HAUSA ARAB CHAPTER 1
A hankali tattausan sauti me dadi na ringtone din iphone ya dinga shiga kunnena……juyawa nayi daya gefen naci gaba da baccina me dadi peacefully saidai sam mai kiran yaki hakura domin tana katsewa wani kiran zai sake shigowa. Dakyar na bude idanuna da nannauyan bacci ya risinar na kai kwayar idanuna kan side drower inda wayar ke aje na saka
hannu na dauko ina danasanin rashin sa wayar a silent. Saidai ganin sunan da ke kan screen din wayar ya sanyani swiping wayar da sauri cikin doki. Da muryar da bacci ya harde nace “Mamina good morning” can bangaren Mamin kuwa cewa tayi “wanne irin bacci kike zara? Na kira ya kai sau goma fa?” Tausasa murya nayi nace “Mami i slept very late wallahi shiyasa baccin yayi nauyi.i’m sorry” cikin sanyi tace “issokay cewa zanyi ki tambayi Dada ki shigo da yamma inason ganinki” murmushi nayi me sauti na amsa da “ok Mami zan gaya mata sai nazo” da haka mukai sallama na aje wayar. Agogon wayar na duba 11:00am. nayi maza na mike na shige toilet ina mamakin yanda rana tayi ina ta bacci. Brush kawai nayi da alwala na futo sannan na zura katon hijab fari sol na shimfida sallaya na gabatar da sallar walha raka’a hudu wadda bana iya fashinta komai tsanani. Ina idarwa na ninke kayan sallar na futo parlour. Dada na samu zaune akan kujera Daddy na kasan kujerar yana danna mata kafafunta da suka kumbura a hankali cikin tausasawa.
Cikin nustuwa na iso na zauna na soma gayar da Dada ta amsa cike da kulawa sannan na gayar da Daddy. “Sai yanzu kika tashi Zara?” Inji Daddy. Dada ce tace ai yau babu makaranta bacci ake a more…sai an biya bashin na kwanaki biyar din da ba’ai ba.” Murmushi yayi yace “Dada weekend din kenan” har na mike zan tafi Daddy yace “ahmm Zara ran Monday ki shirya da wuri babu zuwa makaranta zakuje da Omar kiyi renewing passport dinki don inaga a satin nan zamu tafi Jedda da Dada kafar nan ta matsa mata” duk da gabana yayi mugun faduwa da jin zancen tafiyar ban kasa risinawa nace “toh” ba. Sannan na wuce kitchen na samu Baba Rabi tana goge goge. Da murmushi tace “zahra’u an taso?” Nima murmushin na maida mata sannan na gayar da ita. Na dora da cewa “me aka yi mana ina bude warmers din dake kan table. “Lalala..wow” Baba Rabi moimoi?” Na fada ina murmushi domin ina matukar son naci moi moi da kunu da safe fiye da komai. “Ai naga yau ba makaranta nasan ba da wuri zaki tashi ba har na kammala kulelen. Cikin jin dadi nace “nagode sosai Baba rabi… kawo plate da yaji yanzu na tashe shi aiki” dariya take sosai taje ta dauko mun plate da cup tayi serving dina delish dinta na alalen da aka nannade cikin ganye yaji kwai da kifi da kuma kunun tsamiya mai dan karen dadi. Inaci ina santi tana yimun dariya har na kammala na mike na koma dakina. A gado na fada ina tunanin wannan tafiya da ake jajibowa kullum ba’a la’akari da karatuna…tun ina sha’awar tafiyar har na daina. Na zama jelar Dada duk inda zata je sai an hada dani. Ya ilahil arshi ya zanyi da karatuna da ya dau zafi wanda muke dab da kammalawa. Mtsweeew. .gaba daya raina ya gama baci wataran saura kiris ayimun repeating a school sai da Daddy yaje yayi bayani da kansa.
Karfe biyar na kammala shirina cikin sassaukar shiga na dau key nayiwa Dada sallama na futo harabar gidan wajen adana motoci na isa na bude motata na shiga ina kiran sunan Allah. Bayan na kunna motar na saka CD nan da nan sautin muryar Maher zain ta soma tashi cikin wakar “Madeena Madeena” sannan na ja motar na futa daga cikin gidan ina bin wakar a hankali nutsuwa tana saukarmun da nishadi me yawa a dalilin son da nakewa wannan mawaki da wakokinsa…. har na isa Ministers hill.
A bedroom na samu Mami ta baza kaya a tsakar dakin kamar hauka. Atamfofi,laces,voils da sauransu.
A comfy bed din Mami na kwanta ina “wash Allah i missed this bed” kallona kawai ta tsaya tana yi har ma ta bani dariya. Cewa nayi “Mami me nayi ne?” Girgiza kai tai tace “babu Allah ya shirya” na kyalkyale da dariya. Sannan na soma gaisheta. Sake bararrajewa nayi a gadon ina sinsinar sassanyan turaren da ya like a jikin bedsheet din.
Cewa tayi “kinga ba dadin gado na kiraki kiji ba kayan sallarki zaki zaba zan kai shago kafin aiki yayi mana yawa. Tsalle na buga na tashi ina cewa “wow…that’s my mami” “ah ah karki balla mun gado…meye hakane Zara?kamar wata yarinya zakimun tsalle a gado? Sauka ki duba kiyi maza kizo ki tafi banason kina driving da dare. Tare muka shiga duddubawa tana tayani na zaba duk wanda nakeso muka zuba a leda.
Sannan na dubeta cikin soyayya mara misaltuwa nace “Mami nagode Allah ya kara arziki” murmushi kawai tayi tace amin. Na sake cewa “Mami kinsan wai nextweek zamu tafi Jeddah da Dada? Wai meyasa akemun haka? Karatuna ya dau zafi gashi muna shirye shiryen grad duk ba’a dubawa kawai sai a daukeni asani a gaba mu tafi.” Na karasa maganar cikin bacin rai.
Dafani Mami tayi cike da kulawa tace “haba Zara Dada ce fa? You are the only female grandchild acikin jikokinta ku 25 bayan Nuratu….she worths kowanne kulawa da taimako Zara kiyi hakuri zama da manya sai an yi hakuri an daure kinji? Kafar tata ce?” A sanyaye na amsa “eh duk sun kumbura ko waje bata iya takawa ta futa.” Cikin tausayawa Mami tace “ayyah wannan kafa ta takura mata Allah ya sauwake” nace “amin.” Sannan ta sake cewa “yauwa Zara plaease karki bata rai har ta gane bakyason tafiyar kinji? Kici gaba da yi mata biyayya. Dada tana da matukar girma a wajena ta nunamun so da kauna irin wanda bazan manta ba. Zanje school dinku nayi reporting tun kafin tafiyar za’asan yanda za’ai” cikin jindadi na rungumeta ina cewa “yauwa Mamina….zanyi duk yanda kikace..i love you” kankameni tayi a jikinta tace “i love my baby too” duk yanda naso muyi hira sosai Mami ki tayi ta koroni gida wai batason magrib tayimun a waje batason tukin dare. Haka na dawo cike da kewar Mamin tawa.1
STORY CONTINUES BELOW

Ina shiga gida na ga motar gidansu Aisha anyi parking. Cikin murna nayi sauri na futo daga motar na kulle. A parlour na sameta tare da Dada an cika gabanta da kayan kwalam. Na taho da gudu na rungumeta ina “oyoyo bestie you didint tell me you were coming” Dada ce ta katseni da cewa “yau nakejin hauka toh balla ta zakiyi? Kin wani bata mata suna wai besti kamar wata kwano.” Muka kyalkyale da dariya ni da Aisha sannan muka soma hira daga bisani muka shige dakina. Anan nake sanar da ita zancen tafiyarmu. Itama dai lallashina ta dinga yi tace “babu komai besti inshallah Allah we will make it kar kiji komai.” Sai bayan munci dinner ta tafi gida. Ina rakata Ya Sadik na shigowa muka shigo dashi gidan tare. Har 10 muna tare da shi muna ta hira akan bikinsu da ke karatowa shi da Ya Omar. Sannan yai mana sallama ya tafi. Dada na gyarawa gado na shafa mata man zafi a kafarta sannan na kashe mata fitila na dawo dakina na fada toilet nayi wanka na futo na zura pyjamas dina na “hanna Montana” na kwanta ina karanto addu’o” kafin barawon ya silalo ya kwasheni.
Cikin kwanaki biyar shirin tafiya ya kammala sai jirgin Daddy da ake jira yana America service don haka sai washegarin ranar da aka tsara ya dawo. 8 Daddy yace zamu tashi. Banason tafiyar safe saboda bana iya bacci daddare sai can karshen daren zan fara baccin ina farawa kuma za’ai sallah shikenan.
Bayan na cika manyan jakunkunana guda biyu na janyo su na kawo parlour. Dadin private jet kenan. Ka kwashi duk tarkacen da kake so kayi tafiyarka dasu babu zancen kg zai yawa.
Toilet na fada na hada ruwa cikin jacuzzi na zauna ina jin dumin ruwan kamar kar na futo.ganin lokaci na taciya nayi wankan na dauro towel na futo ina qamshin shower gel din “Moringa” na “Body shop”na goge jikina na sake shafe shi da “body shop Shea bodybutter” product din da skin dina take karba kenan tayi wani smooth da fresh kamar an baro ta daga kwai. Sau da yawa mutane na tambayata abinda nake amfani dashi na mallaki wannan rantsatstsiyar kalar fata. Abinda zance shine daga Allah ne. Naturally haka fatata take me bala’in taushi da sulbi kuma wata irin kala ba fara ba ba baka ba kamar ta yan ethopia ko black americans. Yanda kikasan an cakuda furanto da madara ita kadai take kyalli. Shiyasa sau dayawa ban cika kwalliya a fuska ba don wani sinadari da kalar fuskar ke dauke dashi. Har naje na gano duka kalolin foundation da powder da yayi dai dai skin tone dina wanda ba zai sauya mun kalata ba. Ban taba amfani da wani mai ko soap don karawa fatata fari ba sai dai taushi da inganci. Duka kayan gyaran fata ta na brand din “Body shop” ne. Shi kadai fatar take karba ta yarda dasu. Hakana body sprays da turarukana yawanci na body shop dinne masu sanyi da kwantar da hankali.Kayan kwalliya kuwa bani da kamar “MAC” musamman shade din lipstick dinsu da suke mun kyau kwarai.
Salon gayuna mai sanyi ne da kwantar da hankalina ba mai hayaniya ba. Nakanyi kokari duk inda zan shiga nayi shigar data dace da wajen. Thats me! Lol!
A gaggauce na taje dogon gashina na hade shi cikin dan qaramin dounut na rufe da gashin.yayi kamar gammo don yawansa da tsayi. Wardrobe na koma na ciro pyjamasa bakake na saka na dora abaya akai! (Who else wears pyjamas under abaya? Weird? ) bansa ko powder ba sai kohl da chapet kawai. Na hada tarkacena cikin katuwar jakar Aldo sannan na zura flat shoe . ‘i want everything natural idan zanyi tafiya.’1
Kafin 7 mun kammala duk wani shiri Ya Omar ya daukemu zuwa Airport cikin mintina talatin jirginmu ya daga. Na sauke ajiyar zuciya sannan na zame jikina na kwanta na rufe fuskata da gyalen jikina na soma bacci…(is there anything more relaxing than baccin jirgi?) Mafarkai masu dadi na dinga yi sai farkawa nayi naganni a “king Abdul’azeez International Airport jeddah” Daddy ne ya tasheni yana cewa “toh sarkin baccin jirgi mun iso!!what? How? I cant believe nayi baccin awanni hudu da kusan rabi.
Muna futowa daga airport “Auwal ya iso yana mana sannu da zuwa.” Shi yazo da mota kamar koyaushe muka shiga zuwa gidan Daddy na garin Jeddah.
A gajiye tibis muka shiga gidan me hawa biyu. Nida da Dada muna hawa na farko Daddy na hawa na biyu.
Nan mukai wanka tare da biyan bashin sallolin da ake binmu.
Wata sabuwa! HAJIYA wato tikarin da ke zaune a gidan domin girkin abinci ta tafi madina. Don haka Auwal ne yaje yayi mana take away. Muka ci muka kwanta.
Washe gari muka je asibiti da Dada daman tuni anyi appointment da likita. Gwaji suka bayar kala kala da xray da sauran tarkacen leken asirin likitici sai komai ya kammala za’a koma wajen likita. Don haka Dada tace washegari kawai mu tafi Makkah muyi Umrah mu sauke nauyi.
A daren sai ga Ya Nuratu da amal yarinyarta yar shekara shida “Ya ilahi i love this creatures” Ya Nuratu cousin dina ce the only female cousin i have on this planet. Tana aure da Doctor Mansur kwararren orthopaedic cunsultant a asibitin saudi germany da ke Jeddah.
A guje na rungume ta bayan na bude kofar ina “oyoyo Ya Nuratu i miss you i miss my Amal” kankame da juna muka isa falon sama itama Dada tuni ta hau murnar ganin jikarta ta. Nan da nan gidan yayi dadi. Duk lokacin da muka zo da Adda Ya Nuratu tattarowa take ta tare a gidanmu sai zamu tafi take komawa gidanta.
Washe gari Daddy yace mu shirya a tafi Makkah umrah buya nayi a daki na barwa Ya Nuratu sakon bazan iya gabatar da Umrar a wannan lokaci ba ta sanar da Dada. Bansan wa yayi wa Daddy bayani a cikinsu ba kawai dai an tafi an banni daga ni sai Amal a gidan domin suna kammala Umrar zasu juyo.
Ni da Amal mukai ta buurinmu har yamma sannan na sauko don yin abinci kafin su dawo. Ina cikin aiki na Amal ta runtumo a guje tana cewa “somebody is by the door” daman nima ina tajin karar kararrawar don haka na tsame hannuna daga cikin kwabin danwaken fulawar da Ya Nuratu tayi mun magiya nayi mata.
Yar gown ce da ta dan wuce guiwa a jikina mai zanen strokes “pink and yellow” samfurin “Dolce and Gabbana” na daure kaina da fashmina pink da farin rigar girkin da tayimun yawa. Cikin sauri na bude kofar domin an soma bugu kamar za’a balle kofar.ina budewa nayi turus tare da yin baya a tsorace.
Halittar da na gani tsaye a bakin kofar kai tsaye bazan ita tantance nationality dinsa ba amma idan akace nayi kiyasi toh zan iya cewa ya bullo ne daga Sudan ko kuma halfcast of Arab and Africa. Wani dogon balarabe ne mai duhun fata wato ba fari tas ba amma ya zarce layin bakake wata irin kala me bayyana hutu da kwanciyar hankali da cikakkiyar samun kulawa ta kowanne bangare. Dogon gaske ne kamar reshen bishiya mai wata irin structure ta mazan da suka amsa sunansu. Kansa kamar an kifa kwando da wata irin yala yalan suma baka wul ta kanannade sai sheki take. Hakana wannan gashin ya biyo kyakykyawar doguwar fuskarsa ta kewaye ta dira a habarsa kamar an zana da biro. Hancinsa kamar kasa hannu ka dauke saboda tsini..idanunsa kuwa dara dara ne farare sol masu lumshe kansu ba tare da umarni ba. Yana sanye cikin coffee jeans da farar shirt ya ratayo wuyansa da scalf din “burberry” yayinda yake rataye da jakar laptop dinsa a kafadarsa. Nidai sandarewa nayi ina kallon wannan beautiful creature of Allah!! Kamar wata doluwa.
“Hey give me way and stop staring at me like an alien” Ya Ilahi!! Da wani irin accent yayi amfani wanda zai sake jefaka tunanin nationality dinsa domin harshen a harde yake da yarika dayawa wanda suka kasa barin yare guda daya yayi aikinsa. Is he an Arab? French? Sudanese? Indian? Black american? Oho!
A guje Amal ta taho tana ihu kamar zata fadi “welcome Uncle” ya tare ta da wani wide smile duka kumatunsa suka koma ciki(dimple)!! fatabarakallahu ahsanul khaliqeena.! Nidai tunda nake ban taba ganin halitta me kyau kwarjini da daukar hankali irin wannan bawan Allah ba. Mutum kamar aljani? Kaurin girkina ne ya sanyani dawowa daga hayyacina nayi kitchen din a guje. Na bar Auwal na shigo da akwatina designers bakake wul.a raina nace “wannan wanene?? Kuma ya akai Amal ta sanshi? Ko dai irin yayan abokan Daddy ne? Da alama dai wani babban mutum ne don naga yanda Auwal yake girmama shi kamar zai masa sujjada.
Ina girkin ina tunane tunane har na kammala tuka lafiyayyen tuwon shinkafa na nade shi cikin leda nasa a warmers. Sannan na hada miyar busashshiyar kubewa na burge mata kaji suka ragargaje aciki. Gefe guda kuma soup din naman rago ne da dankali. Ga kunun gyada sai kamshi yake. Idan muna wannan gidan yanda kasan a Nigeria domin komai muna taho dashi na amfani irin na gida hakana Hajiya mai abinci tana aje komai. girki ake kaman ana Nigeria a kullum saidai idan ka gaji da ci kaje ka siyo na larabawa a wuraren abincinsu. Ko kuma na kamfani irinsu mc Donalds da KFC.
Bayan na kammala na gyara kitchen din tsaf sannan nan na kai kayan abincin sama na shimfida ledar cin abinci na jera komai yanda ya kamata kafin na shiga toilet na watsa ruwa saboda kamshin abincin da ya likemun a jiki. Wata purple silk gown na zura na dora hijab na futo jin shigowarsu Dada.+
Bayan sunyi sallah ne na daga wayar falon na kira dakin Daddy nace masa angama. Sannan na zauna na fara serving din su Dada. Minti biyar Daddy ya murda kofa ya shigo cikin sallama duka muka amsa a ladabce tare da mishi sannu. Yanayin saukin kai da sanin darajar dan’adam na Daddy yana matukar bani mamaki da sha’awa. Duk iya dukiyar da ya tara bai sanya shi rage biyayya ga mahaifiyarsa ba. Kamar zai mata sujjada idan yana gabanta. Ya baro duka ayyukansa da harkokinsa ya dauko ta a jirginsa musamman don a duba lafiyarta. Duk sanda za’a kai Dada asibiti toh da Daddy ne saidai idan munje munga likita ya tafi ya barmu ko kuma mu mu soma tafiya ya same mu acan. Hakanan garemu wani irin mutum ne mai kulawa da karamci da kyautatawa da wuya kaji kalmar da zata bata maka rai daga bakinsa sai dai nasiha da rarrashi kai ba zakace Dada ce ta haife shi ba.
Yana zama aka sake murda kofar a hankali. Santalelen balaraben dazu ne ya shigo sanye cikin jallabiyya fara sol wadda ta bayyana broad figure dinshi. Sumar nan kamar an kufa masa ita ta dan cukurkude alamar ba’a bata kulawar da aka saba bata ba .hannunsa rike da dogon farin tasbih. Sai ya koma kamar balaraben madina.
Yana sallama Dada ta wancakalar da plate din abincinta ta mike tsaye dakyar kamar zata fadi har Daddy yana tayi a hankali. Ai bata ma bi ta kansa ba ta soma rangadawa matashin kirari cikin tsananin murna da dokin ganinshi. Da sauri ya isa gareta ya rungumeta yana cewa “i miss you soo much granny” dakyar ta bambare daga jikinsa tana hawayen murya sannan ya zaunar da ita ya wuce wajen Daddy shima ya rungume shi ya dawo gaban kujerar Dada ya zauna ya soma gayar dasu cikin ladabi. Sannan ya dubi Ya Nuratu yace “sister ya kike?” Da wani wawakeken smile dinta ta sauya maganar da gaisuwa cike da ladabi da so da kauna. Sai na koma bare a cikinsu.
Kaina ne ya daure tamau tun lokacin da mutumin ya shigo Dada ta barar da abincin da take ta zuzuta dadinsa ta mike kan kafafun da ake lallabawa dakyar don murnar ganinsa. Sannan Daddy expression din da ke kan fuskarsa ya nuna zallar so da kauna mara gauraye akan wannan bawan Allah. Toh ita kuma Nuratu ina tasan shi har yayi sabo da diyarta Amal haka? Duka wadannan tambayoyin ne suka ta yawo a kaina ban ankara ba naji Dada tana cewa “ke Zara bakiga Yayanku ba ki gaishe shi?” (A gidan wa ya zama Yayana kuma) a fili kam kasa nayi da kai na gayar da shi ya amsa a gwasale kamar bayaso. Daddy ne yace “Zaran marigayi ce fah” da wani irin mamaki ya zubo mun duka idanunsa da dafin da ke dake cikinsu wanda suka sanya ni kasa da tawa kwayar idon. Cikin hardadden yaren shi yace “what? Daddy Zaran Mami? She’s all grown up!..Daddy bangane ta ba” kafin Daddyn yace wani abu Dada ta soma zazzaga masifa kamar ba ita ce me runguma da kirarin dazu ba.
“To dama ina zaka ganeta? Zaka soma yi mana turancin banza da wofi?.Ina zaka santa ka tsame kanka daga dangi? Ina bakin halinka zai bari ka gane wani bayan zumuncin ba damunka yayi ba? Ka mayar da kanka baturen karfi da yaji ka zubar da yan’uwa ka rungumi masu jajayen kunnuwa wadanda basu san Allah da Annabi ba sai hauka da sakarci…………….ta inda ta shiga ba tanan take futa ba.
A hankali na sulale na bar falon ina tausayin wannan bawan Allah domin babu wanda ya kaini sanin zafin fadan Dada. Akan Dada tayi ma fada gara a gayyato karti a basu dorina suyima dan iskan duka domin idan zata yima fada ko zata zageka sai ta je ta nemo kakan kakan kakanka ta lalubo aibunsa ta hadashi da kai ta zage ku tass.
STORY CONTINUES BELOW

Na kai hour daya da shigowa sannan Ya Nuratu ta shigo sabe da Amal a kafadarta ta kwantar da ita akan gadonsu. (2beds ne a dakin) sannan ta dubeni cikin damuwa tace “har yanzu Zara Dada bata daina wannan fadan nata ba?” Murmushi nayi nace “Toh Ya Nuratu me zai sauya? Me hali ai baya fasa halinsa balle yanzu ga girma ya sake kamata” zama tayi cikin sanyin jiki tace “gaskiya fadan da tayiwa Ya Mahmud yayi yawa. Daga zuwansa?” Kallonta nayi a nutse nace “wai wanene shi?” Cikin mamaki ta kalleni tace “dont tell me baki san shi ba?” Cikin rashin damuwa nace “so? Nima ai bai sanni ba” kallona tayi cikin nutsuwa tace “Ya Mahmud first born din Daddy wanda yake London?” Kafin ta kammala bayanin tuni na hangame baki cikin madaukakin mamaki da firgici? Toh waye a family baisan Mahmud ba? Mutumin da bashi da aiki sai sa iyayensa damuwa da bakinciki? Wanda ya gujewa kowa ya sallama mahaifarsa da duk danginsa ya zabi boko da aiki. Mtsw! Ashe kyan dan maciji ne.” Cewa tayi “me kike tunani? Kin hangame baki kina kallona” rufe bakin nawa nayi a hankali kawai na juya na kwanta domin idan har zan fadi wata kalma akansa toh ba me alkhairi bace sannan a gaban Ya Nuratu nake duk duniya banga wanda yake kare shi kamarta ba! Toh nace me? Ta bubbugemun baki! Shirun yafi mun alkhairi. Itama a sanyaye ta kammala shirin baccin nata ta kwanta a raina nace “an tabo dan gwal kenan toh me ma ya kawo shi garin bayan yasan muna nan? Mutumin da zaije har garin Abuja yayi harkokinsa ya juya bai ko kalli kofar gidansu ba. Mtsw! Allah ya shirya wannan bawa. Da tunanin labaran da nasha ji anayi akansa bacci ya daukeni.
Washe gari da wuri na tashi na hada break fast. Na kammala ina cikin gyara kitchen din Ya Nuratu ta sauko. Cikin mamaki tace “ba dai Zara har kin tashi kinyi wadannan abubuwan ba? Amma kinyi kokari. Cikin murmushi nace “kai Ya Nuratu kamar wanda nayi wani abun kirki? Break fast din? Bude warmers din ta shiga yi tana murmushi sannan tace “yan matan Dada an kware a girki gaskiya” nayi dariya kawai sannan muka soma hawa da kayan muka hada wajen breakfast din a parlour tare. Ni na kira wayar dakin Daddy na sanar dashi sannan na shiga na gayawa Dada muka futo tare.
Mintina goma Daddy ya shigo ko zama baiyi ba sai ga Matashin balaraben cikin shigar jallabiyya me kauri ruwan toka. Gaban Dada ya wuce ya soma diban gaisuwa cikin far’a take amsa mishi kamar ba itace ta jiyan da ta dinga sauke mai kwandon bala’i ba. Sai hira sukeyi cikin so da kauna.cikin ladabi muka gayar da Daddy sannan dan gatan nasu. Kafin Daddy yace “bismillah” kowa ya soma cin abincin. Na kai kofin shayin bakina kenan naji Daddy yana cewa “Zara ki shirya anjima Yayanku zaije Umra sai ku tafi tare” a tare muka dago muka kalli Daddyn dagani har Ya Mahmud alamun dukanmu bamuji dadin hadin tafiyar ba amma ban bari hakan yayi tasiri akan fuskata ba na hadiye komai nace ” Toh Daddy”
Bayan mun kammala breakfast ne na koma daki na kwanta na soma bacci domin daren jiya a tsitstsinke nayi baccin. Nan da nan kuwa bacci me nauyi ya dauke ni. Saidai banfi awa daya da baccin ba naji Ya Nuratu tana tashina. Cikin bacin rai idona a rufe nace “please Ya Nuratu let me sleep i’m so tired” daga murya tayi tace ” ke ki tashi Ya Mahmud tuni ya shirya yana falo yana jiranki.” Ai bata karasa ma maganar ba inajin tace Ya Mahmud na duro daga gadon idona rufe na laluba na fada toilet. Wanka nayi sannan na dora wankan niyyar umrah na futo cikin sauri ina goge jikina da towel.
Nayi maza na bude akwatina na ciro haramina. Nayi umrah ya kai goma sha biyu amma ban taba daina sa harami ba duk da ina da damar yin hakan a dalilin sha’awar da nake masa. Doguwar rigar farin yadi ne da katon hijab. Na zura slippers baki a kafata na ciro yar jakata na watsa yan komatsaina aciki nayi sallama da Ya Nuratu na futo falon.
Dashi na fara tozali! YA Ilahi!!! ya jameelal munzar!!!! Fatabarakallahu ahsanul khaliqeena! Na fada a zuciya ta domin ban taba ganin wanda harami yayiwa kyau kamarsa ba. Bashi da maraba da laraban kasar sai dan dubun fata da ya fisu.
Yana gaba Dada a zaune. Sai hararata yake faman yi kamar ni nace zan bishi. Da sauri ya mike yana yiwa Dada sallama ya futa. Nima nayi sallamar nabi bayanshi. Ashe har an samo mota tana waje tana jiranmu.
Gidan gaba ya bude ya shiga nikuma na shiga gidan baya. Acn motar da tattausan kidan wakar larabawan da driver ya saka suka sanya komawa bacci. Sai farkawa nayi naji ana tashina. “Hey…you sleeping huh?..oya let lets going” a hankali na yunkura na futo ina kwaikwayon irin maganarsa a raina. Wata kwalleliyar rana ce ta bugi idona da fuskata. Ga wani hucin zafi kamar na tsaya a bayan engine. Yana gaba ina biye dashi muka shiga cikin harabar masallacin. Wata harara ya watso mun yace “haka zakiyi umrar babu alwala?” Cilla idona nayi can wajen famfunan dake wajen daya naje nayo alwalar na dawo sannan muka wuce. Munzo daidai kofar shiga ya sake juyowa yace mun “dawaf zamu fara” nace “toh”
Ranar da ake ba mai sauki bace ga wata irin cikowa a dalilin ana gab da soma azumi mutane sun fara cika garin. A wahalce nayi dawafin nan muka futo sannan muka wuce safa da marwa. Wani zubin sai nima nayi sassarfa nake taddashi domun saurinsa. Inaso na tsaya nasha zamzam amma sai naga kamar zai bacemun kafin na gama sha haka na hakura da kishirwar har muka kammala. Lokacin da muka futo tuni yamma tayi. Ranar ta soma raguwa. Juyowa yayi ya watsa mun harara yace “hey you sit here ki jirani ki daina bina kamar wata jela” duk yanda naji rashin dadin maganar ban kasa cewa “toh” ba. daman a gajiye nake don haka na nemi waje na zauna. Shikuma ya tafi. Mintina ashirin da biyu ya dawo da kwalayen KFC da kofunan coca-cola akan wani kwalin ya aje a gabana shima ya zauna.
Kwali daya ya turomun shima ya ja nasa ya soma ci. Muna cikin cin maguna suka soma shawagi a wajen saboda kamshin naman da suka jiyo. Shi kuma ya shiga jefa musu tsokar kazar. A rayuwa ta na tsani mage ina mugun tsoronta don haka na dinga ja da baya. A guje wata ta taho ta gefena na mike da sauri na koma wani wajen. Ai yana sake wulla mata wata ta kuma yo tsalle ta biyo ta gefena. Wata kara na saki na mike da sauri. Cikin tsautsayi hijabina ya tadeni na fadi ji kike “tim” kofin cock din gabadaya ya kife a jikin Ya mahmud!!
Cikin tsananin bacin rai ya kalli kayansa da suka yi kaca kaca da cock. Sannan ya mike tsaye yana huci. Wani irin mugum kallo ya jefamun wanda ya sanyani soma hawaye domin irin wannan kallon da dabba ya dace ba da mutum ba. “I will break you into pieces if you dare let those tears out! Stupid girl!!
Yanda yayi maganar cikin temper ya sanyani shanye kukan da sauri cikin tsoro domin zai iya kakkaryanin dagaske. Wayarsa ya ciro daga cikin jakarsa ya soma danna wasu lambobi ya kara a kunne! “Hey.. Where are you?” Ya dan jima sannan yace “ok.ina nan zuwa” daga nan bai kalle ni yai fatali da abincin ya wuce yayi tafiyarsa. Bat!! Ya bacewa ganina.
Awana daya da rabi ina zaune ina jiransa amma babu alamunsa har aka kira sallar isha’i. Nayo alwala nabi jam’in sallar. Lokacin ne hankalina ya tashi na soma kuka don azabar tsoro! Ta ina zan tafi gida? Wa na sani anan? Ina zanje? Ganin kukan ba zai mun ba na goge hawayen na mike na soma safa da marwa tsakanin hotels din da ke jere opposite din masallacin. Nafi mintin arba’in ina wannan zarya ina kuka.
Ji nayi an fizgo ni da karfi na juya sai nayi ido hudu da shi. Ya sauya zuwa lafiyayyar blue jallabiyya sai kamshin turaren shi yake. Wasu matsiyatan rankwashi ya zubamun wanda suka sani kusan sakin fitsari a tsaye. “You’re very stupid! Useless girl” abinda ya fada kenan tare da janyo hannuna da karfi yatsuna suka lankwashe suka ce wani “qas!qas!!qas!! Wata irin azaba ta shigeni na fashe da kuka. Na janye hannun da sauri. A zafafe ya kalleni cikin tsananin fushi ya sake damkar yatsun da ya jiwa ciwo muka soma tafiya ina kuka har ya samu mota ya cillani gidan baya. Shikuma ya bude gaba ya shiga. Wani irin kuka na saki har balaraben ya juyo ya kalleni. Cikin tsawa Ya Mahmud yace
” if you dont close this toilet i will disorganize you face” dif! Na shanye kukan naci gaba da yin na zuci hannuna kuwa wata irin azaba yake yi kamar zai cire. “Qilama ya karyani” na fada a raina. A wahalce muka iso gida. Na balle murfin motar na futa. Allah yasa kofar gidan ba’a hadeta ta ta kulle ba na wuce a guje na shige cikin gidan. Babu kowa a parlour don haka na wuce dakinmu na soma zarya ina rike da hannun ina kuka don tsananin radadin da nakeji.
A haka ya Nuratu ta shigo ta sameni.
Da sauri ta
Kamani tana cewa “ah Zara yaushe kuka dawo? Me ya sameki? Menene? Hannuna kawai na dago na nuna mata wanda ya kumbura sosai yayi wani lage lage yana lilo sai kyalli yake! Zaro ido tayi tace “how comes? Da me kikaji ciwo haka?” Bansan yanda akai na tsinci kaina da cewa faduwa nayi ba. “And where is Ya Mahmud?” Ta fada cikin fushi! A galabaice nace “please Ya Nuratu stop this questions and help me”
Tashi tayi ta futa suka dawo tare da Dada. Ta ballo pain killer guda biyu ta bani da ruwa nasha. Sai sannu sukemun. Dada ce ta sanya Ya Nuratu ta kira Auwal muka tafi asibiti. Hoto aka soma yimun sannan aka gyara karyayyun yatsun aka nannade mun su da tsumman bature akaimun allurai suka bani magunguna.
Bayan mun dawo muka samu Daddy a kofar gidan da wani mutum.
Da mamaki yace “ke meye wannan? Ma ya sameki Zara?” Cewa nayi ‘faduwa nayi’ yace mu shiga ciki yana zuwa.
Lokacin da ya shigo ina gaban Dada tana kallon yanda suka like hannun yazo ya zauna yana cewa “garin yaya haka ta faru? Ina Mahmud din ya barki da wannan hannun kuka taho?” Cewa nayi “Daddy bamusan zai kumbura ba sai bayan na dawo gida nagane naji ciwo ne”
Da dabara nayi wanka Ya Nuratu ta hadamun tea nasha ta bani magani sannan na kwanta. Ban dade da yin baccin ba hannun ya matsa mun da ciwo na mike ina sintiri. Kukana ya tada Ya Nuraru ta mike da sauri tana cewa “Zara hannun ne?” Sannu! Haka muka kwana ina shan azaba sai wajen asuba na samu nayi bacci. Bayan kwanaki buyi na soma samun sauki. Lokacin azzalumin jikan Dada ya tafi Madeena don haka naji dadi sosai. Domin yanzu na tsane shi tsana me tsanani har bana kaunar ganinshi.
Dada ta koma asibiti an karbi result din hoton guiwar sunce aiki zasuyi mata a qoqon guiwar bayan kwanaki uku. Ranar da za’ayi aikin duka a sibitin muka wuni sai da muka ga ta farfado munyi magana da ita sannan muka taho gida don basa bukatar me jinya.
Sati biyu bayan wannan lokacin aka soma azumin Ramadan. Tuni an kwance mun hannun saidai ba komai nake iya yi dashi ba sunce sai a hankali sun koyamun yanda zan dinga exercising dinshi lokaci lokaci.
Yau mun kai azumi na goma sha biyar. Babu kowa a gidan daga ni sai Amal sai Hajiya mai abinci. Wannan shekarar kam visa tayi matukar wahala don haka babu kowa a gidan. Dada tana da appointment da likitanta. DR.Mansur mijin Ya Nuratu ne yazo da kansa suka tafi asibitin tare. Daddy ya tafi Riyadh wajen babban amininsa ambassador Ahmad kibiya. Auwal kuma Daddy ya aike shi Makkah ya kamawa abokinsa Dr.Ilyas masauki yana tahowa gobe. Da yake Daddyn daga baya tafiya yayi sai shekaranjiya ya dawo.
Shara nayi mai kyau na goge ko’ina sannan na kunna burner na zuba sandal woods bayan na karo karfin Ac. ko’ina ya dau kamshi mai dadi. Daki na koma na shiga toilet nayi wanka na shirya cikin three quarter baki da jar tea sanin babu wanda zai shigo gidan.
Kitchen na sauko na soma taya Hajiya aikin abincin muna yi muna hira tana bani labarin yan’uwanta da ke jihar katsina a kano. Yau shekararta goma sha hudu kenan bata taba zuwa gida ba sai dai tayi musu aike. Duk mamakinta ya cikani. Na dube ta nace “danAllah Hajiya ki taimaki yaranki ki koma gida kada da su manta ki” dariya tayi kawai tace “Zara baki da dama. Ya za’ai su manta ni? Ai muna waya koda yaushe kuma idan na samu ina turawa wani kudi yazo da Hajj sai na gansu.” Kai na girgiza ina tunanin wannan karfin hali nata. Salad din da na kammala hadawa nasa a fridge sannan nasa parker na kwashe sharar da na tattara na futo corridor domin na zuba a dustbin.
Baya nayi da sauri!!..Kadan ya rage na fadi saboda tsoratar da nayi a sakamakon ganin mutum a tsaye.
Sai da na sake kallonsa nagane Ya Mahmud ne cikin shigar da yafi kauna tun saukarshi garin. Wato jallabiyya. Wannan blue black ce mai shaking sai kyalli take. Hannunsa rike da kwaton kwalin inibi.
Habawa! Kifar da sharar hannuna nayi na bi ta gefensa na haye sama a guje ina haki domin zuwa yanzu tsoronsa nake ji bayan tsanar da nayi masa. I hate him with passion!! Bashi da kirki ko kadan kuma bashi da tausayi. Haka kawai ya kama ya balla mun yatsuna saboda an hadashi tafiya dani ba’ason ransa ba. He is soo selfish and arrogant! Kyawun da Allah ya bashi da dukiya su suke zugashi yake butulcewa rahamar ubangiji. Ya manta cewa wataran rami za’a haka a saka shi a ciki tsutsotsi su cinye. A duk lokacin da Daddy yake nunamun extra care sai na dinga tunanin inda shi Mahmud ya samo nashi halin? Meyasa bashi da kirki ko na cikin karamun cokali? A duniya ban taba samu mutumin da ya tsaneni lokaci daya ya gwadamun zalinci kamar Mahmud ba idan aka cire Mummy! Toh ko itace mamanshi? Ahh no!!! It cant be!! Mummy ba zata zama mahaifiyarsa ba. Ya fita kirki! Kuma ko babu komai ai shi yana son Dada kuma yana da addini da girmama nagaba da shi. Kuma baya shiga abinda babu ruwansa! Ba ita ce mamanshi ba! Duk tsanar da nayi masa bana so hadashi da wannan mata ba.
Bayan kwanaki biyu muka tafi Madeena lokacin da muka isa karfe biyar na yamma Kai tsaye “daruq taqwa” muka wuce domin tuni an mana booking. Wanka mukayi muka shirya domin mu samu shan ruwa a masallaci. Ni ke tura Dada akan wheel chair dinta Ya Nuratu na rike da hannun Amal.
Kwanakinmu takwas a madeenatul Munauwara. Gari mafi soyuwa acikin zuciyata. Babu abin da nafiso kamar naganni cikin Rawdah nakanyi ta zama ina kallon “green throne” ina salati ga Shugaban Annabawa saw. Ina addu’a sosai musamman ga mahaifiyata da mahaifina kafin nayiwa kaina.
Sallar farilla bata taba wucemu a masallaci ba hakana Asham da tuhajjud damu akeyi kullum . Wani lokacin kuma mukan shirya mu shiga manyan malls muyi siyayya. Hakana muka kammala zaman garin Madeena muka taho makkah cikin kewa da shaukin garin.
Ashirin da biyar ga wata muka taho Makkah ambasada ne yayi mana masauki a Intercontinental wato daral tauhid!! Masaukin da sai kasaitattun mutane kadai ke zama aciki. daren sab’a wa ishirun. Daren ashirin da bakwai ga watan Ramadan! Daren da musulmi daga kowacce nahiya suke tururuwa su taho saboda shi. Sheikh sudaith ya dinga kwararo addu’o’i muna amsawa da ameen. Masu kuka nayi masu hawaye nayi kowa ya mika kansa ga Ubangiji.
Anyi azumi an kammala daren asabar aka buga bindigar ganin wata. Nan da nan gari ya kacame da shirin sallah kowa yana murna. Washegari da safe akayi sallar idin sallah karama. Su Dada tun karfe uku suka tafi masallaci da YA Nuratu sai ni da Amal kadai a gidan.
Tun jiya Daddy ya sanar damu cewa zasu shigo da manyan aminansa su gayar da Dada. Don haka muka tafi da Ya Nuratu Bin dawud muka siyo royal coolers na alfarma da flasks din ruwan zafi da plates da sauran tarkacen abubuwan bukata. Daga jeddah Hajiya tayo tuwon sallah Auwal ya kawo shi da sassafe. Mu kuma mukayi su P.soup din naman rago aka soya kaji suyar gida aka hada kunun gyada da sauran dai kayan abincin gargajiya wadanda zasuyi marmarinsa.
Ina cikin aikin naji kararrawa. Na wanke hannuna naje na bude kofar su Dada ne suka dawo nayi musu sannu da zuwa. Cikin sauri Ya Nuratu ta wuce kitchen tana cewa “Zara muyi sauri mu kammala Daddy yace anjima kadan zasu shigo…….'” mamaki ne ya kamata ganin na kammala komai sai suyar kajin kawai “wow!!weldone my girl!” Ta fada tana murmushi. Sannan ta dubeni tace “oya je kiyi wanka kiyiwa Amal nikuma na kammala ragowar abinda ba’ayi ba. Nace “toh” na wuce daki.
Bayan na kammala shiryawa ne na tsaya a gaban full size mirror ina kallon kaina. A kowanne lokaci idan na kalli kaina a mudubi nakan godewa Ubangijin da Ya kawata mun surata. Zaka iya kirana fara idan babu fararen mutane a waje amma kuma acikinsu ni ba farar bace wata irin kala ce kamar an cakuda furanto da madara. “Chocolate colour” kenan inji bature. I am moderate in height da wata irin body
madara. Chocolate colour kenan inji bature. Kalar Irin ta asalin ethopians amma wannan ta sake samun armashi da samun ingantacciyar kulawa da sanin abinda ya dace da ita.
I am moderate in height da wani irin body structure mai tsada. Bani da jiki ko rama saidai shape mai tsari. A fuska kuwa me kyau ce domin ban taba jin wanda ya kushe fuskata ba musamman dara daran idanuna masu haske da dogon gashin da yai musu rumfa ga kananun lips dina masu taushi da sulbi. I am cute! Very cute!! Lolz!
Atamfa ce yar holland a jikina koriya shar mai zanen ganye an dan ratsa mata orange. Dinkin simple and elegant straight gown sai akabi duka pattern din da swarosvki stones sai walwali take. Nayi dauri mai sauki fuskata babu komai sai powder da chapet. yanayin kalar fatata bata bukatar sai nayi kwalliya zanyi kyau. Da siraran saitin diamond nayi amfani a kunne da wuya da hannayena. Sannan na yafa gyale Orange na “kashka” na feshe kwalliyar da turaren body shop mai suna “smokey rose” na zura flat shoe orange samfurin “chloe” na futo parlour.
“Kai! kai!! kai!!! cancadi! Wannan wacce irin atamfa ce?” Cewar Dada tana kallona. Murmushi nayi na karaso na zauna sannan nace “kai Dada irin taki ce fa wadda kika saka ranar da zamu taho daga Abuja” cikin mamaki tace “kai yar nan! Qarya ne Ba irin wannan bace wannan tafi kyau” dariya ta bani nace “Dada wallahi irinta ce sak kala ce kawai ba daya ba. taki ruwan kasa da ratsin pink” cewa tayi “amma wannan tafi kyau ai da na ganta ita zan dauka kamar ba iri daya da tawa ba” dariya na sake yi nace “ke dai Dada kawai kice kwalliyata tai miki kyau ba wata atamfa kyawun ai daga jikina ne” dariya tayi irin ta manya sannan tace “kayya! ina wani kyau anan mutum kamar a kife shi da kwando? A layin kyawawa ai babu gajere?! Nan da nan na cika nayi fam kamar zan fashe domin na tsani ace mun gajeriya koda bani da tsayi mai yawa amma ai babu yanda za’a kirani gajeriya. Ya Nuratu dai tana gefe tana yi mana dariya ni da Dada. Karar kararrawa ne ya tashe ni na tafi da sauri na bude kofar. Daddy ne a gaba sai manyan aminansa irinsu Ambasada Ahmad Kibiya da Dr Ilyas da engineer Nuhu salihi tsohon kakakin majalisa Alaji Ibrahim kurmi mai atamfa da Dr Haruna Madugu tsohon gwamnan Taraba. Dukansu aminai ne na gaske makaranta daya sukayi amma duk duniya Daddy bashi da kamar ambasada aminai ne na gani kasheni sannan Dr Mansur mijin Ya Nuratu kanin ambasada ne uwa daya uba daya. Shi da Daddy suka kulla auren a lokacin Ya Nuratu ta kammala secondary school Dada tayi tsallen albarka tace sam ba zata ci gaba ba sai dai a dakinta. Dada ta tsani ilmin boko kuma tayi masa mummunan fahimta don hakane bata goyon bayan mace tayi karatu mai zurfi ko mazan ma sai da akayi dagaske ta hakura ta kyale su. Biyayya ce kawai tasa Ya Nuratu ta auri Dr.Mansur amma a hankali ta gano qualities dinshi da kyawawan dabi’unshi da uwa uba kyautatawa da kulawarshi a gareta wanda suka sanya mata soyayyar mai karfi. Haihuwar ta daya ta samu ya mace aka sanya mata sunan Dada wato Fatima suke ce mata Amal! Shekarunta shida suna zaune cikin kwanciyar hankali da kaunar juna. Duk lokacin da mukazo Ya Nuratu tattarowa take ta dawo wajenmu sai zamu koma take tafiya.
Cikin ladabi muka gayar dasu sannan muka shimfida katuwar ledar cin abinci muka soma hada musu kayan da muka tanadar musu. Nan da nan muka cika gabansu da kayan abinci iri iri. Dukansu nishadi suke da murna mai yawa domin sun dade rabon da su hadu gabadayansu lokaci daya. Na dauko katon flask din bakin shayi ne naji karar kararrawa don haka na ajiye shi a gaba Daddy na mike da sauri na nufi kofar.
Gabana yayi mugun faduwa da ganin Ya Mahmud! Inaga bayan tsanarsa da nayi har tsoronsa nakeji. Da sauri nayi baya har da sassarfa na koma kitchen.
Ya Mahmud ne akan gaba cikin shigar manyan kaya ta fara sol din getzner an kawata ta da dinkin hannu da zare coffee. Ya dora hula coffee akan gyararriyar sumarsa wadda ta kwanta lambau har keyarsa. Hannunsa ma lafiyayyen agogon fata ne samfurin “Calvin Klein” shima coffee. Ya sinkife kafarsa da covered shoe dan gidan Luis Vuitton(LV) shima coffee. “He is the most classy guy ive ever seen in my life!” Biye da shi matasa ne guda shida masu shekarunsa da wadanda suka zarta shi kadan kowanne cikin shiga ta alfarma kana ganinsu kasan sunci sun tada kai a boko, da kudi, exposure!
Gaban su Daddy suka zube suna diban gaisuwa kafin su hau dinning kamar yanda Ya Nuratu tayi insisting.
Suma kamar yanda muka hadawa su Daddy abincin haka muka yi musu. Na dauko plates nazo na ajiye sannan nayi musu gaisuwa guda daya ba tare da na dube su ba. “Designer Guy wannan sister dinka ce?” Maimaita sunan nayi a raina “lallai kam yaci designer guy din domin ko handkerchief ka gani a hannunsa akwai brand din shi” kafin ya bashi amsa na shige kitchen don haka banji abinda yace masa ba.
Bayan sun kammala cin abincin Dada ta futo sukayi sallama da aminan Daddy. Nan fa suka cikamu da kudi ni da Ya Nuratu da Amal.
Na kulle kofar na dawo ne na hango su Ya Mahmud suma sun taso zasu tafi. Rabewa nayi ta gefensa na wuce. Ji nayi an kira sunana na juya da sauri a dalilin gane muryar me kiran da nayi. A hankali na isa gabansu. Wani kyakykywan saurayi ne fari sol a gefensa ya watso mun murmushi sannan ya sanya hannu cikin aljihu ya futo da sankararrun dollars ya miko mun yana cewa “sister ga barka da sallah” wani irin kallo nayi masa sannan nace “ka barshi nagode” na juya da sauri na wuce yana ta kwallamun kira naki tsayawa na shige daki. “Mtsew ina ruwana da abokanka da wani kudinku? Me kuma zai sake hadani da kai? Aikin banza” abinda nake a zuciya kenan na kulle kofar dakin na shige toilet don kar a dameni.
Washe garin sallah muka koma Jeddah. ranar litinin muka je asibiti da Dada likita ya sake dubata tare da sallamarta sai bayan watanni shida. Ban sake ganin Ya Mahmud ba ashe tun ranar sallah ya tafi. Ran talata da yamma tuni muna cikin jirgi bayan munyi sallama da Ya Nuratu tana ta kuka abun dariya. Nima na tabbatar zanyi missing su ita da Amal. Amma ya muka iya? Kowa da yanda Allah ya aje shi.
We are finally Home!! An dawo daga wannan tafiya saura wata kuma in ta taso. Don kadan daga cikin aikin Daddy bayan sati hudu yace muje Dubai ko Cairo Dada ta huta. Kwanan mu biyu da dawowa Mami tazo tayiwa Dada sannu da zuwa murna kamar ta kasheni. Na kwaso mata duka tsarabar da na jibgo mata Dada tana yimun dariya.
Lokacin da muka dawo ana cikin hutu sai bayan sati daya muka koma school. Duk inda nake tunanin abubuwan da nayi missing sun wuce haka don haka karatu na dukufa yi bani da time din kaina domin muna gab da zana finals dinmu.
Ran saturday da la’asar na idar na sallah kenan Dada ta shigo dakina tana cewa “Zara yi maza ki karasa ki shirya kizo zan aike ki” gyaran murya nayi mata a sakamakon azkar din da nake yi. Ina kammawala na shiga toilet na ware warm shower nayi wankan cikin sauri na futo. Sannan na shirya cikin embellished super mint green mai ratsin baby pink. Dinkin skirt and blouse babu komai na kwalliya sai fitting da yayi kamar a jikina aka kera kayan. Na sauya barimar kunnena daga gold zuwa silver hakana bracelet din hannuna da anklet. Fuskata babu komai ruwan hodar merrycay da pink jambakin “mac” wanda ya mayar da kwalliyar tawa abun sha’awa. Ina cikin daura sandal dina samfurin “Chanel” naji kiran Dada don haka nayi maza na yafa gyalena dan siriri pink na ciro babbar jakar “ALDo” domin ina tunanin kila aiken na kudi ne. Da daya daga cikin turaren “Ralph Lauren” da ke kan mudubina na feshe kwalliyar tawa sannan na futo ina daure hannuna da agogo silver dan gidan “Armani”. I sometimes call myself designer baby! Kamar yanda naji ana kiran Ya Mahmud domun Daddy da Mami na matukar kulawa da bangaren gayuna komai tsadar jaka ko takalmi Daddy zai siyo ya kawo mun bai taba yin tafiya bai mun tsaraba ba. And you know? Mutum like Daddy bai shiga karamin kanti. Ga Mami daga gefe duka abinda tagani na sha’awa ni take tunowa komai siyemun take komai tsadarshi musamman da ta gane ina matukar son classy abubuwa don hakane na hada wani karamun designer room.
Kamar yanda nayi tunanin hakane! Kudi Dada tabani rafar yan dubu dubu guda biyar guda goma 500k kenan. Ta miko mun envelop na saka aciki na like.
“Gidan Hajiya Maryam zakije ki kai mata kice gashinan injini ba yawa a siye wa Amarya tsintsiya” dariya nayi sosai nace “Dada manya 500k dince na siyan tsintsiya?” Itama dariyar tayi tace “ke kamar ba bahaushiya ba haka ake cewa idan za’a kai gudunmuwar buki komai yawan kudi sai ace a siya tsintsiya” dariya na sake yi ina sarawa Malam Bahaushe da tunaninsa masu wuyar fahimta. Bayan nayi mata sallama na futo. Idona ne ya kai kan sabuwar Range rover red colour tasha wanki sai kyalli take. Tuni yawuna ya tsinke! Cikin sanda na dawo parlour na duba kan side table na dau mukullin motar Ya Omar wadda yake ji a ita kamar ransa a zuciyata ina cewa “nima yau sai na dana wallahi sai dai komai zai faru ya faru”
Ina shiga wani kamshi ya doki hancina. Ya Omar is crazy har turaren wuta yake yi acikin motarsa don tayi kamshi unique! Kunna motar nayi na ware AC sannan na duba cds dinshi na zabo na mutuminshi “chris brown” ma saka nan da nan wakar “with you” ta soma tashi na baiwa motar wuta malam Lawan ya bankade mun gate na futa a guje ina dariyar mugunta ni kadai tare da tunanin yanda zamu kare da mai motar.
Gidan Hajiya Maryam da ke Maitama na dau hanya. Ina isa na tarar da ita cikin mota zata futa don haka na bata sakon anan babu yanda bata yi dani ba nazo mu shiga ciki nace mata babu komai nima sauri nake. Ta debo kudi ta bani nayi mata godiya mukai sallama ta futa nima na koma motata na futo! In gaskiya ne na dawo gida mana? Amma saboda dokin motar aro sai na dau waya na kira Aisha. “Hello bestie ” cewa nayi “kina ina Aisha gani hanyar gidanku? Da sauri tace “No bana gida ina Maitama park da yaran A.saudah sunzo gidanmu” cewa nayi mata gani nan zuwa don ji nake idan banyi yawo da motar nan ba na bar banza.
Lokacin da na isa dakyar na samu wajen parking a dalilin weekend ne. Ina cikin tafiya naji alamun mutum a bayana sai na juyo.
Wani kyakykywan saurayi nayi tozali da shi fari ne sol har farin yaso ya mishi a yawa a sakamakon hutu da jindadi da ilmi da danshin naira da sukai mata rubdugu. Kyakykywan karshe ne domin ba don shigar da take jikinsa ta farin voil ba cewa zanyi ba’indiye ne. Hannunsa dama da hagu rike da yaro mai kama da shi sak. A take na gano yaran twins ne an musu kwalliya mai kyau kamar ka sure su ka gudu “Hello beautiful” ya fada a lokacin da na juyar da kaina daga garesu. Kirjina na bada wani sautuka “dum!dum!! Sai bugawa yake! Yayinda Kafata ta soma rawa kamar ba zata daukeni ba.!Kunsan “love at first sight?” Shine abinda ya faru dani a yau.
Tsayawa nayi cak a sakamakon jin kafafuna na niyyar zubewa a wajen. Wannan ya bashi damar karasowa gefena tare da yan yaran da baza su wuce shekaru shida ba. “Assalamu Alaikum” ya sake magana a karo na biyu. Ji nayi kamar a mafarki scene din yake faruwa. “Daman anawa musulmi sallama yaki amsawa?” Yayi magana a karo na uku. Sai a lokacin na saisaita kaina na kirawo nutsuwata da class dina na kalle shi cikin isa nace “wa Alaikumus salam, amma kuma bai dace ka tsayar dani cikin public haka ba” murmushi yayi duka hakoransa talatin suka bayyana farare tas sai na soma ganin kamannin wani indian actor mai suna “Shahid kapoor” a tare da shi. “Ok..I’m sorry ma’am ki bani phone number please idan kinaso na daina binki” rolling eyes dina nayi nace “kawai kuma sai na baka number na ko?” Yayi murmushi sannan yace “fine…idan baki bani ba kuwa yana nufin duk inda kikasa kafa zan mayar da tawa daga nan har zuwa duk ranar da kika shirya bani bazan gaji da binki a baya ba” juyawa kawai nayi na tafi ina ganin kamar babu class na bada number da sauki haka. Amma kuma me? Duk inda nayi yana biye dani da yan yaransa! Wannan ya sanya na sake juyowa cikin fushi nace “Malam please ka daina bina banaso” cikin kwaikwayon muryata shima yace “Malama please ki bani number sai na tafi” murmushin mugunta nayi a lokacin da na tuna zan iya bashi number bogi. Sai dai kuma ya zanyi da sonsa da ya yi mun shigar sauri lokaci daya? Dole na shiga kira masa numbobin yana shigarwa a wayarshi sannan ya kira. A hankali sautin ringtone din iPhone dina ya soma tashi. Yayi murmushi mai kayatarwa sannan yace “na zata zaki bani fake ne ko wadda ta daina aiki! Sannan ya dubi yaran yace musu “my babies meet your new Aunty name? Ya dubeni yana dage giranshi. “Zara” na fada a sanyaye. “Good!! meet your new Aunty…. Aunty Zara” duka yaran suka soma dariya suna kallona. Sannan daya yace “Aunty Zara do you have sweet?” Dariya sosai yaran ya bani na soma murmushi. Cikin high tone baban yace masa “what’s wong with you Fahad? Kowa ka gani sai ka roke shi sweet?” Jakata na balle duk da nasan bani da sweet din sai chocolate din bounty da muka futa da Aisha ran nan ta siya ta bani. A jakar na barsu ban sake bi takansu ba sai yau din da na dauko jakar. Guda hudu na ciro kowanne na bashi biyu suka amsa suna ta murna. Kallonsu yayi yace “oya what do you tell Aunty?” Gaba daya suka hada baki suna dariya suka ce “Aunty thank you” nayi murmushi nima nace “you are welcome” sannan na wuce da sauri don ganin maganganun na shirin yin yawa.
Dakyar na lalubo Aisha da yaran suna ta bata wahala ita kuma ba gwanar son yara ba. Na shiga yi mata dariya. Rai a bace tace “wallahi Zara yaran nan ba karamar wahala suka bani ba yau” cewa nayi “ke dai Allah ya baki yaya kamar goma muga yanda zakiyi? Yara biyu su dagula miki lissafi haba Aisha?” Tabe baki tayi tace “Allah ma bazai amsa addu’arki ba Insha Allahu. Yaro daya ko biyu zan haifa” nayi murmushi kawai ina mamakin wacce irin mutum ce Aisha!
Tare muka futo da ita ta shiga motarta nima na shiga tawa na dau hanya! Lokacin da na iso gida ana ta kiraye kirayen sallar magrib. Sai lokacin na tuna motar aro na dauka. Gabana yai wata irin faduwa a dalilin tuna halin mai motar nayi idan an bata mishi rai. A hankali nake tukin har na isa kofar gidanmu bugun kirjina na karuwa. Ba Lawan ya wangale mun gate na shiga a hankali. Bayan nayi parking motar dai dai yanda na daukota na balle murfin na futo ina addu’ar Allah ubangiji yasa Ya Omar bai zo gidan bayan na futa ba.
Kai ai da yazo ma da tuni a farfajiyar wajen nan zan ganshi yana tsaye yana huci yana jirana! Wannan ya bani kwarin guiwar shiga falon.
Sallamar tawa ce ta katse dai dai lokacin da na shigo cikin falon a sakamakon ganin Ya Omar zaune akan kujera fuskarnan babu rahama babu sassauci. Dada na tsaye ta zumbula dogon hijab dinta tana niyyar tayar da sallah. Habawa ai cillar da jakar nayi a guje na ari ta kare na bude kofar na futa da gudu. Ya Omar ya taso shima ya biyoni a guje abinda ya karamun kwarin guiwar gudun. Filin gidan muka shiga zagayewa yana bina a guje cikin tsananin fushi nikuma gani ba dai iya gudu da zillo ba duk dabararsa ya kasa kamani. Jin an idar da sallah ya sanya yayi wata irin kwafa ya futa daga gate din gidan.
Nikuma nayo cikin gida a guje na shige dakina na bar Dada tana tikar dariya. Ko ta mecece? Oho!!.
Bayan na zura key ne na fada gado ina mayar da numfashi kafin na kece da wata irin dariyar mugunta. “Gaskiya na iya gudu” idan na tuna yanda na dinga wana Ya Omar ina zizzille masa sai naji dariyar ta dawo sabuwa domin fuskarsa a wannan lokacin kawai abun dariyar ce. Iya haushi na shaka masa saidai fatan Allah ya hana haduwar mu a wannan kwanakin don na tabbatar sai na raina kaina.
A karshe dai toilet na fada nayi wanka da alwala nazo na shimfida dadduma nayi sallah. Ina matukar jin yunwa amma babu yanda na iya domin babu tsautsayin da zai sake futar dani daga dakin nan kafin shabiyu na dare.
A maimakon nayi zaman banza sai na dauko cardboard da drawing materials dina na soma zana hoton wani jibgegen mutum mai katon ciki tsaye ya rike kugu gefe guda na zana wata siririyar yarinya doguwa mai kyau rike da flower da dan card. a saman card din na rubuta “I’m sorry Ya Omar…i will never ever go near your car again” ina colouring zanen ina tikar dariya domin na tabbatar wannan zanen sai yafi daukar motar bata wa Ya Omar rai yanda ya tsani qiba a rayuwarsa kullum yana gym yana work out wannan 6pack din yanda yake ji da shi kamar ba mutuwa zaiyi wataran a binne shi ba. Ya tsani yaga mutum mai qiba a rayuwarsa ko mace ko namiji musamman yaga katon ciki……
I’m stubborn right? Daya daga cikin manyan halayena kenan da kowa ya sanni da su. Allah ya hore mun tsokana. Idan na saka mutum a gaba komai girmansa sai yayi kuka.
Sai dai kuma kafin nayi sabo da mutum har ya gano hakan ana dadewa.i look very innocent da zakai tunanin idan aka samun yatsa a baki ba zan iya cizawa ba.
A karshe dai ban futo daga dakin nan ba sai shabiyu da kwata sannan na shiga kitchen na hada tea mai kauri na debo damnbun nama acikin karamun plate da goran ruwan Faro karami na dawo dakina. A gaggauce na kammala ci na saka pj dina na kwanta. Na dauki wayata na sa a charji naga miscall guda goma daga wata kyakykywar special number. Babu tantama mutumin da na hadu da shi yau ne. Ya salam! Ya akai banji wayar ba? Ina can ina jan fada na yar da jakar a parlour. Mtsw! Yanzu ya zanyi? Sake duba wayar nayi sai naga messages guda biyu sun shigo na farko yana cewa.
“Salam beautiful! How was your day? Na kira ki bakya picking dafatan kina cikin koshin lafiya?” ..Imamu.3
Wow! I chuckled! Thats lovely. So sunanshi Imamu! What a sweet name!
Na sake bude dayan shikuma cewa yayi.
“I Love you Fatima!! …. ..i just cant wait to tell you this words”
Wata irin ajiyar zuciya nayi idanu na ya cika da kwalla. This is the most beautiful message ive recieved this year! Masha Allah. I love you too Imamu! Na fada a fili ina murmushi!
Ban iya bacci ba a wannan daren sai tunane tunane kala kala.
Kiran sallah ne ya tashe ni daga nannauyan baccin da bansan lokacin da nayi shi ba. Bakina dauke da addu’ar farkawa daga bacci na tashi zaune sannan na laluba dankwalina na daure kaina na shiga toilet nayi alwala. Bayan nayi raka’atanil fajr na saurara masallaci suka tada sallah na bi jam’i. Kamar kullum bayan na kammala azkar din safe alqur’ani na na dauko na bude surah kahfi na karanta na karanta surah maryam da surat Daha. Favourite surorina a alqurani. Sannan na nade kayan sallar na koma gado na kwanta. Ban tashi bude idona ba sai shadaya na safe.
Cikin sauri na shiga toilet nayi brush na dora hijab akan kayan baccina na futo muka karya tare da Dada.
“Jiya haka kika kwana baki ci komai ba kenan?” Cewar Dada. Murmushi nayi mai sauti sannan nace “na futo Dada amma sai wajen Shabiyu da rabi na sha tea na koma daki”
Girgiza kai tayi tace “sai ki zauna cikin taka tsan tsan kuwa don ina jiye miki haduwarku. Dariya nayi sosai.
Ta sake cewa ” idan ya ritsaki a parlour ko a kitchen naga filin da zaki irin gudun jiya. Yarinya kamar dila? Bansan inda kika koyo tsokana ba nikam! Indai Aliyu ne kinci bashi don ba’a cin bashinsa a kwana lafiya” har ta gama maganar ban daina dariya ba. “Dada kawai daga daukar mota? Sha’awa ta bani wallahi. An wanke sai kyalli take” girgiza kai tayi tana cin sandwich. “To an gaya miki wankin na banza ne? Shiryawa fa yayi zaije zance safiyyan ta dawo daga Amrika jiya” wow!!! Bakina yayi forming “O” shape.” Allah sarki Ya Omar. Gaskiya ban kyauta ba…..wallahi bansani ba Dada. Shiyasa temper dinshi tafi na kullum”
Murmushi Dada tayi tace “kya dai hadu dashi.” Sosai naji tausayin sa. Domin nasan irin son haukan da yakewa Sofiyya amaryarshi nan da watanni hudu. Sofiyya yar gidan minister of women affairs ce Hajiya Naja’atu saleh. Her only child a duniya. Duk da gatan da take ciki Tana da mutsuwa da kamun kai da kuma addini ga ta kyakykywar gaske. A halin yanzu likata ce kwararriya ta bangaren paediatric (yara). Kwata kwata satinta hudu da kammala karatun amma sai jiya ta dawo Nigeria daga kasar NewYork din America.
Toh ba dole kuwa Ya Omar ya wanke mota ba. Gaskiya ban kyauta masa ba.
Ni kaina na saba da ita sosai tun lokacin da Ya Omar ya kawo ta ta gaida Dada mukai exchanging contact muna yawan magana ta WhatsApp wani lokacin kuma nakan kirata mu gaisa. She is very nice and friendly!
Sau biyu yana kaini gidansu.
Ita kuwa wadda Ya Sadik zau aura balarabiyar Hurgada ce ta kasar Egypt. Mazauna Nigeria gabadaya hausar ta bata futa. Daga Arabic sai turanci. Tare sukai karatu da Ya Sadik a American University of Paris. Daga nan sukai matukar shakuwa wadda ta rikide ta koma soyayya. Wannan kenan!
Ina komawa daki waya na dauka na kira Aisha! Yeah to tell her abinda ya faru jiya da yamma a Maitama park. Bamu taba boyewa juna wani abu ba. She is my best friend and the sister i never had. Tare muka taso makaranta daya islamiyya daya komai tare muke yi. Mun wuce kawaye mun wuce aminai mun koma yan’uwa domin har iyayenmu mun kulla su zumunci mai karfi. Bayan na kammala bata labarin ihu ta sanya mun da ya kusa kashemun dodon kunne! “So bestie has finally…” katseta nayi a cewa “kinga don Allah sai mun hadu a school gashinan yana kira” ban jira komai na na katse kiranta na dauki na Imamu wanda yake ta shigowa tunda na fara wayar.
Hello dearis! How is this page?
Am i boring you? I need your comments.inaso naji daga gareku.1
Futowata daga exam kenan na nemi waje cikin kujerun da ke kafe a harabar makarantar mu na zauna. Tunani nakeyi akan zuwan Imamu gidanmu a yau wanda bansan yanda zai kasance ba. Wayata na zaro a hankali na boye daga cikin jakar nake dannawa na bude messages Imam da suka shigo yanzun nan! Sako ne akan fatan alkhairi da samun nasara a jarrabawata da kuma kalamai masu saka kwarin guiwa da kwantar da hankali. A rayuwa ban taba samun wanda zuciyata ta kamu da sonsa ta farat daya raina yake shaukin kaunarsa ba irin Imamu. Domin mutum ne shi mai tsananin kulawa da nuna so da kyautatawa ga abinda yaje kauna. Tunda muka hadu dashi yau sati biyu bai taba ko kusa da gayamun maganar da banji dadi ba. Mutum ne shi mai hakuri da juriya da kuma sanin ya kamata. Yasan darajar mutane fiye da tunani. Sau dayawa idan ya zauna yana gayamun kalamai akan yanda yake ji a kaina sai naga kamar a mafarki domin mutum ne shi wanda Allah yayi wa baiwa irin wadda zai iya kowacce irin isa da kasaita. Yana da kyau, kudi, ilmi, gata da duk wani abu da yake sa mutum yaji kansa amma sam Imam bai damu da wannan ba. Rayuwa yake da kowa cikin mutuntawa da darajawa.
Ya gayamun shine first born a gidan
Late. Eng.Mukhtar Jega da Dr. Sa’adatu Karaye. Mahaifinsa ya rasu ne a sakamakon hadarin jirgin sama tun yana shekaru sha biyar. Mahaifiyarsu ce ke dawainiya dasu.
Su uku ne shi kadai namiji sai kannensa yan mata Yusra da Yasmin. Duka suna kasar waje suna karatu.
A halin yanzu shi yake kula da duk wani harakar dukiyarsu musamman construction conpanies din mahaifinsu da ke da rassai a kasashen duniya. Har Eng.Mukhtar ya mutu mutum ne wadda aka sani da zuciya mai kyau da kuma kyautatawa iyali ga zafin nema ga tausayin da jin kan na kasa da shi da yawan alkhairi. don haka mutuwarsa ta girgiza zukata dayawa. Ashe kuwa Imam ba a kasa ya samo nagartattun halayensa ba. Zan iya cewa addu’ar Mamina da Ya Nuratu ta amsu a kaina na samun miji nagari idan har Allah yasa Imamu ya kasance miji a gareni.+
Ji nayi wani lallausan hannu ya dafa kafadata wanda ya sanyani saurin juyowa. Aisha ce zaune a gefena tana murmushi “anya kuwa Juliet kinyi abun kirki a exam din nan?” Ta fada cike da tsokana! Harara na watsa mata nace “No sunan Romeo na cika paper dashi” ta kuwa kwashe da dariya harda rike ciki.
Sannan kuma ta dago kamar me tunanin wani abu idonta cike da hawaye tace “zara i’m surely going to miss you wallah…..i will miss every moment da muka yi tare a school din nan!”
Jikina ne yayi bala’in sanyi a sakamakon tunawar da nayi saura sati biyu ya rage mana mu kammala secondary school. Shikenan mun rabu da Aisha. Mun daina ganin juna kullum, musamman ma da ita babanta jira kawai yake ta gama ya kaita Harvard’s. Shikenan rayuwa zata juya kowa ya kama gabanshi.
Nikam bansan meye makowamata ba. Zanci gaba ne da karatun? A ina? Dada zata hanani? Ko kowa aure zanyi? Wannnan tunanin da ma wasu ya sanyani hawaye shabe shabe. muka rungume juna muka shiga rera kukan tausayin junanmu.
“I will miss you more Aisha.. i will miss you sooo much!” Cikin kuka nake maganar. Rabuwa da junanmu ba abu ne mai sauki ba domin ni da Aisha kamar tagwaye muka taso. Bacci kadai ke rabamu. Tun daga playgroup muke tare da ita har kawo wannan lokaci. Islamiyyar mu daya komai tare mukeyi a rayuwa. Tuni muka kulla iyayenmu alaka mai karfi a dalilin shakuwar mu har ya kasance daya zaije gidan daya yayi kwanaki wani lokacin ma idan iyayenta sunyi tafiya muna cikin karatu gidanmu take dawowa mu dinga tafiya school tare. Babu abinda muke boyewa junanmu. Babu abinda bamu sani game da juna ba. Mun wuce kawaye mun zarce aminai mun zama yan’uwa na jiki! Don haka rabuwa lokaci daya baya abu ne mai sauki a garemu ba. Sai da mukayi mai isarmu sannan muka share hawaye kowa cikinsa a mace. Cikin low tone tace “yaune Imam zaizo din?” A sanyaye na daga mata kai sannan na dora da cewa “zaki zo da wuri dai ko?” Ta amsa “insha Allah ina komawa zan shirya na taho” haka muka rabu duk zuciyarmu babu dadi da alkawarin zatazo gida mu tarbi babban bako tare. Don na riga na gama cika shi da labarinta kamar yanda shima na cika shi da labarinta. Sai dai kowa ban gaya masa sunan kowa ba ban gaya masa komai na rayuwar kowa ba sai dai alakar da ke tsakaninmu nace sai ranar da muka hadu gabadaya za’ai wannan intro din.
LIVER POOL LONDON
A hankali yake tukin cike da gajiya ya ware heater cikin motar duk da cewa lokacin summer ne amma ruwan da aka kusan wuni ana yi ya sauya garin gabadaya ya dau wani irin sanyi mai ratsa kashi. Musamman ga mutane irinshi da basa shiri da sanyin ko kadan. Sautin kira’ar sheik Abdurrahman Sudaith ne cikin Surat Maryam yake tashi a hankali cikin motar yana saukar masa da wata irin nutsuwa.
Bayan ya isa gidan ya zagaya gareji yayi parking motar sai ya kwantar da kujerar baya yana sauraren karatun har zuwa karshen surar. Sannan ya balle murfin ya futo. Ya bude kofar baya ya kwaso wasu files da kuma jakar laptop dinshi ya soma takowa cikin gidan a hankali kamar me tausayin taka kasar don tsananin gajiya.
A kitchen ya samu Sherifah tana ta goge goge. “Good evening sir” ta fada cikin ladabi. Ba tare da ya dubeta ba ya amsa sannan ya dora da cewa “you do not have to cook dinner …” ta sake amsawa cikin ladabi “yes sir” daga nan ya karasa falon ya aje tarkacen hannunsa ya wuce daki. A hankali ya soma cire boturan fara kal din labcoat din da ke jikinshi daya bayan daya sannan ya zare ta. nan da nan bakar suit din da ke jikinsa samfurin Armani ta bayyana. Sai da ya zare komai a aje sannan ya shiga toilet ya sakarwa kansa warm and relaxing shower.
Mintina talatin ya kammala wankan ya futo yana kamshin designers mayukan wankan da yayi amfani dasu a jikinsa da sumar kansa.
Bacci ne fal a idonsa wanda ya hanashi ko shiryawa ya haye english royal bed din nashi ya soma bacci peacefully.
Bai bude idanu ba sai karfe shida da rabi bakinsa dauke da addu’ar farkawa daga bacci. “Ya salam! Ya fada lokacin da ya duba agogon wayarsa. Yayi missing sallar la’asar . Toilet ya fada ya watsa ruwa cikin sauri tare da alwala ya futo ya shinfida sallaya yayi sallah. Mintina ashirin da biyu yana azkar dinsa da addu’o’i kafin ya nade kayan sallar ya mike. Alarm din wayarshi ne ya soma kara ya karasa ya duba. Reminder din da ya saka ke tuna mishi yau ne ranar da Eng.Garba Galadanci ya gayyace shi dinner a gidanshi. Wani mugun tsaki yayi tare da dafe kansa. Iya gajiya ya gaji wani stressful meeting sukai da yayi exhausting dinshi. Gashi gidan ba kusa ba. can cikin garin London ne. Sai dai ba yanda zaiyi ya saba alkawari musamman ga mutum irin Eng. Mai karamci da sanin kimar dan’adam. Gaban mudubin ya isa ya bude drower ya zaro hand drayer ya soma busar da jikakken gashin da ya kwanta yalo yalo a kansa tare da shafe shi da mai ya dauki wani irin kyalli da sheki.
Mintina goma ya kammala shiryawa cikin shedda hilton blue black wadda ta dauki dinkin hannu irin na mutanen kasar Senegal. Daga kasan rigar ya saka sweater mara nauyi ya daure hannunsa da ruwan sarkar agogon “Dior” silver. Bai saka hula ba sai scarf din burberry ruwan toka. da yayi amfashi dashi wajen nade wuyansa. Wanda ya maida shi unique. A bakin gadon ya zauna yana sinkife kafarsa da covered shoe dai dai kalar sheddar sannan ya feshe jikinsa da turarensa na yau da kullum wato LA NUIT na LV ya kara da SAFARI na Ralph Lauren. .
Ya kwashi wayoyinsa ya zuba a aljihu da wallet dinshi ya futo. Tuni Sherifah ta tafi don haka ya kulle gidan ta baya da gaba ya futo. Motar kamfani da yayi kira ya tsaya jira minti uku ta iso ya shiga don bazai iya driving ba.
Yana shiga motar ya ciro wayarsa ya soma danna lambobin Nigeria. Bugu biyu wanda yake kiran ya dauka “Hello Hausa Arab ina ka shiga ne?”
Cikin taushin murya yace “kyaleni Faisal wallahi I’m stuck cikin ayyuka dayawa sai da na dawo nake ganin miscalls dinka” cikin tausayawa Faisal yace “kaga ka raba kanka da wannan matsanancin aikin in ba haka wallahi ka tsufa da wuri.” Murmushi yayi duka kumatunsa suka lotsa yace “tohh naji…yanzu dai me ya faru?” Cikin tsananin farinciki Faisal yace “su Abba sunje gidansu Ihsan an tambaya an bani an saka rana watanni shida” fadada murmushinsa yayi yace “Alhamdulillah Allahumma barik. Allah ya sanya albarka Friend i’m so happy for you” Faisal yace “thank you aboki..Allah ubangiji ya kawo mana ranar da wata zata sace mana zuciyarka kaima muzo musha shagali” dariya sosai ya dinga yi “you are not serious” ya fada da hardadden harshensa. Faisal ya sake cewa “ohk… joke aside my wedding is in six months and you are my best friend my favourite brother….dont say ban gaya maka ba billahil azeem kaki tahowa Nigeria aurena kar ka sake tunanin ma kasanni” cikin dariya yace “wait…calm down! Ka bar rantsuwar mana sai kaga lokacin yayi banzo ba.” Faisal cikin nutsuwa ya sake cewa “ina gaya maka ne don kasani. Rabonka da Nigeria shekara goma duk abinda ya faru kace aiki kamar inji sai angama kayi ta baiwa mutum hakuri toh wallahi ba dai a wannan lokacin ba i am telling you this from the bottom of my heart rashin zuwanka wajen bikina zai iya lalata duk wata alaka dake tsakaninmu” yana kaiwa nan ya katse wayarsa.
Wata irin iska ya furzar mai zafi zuciyarsa tana azalzala. Duk lokacin da ya tuna gida sai yaji wani irin faduwar gaba da tashin hankali. Toh amma this time shi kansa yasan bazai iya dojewa ba he cant escape this. Ba zai iya yiwa Faisal haka ba. Mutumin da ya tsaya masa a rayuwarsa a kowanne lokaci a kowanne yanayi wanda yake karanta zuciyarsa ba tare da yayi magana ba. Wanda yasha shiga damuwa da masifa iri iri a dalilinsa wanda yake tasowa takanas ya zo wajenshi ya ganshi yaji damuwarshi. Ba zai disappointing dinshi a wannan babbar ranar ba. Dole ya soma shirin tafiya Nigeria saboda mutane biyu masu muhimmanci a rayuwarshi.
Wannan tunanin ya sauya mishi mood gabadaya ransa ya jagule kirjinsa yayi nauyi kansa ya dau zafi. A hankali ya jingina kansa jikin kujerar motar ya dinga maimaita “lahaula wala kuwwata illa billahil aliyyul azeem” har suka isa gidan Eng.Garba da ke Sussex Garden. Gidan yana opposite gidan Daddy na garin London. Cikin nutsuwa ya isa kofar ya taka steps din guda uku sannan ya danna kararrawa.
Minti daya akazo aka bude kofar!
Take idanunsa sukai arangama da santaleleliyar black beauty mai wani irin tsayi da za kai mamaki mace ce ta mallakeshi. Duk da tsayin ne kawai babu structure mai kyau. Tana sanye cikin suit din “George” na mata jajaye.
Dogon gashinta cikin pony tail. Kana ganinta kaga rainon turai.
Gabadaya kyawun da take tunanin tana da shi ta matso tana blushing.
Mamaki ya kamashi ..me take nufi da yi mishi irin wannan tarbar? Oho! Ya baiwa kansa answer. Ganin bata da niyyar matsawa ya sanya ya kunna radion bakinsa ya murdo tashar CNN yace “hello! gimme way” sai lokacin ta farga da kataborar da takeyi ta matsa mishi a hankali ya kutsa kai cikin falon..
A hankali na murda kofar falon na shiga cikin sallama!. Da wani kyakykywan saurayi nayi tozali.
Fari ne sol wanda ya cakude da hutu da jindadi da da kwanciyar hankali. Sanye yake cikin wani bakin Voil wanda ya sake futo masa da hasken fatarsa. Damtsen hannunsa daure da sarkar agogon “ROLEX” kwandalele sai walwali yake. Falon gabadaya ya gauraye da kamshin “Tamford”
Wani tsadadden murmushi ya saki a daidai lokacin nake zama kan kujerar da ke saitin tashi. “Sannu da zuwa” na fada cikin tatatusar murya! “Yauwa sannu beautiful” nima murmushin nayi mai kayatarwa. I cant resist smiling anytime ya kirani da “beautiful” din nan.
Cikin so da kauna me yawa muka gaisa tare da tambayar mutanen gida.
Sannan ya dora da cewa “Zara dafatan kin gayawa Dada cewa ba da wasa nazo ba…Allah yasa sun shirya yi miki aure yanzu!” Murmushi kawai nayi kaina a kasa bance komai ba. Ina “twins?” Na sauya maganar. Nan da nan ya wangale baki ya soma far’a a dalilin tambayar yayanshi da nayi. ” twins suna lafiya suna kuma gaishe ki” nace “ina amsawa” “ina Mamansu?” Na sake tambaya cikin faduwar gaba don na kosa kwarai naji wani abu game da Maman yaran. Shikuma duk lokacin da na dauko maganar sai ya sukwane. Kuma shi don kanshi bai taba mun magana akanta ba. Wannan yasa na soma tunanin ko suna tare ko sun rabu?
Murmushi yayi yace “she is doing fine…itama tana gaishe ki” zaro ido na danyi kirjina ya buga da karfi har nayi dana sanin tambayar! Ko gane hakan yayi? Cewa yayi “Ai zamu je very soon ku gaisa da ita ne” a sukwane na dago na dube shi idona sun sauya kala don tsananin kishi.
Sai ya sake sakin murmushi baice komai ba.
Knocking din kofa ya dawo dani daga balaguron da na tafi. Aisha ce ta shigo dauke da katon tray wanda aka shake da kayan motsa baki ta iso a hankali. Sai dai tana karasowa naga annurin fuskarta ya dauke firgice, tsoro, mamaki, da tashin hankali ya maye gurbin sa. Mamaki ya kamani domin bansan dalilin faruwar hakan ba sai dai kafin nayi wani motsi tuni ta shanye su duka ta nemo nutsuwa ta dora akan fuskarta. Akan center table din dakin ta aje tray din sannan ta janyo shi gaban Imam a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Shine ya fara nuna ta yana cewa “i have finally got to meet our besty”
Da wani irin yanayin da ban taba sanin Aisha dashi ba ta soma gayar da Imam kanta a sunkuye. Duk yanda yaso ya jata da hira ta kasa sakewa kamar ba Aisha magadisu ba wadda take sabo da mutum ta mayar dashi dan gida cikin mintina kadan. Son tambaya, son jin abinda ya shafe mutum, son sanin komai Aisha ce kan gaba. Bata da kwauron baki ko kadan don hakane ma duk inda ta shiga sai tayi qawaye kuma duk inda ta tsinci kanta bata shan wahala don bata da bakunta ko jin nauyi. Sai gashi yau tayi ligib ta nabba’a a gaban mutumin da take ta cin burin ranar da zasu hadu tayi cheking shi from head to toe. Tayi masa duka tambayoyin da take ganin sun dace har sai ta gano in ya cancanta ya zama mijin aminiyarta.
Kaina ya daure tamau da mamakinta.
A karshe ma dai sallama ta mishi tace mun sai na shigo. Sai na fara tunanin ko bayan futowata ne wani abu ya faru ko wani abu akai mata.don haka hankalina ya rabu biyu. Mintina talatin muna zaune sannan ya duba agogon hannunshi. Cewa yayi “ya kamata na tafi kada Dada tace na rike ki dayawa. Kuma ina da family meeting after magrib! Am i permitted?” Nayi murmushi kawai tare da mikewa. Shima tashin yayi yana gyara zaman hularsa a kansa.
Kallona yayi a tsanake yace “ga wannan (ya nuna wasu manyan jakunkunan kwalaye masu tambarin Gucci da Chanel da kuma wata katuwar leda) na kine. Wannan kuma (ya nuna wata ledar fara sol me tambarin Rasasi) na Dada ne. Sannan ya saka hannunshi a aljuhu ya ciro sabbin bandir din 200 ya aje kan table din yana cewa “wannan na besty ne duk da taki tsayawa muyi hira tare”
Kyam na tsaya ina kallonshi har ya kai aya sannan nace “No gaskiya sunyi yawa ka barshi. Dada ma fada zatayi” tafiya ya soma yi yana cewa “a’a ko dai kadan sukayi Zarah. Kicemun Dada bata karbar karamar kyauta”.
“Ba haka bane don Allah ka rage daga zuwa……” ban karasa ba yace “shhhhh. Its okay! Ki bayar sadaka idan bakyaso” ganin ranshi ya baci kawai na hakura. Har bakin motar na raka shi sai da ya bude ya shiga ya zauna sannan ya dubeni yana murmushi “i’m leaving….” cikin sanyi nace “sai yaushe?” Ni kaina bansan lokacin da maganar ya futo ba.
Da wani smirk a fuskanshi yace “will you miss me?” Na rufe fuskata ina yiwa kaina dariya.
“Lalala wato su Romeo hirar har a bakin mota ko?” Na juya da sauri don jin muryar Aisha! Itace ta iso tana ta faman murmushi wanda yayi confusing kwakwalwata domin dazun nan ba haka yanayinta yake ba.
Dariya yayi sosai sannan yace “bayan bestyn mu bata tsaya anyi hirar da ita ba? Amma kin dau bashi. Next time babu inda zakije!” Cikin dariya itama tace “gaskiyane ka biyoni bashi zan biya kuma” mun jima muna wasa da dariya kafin yayi mana sallama ya tafi.
Ganin ta warware sosai ya sanya kawai na kyaleta ban tambayeta game da abinda ya faru dazu ba. Ita ta kwaso kayan ta kawo su gaban Dada ta aje. Dadan tace ta bude mata. Manyan turarukan mata ne guda biyu yan gidan “Gucci” da kuma agoguna guda biyu kirar “Swatch” sai abaya hadaddu guda uku na Armani. Ita kuma Dada turaruka ne guda shida masu kamshi. Dakinta aka kwashi kayan aka kai aka aje muka koma dakina da Aisha don gabatar da sallar magrib!+
STORY CONTINUES BELOW

LONDON
Sai lokacin ta gane katobarar da takeyi ta matsa a hankali ya wuce cikin shiryayyen English sitting room din. Komai na wajen cream ne. ko’ina yasha gyara na musamman yana daukar ido sassanyan kamshin air freshner din “Aqua” ya mamaye ko’ina.
Daga gefen kujerar ya zauna yana cire takalman kafarsa sannan ya zagaya ya zauna kan kujerar sosai yana nazarin wajen.
Mintina uku matashiyar ta dawo dauke da tray an shirya masa kayan motsa baki a kai. Sannan ta zauna kujerar gefenshi tana gayar dashi cikin yanayin da shi kam ya gaza fassara shi.
“Dad will be here in few minutes, before then, Bon appetite!” Ta sake fada cikin american accent dinta.
Robar ruwan kadai ya janyo ya dauki garai garai garai din glass cup ya zuba rabin cup din yana sha a hankali.
Mintina bakwai suna zaman kurame kafin suji kararrawar kofa. Cikin sauri ta mike ta tafi bude kofar shikuma ya bita da kallon mamakin tsayinta. (Allah mai halitta) ya fada cikin ransa.
Sallamar iyayen ce ta katse masa tunaninsa ya mike tsaye cikin girmamawa Eng yayi maza yace masa “no zauna don Allah!” Sannan ya karaso gabansa ya miko masa hannu sukai musabaha. “I’m very sorry Doctor!. Wani muhimmin abu ya futar dani” cikin murmushi Mahmud yace “babu komai” sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya wadda ta cakare cikin coperate trouser baki da shirt mai stripes black and white ta nade kanta da dan karamin gyale. Kai ba zakace itace ta haifi zaratan yaya haka ba. (Me matan hausawa suke shirin mayar da kansu ne?) Cewar Mahmud cikin zuciyarsa. A fili kuwa dukawa yayi ya gaishe ta. Ta amsa cike da far’a da kulawa. “Ya Farida da babies?” Tace “lafiya kalau wallahi suna Nigeria”
Wucewa daki sukayi sannan suka sake futowa a tare hannunsu a sarke. (Mahmud yace yau nake ganin ikon Allah) Eng ne yace “Mahmud bismillah! Muje table” agogon hannunshi ya kalla karfe tara da talatin da tara. yace “saura minti hudu ayi sallar magrib” Eng yace “ohh. Ya kamata mu soma sallah tukunna”
Daki ya koma shikuma Mahmud ya shiga toilet din baki na falon ya musanyo tashi alwalar don bai zama babu ita sai dai hakan bai hanawa ya maimaita wata idan ya samu dama.
Safna ce tayi spraying katuwar dadduma daga gefen falon suka yi sahu. Matan suka dawo bayansu suma suka tayar. Mahmud ke jan sallar da daddadan harshensa mai futar da wani irin sautin kira’a mai sanya nutsuwa.
Dukansu basu so aka idar da sallar ba don dadin karatun Mahmud. Shikadai ya mike ya dora da nafila bayan sun idar da sallar kafin ya cimma su daga baya akan tebur din cin abinci. Wata gajeriyar baturiya ce da yaji suna kira Samantha cikin shigar kuku take ta kaiwa da kawowa akan table din. Ta aje wannan ta gyara wancan.
Dafe kansa yayi yana tunani lokacin da Eng yace “bismillah”.
Gaba daya cikin kalolin abubuwan da ke dinning din bai ga wanda zai iya kaiwa bakinsa ba domin gabadaya jagwalgwalon turawa ne.
Yes, shekarunsa goma a kasar Turai amma har yau ya gagara koyan cin kowanne abincinsu. Wani irin mutum Allah yayi shi mai bala’in kyankyami da rashin yarda. Abu daya yafi ganewa. Yayo cefane a dafa mishi abinci a gida yaci! Hankalinsa yafi kwanciya da hakan sai daidaikun Halal restaurants din da ya yarda dasu irinsu “The Meat co” da ke Westfield London da Tulay Turkish BBQ a liverpool da Fattush. Amma shi idon ta son ransa ne yafi kaunar Nigerian and Senegalese dishes.
Shine zai sake yaci ya koshi hankali kwance.
Eng ne ya kula da Mahmud yace masa “Mahmud ya baka soma zuba komai ba ko babu abinda yayi maka ne?” Yake yayi yace “no..ba haka bane zan zuba” yana rufe baki Samantha ta aje wani dogon tangaran an rufe shi da murfin glass. Yana dubawa yaga grilled fish da sauce ne yayi hamdala ya zuba. Yana ci yana kallon yanda family din suka bada hankali suna narkar abincin suna santi. (Oh Allah daya gari bam bam!) Ya fada a zuciyarsa. Bayan sun kammala Safna da Mamansu ne suka soma shiga ciki Eng yace masa su koma kujerun cikin falon. Bayan sun zauna Eng ya dubi Mahmud a nutse sannan ya soma rattabo masa jawabi cikin karyewar zuciya da damuwa mai yawa!
“Mahmud abinda yasa na nemi alfarmar kazo muyi dinner inaso ne nayi amfani da wannan damar na roke ka wata alfarma mai girma akan wani abu da yake matukar damun zuciyata. Wani abu a yanzu da yafimun komai muhimmanci wanda zan iya cewa bani da matsalar da ta kai shi” cikin mamaki Mahmud ya dubi Eng yana tunanin ta inda yaga dacewar yaji wannan matsala a matsayinsa kawai na likitan diyarsa.
Cigaba yayi da cewa :
“Mahmud tun ina karami iyayena suka rasu suka barni a hannun yayata wadda a lokacin watanta biyu kacal da aure. Ita ta rikeni ta mayar dani kamar ‘Da ba kani ba. ta bani dukkan wata kulawa da iyaye suke baiwa yayansu ta sanyani a makaranta ta bani tarbiyya har na kai matakin secondary. Tare da taimako da tallafin maigidanta Late Shu’aibu Barewa. Sai dai wani abun tausayi Allah bai basu haihuwa ba tsayin wadannan shekaru. Babu abinda basu yi ba akan neman maganin haihuwa har suka gaji suka dangana. Lokacin da na kammala karatun jami’a nayi bautar kasa maigidan nata ne ya samo mun aiki a construction company na abokinsa sannan ya aura mun kanwarsa da suke ciki daya Hafsatu. Watannin mu shida da aure kwatsam yayata ta soma rashin lafiya gwajin farko a asibiti suka gano ciki gare ta. Ba sai na baka labarin yanda mukai farinciki ba. Domin kowa ya fidda ran zata haiwu don shekarunta hamsin cif cif a duniya. Shekarunta kuma talatin da biyu da aure. Tunda aka samu cikin Alaji Shu’aibu ya tattara ta suka koma America domin ta dinga samun ingantacciyar kulawa. EDD dinta saura sati biyu muka tafi. Ranar kuwa da za’ai mata theatre gabadaya muna asibitin kowa jikinsa a sanyaye a ransa kuma murna da farinciki. Anyi nasarar ciro diya mace sai dai ita uwar bata sake farfadowa ta ga me ta haifa ba Allah ya karbi abarsa. “
Sosai hawaye yake sharewa a lokacin da yazo nan. Tsananin tausayin labarin ya karyawa Mahmud guiwa ji yake kamar shine da Maminsa hakan yake faruwa a gare su. Sai da ya dau lokaci sannan ya tsagaita da kukan yaci gaba.
“Ranar munga masifa da tashin hankalin da har abada bana fatan sake ganin irinsa. Ranar na zama maraya na hakika Mahmud domun Yayata bata taba barin nayi kukan maraici ba. Haka muka taho Nigeria cikin matsanancin hali. Kanwar Alaji Shu’aibu ce yayar Hafsat ta karbi yarinyar a dalilin tana shayarwa a lokacin. Tuni aka mayarwa da jaririyar sunan mahaifiyarta Nafisa muke kiranta Safna. Tun bayan mutuwar Yayata Alaji Shu’aibu yaki lafiya kullum cikin ciwo da damuwa aka gano ciwon zuciya ya kama shi in takaita maka Mahmud mutuwar Yayata ce shima sanadin sa. Ganin na rasa duka iyayena yasa na dage sai da na karbo Safna a hannun kanwar babanta naci gaba da rikonta a lokacin an haifar mun babbar diyata Shukhra itama sunan Yayata na saka mata. sai suka taso tare komai nasu daya bamu taba bambamtasu ba. Safna bata taba sanin bamu ne iyayenta ba sai da ta shiga jami’a. Yarana uku ne. bayan Shukra sai Farida sannan Muhammad. Safna bata taba kukan wani abu a a duniya nida Hafsa bamu magance mata ba shi ba. Tun bani da karfi mai yawa har Allah yayimun arzikin da nake ciki. Ita da Shukra duka anan sukai University dinsu sai dai Shukra na kammalawa ta samu miji akai mata aure ta dawo gida Nigeria ta bar Safna da bata da ko tunanin auren a wannan lokaci.
Duk sanda akai mata maganar aure sai ta saka kuka wai ita tafi so tayi karatu ta kammala. Bayan ta kammala karatunta na lawyer na sake yi mata zancen aure shima fir taki har tazo ta fara aiki. In takaice maka Mahmud har akaiwa Farida aure Safna tana nan. Babu kokarin da bamuyi ba akan Safna tayi aure taki yarda. Nikuma bana kaunar tayi kuka akan wani abu banso na tirsasata akan abinda bataso don haka muka zuba mata idanu. Safna bata tashi tunanin yin aure ba sai da ta cika shekaru talatin a duniya. A lokacin kuma maneman suka ce basayi don tun samari suna zuwa tana korarsu har suka daina kowa ya daina kulata. Hankalinta ne yai masifar tashi ganin tana shirin shekara talatin da doriya babu miji. Sai dai tulin turawa nikuma tasan halina babu yanda za’ai na yarda ta auri wanda ba musulmi ba. Wannan damuwar ta saka a ranta gabadaya ta rame ta bushe ta daina walwala. Tun abun bai damuna har ya soma don dagaske takeyi. Ta aje aikinta ta daina futo ko’ina kullum sai tunanin. Kwatsam Allah ya hadamu da kai a sanadin Farida da ke fama da matsalar bari ka dora ta akan medication har Allah ya sanya ta haifi twins dinta.” Yaja numfashi mai nauyi sannan ya sake kasa da murya cikin rauni yaci gaba. “Mahmud tunda Safna ta ganka Allah ya jarabce ta da kaunarka.”
A sukwane Mahmud ya dago cikin kaduwa da firgici da tsananin mamaki da tashin hankali yana kallon Engineer.
Expression din da Eng ya gani akan fuskar Mahmud shine ya sage masa guiwa ya kuma shiga tsoro da zulumi amma duk da haka bai yi shiru ba.
“Mahmud lokacin da Shukra take gaya mana bamu dauki zancen da muhimmanci ba sai da Safna tazo ta sakani a gaba tana kuka ita lallai kai kadai take so. Tun ina mata nasiha ina kwantar mata da hankali har ta kai ta kwanta bata da lafiya. Babu yanda bamuyi mu shawo kanta ba mun gaza. Kullum daga kuka sai kwanciya. Ta koma aikin nata ma ya gagara. Ban shiga tsoro da fargaba ba sai da ta fara wani irin ciwon kirji muka dauketa mukaje asibiti. Likitan ya tabbatar mana da cewa idan bata bar damuwa ba lallai ciwon zuciya na gab da kamata. Hankalina yayi bala’in tashi domin ji nake idan wani abu ya samu Safna bazan taba iya yafewa kaina ba. A karshe nayi tunanin nayi kundunbala na nemeka na gaya maka amma tsoro da shakkar yanda zaka kalli zancen yake hanani. Nayi kokarin sanar maka ya kai sau hudu amma sai na kasa. Sai wannan lokacin nayi shahada Mahmud. Amma duk da haka ba wai inaso na tilasta ma bane, kada kayi abinda zaka takura kanka Mahmud idan bata yi maka ba ka gayamun bazan damu ba. Amma atleast nasan nayi kokari akan wannan al’amari. Kada ka dauka wai don Safna ce tawa nayi son kai dayawa, kaima naji tarihinka naji komai game da rayuwarka, naji yanda ka rasa matarka da dawowarka kasarnan da kuma rufe babun soyayya da kayi a rayuwarka. Na tausaya ma matuka sai dai hakan ba zai hana na baka shawarar cewa ka daure kayi aure ba. Ba don inaso ka auri Safna na kuma ba sai ita nake nufin ka aura ba! Mahmud duk wacce kasamu ko baka sonta kamar yanda kakeson marigayiya ka daure kayi aure domin farin cikin mahaifanka. Su iyaye daraja ce da su Mahmud ba zaka tana gane muhimmancinsu ba sai lokacin da ka rasa su.”
Gabadaya zufa ce take karyowa Mahmud duk sanyin da ke ratsawa. Kansa yayi wani irin nauyi gabadaya tunaninsa ya tsaya cak. Komai na duniyar ya dauke masa wani irin yanayi yake ciki wanda ba zai iya fassarawa ba a dalilin famo masa tsohon mikin da yake cikin ransa da Eng yayi. Mikin da yake tunanin ba zai goge ba har ya koma ga Ubangiji.
Cikin sanyi Eng ya dafa kafadar Mahmud yace “don’t worry Mahmud, kada ka tsanantawa kanka! Take everything easy kayi tunani a hankali ka nutsu. Ko text ne ka iya yimun daga baya. Ko daya kada kayi tunanin ka bata mun ko ka munana mun don kaki karbar wannan abu Mahmud. Nima a dole nayi ma wannan maganar domin wani nauyi ne mai girma a kaina wanda nake jin dole na sauke shi. Alhamdulillah nayi iyaka kokarina akan lamarin Safna na kuma barwa Allah komai shine zai futar dani daga wannan qangin. Ka tashi ka wuce kada dare yayi ma.”+
NIGERIA
Karfe shida na safe na bude idanuna ba dora su kan agogon dakin. Addu’a na karanto tare da mikewa zaune raina fari sol da murna da annashuwa. Mikewa nayi na yaye labulayen dakin haske ya keto ciki yana karamun wani farin ciki. Yau babbar rana ce a wajena domin mun kammala karatun secondary lafiya yau zamuyi graduation. Wayar Aisha na soma amsawa inda tace mun tana isowa zuwa karfe bakwai sannan na futa kitchen na futo da cake dina mai hawa biyu da na bata lokaci akansa jiya na hada wheaped cream na soma decorating dinshi. Sai da naga yayimun dai dai yanda nake so sannan na mayar dashi fridge na wuce dakin Dada muka gaisa. Ita ta soma tayani murna a yau ta kuma yimun addu’o’i akan rayuwa ta gaba.
Ina cikin breakfast Aisha ta iso da katuwar troley dinta ta zauna muka karasa tare sannan muka shige dakina.
Wanka na fada don ita tayi nata tun a gida. Ina futowa naga bakuwar tawa ta iso wato “GLAMDECK” make up artist din da Imamu yace zai turo mun tayi mana kwalliya. Cikin far’a na isa gareta muka gaisa. Sai tace bari ta soma da Aisha kafin na shirya.
Karfe tara aka kammala mun tawa kwalliyar wadda za’a kira da “simple glam” ko “nude look” babu abinda zaifi daukar hankalinka irin kalar fatata wadda ta na dinga baiwa extra care ta hanyar amfani da face mask mud mask da kalolin toners masu inganci don wannan rana. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu na futo fiye da tunanina. Sanye nake cikin gown wadda ta tsaya iya kwaurina mai dige digen black and white samfurin “Dior” sai na dora bakar graduation gown din kai. Gabadaya yala yalan gashina a gadon bayana na zubo dashi yana sheki. Na dora hular akaina ta zauna cif. Siririn yarin kunne na ainihin diamond sai kyalli yakeyi yana haska fuskata. Irin sarkar ce sak a damtsen hannuna da idon sawuna na kafar dama. Hannuna na hagu kuma agogo ne silver na “Kalvein Klein” sai kwalliyar tawa ta zama very classy. Ita kanta mai kwalliyar sai da ta tace “tabarakallah”
Lokacin da na tsaya a gabanta ina murmushi. Tayi mun pics masu kyau sannan ta tafi. Ya Sadik ya daukemu zuwa wajen taron da alkawarin anjima zasu taho gabadaya.
Karfe shadaya na safe tuni hall din ya cika taf da baki daga kowanne fanni. A lokacin ne kuma aka soma raba kyaututtuka ga dalibai a ranar ne amintar mu ni da Aisha ta tabbata domin idan aka kira best in science subject naje na karba toh ana zagayowa Art subjects ita zata mike. Ihu, tafi, mun sha su a wannan rana. Daga bisani head girl tazo tayi speech dinta aka ci gaba da gabatar da taro cikin tsari.
Bayan mun futo ne muka soma daukar hotuna da su Mami da Umman su Aisha da su Ya Sadik dukanmu cikin tsananin farin ciki. Saidai lokacin da muka tabbatar yaune final mun gama da zaman tare a makaranta sai muka barke da kuka. Tun ana mana dariya har muka basu tausayi suka shiga rarrashinmu. Dakyar babansu Aisha ya sata a mota suka tafi nikuma muka tafi da Mami gidanta. Sai bayan na dauko wayata ne naga tarin messages din Imamu na fatan alkhairi da tayani murna. Yaci burin halartar wannan rana amma tafiya ta taso mishi zuwa Paris dole ya tafi.
TWO MONTHTS LEAP
Zuwa yanzu alakar mu tayi matukar karfi da Imam babu wanda bai san tsakanina da shi ba da kuma irin son da nake masa duk kuwa da yanda nake kokarim boye hakan a fili. Yanayin aikinshi bai bari mu kasance koda yaushe sai dai kullum cikin kirana a waya yake da turo sakonni na so da kauna da sanyaya zuciya. Ba shakka Imam is a heaven sent. Domin duk wani buri da nake da shi akan mijin aure ya hada su. Matsaloli na da Imam guda biyu ne. Na farko matarshi da nake burin nasan wani abu a kanta shikuma yaki yayimun cikakken labari akan hakan nikuma jin kaina ya hanani yi masa tambaya a kanta kai tsaye. Na biyu kuwa shine banga Dada da Mami suna dokin da nayi tsammani zasuyi idan hakan ta faru ba kuma bansan dalili ba. Hakana Aisha aminiyata na lura ko zancen Imam bataso yayi tsayi a tsakaninmu. Wannan damuwoyin kadai nake fuskanta bayan haka bani da kowacce irin matsala.
Ana cikin haka iyayen Imamu suka zo tambayar aurena wajen su Daddy aka kuma amsa musu tare da bada izinin zasu iya kawo kudin aure kowanne lokaci. Daga ni har Imam din murnar mu ba zata lissafu ba. A ranar ne kuma ya gayamun zamuje na gaishe da Mamanshi domin ta matsa lallai tana so ta ganni. Cewa nayi ya tura Ya Sadik ya gayawa Dada don nikam bazan iya ba. Ina daki ta kirani ta gayamun cewa jibi na shirya zamuje gidansu Imam na amsa cikin ladabi na tashi na koma daki.
Mami na dau waya na kira bugu daya ta dauka. Bayan mun gaisa na dora da cewa “Mami yanzu ya Dada ta kirani take gayamun wai Imam ya turo ya Sadik ya gaya mata zamuje gidansu Mamanshi tana so ta ganni.” Shiru tayi na seconni sannan tace “ita Dadan me tace?” Nace ” cewa kawai tayi na shirya zamuje jibi” Mami ta sauke ajiyar zuciya muryar ta ta kara sanyi tace “ok.Allah ya nuna mana zan aiko miki kayan da zakiyi amfani dasu” jikina a sanyaye nace “toh Mami nagode” haka mukai sallama a sabule. Cillar da wayar nayi ina tunani. Menene yasa Mami bata dokin aurena? Meyasa? Meyasa jikinta yake sanyi take sauyawa a duk lokacin da hirar Imam ta shigo? Rashin sanin amsar tambayata ya sanya ni damuwa matuka domin ba haka nakeso Mami ta dau al’amarin ba. Inaso naga tsananin murnarta da farincikinta. Wayar da na cillar na sauka daga gadon na dauko na danna lambobin Aisha bugu daya itama ta dauka.
“Aisha jibi zamuje gidansu Imamu din Allah kizo gida da wuri” shiru kamar ba za tai magana ba sannan tace “Allah ya kaimu, Insha Allah Zanzo”
Kaina na dafe cikin tsananin bacin rai! Itama Aisha irin sanyin jikin Mami nakeji a tare da ita. Na rasa dalilin da ya sanya Aisha bata sakewa muyi maganar Imamu kuma ko da wasa ita bata sako zancenshi idan muna magana. Kasa hakuri nayi nace “Aisha wai me ke faruwa ne? Gabadaya bakwa nuna murna ko doki akan alakata da Imamu. Daga Dada, Mami har ke bakwa farinciki kamar yanda nake tunani ko dai bakwa sona da Imam ne? Ko yana da wata matsala ko aibu da bakwa so wanda kuka gagara sanar dani?” Cikin shaking voice Aisha tace “haba Zara ba haka bane wallahi…idan da akwai wani abu ai kinsan dole za’a sanar da ke kuma da yana da wani aibu kinsan su Daddy ba zasu amince da shi ba ko? Nidai Zara ganin abun nake kawai kamar mafarki mun rabu zan tafi makaranta zakiyi aure shikenan rayuwa zata sauya mana”
Duk da ban karbi uzurin da tazo dashi 100% ba na dan samu relief. Amma lallai inaso nasan menene a cikin ran su Mami da Dada da yake sagar musu da guiwa akan wannan lamari. Mun dan dade muna hira daga bisani mukai sallama na kira Ya Nuratu sai dai wayarta bata shiga. Na koma gadona na kwanta ina tunani duk raina babu dadi. Da naga tunanin na neman yin yawa sai na makala earpiece a kunnena na nemo kira’ar Juhany cikin Surat Yusuf na soma ji ina bi a hankali. Take wata nutsuwa ta dinga shigata raina yana sanyi bansan lokacin da bacci ya lalubo ya saceni ba.
Ranar asabar da yamma nida Aisha ne a dakina tana tayani shiryawa cikin kayan da Mummy ta aiko mun da su jiya da daddare.
Leshi ne mai tsananin kyau da tsada fari sol mai ratsin peach da gold. Style din simple skirt and blouse ne sai wani yadi mai shara shara da akai ado dashi a jikin wuyan rigan da hannun da wasu totoci.
Fuskata tas da ruwan hodar “merrycay” na fente lips dina da pink din jambakin “Mac” da saitin gold dina kirar “Dubai” nayi amfani. Na yafa mayafin kayan peach. Takalmina da jaka gold duka samfurin “Michel kors”
Nayi kyan da nake tunanin kamar ban taba yin irinsa ba. Don ba kasafai nake kwalliya mai nauyi haka ba idan ba wani occasion zan halarta ba.
Karfe biyar dai dai Imam yayi parking a cikin harabar gidanmu ya ciro wayarsa ya danna lambobina ina gaban Dada tana mun addu’a da nasihar cewa na kula na kame kaina wayar ta soma kara.
“Shine yazo?” Dada ta tambaya! Nace daga kai a sanyaye domin jikina ya fara sanyi ganin dagaske fa shirin aure nakeyi.
Har bakin mota Aisha ta rakani.
Tunda muka nufo motar yake kallona with alot of feelings acikin idonsa.
“Bestinmu ba zaki rakamu ba?”
Abinda ya soma fada kenan yana kallon Aisha! Murmushi tayi tare da cewa “a’hh wa yake shiga tsakiyar masoya ai sai kun dawo kawai…ka isar mun da tawa gaisuwar!”
Shima murmushin yayi yace “au hakane?” Ta gyada kai tana murmushi.
Ina daga gefe ina kallonsu…. abubuwa na yawo a raina. Duk lokacin da Imam da Aisha suka hadu sai na dinga jin kamar akwai wani boyayyen al’amarin da kowanne yake kokarin boyewa akan fuskarshi….sannan basa gajiya da magana ko don halinsu daya? I dont know! Wata zuciyar tace “kishi?”
Nooo! Ba kishi bane! Bazan taba zargin Aisha akan Imam ba. It cant be. Nayi maza na kawar da wannan tunanin acikin raina. A hankali na dago na dube shi jin rufewar kofar motar Aisha na daga mana hannu har muka futa daga gate din.
Murmushi yayi mun mai sanyaya rai. Nima na mayar masa tare da sunkuyar da kaina. Yana sanye cikin kaftan ruwan toka wanda ya amshe shi sosai. Muna tafiya gabana yana faduwa babu wanda yace da wani kala. Na lura yau kamar akwai abinda yake damunshi. Ya rage magana sosai.
Lokacin da muka iso Asokoro kirjina ya tsananta bugawa har sai da ya dubeni yace ” ki nutsu Zarah,,kisa a ranki kamar kamar gidanku zakije”
A hankali na daga masa kai. Kafin nayi magana har maigadi ya wangale gate din tafkeken gidan
Bayan yayi parking ya bude ya futa sannan ya zagaya ya budemun na futo a hankali.
Yana gaba ina biye da shi har muka iso babbar kofar gidan ie.the main door. Zai danna bell kenan aka bude kofar.
Wadda ta bude kofar photocopyn fuskar Imam ce sai dai ita ba fara bace tas kamar shi. Cikin murna da far’a mai yawa ta rungume ni tana cewa “You are welcome Zara!come in”
Taja hannuna cikin tsararren parlorn da ya kawatu cikin Formal setting. Sai da muka isa wajen tangama tangaman royal kujerun da suka kwarzanta falon ta saki hannuna tare da cewa “zauna Zara. Feel at home plaease! bara na yiwa Mummy magana” na amsa mata cikin murmushi. Tana tafiya Imam ya dubeni yace “Yasmeen kenan yar’auta lastweek ta dawo daga school hutu” girgiza kaina nayi cikin yabawa da kirkinta. Zanyi magana kenan wata yar gajeriyar chinese cikin gajeran skirt da farar shirt ta shigo hannunta dauke da tray dake makare da kayan tarbar baki na girma ta aje a side table dina tare da risinawa “good day ma’ you are welcome” na mayar mata da murmushinta na amsa ta wuce ta tafi.
Imam ne ya taso da kansa ya zuba mun lemo a cup ya miko mun sannan ya wuce gaban tangamemiyar curved TVn da ke zaune kan wani shegen royal tv stand ya sauya channel zuwa MBC Bollyhood. Kallona yayi yace “ina zuwa” na girigiza kai shikuma yabi hanyar da Yasmin tabi ya shige cikin gidan.
Mintina wajen goma ina zaune har na fara gundura da gidan ina tunanin inda suka shiga suka barni ni kadai a matsayina na bakuwa. Sautin takun talkami na dinga ji karas karas! Ana saukowa daga bene nayi maza na aje kofin lemon na gyara zamana da zaman mayafina a kaina. Can sai ga wata farar mata kyakykyawa wadda kallo daya zakai mata ka gane itace mahaifiyarsu Imam ta iso cikin tafiya ta isa da ji da kai da kasaita. Fuskar nan a murtuke babu far’a sai dai kyau kamar aljana. Tana sanye cikin shigar da ta bayyana tarin arziki da alfarmar dukiyar da take ciki. A nutse ta isa kujerar dake saitina ta zauna sannan tace “sannunki da zuwa” cikin ladabi na sulmuyo daga kujerar da nake kai na soma gayar da ita. Ta amsa babu yabo ba fallasa domin na gane rashin far’ar a jininta yake ba kamar yayanta ba. Sannan ba tace na koma kujerar na zauna ba kamar yanda nagartattun manyan mutane suke yi idan aka girmama su. Don haka na sake takura sosai. Cikin muryarta mai fadar da gaba ta sake cewa “a wanne unguwa kike ne?” Nace “muna Gwarinpa” ta sake cewa “ke yar gidan Alh Ahmad Lamido ce ko?” Na sake kasa da kaina nace “eh Uncle dina ne” cikin mamaki tace “au ba shine babanki ba?” Sosai tambayar ta bani haushi domin yanayin da take yinsu cikin raini da jin kai! Zan bata amsa kenan akayi sallama. Matar da ta shigo itama kamarsu daya sai dai ita mai far’a ce da son wasa don tana shigowa ta fara cewa “la la ba dai bakuwar ta rigani zuwa ba Imamu!” Har gabana ta karaso ta dagani ta mayar dani kan kujerar tana “Masha Allah Zara” cikin tsananin mutunci da karrramawa. A kunyace na gayar da ita wani abu kuma sai naga kamar na santa a wani waje ko kuma me kama da ita ce bansani ba. Itama wani kallo takemun kamar na son tuna wani abu kafin tayi sauri tace “zara ko dai kece Zaran Hajiya Zainab?” Cikin mamaki nima na daga mata kai ima cewa “eh mamana ce” nan da nan murnarta ta karu ta soma salati tana al’ajabi.
Mamansu Imamu ta kalleta tace “Zeenah lafiya dai? Kinsan Mamanta ne?” Cikin far’a tace “Yaya kema ai kinsanta. Zainab fa classmate dina a St Luis” cikin mamaki itama Maman ta sake kallona tace “yanzu wannan yar Zainab ce? Ikon Allah! Ashe yar har ta girma haka” Zeena ta dafa kafada ta tace “haba Yaya ai shekarun da yawa. Girman dan mutum ba wuya!baki sanni ba ko Zara?” Murmushi nayi na sunkuyar da kai! Tace “ko da yake ba’a wajenta kike ba shiyasa! Ina kuwa Dada?.” Nayi murmushi nace “tana nan kalau tana gida” cikin zakuwa Mamansu Imam ta sake tambayar Zeena “Zeena ita Zainab din ba Alh Ahmad Lamido ta aura bane?” A nutse ta kalleta tace “a’a kaninshi ta aura. Ita Zaran ai yanzu a hannun Alh Lamidon take tare da kakarta tun bayan rasuwar mahaifinta.” Hakan bai ishe ta ba ta sake cewa “ita wanene babanta?” Na lura dukansu basa jin dadin yanda take tambayar da alama kuma halinta ne hakan. Zeena gyara zama tayi ta kalli yayarta sosai tace bari kiji.
” mahaifin Zara kanin Alh. Ahmad Lamido ne uwa daya uba daya. Mahaifinta Shine El-Yakub Lamido former Governor of Adamawa state, kuma Senate President of Nigeria har rasuwarsa. Yana kan kujerarsa ya rasu!” Cikin tsananin mamaki ta dube ni ta dubi Zeenah tace “what? El-Yakub dai wanda nasani? Au kina nufin El-Yakub dan uwan Alh Ahmad ne?” Gaba daya ta rude! Murmushi tayi da wani smirk a fuskanta tace “kwarai kuwa Yaya uwa daya uba daya ma kuwa. Kuma zaki mamaki idan kika gane Zainab din Mamanta itace dai me Zara Couture ko? One of the mostsuccessful fashion designer a Nigeria” abun zai baku dariya yanda Maman su Imamu ta rude tana mamaki. Sai yanzu na gano halinta. Wato ita irin mutanen nan ce da kudi ya tsonewa ido basa ganin kowa da gashi sai mai kudi. A tunaninta ni yar Daddy ce da nace mata bashi bane babana ranta ya baci don bataso danta ya auro wadda iyayenta ba wasu bane a kasar nan! Wa iyazu billahi da mutane masu irin wannan tunani. Nan da nan ta saki fuskarta ashe wai har dariya ta iya! Ikon Allah! Ikon gaske! Ni dai gabadaya bata kwanta mun ba. Halinta bai bani sha’awa ba don haka jikina yayi sanyi kalau. Muna zaune ana hira har akai sallar magrib. Yasmeen ta jani dakinta nayi sallah muna zaune muna dan hira Imam ya shigo yace na taho mu tafi. Muka taso.
Har bakin mota A. Zeena da Yasmeen suka rakoni da manyan ledojin M&S Yasmeen ta bude mun kofa na shiga na zauna suna ta daga mana hannu har muka bar farfajiyar gidan.+
STORY CONTINUES BELOW

Sooo Zara yanzu hankalinki ya kwanta?” Imam ya tambayeni cikin tsokana. Murmushi kawai nayi a raina ina tunanin halin Mummyn tashi wanne iri ne. Sai kana da kudi zata karbeka kenan? Gabadaya sun fita kirki sun fita son mutane sun fita sanin ya kamata har yayan nata.
Bayan na dawo ne muke waya da Mami cikin farinciki tace “Zara ashe Imam dan sister din Zeenah ne? Yanzu muka gama waya da ita” cikin murmushi nace “eh Mami nima sai da ta fada na tuna hotonta da nake gani a wajenki da labarinta da kike bani” dariya Mummyn tayi cikin murna tace “Zara sai yanzu hankalina ya kwanta…sai yanzu na samu nutsuwa domin fatana shine kije gidan da za’a mutunta ki a rike ki da amana su Zeenah mutanen arziki ne wallahi masu mutunci da sanin ya kamata” wani murmushi nayi zuciyata fess da wani irin sanyin dadi nima sai yanzu na samu nutsuwa da naji Mamin ta karbi batun da farinciki har karkashin zuciyarta. Mun dade muna hirar gidansu Imam kafin muyi sallama zuciyata cike da annashuwa.
Bayan sati biyu aka kawo kudin aurena daga gidansu Imam da alkawarin aure bayan watanni takwas wato december karshen shekara. Sannan sun nemi da na ci gaba da karatuna babu matsala tunda dai abinda Dada bataso din a shiga makarantar sannan ayi aure toh ga mijin an samu an saka rana. Don haka ta amince. Bazan taba iya bayyana farincikina da jindadi game da wannan al’amari ba haka ma Mami. Dada dai har yau babu wani doki da take yi sai dai kawai tace Allah sanya alkhairi
Saidai kwanakin nan gaba daya Imam ya sauya kamar akwai abinda yake damunsa duk da ko kadan bai rage kulawarsa da kauna a gareni ba. Da nayi masa magana sai yace babu komai kawai wasu abubuwane suka taso mai ta fannin aiki. Abu daya na kasa ganewa kuma nake tsoron tambaya! Shin ina matar Imamu? Ina yaranshi? Banji wani yayi maganar Imam na da aure ba! Kuma banji ance yana da yara ba bayan kalamansa da idanuna sun tabbatar mun da hakan!
Cikin lokaci qalilan na samu admission a Nile Turkish University zan karanta English studies.
Ranar da na fara zuwa school bazan bayyana farin cikin da na tsinci kaina a ciki ba illa dai kawai nayi tayi wa Allah godiya. Bayan mun kammala lecture wajen shabiyu na rana na futo daga lecture hall kenan mukai karo da wata yarinya jakata ta fadi tayi maza ta dauko ta mikomin…. a lokacin na daga ido na kalleta. Kyakykywar gaske ce fara sol kamar balarabiya. Da murmushi akan fuskarta tace mun “I’m sorry..” nima na mayar mata da murmushin nace “nagode”.. “Sunana Ihsan Gumel nima yau nayi joining class” lokaci daya naji hankalina ya kwanta da ita. Nace “Nikuma Zara El-Yakub nima yau na fara lectures”.
Murmushinta ta fadada ta miko mun hannunta tana cewa “nice meeting you Zara” na mika mata nawa hannun nima ina murmushi….daga nan tare muka wuce capteria duk yanda naso ta bar biyan kudin abincin da mukai order bata yarda ba ita biya kudin komai muka gama muka koma class. “The lectures were extremely boring and annoying…i couldn’t understand anything” malamin ma gabadaya bana gane me yake cewa kawai burina a tashi na tafi gida. Sai karfe hudu muka kammala muka futo tare da Ihsan.
“Zan jira azo daukana ne” ta fada tana kallona. Nace mata “ohh nikuma da kaina zan tafi. Ko zanyi dropping dinki sai na wuce?” Cewa tayi “babu damuwa?” Na girgiza kai nace “nooo babu komai wallahi.”
Muna futa daga cikin gate din nake tanbayarta ina zamuyi? “Asokoro” ta bani amsa. Daga nan na dau hanya muna yar hira har muka isa tana nuna mun hanya. Gabana ne ya fadi ganinmu a kofar gidansu Imam. Makota ne daga gidansu sai na su Imam. Bayan na aje ta mukai musayar number waya sannan tace tagode ta shiga gida nikuma na dau hanyar gida.
Ina shiga gida Aisha na shigowa itama. “Yan makaranta tell me how was it?” Ta fada tana tsokana ta.
Sai da na cire duka kayan jikina na daura towel sannan na dubeta nace “it was sooo boring iswear….karon farko na tsani lecturer din farinshi yayi mishi yawa kamar zabiya ga wani turancinsa kamar yartsana”
Aisha ta kyalkyale da dariya tace “ke dai Zara baki da gwani komai na rayuwa ba zaki rasa yanda zaki ki kushe shi ba” tsaki nayi nace ” ke dai ba zaki gane bane wallahi amma ba wani dadi fa”
Cewa tayi “zaki saba ne a hankali zaki soma jin dadin komai” nace “hakane” mun dade muna labarin makarantar kafin na shiga nayi wanka na futo. Sannan muka shiga kitchen tare mukai abincin dare. Baba Rabi taje kano. Sai wajen karfe tara Driver gidansu yazo ya dauketa don ba’a barinta tayi driving da dare.
A hankali na soma sabawa da makaranta na fara jin dadin karatuna sannan ina gane komai…ga taimakon Ihsan domin ita irin mutanen nan ne da ake kira gifted(yan baiwa) nikuwa ina cikin second class ne wato wadanda ke ganewa bayan an musu bayani sannan su zauna suyi nasu karatun don karin fahimta. Duk abinda ban gane ba ita take fahimtar dani cikin ikon Allah sai karatun ya zamar mun me sauki sosai.
Mun shaku da ita cikin lokaci kalilan domin na fahimceta tsaf ta samu tarbiyya me kyau duk da futowarta daga gidan hamshakan masu kudi kuma ita kadai ce ga iyayenta tace mun Mamansu barinta goma kafin Allah yasa da addu’a da taimakon likitoci cikin ta ya zauna. A America aka haifeta. Tsananin wahalar da maman nata tasha ya sanya aka juya mata mahaifar gaba daya. Don haka idan kikaga yanda ake ji da ita a gidansu abun zai baki mamaki. Yan asalin Gumel din jihar Jigawa ne aiki ya kawo mahaifinta garin Abuja.Mamanta kuma likitar yara ce tana aiki a National hospital. A yanzu haka saura wata biyu aurenta da Jameel dan gidan Former Vise President.
Hello! Its been long!
Sooo people are asking me why everyone in the story is rich?lolz.
Well, akwai wani hashashe da ake akan masu kudi wanda kuma ba haka yake ba. Na farko wasu na tunanin idan mutum na da kudi toh bashi da matsala baisan kuncin rayuwa ba baisan tashin hankali ba. Wanda kuma ba haka bane! Komai kudinka komai arzikinka akwai ta inda Allah yake jarabtarka ta yanda zakaji rayuwa tai ma zafi tayi ma kunci. Toh irin wannan matsalar na hasko a wannan labari.
This is just the beginning of the story akwai abubuwa masu tarin yawa da zasu biyo baya masu dadi da marasa dadi wadanda kuka zata da wadanda baku taba tunani ba!
Ku dai kuci gaba da karatu! Thank you!!