta soma kuka har idan ta tuna sai tayi
hawaye. Abubakar yana kiranta kuma yana zuwa wajenta. But the heart wants what the
heart wants. Bilal take so wannan karan, tana tausaya ma yadda Abubakar zaiyi idan yaji
labari.
Tunani takeyi akan meyasa ta bambanta da sauran yan mata. Koda yake taga wautan ta.
Bilal ba namiji bane wanda zai kalle Fijr, itama ta sani kowane tukunya da murfinsa, kwarya
tabi kwarya. Bilal is very classy and elegant. Yanada kudin da duk macen dayake so zai iya
mallaka. Sannan ga ilimin boko dana Arabi.
Anan ta tuna ta dade dama kanta sauka a islamiya. Koda yake an hanata zuwa ne saboda
yadda take kilar yaran mutane. Bokon kuma ta kasa tanata bin Isi yanzu ya kaita kuma ya
baro. Tana tuna past dinta tana bala’in jin kunya. Dole Bilal yayi mata kallon annoba ya
guje ta.
Bama Bilal kawai ba Isi da Ghali suma sun gujeta, bayan ga dubun samarin da idan ta
wuce ko kallon arziki baya hadasu. Tanada tabbacin cewa eh lallai ita annoba ce, yanke
shawara tayi akan ta cire Bilal a ranta saboda babu dole.
Randa ya ika kwana goma rabon da taji daga gareshi, ta riga ta yanke cewa lallai Bilal
baya yayinta. Abinda yafi bakanta mata rai sau da dama zataji yana waya dasu Daddy ko
Anty Fadila, ita din ce ya tsana. Ita data ke rainan mashi yara. Yanzu idan tace zata soma
yima Ajwad wani mugun abu fah?
Tana shagon ta tana zaune, ranar harda Hafsee taje. Ajwad yana cradle yana barci. Cheat
din WeChat tayi na mtn inda zaka bada naira hamsin a baka 5GB. Instagram Explore page
ta shiga abinta tana kallon comedy skit tana babbaka dariya.
Kamshin cologne taji na OUD yana tashi, yana mata Kamshin na Bilal amma tasan bashi
bane. Daga kanta tayi sai tagansa sanye da farin yadi, ta lura Bilal yafi san saka fareren
kaya. Kuma manya bai fiye saka kananan kaya ba. Dinkin simple ne babu ado ko daya sai
gajeren hannu.
Ya saka silver links na wuya a maimakon buttons sannan kuma akwai a hannun sa. Hular
sa yan Maiduguri na alfarma yana bala’in sheki mai gray, blue da brown akai. Takalmin
Valacci ya sanya slippers. Agogon Fossils ya makala a hannunsa na hagu. Sallama yayi yana
kallonta yana murmushi.
Bata iya amsawa ba illa mikewa tsaye ta sandare kamar taga dodo. Ajiye wayarta tayi
Infinix note 4. Kyau yayi mata sosai amma kuma ita tafi karfin a raina mata hankali. Idan
baya santa ai nan take zai iya fada mata ba ya tafi MIA(Missing in action) on her ba. Zaiyi
magana ta daga mashi hannu alamar tayi mata shiru.
“Banso naji yadda baka sona, koko yadda am not your type ko wani namiji. Idan bakaso
ai ba’a dole nan take saika fada min…Amma fisabillahi daga kaje kayi tunani kamar an
aika baiwa garinsu… I get it banida kalar kyan daka ke so, am not skinny or hot. Banida
degree a Harvard ko Oxford.. Still i refuse to be disrespected” saita soma numfashi, tasan
idan ta cigaba da magana zata iya hawaye kuma shine last abinda takeso Bilal yasan
tanayi.
“Kinga ma min masifan? ” yace yana kallon ta.
“Ba masifa nake maka ba” tace saita murguda mashi baki tareda Wulla idanta. Asalin Fijr
din ya soma motsawa.
Zama yayi a kujera yana fuskantar ta, “Ina jinki idan kin gama sai kiji me nazo fadin
maki” yace yana dariya kasa kasa.
“Ni na gama” tace a shagwabance saita sake murguda mashi baki. Kallonta yakeyi yana”Ni na gama” tace a shagwabance saita sake murguda mashi baki. Kallonta yakeyi yana
mamakin yadda bata tsoron shi sai bala’in tsiwa, shifa baya ta’ammali da mata masu tsiwa,
ya saba shine yake juya su yayi abinda yaga dama. Wannan kenan!
Kallonta Bilal yakeyi, mamaki komai yake bashi. Wai shi da Fijr! Da kamar wuya gurguwa
da auren nesa. Saidai ko baima kansa ba zaiyi ma Ajwad, yana so ya tashi cikin lafiya da
walwala.
“Zauna” yace tareda nuna mata kujera, babu musu tayi abinda yace. Anan ya soma mata
bayani.
“Aiki ne ya kacame min yasa bakiji niba, wannan maganar is very important bana waya
bane nafiso muyi ido na kallon ido… Anyway nasan ban kyauta ba na rashin kira, kawai
naga idan na kira ne zaki so kiji amsa… Hope kin gane?”
Da kai ta amsa mashi, ita kawai tanaso taji menene ya yanke. Murmushi yakeyi saboda ya
lura ta kagu.
“kwantar da hankalin ki amaryar Bilal in sha Allah” yace mata.
Murna ya kamata harta so ta tashi tayi rawa, amma kuma tana kunyarsa. Shima ya fahimci
cewa kunyarsa takeyi yanzu. Wasa da yaronsa yayi suna hira sama sama. Mostly shine yake
maganar.
Haisam yana dakin Abubakar yana kwance, ya rufe ido tunanin Shamsiyya. Yasmin ne ta
shigo, anan ranshi yayi mummunan baci. Zama yayi domin ya balbale ta da masifa. Harya
fara saita fara murmushi tareda magana.
“Kayi hakuri Ya Haisam… Na takura maka koh? Karka damu so ne yake dawainiya dani..
Haka kurum ai bazan yi haka ba, kai da kasan zafinsa da kuma dadinsai expected you to be
understanding amma ba haka bane, koda yake bazanga laifin kaba. Baka sona bai kamata
na takura maka ba…”
No Yasmin ki fahimce ni Dan Allah.. ljust lost Shamsiyya “
” Na gane komai, kuma nima naga wauta na… Bai kamata na takura maka ba.. Shiyasa
nazo na gaya maka zan baka lokacin da kake bukata domin kayi grieving…1, 2, 3, 5 years
Yaya ina jiranka… In sha Allah zaka gane cewa ni mai sanka ne… Shekarana Ashirin so zan
iya jiranka.. Bana saurin komai… Meye amfanin naje inda bazan ji dadinsa ba, gwara
uncertainty dakai”
Tana hawaye amma tasan wannan shine ya dace, gwara ta barshi ya sha iska kamar
yadda ya bukata. Idan rabonta ne ko ana ha maza ha mata sai sunyi aure, idan kuma ba
rabonta bane duk yadda ta matsa bazai taba zama nata ba. Kuma ita yanzu zabin Allah take
nema, sau da dama mutum yana san abu amma babu alheri ciki kuma Allah ya musanya
mashi da wanda yafi dacewa dashi.
Haushin kanta tayi sosai, ta watsar da duk wani tarbiya da kimarta na ‘ya mace. Mikewa
tayi daga zaman datayi akan kapet. Hannu tasa ta goge hawayen ta. Baice komai ba
kallonta yakeyi yana nazari, ita ma bata bukatar sa akan yayi magana.
“Okay Yaya am sorry once again” Sai tayi mashi murmushin ta mai kyan gani. Daga nan ta
juya ta tafi.
Maman Bukola da kanta tabi kudinta bayan taga Saif a TV yana sakin Laila. Idansa ya
soma cika da ruwa yace wai Laila ta kwashe kudin tun ranar daya kai. Gata yar ta’adda
balle yayi mata magana ta kashe shi. Bata gamsu da maganar ba kawai dai ta bar masa. Sai
tace shikenan yaje ya kawo masu takardar sakin Bukola, auren an fasa. Babu yadda baiyi
ba harda kuka wiwi tace a’a. Anan ta tafi tace ta bashi sati daya kokuma ta maka shi kotu.
Baida kudi baida dalilin samu, yasan Sameera bataza bashi ko sisi ba balle haihuwan ta
sai danno kai yakeyi. Ya fita yana yawo sai yaga wani LEA ana neman mai gadi. Bana kwana
ba sunada wannan, shi kawai zai zo tun shidan safe zuwa biyar na yamma. Temporary ne
dayan ya karya kafa.
Aikam yaji dadin abin koba komai zai rinka ma yara kwace. Saidai kuma kudin bazai ishe
shiba samun lawyer domin a bar masa aurensa da Bukola. Shi fa ya riga ya yarda ita ce
silan arzikin sa. Yasa duk yadda zaiyi abar auren sai anyi. Yana ganin idan ya yarda ya
sallama mata zaiyi musabaha da talauci.
***
Bayan shekara biyu…
Fijr tana zaune a falonta, jaririyar data haifa yar wata uku mai suna Shamsiyya ke kwance
akan cinyarta tana barci, kallonta takeyi taga bata bambanta da marigajiya Haske, saidai
kalar fata wannan bata kai wancan ba. Tana so ta girma ta bata labarin yadda wancan tayi
rayuwar ta koba komai ba za’a maimaita wannan mistakes dinba.
Ajwad an saka shi a makaranta yana Step one ranar ya fara zuwa. Ita kuma Hafsee tana
Step two (Play class) kuma Bilal ya bata sunar shi, yanzu haka suna Abuja kuma babu
wanda yasan ba ‘yarsa bane. Kawai ana ganin tayi gwarne ne.
Yau ta samu tana hutu saboda kullum suna jikinta ko saurara ma Haske basa yi. Sallama
taji na mijinta, anan ta daga kai ta kalle shi. Ya dawo daga kai yaran school kenan shima
yanaso ya kebe da matarsa.
“Rabin raina kina zaune abinki keda Haske” yace yana mata murmushi mai laushi
“Ai yafi wallahi nima na samu na huta”
“Wani hutu yanzu kuma bayan gani, yanzu za’a soma ji dani” yace yana dariya. Hannu ya
mika mata domin taje kusa dashi. Babu musu ta mike ta karasa.
“Mrs B” yace a hankali yana sumbatar goshinta.
“Na’am Mr B” sai suka wuce dinning domin suyi kalaci.
Yasmin yanzu tana aiki a NDIC, caskan kudinta takeyi abinta babu kama hannun yaro. Ta
cire tunanin Haisam yanzu ta zama focused a career dinta. Tana zaune a daki da safe zata
fita. Wani bakon lamba taga yana kiranta. Da sallama ta dauka tana saurara. Muryan da
bazata taba mancewa bane daga dayan bangaren.
“Chiquita dina, nasan it took so long amma ina ganin lokaci yayi yanzu” murmushi tayi
tana hawayen farin ciki. Wannan kenan daga labarina mai suna HASKEN LANTARKI
Alhamdulillahi rabbil alamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *