HAUSA ARAB CHAPTER 10
A wannan lokacin ba zan iya tashi kafafuna basu lankwashe ba, bazan iya mikewa ba tare da support ďin wani abun ba, don haka na soma rarrafawa kamar gurguwa har na isa gaban shi, idona a kasa, na soma magana cikin shaking voice
“Allah yayayyaaaaa baaaaaaka hakuri! In…….shaaaaa Allahu ba zan saaake ba!”
He answered with the most soothing voice.
“It’s ok! Babu komai!”
Sai kuma na tsinci muryar shi yana cewa
“Dada kiyi hakuri”
Ta kuwa kwaďa mi shi harara ta mike tana cewa
“Dallah ja can! Wani solobiyo da kai! Kana kallo zata sa kafa ta futa kana zaune kamar wani gunki! Ku haka kuka ga anayi?
Toh ban lamunta ba! Idan kuma a cikin darusan bokon naku wannan shirmen dai dai ne toh ku dinga zubar da shi a gabana. A haka gaku maza har maza amma duk taran ýan nanaye ne…”
Sai da ta shige ďaki sannan muka samu kunnen mu ya huta da hargagin ta.
Mami ce ta soma tashi ta shiga ďakin ta, komai kurillar ka ba zaka gane yanayin da zuciyarta take ciki akan fuskar ta ba.
A.laila ta tashi itama ta shige ďaki don yin alwala, Ya Nuratu ta ďauki Asad ta goya shi taja hannun Ihsan wadda ta koma kamar kazar da aka jiqa da ruwan sanyi suka shige ciki, sai lokacin ne kuma nayi realising su Ya Omar basa falon!…….
“Zara”
Ya Mahmud ya kira sunana with his most beautiful voice.
Ban amsa ba kuma ban kalle shi ba.
“Kije kiyi sallah zan je masallaci na dawo”
Sai da ya futa sannan na samu na mike cikin rangaji na shiga dakina na kullo kofar sannan na samu damar fashewa da matsanancin kukan da nake ta faman riritawa kada ya taho.
A tsakar ďakin na cire duka kayan jikina ina wurgi da su ďaya bayan ďaya kamar su suka yi mun laifin sannan na shiga toilet naci gaba da kukan a ciki. Sai da naji masallatai sun idar da sallah sannan na daure nayi alwalar na futo na saka dogon hijab nayi sallah.
Ina wuridi ina hawaye, sai dai a maimakon ďazu da nake jin zafin maganganun Dada, yanzu laifina nake karantowa dalla dalla ina ganin rashin dacewar abinda nayi. But I’m new to the system, me yasa Dada ba zata yi mun nasiha ba? Me yasa ta zabi yi mun wannan cin zarafin a gaban kowa da kowa ciki har da aminiyata wadda zamu tafi gidan bikin tare?…….
Sai amsa tazo mun!
It was all because of Him! Yes!
Saboda Ya Mahmud ne, Dada na using any slight opportunity da ta samu ta nuna mi shi cewa yana da daraja da mutunci da kuma kima a wajenta da family bakiďaya.
Tana son ta goge mi shi tunanin da yake yi ya gane cewa shi ba bare ne a cikin mu kuma ba cin arziki yake ba, tana so ta dinga nuna mi shi cewa har yanzu matsayin sa bai chanja ba kuma abubuwan da tayi mi shi bata yi su ne don ta tozarta shi ko ta wulakanta shi ba, nagane duka take taken Dada akan Ya Mahmud tun daga ranar da ta shirya taro a kan shi.
Zan iya bugar kirji nace ko su Ya Sadik basu da matsayin da Ya Mahmud yake da shi a wajen Dada. Kuma abinda tayi tayi shi ne for his own sake, for his own good! May be ba lallai mu gane yanzu ba, amma a gaba zamu fahimci dalilin da ya sanya ta tona asirin asalin Ya Mahmud a gaban kowa da kowa.
Bayan zuzzurfan tunani sai naji hankalina ya kwanta, zuciyata tayi tas! Nasan Dada nasan kuma son da take mana, har abada alkhairanta gare mu ba zasu bamu ikon kallon kuskurenta ko sharrin ta ba, ko da zata yi ďin! Faďa da zafi halinta ne, wanda ba za’a iya chanja mata shi ba, but I can safely say Dada has never means harm to anyone. Tana da kirki da yakana da sanin ya kamata kuma sau da yawa ta kan zabi bare ta ajiye nata saboda kawaici.
Mace ce mai gaskiya da tsayawa akan ta, komai tsanani, bata da tsoro ko shakka kuma bata ďaukar wargi ko raini.
Wasa yayi nan tayi can, don haka ne wanda bai fahimce ta ba sai yayi mata mummunan fassara, sai ka zauna da ita ka karance ta sannan zaka gano tana da unique qualities irin wanda mutane da dama basu da shi.
STORY CONTINUES BELOW

Ban gushe ba ina wannan lissafin da tunanin har naji zuciyata tayi sanyi! Na tashi na tsince kayan da na zubar na gyara ďakin sannan na goge fuskata da baby wipes na cire hijab ďin da na saka na mayar da doguwar rigar lace mara nauyi cream and purple na ďaura dankwali.
Jin ana kiran sallar isha’i ya sanya ni tsayawa nayi sallar sannan ďauko wayata na futo parlour! Babu motsin kowa sai karar Ac, sai na wuce kitchen na samu Baba Rabi tana hidimar abincin dare. Murmushi tayi mun sannan tace
“Uwar ďakina Allah ya huci zuciyar”
Na mayar mata da murmushin nima nace
“Ta huce tuntuni”
Muka yi dariya na soma taya ta aikin muna labarin abinda ya faru, tare muka haďa wajen cin abincin a tsakiyar falon, na koma kitchen ďin domin haďa chicken salad, kasancewar I’m on a diet kuma duka abubuwan da ta dafa ba dangin cina bane.
Ina kitchen ďin na dinga jin futowar su ďaya bayan ďaya, amma tuni Ihsan ta tafi inji Baba Rabi, nayi dariya da na tuna yanda Ihsan ta tsorata, I doubt idan ta taba ganin bacin ran Dada, shiyasa ta ruďe ta susuce ta gudu ba tare da sallama ba.
Kafin na kammala naji shigowar mazan sun zauna suna kiciniyar zuba abinci, na tabbatar saboda faďan Dada ne suka dawo, domin kada su tafi tace faďan da tayi ne ya kore su, babu abinda ta tsana irin tayi maka faďa kayi fushi, har ka futo fili ka nuna mata fushi kake yi, zaka gayawa aya zakinta kuwa don sai ka gwammace baka yi ba.
Nayi murmushi kawai na ďauki tray ďin da na haďa abubuwan da zanci na futo parlour trying my best na zama normal.
Ina futowar kuwa idanun kowa suka yo kaina har naji kamar na koma kitchen ďin, na san mamaki suke yi, mamaki suke da na iya futowa cikin su a wannan lokacin da ya kamata ace ina ďaki, ko ba kuka nake ba ina bitar tijarar da Dada tayi mun ina malelekuwa a gado.
Ganin zasu rikita ni sai na juya na koma can gefe da tray ďin nawa na zauna a gefen kujera kamar irin ýar bora ďin nan a gidansu.
“Taso ki dawo kusa dani”
Na tsinci muryar Dada a hankali.
Sannan na ďago na kalleta, itama ni take kallo, na mike a hankali na koma kusa da ita na ajiye kayan abincin nawa, sannan na janyo plate nayi serving ďinta na tura mata gabanta.
“Me yasa zaki ci salad shi kaďai?”
Ta sake yi mun magana, na ďan yi murmushi sannan nace
“Rage qiba nake yi Dada!”
Ta haďiye lomar da take bakinta sannan ta ďauki cup ďin da na cika mata da kunun gyaďa ta kafa kai ta shanye ta ajiye kofin tana yin hamdala. Sannan ta dube ki a tsanake tace
“Zahra’u”
Na amsa cikin fargaba
“Allah yayi miki albarka! Allah ya sanya alkhairi da albarka da arziki a cikin auren ki, ya baki ýaýan da zaki yi alfahari da su”
Sunkuyar da kaina nayi kasa ina tauna abincin a hankali zuciya na yi mun sanyi, domin duk ďan arziki yana fatan irin waďannan kalaman daga bakin iyayen sa.
Su A.laila ne suka amsa duka suna murmushi tare da mamakin halin Dada da kuma sha’awar irin mu’amalar da muke yi da ita. Ita dai Mami bata ce komai ba abincinta kawai take ci hankali kwance tare da Ya Mahmud a plate guda.
Bayan mun kammala ne Ya Sadik yayi gyaran murya ya soma magana a ladabce
“Dada Daddy yayi miki bayanin tafiyar mu Jibi?”
Ta gyara zama tace
“Yaya tafiyar take ne?”
Ya kaskantar da kai yace
“Yace ni da Manager mu same shi a Texas(Holland), sai yayi mana bayanin abubuwan da suka kamata ya bar komai a hannun mu ya wuce Riyadh, gobe da Yamma Ya Mahmud zai bi jirgin emirate zuwa Dubai suna taron likitoci na hukumar W.H.O, suna gamawa zai wuce Riyadh ya wakilci Daddyn a taron da zasu yi saboda zai riga Daddyn sauka a can! Bansan plans din shi ba bayan haka, amma ni daga Holland zan wuce Egypt ne mu taho da Anis tunda ban samu na rakata ba.”
STORY CONTINUES BELOW

Dada ta dubi Ya Mahmud tace
“Zaku daďe ne a Riyadh ďin?”
Ya kaskantar da kai yace
“Ina ganin ba zai wuce kwanaki hudù ba duk da har yanzu bai yi mun bayanin wanne irin taro bane, amma daga nan zan wuce Nayi Umra, kamar dai kwanaki goma nake so nayi a makkah da Madeena.”
Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta dubi Ya Omar tace tace
“Kakana fa? Sai ina?”
Murmushi yayi yace
“Dada ina tare da ku a Nigeria”
Tayi murmushin itama sannan tace
“Toh ba laifi! Allah ya kai ku lafiya, Allah ya bada sa’a! Nima naso zuwa umrar sosai amma tunda lokacin ganin likita saura wata ďaya sai na hakura kawai na tafi gabaďaya……”
Daga nan suka yi mana sallama suka mike zasu tafi. Dada ta kira Ya Mahmud da ke kokarin futa tace
“A ina kake kwana ne?”
Ya ďan sosa keya yace
“Ina Mississippi gidan Daddy”
Har zata yi magana kuma sai ta fasa tayi masa Allah ya kiyaye suka tafi! Da hannu ya kira ni na rangwaďar da kai na mike cikin jin nauyi na warware dankwalina na yafa nabi bayan su.
A parking lot na same shi yana buďe motar shi, tuni su Ya Omar sun futa daga cikin gate ďin sun tafi. Da hannu yayi mun alama na buďe gefen shi na shiga zauna. Shiru muka yi na wasu dakiku kafin nace
“Kayi hakuri da abinda ya faru, Allah yana kallon zuciya ta banyi hakan don raini ko wulakanci ba, wallahi na manta ne, abun bai zo kaina cewa I’m married now I need your concent…….”
Hannuna ya kamo dalilin da ya katse mun maganar da nake yi kenan.
“Look at me”
It feels very awkward and strange……
A hankali na ďago ina kallon shi, ya fara magana a tausashe
“Ni baki yi mun laifi ba, idan ma kinyi laifin toh bai wuce na kayan da kika saka ba da kuma ďan mitsilin gyalen da bai rufe miki komai a jikin ki ba……….
You are married, ya kamata kiyi kokari ki ďan gyara shigar ki, Allah baya so, nima bana so!…… idan zaki futa sau goma a rana in dai kina da uzurin yi a wajen bani da matsala, bukata ta kawai ki Killace jikin ki da kyakykyawar shiga Zara!…..”
Oh God! Today I’ve seen the jealous Ya Mahmud!! Nayi chuckling a hankali, amma kuma naji daďi! Rashin nuna damuwar da yake a kaina da lamarina ashe ba karamun bata mun rai suke yi ba, yau kam I feel married…….lolz!
Yes! I’m feeling like a married woman and I love the feeling!…
“Kina jina?”
Na dawo da nutsuwata nace
“Baka da matsala Ya Mahmud bazan kara ba, wannan ma kuskure ne kuma a maimakon ayi mun nasiha sai aka balbaleni da faďa”
Yayi murmshi yana kallon zoben hannuna
“Dada is just unpredictable! Kuna cikin wasa da dariya sai ta juye, a cikin wasan zaka yi rashin hankalin da zata dawo da kai cikin taitayin ka! But she is always right! Dada bata faďa akan rashin gaskiya……..”
Na katse shi da cewa
“Dada’s talk aside! Ina so na tambaye ka please”
Hannuna ya saki ya gyara zama sosai yana fuskanta ta tare da miko mun gabaďaya attention ďin sa, sai na tausasa muryata na soma magana
“Na daďe da gane cewa yanayin ka ya chanja kuma walwalar ka ta janye sosai, da farko na ďauka case ďin Mami ne, amma yanzu I’m sure ba shi bane, akwai wani abu da yake damun ka, damuwar kuma mai yawan gaske, wadda bata iya bacewa akan fuskar ka komai kokarin da kake yi ka boye ta.
Will you share your problem with me?”
Na karashe maganar a ďarare.
Ajiyar zuciya ya sauke kuma a take fuskar ta shi ta juye zuwa tsananin damuwar, idanun shi suka yi jajazur kamar gauta. Sai jikina yayi sanyi naji babu abinda nake so naji kamar damuwar ta shi.
“Ba zaka gaya mun ba?”
Ya tsura mun idanu sannan ya buďe baki a hankali yace
“I will share it with you……but as a husband and wife secret! Kin yarda?”
Nayi sauri na girgiza kaina, ba tare da na tsaya processing maganar ba.
A sanyaye yace
“Zara I really want to meet my Father! Ina matukar son na sadu da mahaifina Zara, I need him sooo much…..ba zaki taba gane yanda nake ji ba, zuciyata tana zogi da ďaci wasu lokutan na kan ji kamar na ciro ta na yar na huta da azabar da nake ji, wasu lokutan na kan ji kamar na shiga jirgi na tafi Lebanon nayi ta bi gida gida ina neman shi. Wani lokacin kuma sai naji kamar na mutu na bi mahaifiyata Zara!
Daddy and Mami are my world and my happiness, wannan matsayin na su yana nan kuma ba zai yi ko rawa a cikin zuciyata ba, kuma har abada ba zan samu wanda na shaku da su irin su ba, but Zara, I still need my biological parent! Mahaifiyata tayi mun nisan da bazan iya cimmata ba, sai dai nayi mata addu’a! Amma mahaifina fa? Tunanin yana nan raye ko ya mutu kawai yana sanyawa naji kamar kaina zai kwance, Zara a wannan family ďinne kawai nake da mutunci da daraja amma a wajen mutanen gari sunana mara asali! Marasa kara ma shegantani suke yi, and they are right! Idan ina da asalin a bayyana mana? It breaks my heart idan na tuna cewa watarana zamu haifi yara su taso ana yi musu kallon masu yankakkiyar nasaba da gurbatccen asali.
Zan iya jure komai amma zuciya ta ba zata iya jure jin sabon sunan da al’umma suka raďa mun ba…….
Daddy yayi mun alkawari zai nemo mun mahaifina amma shiru babu wani labari, kuma shi kan shi Daddyn na lura kamar tsoron binciken yayi, watakila saboda yana jin tsoro kada ya bincika ya tarar mahaifin nawa ya mutu ýan’uwan shi su ki karbata, watakila kuma yana tsoron kamar zai kwace masa ni.
Ni kuma tsoro nake yi Zara kada na makara……………”
Sai ya fara kuka, kuka harda shashsheka, irin kukan nan mai cin zuciya mai bayyana halin bacin rai da bakin cikin da mutum yake ciki.
Nima ji nayi inason yin kukan, amma ina so na karfafa mi shi guiwa, I want to be strong for him! Ina so na kwantar mi shi da hankali ya samu relief, domin yana cikin wata irin damuwa ne irin wadda babu mai magance masa sai ubangijin da ya halicce shi. Damuwa mai tsanani, mai tsananin gaske kuwa, irin wadda take ruguza mutum lokaci ďaya ko kuma ta dinga cin jikinsa a hankali har ta kai shi rami. Hakika kaddarar Ya Mahmud mai zafi ce kuma mai tsananin zafi da cin zuciya, sai dai muyi mi shi fatan Allah ya sanya ya cinye jarrabawarsa.
Barin shi nayi yayi kukan har ya gaji, domin a wasu lokutan fitar hawaye na sanyaya zuciya su nemo wa zuciya nutsuwa da relief!
Sai da yayi kukan ya gaji yayi shiru don kansa, na soma zaro mi shi tissue ďin da take tsakanin mu ina mika mi shi yana share fuskar sa da hancin sa sannan na saka hannu seat ďin baya na ďauko ruwa, duk da ba mai sanyi bane he needs it.Barin shi nayi yayi kukan har ya gaji, domin a wasu lokutan fitar hawaye na sanyaya zuciya su nemo wa zuciya nutsuwa da relief!
Sai da yayi kukan ya gaji yayi shiru don kansa, na soma zaro mi shi tissue ďin da take tsakanin mu ina mika mi shi yana share fuskar sa da hancin sa sannan na saka hannu seat ďin baya na ďauko ruwa, duk da ba mai sanyi bane he needs it.
Ya karba ya kafa kan shi ya dinga shan ruwan kamar ba zai bar shi ba, sai da na saka hannu na karbe robar sannan ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanu.
“Are you ok?”
Ya girgiza kai a hankali.
“Da farko ina so na tuna maka cewa kowanne bawa yana da tashi kaddarar kuma babu mahalukin da yake iya tsallake kaddarar shi! Wani tashi mai sauki wani kuma tashi mai zafi, ka gode ma Allah ka futo a cikin tsatson musulmai masoya Manzon Allah, sannan ka futo ta hanyar aure, ka girma cikin tarbiyyar addini ka samu Ilmin boko da na islama, ka samu makusantan da suke sonka, soyayya irin wadda zasu gwammace su rasa duk abinda suka mallaka akan su rasa ka.
Kace Alhamdulillah Ya Mahmud!”+
Idanun shi a rufe yace
“Alhamdulillah”
A sanyaye.
Naci gaba da cewa
“I don’t how you feel, kuma idan nayi kokarin saka kaina a matsayin ka ma sai naji zuciyata ba zata ďauka ba, which means kana da karfin ihmani da tawakkali, amma abinda nake so ka fahimta shi ne, wallahi tallahi komai juyin duniya Kai ďin mai daraja ne mai mutunci kuma abun so da alfahari a wajen waďanda suka san waye kai, ina da tabbacin har abada za ka ji kunya ba in har kana kan wannan tafarkin da kake kai baka sauka ba.
“Damuwa ba zata yi maka maganin matsalar da kake ciki ba sai dai ta illata ka, mafuta guda ďaya ce Ya Mahmud! Kayi addu’a! Kayi addu’a mai yawa, ina tabbatar maka da cewa zaka samu ko menene kake nema! Ka tattara komai ka mika shi a gaban Allah, ka bar mi shi komai ka koma ka zauna kaga abunda zai faru! Addu’a ba karya bace, ni shaida ce, na shiga hali mai tsauri da tsaka mai wuya, addu’a tayi mun rana kuma ta warware mun komai ba tare da yunkurina ba. So kaima ina baka shawara kayi addu’a ka mayar da sujjada mafi yawan ibadar ka, kayi wa Allah kuka fiye da kowa, ka yarda ka sakankance zai amsa maka kuma zai duba ka, I promise you will see a miracle! Nayi maka alkawari Ya Mahmud wallahi zaka haďu da mahaifin ka, idan har kaga baku haďu ba? Toh sai dai idan baka yi addu’ar ba……..
Addu’a tana saka abinda ba zaiyu ba ya yiwu, addu’a tana juya al’amari komai tsaurin shi, tana warware matsala komai cakuďewar ta, tana chanja kaddarar komai girmanta, kuma tana baka abinda ko duk duniya zasu haďu ba zasu iya tara maka ba………..
Ka koma ga Allah!.
Ka fuskanci Allah da wannan damuwar! Zai yaye maka……”
A hankali ya buďe idanun shi da ke kyallin hawaye ya dube ni, sannan yayi yalwataccen murmushin da hakoran shi suka bayyana! Ya buďe baki a hankali ya soma magana
“Thank you my darling wife and I look forward to your advice “
Zan mi shi magana kenan wayar shi ta soma ringing.
Yace
“Nuratu ce”
Sannan ya kara a kunnen shi
“Hello”
Tace
“Ya Mahmud Dada tace wai agogon motar ka da na wayar ku duk sun daina aiki ne? Idan tare zaku tafi wai ku kama hanya a kulle mata kofa”
Iyakacin abinda ta faďa kenan ta kashe wayar kit! Na tabbatar tana gaban Dada kuma itace ta karanta mata abinda zata faďa ta faďa ďin.
Tare muka sa dariya sosai har muna rike ciki……
STORY CONTINUES BELOW

“Take care of yourself Ya Mahmud and please ka daina tunani da damuwa!
Whenever you feel lonely just remember that you have a caring Mother, a protective Dad….and the most supportive wife……and they love you more than you could ever imagine!
Zan taya ka da addu’a kuma zan tsaya a kusa da kai a kowanne yanayi a kowanne zamani a kowanne hali…
I promise…”
Na balle hannun motar na zille ina dariya, sannan na mayar da murfin na rufe ina ďaga mi shi hannu.
Sai da naga futar motar ta shi daga gate sannan na kamo hanyar gida ina fargabar Hajjajuwa Dada! Sai dai kuma da na shigo ďin ban samu kowa a falon ba sai kwaramniyar Ac da ke aikin zukar wuta tana watso sanyi mai ratsa kashi.
Na lallaba na shige ďakina nayi wanka na dawo nabi lafiyar gadona na kwanta ni kaďai ina murmushi kamar wata shashasha, wani irin tunani nake mai daďi wanda ni kaina bansan dalili ba.
I can’t remember lokacin da na fara jin wannan abun, wanda nake tabbatarwa da kaina sunan shi “love”
Akan mutumin da kullum nake wa kallon ďan’uwan da muka haďa mahaifiya guda…….
Ina cikin wannan tunanin sai kiran shi ya shigo, nayi wani juyi na lalubo wayar na saka a kunnena
“Hello”
“Salamu alaik ya albee, ya rooh, ya azeezati, ya qurrati ain, ya habibal qalb…..”
Na tuntsire da dariya
“Me kenan Ya Mahmud?”
Shima dariyar yayi sannan yace
“Ba daďi sunayen naki?”
Nace
“Ko meaning ďin bansani ba balle na gane akwai daďi! Kaje gida lafiya?”
Ya sauke ajiyar zuciya yace
“Lafiya hayyan, har nayi wanka na kwanta a gadona ina tunanin maganganun da suka yi tasiri a gare ni fiye da kowacce magana a rayuwata! Ina yin addu’a ba zan ce bana yi ba, amma not with the energy ďin da ake bukata irin yanda kika gaya mun! Lokaci guda naji kamar an ansamun addu’ar tawa ma tun kafin nayi………
Allah yayi miki albarka”
Nayi murmushi
“Ameen! Ga ka ma ga best opportunity, zaka je Saudi! Ga madeena ga ka’aba Ya Mahmud say goodbye to your problems domin sun kusa barin ka, ko baka yi musu sallama ba sai sun tafi”
Yayi dariya yace
“Insha Allah Zara! Insha Allah”
Sai kuma yayi shiru, sannan yace
“Zara ina yin wani tunani amma kuma bansan me Dada zata ce ba, so idan mun haďu da Daddy zan mi shi maganar naji me zai ce”
Nace
“Wanne tunani kake yi?”
“Akan karatun ki Zara! Kina ta zama lokaci yana tafiya…… Ina son kiyi karatu sosai, it will help you alot musamman a wannan lokacin, idan baki tsaya yanzu kin fuskance shi ba kasawa zaki yi nan gaba! Amma ba zan iya gayawa Dada ba, sai dai Daddy! Wai meye ma dalilin ya sanya aka rike ki a gida bayan an gama auren anyi biki? Haka ake yi daman?”
Ýar dariya nayi sannan nace
“Ni ina zan sani Ya Mahmud! Nima maganar karatun tana cikin raina wallahi…..Ina da buri mai yawa akan shi, amma yanzu na fara tunanin hanyar da zan bi na taimakawa Mami a business ďinta….
Kwana biyu tayi rauni sosai, har kasuwancin nata yana kwanciya da kaďan kaďan, tana bukatar hutu da kwanciyar hankali, so idan son samu ne, na maye gurbin ta a office for a while, ina da plan akan brand ďin ta wanda nake tunanin zai sake farfaďo da shi ya bunkasa!
Amma bansan ta inda zan fara ba…….”
Cikin nutsuwa yace
“Kinyi tunani me kyau, nima ba’a son raina harkokin office ďinta suke tsayawa ba, kafin mu shiga maganar karatun kuma inaga abinda ya kamata mu fara yi kenan! Idan wannan ne zan samu Mamin muyi magana sannan nayi wa Dada magana da kaina! Na san ba zata ki amincewa ba………
Toh amma ke da ba mazauniya ba, idan kika fara lokacin tafiyar ki yayi fa?”
STORY CONTINUES BELOW

Nace
“Bangane ba! Lokacin tafiya ta ina?”
“Lokacin tafiyar ki matrimonial home ďin ki”
Nayi shiru ina tunani….
Wai bin shi zan yi can London kenan?
Ai ni ban ma taba zama nayi wannan tunanin ba
“Ko a Abuja kike so ki zauna?”
Nayi sauri nace
“Ba haka bane!”
“Toh ya ne?”
Nace
“Wannan maganar ku ce ni ba tawa ba. For now, ka fara zuwa kayi addu’ar ka ka samu nutsuwa sai mu fuskanci wata maganar kuma”
Daga nan muka ci gaba da hira akan abubuwan da suka shafe mu musamman case ďin Mami, anan ne kuma nayi mi shi bayanin abinda Imamu ya gaya mun yace shima sunyi magana ya sanar da shi, ashe wai har an tura wa Alhaji Muktar ďin sammaci daga EFCC, ana ta bincike, an kusa shiga court!
Bamu ankara hira muke yi lokaci yana tafiya ba sai da naji ana kiran sallah. Nayi wani salati na hantsila na tashi zaune
“Ya Mahmud ka san kuwa me nake ji a kunnena?”
Yace
“Me kike ji?”
Nace
“Kiran sallah ne fa? Sallar asuba! Ya Mahmud yanzu ba ka kallon lokaci ka bar mu muka kwana muna hira”
Yayi dariya kawai sannan yace
“Ke ina naki hankalin ya tafi baki duba agogo ba sai da kika ji kiran sallar? You were out of this world ko? Soyayya tayi daďi……….”
Nayi sauri na kashe wayar ina matukar mamakin yawan lokacin da muka ďauka tare, kamar fa yanzu muka fara magana, kamar yanzu ya kira.
Na duba wayar na ga missed calls ďin Ihsan da tayi ta kira muna waya da Ya Mahmud da tunanin wai idan munyi sallama da shi zan kira ta, gashi mun yi kwanan zaune. Yau Mami ko kyalli na bata gani ba. Oh ni Zara!
Na mike na shiga toilet nayi alwala, nazo nayi nafilfili na, this time daga Mami sai Ya Mahmud nafi mayar wa da addu’o’i na kansu. Bayan nayi sallar asuba dakyar nayi azkars ďina saboda wani azababben bacci da nake ji! Na saki blends mai duhu na karo karfin Ac sannan na shige cikin duvet na kwanta ina jin kamar babu abinda yafi bacci daďi a rayuwa.
Ringing ďin da wayata take ne babu kakkautawa ya sanya na buďe idanu na da bacci ya galabaitar na saka hannu akan drawer na dauko ta.
Ya Mahmud ne again…….
Nayi gyaran murya nayi mi shi sallama
“Ba dai bacci kike ba har yanzu?”
Nace
“Idan banyi bacci Ya Mahmud ai faďuwa zanyi idan na tashi, kwana fa muka yi muna waya”
Yace
“Maza kici gaba da faďa Dada taji”
Nayi murmushi nace
“Karfe nawa ne?”
Yace
“Karfe shaďaya ne da rabi! Tun ďazu nazo gidan nayi breakfast na tafi!”
Na zaro idanu ina durowa daga gadon cikin sauri na wuce toilet da wayar makale a kunnena.
“Kai kai kai! Kuma shi ne ba’a tashe ni ba? “
Yace
“Dada ce tace a kyale kiyi baccin ko more saboda……..kinga just get out of bed kiyi wanka kici abinci! You will call me later!”
Ya kashe wayar ba tare da jiran amsa ta ba. Kuma wai i will call him? Which means akwai wani abu? Kawai sai nayi wanka gabaďaya na shirya na futo parlour cikin wata masifaffiyar yunwa.
Na durkusa na gaishe da kowa da kowa na ďauki Asad nayi mi shi wasa sannan na mayar da shi cikin cradle ďin shi. na shiga kitchen na haďo breakfast na dawo falon na zauna.
STORY CONTINUES BELOW

A.laila tace
“Yau wanne irin bacci kika yi ne Zara? Gajiya kika yi haka?”
Murmushi nayi kawai bance komai ba, naci gaba da shan kunun gyaďa garďin shi yana ratsa ilahirin jikina, kai Baba Rabi kata’i ce a girki.
Na lura duk kallona suke yi musamman Ya Nuratu har wani gimtse dariya take yi! Na girgiza kai nace
“Ya Nuratu kin mike kafa da yawa a gidan nan, anya ma kuwa kina lissafi? Toh saura sati biyu hutun ki ya kare!
Waďannan kayan alatun na Baba Rabi sai dai ki gani a vedio call”
Ta kuwa kwashe da dariya har da rike ciki! Sai naji dariyar ta ta kamar akwai wani abu a ciki. Sai kuma na share na dubi A.laila cikin tsokana nace
“A.Laila zaki missing Nigeria ko?”
Ta kuwa miko mun dakuwa na kwashe da dariya.
“Zamu ga wanda zai yi missing ďin Nigeria ďin tsakanin ni da ke”
Nace
“Don Allah A.laila dagaske sai bayan sallah zaki koma?”
Cikin nutsuwa tace
“Ai ni da America sai dai da yawo Zara! Na dawo gida”
Na ajiye kofin kunun cikin tsinkewar gaba nace
“Kamar Yaya?”
Murmushi tayi tace
“Daada(mijinta) yayi retire, but da bai yi niyyar mu dawo ďin ba sai ya kammala tattara komatsan sa a hankali, ni kuwa tun zuwan da nayi naji America ta fuce mun a rai gida kawai nake so.
Soo ina shirin komawa yace no need har gidan namu ma an siyar shirin dawowa yake yi”
Cikin wani irin farin ciki nace
“I’m soooo happy A.laila! Ya rabb! This is sooo great! Wannan abu yayi mun daďi? Toh a ina zaku zauna?(sanin da nayi cewa Dadan ďan garin Sokoto ne ita kuma ýar katsina)”
Ta sake yin murmushi tace
“Ana nan ana polishing gidan mu a Wuse, bayan sallah zamu tare”
Wani uban tsalle na daka ina ihu na rungume A.laila ina cewa
“Wayyo daďi! A Abuja zaki zauna A.Laila? This is soo beautiful”
Itama rungume ni tayi tana dariya, Ya Nuratu da Dada na taya ta
“Toh ďaga ta haka tunda ke ba zaki taba girma ba da tsalle tsalle da hayewa jikin mutum kamar wata ýar biri”
Cewar Mami
Bata fuska nayi ina gyara zama na a cinyar A.laila kamar wata Amal. Nace
“A.laila aikin ki fa? “
Ta shafa bayana tace
“Na bar musu a can Zara! Yanzu fashion house ďin Mami nake so na mayar da hankali a kai! Ita ta zauna ta huta ni kuma na ba shi kulawar da sunan shi zai dawo yana kuwwa a ciki da wajen Nigeria….”
Kawai sai naji na fara hawaye, na sake rungume ta na fashe da kuka….
“A.laila do you read people’s heart? Abinda yake raina kenan! Burin da nake da shi kenan, yanda zanyi nayi overtaking business ďin Mami ita kuma ta huta! ALLAH nagode…..”
Naci gaba da kukan
Bubbuga bayana ta dinga yi cikin sigar rarrashi dakyar nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya.
Ya Sadik ne ya shigo cikin sallama da tickets a hannun sa, ya karasa gaban kujerar Dada ya gaishe ta sannan ya dawo da idon shi kaina yana cewa
“Ke kuma meye haka?”
Na tashi daga cinyar A.laila na koma gefenta ina share hawayena. Ya sake cewa
STORY CONTINUES BELOW

“Me kike yi baki shirya ba?”
Zan yi magana kenan Ya Omar da Ya Mahmud suka shigo, na bude baki ina kallon shigar Ya Mahmud ina tunanin when last yayi irin ta.
Suit ne royal blue a jikin shi da farar shirt a cikin yayi wa gashin sa irin gyaran da yake yi mi shi only on special occasions, ya kifo kamar kwando yana sheki, sabanin kwanakin nan da kullum yake cikin jallabiyyas da dogayen rigunan ladika.
Kamshin “la Nuit” ya karaďe falon gabaďaya kamar wanda aka fasa kwalbar shi a wajen.
Ya Omar ya kalle ni cikin murmushi yace
“Hajjaju ina jakar ne?”
Sai naji kaina ya kulle kuma jikina yayi Sanyi! Na daga idanu na kalli Dada, sai ta yi mun alamar nazo da hannunta.
A sanyaye na mike na isa gabanta na zauna. Sai ta dafani cikin kulawa ta soma magana a tausashe
“Zara na saka an yarkar miki tikiti, tare zaku tafi da Mahmud, idan ya gama abinda yake yi a Dubai da Riyadh ďin sai ku wuce kuyi umrah kuyi addu’a”
Wani mahaukacin bugu naji kirjina yayi!wani irin tashin hankali naji ya mamaye ni, kamar ban taba sanin wanene Mahmud ďin da za’a haďani tafiya tare da shi mu kaďai ba.
“Dada ni kaďai?”
Yanayin yanda nayi tambayar cikin matsanancin tsoro da fargaba ya sanya su A.laila yin dariya kasa kasa.
“Ke da shi ku biyu a bisa umarni na! Na kuma tabbatar ba zaki yi mun gardama ba. Domin ke ďin mai biyayya ce ga umarnina a kowanne lokaci! Zara ina son na tabbatar miki da cewa ke ďin kina da wani irin kadari a idona irin wanda ba zaki taba ganewa ba, biyayyar ki da soyayyar ki da sadaukarwar ki a gare ni sun gayyato miki mutunci da kima da daraja masu yawan gaske a zuciyata.
“Kullum kwanan duniya addu’a ta shi ne Allah ya baki miji nagari wanda zai rike ki da dukkan gaskiya da amana! Allah ya baki yaýan da zasu bi ki su ji kan ki kamar yanda kika yi hidima da ni babu gajiyawa babu bacin rai babu ganda.
Sai Allah ya amsa mun addu’a ta ya baki mijin da ko mu ba lallai mu baki kulawar da zai baki ba! Ina yi miki fatan alkhairi a rayuwa Zara! Allah ya albarkaci rayuwar auren ku, Allah ya haďa kan ku Allah ya baku ýaýa masu albarka Allah yasa anyi kenan mutuwa ce zata raba!………”
Wani magigicin kuka na fashe da shi na faďa jikinta jikina har rawa yake yi.
Hankalina ya kai kololuwar tashi!
Ni kuma irin auren da za’ayi mun kenan? Babu rakiya babu saka ranar tariya kawai ina tashi daga bacci za’a gaya mun na shirya mu tafi kamar a cikin littafi? Kamar wata ýar tsana? Haka ake yi?”
Cikin kukan nake cewa
“Don Allah kiyi hakuri Dada! Wallahi ba zan sake ba! Bazan kara futa ba da izinin shi ba! Kiyi hakuri Dada ki bari ayi mun irin yanda ake wa kowa! Don Allah ki bari nayi sallama da ku a nutse”
A hankali ta dinga jijjigani tana shafa kaina sannan tace
“Kiyi shiru Zara! Ba ina nufin gidanku zaku tafi ba, ko kin ji nace London? Ba tarewa zaki yi gabaďaya ba!
Wannan tafiyar kawai nake so kuyi tare saboda kuje kuyi addu’a ku samu albarka da ladan Umrah a farkon auren ku! Tarewar ki ai a hannun babanku take, shi ne yace a dakata ya kammala shirin sa. Baki ji yace sai yayi wani bukin ba? Ba tafiya zaki yi ba Zara”
Wani irin lallashi take mun irin wanda wani mahaluki bai taba yi mun irin shi ba, irin wanda kuma babu wanda zai yi tunanin Dadan ta iya shi kuma akwai wanda zata zauna tayi wa irin shi.
Da kanta ta mikar dani muka shiga ďaki ta rakani har toilet na wanke fuskata nayi alwala na futo, da taimakon ta na gyara jikina na shirya cikin sabuwar dandakekiyar bakar abaya samfurin Swarovski wadda aka yi wa wani irin zubin duwatsu masu ďaukar hankali. Na naďe kaina da mayafin rigar bayan ta saka ni na saka kwalli da powder da lipsgloss.
Gefe ďaya Ya Nuratu na aikin haďa mun kayan bukata na na sakawa da toiletries komai sabo fil cikin babbar jaka da karamar trolley.
A karshe Dada ta feshe ni da turarukan body shop sannan ta kamo hannuna, Ya Nuratu ta ajiye mun sabbin slippers ďin “Vinci” na saka ta rataya mun jakar aldo wadda ta cika da tarkacen abubuwan da matafiyi yake bukata a hannun shi.
Scene ďin da yake faruwa a wannan ranar kamar irin sina sinan films ďin Hindu masu karya zukatan mai kallo ya saka shi kukan da bai niyya ba.
Babu wanda bai yi hawaye ba, har Mami ta cire kunya ta rungume ni tayi mun fatan alkhairi, Ya Nuratu kuwa kuka ta saka ta koma cikin gida, haka ma Baba Rabi, A.laila ce ke ta faman share mun hawaye tana lallashina, Dada tana bi na da addu’a.
Su Ya Sadik da Ya Omar duk jikin su yayi sanyi.
Abun mamaki yau sarkin kukan bai yi halin na shi ba, sai murmshi kawai yake yi amma shima jikin shi yayi sanyi.
A karshe Ya Sadik yace kada muyi missing flight sallamar ta isa haka.
Dada ce ta buďe gidan baya ta saka ni ciki tana mun addu’a, Ya Mahmud ya zagaya gefena ya zauna.
Ya Sadik na gefen Ya Omar da ke kokarin kunna motar, na juya gefena na kalli su Mami suna ďago mana hannu, nima sai na tsinci kaina da ďaga musu nawa hannun hawaye na bin kuncina.
Ya Omar ya juya alakar motar ya nufi gate, security ya buďe mana kofa, na sake juyawa na hango Su Mami still suna tsaye suna ďaga mana hannu, na sukuyar da kai ina kokarin rike kukan da yake taho mun.
Ya Omar ya harba motar kan titi cikin kwarewa, muka ďauki hanyar airport zuciyata cike da wasu irin emotions waďanda ban taba jin irin su ba a rayuwata………………..
Assalamu Alaikum my dear readers!
Soo far menene comment ďin ku akan labarin Hausa Arab? Meye hasashen ku game da karashen labarin? Me zai faru? Me kuke hangowa?
Please share your views with me!
It will means alot.
Ina godiya ga dukkan wanda ya ďauki precious lokacin sa ya karanta labarin Hausa Arab kuma ina yi muku fatan alkhairi! Allah ya bar kauna da soyayya!
Da wannan shafin nake rufewa sai Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya!
Ina yi mana fatan shiga watan Ramadan da rai da lafiya cikin aminci da albarka!
Ina fatan zaku sanya ni cikin addu’o’in ku? ALLAH ya amshi ibadunmu ya sanya mu cikin bayin da yake ýantawa a wannan wata mai tarin albarka.
Allah ya sada mu da alkhairi!!
Ma’assalam!
Cutyfantasia.Emirates Hills,
Dubai.
Tsaye nake a jikin tangamemen gilashin da ya mamaye duka bangon yammacin ďakin da nake zaune, ina kallon view ďin da ke gabana na korama da wasu irin setting ďin kujeru da aka yi a gaban ta da tebura masu wani irin shape a lankwashe. Duk yanda zan bayyana kyawun wannan gida da wannan waje bazan yi mi shi adalci ba, abun sai wanda ya gani kawai, abinda kawai na fahimta shi ne kasar Dubai tana developing na ban mamaki kuma tana ďaya daga cikin kasashen da suke takama da kyawawan gine ginen zamani masu ďaukar hankali.
A sanyaye na sauke ajiyar zuciya na kai idona ga agogon fatar da ke hannuna kirar “swatch” wanda ya nuna karfe biyu da kwata na daren kasar. Damuwa ta lullubeni, to a ina Ya Mahmud ya zauna shi kuwa? Tun karfe hudu na yamma ya shirya ya tafi taron da muka zo domin sa, ya kuma tabbatar mun da cewa awanni biyu kawai zasu yi, daga nan zai wuce airport su ďauko Daddy ya raka shi masauki sannan ya dawo, duk wannan lissafin ya isa ayi su a cikin wannan lokacin a kammala, idan ma ba haka ba, ya kamata ce ya neme ni a waya ya sanar da ni dalilin jinkirin dawowar sa.
Na sake swiping screen ďin wayata na kira shi a karo na shida amma babu reply, na ja da baya na koma kan farar counch ďin da ke gefena na zauna sannan nayi amfani da remote na zuge labulen glass ďin da na tsaya a gaban shi na kara hasken ďakin ta hanyar kunna kyakykyawar chandelier me wasu irin kananan fitilu masu ban sha’awa.
Na kuma ďaukar wayar zan dialing number Ya Mahmud a karo na bakwai sai shigowar wata number ya katse ni.
Na sauke ajiyar zuciya ganin number kasar, na tabbatar shi ne ya kirani.
A hanzarce na ďauka tare da kara wayar a kunne na.
“Hello”
Sai dai a maimakon naji muryar wanda nake tsammani sai naji muryar wani mutum daban.
“Please are you Mrs Mahmud Lamiďo?”
Cikin bugawar kirji nace
“Yes! Where is he? Where is my husband?”
“Calm down madam! He had an attack and we have taken him to the hospital and we are happy to tell you that he has regained his consciousness! I’m Bala Sabo Alhaji’s co,worker. A driver will come and pick you up now and bring you the hospital!”
Tuni hawaye ya wanke fuskata…
Daman tunda muka zo nake tsammani da tsoron faruwar hakan.
Ya Mahmud has changed to a completely new person, baya dariya baya walwala baya magana, ya saka wata irin damuwa a ran shi wadda take hana shi kowanne irin sukuni da kwanciyar hankali.
Baya bacci sai tunani, sai kuka sai damuwa kawai, a cikin kwanaki ukun da muka yi a garin ko kofar gidan da muke ciki bamu leka ba sai safiyar yau da wannan Bala Sabon(tsohon ma’ikacin Daddy ne ya samu aiki a Dubai ya bar company ďin Daddy ya dawo) ya kira shi suka futa sannan ya dawo ya shirya suka tafi wajen taron.
Na rasa dalilin da ya sanya ya kwallafa ran shi akan mahaifin shi da yawa irin haka bayan yana da sanin cewa haďuwar su wani abu ne da yake hannun Allah, sannan Daddy na can yana iyaka kokarin shi kuma yayi mi shi alkawarin sai inda karfin sa ya qare amma a maimakon ya kwantar da hankalin shi kullum kwanan duniya kara damuwa yake yi.
Ga ciwon shi babu abinda yaki irin damuwar, don haka ne nake tsoron abinda zai faru da shi domin yana cikin haďari.
Na goge hawayena na ďauko abaya na ďora akan kayan jikina na ďauki jaka ta na futo domin kasa jiran isowar driver ďin nayi.
Kwanaki biyu Ya Mahmud ya kwashe a asibitin kasar Dubai karkashin kulawar manyan likitocin zuciya da taimakon Allah da taimakon addu’a ya samu sauki. Daga ni har Daddy hankalin mu bai kwanta ba sai da muka ga ya warware ya koma hayyacin shi kuma yana iya saka abinci a bakin shi yaci.
Muna zaune ni da Daddy a babban falon gidan da muka sauka, a tsarin Daddy ba anan zai sauka ba duk magiyar da Ya Mahmud yayi mi shi akan hakan saboda gidan shi ne idan ma baya son zama tare da mu sai mu mu koma hotel ďin da ya sanya aka kama masa amma yaki. Toh sai kuma rashin lafiyar Ya Mahmud ďin ta rushe komai, yanzun ma da muka zauna tattaunawa muke yi akan matsalar ina baiwa Daddy labarin irin damuwar da ya sanya kan sa a ciki.
STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan yace
“I have done my best Zara! Nayi dukkan kokarin da nake ganin zan iya kuma na damka aikin a hannun wanda nake da tabbacin ba zai bani kunya ba. Ko da ace Ilyas baya raye, da izinin Allah za’a samu dangin shi kuma zasu karbe shi hannu bibiyu.”
Cikin damuwa nace
“Daddy amma ai baban na shi bai gaya musu cewa yana da ďa ba, so basu san komai game da Ya Mahmud ba, kana ganin zasu yarda su amince da shi a matsayin jinin su kuma ahalin su bayan dukkan abubuwan da suka faru tsakanin mahaifin shi da mahafiyar shi?”
Murmushi Daddy yayi yace
“Nayi imanin zuwa wannan lokaci Ilyas ya sanar da wani ko wata ko wasu ko kuma ya bar wasiyya akan Mahmud! A sanin da nayi wa Ilyas da kuma irin ďimbin soyayyar da yake yi wa Esha da Mahmud na tabbatar watarana zai baiwa dangin shi labarin abinda ya faru a tsakanin su.
Kuma ko da bai faďa ba, duk wani idon ya taba ganin Ilyas idan ya kalli Mahmud zai tuna da shi, ko da dangin Ilyas sunyi jayayya da labarin da za’a gaya musu toh da zarar sun yi arba da Mahmud zasu ajiye duk wani makamin gardama da rashin yarda saboda Mahmoud photocopying baban shi ne, hasken fata kawai Ilyas zai nuna masa, domin shi kalar Esha ya ďauko lokacin yana yaro so suna ganin shi magana ta kare. “
Na girgiza kaina cikin gamsuwa a raina ina cewa
Yanzu ma bana tunanin zai nuna mi shi wani fari ko hasken fata domin ya rikiďe daga wancan wankan tarwaďan ya koma fari sol kamar ka wanke hannu kafin ka taba shi. Ina matukar fatan cewa Allah ya amsa addu’ar mu ya sada Ya Mahmud da mahaifin shi domin kwanciyar hankalin mu da shi gabaďaya ta ta’allaka ne akan hakan.
……………………………………………………………….
Kwanaki shida muka kwashe a Dubai muka kammala duk wasu abubuwan da suka kai mu ko nace Daddy ya kammala abubuwan shi da kansa saboda jikin Ya Mahmud bai gama kwari ba.
A ranar kwanaki bakwai ďin muka yi sallama da Daddy muka wuce Madeenatul munawwara cikin jirgin Emirate.
Da yamma muka sauka a Prince Mohammad bin Abdulaziz International Airport na Madeena, bayan mun kammala abubuwan da zamu yi a airport mota ta ďauke mu zuwa masaukin mu da ke dab da harabar Masjidun nabawi mai suna
“Daral~Eman” a suit hawa na goma sha biyu.
Kasancewar babu wata gajiya a tare da mu ya sanya kowannen mu ďaukar kayan shi zuwa ďaki guda.
Sai da nayi matukar kokari kafin shiga wanka ina tsaye jikin window ina kallon view ďin masallacin madeena wani shauki da wasu irin emotions suna tsirga mun.
A gaggauce na kammala wankan nayi shafa na shirya cikin nude colour abaya samfurin “zara” sannan na shafa sassanyan oil perfumes ďin “Ajmal” marasa karfin da sai kazo dab da jikin mutum kake shakar kamshin su.
Na haďa duk abinda nake bukata a cikin ýar karamar Gucci hand bag ďina sannan na saka takalmi na futo ina duba waya ta, kamar haďin baki shima a lokacin ya turo kofar ya futo, na tsaya ina kallon shigar sa, sabuwar farar jallabiya mai ďan kauri ya gyara gashin sa ya ďora naďin larabawa da shemagh da egal, ya zauna dai dai a kan shi.
Nayi imanin babu yanda za’ayi na gano shi idan muka futa ya shige cikin larabawan garin madeena.
First time da naji na raina kaina kuma nayi shakkar futa tare da shi, don haka sai na koma gefe kawai na tsaya jikina a sanyaye.
Cikin nazarina yace
“Are you ok? Muje mana”
A sanyaye nace
“Ya Mahmud kowa tafiyar shi daban, gaskiya ba zamu jera tare mu futa ba”
Ya waro ido cikin rashin fahimta sannan yace
“Why? Me nayi miki?”
Na sake haďe fuska ina magana bilhaqqi
“Saboda dai dai gwargwado ina da kyauna kuma kullum ina godewa Allah, jerawa da kai na nufin duk wanda ya kalle mu sai ya gano muni na ya kuma yi tunanin abinda ya haďani da kai kila wani ma ya kasa hakuri ya tambaye mu!
Soo kayi tafiyar ka nima nayi tawa, idan muka dawo hotel ma haďu”
Tsayawa kawai yayi kallona with a straight face sannan ya girgiza kan shi yace
“If that’s what you want, fine!”
Ya ajiye key ďin ďakin a kan table sannan ya ratse ni ya wuce ya futa ya barni da kamshin “la nuit” da kuma mamaki maďaukaki.
He has changed! He has really changed!!!
Abinda nake gayawa kaina kenan har na futo daga cikin ďakin na sauko kasan reception, sannan na futo daga hotel din jikina a sanyaye, a can gabana na hango shi yana gab da shiga masallaci kasancewar hotel ďin yafi kusa da kofar maza, ni sai da na ďan yi zagaye sannan na koma gate 16 gate ďin ziyarah.
A wannan rana nayi Addu’a irin wadda ban taba yi ba a rayuwata, nayi nafila bansan raka’a nawa ba, har sai da guiwoyina suka yi laushi suka yi sanyi suka sage. A cikin masallacin nayi sallar magrib da isha’i na zauna dogon zama har lokacin da aka buďe shiga ziyara cikin kabarin Manzo na shiga, mune farkon shiga amma nice karshen futowa saboda sai da aka fara kora sannan na hakura na taso, idanuna sun kumbura sunyi nauyi, guiwoyina sunyi sanyi, dukkan gabobin jikina kuma ciwo suke yi dakyar nake ďaga kafata.
Cikina ne yayi wani irin damka ya saki wanda ya tuna mun cewa rabona da abinci tun a cikin jirgi, yanayin da nake ciki gabaďaya ya ďauke mun yunwa da kishirwa, sai zam zam da nayi ta sha da niyyar waraka da magani da neman albarka ba don kishi ba.
Na futo gate ďin mata kenan na hango Ya Mahmud a tsaye ya naďe hannayen shi a kirjin shi yana kallon kofar futowar carefully baya ko kiftawa kuma ina ganin lokacin da ya sauke wata irin ajiyar zuciya da muka yi ido huďu da shi.
A hankali na isa inda yake ina kallon shi , ba tare da yace komai ba ya kama hannuna muka soma tafiya, nima bance komai ba sai wani tsoro da na dinga ji, I have never seen him this angry (with me).
Bamu tsaya ko’ina ba sai da muka dangana da hotel ďin mu, ya wuce direct zuwa wajen lifts ďin da ke jere babu bata lokaci ya buďe muka shige zuwa hawan da muke.
Sai da muka shiga parlour ya zaunar da ni akan ďaya daga cikin kujerun wajen sannan ya zauna a gefena.
Cikin nutsuwa ya soma yi mun magana
“Zara!”
Ban amsa ba ban kuma ďago na kalle shi ba saboda tsoron ganin yanda yanayin idanun shi ya koma.
“Zara”
Ya kira ni for the second time, shima ban ďago ba sai dai amsawa da nayi cikin sanyin murya.
“Wannan shi ne karo na farko da kika yi mun abinda ya bata mun rai ya kuma sanya mun shakku akan yardar da kika yi dani da kuma rayuwar da take gabanmu ni da ke! Idan har irin hakan zai sake faruwa ko yaci gaba da faruwa toh zaki yi matukar mamakin sauyin da zaki samu a tare da ni, I won’t lie to you I cannot take this!
I don’t know if I have ever told you this, amma yanzu zan sake gaya miki, for the last time, for the one last time Zara bana so wani dalili ya sanya ki kuma gangancin yi mun magana akan halittar jikina.
Ni mutum ne, mahaifina balarabe ne mahafiyata baturiya dalilin da ya sanya kamannina haka kenan ba zabo ni aka yi cikin hausawa ko fulani aka kebanceni da halitta daban ba, ba kuma wata matsala ko case irin wanda ake samu na jirkitar halitta ko sauyawar abin haihuwa a cikin mahaifiyar sa a dalilin wani condition ne ya faru da ni na zama haka ba. Na ďebo kamanni da siffa da jinin iyayen da suka haifeni ne kamar kowanne normal abun haihuwa saboda haka baki da wani dalili da zai sa ki dinga kallona a matsayin wata halitta daban.+
Ni ba bahaushe bane, kaddara ce ta tsallako dani cikin hausawa ba don wannan kaddarar ba bazan taba zama cikin ku ba balle na zama alien.
Abu na biyu shi ne kyau ko farar fata ba sune mutum ba, addini da kyawun hali da tarbiyya da nagarta su suke baiwa mutum kowanne irin kyau, a wajen mutane ma asali sai yazo ya doke su gabaďaya, sau nawa kika ji Inna Badi’a tana cewa kyawun ďan maciji nayi? Sau nawa tana cewa mutum har mutum amma babu tsatso mai kyau? Sau nawa tana cewa Allah ya san niyyar jaki shiyasa bai ba bashi kawo ba? Ma’ana da ina da asali da girman kai da ďaga kan da zanyi sai yafi haka.
A gaban idon ki yarinyar da take sona kamar ranta ta turo mun sako tace ta fasa aurena saboda bata san me zata cewa ýaýan da zamu haifa akan asalin uban su ba………”
Ya dakata ya goge hawayen da suka sauko masa sannan yaci gaba
“A mutanen da nayi mu’amala da su ta gaskiya idan zasu yabe ni halina suke faďa ba siffa ta ba, nagarta ta suke kallo ba kyauna ba, kuma ba don halin nawa ba da ban samu shaida me kyau daga wajen waďannan mutanen ba.
“Ni da ke aure muka yi, rayuwar aure ba wasa bace ba zaman kwana biyu ko sati bane, rayuwa ce da ake fatan mutuwa ce kaďai zata yanke ta saboda haka babu zancen shigo da wasu al’amura daga fannin ďaya wanda ďayan ba zai lamunta ba.
“Zara kada ki kuma kallona da yanayin da kika kalleni ďazu, kada ki kuma yi mun lafazi makamancin wanda kika yi mun daźu banaso! Kuma ba zan lamunta ba, saboda wani abu ne wanda bashi da bambamci da kin soka mun kibiya a kirjina, it reminds me of who I am and where I belong , yana kuma kara mun jin cewa I do not belong a wajen da nake yanzu, yana sakawa naji duka habaice habaice da gorin da aka yi mun sun dawo zuciyata sabbi fil ina jin bukatar sanin inda mahaifina yake da zogin son kasancewa da shi cikin ahalinsa, ina kuma tsanar wanda yayi mun kalamai ko kallo irin wanda kika yi mun saboda haka Zara let it be the last time! Please!!”
Ya mike da sauri ya shige ďakin shi ya kullo kofar ya bar ni da sanyin jiki.
He completely misunderstood me, kuma hakan ya faru ne a dalilin halin da yake ciki na anxiety disorder da kuma depression, kowanne action kwakwalwar shi bata mi shi interpreting din shi dai dai da sauran kwakwalen mutane sai ta sauya mi shi meaning zuwa wani abu wanda ya shafe shi wanda zai dagula mi shi lissafi ya hayayyako da zuciyar shi.
STORY CONTINUES BELOW

Ni har ga Allah ba da wata manufa nayi maganar ba, a tunani na ma abun dariya zai ďauke shi, ban taba tunanin wannan reaction ďin daga gare shi ba kuma banji daďi ba.
Amma nagode Allah da hakan ya faru, ya zama lesson a gare ni a gaba kuma zan san irin matakin da zan ďauka na zama da shi kuma zan tsananta mi shi addu’a domin ita yafi bukata fiye da komai.
……………………………………………………………….
Ko jakata ban ajiye ba na mike na sake futa zuwa gidan abincin “SANABIL”
nayo mana take away sannan na tsaya a wani kiosk na siyo mi shi matsatstsen lemon zaki da abarba irin wanda yake sha a kullum sannan na ďauko hanya na dawo hotel ďin mu.
To my biggest suprise a reception muka sake haďuwa da shi ya sauko, looking disturbed and worried, muna haďa ido ya sauke ajiyar zuciya……
Allah sarki! He thought fushi nayi na sake tafiya wani wajen ko kuma na koma masallacin….
Cikin murmushi nace
“Where to?”
Ya harare ni sannan
“Na zata guduwa kika yi”
“Na gudu naje ina?”
“Rashin sanin hakan ne ya ďaga hankalina na futo nema”
Nayi murmushi nace
“Zara will never leave you Ya Mahmud no matter what….
I promise to be with you cikin kowanne hali kowanne yanayi kowanne lokaci komai tsaurin sa……
Abinci naje na siyo mana naga bai kamata mu kwanta da yunwa ba kamar yanda kayi niyya! And I’m sorry for everything”
Wani genuine smile yayi escaping lips ďin sa, duka dimples ďin sa suka koma ciki, nayi imanin wannan farin cikin daga cikin zuciyar sa ya taho….
Bai ce komai ba ya rage mun kayan hannuna muka koma ciki muka haye ďakinmu….
Sai kuma muka koma tsokanar juna akan abinda ya faru, muna dariya kamar ba mu ne na ďazu ba…….
Shikenan muka shirya…..
Ni kuma da yake na gano matsalar da yake fama da ita sai na shiga taitayina nake taka-tsan-tsan da maganar da zan gaya mi shi, domin zuciyar shi a kusa take, kiris yake jira ya soma faďa kamar zai cinye mutum ďanye, sai daga baya kuma ya dawo yana regretting saboda haka sai bana ďaukar faďan na shi da gaske, I will just watch him yell and shout ya gama bana cewa komai, idan kuma ya sauko bana nuna mi shi komai wani lokacin ma ni nake soma yi mi shi magana, dalilin da ya sanya zaman namu ya ďore kenan.
Kwanaki shida muka yi a madeena muka tafi Makkatul mukarrama cikin karamar mota mai ďan karen gudu da sanyi…….
Muna isa muka wuce “Swiss òtel” muka ajiye kayan mu muka yi alwala muka faďa harami domin sauke umrah
I will say it’s very different da dukka umrar da na taba yi a rayuwata, very peaceful ga kuma wani emotion na daban, a wannan karon addu’a ta guda ďaya ce ita nake yi nake karawa
“Allah ina tawassali da tsarkin mulkin ka, da girman zatin ka da soyayyar da kake yi wa Shugaban halitta Annabi Muhammad saw Allah ka haďa Mahmud da mahaifin shi ko Aina yake cikin duniyar nan ka sada su da alkhairi, idan kuma ba ya raye Allah ka haďa mu da zuri’ar shi su karbi Mahmud da farin ciki da murna da jindaďi. Allah ka yaye mi shi damuwar da yake ciki ka bashi juriya da hakuri ka kuma yaye mi shi lalular da take damun shi don alfarmar masoyin da babu kamar shi a wajen ka saw”
Kullum a harami muke kwana muke rabin wuni, don shi wanka ne kawai da cin abinci suke dawo da shi hotel amma ko bacci a cikin harami yake yi ……..he was sooo attached to the place har na soma tunanin anya zai iya yarda mu taho kuwa?
Saboda ďawafi kafar shi har kaushi tayi tana saba, idanun shi sun zurma saboda kuka da rashin bacci, idan yana addu’ar jikin shi har wani shaking yake yi kamar ana vibrating ďin shi abun tsoro kamar zai shiďe.
Dukan mu mun rame munyi duhu a kwanaki goman da muka yi a garin Makkah saboda bamu huta ba bamu samu bacci ba, shi kullum azumi yake yi, nima kuma nayi loosing appetite bana jin sha’awar komai cikin raina.
“Ya Mahmud ka zauna don Allah ka kwanta kayi bacci just for today! You look soo pale, Allah sami’uddu’ai ne, yana jin ka yana ganin ka kuma ya amsa maka, domin babu bukatar da bawa zai kawo ta nan bata biya ba sai dai jiran lokaci. Wannan rashin hutun da rashin bacci ba shi ne zai saka ayi saurin amsa maka ba, Allah zuciya yake kallo kuma yafi ka sanin abinda take ciki da abinda take so kuma shi ne zai maka maganin damuwar ka………”
I had to give him about 30min lecture kafin ya hakura ya kwanta, nan da nan baccin kuwa yayi gaba da shi. Sai na shirya na futa chemist domin samo mi shi man zafi, tun da baya shan pain killer.
Ina futowa sai na zagayo nayo harami, kofar zam zam tower na kalla sai naji nayi sha’awar shiga, tunda muka zo bamu kalli kanti ba don haka na karkata na shiga ina kallon agogo.
Shop ďin abaya kawai zanje da na turare, tunda nazo ban siya sabuwa ba wanda nazo da su nake sakawa.
Cikin sauri na shiga kantin abaya na zabi abayas ďin na biya na futo na nemo shop ďin “Abdussamadul Quraish” na shiga domin na yo wa Daddy da su Ya Omar tsarabar su, sai dai me? I got the shock of my life a lokacin da na zura kafata a cikin Shagon
Kunsan me nagani? Wani dogon matashin balarabe ne tare da wata balabiya wadda alamu suka nuna matar shi ce, kuma ba matashin ne ya kaďani ba, matar tashi ce, tunda nake a rayuwata ban taba ganin kama irin wadda wannan matar tayi da Ya Mahmud ba, like komai da komai nasu iri ďaya ne, hasken fata kaďan zata ďara shi, shi kuma ya fita tsayi, bayan wannan dai dai da yatsun su iri ďaya ne.
Luuu nayi zan koma baya cikin taimakon Allah na dafa jikin shelve na tsaya da kafafuna without blinking my eyes on the woman!
A hankali na matsa gefen da suke tsaye da tarin turaruka a gaban su suna zaba suna ragargazar larabci duk da ita muryar ta a kasa take amma wallahi ko amon sautin nasu iri ďaya ne, kawai ita nata na mace ne shikuma na namiji.
Tsayawa nayi still na rasa ta ina zan fara? me zanyi? Wanne mataki zan ďauka? Kaina gabaďaya ya kulle kwakwalwata ta tsaya cak!
Wani matsanancin danasani nake ji na rashin iya yaren larabci, domin shi ne kawai hanyar da zata bani damar yin magana da ita cikin sauki da fahimta.
To ya zanyi? Me zanyi? Ta ina zan fara?
Ina can duniyar tunani ina sakawa da kwancewa da tunanin ta hanyar da zan bullowa waďannan bayin Allah naji murya mai karfi tana mun sallama, nayi maza nayi firgigit na ďago kaina, coming back to my full senses.
Balaraben shagon ne yake mun magana ganin na kafe waje ďaya na tsaya kamar gunki, ban maida hankali gare shi ba nayi maza na wurga manyan idanuna ga direction ďin matasan larabawan da ganin su ya sakani cikin wannan halin amma sai me?
Wayam! Kamar an saka na’ura an goge su daga view ďin da na ke kallo mintina kaďan da suka shuďe, na sake murza idona sosai, hoping na’urar da ta ďauke su ta dawo mun dasu amma sam, babu su babu dalilin su kamar sun bace bat.
Wani matsanancin tsoro da tashin hankali suka kamani, na juya na sake juyawa ko alamar su bangani ba, sai na mayar da dubana ga larabawan da hankalin su ya dawo kaina a dalilin tsarguwa da suka yi da ni, a haka gani mutum presentable amma nazo ina abubuwan marasa hankali.+
Cikin matsananciyar damuwa da faďuwar gaba na soma yi musu magana cikin harshen da ni da su muke ji gabaďaya wato ingilishi.
“Don Allah mutanen da ke tsaye a wajen nan ina suka yi?”
Ďayan ne ya amsa mun da cewa
“Sun futa yanzun nan”
Kalmar yanzun nan da ta ratsa kunnena ya sanya ni juyawa a sukwane na futa daga kantin wai da nufin na cimmasu. Laraban wajen suka bi ni da kallon majnoon domin rashin nutsuwar da na tatara musu.
Duk inda zan duba na duba, duk wani langu da sako na wannan hawan sai da na duba shi babu su, na dawo da sauri nabi escalator na sauko kasa, nan ma na bazama nema idanuna a warware amma sam babu su babu alamar su.
Ban ankara ba naji na gaji likis guiwoyina sunyi mugun tsami, toh waje na mai girman gaske, na dinga kurďawa ina zagayewa ba tare da na ankara da nisan tafiyar ba saboda tsabar tashin hankalin da na shiga. Ya aka yi nayi irin wannan sakacin? Ya akayi na bari suka kubuce mun? Wanne irin shirme da sakarci ne ya shiga kaina ina ji ina gani halittar da tafi kowacce halitta kamanni da Ya Mahmud ta subuce mun? Nayi imanin wannan matashiyar irin jinin Ya Mahmud ne ke gudana a jikinta, duk inda za’aje a juyo kuma iyaye daya suka haifesu, ko uwa ko uba, toh tunda shi tashi mahaifiyar shi kadai ta haifa tabbas mahaifinsu ne daya da wannan kyakykyawar yarinya
Ganin zaman da nake yi da tunani ba zasu amfana mun komai ba ga kiran sallah ana tayi sai na lallaba na tattara kayan hannuna na kama hanyar hotel dinmu ina tunanin wannan abun almara da alajabi da kuma bakin ciki da ya faru dani.
A gurguje na karasa cikin dakin mu ina tunanin kila Ya Mahmud ya tashi ya gaji da jira ya futa masallaci tunda gashi har ana sallar magrib ni da na futa tun karfe hudu da rabi amma sai na same shi kamar yanda na bar shi, ko juyawa baiyi daga side din da yake kwance ba.
mamaki ya kamani na wannan bacci me nauyi da yake yi wanda sam bai saba irin shi ba, shi ba mutum ne mai yawan bacci ba ko a gida balle idan akayi tafiya, koda yaushe yana waje yana exploring cikin kasar da yaje idan kuma ya dawo cikin hotel bincike da karatu cikin computer yafi maida hankali a kai. toh amma bashin baccin nan da yaci na wadannan kwanaki a garin nan dole ya tambaye shi kuma dole ya biya. Sai na ajiye kayan hannuna na karasa ina kiran sunan sa, dakyar ya farka yana karanto addu’ar tashi daga bacci yana kallon time.
ya yamutsa fuska yace
“yanzu zara shine kika barni ina wannan barcin asarar har ana yin sallah baki tashe ni ba? me kike nufi dani ne? ibadar ce bakya son nayi? a irin wannan garin kisa na rasa sallah a jam’i kawai saboda kinaso na huta? haka akeyi?”
rabuwa nayi da shi ya karaci fadan da ya saba sannan ya shiga toilet ni kuma na gyara gadon da dakin kafin ya futo na shimfida masa sallaya.
bayan ya futo nima na shiga nayi alwala muka yi jam’i tare. bakina sai kaikayi yake yi mun, na rasa yanda zan saka kaina naji dadi kawai so nake na samu wanda zan fesarwa da abinda nagani ko naji sauki and definitely not Ya Mahmud don na san sai ya kusa shakeni na daina numfashi idan yaji sakacin da nayi masa don haka ko doguwar hira ban yarda munyi da shi ba because i’m use to telling him irin wannan labaran mu kashe mu binne babu wanda ya sani akan wasu, toh this time dole na nemi abokin magana. ga dakin mu biyu ne kuma bai wani cika girma ba babu privacy, kuma duk inda zai je tankada keyata yake yi bai barina ni kadai i think anxiety din na shi ne yake saka mi shi jin cewa zan gudu ko zai neme ni ya rasa don hake nake yi mi shi uzuri.
STORY CONTINUES BELOW

tun daga wannan lokacin nake wara idanu ina addu’a akan Allah ya dubeni ya sake hadani da wannan baiwar Allah yar’uwar Mahmud, idan ina cikin masallaci bani da aiki sai dawafi ina addu’a ina rarraba idanu, idan na futo na kan shiga zam zam tower sau uku ko hudu a rana ina dubawa ko zan sake ganin su, amma cikin ikon Allah ko me kamar su babu sai dai masu yi mun gizau daga nesa naga kamar su ina matsowa kusa kuma zan ga basu din bane.
Ranar jumua muna idar da sallar jumua a harami muka taho gida domin a masallacin muka kwana muka hantse, shi daman azumi yake yi, ni ya futa ya siyowa laban da dabino naci kafin mu koma hotel dinmu.
ya tashi ya tafi kenan askar suka zo suka gyara sahun mazan da ke gaban mu mu mata muna baya, duk suka tashi kowa suna gyara tsarin zaman wajen, na tashi na nannade daddumata da ta Ya Mahmud ina mita na rataya jakata na koma gefe na tsaya ina tunanin kar na chanja waje ya dawo ya neme ni ya rasa, kamar ance juya kawai sai na ga fuskar wannan mata ta wulga ta gefena, cikin wani irin speed na juyo gabadaya ina kallonta, tabbas itace, cikin bakar abaya mai adon gold din leshi a bakin hannun da kasan rigar………
nayi wani irin juyi na bi bayan ta cikin sauri amma cikin ikon Allah walahi kamar aljana haka ta bace mun, na dinga safa da marwa tsakanin inda na ganta da hanyar da ta bi amma sam babu ita ba alamar ta.
wani irin hawayen bacin rai ya shiga sauko mun, wannan wanne irin ibtila’i ne? wanne irin al’amari ne mai hargitsa kwanya da lissafi?
Dakyar na samu na dawo wajen da nake Allah ya taimakeni na samu Ya Mahmud din bai dawo ba sai bayan na zauna. bayan mun idar da sallar muka tattaro muka taho hotel dinmu kowanne ran shi a jagule. ina kwance a kan gado idona a rufe ina tunanin abinda ya faru naji Ya Mahmud yana cewa
“zara bacci kike?”
na bude idona na kalle shi zaune a gefena nace
“idona biyu”
“i’m boring you right?”
na girgiza kai sannan nace
“no! you are not”
“nasani you are bored and tired of the new me, nasani kina hakuri nasani it’s only you that can tolerate me………
i’m sorry you have to go through this because of me”
na tashi zaune tare da daukar pillow na rungume ina kallon yatsuna.
“stop all these negative thoughts and assumptions! non of them is through! kuma bana son irin wannan maganar domin haushi take bani. even though you are my husband you still occupy that brother position da kake da shi wanda muke zama muyi sharing damuwar juna mu magance without feeling wani favour mukewa kanmu.
kuma auren da muka yi bai chanja komai ba a wajen in dai ba kai ne kake son ka chanja ba”
he smiled genuinely and said
“kinsan mafarkin da nayi jiya Zara?”
na gyara zama ina fuskantar shi sannan nace
“sai ka gaya mun”
yace
“mafarki nayi na hadu da Babana Zara! ban taba mafarki irin wannan ba, duk tunanin shi da nake yi, da damuwar da nake yi a kan shi ban taba mafarkin shi ba! ni ba mutum ne mai yawan mafarki ba, kuma idan har nayi mafarki akan abu toh da wuya bai faru ba…..”
murmushi nake yi hakorana a washe ina jin relief daga can cikin zuciyata, atleast zai samu nutsuwa.
nace
“shikenan damuwa ta kare! sai mu fara shiryen shiryen tarban shi”
STORY CONTINUES BELOW

sai kuma naga yayi shiru cikin damuwa da tunani
na sake cewa
“what again?”
a sanyaye yace
“zara da wuya idan yana raye”
Na yamutsa fuska cikin rashin fahimta sannan nace
“who told you? ya akai kasan hakan?”
ya sake sanyaya murya yace
“na gan shi ne cikin wani lambu me kyau da shigar fararen kaya, na taho da gudu zan rungume shi sai naga ya daga mun hannu, sai ya nuna mun wani gefen yace ka koma kaci gaba da zama a hannun babanka, rayuwata tayi maka nisa……..”
sai na farka, da farko murnar ganin shi cikin mafarkin ne ya kamani, sai da na zauna nayi tunani na tattauna ma’anar shi sannan jikina yayi sanyi nake tunanin da wuya idan ba mutuwa yayi ba.
i wouldn’t have seen him cikin kamannin da na gan shi da kuma bai mun maganganun da yayi mun ba.”
shiru nayi nima ina nazarin maganar shi da kuma gamsuwa da bayanin da yayi wanda ya sanya nima jikina yayi sanyi sosai tausayin shi ya kamani domin yanda ya kwallafa rai akan baban nan nashi da kuma gorin da ake mi shi akan shi ba abu bane mai sauki a bincika a ce masa baya raye.
nayi ajiyar zuciya nace
“khairan insha Allah ya Mahmud! mafarki ba gaskiya bane, muci gaba da addu’a! Insha Allah zamu samu mafuta”
ya jinjina kan shi kawai yana share hawayen da suke zubo masa, saura kiris mayi subutar baki nace masa naga me kama da shi sai wani sharp pain daga cikin cikina ya tsayar dani, na dafe cikin da sauri ina runtse idanu ya dube ni da sauri yace
“what? are you ok? what happen Zara?”
Ai ban samu wani ikon da na iya futo da wata kalma daga bakina ba saboda matsanancin ciwon da nake ji daga can kasan cikina wanda ban taba jin irin sa ba. sama sama nake kallon shi idona blurry har ma komai ya disashe mun nayi diff.
ban sake sanin inda nake ba sai bayan awanni biyar, kwance na ganni akan gadon asibiti da rigar marasa lafiya a jikina hannuna dauke da carnula wanda ya tabbatar mun da ruwan likita nake sha.
Na juya gefena a hankali sai naga Ya Mammud a zaune kan kujera idon shi yayi jajazur da alamun yaci kuka yaci ya koshi.
ganin na farka ya sanya shi mikewa da sauri ya danna kararrawar kiran nurse, nan da nan kuwa suka shigo suka zo kaina, daga nan suka kirawo likita shima yazo yayi examining dina suka yi rubuce rubucen su suka kammala sannan Ya Mahmud yabi likitan office din sa.
a asibitin na kwana sai washegari aka karasa mun allurai na suka sallameni, Ya Mahmud ya ciro mun abayar da ya siyo mun na saka akan rigar asibitin sannan ya kama hannuna muka futo daga dakin muna tafiya a hankali, na lura ya kara zama wani bebe tsakanin jiya da yau, kawai sai dai yayi hawaye ya goge yayi ajiyar zuciya. rashin dadin jikina da nake ji ya hanani yi mi shi magana, toh me zan ce mi shi ma bayan kusan duk kalaman nawa sun kare.
gaban lifts muka zo yace na zauna a kan kujera kafin lifts din yazo, na koma na zauna jikina very very weak, not jikina alone har da zuciyata ma is weak.
muna saukowa zuwa reception yace na sake zama ya kira mota, na zauna ni dai bance komai ba, he is caring but he is super caring daga jiya zuwa yau, nasan kuma duka tsoro yake yi kada nace zan bar shi ko guje shi ko zan daina supporting din shi. he feels insecured a halin yanzu gani yake yi he is not enough for me and he do not worth me, gorin da ake mi shi na saka jin kamar shi ba cikakken mutum bane mai daraja kamar kowa, he is going through alot which breaks my heart.
mintina biyar ya dawo yace na taso muka futo muka shiga cikin motar da ta kai mu hotel dinmu, to my greatest suprise sai na ga kayan mu a hade komai ya shirya su waje daya, na kalle shi cikin rashin fahimta nace
“tafiya zamu yi? wani abun ne ya faru?”
take kalar idanun shi ya chanja but he didint say a word kawai toilet ya shiga ya dan jima ya futo, this time fuskar shi a hade kamar hadari.
“na hada miki ruwa shiga kiyi wanka carefully! Doctor yace ki daina hanzari da yawa zai janyo miki ciwon ya dawo”
ganin yanayin shi ya sanya na girgiza kai kawai na shiga bandakin nayo wanka da alwala na futo na rama sallolin da suke kaina sannan na shirya cikin sabbin pyjamas din “victoria secret” na kawo abaya na dora akai na nannade kaina.
ko handbag bai bari na dauka ba, sai ma abinci da ya hadani da shi yace lallai na cinye. sai da ya gama sauka da komai tare da room service sannan ya shigo ya bude ledar magani ya ballo mun nasha ya mayar da su cikin brief case din shi yace na taso muka sauka.
karamar mota ce ta kaimu Jidda, i thought a daren zamu tashi sai naga mun sake zuwa wani hotel din daban, ina shiga dakin na kwanta a kan gado na rufe idona saboda hajijiyar da nake ji ana yi dani, sai kuma bacci mai nauyi ya dauke ni, i think akwai sedative cikin magungunan da nasha na asibitin don a motar ma bacci kawai nayi.
i work up to the phone conversation din da yake faruwa tsakanin Mami da Ya Mahmud, ya ajiye wayar akan mirrow ya saka handsfree yana shiryawa
“Na gaya maka wallahi jikin sa da sauki Mahmud kuma ba tsananin ciwon ne ya akace lallai ku dawo ba, so yake ya ganka kusa da shi Mahmud kasan dai soyayyar da Daddy yake maka!”
a sanyaye yace
“mami idan hakane meyasa aka hanamun jin muryar sa? me yasa na kasa magana da shi? Ya za’ai ace Daddy yana cikin hayyacin shi bai dauki wayata ba? i’m not a kid Mami ki gaya mun gaskiya”
cikin daga murya tace
“Gidanku mahmud! wai qarya zanyi maka ne! na rantse maka fa da Allah toh me kake so nace maka? likita ne yayi gargadi akan kada a yarda ya daga waya sai bayan kwana biyu, allurar bacci ake yi masa”
“im sorry Mami! Allah ya bashi lafiya, flight dinmu karfe takwas ne na safiyar gobe, zamu yi transit a Dubai, jibi zamu sauka a Abuja Insha Allah”+
daga nan suka yi sallama, a hankali na tashi zaune hankalina a tashe, zan sauko daga gadon ya karaso da sauri yana cewa
“be careful- how are you feeling?”
nace
“me ya samu Daddy?”
yayi shiru, na sake maimaitawa sannan yace
“bashi da lafiya amma ba shine dalilin da ya sa zamu tafi ba, ki kwantar da hankalin ki please and have a good rest kafin mu tafi as the doctors said”
na harare shi nace
“as the doctor said, as the doctor said inaga ka manta kai ma doctor din ne for long!”
yayi murmushi kawai yace
“na hada miki ruwa kije kiyi wanka”
Banyi musu ba kuma ban ci gaba da tambayar shi akan jikin Daddy ba tunda na gane shima bai sani ba amma hankalina bai kwanta ba. ina futowa na an shirya mun breakfast akan gado kamar wata sarauniya, shima bance komai ba na zauna naci abubuwan da suka bani sha’awa na bar na bari domin komai cina bazan iya cin komai ba.
ko motsin kirki banyi a wannan dakin ba, ina tashi zai ce “doctor Yace kaza Doctor yace kaza”
sai na sallama nayi kwanciyata ina biyan bashin baccin da naci a makkah da na maganin da ake duramun wanda bansan dalilin shi ba.
finally bayan munyi kwanaki uku a Jidda muka tashi zuwa kasar Dubai, anan ma wani hotel din muka samu kusa da airport muka kwana daya sannan da sassafe muka taso zuwa Nigeria. muna zama cikin jirgin naji wani irin calmness da peace da happiness na komawa gida. lallai there is no place like home kuma kowa ya bar gida toh lallai gida ya bar shi.
kamar kuma ance ciwon ya dawo, bamu dade da zama ba cikina ya fara ciwo, na soma amai kamar zan amayar da kayan cikina, duka hankalin ma’aikatan ya dawo gare ni, su suka gyara seat din namu suka taimaka mana muka gyara jikin mu da aman ya bata sannan na sake wasu kayan na kwanta. maganin bacci ya fara aiki a jikina bacci me nauyi ya daukeni wanda ban farka ba sai da muka sauka a garin Abuja.
STORY CONTINUES BELOW

Na tashi na ga yan tsirarun mutanen da ke tare da mu a first class din firi firi ashe wai jirgin ne yasha tambal tambal da hajijiya kafin ya sauka a dalilin bad weather, ruwan sama ake yi kamar da bakin kwarya ni ina can ina duniyar bacci, da sai dai na farka na ganni a lahira.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
HOME SWEET HOME
Da taimakon Ya Mahmud na futo daga cikin jirgin ina jin wani irin farin ciki na musamman da kewar iyayena musamman Mami da Dada wanda ban taba wata tafiya mai tsayi ba tare da daya daga cikin su ba. da aminiyata Ihsan wadda exams ta saka a gaba ko wayar kirki bama yi, da su Ya Sadik da Ya Omar!
kai har da Baba Rabi….
i miss home! i miss Nigera.
Muna futowa na soma wara idanu na ga su Ya omar sun zo amma sai naga shiru, sai can Faisal ya iso shi kadai tak shima jikinsa ba wani kuzari sai dai yaci yar banzar kwalliya da wani irin yadi da dinkin da tantagaryar yan gayun mazan Abuja ke yayi, ya kafa hula “tangaran” matching color din kayan shi.
yana isowa suka rungume juna da Ya Mahmud wanda ya shima yake sanye cikin traditional attire ta farar shadda mai aikin hannu na coffee din zare, bai saka hula ba kuma bai gyara gashin sa ba, dalilin da yasa kwaliiyar tashi zata yi confusing din ka kenan.
nayi mamaki da nagan shi da kayan a Dubai tunda naga yayi musu yaji sai jallabiya yake sakawa, amma gudun bacin rai ya sanya na tsuke bakina nayi shiru.
“Hajiya Zara welcome home! you guys look soooo fresh Masha Allah— hope you had a wonderful honeymoon”
duka ya Mahmud ya kai mi shi ni kuma nayi gaba ina tafiya don ba wasa muke yi sosai da Faisal ba.
amma gaskiya ya fada munyi kyau ko da hankalin mu ba kwance yake ba, mun rame sosai amma kuma fatar mu da kalar mu ba karamun wulkanci suka karo ba, ni kaina wata yar karamar balarabiya na zama idona yayi fari sol, hancina ya kara tsukewa, ga wani tsayi na godiyar Allah da na karo which makes me more cute.
na saka annakakkiyar abayar amani “nude color” da mayafinta, nayi imanin ko a ethopia za’a sha wahala kafin a samo mace mai rantsatstsiyar kalar fata irin wadda na mallaka
ina so na tambayi mutanen gida da dalilin rashin zuwan su tarbar mu ina jin tsoro, su kan su abokan ba hira suke ba, Faisal tuki yake cikin kwarewa da kiyayewa, Ya Mahmud kuma yayi balance a jikin kujera yana jan carbi sai yayyafin da yake sauka akan gilasan motar wiper tana sharcewa duk bayan sakwanni uku.
garin yayi luf luf da wata irin ni’imtacciyar iska mai sanyi da sanyaya zuciya, furanni sai rangaji suke suna fidda kamshi mai laushi da tausasa kirji.
tafiyar mikakkiya mai tsayin gaske daga airport zuwa cikin abuja amma ban kosa ba saboda kallon yanayin garin yana samun wata nutsuwa da kwanciyar hankalin da na rasa tunda naji rashin lafiyar Daddy
cikin wannan yanayin kawai na ganmu a gaban makeken gidan nan na Daddy na mississippi street.
sai naji gabana ya fadi! me ya kawo mu gidan nan? gidan da kullum dalilin zuwan shi yake kasancewa tashin hankali da tarzoma da abun al’ajabi da mamaki? sai kuma na tuna cewa Daddy bashi da lafiya kuma yana bukatar hutu sannan naji na samu nutsuwa.
Sai da Faisal yaje har kofar shiga cikin gidan sannan yayi parking Ya Mahmud ya bude ya futa sannan ya bude mun nima, na futo ina jin wasu irin mixed feelings da bansan ma’anar su ba. maida kofar yayi ya kulle sannan ya kama hannuna…..
na kalle shi cikin tambaya
yace
“amanar Dada zan mayar mata yanda na karba”
muka yi murmushi Faisal ya wani tura hular shi gaba wai irin bai ga komai din nan ba, which makes him look funny.
kasancewar ba’a kulle kofar ta rufu ba ya saka bamu sha wahalar danna kararrawa ba, Faisal ya bude kofar ya bamu hanya muka shiga a tare cikin nutsuwa.
babu kowa a babban falon na farko, sai tarin takalma a kofar parlour na biyu, muka zarce ciki kowanne da abinda zuciyar shi take saka mi shi
a tare muka shiga cikin falon tare da sallama lokaci daya hannun mu sarke da juna! sai dai me??
wani mugun shock, wani irin mugun shock da al’ajabi da mamaki ne suka dakatar da mu suka tsayar da mu cak kamar an zuke mana jinin jikin mu.
ni dai babu wanda idona ya fara tozali da ita sai wannan matshiyar baiwar Allah da na gani sau biyu a garin Makkah!, na runtse idona na bude ko zan daina ganin ta ko irin gizon da ta dinga yi mun a wancan karon ne amma ina budewa sai na sake ganin ta tarr cikin shigar wata irin riga sakar larabawa mai ruwan gwaiduwar kwai da fari.
wai ina sake daga kaina zan juya sai idona suka shige cikin na dattijon da ke gefenta a kan kujera ita tana daga kasa gefen kafarsa.
wani mutum mai kamala da kwarjini da haibar da ban taba gani a wajen kowa ba, wani mutum mai fari da kyawun da kallo daya zaka yi mi shi bakin ka ya hau tsarkake ubangijin da ya halicce shi authomatically!
wani farin balaraben da bai wuce shekaru saba’in zuwa da biyu ba, wanda wadatar ilmi da addini da hutu da jindadi suka mayar kamar ruwan gold don kyau da haske! idan ba don farin gashin da ya cika gefe da gefen fuskar sa da habarsa ba, da babu abinda zai hanani kwalla mi shi sunan Ya Mahmud saboda tsabar kamannin da suka yi da junan su.
cikin second biyar na gama kare mi shi kallo, kwakwalwata kuma bata yi jinkiri ba ta hankadowa zuciyata bayanai game da shi
“shine Dr Ilyass mahaifin Ya Mahmud”
Duk wata dauriyar da nake da ita malalewa tayi ta zube a wajen nan kafafuna suka soma rawa suna yi mun warning cewa ba zasu iya cigaba da daukar gangar jikina ba…….
ga Mahmud kuwa abun yama fi gaban haka
domin shi yana shiga falon da fuskar Daddy yayi tozali, looking fit and fine har ma da wani karin annuri da nishadi yagani akan fuskar shi, yana shiirin juyawa ya nemo fuskar Mamin shi sai yaci karo da fuskar da ta gigita tunanin shi ta tsayar da numfashin sa tsaye cak! shi kam a cikin second daya ya kalli wannan mutum kuma ya tabbatar mahaifin shi ne ba wani ba, yaso ace yana da sauran kuzari da iko da karfin da zai iya motsa ko dan yatsan sane ya isa da jan jiki gare shi amma bai samu wannan damar ba……
lokaci daya suka koma baya suka yi luuuu dashi daga shi har Zaran zasu fadi kowanne wuta ta dauke mi shi diff!
faisal da ke bayan su ne ya taro Mahmud da saurin gaske, yayinda Ya Sadik yayi tsallen albarka daga gefen da yake ya tallafo Zara parlour ya hargitse da hayaniya.
blurry Mahmud yake kallon Zara ta gefen shi a hannun Sadik babu ko alamar numfashi a tare da ita….. kamar yanda shima nashi numfashin ke dab da daukewa, sai dai bai dauke din ba duk saurin shi sai da sakon da Mahmud yake son isar wa ya futo da karfin gaske ya karade lungu da sakon falon ya kara gayyato wani mugun shock din da ya sanya kowa tsayawa yayi tsit suna kallon shi…….
wani galabaitaccen sauti mai azabar sauri da karfi a lokaci daya yayi amfani da shi wajen cewa
“caaaaaall the docccctooorrrrrrr………….please save her and my child…………..”
Daga nan ya sulale gabadaya a jikin Faisal shima yana kokawa da numfashi.
Assalamu Alaikum my dears
anzo wajen,😁😁😁
A maimakon a dauko likita Daddy umarni ya bayar a tafi da su asibiti gabadaya, cikin gaggawa aka saka su a mota aka yi asibiti da su, Daddyn ne kuma ya hana ayi zuga a tafi, Daga A.laila sai Ya Omar da Faisal ne suka tafi asibitin saboda he is sure shock ne kawai ya saka su cikin wannan halin, yana fatan kuma ana zuwa asibitin za’a shawo kan matsalar. sai dai ya kasa daina maimaita kalaman Mahmud na karshe, wai Zaran is pregnant kenan? me ya kai wannan labari dadi a cikin zuciya on this special day? lallai Allah Al-kareemu ne.
suna zuwa asibitin aka karbe su aka basu taimakon gaggawa, Mahmud ya riga farkawa domin Allah ya taimaka zuciyar tashi bata tabu ba, mamaki ne kawai ya kidima shi, Zara ma Allah yayi saving ta da cikinta, an yi mata duka taimakon da za’a yi mata amma doctor yace lallai ta samu kyakykyawan bed rest na sati biyu……..
jin hakan da Daddy da yayi waya yace idan ta farka a sallamo su gabadaya, in yaso sai a samu nurse ta dinga zuwa gida tana kulawa da ita.
BAYAN AWANNI ASHIRIN DA HUDU
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Cikin dare Zara ta farka, tana bude ido ta ga A.laila a gefenta hannunta akan goshinta yana shafa mata kai.
ta lumshe idanu cikin kasala ta bude sannan tayi kokarin yin magana a sanyaye
“A.Laila dagaske ne? dagaske ba mafarki nake yi ba Baban Ya Mahmud ne da yar’uwarsa muka gani?”
murmushi A.laila tayi cikin farin ciki ta soma yi mata magana
“Duk abubuwan da suka faru Zara ba mafarki bane, everything is real, komai a gaske yake faruwa yau farin cikin da muke ciki ba kadan bane Zara, ga wani sabon farin cikin kuma da kuka sake taho mana da shi, me zamu yi wa Allah idan ba godiya ba?”
+
murmushi kawai Zara take yi, she is too weak to ask all the questions da suke ranta don haka ta koma ta gyara kwanciyar ta taci gaba da wannan mayataccen baccin da ya kasa barinta.
ba ita ta wartsake ba sai washegari da safe, Mahmud kam a gida ya kwana bayan an sha tataburza da shi don cewa yayi kafar shi kafar Zara sai da Daddy yasa baki.
Faisal ne ya dauke shi zuwa mississippi yana bashi labarin yanda zuwan bakin ya kasance
“Friend akwai matukar almara da mamakin cikin lamarin nan, Daddy has done duk wani kokari da zai yi wajen gano inda family din ka suke amma wallahi ko’ina aka bi babu nasara babu wani haske, duk wani taimako nigerian embassy da ke Lebanon sun baiwa Daddy amma an kasa binciko inda family din ku suke a Beiruit.
dalilin da ya sanya Daddy fara rashin lafiya mai tsanani kenan, don ya ga wankin hula na neman kai shi dare…………….
kwatsam rannan da yamma Daddy yayi recieving call daga Daddynka da kan shi, sumewa ne kawai bai yi ba don mamaki da dadi, wannan wayar ce sanadin warwarewar komai, har zuwa shekaranjiya da suka taho bakidaya suka sauka a Abuja bamu san komai game da yanda akai abubuwan suka faru ba.
Anyi tunanin wacce dabara za’a yi muku ace ku taho da gaggawa an rasa saboda kowa ya gane baka da niyyar dawowar a kusa, shine Mami tace maka Daddy ne bashi da lafiya yake bukatar ganin ka.
wannan zaman da akai na jiya saboda tarbar ku ne da kuma warware mana komai sai dai halin da kuka shiga ya katse wannan niyyar.
musamman wani sabon farin cikin da kuka taho mana da shi………………”
Faisal ya dara sannan yace
“friend an kusa zama Daddy!”
Mahmud ya harare shi yace
“duk yayan da kuka haifa mun basu isa a kira ni Daddy ba sai yanzu?”
Faisal yayi murmshi yace
“gumin ka ai gumin ka ne”
Mahmud ya kwada masa duka a kafada ya kyalkyale da dariyar farin ciki. a kullum addu’ar shi ga Mahmud itace Allah ya kawo masa farin ciki da walwala a rayuwar shi domin he has gone through alot, ya ga rayuwa kuma ya sha bacin rai, gashi Allah ya kawo mi shi mafuta a lokacin da aka kusan fidda rai da hakan.
STORY CONTINUES BELOW

suna tafe suna raha suna nishadi har suka isa gidan Daddy!
A cikin wannan falon na dazun dai suka sake samun su, sai dai wannan karon mazan ne kawai, Daddy da Dr Ilyas, da dan’uwan Dr ilyas Khaled, tsayawa Mahmud yayi kyam yana kallon kallo tsakanin Daddy da baban shi, wani irin emotional feeling na taso mi shi, ganin bashi da niyyar motsi sai Daddy ya mike da kansa ya taryo shi, ya kamo hannun shi har zuwa gaban Dr Ilyas ya durkusar da shi a gabansa yana fidda kwallar zallar farin ciki.
Mahmud ya karasa jikin mahaifin sa yayi mi shi wata irin runguma ya fashe da kuka, Dr. Ilyas yayi mi shi kyakykyawan riko yana shafa kansa trying his hardest not to cry shima amma cikin zuciyar sa kukan yake yi soyayyar dan na shi na kara lullube shi. ashe wai watarana zai sake haduwa da Mahmud a karo na biyu, ashe zasu zauna a karkashin inuwa daya har ma su rungumi juna? ashe zai sake samun Mahmud a karo biyu suyi rayuwa?
ya dade da fidda rai da hakan kuma ya sakawa kansa hakuri da salama tunda ya san alkawari ya dauka wanda ba zai taba karyawa ba.
bayan series of crying and hugging and everything sun samu nutsuwa sosai, Mahmud ya koma wajen uncle din shi Khaled ya rungume shi shima, suka gaisa da bebanci domin shi Khaled bai jin inglishi kamar Dr Ilyas shikuma Mahmud babu larabci.
bayan sun gama gaisawa suka yi kalaci tare sannan Daddy yace ya kamata kowa yaje ya kwanta ya huta, it was a long day gobe idan Allah ya kaimu sai a sake zama gabadaya ayi taron.
Daddy yana mikewa Mahmud ya tashi ya bi shi, sai ya kama hannun shi yayi murmushi yace
“tonight you will be with Dr…….. i cant call him your father saboda hakan zai sa naji kamar na rasa ka ne, amma you two need time with each other don Allah ka bi shi dakin sa ku kwana tare”
a sanyaye Mahmud yace
“All he can be is my biological Dad, wanda ya zama silar zuwana duniya, wanda jininsa yake zirga zirga a jikina, amma maganar soyayya da shakuwa Daddy har abadan kaine gaba da kowa a zuciyata! i’m your son, kuma wannan title din ba zai goge ba har abada.
Mahmud is forever yours sai dai ka bada aron sa”
wasu kwalla suka zubowa Daddy Mahmud yayi maza yasa yatsun sa ya goge mi shi sannan ya rungume shi. sai da ya raka shi har kofar shiga dakinsa sannan ya dawo, ya samu uncle Khaled ya shige dakin da aka bashi sai Dr Ilyas kawai a zaune yana shan fruits a nutse.
ya karasa gaban Dr Ilyas a sanyaye ya zauna a gaban shi, feeling wani irin yanayi mara misaltuwa, ga wani peace and serenity na musamman da suka saukar wa gangar jiki da zuciyar sa.
kawai sai ya dora kan shi akan kafar baban, shi kuma ya zagaye shi da hannayen sa yana shafa kansa cikin tausasawa, a maimakon hirar baki da baki, sai ta koma ta ruhi da ruhi, domin ko kwakwkwaran motsi Mahmud bai sake yi ba, ji yake kamar moment din ya tsaya a haka kada ya wuce, ji yake kamar su ci gaba da zama a haka su dawwama cikin wannan kwanciyar hankalin.
bacci mai dadi ya lalabo ya kwashe Mahmud akan cinyar Dr Ilyas ba tare da sanin sa ba, shi kuma bai ko motsa shi ba sai ma sumar sa da yake shafawa yana kwararowa Allah godiya da tasbihi da tasdiqi da kabbara.
sai wajen karfe biyu Mahmud ya bude idanu ya gan shi jikin mahaifin shi kamar a mafarki, yayi maza ya tashi zaune yana cewa
“kayi hakuri na sagar maka da kafa, bansan lokacin da bacci ya kwashe ni ba”
murmushi kawai yayi sannan ya gyara zaman sa, ya soma yi wa Mahmud maganganun da suke makale a ransa
“Mahmud Daddynka Ahmad mutumin kirki ne! ban taba ganin mutum irin sa ba tun da Allah ya halicce ni, ya rufa mun asiri a lokacin da nake dab da tozarta, ya bani a lokacin da bani da shi, ya taimake ni a lokacin da nake cikin wani yanayi na kaka-naka-yi, ya yi mun halacci kuma yayi mun alfarmar da har abada bazan iya yi mi shi sakayya ba!
“Mahmud ni haihuwar ka kawai nayi amma wallahi duk wani duty wanda uba yake wa da Ahmad ne ya fara yi maka su, tun kana cikin cradle din ka ya nuna mun yafi ni sonka, kuma yafi sonka fiye da komai a rayuwar shi, and he lived to prove wannan soyayyar da yake maka har zuwa wannan lokacin. shi din dan halak ne kuma mai cika alkawari ne kuma mai dattako da alkhairi don haka ban yarda ka nuna wata alama ko guda daya wadda zata saka yaji cewa matsayin sa ya chanja a gare ka ba bayan dawowata gare ku, call me Uncle and continue calling him Daddy!
sune sunayen da mukai deserving dani da shi.
STORY CONTINUES BELOW

“Ban yarda ka saba masa ba, ban yarda ka juya masa baya ba komai wuya komai runtsi komai wahala komai dadi!”
wannan daren gabaki dayan shi babu hirar da ta gudana tsakanin Dr Ilyas da Mahmud sai ta karamci da alkhairin Daddy da kuma sadaukarwar shi ga rayuwar su. basu ankara ba suka ji ana kiran assalatu “
WASHE GARI
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Safiyar yau da sauki sosai na tashi, har da wani dan karfi nake ji, likita yana zuwa ya rubuta mana sallama Ya Sadik ya dauke mu zuwa gidan Dada! ashe mazan ne kawai a can mississippi, matan suna gidanmu.
babu kowa a parlour don haka muka wuce dakina A. laila ta hada mun ruwa nayi wanka sosai, ta shigo ta wanke mun gashina sannan muka futo gabadaya zuwa dakin, da taimakon A. laila na gyara jikina na shirya cikin sabon luxury lace ruwan gold skirt and blouse wanda suka karbe ni sosai, ta futa dauko mun saitin kayan gold dina da ke dakin Mami kenan naji sallama, ina juyawa na ga Ya Mahmud cikin shigar yadin kufta ruwan toka babbar riga da hula kamar wani sabon ango! that’s when i realised how much i missed him!
i stood up da sauri naje wajen shi amma sai ya riga ni, yana isowa yayi taking dina into a bone crushing hug which expresses how happy and grateful he is……
maganar A.laila ce ta katse mu, nayi sauri na koma bayan shi na tsaya, feeling soo awkward.
ita kuwa murmushi kawai tayi ta ajiye mun box din jewelry din ta juya ta futa ba tare da tace komai ba.
sai lokacin ya juyo yana mun dariya…….
nace
“dadin ta dai ni ba kunyar A.laila nake yi ba, kalli yanda kake blushing da ta tsaya na tabbatar bayan gado zaka koma ka buya”
bai ce komai ya isa gaban box din ya bude ya taimaka mun na saka sarkar da dan kunnenta tare da awarwaraye guda shida yan siri siri.
na tsaya a gaban madubin ina kallon farin da nayi da wani kyau na musamman kamar an baro ni daga kwai.
“why am i becoming soo cute?Ya Mahmud kaga fa yanda na dawo kamar wata balarabiya, Allah muna hutawa zamu tattara mu sake komawa Saudi duk yanda aka yi sirrin acan yake, just look at my nose…
ya Ilahi wannan kyan ai ko Ya Anis albarka”
karasowa yayi ta bayana ya tsaya shima yana kallona ta cikin mudubin sannan yace
“wannan shine karo na farko da kika je Dubai da Saudi?”
na girgiza kai
“duk lokacin da kika je kina kyau irin haka?”
na sake girgiza kai
“toh why this time?”
na dan juya idona nace
“may be it’s the weather, kasan mun fi zuwa lokacin zafi, kuma skin dina bata son rana”
sai yace
“duk zuwa London da kike yi lokacin spring da winter kin taba wannan kyan?”
na juyo cikin kosawa ina cewa
“what exactly is your Point wai Ya Mahmud?”
ya harde hannu yac
“the point is this time you went there with your love, and he gave you love, and its that love that’s making you glow like this……….”
rufe bakina nayi da hannu ina salati
“Ya Mahmud when did you become naughty? who gave who love? tuna mana! i was the one that performed all the husband duty you just……….”
shima wani salatin ya dauka wanda ya sakani kwashewa da dariya, he knows ba karyan nayi ba, i was the one that made the biggest move, just to make him happy amma he is now claiming i’m glowing because of him.
“Naji naji duka abubuwan da kike fada, zancen zucin a fili kika yi, kuma naji kuma nagode, i will never forget your love and sacrifices but girl…………….
wannan dai glow din dole ki yarda it’s from me”
na tabe baki nace
“prove it”
ya sake yin wata dariyar yace
“The Doctors have proved it already!”
Assalam!
the last two chapters comments are very funny, why are you people this like this? ga center of attraction can balaraben Beirut mahaifin Mahmud amma ku bata tashi kuke yi ba, toh Allah ya kyauta😂
sadly we are in the last episodes, i think we have less than 5 chapters to round up. so keep the commenta flowing as we come to the end of this beautiful love story.
labari na gaba zai zama daya cikin wadannan labaran, i need you to vote so that i can start working on the next story.
1 Wacece ni?
2 Hasken Rayuwata
3 Habibul qalbSai lokacin kaina ya tafi wani dan kwarya kwaryan tunani, right from lokacin da na fara ciwon ciki a Makkah, kwanciyata a asibiti, the bed rest in Jidda, the extra care, all the “doctor said you should do this and stop that” statements, the sleeping, and finally jiya da na suma aka kaini asibiti, i heard clearly lokacin da A.laila tace suna cikin farin ciki sannan muka sake taho musu da wani, i clearly heard the doctor saying i should have 3wks bed rest for the safety of the baby…..
a lokacin sedative na aiki a jikina ban wani bi ta kan maganar ba balle nayi processing din su.
wato…………………
i feel very heavy, emotional and super suprised! sooo soo soon? i am going to be a mother! ya rabb wannan wanne irin almara ne?
sai kuma na sake wani tunanin da ya daga mun hankali, kowa ya sani kenan? kowa yaji? kuma a hakan i will face of all them?
yanzun ma bansan a fili nake maganar ba sai da naji yace
“yes all of them! ni nayi breaking news dina da kaina, Daddy, uncle Ilyas, Dada, Mami da duk wani mahalukin da yake tare da mu jiya ya san you are carrying my child……
Baban Kurfi ne kawai ya rage da Nuratu…….”
zan yi magana kenan A.laila tayi sallama, sai da muka amsa sannan ta shigo da katon tray din da ta cika kayan breakfast akai ta ajiye a tsakiyar dakin
“kuna tsaye kamar wasu zakaru ku nemi waje ku zauna kuyi breakfast, ke Zara ko gaisawa baku yi da su Dada ba balle bakin mu, kiyi sauri ku futo”
ban iya dago ido na kalleta ba, har taje ta dawo da wani tray din mai dauke da cups da ruwa da lemo, nayi maza zan karbe ta ta janye tana cewa+
“me likita yace miki ne? ki dinga kula fa Zara ba’a wasa da lafiya”
ta ajiye kayan ta futa, na juyo na kalli Ya Mahmud da ke ta kunshe dariyar shi na harare shi nace
“kaci bashi na rantse zan rama”
muna kammala cin abincin ya mike yana cewa toh sai ki taso na kaiwa Dada amanarta hannu da hannu kamar yanda ta bani, har ma da kari ta samu saboda albarkata.
na sake tsayawa still sannan nace
“wai Ya Mahmud me ya shiga kan ka ne don Allah?”
yace
“farin ciki da kwanciyar hankali”
nace
“toh Allah ya kyauta”
muna futa falon naci karo da fuskar matshiyar da ta shiga raina farat daya ta dinga yi mun gizau a garin Makkah kamar zata zautani, a yanzu da nayi mata kallon tsaf nagane zata yi sa’ar Ya Nuratu, sai kanwarta da ke gefenta wadda ba zata fi shekara shatakwas zuwa ashirin ba, ita kam basu yi kama sosai ba sai dai farin ta da yake barazanar kashe mun ido.
daga kan kujerar da kebayan su kuma wata balarabiya mai kamar shekarun Mami kyakykyawar karshe sai murmushi take zubawa.
Nayi ajiyar zuciya na kalli gefen dama inda Dada ke zaune da Mami a kasan kujerar ta, na tafi da sauri na fada jiki Dada na rungume ta ina hawayen da bansan ko na menene ba.
“haba Zahra’u kukan kuma na meye? me yasa kike son ki zama baure ne da an taba ki sai kuka? ai murna zaki yi da farin ciki ba kuka ba! dakyar ta shawo kaina na daina kukan na zauna sannan na gaishe da Mami, ta amsa cikin far’ar da na dade ban ganta a ciki ba.
“are you Zara?”
wata murya me shegen zaki ta shige kunnena
na dago ina kallon matashiyar da sautin ya futo daga bakinta. wannan yarinya Allah ya zuba mata kyawun halitta da dadin sauti.
A.laila ce ta soma gabatar mun da su cikin harshen turancin da duk su ukun suke ji.
ta nuna babbar mace tace
STORY CONTINUES BELOW

“This is Umm Ikhlass matar baban Mahmud”
wannan kuma sunan ta “Eesha” ta nuna mun matar da na gani a Saudi
itace yarsu ta farko sannan wannan
“Ikhlass”
ta nuna mun karamar, dukansu sai far’a suke mun hakoransu suna haske fuskata.
umm Ikhlas ta bude mun hannu na isa gabanta ta rungume ni tana yi mun addu’a da harshen larabci har da ce mun wai kyakykyawa don karfin hali.
bayan ta sakeni Itama Eesha ta rungume ni tana dariya, na yarda soyayya gamon jini ce, domin wannan baiwar Allah tun ranar da na fara ganinta naji ta kwanta mun a rai kuma na yarda da ita dari bisa dari.
Ya Mahmud gabadaya bakin shi yaki rufuwa, sai magana yake zarowa wadda daga ji farin ciki ne yayi mi shi yawa yake zaro ta! ya dade damu a zaune sannan ya mike yace zai tafi, daman jikina yazo dubawa, a gaban su Mami fa ya kalle ni yace
“Do you need anyting?”
nayi kamar ban gane da ni yake ba sai ma mayar da hankalina da na sake yi akan Eesha wadda take bani labarin zumudin da suka dinga yi kafin mu iso su ganmu, ita kanta tana mamakin kamar su da Ya Mahmud duk da tace daman Uncle Ilyas yana gaya musu.
“zara zo ki karbi sako”
muryar Ya Mahmud a karo na biyu bayan yayi sallama da su Dada ya isa bakin kofar futa. i was embarrassed wlhy yanda kowa ya kalleni ya kalle shi, i dont know abinda ya shiga kan shi, but definately da akwai domin ba haka yake ba kuma bai saba yin hakan ba, especially a gaban manya.
a dole na mike na bi shi waje, yana gaban motar shi a tsaye ya sarke hannunawa yana murmushin da yanzu sam baya rabuwa da fuskar shi. raina a bace nace
“Don Allah Ya Mahmud wai ina kunyar ka da kawaicinka suke ne? manta su kayi a Makkah ko Jidda mu koma mu dauko?”
cikin murmushi yace
“lala lala! siyar da su nayi na siye farin cikin da nishadi da soyayya”
na bude baki kawai ina kallon shi
“Yes! i’m a new person! a changed person! and the happiest person on this planet………..and also the newest Dad in town”
nace
“zan koma ciki idan ka gama”
sai kuma ya koma serious
“Zara gobe za’a yi taron family, yau ya kamata a zauna sai Dada tace lallai sai Kawu Sulaiman da Inna Badi’a da Baban Kurfi sun iso, ta gaya musu tana neman kowanne kamar wancan taron da ta tara a baya!……….”
sai kuma yayi shiru sannan ya bude mun gefen shi yana cewa
“come and have a seat zaki gaji, doctor said ki daina tsayuwa”
“i hate this “doctor said” maganganu don Allah”
yayi dariya yana cewa
“sorry! zagayo ki zauna”
ina shiga motar ya tayar da ita ya ja, cikin tsoro na soma magana
“me kake nufi? ina zamu je Ya Mahmud don Allah ka rufa mun asiri kaga fa ko gaisawa bamu gama yi da su Dada ba………”
tuni an wangale mi shi gate har ya hau titi ya soma tafiya, idon shi akan hanya kamar ba da shi nake magana ba.
“kasan Allah yanzu a Nigeria muke ba’a Saudi ba, na daina daga maka kafa! ka mayar dani gida, idan na fara nawa tantrums din ba zaka ji da dadi ba”
“i will welcome them happily with love”
sai nayi shiru da bakina saboda naga asarar kalamaina nake yi shi kuma neman magana kawai yake yi, banyi aune ba kawai sai ganin mu nayi a gidan Daddy!
na kalle shi nace
“Yanzu don Allah ka kyauta kenan? ko waya ta ban dauko ba banyi sallama da kowa ba kawai sai tashin mota suka ji mun futo kuma ka kawo ni nan bayan ba kai ya kamata ka kawo ni ba……”
bude motar yayi ya futa bayan ya gama parking sannan ya zagaya ya bude mun, i have no choice dole na futo na maka mi shi harara. yace
“naji dai tunda idon ba fadowa zai yi ba ai da sauki”
a falon farko muka samu Daddy da Uncle Ilyass da Khaled suna zaune akan babban tattausan farin kilishin da aka shimfida a tsakiyar falon suna shan tea, tea irin nasu na larabawa wanda basa iya rayuwa babu shi.
a kunyace na rakabe gefe guda na zauna jikin kujera na sunkuyar da kaina ina jina a takure, wannan balaraben yana da wani irin effect a kaina da yake hanani nutsuwa, kwarjinin sa yayi yawa.
“zara kamar wata bakuwa? shigo ciki sosai, waye bakon ki anan?”
cewar Daddy cikin murmushi.
kafin na motsa naji wata murya mai taushi tana cewa
“zara dukanmu iyayen ki ne, ki dauke mu kamar Ahmad ki daina jin kunyar mu”
cikin turanci yayi maganar, amma shi kanshi accent din turancin na shi abun begen saurare ne, so daga wajen mahaifin su suka gado dadin sauti kenan? domin daga Ya Mahmud har Eesha din da Ikhlas idan suna magana baka so su daina, musamman su idan suna yaren larabci, sai kiji kamar karatu suke biyawa.
a nutse na mike na karasa kusa da su na gaishe su cikin ladabi ba tare da na kalle su ba, duk yanda suka yi kokarin jana da hira basu samu amsa ta ba domin in dai Uncle Ilyass din nan yana nan bazan iya motsin kirki ba.
Daddy ne ya mike ya shige study room sannan ya kira Ya Mahmud yace mu shigo tare, ashe daman kiran nasa ne. bayan mun zauna ya soma yi mana bayani kamar haka
“Kafin kuyi wannan tafiyar akwai maganar biki da na jinkirta nace zanyi, toh daman ba wani abu nake fata ba illa Allah ya taimakeni na gano Dr Ilyass ko danginsa a karasa bikin da su! ba karamar wahala nasha ba, ba karamar addu’a nayi ba akan wannan al’amari kuma wani abu bai taba tsayamun a rai kamar wannan ba, sai dai cikin taimakon Allah da tasirin addu’a sai Allah ya cika mun burina.
saboda haka na yanke shawara idan Allah ya kaimu ranar goma sha shida ga wannan watan, in two weeks kenan, za’a gabatar da bikin, duk wani wanda ya kamata yazo daga bangaren Dr zan dauki nauyin visa da ticket da accommodation da sauran abubuwan bukata har ayi biki a kammala, ko da sun kai su dubu ko sama da haka i will welcome them wholeheartedly da murna da farin ciki da jindadi.
gobe idan Allah ya kaimu za’ayi taron family, irin wanda aka yi kwanakin baya akan ka Mahmud! yanda aka tara kowa da kowa aka fede biri har wutsiya akan tarihin ka, haka za’a sake tara kowa da kowa a gabatar musu da ahalinka da tushen ka da nasabar ka kowa yaji ya gani. kaga ikon Allah ko? kaga sakayyar hakuri da dogaro ga Allah ko? kaga cikin kankanin lokaci yanda Allah ya sauya al’amura ko? hakika Allah yana sona Mahmud! Allah ya ga niyyata ya ga nufi na kuma ya ga zuciyata, ya kawo mun mafita a lokacin da nake cikin bukatar ta! Allah ya futar dani kunya a lokacin da makiya suke gab da yi mun dariya saboda haka bani da sauran buri a duniya sai fatan cikawa da imani!
Allah ne ha hada ni da kai Mahmud saboda haka babu wanda zai iya raba mu sai dai mutuwa. “
Daddy ya share kwallar da ta saiko masa, nima na share tawa, daman sarkin kukan tuni ya fara na shi har da shashsheka da ajiyar zuciya.
“Mahmud na kira ku ne don naji menene plan din ka bayan anyi biki? me ka shiryawa rayuwar ku? kafin nasan abinda zanyi”
sai da ya bata lokaci yana goge hawayen shi
“common Mahmud wannan saurin kukan na ka dole ka ajiye shi a gefe, ka zama babba fa! you will be a father soon gayamun idan babyn yazo taruwa zaku yi ku dinga kukan tare?”
kamar karamun yaro haka Ya Mahmud ya saka hannuwan shi biyu a fuska yana blushing wai yaji kunya kenan! shikuma Daddy ya soma dariya, daman bashi da burin da ya wuce ya tsokani Mahmud ya fara wannan jin kunyar kamar mace.
idan yana gaban Daddyn wani babyn shekara daya yake komawa shikuma Daddyn ya dinga biye masa.
kai kuma da kake gefe a irin wannan lokacin zaka fahimci tarin soyayya da kauna da amincin da yake tsakanin su kamar yanda nake yi yanzu.
sai da ya nutsu sannan yace
“Daddy ina son zaman London ina son career ta amma kuma lokaci yayi da nayi shawarar barin London gabadaya na tattaro na dawo gida. i need time with you! wannan lokacin nafi bukatar ku fiye da komai a rayuwata don haka na yanke hukuncin yin sallama da London zan dawo Abuja as soon as possible!”Daddy ya sake share kwallar farin ciki, yana mafarkin ranar da zai raba Mahmud da kasar turai ya dawo yayi aure yayi settling ya zauna a tare da su kamar su Sadik da Omar! ya dade yana tunanin ranar da zai cika wannan burin har ma ya fidda rai domin ya fahimci cewa Nigeria bata ran Mahmud kuma bashi da marmarin sake zama a cikinta tun bayan mutuwar Jawahir. wai yau gashi Allah ya cika masa burin sa Mahmud din da bakin sa yace zai dawo gida? wai shi kam wacce irin godiya zai yi wa Allah?
“Idan hakane sai ka duba tsakanin gidajen Maitama da na Asokoro ka zabi wanda yayi maka, idan kuma babu irin tsarin da kake so ka nemi Abdussamad(architect din company) ko Omar ka gaya musu tsarin da kake so sai a soma aiki.”
wani kasaitaccen murmushi Mahmud yayi, yana tunanin irin son da Daddy yake mi shi a ran shi kuma yana dariyar yanda akai Daddyn bai san komai game da shi ba. but it’s time da ya kamata ya dan fasa wani kwai ko guda daya ne. don haka ya gyara zama ya soma magana+
“Daddy nagode Allah ya saka da alkhairi! amma this time ina neman alfarma ka barni a karo na farko nayi wani abu da kudina don Allah Daddy! kayi mun komai amma ka bar mun hidimar wajen da zamu zauna i will take care of that”
Daddy yayi murmushi yace
“nayi maka Mahmud nayi maka”
sannan ya sake cewa
“game da aikin ka fa? what is your plan?”
ya sake gyara zama yace
“Daddy wannan ma i will take care of it kar ka damu”
Shiru Daddy yayi yana nazari akan maganganun Mahmud yana kuma tabbatar da zargin da ya dade yana yi akan shi amma sai yayi shiru da bakinsa yabi shi da yanda yake so.
Daddy ya dawo da kallon shi gare ni yace
“Toh yarinyar Daddy kuma me take shiryawa? meye plan din ki?”
murmushi nayi mai sanyi ina jaddada karamcin Daddy a gare mu sannan na sanyaya murya nace
“Daddy bani da wani plan sai wanda kuka shirya mun”
ya sake fadada murmushin sa yace
“ni burina idan komai ya kammala kunyi settling ki koma makatanta! bana son karatun ki ya lalace, karatu na da matukar muhimmanci a rayuwar mace! bayan haka kuma na baki zabi idan kina da sha’awar wani business da kike so zan baki jari da wajen zuba kayan sana’ar amma sai kinje kin tsara business plan din da komai kin kawo mun na duba nagani kafin nayi approving da kuma yarjejeniyar cewa karatu da sana’a ba zasu hana ki gabatar da wife duty dinki ba, komai zaki bashi lokacin sa kuma zaki tsare kan ki daga kawayen banza da mutane barkatai. idan kika fara naga alamar halayenki suna son chanjawa nayi miki alkawari zaki koma full house wife”
kawai murmushi nake yi na kasa cewa komai domin kamar Daddyn zuciyata ya shiga ya karanta abinda yake cikinta. me zamu yi mu sakawa wannan bawan Allah da alkhairin da yayi mana a rayuwa? me zamu yi mu gode masa?
a sanyaye na soma yi mi sho godiya yayi maza ya dakatar dani sannan yace
“game da shirin biki duk zaku ji alert kowa yaje ya shirya, inason ku gayyaci kowa da kowa, inason wajen bikin ya cika ya batse da mutane! inason a san cewa biki nake yi bikin yayana kowa yazo yaci yasha yayi nishadi yayi farin ciki ya kuma shaida cewa dana yana da asali da nasaba da dangi irin wadanda za’a nuna a ko’ina ayi alfahari da su.”
Duk mu kai murmushi! Mahmud yayi gyaran murya yace da Daddy
“Daddy!”
sai kuma yayi shiru
Daddyn ya kalle shi yace
“ina jinka me kake so kace?”
ya sanyaya murya yace
STORY CONTINUES BELOW

“Daddy wata alfarma ce nake nema a wajenka alfarmar da duk duniya babu wanda zai iya yi mun ita, kuma idan kayi mun har abada bazan sake neman wata alfarmar a wajenka ba”
daga ni har Daddyn kallon shi muka yi muna mamakin wacce irin alfarma ce kuma tsakanin su wadda ba zai iya futowa direct ya furta ba? wacce sauran alfarma Daddy zai yi masa? me yasa ma ya kira bukatar da alfarma?
cikin kwantar da murya Daddy yace
“alfarma kuma Mahmud? akwai alfarma a tsakanin mu? kowacce bukata kake so a wajena ka fada kai tsaye ba sai ka nemi alfarma ba, duk abinda kake so ni mai yi maka idan har zan iya da karfina da aljihuna.”
ya sake kwantar da murya yace
“Daddy ka amince zaka yi mun ba tare da na fada ba don Allah i promise ba zaka yi danasanin amsa mun ba”
Tunani Daddy ya tafi na wasu dakiku, toh wannan wacce alfarma ce? anya kuwa? sai kawai ya tuna ranar da ya kira Mahmud yace masa ya saka hannu cikin takardun nan na kadarorin sa kuma ya saka bai nemi ba’asi ba ya kuma yi mi shi wasu maganganun da duk lokacin da ya tuna yake jin kaunar Mahmud tana ninkuwa a zuciyar sa
“Daddy ka zartar da duk hukuncin da kake so a kaina kamar yanda za ka juya yan yatsunka, ko su sunyi maka gardama Daddy zuciyata zata kasance mai biyayya a gare ka”
ya sake cewa
“Ko mutuwa ka aiko wajena zan mika wuya ta dauke ni da tunanin cewa kasan itace tafi dacewa dani a wannan lokacin, babu takura ko cutarwa a tsakanin mu Daddy idan har kaga ban aure ta ba toh sai dai idan bana raye ko kuma kai ne ka dawo kace ka fasa! menene umarni na biyu?”
wannan tattaunawar ta gudana ne a ranar da yayi kiran Mahmud wannan gidan ya umarce shi da sanya hannu a takardun dukiyar shi ya kuma ba shi umarnin auren Amina yar gidan Alhaji Ibrahim mai Atamfa.
Ya za’ai ya manta da biyayya da sadaukarwar Mahmud a gare shi! ba tare da wani dogon tunani ba ya amsa da cewa
“Na amince Mahmud da kowacce irin bukata ce komai girmanta! Bama ita kadai ba, da ita da duk wata bukatar da zata biyo bayanta a shirye nake da na biya maka su in dai har ina da ikon yin haka”
Mahmud yayi lallausan murmushi yana hamdala a cikin zuciyar shi sannan yayi wa Daddy godiya.
Daga nan suka yi sallama suka futo zuwa falon gabadaya, Zara ta tsuguna a gaban Uncle Ilyas tayi mi shi sallama, ya amsa fuska a washe cikin matsananciyar kauna da jindadi sannan tayi wa Khaled irin maganar da suke yi da shi da ido da hannu shi kuma ya amsa da yaren larabci yana saka musu albarka.
Mahmud kam ya gama sabawa da su, kai ba zaka ce kwanakin su biyu ne kawai tare ba, don karfin hali wai har hausa ya fara koya musu, idan ana lesson din sai cikin ka yayi ciwo.
Gidan Dada ya mayar da ita bayan sun futo daga gidan Daddy, bai shiga ba yace sauri yake yi zasu hadu da Faisal yanzun nan, yana rufe baki motar Faisal din tana shigowa cikin gate din gidan Dada!
Ganin Ihsan a gaban mota ya sanya ni balle murfin mota na futo da sauri kamar yanda itama tayi, cikin wata irin murna muka rungume juna kamar zamu tsaga kashin juna mu koma abu daya
sai da Faisal yayi mana magana sannan ta sake ni tana kare mun kallo!
“iyeee! did you see yourself kuwa? kinga yanda kika dawo babes?”
Na juya idona dramatically nace
“yes dear i know”
muka kyalkyale da dariya, Ya Mahmud yace
“wai me yasa idan kuka hadu hankali yake muku karanci ne? a kofar gida fa kuke? ku shige ciki don Allah”
Sannan muka juya muka shiga cikin muna kankame da juna muna dariya. wannan ya goge mun kunyar shiga cikin gidan ni kadai.
Mami na ganin mu tace
STORY CONTINUES BELOW

“ahaf! ai na san ba zata wuce su din bane! ai ban ga ranar da wannan yaran zasu girma su daina shashanci ba”
Ihsan ta janye jikinta cikin jin kunyar ganin su Umm Ikhlass ta koma wata ustasiyar karfi da yaji, ta isa gabansu suka gaisa cikin karrama juna da mutuntawa. dakyar muka samu kan mu muka shige cikin daki muka soma hirar yaushe gamo
“You look absolutely gorgeous Zara! i wish haka zaki ci gaba da kyau in your next trimesters”
na balla mata harara na sauya maganar da cewa
“saboda rashin m nayi tafiyar ma na dawo ba zaki taho mun da Amani na ganta ba, Ihsan you are a wicked mum!”
dariya tayi tace
“ke wannan yarinyar barin ta a gida shine kwanciyar hankali, duk inda muka je sai tayi musu barna kafin mu taho, kuma bata son mota, da wuya mu futa mu koma gida bata yi amai ba, wataran haka zamu hakura da unguwar mu koma gida ta lalata mana kaya da mota”
nace
“don ba kya futa da ita koda yaushe ne bata saba ba! ko kuma ki dinga tafiya spare kaya a leda sai ki chanja idan kinje inda zaki je”
tace
“Toh Mammy Zara! you will soon join the claque ai zaki gane darasin”
sai yamma Ihsan tayi mun sallama ta tafi, Easha ta shigo dakina muka zauna muna sabuwar hira da alama kamar yanda ta shiga raina nima haka na shiga ran ta, anan take bani labarin cewa tana da aure har da yara biyu Ayman da Fattu a Qatar suke zaune.
nace mata ina yaran tace
“Suna can Qatar suna school nima Umrah muka je ni da baban su, acan naji cewa an samu labarain dan’uwana Mahmud, daga can ni na yanki ticket na taho na shikuma Abdallah ya koma Qatar”
Anan nake bata labarin ganin su da nayi a cikin shop da yanda suka bace mun da wahalar da nasha akan neman ta!
Tayi ta mamaki tana al’ajabi ni ina ganin kamar ta subuce mun kenan ba zan sake ganin ta ba sai gashi ta riga ni zuwa gida ma. That’s the power of a sincere Du’a!
Mun sha hira sosai, lokaci guda muka saba kamar daman mun san juna mun zauna tare, sai da aka yi kiran sallar magrib sannan ta koma dakin su,(Dakin da A.Laila ta zauna)
Nikuma na saka hijab na shiga dakin Dada, na same ta tana karatun ta na bayan magriba don haka na juya zuwa dakin Mami! knocking nayi ta bani damar shiga sannan na bude kofar na shiga a nutse!
Tana zaune a kan carpet da katuwar akwati a gabanta wanda ke makare da designer baby wears irin wanda bata rabo da siyo su idan tayi tafiya saboda sha’awar da suke bata, ana yi mata haihuwa zata janyo ta zaba ta hada da atamfa ta kai barka wasu lokutan ko bakuwa tayi mai dan baby sai kiga ta shiga ta hado mata kaya…………….
Mami kenan!
cikin murmushi na karasa kusa da ita na zauna ina cewa
“Mami waye kuma ya haiwu aka janyo wannan akwatin? Mami kiyi ta saka uban kudi kina jibgo kaya kawai kina rabar wa yayan mutane”
“Toh idan ban rabawa yayan mutane ne ba ya zan yi da su tunda ni ba yayan da zan sakawa ne da ni ba?”
Nayi murmushi nace
“sai ki daina siya”
tace
“Da yake da kudin ki nake siya sai ki hanani”
ture jakar kusa dani nayi zan bude ta tayi maza ta rike hannuna tana cewa
“kar ki ja wannan kayan da nauyi! ki daina wannan dan banzan garajen naki ki dinga lallaba lafiyar ki”
Murmushi kawai nayi na barta ta gyara mun akwatin ta bude mun, gabadaya baby wear din gucci da versace ne masu azabar kyau.
na dago na kalle ta ina cewa wannan
“wannan kuma Mami?”
ba tare da ta kalle ni ba tace
“Da ke da matar Mahmud nake wa tanadi duk lokacin da nayi tafiya sai na siya, without knowing that kece matar Mahmud din kuma kece Zara! so gabadaya na babyn da zaki haifa ne”
mayar da murfin nayi na rufe da sauri ina rufe fuskata da mayafina
ta kalleni tayi tsaki sannan tace
“Daga baya kenan! Gobe naso muje asibiti a nan garin ayi miki check up, amma saboda wannan taron zamu bari sai jibi! nayi magana da Mahmud akwai aminiyar Jawahir, Dr Sa’ada wajenta zamu je kwanan nan ta dawo daga Florida ance ta iya aiki sosai”
Ni dai ban ce komai ba har ta karaci maganganun ta ta sauya maganar zuwa taron da za’ayi gobe, ranar a dakinta na kwana muka raba dare muna hira peacefully. anan nake tambayarta akan maganar case din su da Alhaji Muktar tace ana nan anayi ba’a kammala ba, amma tunda kudinta suna hannunta kuma babu igiyar auren shi a kanta ita bata da damuwa.RANAR TARO
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
A wannan babbar rana wadda family din Dada ba zasu taba mantawa da ita ba, kanannadden qullin da yayi shekara da shekaru a kulle ya kunce, komai ya warware gaskiya tayi halinta, karya taji kunya.
A cikin gidan Dada, a babban dakin da kwanaki ta hada irin wannan taron akan tona asirin alakar Daddy da Mahmud wanda yake ta rairaito yana riritawa tsayin shekaru talatin da tara, ta baje komai a faifai ta kuma tauna tsakuwa don aya taji tsoro sannan tayi kyakykyawan kashedi da kuma nasiha mai ratsa gangar jiki da kwakwalwa.
A wannan taron Daddy da Mahmud sun sha kuka, sun sha kunya, sun sha gori, sun sha kunar zuciya da takaici da duk wani mahalukin da yake kaunar su.
A wannan karon ma haka aka sake taruwa karankataf kwai da kwarkwata har ma da qarin idanun da babu su a wancan zaman, domin musamman Daddy ya kira babban aminin shi Ambassador da kuma roke shi da ya bi hanyar da zai kawo mi shi Alhaji Ibrahim mai atamfa wannan taron, ya sake gayyato iyayen Aisha yace suma sun zama family suzo su kasance shaida, domin Daddy ji yake yi kamar ya gayyato duka mutanen duniya ayi wannan taron a gabansu, kamar ya saka masu daukar vedio suzo suyi recording su yada a media kowa ya gani. Don haka ya dinga kalato mutane da gangan yana cewa suma sun zama family, ko Inna Badi’a sai da ya gayyato maigidan ta yace shima family ne.
A daren ranar Baban Kurfi ya sauka, sun taho tare da A.Laila wadda ta kai mijinta da yayanta ganin gida bayan dawowar su, sati daya kenan da saukar su a Nigeria sun kammala komai sun tare a gidansu na garin Abuja.
Cikin mamaki sai ga Ambasada da Nuratu da asubahin wannan rana, Ambasada yace ko jiya ta koma ai dole yau ta dawo ta halarci wannan taron ta kuma taya Mahmud murnar ganin dangin shi. Nuratu tayi kukan godiya ga Allah da farin ciki, domin wata irin mu’amala ce a tsakanin ta da Mahmud irinta aminai ko wa da kanwa, babu wanda take jin dadin sharing din secret din ta da shi kamar Mahmud kuma yana matukar bata shawara da kulawa fiye da tunanin me karatu.
+
A wannan ranar idan ka tona zuciyar Mahmud tafi auduga da nono haske, wani iri yake jin sa a wannan rana kamar sabuwar haihuwa kamar yau din ya bude idanu cikin rayuwa kamar a cikin gajimare yake yawo, kamar a cikin mafarki!
Nikuwa a ranar tashi nayi da matsanancin zazzabi da kumallo wanda ya sanya muka dangana da asibiti, sai da aka kara mun ruwa leda biyu sannan naji karfin jikina, a son ran su ma sun fi bukatar su rike ni amma ganin Ya Mahmud is a doctor and he will take care of me sai suka yarda suka bani sallama.
sai A.laila ta wuce dani gidanta saboda hayaniya da kuma sa’idawa.
Ya Mahmud ne da Faisal suka kaimu asibitin suka kuma dauko mu, bayan sun kaimu gidan A.Laila suka wuce Mississippi tare.
sai gab da la’asar na samu nayi wanka na shirya cikin shadda kamfala dakakkiya mai kala buiyu, pitch and purple dinkin bou bou ne dai dai jikina an kawata shi da zaren surfani mara hayaniya, na kawo saitin english gold na saka sannan na tattara gashina a keya na daura dankwalin samfurin da ake yayi na gaban goshi. ko da ba make up nayi ba, nayi kyau.
A.Laila ta saka mu a mota da yaranta muka iso gidan Dada, lokacin kowa ya hallara a cikin dakin taron an soma addu’o’i.
Babu wanda bai zuba mun idanu ba, na share na isa gaban kujerar Dada na zauna akaci gaba da addu’a sannan aka shafa! a wannan lokacin Ya Mahmud da family din shi ne kawai babu a wajen, nayi mamakin dalili amma sai na gyara zama domin ganin show din da Daddy ya shiryawa yan kallo.
mikewa yayi kamar wancan lokacin, ya fara da bismillah da godiya da ga Allah da salatin Manzon Allah saw sannan ya dora da bayani kamar haka
“Hakika wannan rana ta kasance rana mai matukar muhimmanci da daraja da farin ciki a gare ni!
Na rayu tsayin shekaru ina fatan zuwan ta, har na soma sarewa, har na soma fidda rai, amma da yake alkawarin Allah ba ya tashi, kuma duk wanda ya dogara da Allah zai isar masa sai gashi komai yazo ya faru kamar a cikin mafarki, komai ya faru cikin farin ciki da kwanciyar hankali!
Ba tare da dogon sharhi ba ina mai matukar farin cikin gabatar da muku da mahaifin Mahmud da yan’uwan shi! kamar yanda na fada a wancan lokacin, Mahmud dan halak ne kuma ya futo daga tsatso na alfarma cikin tushen musulunci amma ba kowa ya gasgata ba saboda hassada da son zuciya! toh daman ance gaskiya dokin karfe kuma ranar wanka ba’a boyon cibi! A yau zan gabatar muku da dukkan shaiduna wanda zasu tabbatar muku da gaskiyata da kuma gaskiyar tsakanin mu da Mahmud! Don haka manyan baki idan kuna jina don Allah ku futo.
STORY CONTINUES BELOW

A hankali daya daga cikin kofofin da suke cikin dakin taron ta bude, wanda ya murda kofar ya soma futowa matashin shekaru talatin da tara ne har da watanni, dogo sosai, fari tas mai wata irin haiba da kamala da sassanyan kyau mai kwantar da hankali, kallo daya zaka yi mi shi ka tabbatar daga kabilar larabawa ya futo musamman idan ka kalli kwayar idanun shi da yanayin gashin kan shi mai kama da an kifa kwando, da kuma yala yalan sajen shi wanda ya kewaye fuskar shi.
Yana sanye cikin dakakkiyar shadda hilton ruwan sararin samaniya, babbar riga da yar ciki sun sha aikin zare mai kayatarwa, ya kawo hula zannah kalar da ta dace da kayan ya murza akan gyararriyar sumar sa wadda ta sake futo da class din kwalliyar tashi.
ba kwalliyar ce kawai za ta dauki hankalin ka ba illa dandasheshen murmushin da ya fiddo da annurin fuskar shi! wani irin murmushi me fallasa halin da zuciya da kwakwalwa da gangar jiki suke ciki. murmushin da yake tabbatar wa da duk wanda kalla cewa Yana cikin matsanancin farin ciki da murna da kwanciyar hankali.
Yana futowa ya ja ya tsaya domin baiwa mahaifin shi hanya, sai ga matsakaicin dattijon da zai dan dara Daddy shekaru da kadan ya futo, idan ka dauke yar furfurar da ta kewaye sajen sa da gashin kansa, ka cire bambamcin wasu shekaru jikinsa, toh komai da komai nashi irin na Mahmud ne, har tsayin su da kalar fatar su da tsinin hancin su, da idanunsu, zuwa yatsun su.
komai hassadar mai hassada komai karyar makaryaci komai musun me musu bai isa ya kalli Mahmud ya kalli wannan bawan Allah yace ba da ne da uban shi ba. kamar is tooo much, komai nasu iri daya ne sak, bambamcin shekaru ne kawai zai iya sakawa ka bambamce su.
Tunda Daddy ya fara magana hantar cikin Inna Badi’a da Kawu Sulaiman da Alhaji Ibrahim mai atamfa ta wuntsila, idanun su suka futo waje, madaukakin tsoro da mamaki da bakin ciki ya kama su, a lokacin kuwa da Mahmud ya bude kofa ya futo mahaifin sa ya biyo bayan shi, ji suka yi kamar saka kibiya mai tsini an soka a kirjin su, wani irin shock suka shiga irin wanda basu taba shiga irin sa ba, madaukakin mamaki da almara suka toshe musu duk wata nutsuwa da basirar da take cikin kawunansu.
A nutse Mahmud ya kamo hannun Uncle Ilyas suka iso cikin falon, Umm Ikhlas, Eesha da Ikhlas suka dafo bayansu cikin shigar su ta larabawa da kamshin oud mai dan karen dadi, sai aka hau kallon kallo! waje yayi tsit zukata suka cika da mamaki da rudani da matsanancin al’ajabi. a wannan lokacin idan aka tsaga jikin Kawu Sulaiman da Inna Badi’a ba lallai a samu jini ba.
Bayan sun zauna Daddy ya kama hannun Dr Ilyas ya tayar da shi tsaye sannan ya soma bayani
“Wannan shi ne aminina kuma abokin aikina Dr. Ilyas kuma shi ne mahaifin dana Mahmud! shi ne ya mallaka mun abu mafi girma da daraja a duniya a lokacin da nake tsananin bukata, shi ne yayi mun karamcin da har abada ba zan manta ba kuma ba zan iya biyan shi ba!”
Ya dubi Dr Ilyas yace
“Dr kayi musu bayani don Allah daga bakin ka akan yanda aka yi ka bani Mahmud da kuma abubuwan da suka faru bayan rabuwar mu, sannan ina so na san yanda aka yi kaji labarin ina nemanka a wannan lokacin har ka samu lambar wayata ka kirani! ina so ka warware mana komai a wannan taron!”
Daddy ya dubi Ya Omar yace
“Taso ka tsaya anan, idan yayi magana da turanci ka fassara da hausa saboda Dada”
Ya Omar ya koma gefen da zai yi aikin tafinta ya tsaya, Dr Ilyas ya bude bayanin sa da sunan Allah da salatin ma’aiki saw sannan ya dora da na shi bayanin
“Kamar yanda Ahmad ya gaya muku alakar mu da shi tayi karfi me a dalilin soyayyar su da Easha wadda Allah bai nufa shi ne zai aure ta ba, asali ma ni na shiga tsakanin su ne saboda na ga ya samu damar bin umarnin mahaifiyar shi ita kuma na tabbatar da cewa bata shiga wani hali ba, toh a cikin hakan Allah yayi ikon sa, kaddarar aure ta fado a tsakanina da Easha muka yi aure, sai daga baya ne muka gano tana dauke da ciwon zuciya. Easha ta mutu ba tare da bude idanu ta ga abinda ta haifa ba, ta rasu ta bar Mahmud a lokacin da yafi bukatar ta fiye da kowa.
“A wannan lokacin tunanina bai wuce yanda zan bai wa Mahmud farin ciki da rayuwa mai inganci ba, yanda zan kula da shi ba tare da maraici yayi ma sa wata illa ba, yanda zan raine shi da tarbiyya da so da kauna. sai dai a duk lokacin da na tuna cewa dangina ba zasu karbe shi ba sai naji komai na rayuwa ya fuce mun a rai, a duk lokacin da na tuna kalubalen da zan fuskanta akan shi sai naji tsoro da fargaba da tashin hankali sun lullubeni.
“A haka na soma rainon Mahmud cikin damuwa da tunani da taimakon Ahmad wanda tun ranar da ya saka Mahmud a idanun shi ya tabbatar mun ko ni ba zan nuna mi shi son shi ba. Tun ranar da aka haifi Mahmud ya dauke mun nauyin hidimar shi, tun daga kan madara da zai sha zuwa nurse din da zata kula da shi, kayan sawar shi da sauran abubuwan da jariri yake bukata daga aljihun Ahmad kudin su yake futowa. And he does it happily with love! kullum yana cikin zirga zirga tsakanin Nigeria da London saboda Mahmud!
“a cikin haka watarana na samu labarin rashin lafiyar kakana ya riskeni, hankalina yayi matukar tashi a dalilin rashin sanin yanda zanyi da Mahmud na tafi, a wannan lokacin Ahmad ne ya bani kwarin guiwar tafiya na bar Mahmud a hannun shi naje na dawo, Shine ya maye gurbin nanny din Mahmud domin idan har Ahmad yana tare da shi, toh Nannyn bata da amfani saboda komai shi yake yi masa ko da kuwa wankin kashi da fitsari ne. har goyo irin wanda ake saka zani a kulle yaro a baya Ahmad yayi wa Mahmud, wasu abubuwan ni kaina na san ba lallai ne na iya su ba balle nayi masa don haka hankalina kwance na shiga jirgi na tafi kasarmu
“Tashin hankali na gaba da na fuskanta shi ne mutuwar kakana! ya rasu ya bar kakata cikin wani matsanancin hali saboda shakuwa da soyayyar da ta wanzu a tsakanin su! ta daina ci ta daina sha gashi itama ba wata isashshiyar lafiya ne da ita ba. sannan ne kadai ne gare su, ni ne koman su nine farin cikin su! babu yanda zanyi na tsallake ta cikin wannan halin na koma London naci gaba da zama hankalina a kwance! a wannan halin she needs me kamar yanda Mahmud yake bukata ta! Kaina ya kulle tunanina ya tsaya cak! a wannan halin dai ko giyar wake nake sha ba zaiyu na shigo musu da zancen Easha balle Mahmud ba domin a tunanin su tuni na rabu da ita naci gaba da rayuwata, yi mata bayanin cewa ban saki Easha har sai da muka haiwu da ita kuma dan yana can London dai dai yake da caka mata wuka a makoshi ta mutu don haka na rasa mafuta! a karshe na yanke shawarar na dauki Mahmud na kai shi gidan marayu, ko kuma na samu wadda zan damkawa amanar shi na dinga biyanta tana kular mun da shi amma wacece na yarda da ita har haka? wanne mahalukin zan iya barwa Mahmud na koma gida na kwanta nayi bacci? hakika babu! Haka ba dinga sakawa ina kwancewa har na koma London bansamu mafuta ba!
ina zuwa na bayyayawa Ahmad halin da nake ciki ina kuka yana kuka saboda tausayina! a take ya gaya mun wata magana da ta girgizani ta kadani ta kuma bani mamaki.”