HAUSA ARAB CHAPTER 11 END KARSHE
“Ahmad da bakin shi yace wai nayi mi shi alfarma na bar mi shi Mahmud ya kula da shi har zuwa lokacin da zan sasanta da dangina a kan shi, idan kuma na bar masa shi gabadaya zai fi kowa farin ciki!
Ban taba jin maganar da ta bani farin ciki da bakin ciki lokaci daya ba, ban taba jin maganar da ta bani kwanciyar hankali da tashin hankali lokaci daya ba kuma ban taba ganin samu da rashi a lokaci daya irin wannan rana ba. Na aminta da Ahmad na yarda da shi na yarda da addinin sa da tarbiyyar sa, da amanar sa da kuma uwa uba soyayyar da yake yi wa Mahmud wadda kana gani ka san daga Allah ne ba hadin mutum ba!
Bana tantama Mahmud zai samu irin kulawa da soyayyar da zan bashi a wajen Ahmad amma ta yaya zan iya komawa gida naci gaba da rayuwa babu shi? yaya za’ai na rabu da Mahmud gabadaya ni ina wata shiyya a duniya shima yana wata? ya zanyi da maraicin Easha da na abinda ta haifa a lokaci guda? but what other choice do i have? wanne option nake da shi bayan wannan? don haka na danne zuciyata nayi shahada na sallamawa Ahmad na bashi Mahmud!
“Ya karbe shi cikin matsanancin farin ciki da alkawarin rike shi amana da gaskiya da dukkan karfinsa. Ni ne na kai su airport suka tashi zuwa Nigeria basu bar mun komai na Mahmud ba sai cikakken adreshi da lambar wayar su ta landline.
Sai da na ga tashin su sannan na koma gida cikin matsananciyar kewa da karyewar zuciya.
bayan kwanaki biyu nima na tattara na koma kasar mu!
“kullum kwanan duniya da tunanin Mahmud nake rayuwa, da shi nake bacci da shi nake tashi, na rame na shiga wani irin yanayi. tun ina daurewa har gazawata ta bayyana a fili! kakata ta sakani a gaba da tambaya amma sai nace mata babu komai!
A hankali ina addu’a ina tawakkali na soma samun relief har na samu aiki a kasar mu na soma.
Bayan shekara biyu ne naji lallai ya kamata na waiwaya gare su naga halin da suke ciki da kuma irin rikon da Mahmud yake samu a hannun Ahmad! na shirya musamman na taho Nigeria, na sauka a Lagos gidan wani student dina da muka shaku a Liverpool mai suna Abiola, shi ne mutum na farko da nayi wa bayanin halin da nake ciki na bude wa sirrina bayan Ahmad kuma da taimakon sa muka samu gidan su Ahmad a cikin garin Adamawa’
“kamar yanda na bukata bamu je gidan kai tsaye ba, bincike muka dinga yi domin mu gane wannen irin hali Ahmad yake ciki tsakanin sa da danginsa dangane da Mahmud kuma wacce irin kulawa yake samu! Anan naci karo da abinda ya girgiza ni! wani al’amari wanda yayi mun girma da nauyi! wai ashe Ahmad da yaje gida a matsayin dan cikin sa ya gabatar musu da Mahmud saboda ya siyowa Mahmud soyayyar su da kulawar su! Ban taba tunanin wani mahaluki zai iya irin abinda Ahmad yayi ba, ban taba jin irin wannan sadaukarwa ba kuma ban taba ganin amana da alkhairi irin wannan ba don haka a take ni kuma nayi alkawari cewa ni da kaina bazan taba neman Ahmad ba, ba zan taba zuwa na bayyana kaina ga Ahmad nace nazo ganin Mahmud ba balle har yayi tunanin dauko shi ya bani! nayi alkawari cewa in dai ba Ahmad ne ya neme ni ba, ba zan taba neman shi har abada. Da wannan alkawari na bar Nigeria na koma Lebanon bayan na dankawa Abiola amanar saka idanu akan rayuwar Ahmad da Mahmud yanda zan dinga jin rahoto akan su da duk abinda yake faruwa da su”
+
Dr Ilyas ya share masu zafi sannan ya juyo ya kalli Daddy ya matsa gabansa ya kama hannayen sa yaci gaba da magana, Daddy kuwa jikinsa har rawa yake yi saboda matukar mamakin Ilyas akan abinda yake fada
“Ahmad duk wani motsin ka da na family din ka na sani kuma ina ji, tun daga wannan lokacin wani abu bai taba faruwa da ku wanda ban sani ba, komai akan idona ake yi, domin Abiola ya saka dukkan wani matakan sirri akan ka wanda zasu dinga kawo mana rahoton halin da kuke ciki, tun daga wannan ranar har zuwa yau! akwai lokuta da yawa wanda nake jin kamar nayi tsuntsuwa nazo na gan ku, akwai lokuta da dama da nake zuwa nayi badda kama na ganku ba tare da munyi magana ba, bayan ka kai Mahmud Turkey takanas nake zuwa na gan shi ba tare da kun sani ba, har lokacin auren shi, har lokacin da yarinyar ta mutu ya shiga cikin mawuyacin hali! Har lokacin da ya koma London da zama! na san lokacin da ka fara nemana da ahalina kuma da gangan na boye maka na toshe duk wata hanyar da da ka sameni, saboda i know that you can handle it! you can take care of it kuma babu wani abu da zan yi wa Mahmud wanda kai ba zaka iya yi masa ba! a duk lokacin da soyayya da kaunar Mahmud ta ingiza ni sai na tuna alkawarin da na daukarwa kaina, sai naji ba zan iya zuwa gare ku ba.
STORY CONTINUES BELOW
“Abu na karshe da ya taso shine tunanin da ka fara yi akan yanda zaka mallakawa Mahmud dukiyar ka ba tare da sirrinka ya futa ba, dalilin ya ballo duk wani ruwa ya kuma warware komai! a wannan karon ne kuma na tabbatar cewa kuna bukata ta kuma dole na bayyana muku kaina saboda halin da kuka tsinci kan ku a ciki na gori, da tsangwama da takura da kuncin rayuwa. billahil azeem ba don Mahmud na bayyana kaina ba Ahmad sai don na wanke ka daga zargin duniya, sai don na bayyanawa ahalinka da sauran mutane irin amanarka da gaskiyar ka da alkhairin ka! Sannan zuciyata tana tafasa, tana zogi a duk lokacin da naji an alakanta Mahmud da kalmar shege mara asali, duk da haka ban yi niyyar bayyana kaina saboda wannan dalilin ba! why? saboda kayi abinda ya dace! Mahmud ya rasa mata ka dauki yarka ka bashi! ka tsaya mi shi a matsayin uban da babu irin shi, ya samu uwar da ko mahaifiyar shi na raye iyakacin kulawa da soyayyar da zai samu daga gare ta kenan sannan ya samu goyon bayan mahaifiyar ka mai dattako da nagarta (Dada) da yayanka masu irin halinka(Sadik da Omar) da aboki mai kaunar sa(Faisal) tell me me Mahmud ya rasa wanda zai sa na bayyana kaina don na bashi? babu!
Amma ganin halin da kuka shiga akan nemana ruwa a jallo da kuma bakin fentin da duniya take neman yi maka a dalilin taimako da dattakon ka sai naji bazan iya zama ina kallo sunan ka ya baci ta wannan dalilin ba! And that’s how na shirya yanda zanyi na same ka!”
“Bayan rasuwar Easha da shekara uku nayi aure da yar’uwata Maryam(umm Iklas) Allah ya azurtamu da yara biyu mata! Ban taba baiwa dangina labarin ka ba sai da Kakata ta kwanta ciwon ajali, a lokacin burinta guda daya shi ne na haifi da namiji, ta dauki damuwar rashin samun da namiji ta saka a ranta har abun ya dinga barazana ga rayuwar ta, anan ne nayi kundunbala na bata labarin ka, na basu labarin Easha da kai Ahmad da yanda komai ya faru, ga mamakina bata dauki zafi ba, kuka ta dinga yi tana cewa me yasa ban gaya mata mun samu rabo ba? me yasa ban kai Mahmud wajen su ba? Ita ma Umm Iklhass abinda ta fada kenan! ko kadan bata nuna bacin rai ko kishin Mahmud ba, sai dai na gaya musu na riga nayi alkawari ba zan taba zuwa na karbo Mahmud a wajen ka ba! don haka sai hoton ka na nuna musu. babu dadewa kakata ta rasu, sai na nemi tranfer a wajen aiki na koma America.
Nayi aiki for 18years a Miami sannan nayi retire na koma gida shekara biyu kenan da suka wuce!…………
Daga Easha har Ikhlass doctors ne, Easha tayi aure da yaranta biyu, ita kuma Ikhlas tana University of Miami tana karasa karatunta………
“Ahmad duk kalmar da baki zai furta ba zata iya daukar yawan godiyar da nake so nayi maka ba……
Ahmad nagode….”
sai suka rungume juna suka fashe da matsanancin kuka su biyun, kuka irin wanda dan’adam yake yi a lokacin da wani buri na shi ya cika wanda yasha matukar wahala kafin ya cika shi! kuka irin na na farin ciki da godiyar Allah! kuka na contentment da satisfaction!
ashe ba su kadai suke kukan ba, rabin mutanen wajen taya su suke yi cikin tausayi da sha’awa da karyewar zuciya.
Su wa’e kuwa sai kallon kallo da mutsu mutsu da zare idanu! an dauki lokaci kafin aminan su samu nustuwa sannan Daddy ya kuma mikewa yaci gaba da bayani na gaba, wanda za’a iya cewa yafi na bayan daga hankali da girgiza zukatan da suke wajen.
“Abu na gaba kuma mafi muhimmanci a wannan taron shi ne maganar da naso bayyanawa tun a wancan taron amma sai Mahmud ya rokeni alfarma akan na rufe mi shi wanan sirrin zuwa gaba! Toh a yau kam da komai ya bayyana dalla dalla bana jin zan iya cigaba da rike wannan magana saboda haka Mahmud ka gafarceni!”
Ya Mahmud ya yunkura da sauri zai taso Daddy ya daga hannu ya dakatar da shi yana cewa
“Go back and sit down Mahmud”
yanayin yanda ya bashi umarnin dole ya koma ya zauna cikin rashin jindadin karya masa alkawari da Daddy yayi. Ya sunkuyar da kai yana jin amon sautin Daddy yana bayani
“Abinda nake so na bayyana shi ne dukiyar Mahmud da take hannuna! ina nufin dukiyar Mahmud da mahaifin shi ya danka mun tare da shi! Mahaifiyar shi ta rasu ta bar mi shi kadara da kudade masu yawan gaske wanda itama ta gada a wajen iyayenta da suka rasu! Nayi-nayi da shi akan bazan karbi komai ba domin Mahmud din kawai nake so ba wani abu ba! Amma sai yace lallai sai na karba saboda haqqin Mahmud ne, dukiyar shi kuma dole ta zauna a hannun na tunda ni ne mahaifin shi a lokacin.
A wannan lokacin ina cikin wata badakala ta karayar arziki, domin Intisar tayi mun muguwar barnar da baki ba zai bayyanawa ba! A lokacin da na saka dukiyar Mahmud cikin kasuwancina sai da nayi kiyasi nayi lissafi kudina 40% ne kudin Mahmud 60% na rubuta komai a rubuce.
Cikin ikon Allah a lokacin kalilan kudin suka yi albarka suka habaka riba ta dinga shigowa ta ban mamaki, musamman harkar home furniture din da na yi a Turkey. Daga lokacin komai yaci gaba cikin albarkar ubangiji da yardar sa har zuwa wannan lokaci! In summary abinda nake so na bayyana muku shi ne Dukiyar da na mallaka a yanzu, 60% dinta ta Mahmud ce.
“Wannan magana mai nauyi ita ce dalilin budewar komai, itace sanadin tonuwar duk asirin da na kwashe wadannan shekarun ina rufewa!
Domin na fara tunanin idan mutuwa ta kasance a kaina me zai faru? waye zai warware wannan kullin mai sarkakiya? wacce irin kura zan bari a bayana? wannan dalilin ya sanya na kira lawyer na muka tattauna muka tsara komai muka futar da komai sannan na fara tunanin yanda za’ai nayi approaching Dada da wannan maganar! Kamar yanda nake tunani kuwa Dada bata dauki maganar da sauki ba, saboda ban bayyana mata ainhin dalilina na yin haka ba, sai ta fassara maganar a matsayin rashin adalci da kuma kokarin rarraba kan yayana da nake yi amma duk da haka sai tace na tafi zata yi tunani! Bana tantana shine dalilin da ya sanya ta tafi Umra domin tayi mun addu’a. Ganin wankin hula yana shirin kai ni ga dare sai na shirya zuwa na gaya mata komai domin na cimata na idda niyyata don gani nake yi mutuwar tana kusa dani, kuma tsorona na shine na bar duniya ban warware wannan kulli ba
a karshe naje nayi addu’a sannan na samu Dada a garin Jidda nayi mata aihinin bayanin alakata da Mahmud tun daga farkon faruwar komai har karshe!
“Duk yanda nayi tunanin yanda Dada zata dauki zafi abun ya wuce haka, duk yanda naso rarrashin ta nayi mata bayani bata saurareni! Dada tayi fushi dani fushi irin wanda bata taba yi ba domin a ranar ta shirya dawowa Nigeria ta kuma rantse ba zata shiga jirgina ba! Bayan mun dawo ne ta shirya wancan taron da aka yi a baya ta tara dukkan family ta umarce ni akan na tashi da kaina nayi bayanin komai kamar yanda nayi mata sannan tayi mun kyakykyawan kashedi akan lallai na nemowa Mahmud mahaifin shi saboda na kankaro masa daraja da mutuncin sa wanda yake tambal tambal a idanun duniya.
“Hankalina bai kara tashi ba sai da naga Mahmud ya saka damuwar son ganin mahaifin shi a ran sa! damuwa mai yawa, damuwar da na tabbatar zata iya kawo wa ciwon sa cikas har ma tayi barazanar farautar rayuwar sa! Don haka hankalina ya kara tashi, Da kaina na samu ambassador na kasar Lebanon, da taimakon ambasada amma duk iya taimakon da zasu yi an kasa binciko Dr Ilyas! Abinda ya daure mun kai kenan naji nima zuciyata na neman bugawa, domin na tabbatar sai dai idan Ilyas bai bani adress din shi dai dai ba idan kuwa ba haka ba babu yanda za’ai a kasa gano shi musamman ma da ya gaya mun cewa family din “HASSAN ELMASARY” sunyi matukar suna a garin Beiruit toh ya za’ai su boyewa hukuma? ashe shi ne ya hana faruwar hakan!
“Ranar da Ilyas ya kirani rana ce da take daya daga cikin ranakun farin cikina a rayuwa! Ranar da bazan taba mantawa ba a rayuwata, ranar da burina ya cika addu’a ta karbu kuma matsalata ta warware!
Yau gashi mun sake taruwa a wannan mazauni cikin farin ciki da annashuwa tare da iyalin Dr Ilyass mahaifin Mahmud ya warware mana komai da bakin sa! Yau Allah ya nufa na sauke nauyin da yake kaina na cika alkawarina. ko yanzu mutuwa ta dauke ni ban tafi da buri ba”An dauki lokaci mai tsayi tsakanin families din ana musayar godiya, Dada tayi gyaran murya tayi nata jawabin wanda ya ratsa zukata kamar yanda aka san ta mace mai hikima da fasaha da kuma hangen nesa
“Tun lokacin da Mahmud ya shigo cikin rayuwar mu Allah ya saka soyayyar shi a cikin zukatan mu, kuma ko da wasa ban taba kaicon ajiye Mahmud a mazaunin da na ajiye shi a zuciyata ba bayan naji ainihin alakarmu da shi! Ko kadan ban dauki zafi saboda matsayin da na baiwa Mahmud a matsayin sa na wanda ba jini ba, sai boyewar da Ahmad yayi wadda ta kusa zama babbar matsala a gaba, musamman da ya kasance akwai sha’anin dukiya a ciki da haqqin magada a duk ranar da ya fadi ya mutu toh lallai zai bar baya da kura da tarzomar da babu wanda zai iya kwantarwa!
“Abu na biyu da ya sanya na nuna hankalina ya tashi na kuma dauki mugun fushi shi ne idan ban yi haka ba lallai ne Ahmad ya mai da hankali wajen neman mahaifin Mahmud ba, musamman saboda na lura yana tsoron kamar idan ya binciko shi zai kwace masa Mahmud din ne, shi kuwa zai gwammace gara ya rasa duk abin da ya mallaka akan faruwar hakan!
Nikuma gaba nake ji, ko yanzu Mahmud bai nemi mahaifin sa ba a gaba zai bukace shi, watakila a lokacin bani babu Ahmad din babu Zainab balle mu tsaya masa mu bashi kariya da goyon kamar yanda muka yi a baya! Zai iya samun daukaka da mukami mai girma, amma mutane ba zasu daraja shi ba a bisa wannan dalilin, rashin sanin mahaifin sa da asalin sa zai janyo masa barazana da kalubale mai yawa a rayuwa wanda zasu hana shi kaiwa ga nasarorin masu yawa wanda yake so ya cimma! ko ya samu kuwa zai samu matukar cikas.+
“Daraja da mutunci da kima da alfarmarma na duk wani dan’adam suna danganawa ne da asalin sa da tushen sa da tsatson sa, komai girman mutum da mukamin sa idan bashi da asali ba za’a ga kimar sa yanda ya kamata ba kuma ba za’a dora shi kan abubuwa da yawa ba.
Muna fatan yayi aure ya haihu ya samu zuri’a, amma wanne bayani zai musu a lokacin da duniya ta goranta musu? wanne dalili ko hujja zai basu akan rashin sanin asali da tushen mahaifin su?
Wannan matsalar ba Mahmud kadai za ta shafa ba, zata yi ta bibiyar ahalinsa ne tana kai musu farmaki da barazana da cikas wajen samun ingantacciyar rayuwa da kwanciyar hankalin da suke bukata
“A sabili da haka na matsa na takura na saka Ahmad a gaba da bacin raina domin ya maida hankalin sa kacokan wajen nemo mahaifin Mahmud a gefe kuma na baza malamai suna ta addu’a babu ji ba gani
“Alhamdulillah Allah maji rokin bayinsa Ya amsa mana ya kawo mana dauki a lokacin da muke tsananin bukatar daukin Sa! Naji dadi nayi murna da farin ciki da bayyanar asalin Mahmud! Daman nasan cewa ko a ina tushen sa yake toh tabbas tushe ne mai kyau mai albarka domin alamomin hakan sun bayyana muraran a cikin halaye da dabi’unsa.
Mahmud mutum ne nagari abun so da alfahari ga duk wanda ya raba kuma wanda duk iyaye zasu yi alfahari da samun shi a matsayin dan da suka haifa!”
Dada ta dauki lokaci mai tsayi tana bayanin da ya kara jefa zukatan su Daddy cikin nutsuwa da farin ciki, Omar na gefe yana aikin fassarar harshen hausa zuwa turanci domin su Dr Ilyas su fahimta, aikuwa babu abinda suke yi sai murmushin da yake bayyana tsantsar farin ciki da jindadin su!
A wannan lokacin idan aka tona zukatan Inna Badi’a, Kawu Sulaiman da Alhaji Ibrahim Kurmi MaiAtamfa babu abinda zaka samu sai tsagwaron tsantsar bacin rai, bakin ciki,mamaki da tashin hankali! Ba bayyanar asalin Mahmud ne ya girgiza su haka ba, ko da kuwa shi ne ba zai wuce kaso arba’in cikin dari din bakin cikin da suke ciki ba, babban takaici da tashin hankalin su shi ne jin cewa Daddyn da bazar Mahmud yake rawa, arzikin sa yake ci kuma ba don dukiyar Mahmud din ba da tuni ya durkushe tuntuni! Toh ko shi Daddy din dukiyar sa ta sanya suke masa wannan hassadar da kiyayya da bakin ciki balle kuma Mahmud din da suka dorawa karan tsana a dalilin son da Daddy yake masa!
Babban burin su a duniya shi ne su ga sun lalata farin ciki da walwalar Daddy, sun dankwafar da darajar shi sun daidaita dukiyar shi wanda suke fatan bakin cikin hakan yayi sanadin rayuwar shi!
Toh sai dai duk manasikar da suke shirya masa da ramunkan muguntar da suke haka masa idan akaje aka dawo sai su ga dai su suke ruftawa ciki domin bahaushe yace
IDAN RANA TA FUTO TAFIN HANNU BAYA KARE TA
kuma
DAN HAKIN DA KA RAINA SHI YAKE TSONE MA IDO
sannan
ABINDA YA BAKA TAUSAYI WATARANA SHI ZAI ZO YA BAKA TSORO
ita kuma
HASSADA GA MAI RABO TAKI CE.
STORY CONTINUES BELOW
A karshe anyi doguwar addu’a an shafa, Daddy ya baiwa matan umarni da su koma cikin gida anjima kadan za’a tafi wajen welcoming liyafar da ya shiryawa su Dr Ilyas a harabar gidan shi na Mississippi kuma yace lallai bai daukewa duk wanda yake wannan wajen ba.
Hannuna cikin na Ihsan muka shigo dakina, na fada kan gado cikin wani irin matsanancin farin cikin da ban taba tsintar kaina a cikin sa ba! nayi juyi na sake yin juyi ina yi wa Allah kirari da baitocin godiya da mika salati ga Manzon rahama Alahissalatu wassalam!
“Zara ina taya mu gabadaya murna! Ina taya mu murna don bazan ce ina tayaku murna ba! domin ba zaki gane irin farin cikin da nake ciki ba Zara! I’m so happy for you, for us, for this family gabadaya”
Na tashi zaune na rungume ta ina hawayen farin ciki, tare da turawa Aisha addu’a ta musamman, domin wani al’amari na farin ciki ko bakin ciki ba zai taba samuna ba tare da na tuno ta ba, ba tare da nayi missing din ta ba, ba tare da nayi fatan dama ace tana raye muyi sharing din shi ni da ita ba.
A falon Dada kuwa wata kasaitacciyar drama ce take faruwa, Bayan kowa ya shigo ya zauna including Inna Badi’a da ke jinta wata cikakkiyar stranger cikin su Mami da Aunt Laila wanda suke ta faman sowa da tafi da wata irin matsananciyar murnar da zata baka mamaki sai kawai suka tsinkayi sallamar Mahmud!
Ya kara wani kwarjini da wani irin kyau a dalilin matsanancin farin cikin da yake ciki, gabadaya hannayen babbar rigar tashi sun sauko yana rataye su suna kara saukowa irin yanda maza suke zama idan suna cikin matsananciyar sabga da hidima, hannayen shi manya manyan ledojin Sahad store ne wanda suke makare da alawar bounty da twix!
Ya tako cikin falon cikin wata irin tafiya ta isa da kasaita har wani rangaji yake yi kamar basarake, sai da yazo tsakiyar falon sannan ya tsaya cak! ya sanya hannu a cikin ledar ya dauko alawar bounty guda daya ya bare ya gutsira, dai dai lokacin da muka futo ni da Ihsan daga cikin dakina! sai muka tsaya muna kallon diramar da ya shirya!
Gutsirar alawar yayi ya lumshe idanu sannan ya shiga rabawa duk wanda yake zaune a cikin falon ledar bounty da twix guda dai dai!
sai da yazo kan Inna Badi’a kawai sai ya ajiye mata gabadaya ledar yana murmushi
“Inna ke kam a wannan rana baki cancanci alawa guda daya ba, kamata yayi na baki carton! amma kuma ba za ta kai ba saboda jama’a sai dai ki biyo ni bashi!”
Ta dubi ledar alawar sannan ta dago ta kalle shi cikin matsananciyar zuciya da bacin rai, shi kuwa ya dallare ta da dandasheshen murmushin sa.
“Baki tambaye ni alawar ta mecece ba? kinsan dai larabawa da hausawa basu cika raba alawa a banza ba ko? sai ana wani shagali ko wani taro ko wata walima”
Ta sake zuba masa wani mugun kallo tana ci gaba da kuluwa domin ta kawo iya wuya!
“calmdown Inna yau din nan ni dan gata ne! dan gatan umma da Abba dan gatan Daddy da Mami dan ango dan lelen amarya!”
Wannan sentences din na Mahmud sune suka saka falon yin diff kowa ya tsaya cak yana kallon shi tare da ba shi dukkan attention
shikuwa ya sake darawa yana rangaji, da yana cikin mutanen da suka iya rawa babu tantama dancing steps zai taka masu matukar kayatarwa
“Yess! Ni din dan gidan ango da amarya ne! a wannan rana a wannan lokaci a wannan yammaci mai tarin albarka na hada auren iyayena ababen sona akan sadaki mafi albarka!”
Cikin matsananciyar firgita da tsumuwa bakin Inna Badi’a ya bude automatically ya furzo wasu kalmomi cikin mugun speed
“ME KAKE NUFI MAHMUD?”
wani irin murmushi ya sake yi a dalilin jindadin yanda da ta kidime ta firgice lokaci daya, sai ya bata amsa dalla-dalla kuma filla-filla irin yanda ko mai koyon hausa zai fahimta ba tare da neman taimako ba!
“INNA BADI’A INA NUFIN A WANNAN RANAR A WANNAN ZAMAN NI MAHMUD ILYASS HASSAN EL-MASARI AKA MAHMUD AHMAD LAMIDO NA NEMARWA DADDYNA ALHAJI AHMAD LAMIDO AUREN MAMINA HAJIYA ZAINAB ALIYU KURFI A WAJEN MAHAIFINTA KUMA YA AMINCE YA BANI AKAN SADAKI NAIRA DUBU DARI LAKADAN BA AJALAN BA! AMBASADA YA WAKILCI DADDY NI DA KAINA NA WAKILCI MAMI AKA DAURA AUREN A GABAN SHAIDU”1
wata azabbabiyar guda mai shegen zaki Baba Rabi da ke kitchen ta futo a guje ta rangada tana juyin farin ciki
Wata zabura Inna Badi’a tayi tace
“KAN UBANCAN! wallahi ba zai yu ba”
Ta mike da sauri za ta futa! sai taci karo da Kawu Sulaiman ya shigo yana bala’i da kumfar baki yana rantse rantse sai ya shiga dakin Dada ta lalata wannan auren da aka daura akan tsagwarar rainin hankali da cin amana, ko amanar wa aka ci ba’a sani ba! Yayansa guda biyu Nasir da Abdallah suna rike shi yana faman zambarwa, sai kawai gani aka yi Dada ta futo daga dakin ta, ta sauya lafayar ta zuwa fara tas a maimakon shudiyar da take jikinta dazun nan!
“Ku sake shi! ku kyale shi ya taho! in ce kuwa nice uwar sa ba shine ubana ba??
a tsawace tayi maganar don haka su Nasir suka sake shi cikin suka tsaya a gefensa suna jiran hukuncin Dada.
“mahassadiyar zuciyar ka ko kuwa tosashshiyar kwakwalwarka ce ta gaya maka cewa ba da yarda ta aka daura auren ba? nace uban waye ya gaya maka cewa ban fi kowa amincewa da lamuntar wannan auren ba? toh bari kaji! Auren Ahmad da Zainab na alkawari ne, wanda naso faruwarsa tun ranar da mahaifin Zara ya bar duniya, Allah bai cika mun burina ba sai yau a sanadin wannan farin watan Mahmud! Don haka wannan aure sunan shi mutu ka raba! Don Allah don Annabi saboda hassada da bakin ciki ka hadiyi zuciya ka mutu!”
Tana kammala maganar ta ta juya ta koma cikin daki a zuciye, zuciyarta na tukuki da bakin cikin haihuwar mutane irin Kawu Sulaiman da Inna Badi’a!
Idan na tsaya bayyana yanda ta kaya da abubuwan da suka biyo bayan wannan al’amari mai girma toh wani lokaci na mai tsayin gaske zan bata ban kammala ba! don haka na barwa mai karatu ya hango ya kissima ya kiyasta ya hararo yanda sauran al’amarin ya kasance. Abinda kawai zan kara da cewa shi ne a wannan rana Daddy da Mahmud da Mami da duk magoya bayansu da masoyansu sun yini cikin wani matsanancin farin ciki da murna yayin da su Inna Badi’a suka yi wuni mafi muni da tashin hankali da bakin ciki a rayuwar su.
Alhaji Ibrahim babu wanda ya san lokacin da ya kubuce daga rikon ambasada ya gudu titi ya tari taxi ta kai shi airport, ya wuce Kano kamar mahaukaci sabon kamu! Yayinda kasaitacciyar walima ta ban mamaki ta biyo baya a Mississippi duk da cewa sabon ango da amaryar basu halarta ba, sai Mahmud da Zara ne suka yi uwa da makarbiya suka rabashe suka cashe suka gwangwaje a maimakon iyayen nasu.
Assalam Alaikum!
It’s another interesting chappy😄
the other tin don hapen
e shock u right?
Daddy da Mami kuma lokaci yayi!
i smiled alot writing this chapter, it was soo soothing to me!
Ina fatan kuma haka readers.
We have two more chapters to go!
Yours truly,
Cutyfantasia.
1
If you are reading this chapter on friday, don’t forget to recite suratul kahf, send alot of salawat to the best of man kind saw
Allahumma salli ala ruhi sayyidina Muhammad SAW.
Ma’assalam!Ashe tsugono bata kare ba kuma kallo bai kare ba?
Sai washegarin ranar da misalin karfe shabiyu na rana, Mahmud ya gayyaci family din zuwa wani suprise mai ban mamaki!
A bisa umarnin Dada Kawu Sulaiman da Inna Badi’a suka yi motoci biyu suka bi su a baya,sun wayi gari ne cikin wata irin nadama da sanyin jiki, kwana suka yi suna tunanin wannan al’amari mai kama da almara suna jin kamar suyi tariya a koma baya su sauya salon takun su akan Daddy! kwarai sun yi danasani da bakin cikin abubuwan da suka faru, amma duk da haka babu soyayyar Daddy da ahalinsa ko ta kwayar zarra a cikin ran su ba! Sun riga sun yi mi shi wata irin ba’aboriyar tsana a bisa umarni da tursasawar bakar zuciyar su don haka har abada wannan so irin na jini ba zai shiga tsakanin su da Daddy ba!
A babbar bakar Jeep din da ke kan gaba Daddy ne! Ya Omar na gefen shi yana jan motar, a gidan baya kuma Dr Ilyas ne, da Khaleed da Umm Ikhlas da yayanta guda biyu!
Mota mai biye su itama babbar jeep ce, Sadik ne yake driving, Baban Kurfi yana gefen shi, a gidan baya kuma Ambasada ne da mahaifin Aisha da mijin Inna Badi’a
motar da ke biye da tasu Mahmud ne ke driving Zara na gefen shi, a gidan baya Ya Nuratu da Anis da Sofiyya, harda Baba Rabi!
Motar da ke biye da su Faisal ne da Ihsan a gefen shi,
a gidan baya Dada ce da Mami da Aunt Laila da mahafiyar Aisha.
sauran motocin na iyalan Kawu Sulaiman ne da Inna Badi’a yayansu suna tukawa.
A jere reras suka isa unguwar Asokoro bisa jagorancin Omar wanda alamu suka nuna ya san komai fiye da kowa akan wannan suprise din. Tafi tafi suna bin shi a sannu Suka lankwaya wani layi suka bullo wani dankareran gidan da ya baiwa kowa al’ajabi da mamaki, sai da suka zo kofar gate din sannan suka gane cewa ashe ginin guda biyu a jikin juna, daya gida dayan kuma asibiti ne wanda aka kammala tsaf aka makala mi shi suna inda akayi amfani da wasu irin bakaken karafe masu daukar hankali kamar haka+
“ZAINAB CLINIC”
Omar ya danna horn, security ya taso ya wangale musu gate suka shiga cikin harabar, duk da ba gabadaya motocin ya cinye ba wasu sai a bakin gate suka yi parking! daya bayan daya suka dinga futowa suna kallon ginin cikin matsanancin mamaki da al’ajabi ba sai an musu bayani ba kowa ya baiwa kansa amsar asibitin na Mahmud ne, kuma sun tabbatar da cewa Daddy ne yayi mi shi wannan kyautar, sai da suka ga shi kan shi Daddyn a cike da mamakin da ya kasa boyuwa a gare shi sannan tunanin su ya tsaya cak suka fara lalube da sake sake.
Asibiti ne na gaske, madaidaici wanda kwakwalwa zata tsaya taci burki idan ta kissima darajar fili a garin Abuja musamman a wannan special unguwa da kuma abinda ginin waje yake nufi da makuden kudaden da yake lashewa! gini ne mai hawa uku, dakunan kwanciya patient guda goma, VIP guda hudu kowanne daki na dauke da kwandisha da fridge da plasma tv da wasu irin arnakakkun customized hospital cot/beds kirar kasar Turkey.
Ga consultation room guda hudu da sauran offices na ma’aikatan asibiti kowanne an kawata an shirya shi irin shirin zamani, ga wani irin shirayyen lab da ya wadatu da dukkan nau’o’in na’urar da lab yake bukata, da wani tankasheshen fully equipped theatre room wanda ko yanzu a iya shiga da patient a fede a mayar a dinke!
Shikuwa Office din Oga pata pata inji inyamuri, zaka iya tunanin ofishin shugaban kasa me na cikin villa! everything is just breath taking and mind blowing!
Reception din kuwa kamar wani otel a kasar Miami din America, kujerar da aka ajiye kawai abar kallo ce!
Iya tsaruwa ginin ya tsaru, iya shiryuwa ya shiryu, kuma iya kawatuwa finishing da furnishing din gidan ya kawatu! sai dai ace tabarakallahu masha Allah!
Sai da aka gama zagaye aka gama kallo sannan aka sauko aka futo cikin harabar asibitin da aka kawata da shuke shuke masu ban sha’awa! sai qamshin furanni ne kawai yake tashi da sassanyar iska.
cikin nustuwa Mahmud ya matsa gefen Daddy ya soma yin bayani da kayataccen sautin sa mai dadin sauraro!
“Daddy tun ina makaranta nake da burin gina asibiti na zuba ma’aikata kwararru na hidimtawa kasa ta da basirar da Allah ya bani, toh sai dai kuma abubuwa suka yi ta shigowa rayuwata ba irin yanda na tsara ko nayi zato ba! kullum muka zauna da Jawahir sai mun yi hirar ginin asibitin nan yanda komai zai kasance, toh muna tamu Allah na tashi, sai rayuwa ta juya mun wani irin juyi mai wahala har nazo na koma London da zama! duk da haka wannan burin yana cikin raina, ina son na gina asibiti ko ban dawo kasar nan da zama ba! Tun lokacin da muka hadu da Safna aka soma maganar auren mu da auren da ka bani na Amina naji tunanina ya soma karkata akan na dawo gida na zauna kusa da kai! kodayake lokacin ma tuni na siya wannan filin har an fara gini ban saka ran dawowa na zauna a cikin sa ba dai sai bayan anyi maganar auren sannannayi wannan plan din na maida hankalina ga burin da nake so na cimma.
STORY CONTINUES BELOW
“Faisal da Omar ne suke jagorantar komai kuma da taimakon su aka gina wannan asibitin, Tunda na yanke shawarar dawowa gida gabadaya na maida hankalina wajen kammaluwar aikin, duk da cewa kamfani muka baiwa order suka yi komai!
Yanzu komai ya kammala, ma’aikata kawai za’a nema a zuba, asibitin zai kasance na mata kawai da matsalolinsu wato bangaren gynae! kuma na saka mi sunan Mamina domin nuna girmamawata da kaunata a gare ta, musamman da yake asibitin na mata ne shiyasa na saka mi shi sunan macen da tafi kowacce girma da soyuwa a gare ni”
Mami sai kuka, kukan farin ciki da sauran abubuwan da ba zata iya tonawa ba, da sauran abubuwan da ba zata bayyanawa ba! Ta karbi Mahmud ta raine shi ta sho shi ta bashi dukkan soyayya da kulawa, without knowing wanene shi without sharing wata dangata ko alaka ta jini da shi, When he was just LITTLE HAUSA ARAB din ta wanda bai san kowa da komai ba sai ita da Daddy kadai
gashi yau ya juye mata zuwa wasu irin tarin nasarori da alkhairai da farin ciki a cure wanda ba zata iya warwarewa ta kayyade yawan su ba! idan kuwa zata kintaci wata kalma ko jumla akan haka, toh kawai sai dai tace
“MAHMUD IS A BLESSING TO HER”
wata baiwa ce da rahama da arziki Allah ya dunkule yayi mata kyauta.
HAUSA ARAB ya rikide zuwa wani kasurgumin babban mutum wanda duk uwar da ta mallaki da irin shi zata yi murna tayi alfahari ta kuma godewa Allah!
Babu wanda bai yaba ya saka wa wajen albarka ba idan aka cire su o’0 da wa’e! babu wanda bai yi murna da farin ciki ba musamman da suka futo daga cikin asibitin suka shiga daya ginin wanda kallo daya zaka yi masa ka tuno da wasu bungalows na garin ONTARIO din CANADA idan har ka taba ziyartar garin.
gidan fari ne da ash hawa biyu, amma bai cika girma ba, domin faluka biyu ne budaddu da rufaffe guda daya a kasa, sai dakunan bacci guda biyu a sama, babban abinda zai kayatar da kai a gidan shine verandas din aka zagaye shi da su an kawata su da luxury home decor! Gabadaya gidan an kammala shirya shi tsab, ko cokali ba zaka nema ba, kitchen din da ake shiga ainihin cikin gidan ta cikin sa abun kallo da tsone ido ne! kar a tsaya baka labarin yanda aka shirya shi aka kuma wadata shi da modern utensils abun sai wanda ya gani kawai
yawancin wuraren gidan a bude suke babu kofa kana hango view din wani daga wanda kake zaune, daga wannan kuma zaka iya shiga wancan sak english home inda masu gidan ke rayuwa a sake ba tare da kutsen unexpected or unplanned guest ba! Rayuwa a sake a more a zamanance cikin gidanka babu me shiga rayuwar ka sai ka san da zuwan sa!
A garin hawa bene, Inna Badi’a ta gangaro ta kurje guiwa, sai ta fashe da kuka kamar wata yarinya, kai kana kallon yanayin kukan kasan ba zafin kurjewar ne ya kawo shi ba, mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki! don haka cikin zolaya aka dinga yi mata sannu ana rarrashi abun gwanin ban dariya! Shikuwa Kawu Sulaiman tun a asibitin ya bar takalmansa lokacin da suka shiga hamshakin office din Mahmud! ya tube su cikin kidima, ashe bai mayar da su kafar sa ba haka yaci gaba da yawo bai sani ba, wanda suka ankare suka dinga sheka dariya a wayance!
“Mahmud a ina kake samun kudi? kar kace mun albashin kane kawai yayi wannan aiki?”
Daddy ya cillowa Mahmud tambaya zuciyar sa cike da mamaki! cikin kwantar da murya Mahmud yace
“Daddy muna yin harka da Faisal sosai, real estate, da kuma harkar motoci, sannan…………..”
Faisal ya cafe shi kafin ya karasa ta hanyar cewa
“Sannan me? Daddy Mahmud zurfin ciki ne da shi! babu wanda ya san irin nasibi da daukakar da ya samu a fannin likitanci! kuma baya so a sani! He is not just a consultant, likita ne wanda asibitin Liver pool suke ji da shi da ma garin London da UK gabakidaya! yayi aikin da ba’a taba tsammanin nasara ba kala kala kuma yaci nasara, manyan mutanen da yayi wa aiki successfully ba zasu kirgu ba, kyautattukan da ya samu daga gare su kadai idan ana lissafi zaka sha mamaki
so Daddy kada yayi misleading din ku da wani kasuwanci da muke yi wanda bai taka kara ya karya ba kuma ba shine makasudin wealth din shi ba,
ko shekara ukun baya da aka yi ta yada hoton wasu yan ukun da wata yar ministan kasar France ta haifa bayan sun karade asibitoci kala kala a duniya an tabbatar mata cewar abu ne mai matukar wahala ta haiwu, Daddy shi ne likitan da yayi mata IVF(In Vitro fertilization) yayi mata aiki ya ciro mata yaya uku lafiyayyu amma da minista ya tambayeshi alfarmar da yake so yayi masa sai yace daya daga ciki yana so a sakaya sunan sa a maimakon hakan sai asibitin su ne ya samu daukakar da yayatu a kafafen yada labarai! sun kara mi shi matsayi sun kuma yi masa kyaututtuka da karrama……….”
Mahmud yayi maza ya sa hannu ya rufewa Faisal baki yana cewa
“ya ishe ka! ya isa haka! bamu yi haka da kai ba kuma alkawari ka dauka”
sai kawai akaga Daddy yana tafi hannaye biyu yana hawaye
“bravo Mahmud! you are a proud son”
2 WEEKs LATER
A cikin sati na biyu da faruwar wannan al’amarin ne aka gudanar da kasaitaccen bikin Mahmud da Zara a Bluevelvet marque da ke Abuja, inda aka tara manya manyan kusoshin gwamnati, attajiran Nigeria da sarakai da kuma larabawan kasar lebanon wadanda suka haska taron suka kawata shi! idan nace zan bayyana yanda taron ya kasance, birona zai iya bani kunya domin wani abun ba zan iya rubutawa kamar yanda ya faru ba! kawai dai anyi biki mai sunan biki wanda ya amsa sunan shi biki!
Amarya da Ango suka tare a gidansu, Dada tayi musu babbar kyautar da ta faranta musu rai wato Baba Rabi wadda zata dinga kula yunwar cikinsu! bayan tsirarun ma’aikatan da Mahmud ya ajiye a gidan masu zuwa suyi aiki su tafi domin bai lamunci na kwana ba, bai ma yi musu wajen zama a gidansa ba!
tuni shelar neman ma’aikata ta bazu a kafafen yada labarai, sai dai ka’idoji da sharadan da ake bukatar ma’aikatan su cika ya janyo tsaiko domin Mahmud ya matsa lamba yayi alkawarin ba zai ajiye bara gurbin ma’aikaci a asibitinsa ba!
Daddy da Mami sun dauke Dada sun tare a sabon gidansu da ke Asokoro District kusa da Villa, da taki yarda su zauna tare Mami ta fashe da kuka tace kafarta kafar Dada, idan har bata yarda ta bisu ba toh sai dai suma su dawo tsohon gidanta su hakura da sabon gidan! Da banbaki da lallashi ta amince ta koma kawwamammen bangarenta a cikin gidan.
Rayuwa sabuwa ta shimfidu, komai na gidan akwai ma’aikacin da yake yi, amma Mami bata yarda Dada da Daddy sunci abincin kowa ba sai wanda ta sarrafa da hannunta, she is a full time house wife domin gabadaya ragamar Fashion house dinta ya koma hannun Aunt Laila, tace ya kamata Mami ta huta taji dadin rayuwarta itama ta samu kulawa kamar yanda ya rayu cikin kulawa da iyalinta babu gajiyawa! Daddy yace wannan magana haka take babu gyara! Aunt Laila ta futo da wani irin salo da tsari wanda ya sabunta brand din ya kuma farfado da martabar sa ya fara trending a karo ma biyu.
Zara ta koma sabon karatu cikin Baze University domin hada degree din ta na farko a fannin “Estate management” domin abinda yafi burgeta kenan a wannan zamanin da ake gasar gine gine da tsare tsaren gidaje musamman a garin Abuja! Daddy da Mahmud suka bata kyakykyawan support da duk wani taimkon da take bukata.
Dr.Ilyas sai da yayi wata biyu a Nigeria sannan ya koma Lebanon, duk wata magiya da naci Mahmud da Daddy sunyi sun gama akan ya dawo Nigeria da iyalinsa da zama ya kekasa kasa yaki! Yace yafi ganewa kasar sa abar alfaharin sa, sai dai ba’a farga da wata kulallaiya ba sai da suka zo tafiya aka ga Ikhlas na kuka tana tumami, ita kanta ta dade da komawa makaranta amma ta kekasa kasa taki tafiya sai online take daukar karatun an rasa dalili an rasa musabbabi ashe nan wata irin soyayya ce ta kullu tsaninta da Ya Omar wanda yabi ya hure mata kunne da dadin baki irin na matasan Nigeria!
toh wai who will say No to this union?
sai Safiyya kadai Maman twins da ta dira tsalle tace sai dai ya zaba tsakanin su! shikuma yace bai san lokacin da yayi mata alkawarin ba zai kara wata bayan ita ba, rigimar da ta dau lokaci kafin ayi resolving, Sofi ta saduda ta hakura domin ganewar da tayi babu wanda yake supporting dinta, idan ma tayi wasa zata ita asarar Omar din gabadaya wannan dalleliyar balarabiyar ta mora! sai ta hakura ta sakawa kanta salama manya suka shiga cikin magana aka nema aka bayar da alkawarin idan ta kammala karatu bayan shekara daya da rabi za’ayi auren!
wai ina Imamu ne???
mu hadu a last chapter domin jin inda ya boye da kuma abubuwan da labarin sa ya kunsa! sannan mu karkare mu karasa jin karashen labarin wannan family gabadaya, watakila har da epilogue watakila kuma iyakaci kenan!
Cutyfantasia ce,
Ma’assalam!Tashina kenan daga baccin da ya zame mun jiki, tun ina kokarin dainawa har na gaji na hakura, la’asar ce liqis ansha ruwa mai yawa a garin Abuja ko’ina ya dau raba, bishiyu sun jiqe suna fidda qamshi da sassanyar iska mai sanya nutsuwa da nishadi!
A hankali na tashi zaune ina yaye quilt din da na rufe dukkan jikina da shi, na tashi tsaye na gyara queen size modern italian bed dina baki kirin me wani irin shape mai ban sha’awa! yasha bed cloth ruwan toka design din “BROOKLINEN” mai taushi. komai na dakin black and ash ne, simple and elegant babu wata hayaniya ko kyalli.
Ina kokarin shiga toilet ringing din waya ta ya katse ni, na karasa vanity table na dauka cikin murmushi ganin sunan da yake kan wayar
“hy dear! how are you?”
“I’m good kana ina ne?”
“Muna asibiti kinsan ana ta screening din staffs!”
“ayyah! hard luck! Allah ya bada sa’a! when are you coming home?”
“did you miss me”?
“you have no idea how much i do”
yayi chuckling
“i will be home soon my love! ki gaya wa Baba Rabi akwai bako tonight a saka abinci da shi”
“bako? wanene?”
“you will see! take care of yourself i love you”
“i love you too!”
sai na shiga toilet dina nayi wanka, sannan na futo dakin na shirya cikin wata irin soft arabian gown grey colour wadda aka yi wa dinkin zare irin na larabawa daya daga cikin kayan da Umm Ikhlass ta turo mun daga Lebanon! na nannade kaina da beige din mayafi kalar zaren dinkin! to explain how good and fresh i’m looking is a whole story amma zan iya cewa ina daya daga cikin tsirarun mutanen da Allah ya baiwa kalar fata mafi kyau! ita ba fara ba ita kuma ba baka ba, gata nan dai CARAMEL inji bature! kamar anyi blending madara da coffee, amma madarar tafi yawa, har wani danko da sulbi take yi tana kyalli!
sai na rasa wai da kwalliya nafi yin kyau ko idan banyi kwalliyar ba? idan banyi kwalliya ba i look too natural to be real, wata iri nake komawa kamar furen flower wajen sha’awa da dadin kallo, idan kuma nayi kwalliyar sai kiga na dawo wata classy woman wadda kallo zaki yi mun ki gane duniya tana damawa dani musamman da yake duk abinda nake amfani da shi wajen kwalliyar da shafe shafe dai dai da skin tone dina ne, baya kara mun haske ko duhu, sai dai yayi enhancing din kalar da kyawun, I AM SOO MASHA ALLAH! inji Esha!
Kasa na sauka na samu Baba Rabi a kitchen tana hidimar girkin abincin dare!
“Baba Rabi sweetheart! Allah ya bar mun ke!”
ta juyo hannun damanta tsamo tsamo cikin kwababbiyar fulawar da take sakawa ta funkaso cikin katon frying pan tana deep frying!
“Allah baya barin wani don wani uwar dakina! sai dai kice Allah yasa rakiya tayi nisa”
nayi murmushi ina bude tukunyar da ke kan gass, miyar taushe ce wadda aka sarrafa da kulawa, taji wadataccen naman rago sai zabalbala take yi! na rufe na bude babbar takunyar, ita kuma shinkafa (mandi) take ta turara an like ta da foil paper! kamshin kitchen din kawai zai tayar maka da duk wata appetite!
“Sannu da aiki Baba Rabi, Allah ya sakawa da Dada alkhairi da ta bani ke! da tuni haka zan dinga jigilar girki ina zirga zirgar makaranta!”
Ta sake yin murmushi tace
“Ai ke yar lele ce ko nace yan lele. da ke da Mahmud din wannene ba wannene ba? idan ba ku ba waye ya isa ya kwace ni a hannun Dada?”
STORY CONTINUES BELOW
Haka muka ci gaba da hira, na futo da kayan aikina na hada “classic chocolate mousse” as desert sannan na futo da grozen samosas na soya! kafin karfe takwas mun kammala hada table, mun gyara kitchen kai ba zaka ce anyi aiki a cikinsa ba sannan na hau sama nayi sallar isha’i na sake gyara fuskata na fesa turare……
ina kokarin mayar da shi na ajiye naji an tsaya a bayana, kamshin LaNuit ya tabbatar mun da shigowar Ya Mahmud!
“You look beautiful babe”
na juyo ina murmushi
“you say it every morning and night”
“because you are always beautiful in my eyes and i never get bored of staring at you! even when you sleep”
I smiled shyly ina jin dadin kalaman, domin an halicci mutum da son jin yabo da wasawa a kan shi musamman daga bakin wanda yake kauna.
“thank you amour! you are as handsome as a pure diamond, as sweet as honey and as caring as a mother! i appreciate you everyday for being the best husband and brother”
“and daddy to be”
muka kyalkyale da dariya gabadaya!
“ke na bar bawan Allah a parlour sauko ku gaisa”
ban tambaye shi ko waye ba, na rike hannun shi da ya miko mun muka futa daga dakin muka sauka!
bakina ne yayi forming “O” shape a lokacin da nayi arba da fuskar da ba zan taba mantawa ba, fuska mai dinbin tarihi a rayuwata!
Fari sol din gaye, wanda a yanzu kamala da haiba suka ratsa shi fiye da da, ya kara fari da haske har yana kashe maka ido, sai dai ya rame sosai, yana sanye cikin filtex black colour(his fav colour) ko don ya san tana yi mi shi kyau ne? ya zama wani cool kamar ba shi ba!
Mamakina na boye na maida murmushi a madadin sa!
“Wa nake gani?
yayi murmushi yace
“bako ne!”
cikin mutunci da walwala muka gaisa yayi mun murnar aure da ta bayyanar Uncle Ilyas da ta auren Daddy da Mami! sannan muka dunguma zuwa dining muka zauna kowa yayi serving kanshi!
So da yawa ina matukar mamakin yanda Ya Mahmud baya nuna kishinsa akan Imamu! kamar wani abu bai taba shiga tsakanin mu ba, kamar abokin shi, kamar ma ba’a dalilina ya san shi ba!
Tun ina jin haushin abun har na tattara na watsar domin ganewar da nayi akwai wata kyakykyawar alaka a tsakanin su wadda suka gina daga baya.
“Zara bayan zuwa ganin gida fa akwai abinda ya kawo ni”
na ajiye spoon din da nake cin abinci na kalleshi sannan na kalli Ya Mahmud sai nace
“wacce magana ce?”
ya gyara zama sosai sannan ya soma magana a nutse with seriousness
“Akan kanwarki ne, na nuna interest dina akanta amma taki amincewa muyi magana wai lallai sai dai nazo na same ki, abinda kika yanke da shi zata yi aiki!”
Na juya idona na daga kaina ina tunanin wacece kanwata? mutum daya ce take bani wannan girman da matsayin da soyayyar na yar’uwar jini itace Ikhram kanwar Aisha sai dai zanyi matukar mamaki idan itace din don haka nayi shiru ina kallon yatsuna sannan a hankali kamar ina jin tsoron futowar maganar nace
STORY CONTINUES BELOW
“kanwata? Ikram?”
wani genuine murmushi yayi sannan yace
“yes! Ikhram!”
zan yi magana sai aka kira Ya Mahmud a waya ya mike yana cewa
“excuse me”
ya futa verandah yana amsawa, da alama Daddy ne!
Imamu ne yaci gaba da magana cikin nutsuwa da nadama mai yawa
“I wish i can rewind time and erase everthing, dama ina da iko da lokaci, dama zan iya juyo da hannun agogo baya na gyara kuskure da son zuciyata! A duk lokacin da na tuna abubuwan da suka faru, na tuna cewa Aisha ta rasu ban nemi yafiyarta ba sai naji kamar na dauki wuka na kashe kaina don bakin ciki! Zara bana son tuna rayuwata ta baya, bana son tuna abubuwan da nayi, suna sare mun guiwa naji kamar Allah ba zai yafe mun ba!
Na fara son Ihkram ne tun ranar da muka hadu da ita a Jabi taje Sahad store siyayya, sai wani tunani ya dar su a raina, why not idan za ta amince dani ta karbi soyayyata na aure ta? itace kadai damar da zanyi amfani da ita wajen goge ko da rabin laifina ne akan Aisha!
Inason na auri Ikhram na kyautata mata, na kula da ita na bata duk wani farin ciki da kwanciyar hankali sabanin kuntatawa da barazanar da nayi wa yayarta a baya! ina son na gyara laifukana na baya ta hanyar being the best husband to my wife and best father i can ever be to my kids! daga cikin matan da na san na yaudara na nemi wasu na nemi gafarar su wasu kuma bansan inda zam same su ba! kullum cikin istigfari nake da rokon Allah yafiya da gafarar sa! ina fatan Allah yasa kada abubuwan da na aikata suyi hunting dina! i need your support on this Zara! Don Allah ki bani damar cimma burin da na kudurce a zuciyata”
Ya bani matukar tausayi kuma ni shaida ce Imamun da ba shine na yanzu ba, ni shaida ce ya chanja kuma ya shiryu, ya zama salihi maganarcin mutum! rayuwa ta koya mi shi darasi da wuri, Allah yaso shi da rahamar sa yayi guiding din sa zuwa hanyar shiriya tun lokaci bai kure masa ba! Amma auren Ikhlas da Imamu sai naji shi wani bambarakwai! ba wai ina kishi ko wani abu ba domin ahalin yanzu babu ko burbushin wani feeling a zuciyata akan Imamu! kawai ina jin Ikhram a cikin zuciyata kamar Aisha, whatever decision i will guide her in making, dole na tsaya na tabbatar cewa abu ne mai kyau wanda ya dace da ita wanda kuma ba zai bata mata rayuwa ba! she treats me kamar Aisha, bond din mu yafi wanda sukai sharing da Aisha domin suna yawan fadan sakwanni idan sun hadu, ita kuma Iky din ma boarding take yi so sai tazo hutu gida! nikuwa a kullum sai munyi magana da ita a waya da social media, bata yin sati bata zo wajena ba, babu wani abu da zata aikata ba tare da shawarata ba!
babu abinda take boye mun no matter how weird ko nauyin abun and i direct her and guide her like a sister! Komai yi mata nake yi idan har ina da iko da dama, kuma kullum kara janta nake yi a jikina!
friendship din mu da Aisha wani abu ne wanda ba zai karye don bata raye ba, har abada bazan manta da ita ba kuma bazan watsar da iyayen ta ba! bana wata daya ban je na gaishe su ba, ba abinda zai faru daga side dina ko nasu side din bamu hasafci juna ba! mun zama da ya mun zama family! And i do think shi ne soyayya ta tsakani da Allah!
ba dai dai bane ka yanke alaka da iyaye da yan’uwan amininka bayan ya mutu wai saboda zasu tuna maka da shi ko ka tuna musu da shi ko dinga jin babu dadi! kamata yayi kuci gaba da alaka ku kara kyautata alakar ku fiye da da domin soyayya ta tsakani da Allah bata yankewa!
Na nisa na jefo mi shi wata tambaya wadda ba domin shigowar wannan maganar ba bazan taba iya yi mi shi ita ba har abada! ba ma shi ba ko wanin shi bazan iya tambaya ba!
“Ina yaranka? ina babar su? wanne matsayin suke yanzu? kuma yaya zaka yi da su”?
sunkuyar da kai yayi cikin sanyi da bacin rai sannan yace
STORY CONTINUES BELOW
“Gaskiyar magana Zara Hassan da Husain yayana ne na halak kuma aure nayi na haife su ba kamar yanda ake tunani ba”
na waro idanu cikin mamaki da son jin karin bayani
“Yes! aure muka yi, i loved the woman so much a lokacin, let me not say love, lust zan ce! amma kuma Zara duk lalacewata ban taba aikata alfasha ba wlh, so i married her in secret na ajiye ta a Paris har ta haifi yaran! iyayenta sun mutu, maraici ne ya saka ta cikin da ta shiga wanda a sanadiyyata ta shiryu! mun rabu ne kafin auren mu da ke a lokacin maganganu suka taso aka fara auren, da banyi niyyar fadar gaskiyar tsakanin mu da ita ba tunda nasan na riga na rasa ki kuma shi kan shi auren nata nasan laifine tunda ban sanar da kowa ba mayi shi! sai da Mummy ta kwanta rashin lafiya haiqan a kaina sannan na gaya kusu komai dalilin kuma da yasa ta yafe mun kenan sannan ta umarceni akan lallai na sake ta! kuma ba zata rike yaran ba! Itama kuma maman nasu tayi rantsuwa sai ta kaini kara idan ban bar mata rikon yayanta ba! i had no option sai na barsu a can Paris saboda sun fi sabawa da kasar kuma akwai security da privacy sosai!”
wata irin ajiyar zuciya na sauke na girgiza kai cikin gamsuwa, zan yi magana Ya Mahmud ya shigo ya zauna, na dauka zai yanke maganar amma sai naga yaci gaba da yi mun magiya da bayani! that’s when i knew cewa Imamu da Ya Mahmud aminci mai girma suka kulla.
Washe gari bayan na kammala lectures na wuce gidansu Aisha, Allah ya taimakeni na samu har Abba yana gida, cikin ladabi na cire tsoro nayi musu bayanin komai akan Imamu amma ban da abinda ya faru tsakanin su da Aisha da ni wannan wani sirri ne wanda muka haqa rami muka binne, kuma daga ni sai Imamu ne muka san da shi don haka har abada maganar ta wuce!
Iyayen Aisha mutanen kwarai ne kuma mutane ne masu nagarta, kamar Aisha haka suke kallona kuma yawancin hidimar da suke wa Aisha tare dani basu daina ba, irin su tsaraba, allowwance din da Abba yake bamu tun muna school da sauran abubuwa kuma duk lokacin da na nuna yin gardama sai sun yi mun tatas har na hakura na daina, nima kuma kamar iyayena haka nake hidima da su, waya, ziyara da duk abubuwan da zasu faranta musu don haka kullum shakuwar mu karuwa take yi!
Bayan amincewar su sai na shiga dakin Ikram na tambaye ta cikin kulawa idan tana son Imamu, idan kuma a ranta bata son kada ta boye babu wanda zai tursasata sai na fahimci cewa ni take jin kunya, gani take yi kamar bai yi dai dai ta auri tsohon saurayina ba don haka na rabu da ita na soma shirye shiryen aure as the big sister din amarya kuma small sister din Ango! a cikin watan aka kai kudin aure aka saka rana bayan ta kammala secondary school watanni hudu masu zuwa sai taci gaba da karatun a gidanta.
Daga gidansu Aisha na wuce gidansu Mami naci abincin dare na bingire muna hira tsakiyar Dada da Mami da Daddy, and that’s the most pleasing moment dina a yanzu ganin kan family dina a hade cikin farin ciki da kwanciyar hankali! A nan Ya Mahmud ya same ni sai shadaya Dada ta kora mu gida, domin da cewa nayi muyi kwanciyar mu kawai dare yayi! Daddy da Mami suna yi mana dariya, sunyi kyau abun su kamar daman can tare suke rayuwa! they are soo perfect together and they love eachother wholeheartedly!
Lokaci yana tafiya satika suka juye watanni bikin Imamu da Ikhram ya tashi, i really played the big sister role domin duk wani abinda Amarya tayi amfani da shi na sakawa from head to toe a dukkan ranaku biyar na bikin daga jaka ta suka futa! sannan na shirya masu coacktail party duk da taimakon Ihsan wadda muka koma kamar ciki daya saboda aminci da shakuwa! Ya Nuratu tana can sai dai bama kwana biyu bamu yi waya ba! babu abinda ya chanja a tsakanin ta damu saboda Inna Badi’a tunda ba itace ta hadamu ba. Ya Mahmud ne yayi lefe akwati ashirin da hudu na designer boxes wanda aka makare da kayan arziki na gani na fada!
Daddy yayi kayan gida karankataf ko cokali Abba bai siya ba, ba don ba shi da shi ba sai don yakana da saka alkhairi! Nikuwa dadi kamar zance wayyo Allah domin ta kowanne fanni na samu goyon baya da support! babu wanda ban gayyata ba, har mutanen Qatar Esha sai da tazo mun da yaranta kuma a gidana ta sauka! haka akayi budiri aka sha shagali aka kai amarya dakinta!
STORY CONTINUES BELOW
Tun kafin lokacin haihuwa Ya Mahmud da Dr Shabana wata ba’indiyar da ke aiki tare da shi a asibitin sa suka tabbatar i can’t not give birth naturally a rayuwata dole sai dai a dinga yi mun cs, kuma ban ji tsoro ba ko kadan because of the good pregnancy and birth therapy da counceling da na samu a wajen Ya Mahmud! i was just very eager to see my babies! yes babies! munyi scanning ya nuna yara biyu ne, mun duba gender mace da namiji ne dalilin da ya saka muka tafi London tare da Aunt Laila muka yi baby shopping a different brands masu inganci daga aljihun Daddy!
one faithful thursday evening Ya Mahmud da Dr Shabana suka shigar dani dakin fida suka ciro yaran successfully! kunsan wata shegantaka? babu da wanda yaran suka yi kama sai Uncle Ilyas! kamar yayi kaki ya tofar, which means kamar su daya da Ya Mahmud amma duk sun fi shi haske! All my family were by my side a jinyar asibitin nan, abinka da gida, wani katon VIP room me parlour muka zauna a ciki!
tun daga kan mutanen lebanon da Riyadh da Qatar babu wanda basu iso kafin suna ba! Kawu Sulaiman ya hadu da karayar arziki wani chinese da hadin bakin abokinsa suka yi mishi 419 ya saka uban kudi a harkar wani kasuwanci wanda suka yi mi shi romon baka zai zama “don” lokaci daya! abinka da mahassadi ba hankali, burin shi har yanzu shine yayi kudi ya kamo Daddy babu musu suka je banki ya tura musu kusan dukan abinda ya mallaka, tun ranar da ya raka su airport da yake harkar a China akace ana yinta har yau wayar su a kulle take! da akayi zuzzurfan bincike aka gano komai nasu fake ne sai dai ya dau hakuri!
a take ya fadi, jininsa ya hau, Allah ne ma ya tsallakar da shi stroke, Daddyn dai da suka tsana shi ne yayi musu visa aka tafi da shi London asibiti, suna can da matar sa da Nasir dan sa.
Inna Badi’a kuwa tayi laushi tayi sanyi domin kishiyar da ta rayu tana azabtarwa yanzu ta yantu ita take gallaza mata! yayan Inna Badi’a guda biyu sun zama kangararru, saboda goyon bayan da ta dinga yi musu tun suna kanana suyi abinda suke so, da suka gagara baban su ya kai su Rehab center yace yana alkali ba zasu janyo masa abun kunya ba! wanda ya san Inna Badi’a idan ya ganta yanzu sai yayi kuka don tausayi, A wajen Nuratun kawai take samun sanyi, da yake ance hannu bai rubewa mai shi ya yanke ya yar, tunda Nuratu ta gane Inna tayi laushi ta saduda ta dinga janta a jiki tana bata kulawa, a hankali sai ta dinga marowa, Duk abinda za’ayi zaki ga tazo tana yake abun dariya da tausayi su Mami kuma babu ruwansu sai suyi sakata cikin hidindimu domin ta ware amma duk da haka bata iya sakewar.
Toh rayuwa fa kenan! duk inda ka dauketa haka zata dauke ka! mugunta da hassada basa kai mutum ko’ina sai kofar danasani da kunya da tozarci wanda kuma kake wa muguntar da hassada ya dinga daukaka kenan, idan baka yi muguwar sa’a bama sai ka dawo kana neman alfarmarsa. THIS IS LIFE
A asibitin Zainab Clinic ranar da Daddy, Uncle Ilyas da ambasada suka zo wani emotional scene ne ya faru! Daddyn ya kalli Ya Mahmud ya kalli babyn hannun shi sai ya tuna ranar da ya fara daukar Mahmud a asibitin Liverpool da yanda soyayyar shi ta shiga zuciyar shi farat daya! ashe it is going to be a long and beautiful journey between them! Ashe Allah zai raya su tare har ya dauki dan da Mahmud ya haifa!, sai ga kwalla! yayi maza ya mayar da su sannan yace
“Mahmud wanne suna kake so?”
shima Mahmud din karyewa yaji zuciyarshi tayi da wani tartsatsin farin ciki
“Daddy har ma sai ka tambayeni bayan su da kan su sun raba gardama sun zo tare boy and girl! ofcourse Daddy da Mamina ne suka zo! You two are my favorite and you’ll forever be”
Sai kuka, ya rungume Daddy!
Daddyn ya rike babyn da hannu daya ya janyo Mahmud jikinsa da daya hannun ya rungume sannan yaci gaba da magana emotionally
“Haba Mahmud! you are not a kid anymore, Daga yau bazan kara rarrashin ka ba na Yaye ka! ka zama babba dole ka daina wannan shagwabar, nikuma na zama granny babu ruwana da kai sai yan jikokina”
STORY CONTINUES BELOW
Uncle Ilyas hawaye yake yi masu matukar sanyi da farin ciki mamaye a zuciyar sa! anya akwai mutane irin Daddy a duniyar nan? Anya kuwa za’a samu mutum irin Daddy?
Ya Omar ne ya karaso ya karbe babyn a hannun Daddy yana cewa
“kunga Daddy ku gama kuka tukunna sai ka karbe shi kada Mahmud ya shafa masa saurin kuka domin shi makarantar sojoji zan kai shi! he will be a strong boy unlike his Dad”
Kowa yayi dariya, zaka yi mamakin yanda Ya Sadik da Omar basa kishin Mahmud a wajen Daddy! anan zaka kara gasgata cewa hassada da kyashi halitta ce, da wani zai wa wani kyashi da hassada da su ne zasu fara yi wa Ya Mahmud but they are always by his side, suna respecting din shi suna bin maganar shi kuma suna matukar kaunar shi!
An zauna tsakanin lauyoyi anyi rubuce rubuce akan dukiyar Daddy da Mahmud, Uncle Ilyas yace babu abinda Mahmud zai karba ko bashi da komai balle shima ya tsaya da kafarsa! Dada da Daddy ne suka tsaya tsayin daka, dakyar Mahmud ya karbi 30% ya saka hannu! aka kammala komai a rubuce a gaban hukuma da shaidu wannan ya kara dimbin girman Mahmud da mahaifinsa a idanun family.
Anyi rainon Ahmad(Na’im) da Zainab(Ni’ima) a gidan Daddy da Mami wadda ko sau daya bata je asibitin ta gan mu ba wai su Aunt Laila ma sun isa! irin wannan karar da take yi ne yake kara wa Dada sonta da yabonta a kullum!
Anyi suna mai matukar kayatarwa a harabar gidan, anci ansha anyi walwala duk da cewa ni ina cikin daki ba’a barni nayi zirga zirga ba saboda CS!
Ya Mahmud yayi mun kyautar sabuwar Toyota Camry 2018 da set din diamond! yaran kuwa bansan nawa ya baiwa Aunt Laila tayi musu siyayya ba.
Kaya kuwa daki guda aka loda su, ko ya Umar akwati biyu ta versace ya ciko da kayan yaran kowanne da nashi, Nikuma laces masu kyau! Daddy, Dada, Mami, Aunt Laila, Ya Sadik, Ya Omar, Ya Nuratu, Ihsan akwatinta daban na Faisal daban, Daga bangaren Uncle Ilyas kuwa abun ba’a cewa komai! idan na tsaya bayyana irin dukiyar da muka tara sai kunyi mamaki!
sati biyu bayan suna Ya Mahmud ya tafi Canada wani course ya barmu karkashin kulawar wadannan mutane ukun da bamu da kamar su a duniya, wato Dada da Mami da Daddy! i was treated like a queen! komai ina daga kwance ake mun kamar za’a maida ni ciki! yaran sunyi girma sunyi kyau!
baby fomular din “Enfamil” da ake basu ta karbe su sosai, cikin farin ciki da kwanciyar hankali muka yi wankan muka kammala! sai Daddy yace muci gaba da zama a gidan sai Ya Mahmud ya dawo! shikenan na koma makaranta ta, bani da matsalar raino ko girkin abinci ko kula da gida!
Yaran kuwa ban saka su a raina ba, domin nasan nice zan sha wahala, korafin Dada ma kawai isata zai yi domin ta tsani mutum mai rashin kunya akan yaya musamman a cikin iyalinta don haka tsakanina da su sai kallo daga nesa! and i know well ba zasu bar mana su ba kwacewa zasu yi a bisa take taken su, so ba namu bane bamu saka rai ba!
sai da suka yi watanni hudu Ya Mahmud ya dawo! ilai kuwa ban koma da su ba, daman sun fi gane madarar fiye da komai, Da niyyar su Dada sai sunyi shekara daya za’a yaye su su rike su gabadaya, Ya Mahmud yace big NO an bar musu! daga mu sai Baba Rabi muka koma muka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Bikin Ya Omar da Ikhlas ya tashi! nayi uwa nayi makarbiya kamar yanda na saba, tun Ya Sofy na jin haushina har ta hakura! muka sha shagali muka rabarbashe! aka gama biki, Daddy yayi mi shi kyautar gida a kusa damu shi da Ya Sadik! sai ya tambayi Sofy zabi, tace ita gidanta zata zauna bata son sabon gida, sai yayi mata gyara ya bata sabuwar mota da kudi. Allah ya bata dangana ta kwantar da hankalinta akayi shagalin biki da ita wasu event din ma har da ita, muma kuma munyi mata kara bamu yi posting bikin a social media ba!
Daga ita har amaryar kuma a Zainab Clinic suke aiki, since they are all doctors! Amma Ikhlas muguwar mai tsokana ce, fitinanniyar yarinya ce, kullum sai ta takali Sofy da fada! sai da Ya Mahmud yayi mata mugun warning ya saitata sannan aka samu zaman lafiya! sannan Ya Anis sai tayi wa Sofy kabilanci ta koma wajen Ikhlas, idan suna ragargazar larabci ba zaka so su daina ba, kowacce kyau kamar ita tayi kanta!
Rayuwa taci gaba da gudana cikin aminci da kwanciyar hankali da farin ciki! babu abinda zamu cewa Allah sai godiya domin yayi mana dukkan ni’ima da baiwa da albarka!
Tammat bi hamdullah
wassalatu wassalamu alaa Nabiyyina Muhammad Saw!
For every beginnings there must be an end, we have finally come to the end of this beautiful journey! Hausa Arab is a wrap!! i can’t be grateful enough,
when i started writing it, it didn’t make sense to me, i took it like a joke, but gradually you people supported me and showered it with love and praises!
Nagode Nagode Nagode, ina mika godiyata ga dukkan wanda ya karanta wannan littafi na HAUSA ARAB! my supporters from day1, wadanda suka zo daga baya sukai joining da duk wanda ya zauna ya dauki lokaci ya karanta!
i really appreciate your love and i am grateful!