HAUSA ARAB CHAPTER 2
Yau litinin ce tunda nayi sallar asuba nayi karatuna ban koma ba. Yau Imamu zai dawo daga doguwar tafiyar da yayi ta wata daya wadda ko samun lokacin hira mai tsayi bamayi domin ayyuka suka tarar masa masu yawa. A dalilin wani sabon kamfani da suke son budewa na cement a garin Kano. Inaso na mishi tarba ta musamman domin nasan kila yau a gidanmu ma zaiyi dinner. Kitchen na shiga na samu Baba Rabi tana ta
kicimullin aiki. Na karasa ciki ina cewa “Baba Rabi wannan aikin fa da sassafiyar nan wane zaici duka wadannan abubuwan?” Murmushi tayi taci gaba da zuba kullin waina fara sol akan tandar waina ta zamani. “bakisan Daddy zaizo ba?” Wara ido nayi cikin mamaki nace “yau zai dawo? Ya akai Dada bata gayamun ba? Kice yau gidan nan zai dau harami kenan! Tayi dariya tace “ba karami ba kuwa amma inaga ba dadewa zasuyi ba. Da abokansa zasuzo gaida Dada su karya. Su tafi.
Wainar guda daya na dauka na gutsira wani dadi malam ba’a magana. Akan cooker daga can gefe ga farfesun kan rago yana ta zabalbala. Daya tukunyar kuma miyar taushe ce da ta wadatu da naman rago da ganyen alayyahu.
Na bude manyan food warmers din da ke kan table duka kayan abincin gargajiya ne irinsu funkaso sinasir da tuwon nikakkiyar shinkafa.
Daga can kuma an feraye doya ne dankali ga kayan miya anyi grating birjik. Na jinjina kai ina cewa “yanzu Baba Rabi tun yaushe kika tashi don Allah kikai wadannan abubuwan? Kamar wata inji?” Dariya tayi sosai sannan tace “tun jiya da dare na kwaba kayan fulawar karfe hudu na futo na fara suya. Na girgiza kai ina jinjina aiki da iya sarrafa abinci da wannan baiwar Allah. Ban taba ganin macen da ta iya lafiyayyen abinci kala kala irin Baba Rabi ba. Gashi bata gajiya kamar inji ko ance za’a kawo mai aiki a hadasu ta rage mata wani hidimar bata yarda sai tace iya tafiso tayi aikinta ita kadai. Kullum ba zaki ganta a zaune ba kwata kwata batasan ta gaji ba. Wannan ya sanya Dada take masifar ji da ita. Bama Dada kadai ba har yayan Dadan da jikokinta don kuwa in kana gidan toh cikinka baya maraici.
Daga kitchen dakin Dada na wuce na same ta kamar kowacce safiya tana nan sallaya tana karance karancen littattafan addu’o’inta. Ta saka tafkeken gilashin karatunta mai kara mata kwarjini. Cikin ladabi na gayar da ita ta amsa tare da tambaya ta yanda na kwana. “Dada ashe yau Daddy zai dawo?” Cikin murmushi tace “nima ban dauka yau bane sai jiya da la’asar ya gayamun wai anan ma zasu karya da abokansa inaga zuwa karfe takwas zasu sauka” murmushi nayi nace “Allah ya kawo su lafiya” tace “ameen ba zaki makaranta bane?” Nace “ina da test ma Dada amma fa sai na bari su Daddy sunzo zan tafi ko da zanyi missing test din kuwa” dariya na bata sosai domin ta gano abinda yasa zan tsaya. “Kudi” don in dai abokan Daddy suka zo gidan nan wata Don nake komawa in don ta naga Daddy ne ai shi yana nan gobe ma zai shigo gidan.
Nima dariyar nayi nace “Dada da gaskiyata fa bikin su Ya Sadik saura sati uku duk inda mutum yasan zai samu kudi ai ba zai wasa ba” ta girgiza kai kawai tana murmushi sannan tace “dan Allah ki futa sitroom din baban naki kiga su Ya’u sun kammala gyarawa?” Mikewa nayi ina cewa “yanzu kuwa Dada akwai sabon turaren wuta na ma shi zan dauko na saka musu” cewa tayi “Allah ya sauwake wa son kudinki Zara” futa nayi ina dariya…. banda abun Dada wanene bayason kudi a wannan marrar? Babu.
Kafin karfe takwas din tuni mun kammala komai gidan ya dau kamshin abinci da na turare kamar wanda za’a kawo amarya. Dada naji da Daddy ajin karshe duk abinda ya shafe shi bata wasa dashi. Duk wanda yake kaunar Daddy ya gama da zuciyarta!
Wanka nayi na futo nayi shafa na gyara fuskata da nude make up sannan na shirya cikin dandakekiyar doguwar riga kirar Oman kalar brown, balloon sleeves akai mata da wani yadi mai jikin damisa. Na nade fuskata da gyalen rigar. Da sassanyar farar humra nayi amfani tare da turaren Beyonce heat. Na hada tarkacen kayan karatuna da purse a babbar jaka na saka takalmana na futo. Kitchen na wuce nayi mana take away din abincin ni da Ihsan na kai mota na dawo. Ina kallon agogo basu suka shigo ba sai karfe goma.lokacin na kagu sosai domin ina da test ne by 11.
Ni da Baba Rabi muka shiga hidima da Daddy da abokansa guda hudu. Yayi matukar farinciki da abincin musamman yanda su Alaji Bala suke santi kowanne yana kwararo abarkacin bakinsa game da taste din abincin bani na samu kaina ba sai 12 na dau hanyar makaranta amma jakata a cike taf don haka ko a jikina banji rashin dadin nayi missing test dina guda daya ba.
Ina hanya wayata ta isheni da ringing nayi parking na dauka. “Aisha ina driving ne fa.. ke in kika fara kiran mutum bakya kakkautawa sai ya dauka” dariya tayi tace “ke malama ya isa haka tambayarki zanyi yaushe zakuzo da Ihsan din? Ohhps sai a lokacin na tuna nayi mata alkawari zan kai mata Ihsan gidansu yau idan mun tashi daga lectures. Cikin low tone nace mata “ayyah I’m sorry my dear yau Imam zai dawo na manta ne ban gaya miki ba but insha Allah gobe zamu zo” da ihu tace “kice yau prince charming yana hanya ba’a ta kowa sau tashi.” Nayi dariya nace “toh ya kika gani? He worth the whole of today don ma ina da test ne da bazanje school din ba.” Ta sake yin shewa tace ” lallai su o’o anyi zurfi ba’ajin kira” dariya nayi nace “ai zaki shigo muyi masa cin cin din nan kinsan kullum sai yayi zancensa wai bai taba cin mai dadinsa ba.” Cewa tayi “oh bestie I’m so sorry wlh ina da ayyuka dayawa yau i cant make it” sosai mamaki ya kamani don ban taba rokan Aisha wani abu ta gaza yimun ba musamman irin wannan. Gashi na uku kenan ina kiranta idan Imam zaizo ta tayani wani abu tana bani excuse. Zuwa yanzu na soma tunanin lallai akwai wani abu. Ba tare da na nuna mata komai ba mukai sallama na karasa makaranta raina cike da tunani kala kala.+
STORY CONTINUES BELOW

Wajen karfe uku muna zaune nida Ihsan wayata tai qara alaman shigowar sako. Na duba lambar Aisha ce “Hello bestie, gani kofar school dinku ki futo donAllah mu gaisa da Ihsan ” ji nayi wani iri. Yarinyar da tace ayyuka sun mata yawa ba zata iya zuwa gidanmu ba ita ta dauko mota kuma tazo school.lallai.
Mikewa nayi na dubi Ihsan nace “zoki rakani” ba tare da ta tambayeni ina zamuje ba ta taso ta biyo ni hannuna cikin nata har muka futo daga makarantar.
Banga motar Aisha ba sai wata kyakywar Mercedes Benz fara sol a parke a gefe. Haushi ya kamani a tunanina tricking dina kawai tayi. Zan kunna wayar kenan naji ana watso mun balloons ta ko’ina masu shape din heart kowacce da rubutu.
A hankali na kama guda daya na duba jikin balloon din “Happy birthday Zara” sai a lokacin na tuna yau 30th June yaune birthday dina. I dont really like celebrating birthdays saidai kawai nayi ta recieving texts da gifts daga qawayena yau kam abubuwa ma sun sha kaina tun jiya ban sake tunawa da wani birthday ba.” Dago kaina da zanyi mukai tozali da wani kyakykyawan saurayi sanye cikin wando da rigar kamfanin “Dolce and Gabbana” masu stripes blue and orange. Yayi wani irin fari da kyau. “IMAM” lebbana suka furta a hankali na tsaya steel kawai na rasa abun cewa. Kofar motar ce ta bude sai ga wata santaleleliyar black beauty doguwa cikin abayar “swarosvki” sai murmushi take. “Aisha” na sake furtawa. “Where did they meet? Why are they here together?” Bansan dalilin da ya sanya naji hakan bai birgeni ba ko kadan. Asalima tambayoyi ne da tunani suka cika kaina. A hankali take isowa ashe camera ce rataye a wuyan ta tana daukana hoto. Daurewa nayi na saki murmushi dukansu suka karaso inda muke.
“HAPPY BIRTHDAY MY PRINCESS” abinda Imam ya soma fada kenan. Murmushi nayi me sauti nace “thank you! Yaushe ka dawo?” Wani kyakykywan murmushi yayi mai fallasa kyawunsa yace “how are you doing?” Ya sauya tambayar nace “lafiya lau” a sanyaye na dubi Ihsan nace “Ihsan this is my fiance Imam” da mamaki akan fuskarta ta dubeni sannan ta dubi Imam ta saki murmushi ta gayar da shi ya amsa cike da kulawa tare da cewa “i have heard alot about you, kina taking good care of Beautiful mungode sosai but your face looks familiar” murmushi tayi tace “kaine brother su yusra ko?” Yayi maza ya girgiza kai. Tace “daga gidanku sai namu” ya fadada far’anshi yace “ayyyahh….ban cika zaman gidan bane shiyasa bamusan juna sosai ba” tace “hakane sannu da dawowa” cikin murmushinsa yace “sannunki kema da hidima” a sanyaye na sake duban Ihsan nace “meet my best friend Aisha” dukansu murmushi suka saki tare da hugging din juna don kowa na cika masa ciki da labarin daya amma basu taba haduwa ba sai yau. Ihsan ce ta duba agogo tace “Zara bara na koma saura 25min mu shiga test” Imam ne ya katseta da cewa “wait itama komawa zatai bazan sa tayi asaran test ba. Amma Yasmeen da Yusra sun shirya miki dinner a gida Zara please be there zanzo na dauke ki” kamar nace banaso amma na daure kawai nace toh. Mukai sallama suka sake shigewa mota suka tafi. Da sauri na danne kirjina inajin wani iri kamar kirjin zai balle. Ihsan ta dubeni tace “lafiya? Are you alright?” Kai kawai na daga mata sannan muka koma cikin aji.
Gabadaya bansan me na rubuta a wannan test ba don tunanina yana can wani wuri daban! Tabbas akwai abinda yake tsakanin Imam da Aisha ko da kuwa basu furtawa junansu komai ba toh lallai akwai wani abu mai kama da soyayya acikin ran kowa. Take wani gumi ya dinga ketomun duk da sanyin wurin. Da sauri na bada script dina na futo.
Waje daya na zauna na zabga tagumi ina tunanin wannan cakwakiya da take shirin bullowa. Meye hadin Imam da Aisha? Menene a cikin zukatansu? A ina suka hadu ba tare da sanina ba ya dauko ta a mota ya taho da ita? Meke shirin faruwa dani ne? Yanzu na fara gano dalilin da yasanya Aisha take dojewa kirana idan na gayyaceta duk lokacin da Imam zaizo. Yanzu na fahimci yawan ambaton Aisha da Imam yake yi nake tunanin kamar duk saboda ni ne yanzu nake gane komai” ji nayi anmun tafi a dab da fuskata na dago da sauri. Ihsan ce fuskarta dauke da damuwa. A hankali ta zauna kusa dani sannan ta dafa kafadata.
“Zara menene yake damunki? Lafiyarki qalau kina murnarki tun safe amma zuwan su Aisha da tafiyarsu gabadaya kin chanja you look confused and worried ko zaki iya sanar dani me yake faruwa?”
Ji nayi idona ya cicciko na daure na mayar da hawayen. Na yarda kwarai da Ihsan kuma na yaba da rikon amanarta a yanzu kuwa banga wanda ya dace na soma tara da wannan al’amari da ya kaita ba. Ban saba gayawa mutane damuwata ba sai Aisha ita kadai gashi ina son na tabbatar da abunda zuciyata take zargi.
Dubanta nayi a tsanake nace ” Ihsan i trust you a iya zaman da nayi da ke na yaba sosai da halinki da amanarki da kaifin hankalinki. Don Allah zan miki tambayoyi ke kuma ki amsamun tsakani da Allah kada ki yaudareni don naji dadi zan tsaneki daga baya. Tell me your truth no matter how bitter it would be” nutsuwa tayi sosai tana saurarena a qarshe tace “naji Zara kuma insha Allah zan gaya miki tsakani na da Allah!”
Ajiyar zuciya na sauke sannan nace ” a iya tunaninki da nazarinki me kika fahimta tsakanin Imam da Aisha kafin nayi introducing dinsu gare ki”
Shiru tayi minti daya sannan ta soma magana cike da nutsuwa da iya gaskiyarta. “A gaskiya Zara am sorry to say nayi mamaki da kikace Imam shine fiance dinki Aisha best friend dinki.” Ta sake yin shiru sannan ta dora “it looks as if they have feelings for each other yanda take kallonsa da yanda shima yake kallonta akwai wani abu a zukatansu ko da kuwa a boye yake basu fada ba. Gaskiya Zara akwai wani abu mai kama da so a tsakanin Imam da Aisha. But kibi komai a hankali dont rush. Please keep calm. Take time kiyi nazarinsu sosai har ki gano komai cikin sauki.”
A take hawayen da nake makalewa suka soma zirarowa. What kind of trial is this? Aisha of all people zatai betraying dina? Wanda aka samun ranar aure dashi take so? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun” rarrashi na ta shiga yi tana gayamun kalamai masu sanyi har na samu nutsuwa.
“Zara a ina kuka hadu da Imam? How close are you da Aisha? How much do you trust her?”
Assalamu Alaikum Hausa Arab readers? how is this chapter? did you smell something coming up? menene tunanin ku game da alakar da ke tsakanin Aisha da Imam??
shin dagaske Aisha zataci amanar aminiyarta? me Zara zatayi?
comments!!!
A tsanake na dubi Ihsan “tsakanina da Aisha is a long story
amma abinda zance miki shine tunda muka taso muke tare kwana kawai ke rabamu. Duk inda zan gaya miki shakuwa da kaunar da ke tsakanina da Aisha sai na rage miki wani abu. Bama iya awa biyar bamu ji halin da juna ke ciki ba. Duka damuwarta ni take gayawa nima duka damuwata ita nake gayawa. Makarantar mu daya ajinmu daya komai na rayuwarmu iri daya. Sai bambamcin hali da kamanni kawai. Don ita tana da sabo da magana da barkwanci nikuwa ban cika son mutane ba.
To cut story shot Aisha is my sister from another mother. ita na fara na kira na gayawa mun hadu da Imam tayi matukar murna da jin hakan kuma! saidai ranar da suka fara haduwane naga wani irin tashin hankali mamaki da kuma tsoro a idonta amma kafin nayi wani abu tuni ta shanyesu ta aro nutsuwa da kamewa ta cike gurbinsu da su. duk yanda naso na fassara dalilinta na yin hakan na kasa har na hakura na bar abun cikin raina. haka rayuwa taci gaba Har akasa mana rana da Imam yanzu saura six months bikina dashi. Na dade da fara gano wani boyayyen al’amari a tsakaninsu. Amma sai na kawar da tunanin a raina ina ganin kamar kishi ne yaimun yawa. Idan muka zauna tare su kadai suke hirar kasancewar ni ba mai son magana bace. Kullum muna waya bamu da hira sai ta rayuwarmu da kuruciyarmu da Aisha. Kullum sai ya tambayeta. Ita kuma sai na soma observing ta sauya gabadaya bataso su hadu da shi idan zaizo na kirata muyi masa girki ko mu futa tare sai ta kawo wani excuse tun bana damuwa har na soma zargin wani abu. Amma yau kam Ihsan abun ya bani tsoro da mamaki. Na kirata fa yau da safen nan mace mata Imam zai dawo tazo gidanmu ta tayani nayi masa cincin tace mun ba zata samu dama ba tana da ayyuka. Toh a ina ta ganshi? A ina suka hadu ya dauko ta a mota? Meyasa zasu zo mun tare? I’m confused Ihsan i dont know what to do” patting bayana ta shiga yi tana cewa “issokay Zara. Insha Allah zamu gano komai..zamu bi komai a hankali kuma zamu gane bakin zaren don Allah ki daina damuwa dayawa ki kwantar da hankalinki. Sannan ki yawaita addu’a akan Allah ya bayyana mana gaskiya” na daga kaina ina goge hawayen da yake zubomun.
Ihsan bata gushe ba tana ta lallamina da rarrashi da kalamai masu taushi har na samu nutsuwa sannan kowa ya tafi gida da alkwarin zamu hadu anjima. saboda bikinta saura 4weeks ne kuma jibi zasu wuce Dubai ta karasa abubuwan da batayi ba tunda tun watanni da hudu da suka wuce suka je shopping din kayan aure har kayan sun iso komai na bukin an tanada rana kadai ake jira.
kasancewar ta ba mai yawan kawaye ba ya bani damar zama babbar aminiyarta cikin kankanin lokacin da mukayi tare daman ance sai hali yazo daidai ake abota. kusan duka halayena irin nata ne har na fita son mutane da magana wannan ya sanya yan’uwanta suke mamakin son da takemun da yawan maganata da takeyi. sai nace kawai Allah ne ya hada jininmu.
ina komawa gida nayi wa Imam text cewa bazan iya zuwa gidansu ba ya baiwa kannen shi hakuri don bani da lafiya! ina turawa na kashe wayar na jefar da ita kaina na wani irin sarawa.
dakyar bacci ya daukeni. cikin baccin na dinga jin dariya ina bude idona na ga Ihsan da Baba Rabi a kaina nayi saurin tashi zaune ina murtsika ido.”ihsan yaushe kika zo?” murmushi tayi tace “yanzun nan kina ta bacci” agogo na duba ga mamakina har karfe shida da rabi da azama na mike na shiga toilet na dauro alwala nazo nayi sallar la’asar. ina cikin sallah Aisha ta iso. a dan rude take tambayar Ihsan meya sameni?”ihsan tace kamar ya fa?” zama tayi a bakin gado tace “Imam ne ya kirani yace ta mishi text ba zata iya zuwa dinner din ba bata da lafiya kuma ya kira wayarta a kashe. ya nemi Ya Sadik yace baya gida. lokacin na kammala addu’a ta na shafa na mike ina cewa “zazzabine ya rufeni ina dawowa ga ciwon kai don haka na yanke kawai bazanje ba” Ihsan dai ta gano kan zancen don haka batai magana ba.
tare muka zauna muna hira Imam wayar Aisha ya kira ta hadamu mukai magana. ana magrib sai gashi da kannensa guda biyu sunzo dubani da uban birthday gifts dinsu kamar hauka.
ban samu kaina ba sai karfe goma da rabi sannan nayi wanka nayi shaf’i da wutri na kwanta. a maimakon bacci sai tunani yabi ya maye gurbinshi na rasa me yake mun dadi. ganin baccin ba zai zo ba na tashi na dauro alwala na soma nafilfilu ina kai kukana wajen Ubangiji. bani na kwanta ba sai da akai sallar asuba.
aikuwa ban iya tashi ba sai azahar.
wanka na soma yi na shirya cikin wata doguwar rigar plane voil pitch. na yane kafadata da bakin gyale na futo.
sai da nayi sallama da Dada sannan na shiga kitchen na dan tsakuri abinci don gabadaya raina da zuciyata a cushe suke. na dade a zaune a motata ina tunani shin wanne mataki zan dauka? ta wacce hanyar zan bullowa wadannan bayin Allah? meya dace nayi? sanin bani da amsoshin tambayoyina ya sanya na saka Cdn Maher Zaina cikin wakar “salam alaika” na kunna motar na soma tuki cikin sanyi a hankali wakar ke saukar mun da nutsuwa har na isa gidansu Ihsan.
yau muke meeting gabadaya kawayenta mu goma akan shirin bukin. order da mukayi na ashobin bukin daga Lagos duka sunzo. ganin su ya sanya na daure na saki raina mukayi abinda ya kawo mu cikin walwala da nishadi. cikin dabara ta janyo ni muka shiga dakin mummynsu muka zauna a bakin gado! a hankali ta soma magana tana gayamun tunanin da tayi da mataki na farko da ya kamata mu dauka.
bansan lokacin da na saki murmushi ba lokacin da ta kammala mun bayanin na rugumeta nayi mata godiya. sai shida na baro gidansu ihsan da niki nikin kayana na buki.
direct gidan Mamina na wuce. a kitchen na sameta bansan lokacin da na wullar da kayan ba na rungumeta ina ajiyar zuciya.
“toh ya isa dagani abinda nasa a oven ya soma kauri tunda ke ba zakiyi hankali ba har yanzu” dagowa nayi na turo baki nace “Haba Mami yaushe rabon da na ganki ina ta doki zanzo wajenki kuma zakimun haka? dariya tayi tana girgiza kai ta dauki gloves din tana sakawa tace “toh bari na kammala abinda nakeyi sai tasa ni a gaba kiyi ta kallo” nayi dariya kawai ina kallon abinda takeyi.
cikin ihu nace “wow!! beautiful” lokacin da take futo da take futo da katon cake din mai shape din heart! juyowa tayi ta kalleni cikin mamaki “Zarah kina tunanin shekarunki nawa kuwa? meyasa kike abu kamar na yayan goye?” sulalewa kawai nayi na bar mata kitchen din na debi kayana na kai bedroom dinta domin na taho da su ne ta bayar a dinkamun. nikuma nabi lafiyar comfy bed din mami na kwanta. ban taba jin gado me dadin shi ba a duniya don haka ina kwanciyar bacci yayi gaba dani.
farkawa nayi Mami tana jijjigani anyi sallah. na sauko daga gadon na shiga toilet nayo alwala nayi sallar magrib.
ni kadai naci gaba da dube duben a dakin har yanzu Mami tana kitchen abinda yasa raina ya dan fara baci babu tantama cake din dana gani maigidanta take yiwa har ma da girkin gabadaya watakila ma bataso zuwana ba shiyasa take ta mun fada. sai naji zuciyata tayi babu dadi. mikewa nayi na gabatar da sallar isha’i na yafa gyalena na rataya jakata na futo. a corridor muka hadu da ita zata shigo cikin mamaki tace “ina zuwa kuma?” raina a hade nace “Mami dare yayi zan tafi gida” cewa tayi “toh meye amfanin zuwan ko gaisawa bamu yi ba sannan nasha gaya miki banason tukin dare ko? na riga na bugawa Dada in Sadik yana nan yazo ya dauke ki tace ki zauna kawai gobe kya taho” tabe baki nayi nace “toh Mami ba aiki kike tayi ba tunda nazo fa baki kula ni ba” dariya tayi tace “Aww abinda ya saki fushi kenan toh Allah baki hakuri na gama aikin muje ciki” juyawa nayi tabi bayana.
sai da tayi sallah muka gaisa sannan na janyo ledojin kayan ashobin na gaya mata dinkunan da za’ai mun.
kallona take baki sake “Zara nikam kaya kala nawa kika dinka tsakanin bukin su Sadik da na Ihsan ne? kinsan kuwa barnar kudinki ya fara yawa?” cewa nayi “Mami nasani wallahi amma kinga duka bukin nice akan gaba dole nayi kwalliyar da tafi ta kowa ko don ma kowa yasan Mamana fashion designer ce” na kare maganar ina dariya. girgiza kai kawai tayi. zatai magana wayarya ta shiga ruri.
ni na tashi naje na dauko mata ita daga kan drower. “HAUSA ARAB” nagani da manyan bakake a kan screen din. a raina nace wacece kuma Hausa Arab ana zaune kalau.? ni dai na mika mata waya na soma hada kan kayan ina maidawa. ji nayi tana cewa “anya kuwa hakan da kayi kana ganin ka kyauta sosai ka bar bukin shakikanka kazo na aboki?” shiru tayi sannan ta sake cewa “na fahimta amma duk da haka ka sake nazari in kuma ba haka ba duka ka hakura don Allah ka dinga ragewa kanka damuwa ” ta sake yin shiru sannan tace “toh insha Allahu ka kula da kanka” daga nan sukai sallama! cikin nutsuwa na dube ta nace “Mami wanene?” kallona tayi domin bata taba yin waya a gabana ta gama na tambayeta da wanda take wayar ba. yau dinma kawai ji nayi na tsinci kaina da sanin wanene din! a hankali tace “Mahmud” cikin yamutsa fuska nace “waye kuma Mahmud?” harara ta sakar mun tana cewa “Mahmud dinne baki sani ba? Mahmud din Daddyn?” wow! sai yau na tuna da wannan halittar tun dawowarmu daga saudi. “Mami ya ake kuke waya dashi bayan ance ya daina kula kowa?” ajiyar zuciya ta saki sannan tace “ke! kin taba ganin inda da ya daina kula uwarsa? ke zaki iya daina kulani?” cikin mamaki nace “Mami har matsayinshi ya kai nawa a wajenki?” daure fuska tayi tamau tace “shi na fara samu ma kafin nasan zan sameki” sosai naji haushin abinda Mami tace har na soma dana sanin zuwa gidan. “gaskiya Mami yau dai i am not welcome a gidannan” banza tayi dani ta mike ta futa.
ina nan a zaune ta saka Hajjo mai aikinta ta kirani na same ta a dinning room!.
tura kofar da zanyi na tsaya galala ina kallon ikon Allah. katon table din aka cika da snacks da lemuka da kuma zungureren cake mai shape din heart a tsakiya an rubuta “My baby is 22” Allah sarki Mami. ashe duka aikin da nake jin haushin ta akansa ni takewa. a sanyaye na rugumeta ina hawayen murna! buga baya na take tana cewa “Happy birthday Zara Allah ya karo shekaru masu albarka ya raya munke cikin aminci da albarkarsa” a hankali na dago fuskata shabe shabe da hawaye nace “thank you soo much Mami i love you” daga ni sai ita muka yanka cake dinmu muka ciyar da juna.
but i can say it is my favourite birthday wallah! bayan mun kammala cin abubuwan da tayi mana ta kuma dauko wani madaidaicin box ta bani. cikin doki na bude! duka idanuna na zaro a sakamakon ganin wata azababbiyar sarka da yarinta na gold masu nauyi. duk yanda naso na nuna mata farincikina kasawa nayi. har tausayi take bani domin bata da wani buri irin ta faranta mun.
har kafe biyun dare muna kwance akan daddadan gadonta muna hira ni dai bansan lokacin da nayi bacci ba.+Duka wasu shirye shirye da tsare tsare sun kammala daga fannin angwaye da amare. invitation card yaje hannun duka wadanda ake bukatar su halarci wannan taro a yau lahadi kenan da ya rage saura kwana biyu a soma gabatar da shagulgulgunan wannan buki. gareni abun ba haka yake ba domin ni kwanakin yinsu nayi cikin gudanar da assignment dina na farko akan alakar da ke tsakanin Imam da Aisha. na fara bincike na ne ta bangaren daga wayar Aisha da ta Imamu wadanda suka kasance basu da wuyar zuwa hannuna. duk da ba karba nayi kai tsaye ba fakar idonsu kawai nakeyi na dauka.
na fara da wayar Imamu ne a ranar da yazo gidanmu ya kai sallar magrib sai ya zube wayoyinshi da hula ya futa da Ya sadik suka tafi masallaci bayan ya ga shigata ciki. suna futa nikuma na dawo na dau wayar. guda daya akwai password dayar kuma babu. ita na dauka na nemi waje na zauna na fara bincikawa. da messages dinshi na fara kirjina na dukan uku uku da fargabar abinda zan gani.
banyi nisa ba naga sunan Aisha anyi saving da besty kamar yanda ya saba kiranta a gabana. swiping nayi sai da nazo na can farko wanda suka fara musaya. sai da na rufe idona na bude ina karanto duka addu’ar da tazo bakina sannan na bude text din. ga abinda idona ya fara cin karo dashi:+
“Na bar diary na a motarka i am begging you with name of Allah kada ka bude mun ko da wasa kada ka bude mun. sirrina ne kuma Allah ya hana bude sirrin wani ina hanyar zuwa gidanku na karba in nazo bakin gate zan ma waya”
Ga kuma kwanan wata nan. na duba wata biyu da suka wuce kenan!
banga amsar da ya bata ba sai wani text din da ita ta sake turowa tana cewa
” Ko da wasa Imam kada ka dauki wannan maganar da muhimmanci domin ko a mafarki haka ba zai taba faruwa tsakanina da Zara ba domin in akwai wata halitta mai muhimmanci a wajena Zarah ce”
kaina yayi mugun daurewa da wannan maganganu da kuma abinda suke nufi. na sake dauriyar cigaba wannan ma itace ta tura masa.
“Kada kayi kasadar yin wannan
gangancin domin babu abinda zai janyo sai kiyayya da gaba da kuma tashin hankali mara iyaka. duk duniya banga abinda ba zan barwa Zarah ba ciki har da farincikina”
Ya salam! na fada gumi na tsatstsafo mun domin rashin sanin yanda wadannan maganganu suka dosa kai tsaye. sanin bani da lokaci ya sanya na sake cigaba sai a lokacin naga reply din Imamu wadda naji kamar zanyi zawo kafin na bude.
“idan hakan na nufin kunnowar
3rd world war i’m never gonna let this go! and i promise you zan tsaya akan maganata a kowanne rintsi”
Gabadaya kaina ya kulle tamau na rasa gane wanne tunani zanyi na fahimci yaren da sukeyi? wacce hanya zanbi nagane inda maganar ta dosa? meye suke jayayya akansa?meye ya harzuka Imam yayi wannan alkawarin? cikin sanyin jiki da rawar hannu na cigaba da karatun text na gaba da Aisha ta turo mako biyu da suka gabata.
“Imam ka sameni a park and zoo yanzu kuma kada ka taho da motarka”
Duka idanuna na zaro hankalina yayi bala’in tashi! har haduwa suke a wani waje? innalillahi wa’inna ilaihi rajiun!! me ke shirin faruwa dani ne?
Text na karshe dake cikin wayar kwana uku da suka wuce Imam ya tura mata! ga abinda ya rubuta
“Thank you! i will try my best insha Allah”
kasa nayi da wayar cikin sanyin jiki da kunar zuciya da fargaba mai yawa. na tabbatar akwai wata alaka mai karfi da ke tsakanin Aisha da Imam. akwai kuma abinda suke kullawa sannan ba wannan text din bane iya communcation dinsu. nayi iya bincike na babu abinda na sake samowa cikin wayar sai na mayar da ita na ajiye.
ko da ya dawo nayi matukar kokari ban nuna mishi komai ba don haka mukai sallama kamar yanda muka saba ya tafi.
Ta fannin Aisha kuwa a E-mail dinta na soma gano wani abu. ranar da zan bude naga ta sake password abunda ya bani mamaki domin babu wani account dinta na social media ko nawa wanda bamusan password din juna ba.(do you see how close we are? do you understand how attach our lives are) kiranta nayi na tambayeta sai tace babu komai kawai ta sauya ne kuma zata turomun sabon Password din. maganar da har yau bata turo ba nikuma ban sake mata maganar ba.
ranar wata monday na je gidansu na samu Aisha bata nan Umma ta aikesu kasuwa da Driver. cikin sa’a na shiga dakinta sai naga system dinta yashe akan gado a kunne da azama na hau gadon na dawo da hasken screen din na saka password. unfortunately tana cikin karanta messages dinta na E-mail aka kirata ta tashi ta manta bata futa daga ciki ba. ban sha wahala ba nagano sakonnin Imam!
zuciyata na bugawa na shiga dubawa ban samu damar gane yaren da suke ba kamar yanda nagani a tashi wayar amma lallai rokonta yake tukuru akan wani abu wanda ita kuma taki yarda. musamman a wata message da yake cewa
STORY CONTINUES BELOW

“Aisha yanda kika dauki rayuwa
ba haka take ba. ba duka abinda kake so kake samu ba kuma ba sai lallai ta yanda kakeso abu ya kasance yake kasancewa ba. Don Allah Aisha ki fahimci maganar nan ki kuma yi adalci kafin ki yanke hukunci. ki saurari zuciyarki da kyau kada ki yanke abinda daga baya zaki yi dana sani”
wasu siraran hawaye ne suke bin karan hancina masu hade da zugi da radadin zuciya. Ya tabbata kenan Aisha da Imam amanata suke ci!
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!! Aisha of all people?? meyasa Aisha zatai mun haka?? meyasa zata yarda da Imam ya shiga tsakanin amincinmu? meyasa zata so mutumin da nayi zurfi a soyayyarsa? meyasa zata zabi son wanda aka samun ranar aure da shi? a hankali na dinga maimaita sunan Allah a bakina har zuciyata ta samu nutsuwa. gaban mirror naje na dau kwalli na saka a idona sannan na shafa powder.
Na dauko jakata da gyale na futo! Umma ce tace “ah ah Zara ya zaki tafi? yanzu fa zasu karaso! murmushin karfin hali nayi nace “wallahi Umma banyi niyyar tafiya ba baki mukayi daga Yola Dada ta kirani na taho?” cikin far’a Umma tace “wai biki fa yazo sai saukar baki toh bakomai zan gaya mata. ki gaida gida” nan mukai sallama da Umma na shiga motata na taho gida.
a gefen hanya na sauka na dau waya na kira Ihsan da ke Dubai bugu biyu ta dauka! cikin kuka na zayyane mata duka abubuwan da na gani. hakuri tayi ta bani tana karfafamun guiwa har na samu nutsuwa sannan tace “Zara mu bar maganar sai na dawo gobe InshaAllah!” nace “toh Allah ya kaimu Ihsan i’m sorry for taking your time” da sauri tace “what are true friends for? haba Zara banason haka duka abinda nayi miki kaina nayiwa. yanzunma kinga muna Dubai mall ne bani kadai bace shiyasa” bayan munyi sallama na karasa gida na same shi cike taf da yan’uwa na Katsina da na Adamawa da Kano. gidan babu masaka tsinke. ni dai kawai tattara kan kayana nayi acikin akwati na saka a mota na wuce gidan Mami domin bazan taba iya zaman wannan hayaniyar ba. musamman yanda zuciyata take a kusa.
Tun ranar talata muka soma buki na gaske kamar ba’a taba buki a Abuja ba. amaren sun dage kowacce tanaso tafi daya burgewa! nikam yanda naci burin bukin ba haka yazo mun ba. ina cikin zulumi, tashin hankali da tunani. Don haka gabaadaya bana gane komai. kullum muna tare da Ihsan da Aisha kamar babu abinda yake faruwa sai mun kebe da Ihsan muke samun lokacin magana. Imamu babu shi akai bukin ya tafi China.
Ranar Juma’a da safe muka kammala shiryawa muka tafi gidanmu domin yau ake daurin aure! gidan a cike yake bamu samu Dada a wajenta ba tana can bangaren su Ya Sadik ni da Mami muka wuce don gaisheta.
tundaga nesa muke jin sautin muryarta cikin tsananin fada da zafin rai. da muka isa kuwa dagani har Mamin bamu samu kuzarin karasawa ba don tsoro. tayi hausa tayi fillanci tayi kuka kamar zata tada iska duka akan wai Mahmud baizo bukin kannenshi ba. kuma ba kowa takewa fadan ba illa Daddy da Kawu Sulaiman da Inna Badi’atu! yayanta kenan! ni dai babu shiri na koma da baya nayi waje bansan lokacin da Mami tayi jarumtar shiga ciki ba.
kai Dada babu kyau idan aka bata mata rai! bata iya fushi ba bata iya fada ba. sai dai abinda yake birgeni da ita kawai bata fada akan rashin gaskiya.
a dakina na samu Ya Nuratu idonta yayi jajawur tasha kuka gefenta Amal na bacci. basu samu zuwa da wuri ba duk yanda taso su taho din sai jiya. a sanyaye na isa muka rungume juna sannan na saketa muka zauna a bakin gadon.
“menene ya faru Ya Nuratu? me hada Dada da su Daddy haka?kinji irin fadan da takeyi kuwa?” cikin muryar tausayi take cewa “nima fadan ne ya futo dani na taho nan bazan iya jurewa ba Zara. wai kawai don Ya Mahmud baizo ba! for goodness sake mutumin nan shekararsa goma baizo gida ba yana can cikin rayuwar kadaici wadda shima ba shi ya dorawa kansa ba amma kullum Dada bata daina ganin laifinshi ba bata daina tara su Daddy ta zaga akan laifin Mahmud ba? su sukayi mata? ya zasuyi dashi? saboda Allah duk taro a maimakon ayi cikin farinciki a kare sai Dada ta hadawa iyayenmu bacin rai a dalilin rai daya tak? mutumin da ita kanta take bada shaidar biyayyarsa da ladabinsa kafin faruwar abinda ya same shi? ta hakura mana?” nidai ban tofa komai ba baya ga sanyin da jikina yayi da kuma tsanar wannan mutum da ta ninku raina! shi bashi da aiki sai batawa iyayenmu rai? bashi da aiki sai sanya mutane bakinciki? mtsw! “Allah ya kyauta” abinda na iya cewa kenan na tashi na shiga toilet!
A central mosque aka daura auren gabadaya suka wuce Transcorp Hilton sukayi reception sannan suka je gidan amaren. mu basu shigo gida ba sai wajen la’asar.
Nan fa aka soma budiri kida ne, hotuna, rabon abinci gidan kamar zai dare duk girmanshi. bamu samu mutane sun ragu ba sai da magriba yau har Ya Nuratu muka tafi gidan Mami don na lura itama yar jam’iyyar Mahmud dince. bata kaunar ace yayi ba daidai ba. ita kuwa Mami can kuryar daki ta shige tana waya tun da muka dawo ko ita da waye oho?!
Anyi taro an kammala lafiya kalau cikin farinciki da kwanciyar hankali sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya. duka baki sun koma inda suka futo kowa ya dauki hanyar garinsu.
Ya Nuratu ma bayan biki da kwana biyu ta koma saboda karatun Amal.
mun matukar shan wahala kafin gidan ya gyaru ya koma yanda yake.
nidai kam ban samu zama ba domin wani bukin ne a gabana.
Ranar litinin Imamu ya dawo daga tafiyarshi amma abun mamaki baizo gidanmu ba. abinda bai taba faruwa ba duk inda yaje ko da tafiyar sati daya ce ranar da ya dawo yake zuwa gidanmu sai dai in saukar dare yayi.
lokacin da ya mun waya yana bani hakuri ina zaune a dakina ina packing akwatina don gobe zamu tafi Gumel in baku manta ba Ihsan mahaifanta gabadaya haiffafun Gumel din jihar jigawa ne. kuma duka family dinsu in zasu yi aure can suke zuwa suyi. maigirma sarkin Gumel Malam Mamman Adamu kanin mahaifin Ihsan ne uwa daya uba daya kuma tun bayar rasuwar mahaifin su baban Ihsan din shine ya maye gurbin uba a gare su daganan aka dora shi a mukamin yayan nashi. don haka a Gumel za’ai buki a daura aure sai ranar juma’a zamu dawo Abuja a karasa dinner guda biyu ta gidansu Ihsan da ta ango. Bayan na aje wayar ne na kira Aisha don naji idan ta shawo kan baban nasu ya yarda zamu tafi tare. yace shi bai san Ihsan ba don haka ba zai barta ta tafi wani gari buki ba sai dai ta hakura taje wanda za’ayi a Abuja.
sai da tayi ringing yafi sau biyar sannan aka dauka.
“Aisha kina ina ne donAllah?” muryar Ikram immediate sister din Aisha da ke boarding a Ulul Albab katsina naji. cikin far’a nace “oyoyo Iky yaushe kika dawo?” cikin dariya tace “dazu muka dawo da Abba” nan muka shiga gaisawa ina tambayarta karatu daga nan nace “ina Aisha take?” cewa tayi “tayi bako wallahi tun dazu amma idan ta shigo zan gaya mata!”
Ras! gabana ya fadi! bako? wanene bakon? iya sanina Aisha bata da saurayin da yake zuwa gidansu saboda tsaurin Abbanta yace in karatu karatu in kuma aure tayi aure! toh wanene yazo wajenta? wani sashen na zuciyata ne yace “IMAM!!”
a fili nace “haba! no! hell no! ita can’t be! wallahi ba zaiyu ba. haukata ni kuke so kuyi? me nayi muku?” wani irin kuka ne ya subucemun na kifa kaina akan jakar kayan da nake hadawa ina kuka mai tsananin ciwo da bakin ciki.
Happy Independence day my dear Nigerians!!May Allah continue to bless our nation!
Happy birthday to my baby girl Salamatu Bello Danbatta! Aka Acici💕💕💕💕
one of Hausa Arab’s Fan💖
i love you girl!! wish you more beautiful years and Allah’s khair!
enjoy this chapter as you celebrate your 30th😛😜sorry 28th😂 birhday!
LONDON
———————————————————–
Zaune yake kan lallausar kujeran da ke falonshi ya mike zara zaran kafafunshi akan center table yana karkada su a hankali. kallo daya zakai masa ka gano tarin damuwar da ke kwance acikin zuciyarsa wadda kyakykyawar fuskarsa ta bayyana.
Idanunsa a lumshe suke yayinda zuciyarsa ke tunkushe da tunani da bacin rai da damuwa marasa adadi.
a hankali ya soma tari yana danne kirjinsa don azabar da yake ji daga saitin kirjin nashi na hagu. sai wani bugawa yake yi kamar zai ballo waje.
Tun yana tarin a hankali har ya soma cin karfinshi. a galabaice yake karanto kalmar shahada cikin saduda da rayuwa da duk wani abunda yake cikinta. cikin mintina kalilan ya birkice numfashi ya soma gagararsa idanunsa suka soma kakkafewa yayinda ya dora duka hannayensa akan kirjinsa. a hankali jini ke futowa ta bakinsa yana gangarawa kunnensa da habarsa har fara sol din shirt din jikinsa ta soma rinewa da jinin.
cikin wannan hali Safna tayi sallama ko nace tayi knocking a kofar kitchen. Sharifa da bata san abinda yake faruwa a gidan ba ita ta tsame hannunta Daga cikin girkinta ta bude kofar. harara safna ta zabga mata ta wuce cikin gidan kai tsaye ba tare da ta amsa gaisuwar yarinyar ba.
tana saka kafarta a parlour taci karo da tashin hankalin da ya sanyata zunduma ihu ta ruga a guje tana girgiza Mahmud. ina! tuni hankalinsa ya gushe ba ya fahimtar komai sai kokawa suke da numfashi.
Ihun Safna ne ya janyo hankalin Sharifa da ke kitchen ta shigo falon a guje! itama ihun ta kurma ganin halin da ubangidan nata yake ciki.
cikin azama ta dauko waya ta nemi asibiti. mintina kalilan kuwa ambulance ta iso aka kinkime Mahmud akai asibiti dashi. tun daga motar suka sanya masa robar taimakawa numfashi Safna na rike da hannunshi tana faman kuka har suka isa Liverpool hospital wato asibitin da yake aiki. nan da nan likitoci suka karbe shi tare da rufuwa akansa don ceto rayuwarsa.!!
———————————————————–
NIGERIA
Na kai awa daya a zaune a wajen ina kuka kafin na tashi na shiga toilet. ruwa na hada na shiga na zauna naci gaba da tunani dakyar nayi wankan da alwala na futo nazo nayi sallar isha’i na kwanta. ranar ko abincin dare bansa a bakina ba. haka na dinga juyi a gado sai wajen asuba bacci ya daukeni. ko da na tashi da safe idona yayi lunkuma lunkuma saboda kuka da rashin bacci. Wayar Ihsan ce ta tasheni da sai na makara magiya take mun na taho da wuri mu wuce tare flight daya. don haka nayi maza nayi wanka na shirya cikin sabuwar Sheraton Super olive green mai ratshin purple. make up din dole na zauna nayi don kar a gane nayi kuka.
bayan munyi sallama da Dada Na shiga mota na wuce gidan Mami inda na sameta tana cikin motarta tana jirana. cewa tayi da kanta zata kaini gidansu Ihsan ta danka amanata a hannun Mamansu lolz!(Mami is overprotective) jakar kayana na ciro daga booth din motata wadda zan bari anan gidan Mami zuwa motarta.
muna tafiya muna hira har muka isa gidansu Ihsan. Da matukar murna da jindadi Mamansu Ihsan da yan’uwanta suka karbi Mami abinda yasa ta kara jin dadi kenan. Anty Batulu kanwar maman su Ihsan ita tace wa Mami “kinga ni zan karbi amanar Zara. kafata kafarta harmuje mu dawo lafiya insha Allah kamar tana hannunki ko kuda bazan bari ya taba ta ba” aka kwashe da dariya. cikin mutunta juna aka rako Mami har wajen mota sannan suka juya. kallonta ta dawo dashi kaina tace “Toh Zara ki kula da kanki! ki kula da kanki don Allah in bana ganinki Allah yana ganinki. banason shirmen banza banason yawo banason shige shige ki rike mutuncinki don wallahi ba don ina ganin mutuncin Ihsan ba bazan taba lamunta ki tafi wani gari buki babu ni ba don haka ina jan kunnenki da ki nutsu.” cikin murmushi nace “duka na rike wannan Mami Insha Allah zan kiyaye bazanyi abinda nasan bakyaso ba” tace “good” sannan ta bude jakarta ta ciro rafar yan dari biyu ta bani. na amsa nayi mata godiya sannan mukai sallama.
muna hanyar Airport naga kiran Aisha. kamar bazan dauka ba dai na daure na daga! “hello besty kuna ina?” bata san yanda in ta kirani besty din nan yanzu nakeji ba da ta daina. “muna hanyar Airport” na bata amsa a takaice! ta sake cewa “banji dadin yanda Abba ya hanani bukin nan ba wallahi Zara ki baiwa Ihsan hakuri” cewa nayi “babu komai zan gaya mata. na kira ki jiya ai naji yanda kuka yi dashi Iky ta dauka tace kinyi bako” sai da ta danyi jim sannan tace “eh wallahi bama bako bane don dai yana sauri ne bai shigo cikin gida ba” tabe baki nayi a raina nace “ya shigo daki ma wannan matsalarku ce macuta kawai” a fili kuwa cewa nayi “ok! ki gaida Umma sai anjima” mukai sallama! Ihsan da ke gefena ta kalleni tayi murmushi nima na mayar mata “take it easy please kada kiyi wani abu da zamu dawo muna da munsani bamuyi ba. har yanzu fa bamu da hujja kuma in mukabi komai a sannu a hankali sai munfi samun nasara” nace “hakane ina matukar kokari Ihsan abun is not as easy as you think amma ina addu’a” dafani tayi tace “yess! addu’a ce kadai abun yi. so please kiyi chasing duk wata damuwa daga ranki it’s your girl’s wedding” ta kare maganar tana dage gira! dariya nayi sosai a raina ina tunanin yanda muke da Aisha da shakuwarmu! hooo duniya gidan rikici!
kafin azahar muna cikin garin kano inda muka tarar da convoy din bakaken luxury cars suna jiranmu.
kyakykywar tafiyar awa biyu babu gajiya ko gargada balle tsalle tsallen hanya saboda ingancin motocin suka kaimu Fadar Gumel.
inda ya kaure da kade kade da bushe bushe da guda na isowar amarya.+
STORY CONTINUES BELOW

katon daki da parlour aka ware mana mu da Amarya. nan fa nishadi da raha ya balle kamar gidan chasu suka ware music a cikin manyan spikun falon suna rawa. nidai tattara kaina nayi da damuwata na koma daki nabi lafiyar royal bed din na kwanta. ban dade da kwanciya ba bacci yayi gaba dani. cikin baccin naji ana mun tafiyar tsutsa a tafin kafata na bude idona na sauri ina janye kafar! Ihsan ce take mun dariya. tashi nayi zaune ina murtsuka ido. a hankali ta taso ta dawo gefena ta zauna ta dafa kafadata “how many times zan gaya miki din Allah don Annabi kiyi hakuri ki taushi zuciyarki Zara ki ragewa kanki damuwa da tunani? do you want to spoil my mood on my wedding day?” murmushi nayi sosai ina matukar girmama kulawar da Ihsan take bani. ta mayar da damuwa ta tata ta karfi da yaji kamar cikinmu daya. cikin murmushi na dubeta nace “bacci fa kawai nayi Ihsan I am fit and fine! Insha Allah babu damuwa har mu kammala buki mu kaiki gidan Faisal” maganar ba karamun dadi tayi mata ba sai wani blushing take. a karshe dai ta tasa ni a gaba muka futo inda aka shirya domin kunshi. Henna Artist kwararru aka debo don yi mana kunshin buki. wadda tayiwa Ihsan ita tamun ga mai gyaran jiki Hajja Yakura. A.batulu ta nemo ta daga Maiduguri tun sati biyu da suka wuce take magic dinta akan Ihsan wadda ta koma kamar an baro daga kwai. wannan karon nima bada kaina nayi aka mun saboda magiyar Ihsan. duk abinda tasan zai debemun kewa shi take yi har tausayi take bani. kafin dare idan ka ganmu ba lallai ka gane mu ba saboda yanda muka futo ras!
A fadar mai martaba aka daura auren Faisal da Ihsan wanda ya samu halartar daruruwan jama’a da manyan kusoshin gwamnati da ma’aikata da shahararrun yan kasuwa harda sarakuna. ranar kam garin Gumel ya cika ya batse bakya jin komai sai tashin algaita da kalangu. maroka sun samu abun nema sai kwarzanta mutane suke ana yi musu ruwan kudi.
a dai dai wannan lokacin muna cikin daki da Amarya “Mamza beauty” na aikin da aka fi saninta da shi. ta kammala wa Zara shiri cikin fararen kayan da sukai matukar amsar ta. sannan nima ta dawo kaina. tawa kwalliyar leshi ne mai nauyi lemon green mai ratsin maroon. ni kaina na yarda da kwalliyar domin nayi kyau.
sauran kawaye “Dazeita” ce take bata basirar ta akansu kowacce kika kalla sai kyalli take kamar duka amaren ne.
A.batulu ce ta iso cikin tata kwalliyar ta futa da Amarya muka dafe mata baya. har babban dakin baki na cikin gidan inda babansu Ihsan da tawagarsa suke. Nan fa aka shiga gaishe gaishe da hotuna. “bigH” da “maigaskiya” na daga gefe suna abinda ya kawo su. bayan mun kammala da Daddynsu Ihsan ne muka futo don isa wajen angwaye da suke ta jiran isowarmu.
gabadayansu ankon gold din shedda sukayi manyan riguna shikuma ango nashi kalar na Amarya wato “white” na dade banga perfect match irin su Ihsan ba da suka tsaya kafada da kafada ana dukansu hoto, kowanne farin shi na haska na dan’uwanshi kamar ka taba fatarsu jini ya bulbulo don tsananin fari da hutu rantsewa zakai daga Beirut aka kwaso su ba yan Nigeria bane.
Ina tsaye na hango Imam na tahowa cikin far’a. sai na tsinci gabana yana wani irin faduwa har sai da na danne da hannunna ina karanto innalillahi wa inna ilaihi rajiun! murmushinsa ya fadada lokacin da yazo dab dani.
” My bride to be is looking breath taking” abinda ya soma fada kenan! murmushi nayi wadda ya tsaya daga fuskata kawai. sannan muka soma gaisawa. mun dade a tsaye kafin ya mun sallama zasu tafi masaukinsu sai anjima zamu hadu wajen lunching.
Ranar juma’a da safe muka juyo garin Abuja cikin kewar Gumel domin iya karramawa an karrama mu. sannan bukin yayi matukar armashi da burgewa. komai yayi tsari kuma anyi an gama lafiya. sauranmu Grand dinner da Mothers eve sannan budar kai da kuma kai Amarya duka a garin Abuja.
muna isa gidansu Ihsan na dauki motarta na tafi gidanmu. a gajiye tibis nake din haka muna gama gaisawa da Dada na shiga dakina na kwanta na huta. daga hutun bacci mai nauyi yayi gaba dani. ga wayoyina duka a kashe. nidai ban tashi ba sai azahar. salati nake ina salallami na mike na sauri na fada toilet nayi wanka da alwala na futo.
ina idar da sallah na zazzage kayan jakar da na dawo da ita daga Gumel na shirya wadanda zanyi amfani da su na kulle jakar. cikin sauri na zura simple gown nayi rolling fuskata da siririn gyale na futo. ban tsaya cin abinci ba na taho gidan Mami abun haushi na sake dakar gurbi batanan tana Office. haka na sake wucewa Zara Couture wajenta sannan na dawo gidansu Ihsan. ko zama banyi ba Imam yamun waya yana cikin gate dinsu Ihsan na futo. nace masa toh.
Yana tsaye yayi kyau kamar kullum duk sanda ya tafiya ya dawo sai kiga kamar wankan inji yake zuwa yi. Yayi wani fari dau!! Da murmushi yace “babbar qawar amarya” nayi dariya nace “tsokana ne abun ma?” Hannunsa yasa saka cikin aljihu yana kallona kamar mai tunanin wani abu har sai da na hure masa ido sannan yayi dariya ya dawo hayyacinsa. “Me kake tunani?”
Wayancewa kawai yayi yace mun “babu komai kinyi kyau ne” na dan tabe baki nace “bansan lokacin da zaka fahimtar dani abinda yake damunka this days ba,,you have changed alot” bai tanka maganata ba illa ma sauya zancen da yayi da cewa “ina bestinmu?” Harara na dalla masa nace “tana cikin jakata” ya kyalkyale da dariya. “Anyway kawai zuwa nayi na ganki bari na koma kar na hana ki shirye shiryenki ko?” Ina shirin magana Aisha ta shigo gate din cikin mota. Gabadaya Imam tsayawa ya kurawa motar ido kamar bai taba ganin mota ba sai yau. A hankali ta bude murfin ta futo…tayi masifar kyau cikin wani jan swiss lace skirt and blouse da yayi fitting figure dinta. ta yana dan mitsitsin gyale a kanta babu dankwali sai wata kwantacciyar suma baka wuluk. She is “black beauty” tana hangomu ta soma wangame hakoranta gabadaya kamar me tallan colgate…
Imam na sake duba gabadaya jikinsa yayi sanyi kamar mara lafiya. Ina ganin yanda kirjinsa ke kai da kawo.
“Heloo.. Romeo and his Juliet” ta fada sanda ta iso dab damu. Duka dauriyar da nake da ita na tattaro nayi mata murmushi ina cewa “sai yanzu?” Ta matso ta dafani tace “wallahi Iky ce bata danji dadi ba mukaje asibiti” cikin tausayawa nace “ayyah meke damunta?” gyara tsayuwa tayi tace “mura ce mai karfi ta kamata” nace “Allah ya bata lafiya” cikin murmushi tace “ameen” sannan ta dubi Imam da wani irin kallo mai ma’anoni dayawa tace “Romeo sai anjima na shiga ciki” a hankali lebbensa suka furta mata “okay..later” ta wuce ni.
Ko bayan ya tafi na dade tsaye a wajen kaina a daure zuciyata na kai da kawo. Wai menene yake faruwa dani ne? Ta ina zanbi na kwance wannan kullin da wadannan bayin Allah suka kulla mun? meke faruwa da rayuwata? menene mafita?”
LIVERPOOL LONDON
———————————————————–
Yau kwanakin Mahmud biyar a gadon asibiti yana karbar kulawa ta musamman. likitoci sunyi iya bakin kokarinsu wajen ceto rayuwar Mahmud a lokacin da numfashi ke mar barazanar yankan kauna. cikin ikon Allah sun shawo kan matsalar sun kuma yi masa abinda ya dace.
Ciwon sa ne na tsayin shekaru tara ya tayar masa wato ciwon zuciya wanda tsananin damuwa da tashin hankali suka haddasa masa. tun bayan lokacin ko sau daya ciwon bai sake waiwayarsa ba a dalilin matukar kokarin da yake yi wajen bin doka da ka’idojin ciwon da kuma gudunmuwar babban amininsa Faisal da Uwar da babu kamarta Mami da kuma girma da darajar Addu’ar da mahaifinsa yake yi babu ji ba gani a kansa. a wannan karon ba wani abu ne ya tada ciwon ba illa tsundumowar Safna cikin rayuwarsa a lokacin da bai tsammani ba ko a cikin mafarki. Bai taba tunanin nan kusa ko nesa wani abu mai kama da soyayya zai shigo cikin rayuwarsa ba domin yasan tuni ya tattara abubuwan masu kama da soyayya ya haka rami
mai zurfi ya binne! rayuwa yake mara hope ko buliding future sai dogara da Allah da kuma bin abinda duk ya shigo masa ba tare da neman zabi ba.
A dai dai lokacin da ya saisaita rayuwarsa ya dau damarar cigaba da rayuwa cikin wannan yanayi ya sadaukar da duk lokacinsa da gabarsa da zuciyarsa da aljihunsa ga ceto ran bayin Allah da taimakawa na kasa da shi sai wani babban al’amari ya bullo wanda yayi masa gingiringim a kai a ranar da ya kai ziyarar amsa gayyata ga Eng Garba Galadanci.
Labarin da ya gaya masa game da Safna ya girgiza shi ya wujijjiga shi ya kuma tsaya mishi rai. ba wannan ne na farko da ya samu mace tace tana sonsa ba ba shine na biyu ba ba kuma na uku ba. hakan ya zama jiki a tare da shi tun daga kan turawa hausawa indiyawa harda larabawa mazauna London babu kalar budurwar da baiyi ba. illa iyaka dai su suke kidansu suyi rawarsu akansa sai kalilan da sharrin tarkon shaidan ya yi tasiri akansa ya dan basu lokacin yin waya da shi na wasu makonni ko watanni daga haka kuma sai ya barar da su ya fuskanci wasu. a karshe ya tattara su yayi holi dasu kwata kwata don ya gano suna bata lokaci ne da surutan banza da na hofi.
Ga Safna har ga Allah tausayin maraicinta da halin da ta tsinci kanta aciki ya ladabtar da zuciyarsa ba wai so ba. domin ya dade da sanin cewa So guda daya ne tak! kuma yayi shi ya gama. sannan ita Safnar wata gwana ce wajen janyo hankalin dan’adam da duk abinda ta fahimci yafi so. da wannan damar tayi amfani ta janyo hankalin Mahmud har ta samu burbushin matsayi a gefen birnin zuciyarsa kuma da alama kofar shiga ainihin zuciyar tashi tana dab da bude mata ta shiga daga ciki. Duk sati take tattaki da kanta ta taho daga cikin garin London tazo Liverpool wajensa ba kuma zaman banza take ba tunda ta fahimci son da yakewa abincin gida musamman na gargajiya ta ware kwanji tana yin abinda bata taba zaton zatayi din ba. wato girkawa wani mahaluki abinci. sai gashi a dalilin soyayya har kalolin da bata sani ba take nemowa ta koya ta sarrafawa Mahmud. wadannan abubuwa suka taru suka hana Mahmud yi mata korar da ya saba yi wa yan matansa. suka kuma hana shi gwale ta. Domin irin so da kulawar da Mahmud yake samu daga Safna babu mahalukin da zai ture su duk iyaka bakin halinsa. balle Mahmud mutum ne mai sanyin zuciya da nagartattun halayen kwarai sai dai kafin ka fahimci hakan sai ka zauna da shi kayi mu’amala da shi.
kwanakin da yayi a kwance Safna kullum tana cikin zaryar asibiti. duk da basa bukatar mai jinya a asibitin yake wuni ta dawo gidanshi ta kwana.shi dai Eng ya zubawa sarautar Allah ido yana mata addu’ar samun shiga a wajen burin nata.+
A ranar da ya cika kwana goma a ranar aka sallamo shi. tare da Safna suka shigo gidanshi. Ita ta tsaya a kitchen ta samar masa dan abinda zai ci shikuma ya wuce dakinsa.
wayarsa ya dauka ya kira Faisal a karo na goma bai dauka ba. lallai Faisal yayi fushi da shi tunda har yayi kwanaki uku yana kiransa bai dauka ba. kuma da alama yana da niyyar cika alkawarin da yayi ikirarin dauka akansa idan har ya kasa halartar bikinshi. gashi yau Thursday tuni anyi daurin aure babu shi. “Ya salam” ya dafe kansa yana tunanin abunyi. da azama ya janyo laptop dinshi ya soma booking din jirgi zuwa Nigeria cikin rashin sa’a bai samu jirgin yau ba sai dai gobe da daddare. sai da ya kammala sannan ya samu nutsuwar shiga toilet yayo wanka da alwala.
bayan ya idar da sallah ne yana shirin kimtsawa Safna ta turo kofa ta shigo.
da mamaki ya kalleta fuskarsa daure!
ganin tana shirin zama yayi gyaran murya yace “Ahm Safna wannan ba tarbiyya bane ki dinga shigomun daki anyhow ko knocking babu! kin manta ni ba muharramunki bane ko? in kin manta na tuna miki! banason wadannan al’adun aron daga addinin da ba namu ba. please ki dinga kiyayewa!”
jikinta ne yayi mugun sanyi bata ce komai ba ta mike ta futa. yayi gajeran tsaki yana la’antar rayuwar da musulmai suka daukarwa kansu a dalilin zama cikin turawa. shi kansa Eng din ya rasa sakaran ina ne da zai bar ‘ya kamar wannan ta taho wajen saurayi kwanaki sama da goma don lalacewa! yana shafa man yana tsaki har ya kammala. shigar bakaken kaya yayi na bacci ya futo ya same ta a falon.
kamar yanda ya saba ledar cin abinci ta shimfida masa a kasa ta jera abincin da tayi masa. Minced meat macaroni da soup din kaza. sai kunun tsamiya a gefe. kasancewar baya jin dadin jikinsa ya sanya kunun kadai yayi shan kirki sannan yasha magungunansa. yana kammalawa ya dauko key din daya dakin ya bude ya nuna mata ta shiga ta kwanta ya dora da cewa “gobe ki tashi da wuri tare zamu shiga London. inason zuwa 7 mun futa” cikin mamaki take kallonsa. a ranta tana so tace masa jikinsa bai gama kwari ba da zai soma futa saidai yanda ya daure fuska tamau kwarjininshi ya hanata cewa komai bayan toh. ya juya ya koma dakinsa ya kwanta.
washe gari kuwa ana idar da asuba Mahmud bai koma ba. parking din dakinsa yayi ya adana duka muhimman abubuwan adanawa ya hada jakar tafiyarsa guda daya sannan ya shiga wanka. cikin minti arba’in ya kammala shiri cikin bakin jeans da farar shirt. Da wuya kiga turawan London da kalar kayan da ya wuce black and white. zama cikinsu ya sabar masa da hakan shima. jibgegiyar jacket ya dora akan kayan nasa ruwan toka yayi amfani da scarve din Lv kalar rigar sanyin ya nade wuyansa. Idan da akwai wani abu da yake sa ka gane mutum kana ganinsa ba tare da saninshi ba shine kwatance. to idan kanaso ka kwatantawa wani mutum Mahmud zaka ce masa a kullum wuyansa na rataye da mayafi ne designer. idan yaga dama ya rataya idan yaga dama ya nade wuyan idan kuma yaso nishadi sai ya daura shi sosai akansa kamar rawani. wannan shine irin nashi style din da anan gaba zamuji yanda ya samo shi.
A gaggauce sukai breakfast din da Safna ta tashi tun bayan assalatu ta girka shi da hannunta. wannan ke sake shigar da ita zuciyar Mahmud cikin sauki. dubanta yayi a tsanake yace “ki hada jakarki zan mayar da ke gida nayi wa Eng godiyar barinki da yayi kizo jinyata” wani murmushi taji ya kubuce mata na jindadin kalaman Mahmud ba tare da la’akari da in tayi tunanin mai zurfi fa magana ya caba mata! rashin gane hakan ya sanya shi me maganar murmusawa.
Jirgin kasa suka bi zuwa garin London daga nan suka dau taxi. amma a maimakon taji ya fadi sunan unguwarsu sai taji yana cewa Driver ya kaisu SELFRIDGES. take kuwa annurin fuskarta ya karu.
Yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin katon shopping department stores din. kana ganinshi kasan yayi sabo ainun da zuwa wajen domin babu waige waige ko jeka ka dawo ya nutsa ciki har ya iso wajen brand din “Louis Vuitton” wata baturiya ta taso tana mishi gaisuwar sani da kuma sabo! sannan ta basu wajen zama. jakunkunan mata take dauko mishi yana dubawa a take ya siya guda uku. sannan ya dubi Safna yace “ki dauki duk abinda kike so”.
daga nan wajen Chanel ya nufa ya kwashi kayan kwalliya na mata masu yawa. ita dai Safna tana kallon ikon Allah! hakana ya matsa kantin “Dior” ya kwashi turaruka. Ita dai Safna banda lissafin abinda yake kashewa babu abinda takeyi. ta gagara daukan komai ta zama kamar wata yar kauye!
tunaninta menene mutumin nan ya taka? ta tabbatar ba da likitanci ya ta’allaka ba! to wanene shi?
shikuwa ya lura da yanayinta tsab wani zubin yayi murmushi wani lokacin ya share ta kamar bai gane komai ba.
sai da ya kusa kammalawa yace “Safna kinsan bazan jiraki ba idan nagama? baki dauki komai ba time yana tafiya kuma ni sauri nake” kawai tsyawa tayi gabanshi tana blushing! kasa daure dariyanshi yayi ya soma zabar mata da kansa. cikin lokaci kalilan suka kammala suka futo.
kanta yayi masifar nauyi domin idan lissafinta yayi daidai to abinda Mahmud ya kashe ya kai 12.5M lokaci daya siyayya daya a rana daya! Dankari. daya tunanin kuwa ya tafi ne akan me zaiyi da kayan matan da yake ta jibga kamar baisan darajar kudin ba? gashi ta gagara yi masa ko da tambaya daya domin harshenta a sarke yake da mamaki!
Mahmud kam rabuwa yayi da wata Safna ya shiga turawa Maminsa sako ta email akan tahowarsa da lokacin saukarsa!
lokacin da suka iso unguwarsu la’asar ce ga kuma himilin kaya don haka a gidansu Mahmud suka sauka ta tayashi shiga da kayan. Anan ma wani shock din ta samu ganin yanayin gidan da yaci uban nasu a tsaruwa da shiryuwa. sallah kadai sukayi ya rakata gidansu inda sukai sabani da Eng sai waya Mahmud yayi masa ya mishi godiya. Mamansu Safna kuwa bakinta har kunne kamar zata zube a wajen saboda dadin ganin alakar Mahmud da diyarsu ta soma karfi.
shidai ya lallaba ya baro gidan cikinsa kulle da dariya. Yana ganin ko dan maganin ciwonsa ya kamata ya karbi Safna don bata gajiya amusing dinshi.
wajejen Assalatu tayoyin Jirgin British Airways suka dira a Nnamdi Azikiwe Airport na garin Abuja. Mahmud na daya daga cikin fasinjojin da jirgin ya kwaso daga garin london a kujera mai daraja ta farko wato first class!cikin wannan lokaci babu abinda zuciyar Mahmud take sai dokawa. yayinda jikinsa yayi sanyi kalau kamar mara laka. hankalinsa yayi mugun tashi tunaninsa ya birkice. cikin azama ya soma kiran suna Allah da ya kawo mishi dauki da nutsuwa da ingantaccen Confidence din da zai fuskanci kasarshi ta gado bayan gudunta da yayi bai sake waiwayowa ba tsayin shekaru goma da watanni uku cif.
lokacin da aka baiwa fasinjojin damar futa dakyar yake daga kafafunshi don tsananin sanyin jiki. yana tafiya yana rangaji ya futo terminal din inda Ya hango kyakykyawar uwar da bata tsufa saidai karin kamala da haiba da nutsuwa cikin fara kal din laffaya tana ta murmushin da kana ganinta zaka tabbatar yana tahowa ne tun daga karkashin zuciyarta.
Yaron nata is not a kid anymore. don ya wuce mukamin da zata kirashi Hausa Arab, dan saurayin da ta rako airport tana kuka yana kuka mai shekaru ashirin da bakwai. wannan yafi dacewa ta kirashi Dr.Mahmud Ahmad Lamido kwararren gyanecology consultant din da ake alfahari da Shi a kasar turai. har yanzu kyawunsa da farinsa da gayunsa na nan tare da shi sai dai wata suma da ta lullube fuskarsa a yanzu wadda ta karo masa haiba da kamala da kwarjini da kuma nutsuwa ta musamman. shekaru goma cif da suka wuce wannan sauyin ya tabbata!
duk iya girman nashi da kamalar tashi da jinkai da takama bai hana shi yar da jakar hannunsa ya runtumo a guje ba lokacin da ya hango Uwar tashi abar alfaharinshi!
cikin hawaye ta rungume Mahmud da wata irin murna mara misaltuwa dukansu suka rushe da kuka mai tsanani kai bakace a tsakiyar jama’a scene din yake faruwa ba.Safiyar Asabar ta kasance mai tsanani sosai gareni a sakamakon tunanin da sukai wa kwakwalwata rubdugun da yake shirin fasata. duk yanda nayi tunanin na kare Aisha ko Imamu daga mugun zargin da nakeyi na gaza domin manyan dalilan da ya kewaye kowanne hasashe nawa a garesu.
jiya akai dinner gidansu Ihsan amma sam Imam baizo ba. na fahimci kwana biyu ko son haduwa dani bayayi idan kuma har mun hadu waje daya bashi da aiki illa ya tsura mun idanu yana kallona yana faman tunani. idan na tambayeshi dalili yace babu komai. ita kanta Aisha na rasa gane kanta domin rabin walwalar da nishadin dana santa dashi sun tafi. kawai yake takeyi amma sanin da nayi mata na tabbatar akwai dankareriyar damuwa a kwance acikin zuciyarta. Da ada ne bazan samu nutsuwa ba idan ba zaunar da ita nayi ba naji matsalarta. ko yanzun ma ina tunanin nasan mecece matsalar ne shiyasa na kyaleta amma duk da haka ba karamun rashin jindadin ganinta a haka nake ba. wannan wacce irin kaddara ce haka take shirin fado mana? nida Aisha muna neman komawa juna complete strangers!! duk sanda muke tare kowa kokarin aro expression din kan fuskarshi yake duk da dukanmu munsan kanmu ba sanin shanu ba kuma kowa yasan akwai abinda yake kokarin boyewa dan’uwansa sai dai tsoron sanin hakan ya hana dukanmu tuhumar junanmu! This is fucking painfull wallah!! i hate this situation! idan akwai wanda nake enjoying bankadawa asirin zuciyata bai wuce Aisha ba domin duk duniya babu wanda yake fahimta ta kamarta! kafin nayi magana take karanta abinda yake kan fuskata harda na cikin zuciyata ta kuma bani shawarar yanda zan warware koma wacce matsala ce take damuna! Aisha bata taba bari na zauna da damuwa ba. sau da yawa takan salwantar da nata farincikin domin nawa. ita kadai nake zama nayi kuka a gabanta banji awkwardness ba kasancewata mutum wadda bata kaunar aga lagonta. Idan akwai abinda na tsana a duniya bai wuce a ganni ina kuka ba. don haka kafin wani yaga kukana ana daukar lokaci sai dai nayi shi a daki ko toilet na wanke fuskata nasa kwalli na futo kamar banyi ba. babu wanda yasan weakness dina irin Aisha babu wanda yasan iya level din patience dina irinta! ku gayamun tayaya zan iya jure rashin wannan mutum mai matukar muhimmanci a rayuwata? tayaya zanyi manejin raba hanya da Aisha? wannan shine abu mafi tada hankali a gareni. na yarda na rasa Imamu duk da son da nake masa duk da halin da nake tunanin zan fada idan babu shi saboda nasan akwai Aisha a gefena wadda zata tsayamun tsayin daka wajen korar bakinciki da sabon da nayi da Imamu daga raina! bana ko tantama babu wani abu da zai shigomun Aisha bata tayani tsayuwa na kare kaina ba. How on earth am i going to manage living this life without my other half?? it’s soo difficult accepting this change!! wallahil azeem am not enjoying what i’m going through with my best friend!! hakan ya kara mun babbar damuwa daga cikin damuwoyin dake damuna har yayi affecting dabi’una da aka sanni dasu! na manta rabon da nayi nishadi da walwala kamar sauran mutane! na manta rabon da na kwanta a gadona nayi bacci peacefully na manta rabon da na tashi daga bacci da karfina da kwazo da kwanciyar hankali. zuwa yanzu wallahi na fara regretting sanin Imamu a rayuwata domin sanin nashi bai amfaneni da komai ba sai tarin matsaloli da ya sakani ciki! ga buki da ya shigo ya takurawa kadaicina. dole na daure na boye abinda yake damuna na mayar komai ba komai ba na shiga cikin jama’a ayi budiri da shagulguna dani. idan akwai abinda yafi cinye damuwar dake ranka cikin duniya toh basu dayawa! it is one of the most difficult situation wallah!
Tun safe naje Office din Mami na karbi kayana da aka rage mun a dalilin ramar da nayi bayan dinka kayan aka sake gogewa sannan na taho gidansu Ihsan! zuwa karfe shida tuni an soma haramar kimtsawa da yin kwalliya domin karfe 8 suka saka a jikin katin bukin kuma ba’a bukatar African time a dalilin manya manyan mutanen da aka gayyata.
zaku so ganina cikin kwalliyata ta yau domin tafi ta kowacce rana a bukin kyau da kuma tsada. wani rantsatstsen luxury lace ne mai nauyi. kalarshi jajawur yayinda roses din da aka shirya pattern din jikinsa da shi suka zama zallar gold! ba’a baiwa leshin wuya wurin dinki ba domin buba and iro ne sai gaban rigar da aka kawata da pattern din lace din aka dora embroidery akai. cif kayan sukai fitting figure dina kamar a jikina aka zana. Mamza ta kawata kwalliyar tawa da make up na ban sha’awa musamman da ya kasance ban cika sa kaya mai kala mai nauyi ba (I am afraid of colours) nafi ganewa brown, peach da kaloli marasa hayaniya! hakana lipstcik kullum nude nafi amfani dashi sabanin yau da ta sakamun Red mai sheki kamar a ciro lips dina don kyau.
ashoke na gold colour ne. zanso ku kalli tafkekiyar sarkar wuyana samfurin Bahrain. hannuna na dama cika nayi da wara warai sirara guda goma yan Dubai. na hagu kuma agogon Rolex da sarkarsa! takalmin kafata ma chanel ja ne mai igiyoyi da tsinin dunduniya.
banajin na taba kyau irin wanda nayi yau cikin traditional attire!
Amarya kuwa tun daga sama har kasa daga kan rigar ta zuwa accessories duka gold ne wanda ya hadu da farar fatarta ya fiddo da wata Arabian queen da ba zaka kaso ka cire idonka akanta ba! Duka bridemaids ashobin red organza lace sukai da gold head.
A bluevelvetmarque. lokacin da muka isa karfe takwas da minti uku tuni marque din ya cika da jama’ar da aka gayyato sai tashin sautin kida mai sanyi daga bakin zabiya Celine Dion ne ke amo a hankali da tausasa zuciya.
abokan ango duka farar shedda suka saka da gold din hula. tare mukayi layi mikakke muka shiga hall din cikin class muna dan takawa a hankali. daga nan couple din suka iso suna haska wajen kamar taurari don kyau da dacewa da juna. Mc na da kwarzanta kyawu da tsarin halittarsu da kwalliyarsu har suka isa wajen da aka tanada domin su suka zauna.
BigH yace dawa aka hadashi ba da mu ba? kewaye su mukai akai ta daukar hotuna kafin kowa ya sauka mu koma barin da aka ware mana a matsayin manyan abokan ango da kwayen amarya!
sannan aka ci gaba da gabatar da taro inda aka bukaci limamin masallacin juma’a da yazo ya bude taro da addu’a. bayanshi Uncle din ango Hashim Dala ya futo yayi jawabin lale maraba daga nan akaci gaba da gabatar da taro yanda ya kamata.
Gefe guda masu rabon abinci na aikin su.
Na kai semosa bakina zan gutsira naji muryar MC ta karade wajen yana neman babbar aminiyar amarya tazo ta bada tarihin amarya cikin mintina biyar.+
Cousin din Ihsan ce Amna ta futa tayi bayani akan rayuwar Ihsan cikin harshen nasara me cike da iyayi da lankwasa kamar wata yartsana. ta kammala aka bita da tafi Mc ma shakiyanci yana sa mutane dariya. Sannan aka bukaci babban abokin ango. ya maimaita hakan yakai sau hudu kafin wanda ake nema ya mike.
Mutumin da ya taso don amsa wannan kira wani dogon matashi ne mai wata irin structure ta mazan da suka amsa sunansu. Fari zaka kirashi amma ba sol ba. Hancinsa ne zai matukar baka mamaki yanda ya taho ya dire kaman an dora saboda tsini. Hakana idanunsa farare sol an diga wasu ilhamomi aciki na kwarjini da kamala .wani irin gashi mai kauri gazar gazar baqi qirin yayi musu Rumfa hakanan idanun suke lumshewa su bude da kansu kamar masu jin bacci. “Ive never seen a beautiful creature like this man”
Sanye yake cikin wani irin yadin da nidai mutane kalilan na taba gani da shi domin tsadarsa da kyawunsa. Kalarsa purple me duhu sosai an cika gabar babbar rigar da wani irin aikin zare mai tsari da kayatarwa. Kai kana ganinsa dole ka bashi hanya domin ya daku ya sake dakuwa a kamala da kyau da tsari.
A lokacin da yake matsowa kusa ne gabana ya soma bada wani sauti dam! Dam! Me idona yake shirin gani ne? Ya ilahil arshi!! Ya rabbis samawati! Wannan ai arrogant jikan Dadan nan ne da suke kira Mahmud. A daidai lokacin kuwa naji MC din ya soma mishi kirari da “likita bokan turai likitan duniya likitan gayu likitan kwalisa wanda samarin zamani ke wa lakabi da Designer guy” gabadaya sai lokacin na tuno komai. To ai Faisal na daya daga cikin samarin da suka zo hotel dinmu a saudi ranar sallah. What a foolishness?? Meyasa bangane shi ba sai yau??tabdi.
Nidai ina can duniyar tunani naji an tabo ni…na juyo ina duban Aisha a kunnena ta radamun “Zara jiyemun wani accent don girman Allah” a lokacin ne na maida hankalina ga abinda yake gudana na kasa kunnena ina sauraren wannan murya da ta dasa mun tsanar mamallakinta da tsoro da fargabar jinta a kowanne lokaci. Murya mai sanyin amo da wani irin tone mai mintsinin zuciya da karkato da hankalin mai sauraro. Accent dinshi kadai zai iya ribatar zuciyar ka ka tsunduma kaunar bawan Allahn kafin ka gano mugunta da zalincinsa. No matter how much i hate him and the pain he has caused me i cant deny the fact that ban taba ganin mutum me kyawu da baiwa irin tashi ba. Allah ya yi masa baiwa saidai ya butulcewa baiwar yana amfani da ita wajen zalinci da kaskantar da dan’adam yana mantawa cewa wannan kyakykywar sura da ya mallaka wataran a rami za’a haka a rufeta ta rube tsutsoci su cinye. Halin shi nagari da kyakykywar mu’amalar shi da mutane ita zata ceceshi a wannan lokaci. A jinsin mutane kakaf ni ban taba ganin mutum mai kasaita da jin kansa irin wannan gayen ba. Tantirin dan wulakancin karshe ne.
Nidai bansan lokacin da ya qari ragargazar hardadden turancin na shi ya koma ya zauna ba. Illa tafin da wurin ya dauka raf! Raf!! Raf!!! Ya dawo dani hayyacina. Na tabe baki ina cewa “rashin sanin waye wannan mutumin yasa yake birgeku”.
Bayan an kammala wannan amarya da ango suka sauko stage domin taka rawa. nan da nan hankalin masu hoto da vedio da wayoyin al’ummar da ke wajen ya koma kansu. daganan mu ma muka shiga filin aka soma cashewa damu musamman da aka bayyana isowar shahararren Artist Davido sai filin ya rude da rawa da liki.
Nikuwa sulalewa nayi bayan na gama nawa likin na nemi hanyar futa ina amsa wayar Imamu. ina futowa na hango shi a parking space cikin kawatacciyar kwalliyarsa ta bakar sheddar da ta haska farar fatarshi. saidai ya dan rame sannan ya rage wannan murmushin da baka rabashi dashi mai futo da asalin kyawunsa.
“ya baka shigo ba? shine sai yanzu kazo ko?” abinda na soma gaya mishi kenan shikuma yana yunkurin daukana hoto da wayarshi!
Nasa hannu na kare fuskata ina cewa
“babu hoton da zakaimun sai mun shiga ciki” sai ya mayar da watar aljihu yana murmushi “toh muje your highness” ban tanka mishi ba na wuce gaba yana biye dani har can cikin wajen bukin gaban su Ihsan suka gaisa mukayi hoto sannan ya shiga yi mana liki harda Aisha. na fahimci duka mu ukun mun daure yau munyi abinda ya dace. sai wajen karfe daya saura kwata taro ya tashi. nida Imamu muka futo ina masa rakiya na hango Mami tsaye ita da Mahmud suna magana. Imamu ne yace “muje nayiwa Mami sallama sai na wuce” ba’a raina don banason haduwa da Ya Mahmud ko kadan! amma ba yanda zanyi nace masa “toh” muka tafi.
sai da muka karasa duka suka juyo suna dubanmu. har kasa Imam ya rissina ya rissina yana yiwa Mami sai da safe kafin ya dago su hada idanu da Ya Mahmud. dukansu wani shock ne ya ziyarcesu na wasu dakiku kafin Imamu yai maza ya kawar da abinda yake ka fuskarshi ya mika masa hannu! amma saboda rashin M na Mahmud sai ya makale nashi hannun ya zura su a aljihu suka gaisa a haka. da sauri Imamu ya wuce nabi bayanshi cikin jin haushin abinda Ya Mahmud yayi masa. amma ga mamakina bai bari maganar ta hadamu ba sai ma wani murmushin yake da ya dinga yi har ya shiga motarsa ya bar wajen.
hello my people! how far?? me kuka gano game da Imamu? meyasa yake da matsala da kowa ne? meye hadinsa da Mahmud? shin kuna tunanin hasashen da Zara take akan Imamu da Aisha gaskiyane? meyasa zasu ci amanarta haka?Da hannu Mami ta kirani na dawo gabansu. cikin daure fuska tace “Zara bakiga Yayanki bane baki gaida shi ba? darajar Mami ba don halinsa ba na dube shi nace “ina wuni?” wani shegen kallo Mami ta jefe ni da shi cikin takaici tace “Zara?haka ake gaisuwa? a tsaye kike gaida shi?” mamaki ne ya lullube ni ganin yanda Mami ta fututtuke ta daure fuska kamar wanda na aikata sabo! raina yai bala’in baci amma sanin wacece takemun magana ya sanya na hadiye bakin cikina na risina sosai na gaishe shi! da murmushi ya amsa wanda na tabbatar na mugunta ne! raina ya sake baci. wayarshi ce ta soma ringing ya ciro ta daga aljihu yana cewa “excuse me Mami” nikam mamakin alakarsu nakeyi mai karfi haka!
bangama tunanina ba Mami ta sake jefomun wani hot glance sannan tace “Zahra kin bata mun rai! ashe haka kika koma baki iya girmama babba ba? Mahmud of all people na duniyar nan? kinsan matsayinsa kuwa a wajena? toh in baki sani ba wallahi ke da shi baku da bambamci a zuciyata. kin taba ji ance yazo garin nan tunda kikai wayo? kin taba ganinsa a Abuja? amma Zara kiyi masa wannan gaisuwar? babu ladabi babu sannu da zuwa babu ya hanya? haka aka koyar da ke? ba laifi!
Gabadaya hawaye ne cikamun idanuna nayi sauri na mayar dasu domin ganin yanda Ran Mami yayi tsananin baci a kaina musamman da yake bata cika mun fada ba balle ta kai ga fadamun wannan deep maganganun! don haka hankalina ya tashi sosai don idan akwai abinda nafi tsoro a duniya bai wuce bacin ran ta ko fushinta a kaina ba! don haka yana dawowa daga wayar da yayi na durkusa har kasa raina na zafin aikata hakan da zanyi ga wanda baisan darajar dan adam ba. cikin muryar kusa da fashewa da kuka nace “I’m sorry Ya Mahmud! kayi hakuri bazan sake ba” hannu ya saka ya dagoni cikin murmushi gabana ga soma faduwa! cewa yayi “Zara you are my sister! my blood darling sister!…so stop making me feel like i’m a stranger to you ok? feel free with me!”
Duk da dinbin mamakin da kalamansa na karya da yaudara suka bani ban kasa girgiza kaina ba kafin ya sake mun hannu! yace “good!
Mami na duba a sanyaye nace “I’m sorry Mami! I’m very sorry bazan sake ba! murmushi tayi sannan tayi hugging dina tana patting bayana! “it’s okay my girl! ya wuce! yanzun kizo mu tafi nayi dropping ki” nace “Mami da Aisha zamu tafi” cewa tayi “Aishan guda nawa ce banda wadda ta yi mun sallama ta tafi?” cikin mamaki na kalli Mami nace “ita da wa Mami?” cewa tayi “bansani ba amma dai ta tafi”.
Jikina a sanyaye na shiga motar su Mami ita ke driving Mahmud na gefenta nikuma ina gidan baya. Gidanta kawai ta wuce damu bance komai ba domin ina tsoron na sake wata magana Mami tayi fushi.
Muna isa na balle murfin motar na futa domin a bala’in gajiye nake! ga raina da ke a bace! dakin Mami na nufa amma ina murdawa naji a kulle sai da na jira tazo ta budemun! ina shiga na soma zage kayan jikina na shige toilet! Ruwan micella na Gievinne na dauka da cotton na goge make up din fuskata tass sannan na samarwa kaina ruwan wanka mai zafi sosai na shige cikin farin jacuzzin ina maida numfashi. saida Mami ta kwankwasa mun kofar na tuna cewa a toilet nake domin duniyar tunanin da na shiga. cikin sauri nayi wanka da alwala na futo. Mami na bakin gado cikin kayan baccinta da alama a daya dakin tayi nata wankan. “bacci kikayi ne a toilet din?” ta tambayeni cikin tsarewa da ido! murmushi nayi nace “I’m so tired ne wallahi ina zaune ina jin dumin ruwa!” cewa tayi “gobe dai za’a gama sai ku huta!” nace “wallahi kam! nagaji da wannan buki” mikewa tayi tana cewa “bari na hado tea ban wani ci abinci a wajen bukin nan ba zakisha?” girgiza kaina nayi ina shafa lotion. ta juya ta futa! ina gamawa na zura lallausan kayan baccin Panda bakake da na gani akan gadon ta futo mun dasu na kwanta! tsananin gajiya da bashin baccin da na ci na kwanaki suka hadu suka saukar mun. ko second goma banyi ba nannauyan bacci ya tafi dani.
bani na farka ba sai asuba. rabonda nayi baccin 4hrs ban farka ba tun kafin matsalar da nake ciki ta shigo rayuwata. Bayan munyi sallah da Mami na koma baccin mai nauyi kamar wanda na kwana a zaune.
cikin baccin naji tana tashina! dakyar na bude idanuna ina karanto addu’ar bacci! Mami ce tsaye a kaina har tayi wanka ta shirya! “zara 11 fa kike wannan baccin kamar wanda kika fara yanzu! tashi muyi breakfast” cikin sauri na mike ina mamakin yanda akai lokaci ya tafi haka. toilet na fada nayo brush da alwala na futo cikin sauri nayi sallar walha!sannan na futo parlour! dif! na tsaya cak sakamakon ganin Ya Mahmud kan dinning din cikin jallabiya baka wul! saida Mami ta dago ta dubeni nayi maza na taho kafata tana Sarkewa! i dont know why nakejin wannan awkwardness din duk lokacin da yake waje! saida na isa gefen kujerarshi na risina na gayar dashi! da murmushi ya amsa kamar jiya harda cemun how was my night! nace lallai wannan mutum ya iya duniyanci wato don a gaban Mami ne yake mun haka! zama nayi muka soma karyawa shi da Mami suna ta hirarsu yawanci ta family ce da abubuwan da suka faru wanda bata samu damar sanar dashi a kafar da take sanar dashi din ba wadda ban sani ba. why on earth bansan yanda akai akwai irin wannan shakuwar tsakanin Ya Mahmud da Mami ba? idan akwai abinda zan iya tunawa game da shi basu dayawa kasancewar bani da wayo lokacin da yake zaman gida. yana kammala secondary school kuma ya wuce Oxford zamanin banfi shekaru tara ba sannan daga lokacin ban sake jin duriyarshi ko ganinshi ba. sai dai labarinshi a bakin manya. labaran kuwa ba masu dadi bane a game dashi don haka babu amfani na mayar da hankalina ga sanin wasu abubuwa a tare dashi.
a hankali sautin wayana yake futowa daga daki wanda ya dawo dani daga hayyacina. aje cup din hannuna nayi na mike na shiga dakin na dau wayar!
number Ummansu Aisha nagani na daga da sauri. “Hello Umma ina kwana?” cikin sarkakkiyar murya ta amsa sannan take cewa “Zara daman jiya Aisha kun kwana bata da lafiya ne?” mamaki ya kamani! ina zanga Aisha har mu kwana tare bayan gida ta tafi???
kafin na gama tunanin ta katseni da cewa “Zara kina jina?! dazu ta shigo gidan tace kanta na ciwo nace ta shiga daki ta kwanta zuwa anjima na shiga na dubata sai zazzabi mai zafi ta dai sha paracetamol amma inaso nasan me ya faru ne tun farko kafin muje wajen likita na mishi bayani. kan nata ya hanata magana me tsawo!
Tohh fa!!! wata sabuwa inji yan caca! Ya zanyi nasan me yake faruwa bayan ba gida daya muka kwana ba? na dai san Mami tace mun Aisha ta tafi gida kila gidansu Ihsan ta koma ta kwana a tunaninta nima can zan koma daga wajen bukin tunda ni banyi magana dasu ba! sai kawai na tsinci kaina da cewa “Umma bara kawai na nazo sai muyi magana” na katse kiran da sauri na lalubi layin Ihsan da tunanin ita tasan abinda yake faruwa! sai da na kira sau uku ta dauka! ita ta soma cewa “nagode da kikai tafiyarki gida Zahra ko sallama bakimun ba kika tafi daga ke har Aisha daga kwanan jiya fa shikenan” wait!! kaina ne ya sara na soma ganin duhu nayi maza nayi baya na zauna bakin gado! Aisha ba’a gidansu Ihsan ta kwana ba? bata kwana a gida ba? ina taje daga wajen buki? a ina ta kwana?! ji nayi jikina yana shivering zuciyata na bugawa. Ihsan ce ta sake cewa “hey! are you there? kinsan akwai budan kai da yamma ko Zara? danAllah ki iso da wuri! ki gayawa Aisha ta manta wayarta nayi mamaki ma da bata kira tayi confirming anan ta bari ba!” sulalewa wayar tayi daga hannuna na runtse idona ina karanto Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Aisha hali ta chanja? wani abu ta taka? wata rayuwar ta sauya? wasu kawayen ta samu? wani ra’ayin ta dauka? menene yake faruwa? A ina Aisha ta kwana? abinda yake ruri a kaina kenan yana amo kamar zai fasa mun kwakwalwata!
Sanin bani da amsoshin abinda yake faruwa ya sanyani mikewa na koma falon a sanyaye! Mami ce ta lura da yanayina tace “lafiyarki?” shikenan jimami nace “Mami Aisha ce ba lafiya yanzu Umma ta kirani” da mamaki tace “Aishar? kamar ba jiya na ganta tana harkokinta ba? me ya sameta?” na amsa “wai ciwon kai da zazzabi” Mami tace “Ashsha!Allah ya sauwake! kila wannan zirga zirgar ce da gajiya!
nidai sama sama na kammala shan tea din na mike ina cewa “Mami bara na shirya naje naga jikin nata na dawo” girgiza mun kai kawai tayi na wuce da sauri na koma daki. cikin azama nayi wanka na shirya cikin bakar abaya mai purple crystals! na feshe jikina da turarukan Mami. na dau jakata da waya na futo!Har lokacin suna kan dinning hirar bata kare ba! “Mami bani aron key dinki naje na dawo!” na fada cikin muryar tausayi! sai da ta dubeni tsab sannan tace “idan Aisha ta tafi makaranta zanga yanda zakiyi Zara” murmushi nayi nace “Allah Mami kullum sai nayi wannan tunanin nasani nima ABU nayi applying ko BUK yanda nima na tafi wani wurin daban.” cewa tayi “yanzun ma zaki iya sauyawa ai” murmushi na sake yi kawai na wuce na dauko key da ke kan console din falon nace “Mami na tafi!” tace “toh ki gaishe ta kuma ki dawo da wuri”! na amsa sannan na dubi Ya Mahmud nace “Ya Mahmud sai na dawo” duk maganganun da muke kamar baya falon sai lokacin ya dago oily idanunshi yace “ok! drive carefully! na amsa ina futa daga falon!
Tunda na dau hanya kirjina yake bugawa don bansan me zancewa Umma ba kuma bansan halin da Aishan ke ciki ba! da na isa cikin gate din kuwa sai naji kamar na juya na koma! dakyar na samo dakiya da karfin zuciya na futo daga motar na zagaya na baya na dau jakata na nufi cikin gidan Ina amsa gaisuwar David mai baiwa flower ruwa!
A parlour na samu Umma tana waya na samu waje na zauna kirjina yana bugu! da hannu taimun alama na shiga dakin kafin tagama! na mike na hau yan steps din da zasu kaini dakin Aisha na murda kofar a hankali.
A can karshen gado na hangota ta cure wuri guda kamar jaririya gashinta ya bazu ya rufe fuskanta. gabadaya tausayinta da kauna irinta yar’uwa ta jini ta kamani. na karasa a sanyaye na aje jakata kan drower na hau gadon! kamshin turarena yasa ta dago fuskanta da ya kumbura yayi jajawur! yarr! tsigar jikina ya tashi! i cant remeber the last time naga Aisha cikin irin wannan yanayin! kafin wani abu ya taba zuciyarta tayi kuka ana dadewa. mace ce very with the most strongest heart. ba abinda yake bata tsoro babu abinda yake gigitata! sannan ina kallon kwayar idanunta na gano ba ciwo kadai ke damunta ba zallar damuwa ce wadda idan kowa ya kasa ganowa ni bazan gaza gano taba a dalilin yanda nayiwa Aisha sanin da ko yunwar cikina albarka!+
Cikin nutsuwa na gyara mata gashin kanta na tattara shi na daure da ribbon din da ke gefenta! sannan nasa hannayena ina goge mata hawayen da yake biyo kuncinta! cikin murmushi na riko hannayenta in kallon ta! “Aisha it’s me! your best friend! your favourite sister….! hankalina ya tashi matuka Aisha da ganin halin da kike ciki!na tabbatar ba ciwo ke damunki ba sai dai idan damuwan ce ta kawo ciwon! Aisha plaease ki gayamun meye yake damunki? mecece matsalarki mu warware ta? meye damuwarki mu magance ta? ki fadi ko menene yake cikin zuciyarki zan baki best listening ears kuma bazanyi judging dinki ba! and i promise you babu wanda zaiji halin da muke ciki kuma zamu zauna kamar yanda muka saba mu warware koma menene tare kinji besty?”
Duk maganganun da nake idonta kirr a kaina ta gaza ko kwakwkwaran motsi sai kirjinta da yake ta dagawa yana bugawa! ta kasa cewa komai!
hannunta na sake matsewa cikin nawa ina cewa “Aisha ko dai kin chanja mun matsayi ne? shin akwai ranar da zatazo wadda zaki kasa gayamun wani abu game da ke? akwai lokacin da zaki boyemun damuwar da kike ciki Aisha? karki manta fa mun saba sharing ma junanmu komai na rayuwa babu wanda yake boyewa dan’uwansa halin da yake ciki! don Allah Aisha ki taimakeni ki gayamun damuwarki!
cikin dasashshiyar murya tace “Babu komai Zahra! ba abinda yake damuna kawai bani da lafiya ne! kirjina na zafi kuma!” hannunta na saki cikin disappointment ina mata wani kallo sannan na mike daga gadon na nufi jakata na rataya! “fine then! nagode da sabon matsayin da kika bani Aisha! zan tafi Allah ya baki lafiya” na wuce da sauri zan futa! na kama handle din kofa naji an riko bayana! na juya ina kallonta! wani matsanancin kuka ta saki me ban tausayi wanda yai masifar sanyayamun jikina gabadaya! dakyar na mikar da ita muka koma bakin gado! a kafadata ta sake kifa kanta tana kukan kamar ranta zai futa nikuma nayi shiru kawai ina saurarenta domin na fahimci kila idan tayi kukan zata samu sassauci!
Helo dearis! people are complaining that i always post late! i am sorry, but i have alot of things i am taking care of! i can’t post a new chapter everyday, nor every two days! but i promise you i will try my best and update as soon as i can!
so back to our Story, meye kuke tunanin ainihin abinda yake faruwa? Ai ina Aisha taje ta kwana? meye ya faru da ita? meye cikin zuciyar Zara? me yake shirin faruwa? shin me ya kawo Mahmud Nigeria? meye makasudin zuwansa gidan bayan bikin Faisal??
kuci gaba da bina cikin labarin!
Thank you all for your love and prayers!Bayan futar Zahra Mami ta juyo da ga Mahmud! sannan tace “ya kamata ka shirya mu tafi gidan Dada kar rana tayi kaga 12 yanzu! gabadaya mood dinshi ne ya sauya annurin fuskarsa ya dauke lokaci daya! a hankali Mami ta mike ta zagayo gefen da yake ta dafashi! “haba my son! be a Man please!! bansan ka da ragwanta ba! ka daure zuciyarka ka karfafa ranka kayi shirin tunkarar koma wanne irin kalubale ne yake fuskantarka! Allah yana tare da kai and your Mami is by your side bazan taba bari naga an kware ka ba! sannan na tabbatar ma tunda kazo da maganar aure to kayi maganin fushin Dada gabadaya! trust me she will be happy with you!”
murmushi yayi har kamutunshi ya lotsa don jin dadin kalaman Mamin tashi kafin ya mike a hankali ya shige dakin da tayi masa masauki a gidan! ita kuma ta Kira masu aiki su gyara wajen ta shiga daki!
mintina talatin ta futo parlour cikin shigar super shudiya wadda ta amshi farar fatarta! hannunta jakar Gucci ce babba da kuma key din mota! waya ta ciro tana shirin kiran Mahmud ya bude kofa ya futo! shigar da yayi ta burge babar tashi domin ya futo a babban mutum sosai! itace tayiwa Faisal transfer din kudi tace ya siyawa Mahmud kaya ya kai a dinka mishi a wurin dinkinshi!
Coffee shedda yar hilton yayi amfani da ita dinkin babbar riga ya aje hular kayan kan kanannadaddiyar sumar kansa da yau bai samu sukunin bata extra care din da ya saba ba! damtsen hannunsa daure da brown din agogon Luis Vuittun na fata da rufaffen talkami mahadin agogon! duka falon ya kacame da kamshin turaren LA NUIT na LV. saidai fuskarsa babu walwala ko kadan amma hakan bai hana kyawunsa yin tasiri ba. Mami ta tsaya tana gayawa Aya tayi wa Zahra lunch ita kadai su zasu dade basu dawo ba. sannan ta fada mata me zasuyi na dinner ta amsa cikin girmamawa Mami ta wuce gaba yana biye da ita.
Ita ke driving domin shi har yau ya kasa ko taba steering din mota tsoron ma driving din yake a garin da ya koma masa kamar bako! don haka yana daga gefen Mami tana sarrafa motar cikin kwarewa yayinda zuciyar Mahmud take faman luguden bugu musamman da suka shigo Garki! ya kalli gidan cikin tunanin wasu abubuwa da suka shude shekaru goma da doriya sai yaji hawaye na son kwace masa.
———————————————————–
Sai da na kyaleta tayi kukanta ta gaji sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta ta dawo ta zauna! cikin tausayawa nace “Aisha are you ready to explain things to me?” kallona tayi sannan tayi murmushi kafin ta soma magana ciki karyayyar zuciya! “Zara kafin nace komai i want to you to know that babu wani mahaluki a duniya bayan iyayena da ya kaiki muhimmanci a gareni kuma har abada bazan sauya matsayin da kike dashi cikin raina ba! but then i also want you to do me a favour, ki hakura da jin damuwata a wannan lokacin nikuma nayi miki alkawari nan gaba kadan zan warware miki komai Zara! ba don baki cancanta na gaya miki ba! sai don kawai inaso na warware miki komai cikin sauki! ina fatan zaki fahimceni ki yarda dani Zahra! trust me, i will never disappoint you!” duk da ba haka naso ba amma jawabin da tayimun ya sanyani hakuri da gamsuwa da ita sannan na yarda da ita har cikin zuciya domin yanda take magana tana kallon kwayar idona na gane duk abinda take fada daga karkashin zuciyarta yake tahowa! nasan wacece Aisha kuma na yarda da ita!
murmushi nayi nace “well, tunda haka kika ce babu komai zan jira zuwa lokacin da zaki warwaremun komai, but you have to promise me something?” tashi tayi ta koma kan drower ta zuba mun ido tana saurarena! naci gaba “promise me zaki daina damuwa da matsanancin tunani kuma zaki daina mayar dani stranger Aisha, i hate the person you are becoming i dont like how you treat me these days” hawaye suka soma saukowa daga idanuna domin kwarai abun yana damuna sosai! rungumeni tayi ta sake sakin wani kukan! daurewa nayi na tsayar da nawa hawayen na shanyesu don banason nayi kuka a gabanta na sanyaya mata guiwa nida nazo rarrasshi! tana kuka take cewa “i promise you Zahra! i promise zanci gaba da kasancewa Aishan da kika sani kuma bazan taba juya miki baya ba! komai tsanani Zahra!” murmushi nayi na dagota daga jikina ina cewa “is okay tohm! ya isa mana kukan kar ki koma raguwa mana Aisha! bansanki da saurin kuka haka ba kuma banso ki koya! kici gaba da zama mai karfin zuciya da jarumtar da kike da!” hawayenta ta shiga gogewa tana kada kai! na sake cewa “oya i want my best friend back! smile!” sai kuwa ta kyalkyale da dariya! nima na tayata kamar wasu mahaukata! nayi iyaka kokarina na jata da hira har ta soma warwarewa muna dariya!
daidai lokacin Umma ta murda kofar ta shigo! da mamaki ta kallemu tana salati! “ba dai ku Kuke wannan dariyar ba Zara? itace ta ware haka har ta samu bakin dariya? yarinyar da take shirin futa daga hayyacinta yanzun ma fa da Abba muke waya yace mu jirashi ya dawo yana meeting ne sai mu tafi asibitin” murmushi nayi nace “Umma ta samu sauki ne” itama murmushi tayi mai sauti tana girgiza kai da alama shakuwarmu ce take bata sha’awa! karasowa tayi ta kara hannunta a goshin Aisha taji temperature din jikinta tace “kan naki yayi sauki?” Aisha ta girgiza kai tana murmushi! sannan ta juya ta futa! Aisha ta dubeni tace “besty saura 5weeks fa tafiyana school kina lissafi kuwa?” bata fuska nayi nace “hey! banson wannan zancen yanzu kar mu sake wani kukan please wani lokacin zamuyi maganan! i got to leave yanzu Mami tace kar na dade kuma kinga anjima budan kan Ihsan!” a sanyaye tace “eh hakane! ki gaida Mamin kicewa Ihsan ina mata Allah sanya alkhairi! sai munzo ganin gida!” na mike ina girgiza kai! “af na manta tace mun jiya kin bar wayarki a gidansu ko?” lokaci daya ta rikice tana duru duru “wlh muna shirin tafiya dinner din nan ne na nemeta na rasa na zata ma a hanya ta fadi” nace “bata fadi a hanya ba tana wajenta zan karba sai na kawo miki” cikin sauri har tana hardewa tace “please kice ta kashemun ita kar ta kunna don Allah zan tura Malam lawwali ya karbo yanzu” murmushi nayi nace “tohm zan gaya mata” sannan mukai sallama zata rakoni nace ta barshi jikinta baiyi kwari ba. na futo nayiwa Umma sallama na taho gida!
Tunda na shigo mota tunani yake dagargazar kwakwalwata saura kadan na wuce gida! gabadaya hankalina ya tashi kuma damuwata ta ninku! bansan meyasa nakejin wani irin tsoro da fargaba ba! saidai maganar da mukai da Aisha da fahimtar juna ya sanyaya mun rai. atleast mun daina fargabar ganin junanmu!
Bansamu Mami ba nayi kiran ta wayarta bata dauka! don haka na koma daki nayi sallah sannan nayi kwanciyata ina abun da ya zamar mun jiki a wannan kwanakin wato tunani! wayar Ihsan ce ta isheni da na taho na taho dole na tashi na futa na dan tsakuri abincin da Aya tayi na dawo na sake wani wankan na shirya cikin bou bou ta leshi yellow! komai nayi keeping shi simple don nagaji da caba kwalliyar plus raina ba dadi yakemun ba! tuni nasan an fara taron don karfe biyu ne na rana! saboda haka kai tsaye na wuce international conference center inda venue din yake!
sosai event din yayi dadi kuma ya qayatar an kuma zuba kudi kamar ba’asan darajarsu ba! abokan ango kakaf na duba banga Ya Mahmud ba! nace ya akai yau baizo ba! oho masa! naci gaba da harkata! sai wajen 6 muka dawo gidansu Ihsan inda aka shiga shirin kai amarya dake Mississippi street! sai wajen karfe goma aka tafi! Amarya sai kuka dakyar aka bambareta daga jikin Mummynta scene din sooo emotional!
Daga nan aka wuce da ita wani American Villa me kayatarwa! komai na gidan me kyau ne kuma classy hakana jeren da akayi mata babu hayaniya ko kauyanci komai english ne! gargadin Mami na tuna na sulale na dauki hanyar gida ba tare da na sanarwa kowa ba don kar ace lallai sai na tsaya Angwaye sunzo! gashi Mamin nayi ta kiranta tun wayar tana ringing har ta daina daga baya a kashe ma take bayan munyi da ita zatazo kai amarya!
cikin nutsuwa nake driving har na iso gida! na dade ina danna kararrawa kafin Aya tazo ta bude! cewa nayi “Is Mami home?” tace “yes Ma. they are inside” na wuce cikin corridor din ina9 cewa “kome yasa bata neme ni ba har yanzu?” zuciyata ta amsa “tunda wannan dan London din yazo ta mayar da duk hankalinta da kulawarta kansa bata ta Zahra! in banda haka ya za’ai na kai shadaya na dare a waje Mummy bata nemeni a waya taji inda nake ba” haushi ya turnikeni naci gaba da tafiya ina kunkuni! A hankali na tura kofar falon na shiga! cak! na tsaya cikin zaro idanu! ganin abinda yake faruwa! Mami zaune kan kujera ta kifa kanta hannun kujerar tana rera kuka a hankali yayinda Ya Mahmud ke tsaye rataye da jakar laptop dinshi da akwatin Versace a jingine gefe shima idanunsa kamar an kada jini aciki! tsayawa nayi still kirjina na mugun bugawa! a slow motion na isa gaban Mami na durkusa “Mami meya faru? wanene ya mutu?” gabadaya bata ce komai ba kuma bata dena kukan ba! mikewa nayi na dubi Ya Mahmud duk da yanda mood dinshi ya tsoratar dani ban fasa mishi magana ba! “Ya Mahmud me ya faru? me ya samu Mami? waye ya mutu don Allah?” shi dinma shiru yamun wasu siraran hawaye na bin kuncinsa kamar an balle fanfo! kaina ne naji yayi mun nauyi juwa ta soma daukana! stress din da nake shiga kwanan nan yamun yawa! kaina ba zai dauka ba! kakwalwata zata fashe! bana iya kuka balle naji sanyi da rangwame sai tsabar radadin zuciya da tashin hankali! wajen Mamin na sake komawa na dago fuskarta da hannayena guda biyu “Mami kuna son zuciyata ta fashe ne? ya za’ai na ganku kuna kuka kuyi mun shiru? kuyi mun bayani don Allah Mami kirjina kar ya buga” kawai janyoni tayi jikinta ta rungume ta sake fashewa da wani kukan matsananci!
karar kofa mukaji alamar shigowar mutane! nayi sauri na dago daga jikin Mami! Ya Omar ne da Ya Sadik dukansu babu walwala! kowanne ya nemi waje ya zauna! da gudu na bar jikin Mami na koma kujerar Ya Sadik! hannunsa na rike cikin gigicewa ina cewa “Wai Ya Sadik ya kuke so nayi da rayuwata ne? Mami da Ya Mahmud suna kuka tunda na shigo gidan sunki cemun komai! kuma kun shigo da alama kukan kuka gama a waje please! tell me what’s going on! please Ya Sadik!” sai lokacin na samu sa’ar da hawaye ya soma bulbulowa daga idanuna! mikewa ya Sadik yayi yaja hannuna muka futa daga falon zuwa can garden din gidan! zaunar dani yayi a kan farin lilon da ke wajen shima ya zauna a gefena! sannan ya soma mun bayani! “kinsan Zahra Yaya Mahmud shekarunsa nawa rabonsa da gida??” na girgiza kaina a sanyaye! yaci gaba “Shekarunsa goma da watanni uku cif rabonsa da gida Zahra kuma bai sake waiwayowa koda sau daya ba koda menene ya faru! saidai idan ta kure Dada taje Jeddah yayi kokari yaje Umrah su hadu! Daddy kuma da kansa yake tafiya London ya ganshi ya dawo! dukanmu idan muka matsu da son ganinsa garin da ya mayar gida muke tattaki muje! sai wannan karon! bai gayawa kowa yana shirin zuwa ba sai Mami kuma da ya tashi zuwa bai sauka ya biya ta ko’ina ba sai gidan Mami sai da ya kwana sannan ta raka shi gidan Dada yau! kinsan me Dada tace tana ganinsu? na girgiza kaina cikin kaguwa da jin karshen maganar! yaja numfashi “cewa tayi ta cire Mahmud daga cikin jikokinta tun ranar da ya cika shekara goma bai nemi gida ba! babu shi ba ita kuma tunda ta gano duk tsayin shekarun nan da yayi Mahmud na communicating da Mami tasan duk halin da yake ciki, itama Mamin ta tafi ta cireta daga lissafin jininta tunda har da ita za’aci amanarta! sannan taji labarin silar zuwan Mahmud ba don su bane bikin abokinsa yazo wannan ne abinda yafi komai bata mata rai ta yanke wannan hukuncin! kinsan halin Dada Zarah idan ta hau fushi abun baya yin kyau masu tsayawa su tunkareta daman Mami ce ko Daddy toh yau da su take fushin don naga alama shima Daddyn ransa yayi bala’in baci ko sallama baiyi ba ya tafi Riyadh! abun gabadaya baiyi dadi ba! ta tsaya ma suyi mata bayani Zahra bata basu wannan damar ba zagi da cin mutunci babu wanda batai ba a gidan nan har da tura Mami waje ta rufe kofar dakinta!
Hawayene suke gudu akan fuskata kamar an balle famfo! tsananin tausayin Mami ya kamani tare da haushin Mahmud wanda ya janyo mata duka wadannan bakin cikin! Nayi matukar jin bacin ran abinda Dada tayi! shin fushi hauka ne? in ka haifi mutane halittarsu kayi? kawai ta dinga batawa iyalanta rai? ina ruwan Mami cikin wannan laifin? meye sukayi mata me zafin da zata ce ta cire su cikin jininta? wannan ba daidai bane! wannan kuskure ne!
“yanzu meye abun yi Ya Sadik? ko Kawu Sulaiman zamu kira mu sanar dashi?” murmushi yayi mai ciwo sannan yace “kin manta wanene Kawu Sulaiman din kenan! idan har bai kara bata al’amarin ba na tabbatar sai dai ya kara lalata shi! sannan wa kike tunanin zai iya fuskantar Dada a wannan yanayin? kawai shiru za’ayi a kyaleta zuwa wani lokacin kafin ma a tare ta da ban hakuri ko wata magana!” girgiza kaina nayi cikin gamsuwa don nasan hakanne kawai mafuta! tare muka mike muka koma ciki! lokacin wani sabon scene ne yake faruwa! Mahmud ya kafe lallai sai ya tafi ba zai sake kwana a Nigeria ba yayinda Mami tace babu inda zaije! kowanne kuma kuka yake kamar ranshi zai futa! dukanmu tsayawa mukai muna kallonsu babu wanda ya tofa har Ya Mahmud ya saba jakarsa ya janyo troley da yazo da ita ya soma tafiya cikin fushi!
Mami tana daga zaune ta daga murya tace “Mahmud ka tafi kenan ka barni? zaka tafi domin ka nuna mun cewa bani ce na haifeka? ka tafi don ka nuna mun iyakata akanka? ka tafi don ka tabbatar cewa zaka iya rayuwa babu ni? kanaso ka nunamun cewa harda ni zakai fushi Mahmud? kaje! ka tafi! bazan mutu ba idan kwanana bai kare ba amma zan rayu da cikin tsananin bakin cikin iyakar da kayimun a rayuwarka!”
Cak! ya tsaya jikinsa har wani kadawa yake don tsabar fushi da bacin rai! kafin ya yarda da jakar hamnunsa ya dafe kirjinsa da sauri yana wani irin tari!lokaci kadan kwayar idanunsa ta juye ya soma futa hayyacinsa gabadaya muka rufu kansa Ya Omar ya tare shi jikinsa lokacin da ya tafi luuu zai fadi! Mami cikin kuka ta zari key tana cewa mu tafi asibiti mu tafi asibiti!
dukanmu muka dunguma muka futa! Ya Omar ke driving cikin high speed nikuma ina gefenshi yayinda Mami da Ya sadik ke bayan bakar Jeep din suna rike da Ya Mahmud da ke ta shure shuren mutuwa hannunsa rike da gefen kirjinsa na hagu! babu wanda yasa rai da Mahmud kafin muka isa Lima hospital ! cikin gaggawa likitoci suka karbe shi suka rufu akansa! dukanmu mu uku kuka muke ba me rarrashin wani sai Ya Omar ne kadai ke kai da kawo cikin asibitin! cikin ikon Allah kafin karfe uku sun shawo kan matsalar har numfashinsa ya daidaita sannan aka turo shi zuwa dakin da aka tanadar mana! Bacci yake yi har aka soma kiran assalatu Mami ta dubi su Ya Sadik tace “Sadik kuje gidajenku kuyi sallah ku dan runtsa da safe sai ku dawo tunda jikin nasa da sauki!” Ya Sadik ne kawai ya yarda amma shi Ya Omar cewa yayi sai ya farka tukunna bai kamata abarta ita kadai ba! sannan tace ya wuce dani ya ajeni a gida nasa su Aya su shirya breakfast na kuma debo mata abubuwan da zasu bukata nace “toh” muka baro asibitin!+
Bayan na dawo gida sallah nayi na kwanta naji ko zan iya runtsawa amma sam baccin yace baisan wannan ba! daga baya na mike na shiga kitchen na soma aikin da kaina duk yanda Aya da Juliet suke mun magiyar na bari! kunun gyada na soma damawa sannan na hada chicken p.soup da dankali na soya doya na zuba ruwan zafi a flask na hada komai cikin babban kwando! sannan na koma daki nayi wanka na shirya na futo! Ya Sadik ne ya sake dawowa ya daukeni wajen 7:30 muka tafi! a hanya yake sanar dani Ya Mahmud din ya tashi kuma jikinda sauki! nayi hamdala! lokacin da muka isa a zaune muka same shi kan gadon yana sallah!
Bayan mun gaisa da Mami na tashi na hada mata tea na zuba mata soup din a bowl na tashi naje gabanta na zauna na kai cup din bakinta idanuna a raunane dole ta karba! a hankali na dinga bata abincin har taci me yawa! murmushi tayi tace “i am okay haka Zahra bani ruwa!” na mike da sauri na dauko ruwa cikin fridge a dauki cup na zuba na bata! “Allah yayi miki albarka!thank you!” wani sanyi naji a raina! shin akwai abinda yafi farantawa iyaye dadi? babu!! mikewar da zanyi na ga Ya Mahmud yana kallona cikin murmushi! na aje kayan na matsa gaban gadonshi na soma gayar dashi! ya amsa cikin kulawa sannan nace “ya jiki naka?” yace “Alhamdulillah Zara! kinyi feeding Mami ga mara lafiya kina kallonshi ko?” murmushi nayi zan magana Mami ta taso itama da cup dinta a hannu tana cewa “kwantar da hankalinka bayan ga Maminka kusa kuma wacce Zarah ce zatazo baka abinci” sosai muka sa dariya gabadaya! ina kallon lokacin da Ya Sadik yake goge kwallar tausayi! Mami ta shiga bashi abincin! yanzun tambayata da akalar tunanina ya juya ga son sanin wacece ta haifi Mahmud? tana ina kuma yanzu? ya akai Mami ta maye gurbin uwa a gareshi?
Mami ce ta dawo dani daga tunanin da nake yi! “Zara kina jina?” na amsa ina kallonta! tace gaba “abinda nake so dake yanzu ki tafi gida ki hada kayanki ki koma gidan Dada. daman buki ne ya kawo ki kuma na kammala banason wata maganar ta sake shigowa kinga ba’a wajena kike ba Dada zata ga kamar nice na hanaki tafiya kinji?” duk da banso ba amma dole nabi umarnin Mami don banason a sake bata mata rai a kaina! da haka mukai sallama Ya Sadik ya sake daukata muka tafi nace kawai mu wuce gidan ai ba wasu abubuwa masu yawa ne a gidan Mamin ba!
ko cikin gate din bai shiga ba ya juya nikuma na iso cikin gida kirjina na bugawa don bansan me zanje na tarar ba nima! babu kowa a parlour na leka kitchen wayam! sai na tafi dakin Dada da sallama a bakina!
Tana zaune akan dadduma ta kammala addu’o’inta tayi shiru kawai!
sai da na daga murya nayi salllama sannan tayi firgigit ta juyo tana amsawa! a sanyaye naje gabanta na zauna na soma gayar da ita! cikin kulawa ta amsa kamar koda yaushe saidai ina iya karanto damuwar da ke kan fuskarta! “An kammala buki lafiya?” nace “lafiya lau Dada ina Baba Rabi ne?” cewa tayi “Baba Rabi taje Kaduna amma da yamma zata dawo” nace “toh bari na shiga dakina”. kwanciya nayi ina maida numfashi! tunani na rasa wanne zanyi acikin damuwoyin da suke damuna! a yanzu babu abinda yafi dagamun hankali irin abinda ya faru tsakanin Dada da Mami! tunanina wacce hanyar zanbi na warware su? me zanyi? kaina yayi nauyi! gashi muna dab da fara exams! kai har makarantar ma ta futa a raina fa! komai ma duniyar baya mun dadi wallahi! mikewa kawai nayi na shiga toilet na futo na nufi kitchen na shiga girki! barzajjiyar wankakkiyar shinkafa na futo da ita na dauko steamer na hada komai na dora akan gas! albasa manya guda biyu na yanka da yellowbel pepper da sweet pepper! sannan nayi grating attarugu na daka spices cikin mini motar! bayan na kammala na ciro hanta da koda a freezer na yayyanka kanana na dora su a wuta su dahu!
cikin mintina kadan na hargitsa wajen da kamshi! kafin azahar na kammala tattausan dambun shinkafa da sauce din hanta da koda! na samu coolers na zuba na asibiti na hada cikin kwando na rufe sannan na koma daki nayi wanka da sallah! sannan na shirya cikin maroon straight skirt na swade da armless top fara sai na dora short kimono akai! na nade kaina da farin gyale na saka farin sandal na dauko jakata na futo! a parlour na samu Dada tana cin abincin dana zuba mata tana korawa da five alive! “kai amma Zara dambun nan yayi dadi! yayi taushi sosai Allah yayi miki albarka!” cikin murmushi na isa gabanta na zauna nace “ameen Dada! zan shiga school ina da test!” tace “toh Allah ya kiyaye! sai kin dawo!” na mike na shiga kitchen na dauki basket dina na futo! kamar zatai mun magana kuma sai tayi shiru! na wuce na futa! asibiti na wuce kai tsaye! Mami tana sallah Ya Mahmud na zaune da alqur’ani a hannunshi yana karatu cikin zuci! na wuce na aje kwandon abincin kan tebur sannan nazo na zauna kan kujerar dake gefen gadon! rufe alqur’anin yayi yana murmushi! kin dawo Zara? nace “eh ya jikin?” cewa yayi “dasauki Alhmdllh” dai dai nan Mami ta shafa addu’a ta juyo tana cewa “Zahra me kika dawo yi nan? banason matsala fa? a ina kika samo abincin nan?” dan turo baki nayi cikin murya kasa kasa nace “Mami i wanted to cook your favourite! kuma makaranta nace wa Dada zanje! bata san ina gidanki ba ta zata daga gidansu Ihsan na koma gida! i am very careful Mami ba zata gane nan nazo ba” kada kai kawai tayi ta mike tana ninke abun sallar ta aje shi! “Mami check what i cooked for you!” na fada da wide smile akan fuskata! murmushi tayi ta wuce gaban tebur din ta bude babbar food warmer din nan da nan bakinta yayi forming O shape! “Zara dambu? kai amma naji dadi! Allah yayi miki albarka!” na lumshe idanuna ina cewa ameen! Mahmud ta kalla wanda yake ta murmushi tace “kaga Mahmud kamar ta shiga ranmu dazu kake maganar yaushe rabon da kaci dambu da danwake” sake fadada murmushinsa yayi beauty point din fuskarsa duka suka koma ciki! baice komai ba! shi ta soma zubawa ta mikowa! ya amsa ya soma ci! lomar farko ya tsaya ya dubeni “wait? did you make this?” na girgiza kai! “with your hands?” na sake girgiza kai! “are you sure?” dariya sosai ya bani yanda yake tambayan yana juya ido kaman wani mace! na dade inaso na gano cewa ko dai bashi ne mutumin da na gani a Saudi ba? wannan is soo caring and kind! wancan kuwa zalinci da mugunta kawai yasa a gaba! koda ke har yanzu ina tunanin kodai saboda idon Mami yake mun haka! cikin annashuwa muke hira suna cin abincin kowanne na yaba dadinshi! kafin ayi knocking kofa! Faisal ne ya shigo hannunsa rike da takardu! “ka dawo Faisal?” cewar Mami! cewa yayi “na dawo Mami an kammala komai inaga zuwa gobe zaku iya tafiya! tunda ya samu sauki!” sai lokacin na gayar da shi tare da tambayar Ihsan yace “ai kin kyauta da kika gudu tana nan zata hadu dake” nayi murmushi kawai! sai bayan ya tafi na dubi Mami nace “Mami ina zakije?” ajiyar zuciya ta sauke tace “London zamu tafi da Mahmud! asama mishi proper medication!” tabe baki nayi kamar zan kuka nace “Mami i will go with you!” dariya tayi tace “kin shirya tambayan Dada ko?” na hade fuska! ta sake cewa “lastweek ne ma take cemun tayi magana da Daddy yace a bari sai kinyi hutu zakuje shopping din kayan daki” duka idanuna na zaro! wanne irin shopping din kayan daki? “kamar baki san komai ba! bikinki saura wata hudu duk da wata dayan da aka kara! idan ba’aje yanzu ba kayan ba zasu zo kafin bikin ba” wani irin tashin hankali naji ya ziyarci kaina! noo! not me! i’m not getting married! not soo soon! infact na soma tunani daban akan auren Imamu! ina sonshi sosai amma na dena burin aurenshi! it can’t be! lokaci daya na mike na hada jakata na dau key nace “Mami sai anjima na tafi” baki sake take kallona sannan tace “meye haka? daga maganar siyan kayan daki? toh haka za’ai auren ba’aje anyi siyayya ba?” cikin muryar kusa da fashewa da kuka nace “Mami bazan yi aure yanzu ba! na fasa!” na bude kofar na futa ban saurari kiran da take mun ba!
+Cikin sauri nake tafiya har na isa parking space na shiga mota na zauna! numfashi nake futarwa mai nauyi kamar wanda nayi gudun shekara! kaina ya soma sarawa! aure? no! in this situation? bazaiyu ba! banajin zan iya auren Imamu yanzu gaskiya duk da ina bala’in sonshi! dawa zanyi magana? wa zan nemi shawararshi? God!! Aisha ce kadai zata saurareni ta fuskanceni ta gane me nake nufi! i have no option than to go and meet her! cdn motar na kunna na saka karatun al’qurani daga bakin Sheikh Abdurrahman Sudais cikin Suratul Ma’idah! a hankali nutsuwa ta dinga saukarmun har na samu sukunin tada motar na hau kan titi a hankali na dau hanyar gidansu Aisha!
Maigadi ya wangale mun gate na shiga ba tare da na sauke gilashin motar ba don banason ya cikani da unending surutunsa! bayan nayi parking na futa daga motar na shiga cikin gida! a parlour na samu Ikhram tana sakawa Abid junior brother dinsu kaya! cikin far’a ta soma gayar dani! “Iky ya Kano?yaushe kika dawo daga gidan Maman?(Aunty dinsu ta kano)” cewa tayi “Jiya Daddy yaje muka taho tare!” nace “hutu ya kusa karewa dai” ta sake murmushi sannan tace “saura 10days na koma Ya Zahra” nace “Allah ya taimaka ina Umma? ina Aisha? gidan shiru haka” cewa tayi “Aw ai Ya Aishan suna asibiti da Umma bata da lafiya” na zaro idanu cikin damuwa “meya sameta? yaushe suka tafi?” ta amsa da cewa “basu dade ba! kanta ne yake ciwo da jiri kuma in ta tashi kamar zata fadi” na girgiza kai cikin damuwa nace “Allah ya bata lafiya wanne asibiti suka tafi?” tace “Nisa ne amma na kira Umma tace yanzu zasu shiga ganin Doctor ba lallai admitting dinta zasuyi ba” na girgiza kai cikin gamsuwa! ina zaune muna dan hira akai sallar la’asar na mike na shiga dakin Aisha don yin alwala! direct toilet na fada nayo alwala na futo nazo na tada sallah! bayan na idar na mike zuwa gaban vanity table na tsaya! lotion na dauka na shafa na gyara fuskata sannan na dawo gaban gado na zauna! na kai hannu na janyo drower sama ta jikin gado! albums dinmu ne na grad! nan na shiga dubawa ina murmushi tare da kewar makaranta da kawayenmu! drower ta kasa na sake janyowa! babu komai sai katon diary da macbook dinta samanshi! mamaki nayi domin ai mun dade da daina wannan shirmen na aje diary da rubuce rubuce a cikinsa! well bari mugani! na fada a raina! ciro shi nayi na zauna a kasa na bude page din farko! da manyan baki aka rubuta “This is my personal diary! do not open my diary without my consent!!” nayi murmushi ina cewa ‘i am exempted’ abubuwane game da ita da wadanda suka faru tayi farinciki mostly an dade sosai har zan rufe na aje sai na bude wani shafi da ya tafi da hankalina! “how he changed my life” rubutun shekaru uku da suka wuce akayi shi cikin harshen bature!+
“ban taba tunanin haka so yake ba! ashe lokaci daya yake shiga jikin mutum ya fada zuciya? ashe dagaske akwai love at first sight? ban taba gasgata wannan hashashe ba sai da yau ya faru a kaina! mujallar Ovation ba wadda zan manta nan kurkusa bace domin ita tazo mun da hoton matashin da tunaninsa ya zamo mahadin rayuwata! hakan ya faru ne lokacin da na shiga motar Baba naga mujallar na dauka ina kallo! ciki harda bukin yayan shahararren dan kasuwan nan Yusif Kashim kyaree na Maidiguri! bayan hotunan ango da amarya na idanuna suka dallaromun hoton wani dogon farin gaye mai kama da balarabe wajen kyau da haskenfata! sanye cikin bakin kaya yana murmushi!! tundaga lokacin zuciyata bata daina bugawa tana amo da hoton shi akanta ba! tunanina ya tsaya cak har muka isa da Baba gidan abokinshi bansan inda hankalina yake ba! bayan mun dawo ban iya aje masa mujallar ba na taho da ita cikin gida! tun daga ranar rayuwata ta chanja ya kasance bani da abun yi illa na kurawa hoton wannan bawan Allah ido nayi ta kalla ina hawaye don azabar da nakeji akan soyayyarshi ba yar kadan bace! abun ya soma shallake hankali har Umma ta fara ganewa a karshe da ta rutsani ina kuka nace mata gabana ke yawan faduwa! umma ta bani addu’o’i wanda da taimakonsu na samu relief din damuwa! daga ranar ban sake kwanciya bacci ba tare da na kalli wannan hoto ba! ban sake daga ido na kalli wani bayan shi ba!”
Murmushi nake ina karkada kai! lallai ma Aisha ashe ta taba fadawa tarkon so amma duk surutunta bata sanar dani komai ba! kodayake an jima kila duk shirmen kuruciya ke dawainiya da ita lokacin! bayan na wuce wasu shafukan da duk yawanci rubutun aka irin son da take mishi ne da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta! banyi nisa ba na sake tsintar abinda ya kadamun yan hanji har na runtse ido na bude don ganin shin gizo idona yakemun ko gasjiya ne?”
STORY CONTINUES BELOW

” Biggest shock! baddest luck!
dama zan iya rubutu da hawaye a maimakon tawadar rubutu domin rubutun ya bayyanar da tsantsar damuwa da tashin hankali da bakin cikina! yau rayuwa ta juyamun baya! abinda yake faruwa yafi kowanne mafarki muni a duniya! yau naga masoyina! mutumin da kullum mafarkina da burina ya ta’allaka akan ranar da zan hadu da shi? yanayin da zan ganshi da hanyar da zanbi na mallakeshi!kullum hasashena yana nuna mun ranar zata kasance rana mafi girma da farinciki a rayuwata! to amma me? A yau na ganshi munyi ido hudu dashi a wajen da ban taba tunanin kawowa ba! ganin baimun amfani ba illa jefani cikin masifa da bala’i da yayi! A yau kawata aminiyata kuma yar’uwar da babu kamarta wajena ta gabatar mun da Masoyina a matsayin mutumin da yake neman aurenta! Nayi tunanin duk abinda yake faruwa gidansu Zara mafarki ne ko kuwa idanuna gizo suke mun don haka nayi sauri na shanye mamakina da shock dina a gabanta! saidai a karshe na tabbatar da babu mafarki ko gizo aciki! abinda yake faruwa dagaske ne a zahiri! ashe Imamun da ta hadu dashi shine masoyina! meye yafi wannan ciwo da karya zuciya?”
Ina karantawa hawaye na bin kuncina kamar an balle famfo! tsananin tausayi! mamaki! firgici! tashin hankali sukai mun rubdugu lokaci daya! Aisha na son Imamu tun kafin na hadu da shi? na shiga uku!
hannuna na rawa na bude wani fejin
“A scrifice”
Da ace ba Zara Imam yake so ba! to da zan kwato soyayyarshi ta kowacce hanya ta kowanne hali a hannun kowacce irin mace ce! Amma Zara?! she is my sister! mutum mai daraja da matsayin da zan iya sadaukar wa komai nawa! bazan iya kwatar soyayyar Imam a hannun Zara ba! koda zanci amanar kowa bazan iya cin ta Zara ba! she is my blood, my supporter, my best friend! bazan iya ba!! Na sadaukarwa Zara Imam da soyayyarshi ko da hakan zai kawo karewar numfashina! she deserves more than that a wajena! na hakura da Imam ko da soyayyarshi za tai ajalina!”
kuka nake wui wui ba tare da tunanin ina kaina yake ba! waye zai shigo ya sameni domin ba’a hayyacina nake ba! wani irin yanayi na shiga wanda bazan iya kwatantawa ba! wani abu ne wanda ya daki zuciyata ya gigita ta! ya akai haka ta faru?
shafi na gaba da wanda ya biyo bayanshi duka akan feelings dinta ne game da Imam da kuma halin da take ciki! na sake bude wani shafin
“I need somone to speak to!”
Abubuwan da nake ciki sun yimun nauyin da kaina shi kadai ba zai dauka ba! waye zanjewa da damuwata? wa zan gayawa matsalata? wa zai fahimceni? wurin wa zan tafi?” amsar Zara ce sai dai wannan matsalar tafi karfin na tunkareta da ita! so da yawa idan nayi kamar zan nemi Jidda na gaya mata halin da nake ciki sai na kasa! gani nake kamar abun kunya ne abinda na fada ciki! ace saurayin aminiya ta nakeso? aminiya irin Zara? no! i can’t! amma ya zanyi? ban iya cinye magana ni kadai ba! inajin kamar kirjina zai fashe idan ban furta ba! dole na nemi Jidda! dole na nemi wanda zai ban shawara akan yanda zan futar da Imam a raina………”
Ban kammala shafin ba naji horn din mota da karar bude gate! a sukwane na kulle diary din da zaren jikinsa na mayar dashi mazauninsa na kawo macbook din na dora akai! toilet na fada cikin sauri na wanko fuskata na dawo gaban mirror na samu kwalli na dinga rambadawa a idona har ya faramun zugi! duk da haka idanun sun sauya kala sai na ciro bakin sun glasses dake cikin jaka na makala! ina shirin barin gaban mudubin Aisha ta bude kofa ta shigo! sunan Allah na dinga kira kafin na juya ina murmushi na isa gabanta! “ohh sannu besty!” na fada ina dafa kafadarta! ta danyi jimm! na wani lokaci tana nazarina da dakin kafin ta riko hannuna muka zauna bakin gado! “ya kikejin jikin naki? what did the doctor say?” nake tambayarta da duka dauriyata! “ammun test dayawa sai nextweek duka results zasu futo muji komenene!” na girgiza kaina ina cewa “Allah yasa alkhairi! Allah ya baki lafiya” tayi murmushin karfin hali tana cewa “Ameen! me ya samu idonki ?” cewa nayi “ciwo yake son yi yayi ja sosai kuma banason haske da iska” tace “hardluck! Allah ya raba ki da apolo!” nayi murmushi nace “Ameen”
ban kara ko minti goma ba nayi dabarar barin gidan domin dauriyata ta kare idan naci gaba da ganin fuskar Aisha zuciyata zata karasa karyewa!
ina mota ina tuki amma hankalina sam baya jikina! kariyar Allah ta kaini gida amma ba irin tukin da nayi ba! ina shiga gidan na fada kan kujera kaina na wani irin sarawa Dada ta tambaya lafiya?? nace mata kaina ke ciwo! ina nan kan 3seater a kwance kaina na wani irin sarawa yayinda zuciyata ke radadi da zugi mai tsanani! kafin magrib wani matsanancin zazzabi yayi gaba dani! tun ina gane duniyar da nake ciki, ina jiyo sautin muryoyin Dada da Baba Rabi a kaina har na daina gane komai duhu ya mamaye idanuna naji diff! komai ya tsaya!!!
———————————————————–
Furucin Zahra na karshe da futarta cikin fushi da kin sauraren kiran da Mami take mata ya baiwa Mamin mamaki ta juya tana kallon Mahmud wanda ya zubawa kofar da ta futa ido! “me kenan? meye haka?” ta fada a fili! Mahmud ne ya dubi Mami cikin damuwa! ya dade yana so yayi mata magana akan Imam da Zara amma ya gaza gane ta wanne siga zai shigo da zancen! yanzun ma sanadin wannan dalilin ya samu damar cewa “Ahm Mami nikuwa inaso na tambayeki?” girgiza mishi kai kawai alamar tana saurare! cikin sanyi yace “A ina Zara ta hadu da wannan Imam din?” babu damuwa ta labarta mishi komai game da yanda Zara ta hadu dashi da kuma alakar ita Mamin da kanwar Maman Imam din!” ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “kuma Mami tana son shi?” murmushi Mamin tayi tace “tana son shi mana Mahmud tunda ita ta kawo shi da bata son shi zata bari magana tayi karfi!” ya sake cewa “amma kuma bakya jin furucin da tayi kamar wadda ta sauya ra’ayi ko aka batawa rai game da batun aure?”
shiru Mami tayi tana tunani a zuciyarta! kwarai Zara ta rage dokin da take akam Imam sosai idan ta hada da farkom haduwarsu yanda kuru kuru ake gano soyayyar Imamun cikin yanayinta da kalamanta da ayyukanta! sannan yanzu ana dadewa bataji tace Imam zaizo ko yazo gidansu ba! koma maganarsa bata yi! tabbas akwai alamun ayar tambaya!
Ganin Mami tayi shiru shima Mahmud ya dinke bakinsa! amma a ransa tunanin yanda za’ai ya raba yar’uwarsa da mutum irin Imamu yake yi domin shi ya tabbatar ko da dagaske Imamu son Zara yake yi kuma ya kai ga aurenta to lallai ba zai gaza bata mata rayuwa ya nakasa mata zuciya da boyayyun miyagun halayensa ba! menene mafuta????