HAUSA ARAB CHAPTER 3

 HAUSA ARAB CHAPTER 3

A hankali nake motsa fatar saman idanuna ina juya su kafin na samu damar dage su a hankali na bude! wanda kwayar idanuna suka dira a kansa wani matsakaicin mutum ne baki mai kewayayyiyar fuska ma’abociyar haiba da kwarjini! ba wani kyakykyawa bane amma sam ba zakaso dauke idonka akan nashi ba! farar labcoat ce a jikinsa wuyansa rataye da stethoscope yayinda idanunsa ke sakaye da garai garai din medicated glasses! a dakikun da basu fi goma ba na yi wannan hasashen!

“are you okay? can you talk?” ya fada cikin British accent da sassanyar murya! What the hell is wrong with me? why am i checking him up?” firgigit na dawo da tunanina duniyar da nake! na soma tunanin toh ina ma na san wannan bawan Allah? meya kawo shi wajena? idan zan tuna ai ina kwance ne kan doguwar kujerar falon Dada kaina na barazanar rabewa biyu! sai na soma juya kwayar idona ina karade dakin da kallo! dan karami ne mai wadataccen haske! daga painting har komai na dakin farine sol! dana kalli jikina sai naga kayan da suke jikina ne dai na dazu sai dai kimono din da aka cire mun aka barni da armless top dina fara sol! farar nurse ce a bayan likitan tana dauke da tasar da aka cika da tarkacen likitoci dukan idanunta akaina! a hankali na sake maida dubana ga likitan da na soma bude ido akan fuskarsa! “He is quiet! just observing and reading my face” saida na lashe busassuna lebbana na samu damar soma magana a hankali!

“meya kawoni nan? Ina Dada? ina Mamina? meya sameni?” murmushi ya danyi wasu lafiyayyaun ingantattun hakora masu bayyanar da samun kulawa ta musamman suka bayyana tare da siririyar wushirya a tsakaninsu! da sautin da yafi na dazu karfi yace “don’t worry! kina asibiti ne! wadanda kike tambaya kuma suna nan tare da ke! amma zaki dan huta zuwa wani lokaci kafin a soma shigowa a miki hayaniya” a hankali na girgiza kaina! ya sake cewa “yanzu me yake damunki?” cikin rashin kuzari nace “Kaina yana mun ciwo!”.

“bayan shi fa?” ya dora da wata tambayar! na girgiza kaina a hankali! sai lokacin tunanin abubuwan da suka faru dani a yau suka sake tariyowa cikin kaina. na kuma tabbatar ba mafarki nayi na tashi ba kuma ba wasa bane! sai naci ciwon kan ya kuma tsauri! “hello!” firgigit na juya ina kallonshi! cikin daurewar fuska yace “kin farka daga halinda damuwa ya saka ki ciki kuma zaki sake cigaba da tunanin abinda zai maida ke cikin damuwar? kinyiwa kanki adalci kenan?” a wannan karon da hausa yayi magana! murmushi kawai nayi bance komai ba! ya kammala examining dina aka tsira mun allurai. kafin su futa na soma bacci!+

Ban sake farkawa ba sai karfe tara da arba’in da uku na safiyar washegari! Ya Sadik na soma gani a gefen gadona kan kujera! na juya idona gefensa Dada ce a tsaye kaina tana tofa mun addu’o’i! Su biyu ne tak a dakin! cikin rawar murya Dada tace “Zara kin tashi? sannu!” a hankali na soma karanto kalmar shahada kafin na daga mata kaina! Ya Sadik ya mike da hanzari yana cewa bari ya kira Doctor! mintina biyar suka shigo tare! Likitan jiya ne ya shigo tare da umartar su Dada su futa! da murmushi ya dubeni yace “kin tashi?” na girgiza kaina a hankali! “yanzu meye yake damunki?” nace “babu komai! inaso na tafi gida ne kawai” wani murmushin ya sake yi sannan yace “idan zuwa gobe munga kin daina wannan tunanin da ciwon kai zamu iya sallamarki!” na dan yamutsa fuska nace “Naji sauki ni! ba tunani nake ba” bai sake magana ba ya soma yiwa Nurse magana yana rubutu cikun file dina sannan ya juya ya barta dani ya futa! allurai tayi mun sannan ta taimakamun nayi brush nayi alwala! bayan nan su Dada suka shigo! Nan aka taimakamun nasha tea na biya bashin sallolin da suke kaina a zaune sannan na koma na kwanta!

Dada ce ta dawo kujerar gefen gadona ta zauna! hannunta ta dora akan goshina ta soma magana a hankali! “Zahra’u! meye yake damunki? meya shiga ranki yake saki tunani irin haka har damuwa take son yi miki illa? me kika rasa? me kikeso? likita yace damuwa matsananciya da tunani suka jefaki cikin halin da kike ciki! ki gayamun ko menene kikeso Zara nikuma nayi miki alkawari zan yi miki shi in dai bai fi karfin ikona ba”

A hankali na dago ina kallonta! nayi mamakin wannan furucin na Dada domin sai ta kure zakiji Dada na rarrashin mutum! tafi ganewa fada da nasiha amma rarrashi har da me nakeso? abun da mamaki! da ace babu matsalar da ke tsaninta da Mamina toh kawai cewa zanyi tamun alfarma ta janye maganar aurena da Imam bana son shi! amma yanzun akwai abinda yafi wannan muhimmanci! naga na gyara tsakaninta da diyarta zaifi komai yimun dadi! duk da bansan yanda zata fahimci maganar ba!

ina cikin tunanin ta katseni ta hanyar jijjiga kaina a hankali! nayi firgigit na dubeta! cewa tayi “Zara wannan tunanin ne fa ba’aso! shine kuma likita yace ya janyo miki halin da kike ciki! duka shekarunki nawa da zaki cinye irin wannan damuwar a ranki? meye amfaninmu idan har zaki kukan wani abu har ya kai ga ta saki damuwa? ki gayamun abinda yake damunki!

cikin karfin hali da muryar tausayi na soma magana! ” Dada kiyi hakuri ki taimaka ki daina fushi da Mami da Ya Mahmud don Allah ki yafe musu!”

wani irin kallo tayimun har sai da cikina ya duri ruwa! sannan tace “waye ya gaya miki ina fushi da su? waye ya gaya miki abinda ya faru?”

Da duk dauriyata naci gaba da magana hawaye na bin kuncina!

“Dada naje gidan Mami ne zan kwaso kayana da na bari na buki sai na samu ciwon Ya Mahmud ya tashi yana ta wani abu har ya futa hankalinsa!” da Su Ya Sadik muka tafi asibiti da shi aka kwantar da Shi a daren! kowa na tambaya me ya faru baya amsamun sai dakyar Ya Sadik yayi mun bayani! Dada kiyi hakuri ki taimaka ki yafe musu! suna son ki Dada kuma suna neman afuwarki don Allah ki yafe musu!” na fashe da matsanancin kuka!

hankali tashe Dada ta dubi Ya Sadik tace “Saddiku? hakane abinda ta fada? Mahmud na gadon asibiti? kuma ciwonshi ya tashi?”

A hankali cikin tsoro Ya Sadik ya daga kansa! cikin matsanancin bacin rai Dada tace “amma baku gayamun ba? yana kwance a asibitin ba’a sanar mun ba? yanzu suna ina? wanne asibitin ne? wanne halin yake ciki?”

a sanyaye Ya Sadik yace “kiyi hakuri Dada! amma babu wanda yake da kwarin guiwar tarar ki da magana akan Ya Mahmud ganin yanda ranki ya baci! amma kiyi hakuri Dada ki mana afuwa!” sake cewa tayi “Yanzu yana ina? ya jikin nasa?”

ya sake tausasa murya yace “Babu laifi Dada da sauki! amma sun wuce London yau da asuba! domin ya samu ingantacciyar kulawa tunda ciwon ba karami bane kuma likitoci sun sake jaddadawa idan aka barshi cikin damuwa da tunani komai na iya faruwa dashi!”

zaraf Dada ta mike tsaye! sai kuma ta koma ta zauna! babu zato ta barke da kuka matsananci! har kasa Ya Sadik ya zuba guiwoyinshi cikin kaduwa yana baiwa Dada hakuri!

cikin kukan take cewa “buga mun babanku ka bani”

sake tausasa murya yayi yace “Don Allah Dada kiyi hakuri ki mana afuwa ba da gangan muka ki sanar miki ba! ba nufinmu mu bata miki ba! sai don ganin yanda ranki ya baci kuma ba laifin Daddy bane wallahi Dada! kiyi musu uzuri!” da murya mara karfi tace “cewa nayi fada zan mishi? ka buga mun kawai bani” ba’ason ransa ba ya shiga neman family line din Daddy, bugu biyu ya dauka! sai da ya gayar da shi sannan ya baiwa Dada wayar! dukanmu na mujiya muka zuba mata muji irin abinda ta tanadarwa Daddy na bacin rai amma ga mamakinmu cewa tayi “idan da hali inason jirgi zuwa gobe idan kuma ba zai samu ba kada ka damu zamu shiga na haya gobe da wuri nakeso na sauka a garin London!” kallon kallo muka shiga yi da ni da Ya Sadik kowanne yana tunanin abinda zai faru!..

———————————————————–______________________________________

Lokacin da muka sauka garin London ruwa ake sosai wanda ya saukar da wani sanyi da ni’ima mai ratsa jiki! Daga Dada sai Daddy mukai tafiyar kasancewar su Ya Sadik suna shirin tafiya honey moon da matansu. la’asar likis muka shiga gidan Daddy na Sussex Garden! komai an shirya shi tsab. an kunna duka heaters din gidan ya dau wani dumi! Duka angle din gidan an aje sassanyan turarukan ruwa masu amfani da iska irinsu Mango and Papaya! wannan duka aikin Helen ce mai kula da gidan!

Daddy ko zama bai ba ya wuce Oxfordshire! Dakin da na zaba na bude na kai kayana sannan na futo na shiga kitchen don samar mana abinci domin Dada bata yarda da cin abincin bature ba! ko kwano Helen ta wanke bata cin abinci a ciki! in an magana tace kafiran banza kafiran hofi! dole ta baka dariya!

komai an aje a kitchen din ga cefane cikin kwaton kwando komai fresh! kifi na dauka nayi marinating na adana sannan na futo da ingredient din Tuna spaghetti. cikin lokaci kadan na kammala aikina na hada wa Dada Kunun tsamiya na jera mana komai a tsakiyar parlour! sannan na koma dakin Dada na sameta tana waya da Kawu Sulaiman! sai da ta kammala nace “Dada na gama abinci bismillah! ko nan zan kawo miki?” cikin murmushi tace “kai, dadina da ke Zara zafin nama da sanin abinda ya kamata! yanzu har kin yi girki?” nima murmushin nayi nace “Dada ai nasan ba abincin Helen zakici ba gashi rabonmu da abinci tun safe!” “Toh Allah yayi miki albarka Zara” cikin jindadin addu’ar Dada na amsa muka futa parlour! tayi matukar jindadin kunun da na dama mata musamman saboda babu abinda tafi so a garin irin kunu! bayan mun kammala na tattara kayan na kai kitchen sannan na shafa mata maganin ciwon kafarta da indai akai tafiya sai an mata amfani dashi saboda zirga zirga!

Dakina na dawo na janyo Ipad dina na shiga Skype na kira Aisha! sau uku tana ringing ta katse bata amsa ba! sai na tura mata message mun iso lafiya na kashe ipad din na kwanta!

washegari ma ni nayi mana break fast sannan na shiga aikin dakina! jera komai nayi cikin wardrobe na jera kayan kwalliya kan vanity table! na sauya bedsheet daga fari zuwa purple na kunna burner na saka sandal wood ko’ina ya dau kamshi mai dadi!

karfe hudu na yamma Daddy ya iso! nayi maza na shiga toilet nayo wanka na shirya! Black pencil Armani trouser da top dinshi pitch na kawo jacket mai kauri black na dora! booth dina har guiwa yake duka jikinsa gashi ne shima black! na feshe jikina da turaren Swiss Arabian masu nauyi wanda suka Dace da wether din!

tare da Daddy muka kama hanyar Liverpool a mota daya! lokacin da muka isa asbitin andawo da Ya Mahmud kenan da dakin aune aunen likitoci a galabaice yake sosai! Mami ta futo daga dakin kenan tana share hawaye tayi tozali da mu! Da wani irin shock, suprise da emotion take kallonmu! kawai sai gani mumai Dada ta karasa ta rungume Mami ta barke da kuka tana cewa Mami ta yafe mata! itama Mamin sai ta fashe da matsanancin kukan ta rukunkume Dada! Daddy kawai murmushi yake yayi folding hannuwanshi a kirji yana kallon wannan scene mai kayatarwa!

Nikam kofar dakin Ya Mahmud na tura na shiga cikin sanyin jiki!

a kwance yake magashiyan yana baccin wahala! duka jikinsa na’urorin likitoci ne kala kala sai dai babu oxygen din alamar numfashinsa na tafiya dai dai! wasu siraran kwalla suka dinga biyo idanuna! ko na menene bansani ba!

hello lovies💞💞 it’s been a while! i am sorry for the late update! I am super busy wallah!

through out this month bazan samu daman update koda yaushe ba! amma i promise you ina samun nutsuwa zan dinga update every 2days!

thanks for your understanding💝💝

Enjoy!!kwanakin da suka biyo baya sauki ne da afuwa suke samuwa ga Ya Mahmud tunda ya bude ido yaga Dada da Daddy a gefensa suna nan nan da shi bayan dramma da aka sha Dada ta rungume shi tana kuka tana cewa ta yafe masa kuma tana tare da shi a kowanne yanayi na rayuwa ba zata sake biris dashi ba! kullum cikin murmushi da walwala yake kasancewar ba mai yawan magana bane!

Abinda bangane ba kawai shine doguwar basamudiyar baturiyar da ke zarya tsakanin gidansa da asibitin wai ita Safna! ban taba ganin mutum mai tsayi irin nata don ko a maza sai an tona za’a samu zankalelen da zai daidaita kafada da ita! babu kunya ba tsoro take nuna kulawarta da soyayyarta ga Ya Mahmud. ta rungume Mami ta rungumeni kullum tazo har ma mun saba. kai har Daddy mika mishi hannu take yi suyi musabaha shi dai sai kawai ya bita da murmushi! ita kuwa Dada ta dinga zabga mata harara kenan! inaga gane hakan da tayi ne ya sanya ta rage matsowa kusa da ita! na lura sun saba sosai da Mami domin matar mai far’a ce da son mutane! ni kaina da muka kwana biyu da ita sai naji ta shiga raina a dalilin kulawarta da kyautatawarta garemu! ga zallar wauta da rashin tarbiyya da ke dawainiya da ita. wani lokacin nayi dariya wani lokacin na ciji yatsa wani lokacin haushi ya turnikeni!

a haka muka kwashe kwanaki goma a Liverpool!

An sallami Ya Mahmud sai muka tattaro muka dawo cikin London gabadaya! akaci gaba a ririta shi kamar kwai! Ruwa wannan a baki Mami take bashi inaga abincin ma da da hali sai ta tauna masa ta hadiye masa zata sanya masa a cikinsa! ko kulani batayi abinda yake cimun rai kenan! hira wannan bansan lokacin da mukayi da ita ba! hankalinta kacokan na kan dan gatan ta wanda suka dora dukan so da tattali akansa! sai yanzu nagano hasashen da nake kan cewa Dada da Mami sunfi sona fiye da kowa ba dai dai bane domin kuru kuru suke nuna ruwan wariyar launin fata da bambamci a tsakaninmu! Tun ina daurewa na mai da komai ba komai ba har na kai bango, tunda kunsan ita zuciya tsoka ce ba dutse ba duk yanda kaso daurewa wani abu wataran sai ka gaza! don haka sai na rage zaman parlour tare da su! sai na shiga dakina na kwanta ko na kira Aisha ko Ihsan muyi hira! idan dare ne nayi ibadata!

Imam kam yanzu muna kwana uku bamuyi waya ba!  ba kira ne baya yi ba nice ban cika daukar wayar tashi ba! tun yana complain har ya hakura. ba kuma wai don na daina son shi ba, No, ina son sanya distance ne a tsakaninmu ne! na soma sabawa da rashinsa kafin na yanke hukuncin da na tanadar mana!

yanzu kam number wayar Jidda cousin din Aisha kawai nake nema, banason na samu ta hanyar da Aisha zata sani don haka nake bin komai a hankali! da ina da hali babu abinda nafi bukata irin a samo mun Diary din Aisha na karanta abinda ban karanta ba, na karasa tone boyayyun sirrikan da ban bankada ba ranar da naje! gabadaya hankalina tashi yake idan na tuna abinda nake shirin yi da abubuwan da zasu iya biyo baya idan hakan ya faru! me zan fuskanta daga Dada? Mami? Daddy da kuma sauran mutane? mecece makomata kuma? lokaci kalilan na zabge na rame kamar mara lafiya! babu abinda yake mun dadi! gashi saura kwanaki biyar mu soma exams wadda nake tunanin bazan samu rubutawa ba! why? meyasa rayuwata take neman tsayawa cak ne? me yake faruwa dani? haka nake yini na kwana tunani  da sake sake! da ni mai saurin hawaye ce da tuni ruwan hawayen nawa ya qare duk da a yanzu babu abinda nake sha’awa irin na dinga kukan ko na samu sassaucin zogin da nake ji cikin kirjina!+

          Yau ma kamar kullum ina dakina bayan sallar azahar. ji nayi duka zaman ya dameni sai kawai na mike na dora jibgegiyar jacket akan gown din jikina skyblue na nade kaina da mayafi na saka takalmi na futo! Suna nan zaune a parlour, Dada na shan fresh fruits!Ya Mahmud na gefen Mami tana aikin dama mishi furar da kullum yake sha irin wannan lokacin! gefensu karamar mp3 ce suna sauraren tafsir daga bakin sheikh Dahiru Bauchi na Ramadan din da ya gabata!

wani abu na hadiye kafin na karasa inda suke! Dada ce ta dubeni tace “sai ina kuma?” a sanyaye nace “zan dan futa ne abu zan siyo” Mami da bata ko dago ba tace “baki ci abincin rana ba fa” nace “uhm! sai na dawo zanci” ga mamakina ba ta ja maganar akan lallai na zauna naci ba sai kudi da ta miko mun wai na taho da mata da kabewa Ya Mahmud yace Tuwon shinkafa miyar taushe yakeson ci!

na karba kawai na futa raina a bace!

sai da na gama zagaye unguwar ina shan sanyi kafin na wuce aiken siyo kabewar!

ina dawowa na samu Daddy yazo don haka sai kawai na shiga dakina na soma parking! sai da na kammala cika akwatina da kaya sannan na dora abaya kan kayan jikina na nade kaina. A parlour duka na same su suna ta hira suna dariya cikin raha da farinciki! Daddy ne ya soma cewa “A’a Zahra me kike tun dazu a daki?” a sanyaye nace “bakomai” sannan  na durkusa daga inda nake nace “Daddy don Allah idan zaka tafi anjima zan bika” sai lokacin duka suka zuba mun idanu kowanne da ayar tambaya a fuskarsa! Daddy yace “a’a! zaki bini kuma? Nigeria fa zan koma Zara? me zaki koma kiyi ke kadai? ga su Sadik na shirin isowa jibi?” kaina na sadda kasa nace “Daddy nafiso na tafi, kuma mun kusa fara exams” murmushi yayi yace “a’a! anya Zara? ba wannan dalilin ya saki son tafiya ba! gaya mun me akai miki? wa ya tabaki? Dada ce ko Mami ko Mahmud?” wai sai naji hawaye ya soma tahomun don tsananin haushi! cikin shashesheka nace “babu kowa”!

ware ido Daddy yayi yace “zo! matso nan! zo kusa dani ki gaya mun menene?” tsam na mike na isa gefen Daddy yasa hannu ya zaunar dani gefen shi yana cewa ” haba Zahra bansanki da saurin kuka ba gayamun menene? ko baki lafiya?” na girgiza kai hawaye na diga a idona! cikin tsawa Mami tace “Malama wanne wulakanci ne zakisa mutane a gaba kina kuka ana tambayar ki kinyi shiru? waye sa’anki? zaki bude baki kiyi magana ko sai……!”

Daddy ne ya katseta ta hanyar daga mata hannu! “Ya isa babu ruwanki! ba dake nake ba!” ya maido da hankalinsa kaina yace “Zara gayamun me akai miki?” cikin kuka nace “Daddy kana gani duk sun tsane ni kowa ya daina kulani sai Ya Mahmud kadai suke so” Daga Daddyn har Dada da Ya Mahmud dariya suka kece da ita banda Mami da ke zabga mun harara!

cikin dariyar Dada take cewa “hohoho! kishi ne yake dawainiya da ke ashe Zahra’u!” taci gaba da dariyarta wadda take kular dani!

Daddy ya dafa kafadata yace “awww hakane Zara? wato abinda yake faruwa kenan ko? an hade miki kai? toh ai kuwa baki ga ta zama ba! kyalesu kawai kije ki hada kayanki muyi tafiyarmu! daman daga Nigeria Riyad zan wuce sai muje kiga Nuratu ko?” na daga kaina ina murmushi! what a lovely Father I’ve gat! cewa nayi “Na hada kayana Daddy” yace “Aww ashe ma a shirye kike Zara? toh shikenan jirani naje wata unguwa na dawo sai mu tafi” na daga kaina ina goge hawayen da sa’ar gaske tasa suka zubo! Hannu ya saka a aljihunshi ya ciro kudin ingila cikin envelope yace “ungo wannan! kije kiyo tsaraba kafin na dawo ai bakyazo ki tafi baki siya komai ba! daman kudin sallamar Mahmud da Zainab ne na ciro su dazu zan basu idan zan tafi! toh sunyi wa kansu na fasa bayarwa ungo na Mahmud ki kashe, ita kuma na Zainab nai sadaka da su a hanya!” na saki murmushi sannan na mishi godiya! Dada dai Dariyarta kawai take nidai na mike da kudadena na shiga daki ina jin kaunar Daddy na kara habaka cikin zuciyata! Allah baisa zan rayu da mahaifina ba amma na tabbata da ace yana raye ba zan samu so da kulawa sama da wanda nake samu a wajen Daddy daga wajenshi ba! 

wai sai lokacin naji inajin yunwa amma sai nace na shiga restaurant naci tunda ai yau ni Don ce! cin abincin gida ma bai kamani ba!

zama nayi nayi sabuwar kwalliya nayi make up mai kyau sannan na ciro sabon bootcut trouser dina maroon  nayi tuck in da farar shirt shaka shaka! na dora bakar jacket dina ta dazu! nayi bala’in kyau musamman lips dina da ke ta shekin maroon din jambakin Mac! na saka dan hijab iya wuyana shima fari. sannan na saka envelope din kudina da waya cikin channel handbag dina na futo!

Safna na samu a parlour tana yi musu halin nata na wauta! tana ganina ta ware mun hannu dole na karasa ta rungumeni tana wai tayi missing dina! domin kwana hudu bata zo ba tana shiryen shiryen komawa aikinta!

ina zakiji ne? gira na dan daga sannan nace mata “yawo zani ko zaki rakani?” da dariya tace “sosai ma. i’m free let’s go” nayi murmushi ina yaba hankalin yar shekaru a kalla talatin da biyu ta mayar da ni wata cikakkiyar sa’arta. yawancin abubuwan da take ni nake ganin kuruciya da childishness dinta ba ita ke ganin nawa ba! mikewa tayi sambal sai gani na dawo wada don kaina iya rabin cikinta ya tsaya! Ya Mahmud ne yayi gyaran murya tare da cewa “nima zanje duk da ba’a gayyace ni ba” kafin nayi magana ta cafe “oh that will be fun! ka taho mana zakaji dadin jikinka” ni dai bance komai ba har ya mike ya shiga daki. mintina biyar ya futo ya dora jacket har guiwar shi mai kauri beige akan bakaken kayanshi! da scarve din shi na alkawari ya nade wuyansa da shi! sai ya rikide ya koma black american! tabe baki nayi naiwa su Dada sallama wadda take ta faman harare harare saboda Safna! nidai ban tsaya sauraren komai ba na tafi! inaji Mami na cewa Ya Mahmud ya kula kar muyi yawo da shi cikin sanyi! kamar wani yaron goye!

Da muka futa ma ita kadai ke faman surutunta kamar aku har muka isa Hakkasan restaurant don cin abinci!

muna zaune duka aka aje mana abubuwan da muka bukata! Ya Mahmud Milkshake ne kawai a gabansa domin yaci ya koshi a gida! ko da ina cin komai amma sam ba zan iya cin jagwalgwalon da Safna take ci tana santi ba! balle kuma Ya Mahmud da kallon abincin nata ma kadai irritating shi yake yi!

muna ci mun yar hira har muka kammala! Daga nan Westfield shopping center muka wuce! Nan na bude bakin jaka nayi ta jidar kaya musamman idan na tuna a jirgin Daddy ne bana bukatar takatsan tsan din kaya zasuyi yawa sai naci gaba da siyayyar! ina cikin duba turaruka naji mutum a gefena! “Ni me za’a siya mun? don in gaskiya za’a bi ma raba mana kudin nan zakiyi dai dai tunda nawane akai murdiya aka baki” Ya Mahmud ke magana! nayi murmushi domin hausar tashi wata iri yake yi indai zaiyi magana mai tsayi sai ka gane shi din ba bahaushe bane! a zuciyata kenan!a fili kuwa cewa nayi “ka dauki turare guda daya amma ba mai tsada ba gaskiya” murmushi yayi sannan ya girgiza kai ya wuce yana cigaba da duba turarukan wadanda sukai masa ya kwasa! a raina nace “kasan wanda zai biya maka wannan bill din amma bani Zahra ba” sai da muka kammala akayi total din kudin turaruka ido ya raina fata don da nashin da nawa da na Safna wacce bansan lokacin da ta debo nata ba kudin sun fi kudin da nake takama ina dasu!

kwalalo idon da nayi ne ya baiwa Ya Mahmud dariya ya girgiza kai kawai ya ciro katinsa aka zare kudaden daga ciki! sannan nayi wata ajiyar zuciya ta relief! mun dade muna yawo da siye siye kafin Mami ta taso mu a gaba da waya lallai mu dawo saboda Ya Mahmud bai gama warwarewa ba!
Nan muka shigo mota muka taho a gajiye! muna isa Safna tai mana sallama ta wuce gidansu cikin murnar siyayyar da Ya Mahmud yayi mata kamar yar karamar yarinya! mu kuma driver ya tayamu kwasar namu kayan zuwa kofar gida! Na daga hannuna zan danna kararrawa kenan Ya Mahmud yayi gyaran murya tare da kiran sunana!
juyowa nayi ina kallonshi sai naci karo da wata serious face mai kwarjini har naji na kasa jure kallonshi! cikin nutsuwa yake cewa “Zara kiyi hakuri kiyi zamanki kar kice zaki bi Daddy kinji? Mami ba zataso ki tafi ba! ke kike ganin kamar bata damu da ke ba amma can kasan ranta komai naki a lissafe take dashi! Mami tana da kawaici sosai kuma ba saboda nine take miki haka ba saboda Dada ne! tana ganin idan ta cika shiga lamarinki tana kulawa da ke Dada zatace tayi rashin kunya kingane? but your Mami loves you soo much! more than anyone can ever explain to you Zara! nida kike kishi is your blood brother Zara! Mami bata fi sona ba akanki! tana kulawa dani ne saboda halin da nake ciki kingane?”
jikina ne yayi mugun sanyi domin kalamansa sunyi bala’in tasiri a zuciya da gangar jikina! sosai tausayinshi ya kamani da kuma kunyar abinda nayi idan nayi la’akari da cewa Mamin fa tawa ce,mahaifiyata mai tsayuwa akan duk lamurana! shi kuwa fa? a rashin soyayyar uwar ya sanya Mami rungumarshi ta bashi kulawar da yake bukata! shin banyi son kai ba kuwa? har na iya kallon idon Daddy na gaya mishi haka? sai naji kunya da rashin kyautatuwar abinda nayi ta kamani! kaina a kasa nace “kayi hakuri Ya Mahmud! i was so selfish! banyi tunani mai nisa ba na yanke hukunci! kayi hakuri!”
murmushi yayi tare da dafa kafadata! “na fahimceki! i just want you to put something at the back of your mind cewa Nidin ba stranger bane a wajenki Yayanki ne blood brother dinki who is ready to protect you and make you the happiest sister in the world, who will always give you support and a shoulder to cry on! so ignore kowanne feeling dake tare dake a kaina ki mayar da kanki aminiyata kinji?”
ya karashe maganan yana daga gira! nayi murmushi! hannunshi ya cire daga kafadata ya miko mun yana murmushi “friends?” ya fada! na mika mishi nawa hannun mukai musabaha nace “friends” duka mukai dariya kafin na danna kararrawa mu shiga cikin gidan!
Daddy ya dawo yana zaune yana cin Tuwon da akaiwa Ya Mahmud! muka dinga shigo da kaya! duka kallonmu suke har muka kammala jera kayan muka dawo muka zauna muna amsa Sannu da gajiyar Dada! Daddy ne yace “toh Zara yi maza kiyi parking wadannan kayan in less than 2hours nake so muna cikim jirgi!”
Kallon Ya Mahmud nayi shima ya kalleni tare da mun magana da ido!
sai na gyara zama nace “ahhmm! Daddy ai tafiyar nan……” na sake kallon Ya Mahmud muka kyalkyale da dariya! da mamaki duka suke kallonmu! Daddy yace “ah ah!! tafiyar nan me? wanne sabon al’amari ne kuma wannan?” Dada ta shanye ragowar kunun ta ta dubi Daddy tace “nima dai abinda nake son ganewa kenan! wacce gulmar ce kuma ta tashi tsakaninsu?” cikin dariya nace “Dada gulma kuma?” tace “toh meye in ba gulma ba? kun tashi zaku tafi ya biku yanzu kuma kun dawo kuna magana da ido kuna dariya bayan rikicin tafiyar da bada kudin siyayyar duka akan Mahmud din kikayi!”
tabe baki nayi nace “toh Dada daman dai so kike kiga muna fada ko? toh kwantar da hankalinki mun shirya kuma na fasa tafiya” Dariya suka sa gabadaya! cikin jindadi Daddy yace “wato hakane Zara? toh ni bari nayi ta kaina kan gulmar ta dawo wajena!” duka mukai dariya! daga nan Daddy yayi mana sallama muka rakashi har bakin mota muka dawo!
wannan shine tushen shirina da Ya Mahmud! ya kasance daga wannan rana muna zama muyi hira muyi wasa da dariya! mu fita tare muje cinema muje park! acikin satin Ya Sadik da Ya Omar suka sauka a London tare da matansu Ya sofiya da Ya Anis!! Nan gidan fa ya kacame da farin ciki da annashuwa da nishadi! tuni na manta damuwar da ke damuna na shiga cikin yan’uwana muna shagali! sati daya muka kara a London muka wuce Dubai gabadaya!
ko kwana bamuyi ba Ya Nuratu ta iso itama! wai Allah! i was soooo happy! mun dade rabonda muyi tafiya mai dadin wannan! duk wanda ka duba cikinmu nishadi yakeyi! bamu aiki da sai zaman hira da wasa da dariya idan rana tayi sanyi kowanne ya shirya mu shiga mota mu futa! watarana gabadayanmu wataran kuma kowa ya hade kai da wanda yake ganin ra’ayinsu yazo daya suyi tafiyarsu!+

STORY CONTINUES BELOW

Yau Ranar asabar ce! tun safe muke bacci don jiya ba karamar gajiya mukai ba da mukaje Sharjah! sai yamma na tashi na duba gadon babu Ya Nuratu wadda muke daki daya da ita! ina shirin shiga toilet Amal ta shigo da gudu! na dubeta ina murmushi nace “Amal? ya akai kike gudu haka?” tana dan hakin gudun da tayi tace “Aunty Zara mummy said you should wake up” na fadada murmushi na nace “tell her i’m up” ta juya da gudu ta futa nikuma na shiga wanka! mintina ashirin na kammala shirina cikin palazzo pant mai stripes black and white da karamar boddy hug na dora hat din da na siya jiya akaina bayan na saki gashina baya! sosai nayi kyau ni kaina nayi sha’awar kwalliyar tawa! flat shoe na zura na futo parlour da wayata a hannu!
Dukansu suna suna zaune da alama ni kadai ce na makara! gaban kujerar Dada naje na soma gaisheta sannan Mami sannan Ya Mahmud sannan Ya Sadik sannan Ya Omar sannan Ya Nuratu sannan Ya.sofi sannan Ya. Anis!
Dukansu suka amsa cikin kulawa da jindadi! ina shirin zama naji Dada tana cewa “Zara Babanki fa ya turo da sako ke kina ta bacci” cikin muradin karin bayani nake kallon Dada sannan nace “Wai Daddy? sakon menene Dada?” goronta ta balla ta soma taunawa tana dan basarwa kafin tace “kudi ya turo ta wayar Zainab na siyayyar kayan dakinki yace tunda an nutsu kuma ana nan garin toh kuje duka ki zabi abubuwan da kike so! miliyan ishirin da biyar ne kuma yace idan wani abu ya gaza ayi masa magana” tunda ta soma maganar bakina yayi forming “O” shape idanuna suka furfuto! yayinda kirjina yayi dan banzan bugun da sai da nasa hannuna duka biyu na danne shi! kaina kuwa juyawa ya soma yi yayinda tunanina ya tsaya cak! wata yar balaguron suma nayi ta dakiku kafin na dawo hankalina sosai! idan na fahimci abinda suke nufi da kyau shirye shiryen aurena ake son farawa wanda ya rage saura watanni uku da sati biyu! da Imam! mutumin da na dade da cire lissafin kasancewarsa miji a gareni! wai meye ma ya daukemun hankali ne daga damuwar da nake ciki? meye ya mantar dani halin da nake ciki da plan din da nake shirin fara taku akai? ina hankalina da tunanina suke har na yarda na sakankance kamar banida matsala kamar kowa nabi yan yarima asha kida ana shagalin nishadi dani? meye abunyi? ta ina zan bullowa wannan al’mari?
ji nayi an cika mun baki da pea nut! a sakamakon wangame bakin nawa da nayi kamar wata wawiya! Ya Omar ne da wannan aikin! sam abun bai ban dariya kamar yanda su suke ta yi da kyakyatawa ba asalima furzar da alawar gyadar nayi daga cikin bakina ma mike ina rangaji na shiga daki suna yimun tsiya da shakiyanci irin na cousins! idan banyi batan lissafi ba Ya Mahmud ne kawai bai dara ba! wayarshi ma ya baiwa hankali kamar baisan abinda yake faruwa ba! yayinda Mami taci gaba da hidimar hadawa Dada abincinta a gabanta!
ina shiga dakin na fada gado na fashe da matsanancin kuka! kuka mai cin rai! kuka irin wanda mutum yake yi idan ya tsinci kansa a tsaka mai wuya! kuka irin wanda mutum yake yi a lokacin da ake cewa gaba siyaki baya damisa! kuka na rashin madafa! kuka na rashin sanin menene mafuta? kuka na rabuwa da masoyin da zuciya take so amma girma da darajar amintaka ya sanya zuciyar amincewa da yin bankwana da masoyi domin ta ceto aminiyarta daga cikin matsala! kuka na sadaukar da farinciki da burin da zuciya ta kwallafawa rai!
A hankali naji ana bubbuga bayana alamar rarrashi amma halin da nake ciki na sanyin jiki da zuciya ya hanani dagowa nagane wanene kusa dani illa qamshin Arabian oud mara karfi da yake nunumun cewa Ya Nuratu ce!
da sautin da ita kadai na sani da shi ta soma magana!
“Haba Zara kamar wata yarinya karama? ai an dena wannan kauyancin! waye yake kukan aure kuma yanzu? kefa kika zabi mijinki da kanki Zara? kuma ki kai sa’a kowa yayi na’am da zabin naki! ko ni da aka shiryawa arrange marriage banyi irin wannan kukan ba! ba fa yaune auren ko gobe ba? idan sha’awar zubda hawayen kike ki hakura mana sai lokacin bukin? yanzu kam lokacin shirye shirye ne da tsare tsare! kinga mun samu damar haduwa duka waje daya yanda zaki ji dadin shopping din kayan ki! duk inda kika juya akwai me baki shawara Zara! c’mon sister daina wannan kukan dan Allah mu soma shagalinmu tun daga yanzu!”
ko gizau banyi ba balle na rage sautin kukana! toh Inama naji duk abubuwan da take cewa bayan zuciyata na can ta tsunduma filin tunani? da ace tasan zancenta kamar busar sarewa yake zuwa ya wuce ta kunnena da ta adana kalamanta ko tayi amfani dasu a inda yafi nan dacewa domin ni din gabadaya bana kan layin hasashen da takewa kanta akaina! gajiya tayi? fushi tayi? oho! nidai naga ta lallaba yan matan kafafunta ta fice mun daga dakin! na kuwa gyara kwanciyata naci gaba da kukan haikan!
Dada ce tace su rabu dani! zan gaji don kaina na daina! al’alada nake rayawa don tabbatar da cewa jinin fulani na zirga zirga a jikina! a ranar dai futar da kowa baiyi ba kenan! domin koda Dada tace a kyaleni babu wanda yaji maganarta daya bayan daya suka dinga shigowa suna rarrashina! ganin babu inda kukan zai kain ya sanya na share hawayena na wanke fuskata! “dauko sweater ki dora akan kayanki an soma iskar sanyi sai muje restaurant muci abincin acan mu biyu kadai kinji sister?”
cewar Ya Mahmud da ke tsaye a gefen gadon na jika da hawaye! koda zuciya ta bata sassauta daga abinda nake ji ba atleast ta karbi rarrashin da wadanda suka damu da ita suke mata!da haka na gyara fuskata na saka sweater muka futo ni da Ya Mahmud! ina futowa parlour suka sakamun waka “ta zama ta zama! ta zama dauko wando! ta zama dauko riga! ta zama dauko buta! ” banda Ya Anis da ke binmu sa kallo da sha’wa don har yanzu hausar da take da ita bata cika karamin cokali ba!
juyawa nayi zan koma daki Ya Mahmud ya rike hannuna ya juya ya maka musu harara! duka suka kyalkyale da dariya! “Kar wanda ya sake tsokanarta! idan wani ya sake tsokanarta zan zakulo labarin wani abu na kuruciyarsa na bada labari wanda zai gwammace bai yi tsokanar ba!” da wannan Ya Mahmud yayimun maganin shakiyancinsu ya tasa ni a gaba muka futa!
a kasa muke tafiya iska mai sanyi tana kadawa a dalilin lokacin sanyi da yake niyyar kawo kai!

Sai da muka isa restaurant din mukayi order komai aka cika gabanmu da abinci sannan Ya Mahmud ya dubeni yace “Zara na tambayeki zaki amsa mun tsakaninki da Allah?” cikin rashin fahimta na dube shi nace “kai,,Ya Mahmud ya zanyi na maka karya!” cewa yayi “just answer me! zaka gaya mun tsakaninki da Allah da zuciya daya tambayoyin da zan miki?” yanda yayi maganar babu wasa ya sanyi ni nutsuwa nima don jin abinda yake so ya tambayenin!
na girgiza kai cikin tabbatarwa sannan nace “i promise you zan gaya maka iya gaskiyata”

A nutse ya soma magana! “Zara meye gaskiyar abinda yake zuciyar ki game da Imam?”
a sukwane na dago na kalleshi! domin tambayar ta mamayeni ban kawo wani abu mai alaka da Imamu zai tambayeni akai ba! ganin halin da na shiga yace “look! relax! muci abincin tukunna sai muyi maganar! girgiza kaina nayi na fara tura abincin da gabadaya sha’awarsa ta dauke a raina! tunanin me zan gaya wa Ya Mahmud nakeyi! abinda yake tsakanina da Aisha wani babban sirri ne da duk duniya babu wanda zan iya gayawa! plan din da nake shiryawa kuma tsakanina ne da Rabbul izzati don ko ita Aishar ba zan bari ta san komai ba! toh ta wacce hanya zan bullo? dakyar na dan tsakuri kadan acikin abincin na cire hannuna nasha ruwa! Shima aje spoon din hannunshi yayi ya dubeni “Ina sauraronki! kinyi alkawari tun da farko zaki gayamun gaskiya!”
Jikina ne sanyi harshena yayi nauyi sosai sannan kirjina ya soma bugawa!
sai da ya sake maimaita tambayarshi sannan na soma magana cikin tsananin sanyin jiki!
“babu komai Ya Mahmud kawai dai ina jin banason auren ne kwata kwata!bama da shi ba da kowaye! i’m not ready! i dont want to get married anytime soon”
murmushi yayi yana girgiza kai sannan yace “akwai alamomin tambaya akanki Zara! dole akwai abinda yake faruwa! ko dai kin daina son shi ne ko kuma yayi miki wani abun wanda kike ganin kamar ba zaki iya auren shi saboda abinda yayi mikin ba, ko kuma kin gano wani abu game dashi da bakya fata ga mijin da kike son aura, ta iya yiwuwa kuma shaidanu ke son miki wasa da hankali!! wannan sai nace ki dage da addu’a domin hakan matsala ce mai girma! idan duka babu daya acikin dalilan da na lissafa miki toh lallai ya kamata ki nutsu ki shiga hankalinki domin aure ba maganar wasa bane! abu ne wanda mutum yake tsayawa ya duba wanda ya dace da shi, wanda yake ganin zai dace da rayuwar shi, wanda zai iya rayuwa da shi ta har abada! tun farko kiyi nazari akan wanda kike so, mutumin kirki ne? kinason shi saboda Allah? zaki iya zama da shi a kowanne yanayi? yana da qualities din da ake bukata akan namiji a addinance ba son rai ba? sai kin gama duka wadannan tunanin sannan zaki zo kiyi addu’ar istihara akan Zabin da kikai wa kanki! idan alkhairi ne zakiji hankalinki ya kwanta da shi idan kuma ba alkhairi bane zakiji zuciyarki na miki wasi wasi!
duk wadannan matakan ana binsu ne kafin ace ankai ga kawo kudin aure Zara, ba irin wannan lokacin da ake shirin biki ba! ki nutsu kisan abinda kikeyi babu wanda zai zauna miki dashi ke kadai za’a kai don haka kada ki zabi abinda zaki dawo kina dana sani! zancen baki shirya ba bai taso ba domin duk wani abu a rayuwa ba shirya masa ake ba! idan yazo kawai karbarsa ake domin ta iya yiwuwa lokacin da ka shiryawa abun shikuma  ya dade da yi maka nisa! kin kammala secondary school kin shiga jami’a kuma kina da damar cigaba a gidanshi toh meye matsalarki? fadamun?!! meye exactly damuwarki?
Shiru nayi idona akan plate din abincina ina nazarin maganganunshi! kwarai duk abinda ya fada gaskiya ne toh sai dai abinda bai sani ba ni tawa matsalar tasha bambam da wadda aka saba gani! ni wasu irin kullallun matsaloline masu tada hankali da jefa kwakwalwa cikin rudani da tunani suke fuskantoni! bansan ta ina zan fara ba balle na gane ta inda zan kare wannan curarren al’amari mara kan gado! abinda nasani kawai guda daya ne!shine “BAZAN IYA AUREN IMAMU BA!” ko da kuwa shine autan maza! bazan iya auren mutumin da Aisha take masifar so ba! bazan auri mutumin da ban yarda dashi ba! bansan ta inda zan warware komai ba amma komai zai faru kowanne irin tashin hankaline zai bullo ba zan sauya ra’ayina ba! hajjoji kadan nakeson samowa na hada da wandanda nake dasu a hannuna na yaki auren da ake shirin yimun da Imamu to kowanne hali!
buga teburin gabana Ya Mahmud yayi kafin na dawo daga duniyar tunanina! cikin sanyi yace
“Na lura akwai abubuwa dayawa da ke cikin zuciyarki! ba lallai sai kin gayamun yanzu ba! amma ko yaushe kika shirya tattauna matsalarki dani toh kofa a bude take! ki nemeni a ko’ina nake zan zo na saurareki na kuma taimaka miki da karfina da shawarata da duk abinda zanyi amfani dashi wajen nemo miki yancinki! abinda kawai nakeso dake shine ki daina wannan damuwar da tunani domin kina tayarwa da Mami hankali! ba lallai ta futo ta bayyana miki ba amma zatafi kowa shiga wani hali idan ta gane bakyason auren nan ba tare da wani kwakwkwaran dalili ba! Dada kam kinfi ni sanin halinta  karki sake wannan maganar tayi zurfin da zata hadaku fada! domin abun bazai miki kyau ba ko kadan! idan har kina da matsala Zara ki gayamun tun yanzu ba sai lokaci ya kure ba! na miki alkawari zan tsaya naga cewa kin samu duk abinda kikeso indai ba son zuciya bane! karki sake Zara ki bar wani abu a ranki da niyyar zaki iya warwarewa ke kadai, saboda ke yarinya ce! bakisan rayuwa ba bakisan rikicin da ke cikinta ba don haka na dauko ki nan naji damuwarki saboda aure ba abun wasa bane!
Ajiyar zuciya nayi! sannan na dube shi nace “Nagode da kulawarka Ya Mahmud kuma insha Allah zanci gaba da addu’a kamar yanda kace! sannan idan akwai wata matsala zan sanar da kai da zaran hakan ya taso” murmushi yayi yace “very good!” daga nan muka bar maganar muka tashi muka futa daga gidan abincin!+
STORY CONTINUES BELOW

Tun daga lokacin kullum da nazarin maganganun Ya Mahmud nake kwana nake tashi ina tattauna su a zuciyata! kwarai nayi matukar kokari wajen hadiye damuwar da nake ciki duk da hakan shine abinda yafi komai wahala a rayuwar duniya! boye damuwar da take ranka cikin iyalinka da masoyanka kayi pretending kamar babu komai mara dadi a tare da kai! Tun daga wannan ranar bamu zauna ba! shopping muke haikan na kayan gida na alfarma!
kasancewar banason abubuwa masu hayaniya da kyale kyale ya sanya komai nawa english ne! babu kala kodaya mai kama ido! kuma babu ko abu daya royal! komai inason shi simple,elegant and classy!
yauma kamar kullum ina cikin bacci Mami ta shigo ta tasheni! na bude ido da kyar domin ban samu nayi baccin ba kasancewar ina shan matukar wuya kafin bacci yayi masarar daukata da daddare!
“wai ke wanne irin bacci ne wannan Zara? karfe hudu na yamma kina kwance tun safe? toh amma kinsan inda zamuje dayawa ko? ga Laila tun azahar tazo ke kina nan kina aikin bacci! toh maza tashi ki kimtsa ki futo”
ko amsata ba ta jira ji ba ta juya ta futa! jin cewar Aunty Laila tazo ne ya karfafa mun guiwar saurin dira daga gadon na fada toilet ina murna domin zuwan A.Laila! ita kadai tak Mami ta mallaka a matsayin yar’uwa shakikiya! tana can kololuwar America da zama tare da mijinta! yanayin aikin mijinta ya sanya sukan shafe shekaru biyar zuwa sama basu zo Nigeria ba! yayanta biyu Ayman da Alwan duka suna jami’a a kasashe daban daban! ta hanyar kafofin sada zumunta na saba da A.Laila da kuma wani lokaci da mukaje Los Angeles din wata rashin lafiya da Daddy yayi akai mishi aiki. A.Laila mace ce mai tsananin kirki da karamci, tana da far’a da son mutane sannan tana sona sosai! bana daukar lokaci mai yawa nake amsar sakonninta na kaya iri iri kama daga tufafin sawa kayan kwalliyar mata masu daraja da tsada!
Da tunanin A.Laila na kammala wanka na shirya cikin suit na mata dizayin din Armani ruwan jinin kare(maroon)! na dora dan karamin farin hijab a kaina na futo!
da gudu na isa wajen A.Laila na rungumeta ina dariya! itama rungumeni tayi tana cewa “masha Allah daughter ta kusa zama amarya” zakayi mamakin yanda hausar A.Laila bata baci ba duk da zaman turai da takeyi shekara da shekaru! cikin murna nace “A.Laila i’m so glad you are here!” murmushi tayi tace “ya za’ai nayi missing siyayyar kayan auren diyata? ai dole na taho” bata fuska nayi nace “au daman abinda ya kawoki kenan?” duka falon suka soma dariya! Ya Omar ne yace “haba Zara zaki balla mata kafa mana ko dan ta miki kawaici bata ce ki daga ba! jibgegiyarki dake ki zauna mata saman cinya babu ko kunya” sake bata fuska nayi na dubi Ya Anis nace “Ya Anis will you please handle your husband?” dariya taci gaba da yi domin zuwa yanzu kowa ya gane mugun yar tsamar da ke tsakanina da Ya Omar! kullum sai munyi fada kamar wani sakona!amma kuma daya bai jin dadi idan dayan baya nan! idan ni ban tsokane shi ba toh lallai shi sai ya sami hanyar da yabi ya tsokaneni mukai fadan! yanzun ma bai ishe shi ba sake cewa yayi “Ke dai ji da kanki da iyayinki! anaso ana kaiwa kasuwa!Aunty Laila bari kiji! ana fara maganar biki zata fara kukan jin baki! irin bata so din nan su kuma suna wani rarrashinta! hmmm! don ma ya rufa miki asiri zai aure ki? gaye kyakykyawa fari sol dashi me zai yi da ke! amma sai ki dinga wani basarwa in anzo siyayya kina nokewa su kuma da basu san dawan garin ba suna lallabaki! toh A.laila kada ki dauki wannan sakarcin wallahi duk bula ce! A ranta ji take kamar ta janyo lokacin”
Wata muguwar harara na watsa masa sannan nayi murmushin takaici ina kallon yanda su A.laila suke kwasar dariya! mikewa nayi daga cinyarta na zauna sosai akan kujera sannan nayi tagumi! don iya kulewa na kule! Ya Mahmud ne ya dubi Ya Omar da warning eyes sannan ya maida kallonsa ga wayar da yake ta faman dannawa tun zamansa!
Ya Omar ya sake cewa “A.Laila ai ba zaki gane son da yarinyar nan takewa Imam ba sai yayi tafiya zai dawo! idan ta tashi hankalin gidan nan da girke girke kowa a unguwa yasan za’ai bako! wasu dishes din ma ni a film kawai nake ganin irinsu amma sai taje ta zakulo ta koyo tayi masa! shimuma ya zauna ya bude ciki ya dinga loda  ga banza ta fadi”
aka sake kashewa da dariya! mikewa nayi na soma tafiya zan shiga daki naji gyaran muryar ya Mahmud! na dan juyo! cewa yayi “ya gama nashi it’s our turn! dawo ki zauna” murmushi nayi na koma inda na taso na zauna ina jiran me Ya Mahmud zaiyi! gyara zama yayi ya soma koro jawabi daya bayan dayaa
“bari na tariyo muku kamar shekaru ashirin da shida baya! Lokacin muna Adamawa akwai wata yarinya dake kawo………”
wani tsallen albarka Ya Omar yayi ya dira a gaban Ya Mahmud ya hada hannunshi biyu yana cewa “don Allah ka rufamun asiri! don’t do this to me! please not here! not this time”
Dukanmu da muke wajen dariya muke muna karawa saboda yanda Ya Omar ya tsuguna yana rokon Ya Mahmud akan kar ya bamu labarin da yake shirin fada! sai da Ya Mahmud ya gama jan ajinsa sannan yace “toh shikenan! na rufa ma asiri! Amma kasani, duk lokacin da ka sake tsokanan Zahra nine zan tare mata” wani sign din relief ya Omar ya saki sannan ya mike ya fuce daga sitting room din muna masa dariya!
Ya Sadik ne ya shigo da sallama amma ganin dariyar da muke yi ya sa shi hadiye ragowar a makogoro! da alamar tambaya yake cewa “tohh! me yake faruwa anan wajen?” babu wanda ya saurareshi da tambayarsa sai dai ya Anis da ta mike tabi mijinta muna sake kyakyata musu dariya!
kafadarsa ya daga cikin ko in kula da amsawar da bamuyi mishi ba yace “Ke Zahra idan kin gama dariyar Imamu yana reception yana jiranki”
Ai tuni dariyar ta tsaya cak! expression din fuskata ya sauya cikin dakiku biyu wani irin mugun bugun zuciya ya kamani! domin Imamu shine least din wanda nake expecting gani a garin nan cikin duka mutanen duniya! last time da mukai magana yana Paris ne fa! me ya kawo shi? me zan masa? me ya faru? Ta ina ma zanyi welcoming dinshi?!!

hello! I am soo sorry for the late updates! ba’ason raina bane ba kuma ina ja muku rai bane!amun afuwa!

Sabuwar tsokana Ya Nuratu ta samun tana dariya. A.Laila tace “Aw ba dai sirikin nawa ne yazo ba?” Ya Nuratu tace “shine mana A.Laila bakiga sai wani blushing take ba” A.Laila tayi dariya tace “kun dai sa mun yarinya a gaba don Allah ku kyaleta haka! Zara tashi kije kar ki barshi yana ta jira ba dadi”
jikina a sanyaye na mike na zura slippers dina zan futa! cikin daga murya A.Laila tace “ke meye haka? dawo nan!'” na dawo ina mata kallon rashin fahimta! cewa tayi “haka zaki tafi? wannan shigar batai mun ba koma daki ki sauya wasu kayan ki danyi make up mana!to look more presentable!” har zanyi magana Ya Mahmud ya kalleni tare da mun magana da ido! na juya a hankali na shiga daki! abaya kawai na ciro wadda aka watsawa swarosvki stones jajaye a jikinta samfurin Zara Couture na saka! na fente lips dina da red jambaki na fesa turare na futo! “yauwa Masha Allah! Masha Allah!! ko ke fa? oya! maza jeki!” na wuce zan tafi Ya Nuratu tace “kuma ki hawo mana dashi mu gaisa don nasan halinki sai ki iya barinshi ya tafi” ko juyawa banyi ba balle na bata amsa na wuce na futa suna sake mun dariya! sai da na shiga wajen Dada muka gaisa da ita da Mami sannan na futo na shiga lift na sauka reception!
A hankali nake tafiya kirjina yana ci gaba da bugawa har na isa bangaren da aka shirya kujeru don hutawa! zaune na ganshi cikin bakaken suit wanda sukai ainihin futo da kyawun sa! waya yake ta faman dannawa cikin sauri ya bada dukkan hankalinshi akai da alama wani abu mai muhimmanci yakeyi! sai da na karasa dab dashi kamshin turarena ya sanya shi dago ido!
gabadaya hakoranshi talatin da biyu ya wangale yana murmushin da kowa ya san shi da shi a mafi yawancin lokuta! “you are welcome beautiful!” ya fada yana mayar da wayar cikin aljihun wandonshi! zama nayi a kujerar da ke gefen tashi ina cewa “kai zanyi wa sannu da kazo yau! ba ka gayamun zakazo ba! daga Paris ta taho nan?” gyara zama yayi yace “daga Paris London na wuce nayi clearing wasu abubuwa sannan na taho nan! kinganni daga Airport fa na taho nan! dan zaro ido nayi nace “lafiya toh? meyasa?”
murmushi yayi yace “lafiya kalau! i just miss you!” kasa nayi da idanuna inajin wani irin rashin dadi! ban taba son wani ba a rayuwa! Imam ya shigo rayuwata dai dai lokacin da nake bukatar abokin rayuwa sannan yayi wata katuwar nasarar siye zuciyata da kyawawan halayensa da so da kulawa! ranar da na fara ganinsa na soma sonsa!daga lokacin kuma da na gano nagartarsa da saukin kansa sa kulawarsa da tausasawarsa soyayyarshi take ta karuwa acikin raina har nakejin babu wadda ta kaini sa’a a duniya! inason Imamu son da ni kaina nake mamaki don ba taba hasashen zanso wani haka ba! a dai dai lokacin da komai ya yi daidai magana tayi karfi soyayya tayi zurfi tsanina dashi a lokacin wannan babban al’amarin ya kunno kai! ashe wai Aisha na da irin burin da nake dashi akan Imam cikin ranta tsayin lokaci! Ita kuma Aishan wata mutum ce a rayuwata wadda banajin akwai abinda ba zan iya sadaukar mata ba komai girmanshi komai son da nake masa don nayi imani itama a shirye take! da taji ina neman abinda take da iko da shi ta dauka ta bani ko kuma ta nemo mun shi duk inda yake! ko kuma ta tayani nemanshi a ko ina yake! to ya zanyi da wannan babbar kaddara da kunno mun kai! inaji ina gani zan hakura da abinda nafiso domun farin cikin yar’uwata, aminiyata Aisha!
“hellooo! are you okay?” Imam ne ya katseni! da sauri na dago ina cewa “babu komai! ya kake? yasu Mummy?” yace “suna can Nigeria suna ta shiri” nace “shirin me kuma” murmushi yayi yace “Wanne shirin zasuyi bayan na aurenmu! yanda kikasan gobe ne auren kullum da abinda zasu futa yi! Visar Mummy ce ma bata futo ba da tuni sun tafi America” ji nayi cikina yace wani “kulululu” yaci gaba da cewa “programs din da suke shiryawa wajen kala nawa inaga sati biyu za’ai ana buki! tun daga Pre wedding dinner! tunanina ya za’ai abokaina suzo su kwashe wannan lokacin bayan kowa yana da abunyi” girgiza kai nayi ina sarawa hankali irin nasu Mummyn tashi bana ce hauka ba! kamar wanda ba’a taba biki ba sai a kanmu? suwaye suke da lokacin halartar biki har sati biyu? idan ma mutum ya rasa abinyi da kudi kawai sai ya soma almubazzaranci da su! a fili kuwa daurewa nayi na kalleshi nace “sati biyu ai yayi yawa ina laifin ma sati daya?” daga kafada yayi yace “kema dai kya fada! Mummy ji take kamar ba’a taba biki ba sai akan wannan! duka family ma kowa shiri yake don bamu cika buki ba sai an dau lokaci! bamu da yawa sosai! kusan kowa an mishi aure sai yara masu tasowa! sai su Yasmin!” girgiza kai nayi don naga alamar hakan!
muna zaune muna hira bayan nasa an kawo mana shayi da dan snacks! sannan nace masa ya hawo ya gaida su Dada! cewa yayi “Haba! da wannan shigar? bakisan ba’a zuwa gaban surukai da kananan kaya ba? surukai ma irin na Hausa Fulani” cewa nayi “me kake nufi toh? ba zaka je ba kenan?” fadada murmushi yayi yace “Gobe insha Allah zanzo mu gaisa! kinga yanzu ya kamata naje hotel na kai kayana na huta ko? driver na waje tun dazu yana jirana!” ajiyar zuciya nayi sannan nace “toh meyasa baka fara zuwa ka huta ba sannan kazo gabadaya?” cikin sauri ya amsa “saboda na kagu nazo naganki” nayi murmushi kawai! da haka na rakashi bakin mota ya shiga ya tafi! ina shigowa ciki na gamu da Ya Mahmud zai futo! cewa nayi “La futa zakayi?” kallona yayi a nutse yace “gani nayi shirun yayi yawa na sauko nagani” da murmushi nace “Ya Mahmud kamar wanda zan bata?” shima murmushin yayi yace “ba zaki bata ba! yana ina ne? daga ina kike?” cewa nayi “ya tafi! rakashi nayi” rage far’a yayi yace “meyasa baki hawo dashi sun gaisa dasu Dada ba? me yasa kike hakane Zara?” cikin sanyi nace “Laaa Ya Mahmud wallahi na gaya mishi ya hawo su gaisa yace ba zai iya shiga wajensu ba da manyan kaya ba sai gobe zai dawo” wani irin murmushi hade da smirk Ya Mahmud yayi sannan yace “Imam din ne yace ba zai iya wajen su Dada da shigar kananun kaya ba?” yanda yayi murmushin da maganar sai naga kamar akwai wani da ya sani akan Imam yake boyewa! a hankali nace “Ya Mahmud please me ka sani game da shi? na lura shima kamar yana boye wani abu a tsakaninku ko dai kunsan juna ne?” nutsuwa yayi yace “Ni da nake London shi yana Nigeria how do you expect me nayi mishi sanin da ke baki masa ba? a ina zan gan shi?” cikin zuciyata nayi tunanin kuma fa hakane! amma meyasa idan sun hadu Ya Mahmud ke mishi wani irin kallo! shikuma sai naga Imamun yana wani sunkuyar da kai yana basarwa wanda ke nuna alamun kamar akwai wani abu a tsakaninsu? ajiyar zuciya nayi na bar tunanin domin na kasa gano amsar tambayata! “tunanin me kikeyi?” girgiza kaina nayi! ya wuce gaba muka koma ciki!
kujerun da muka taso da Imamu muka koma muka zauna kafin order abincin da Ya Mahmud yayi daga restaurant yazo! sannan muka shiga lift zuwa suit din da muke!
gabadaya sun sake yin wata da’ira a falon harda Dada da Mami an baje kayan abinci a tsakiyar falon ba’a bude ba!
Daure fuskata nayi tamau don kar su samu damar tsokanata amma sai da Ya Nuratu ta mike tana wani kalle kalle! ya Sadik yace “ke kuma leken me kike?” cewa tayi “sirikin namu nakeson gani? ko ba zai zo ya kwashi gaisuwa ba?” cewa nayi “gashinan hawowa ki shirya” ta zata dagaske nake tai maza ta dauko air freshener din “Aqua” ta feshe wajen da shi tana cewa “Ya Sofi ku taso mu tattara kayan abincin nan mu gyara wajen! Ya sofi da Ya Anis har da Ya Omar suka shiga tattara kayan abincin suna mayarwa dinning! Ya Mahmud ya koma gefe kawai yana murmushi! sai da komai yayi tas kowa ya kame a inda ya dace dashi sannan tace “toh ki koma kiyi masa magana mana” na juya ns futa kamar gaske! sai dai a maimaikon kiran nashi sai na shiga kitchen na debo mana plate da su lemo na dawo!
A.Laila ce tace “yana ina? ” Ya Nuratu ta sake gyara zaman mayafin abayar da ta nade kanta dashi tace “Malama kice masa ya shigo kin barshi yana jira yau naga shashashar Amarya! haka akace miki anayi?” murmushi nayi na shimfida ledar cin abincin hannuna na aje paper bags na abincin mu nace “Ya Mahmud zai huce” Dada da ke can cikin falon daga gefe da Mami da A.Laila ce tace “bafa wani Imamu da zai shigo! tunda ta ba Nuratu amsa nasan karyane ba shigowa zaiyi ba! shakiyancinta ne kawai ya motsa” Ya Mahmud yayi murmushi yace “Dada kin lakanci halin tsokanar Zara da kyau” bansan lokacin da na kalli su Ya Nuratu na kyalkyale da dariya ba! da gudu ta taso zata kai mun duka na koma bayan Ya Mahmud ina mata dariya!
kareni yayi yana ce mata “Babu abinda zaki mata! kullum da dadi kuke sata a gaba kuyi ta tsokana? gashinan son gulma da sa ido ya saku aikin banza! shi Imamun ma ya dade a hotel dinsa yanzu!” ba karamun haushi na hadawa su Ya Nuratu ba! haka suka tashi suka sake kwaso kayan abincin Dada na bada labarin ranar da na daukarwa Ya Omar mota na futa bayan yasa an wanke mishi motar zai je wajen Safiyya!+
Washe gari kam ban koma bacci ba! don Imamu yace da wuri zai zo kuma gobe zai tafi! wanka nayi na shirya! muka gyara ko’ina da Ya Nuratu bayan anyi breakfast! sannan Dada ta futo! duk muka hallara a babban parlour kamar yanda aka saba! wayata ce ta soma ringing na mike na shiga daki har Ya Nuratu na cewa gashinan yazo! A maimakon Imamu sai naga Aisha! da sauri na daga na kara wayar a kunne!
“heyy bestie! ya kike?” shashshekar kukanta ne ya fadar mun da gaba naji wani irin firgici! “me ya faru Aisha? me akai miki?” bata daina kukan ba kuma batai mun magana ba! “Aisha you are scaring me please! me yake faruwa?” dakyar na shawo kanta ta soma magana cikin kuka!
“Zara Daddy ya hana tafiyata school gabadaya yace bazanje ba” duka idanuna na zaro cikin firgici! domin aibabu wanda yafi kaunar tafiyar irin shi! tun muna JS1 yake cewa Aisha Harvard zatayi! yaci buri mai tsanani akan karatunta toh sai da ya kammala kashe wadannan makuden kudade tafiya saura kwanaki uku zai ce an fasa? dakyar na hadiye yawu nace “Aisha me kikai masa? meye ya bata masa rai? meyasa ya yanke wannan hukuncin?” cikin kuka mai tsanani tace “bansani ba Zara! amma komeye yana da alaka da result din da ya futo na asibiti! bansan me suka ce ba! tun jiya da mukaje karbar result din likita yace na basu waje da ya futo naga fuskarsa ta chanja! har mukaje gida bai cemun komai ba suka shiga daki da Umma! shikenan itama ta shiga cikin damuwa! sai dare Daddy ya kirani yake cemun wai zancen makaranta na hakura sai nextyear in Allah ya kaimu!A madadin haka ya shirya mana tafiya zuwa America! duk yanda naso nayi magana bai bani dama ba yace kawai nabi abinda yace bayason kowanne magana! Zara ya zanyi? meyasa rayuwa take mun haka?ya zanyi da raina? kinsan yanda nake dokin tafiya makaranta na bar kasar nan? wlh ji nake kamar akan kaya nake Zara! banajin dadin rayuwata!

Cikin sanyin jiki na nemi bakin gado na zauna da wayar a kunnena! da tausasawa na shiga yi mata magana!
“Aisha calm down please!ki nitsu ki maida hankalinki! just go out and take a breath of fresh air! kina yi kina cewa Lahaula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem! zaki samu relief! kinga kin fara sarkewa kina magana numfashinki ya soma tafiya ba dai dai ba! relax don Allah! i will call back in 10mins!” cewa tayi “toh” ta kashe wayar! jingina nayi da jikin gadon zuciyata cike da tausayi da kuma tunanin dalilin da ya sanya Daddyn Aisha hanata tafiya karatu a dai dai wannan gabar! sannan me result din likita ya bayyana har ya janyo wannan sauyin ra’ayin cikin gaggawa haka! ko na kira Daddyn Aisha? toh nace masa me? kirana kadai ai ba zai sauya tunaninsa ba balle ya sanya shi ya fasa abinda yayi niyya! gaskiya na tausayawa Aisha matuka domin gabadaya hankalinta da tunaninta da burinta ta dora shi akan wannan tafiya!
wayata ce ta sake ringing na daga cikin sanyin jiki! “Hello beautiful! ina kasa” Imamu ne ya iso! don haka na tashi na yafa gyalena na futo! Dada ce tace “Yazo ne?” nace “eh yana kasa Dada” sannan na wuce na futa!
a reception na same shi cikin wata irin kwalliya kamar yau ne daurin auren! babbar rigar blue black din shedda hilton sai walainiya take! ya dora hular da ta dace! hasken fatarshi ya karbi kalar kayan ainun har ba zakaso ka daina kallonshi ba! gabadaya gefen ya cika da kamshin “Tomford”! cikin murmushi ya taso yana cewa “sannu da saukowa” sanan muka gaisa! daga nan muka shiga lift zuwa hawa na goma sha tara inda suit dinmu yake! daga bakin kofa ya tsaya na shiga! tararwa nayi Mazan duk sun hallara domin da zan futa babu wanda ya futo acikinsu! don haka nayi zamana Ya Omar ya futa ya shigo dashi! kansa a kasa ya shigo har ya zauna akan lallausan farar sallayan da akai spraying daga gefe saboda dashi!
cikin ladabi ya soma gayar da Dada sannan Mami sannan A.Laila wadda Ya Nuratu ta gabatar masa! shi dai ya Mahmud ya dora kafa daya kan daya yana kallonmu irin abun yana amusing dinshi! na rasa meyasa yake wannan abun idan yaga Imamu! duka pride din shi ne yake zuwan masa da wasu expressions masu wuyar fahimta!
mintina goma sha biyar ana gaisawa da tambayar shi wadanda suka kamata a tambaya da aikinshi da lafiyarshi kafin yace zai tafi! envelope ya zaro ya aje gaban Dada yana cewa “kiyi hakuri Dada ban samu tsayawa siyan turare ba” tayi mishi godiya domin ita a tsarin Dada ba’a bata kyauta ta mayar sai dai idan ta rainin hankali ce! Ya sake dauko wani envelope din ya baiwa Ya Nuratu yana cewa ita da su Ya Anis! ita kuwa dakyar ta karba! hannun Amal na rike muka futo dashi nayi mishi rakiya har kasa da cewa gobe zai koma Nigeria kuma ba zai samu daman zuwa muyi sallama ba don akwai abubuwan da suke gabansa masu yawa! nan mukai sallama ya koma mota ya dauko wani madaidaicin jakar kwali ya bani! na amsa nayi mishi godiya don nagaji na daina musu dashi idan ya bani abu domin da fada muke karewa kuma na karba dole! sai da driver yaja motar muka dawo ciki!
Ya Nuratu na ganina tazo ta karbi jakan tana surutu! “mugani! mai aka samo? wato ke bai baki a gabanmu ba sai da kuka sauka!to ai dai zamu ga ko menene” bar mata kayan nayi na koma kujera nayi zamana ba tare da na kulata ba! gabadaya hankalina na ga Aisha da halin da take ciki! sai da ta kwance kullin da akaiwa bakin jakar sannan ta ciro saitin zinare cikin wani irin karamin akwati mai daukar hankali anyi wrapping dinshi cikin jakar gift ja! sarka, dan kunne, bracelet, anklet da zobe! kowanne an sarke tsakiyarshi da harafin farkon sunana! alamun cewa domin ni aka kera su! bayan su sai wata katuwar envelope wadda aka shirya sankararrun yan 100$ guda ashirin! wato dala dubu biyu! “kai! this guy is classy wallahi! wai shin ma ba lefe suke hadawa bane yanzu yake irin wannan hidimar?” cewar Ya Nuratu! Ya Mahmud ne ya bata amsa da cewa “to ai kudin ba matsalarshi bace kila zuwa kasuwar ma yafi masa futar kudin wahala bakiga yace wa Dada tayi hakuri bai samu tsayawa siyan turare ba?” A haka magana kawai Ya Mahmud yake yi! amma nikam sai na dinga jin kamar maganar me harshen damo yake yi! gaskiya ina matukar yakinin cewa akwai wani abu a kasa tsakanin Ya Mahmud da Imamu! to meye shi? kuma meyasa yaki gayamun?kai anya kuwa Imamu bashi da wata boyayyiyar halayya da rayuwa?gaskiya zuciyata na riyamun akwai wasu abubuwa game da Imamu wadanda bansani ba! ji nayi kaina ya soma sarawa na mike na koma daki na kwanta kwakwalwata na zabalbalar tunanika iri iri!
ban samu kiran Aisha ba sai dare! hakuri nayi ta bata ina kwantar mata da hankali, dakyar na shawo kanta daga kukan da takeyi tayi shiru ta fuskance ni! sai wajen karfe biyun Nigeria muka aje wayar na tashi na dauro alwala na soma nafila kafin na maida sallar asuba!+

STORY CONTINUES BELOW

kwanaki goma sha biyar mukai a Dubai, zuwa lokacin munci karfin siyayyar mu sosai duk da ba’a samu gamawa gabadaya ba! A.laila ce ta soma yi mana sallama ta wuce Nigeria don kare hutunta acan!bayan kwanaki uku Ya Nuratu itama ta wuce Nigerian ganin gida! mu kuma muka wuce Saudi Arabia!Jeddah muka soma zuwa gidan Daddy domin Dada ta huta gajiyarta. Ai muna isa gidan kowa ya samu daki sai bacci domin mun gaji sosai! the flight was sooo tiring and boring! Nidai Ya Sofi ce ta shigo ta tasheni tace kowa yana parlour za’ai dinner! brush kawai nayi na wanke fuskata na saka zumbulelen hijab kan kananun pyjamas din jikina na futo!
Dada ce ta kalleni tace “Zara bansan ranar da zaki rage bacci ba! ace mutum idan ya kwanta kamar gawa duk abinda za’ai bazaiji ba sai anje an tashe shi?in an barki na tabbata sai ki kai gobe kina baccin nan baki tashi ba” murmushi nayi na karasa gabanta na sauya maganar da gaisuwa! ta amsa cikin kulawa! sannan na gayar sauran mutanen falon banda Ya Mahmud da bai futo ba!
Hajiya(takari mai mana abinci) ce tayi sallama! ganina ya sanya ta murmushi duka hakoran makanta jajaye da farare rakwacam suka bayyana suna walkiya! nima mayar mata da murmshin nayi! “Marhaba Zara! banganki ba ina ta tambayarki wajen Dada!” nace “ina ta bacci ne Hajiya mun same ku lafiya?” nan muka gaisa ta jera abincin na tashi bita don taimaka mata! muna matukar mutunci da ita kuma tana sona sosai!sannan mun saba a dalilin yawan zuwan da mukeyi! sai da muka kammala shirya abincin sannan kowa ya taso! sai lokacin nacewa Mami “ina Ya Mahmud?” cewa tayi “ya futa”
Bayan mun kammala cin abinci ban tsaya hira ba na sulale na koma daki! Aisha na kira! lokacin suna airport zasu tafi America! sallama mukai nai mata fatan sauka lafiya kafin na kashe wayar!muryarta wasn’t good!jikina yayi sanyi! sai dai muna ajiyewa wayar Ihsan ta shigo! cikin hanzari na dauka “mutanen thailand! sai yau ake jinki?” (Ihsan tun bayan tafiyarmu itama suka tafi honeymoon! nikam bazan iya irga wuraren da suka je ba! illa dai kawai gabadaya bamu yi waya ya kai sau hudu ba tun tafiyarsu)
cikin gajiya take magana “wallahi Zara ba zaki gane ba! gashi dai hutu mukazo amma nidai ban huta ba! wani mayawacin mutum Allah ya hadani dashi! Faisal bai iya zama waje daya ba kullum da inda zamu je! kafin mu dawo nagama gajiya bacci kawai nakeji! washegari haka zamu sake futa! kan kiyi tunanin wani abu ya sake cewa kwanakinmu sun kare a garin mu soma parking! wallahi nagaji! gida nakeso nadawo!” dariya kawai nake mata har ta kai aya! sannan nace “Duk son yawonki an samu wanda ya kureki kenan?” cikin haushi tace “Faisal is something else” na sake yin dariya! “yanzu dai ina tsuntsun soyayyar taku ya kaiku?” sai da tayi ajiyar zuciya sannan tace “muna airport yanzu haka! karfe hudu na asuba zamu sauka a Jeddah! daga nan kuma sai gida insha Allah” cikin murna nace “wonderful! Yau muka iso jidda muma!” ihu tasa tana dariya! “Thank God! i cant get rid of this human being! i’m soo happy i will see you!” inaji ta cikin wayar Faisal na cewa “who is the human being you are getting rid of?” muka sa dariya gabadaya! sai da aka bukace su sannan mukai sallama na aje wayar! naji dadin zuwan Ihsan domin ina matukar bukatar magana da ita! daganan bacci ya daukeni ba tare da na shirya ba!

Bayan nayi sallah ina cikin wuridi Mami ta shigo! tsayawa tayi na kammala na shafa addu’a sannan na juya nace “Mami sabahul khair” batai niyyar yin dariya ba ga shiga yi! “Zara Allah ya shirye ki” turo baki nayi nace “Mami gaisheki fa nayi! kuma ba ance “when in rome speak like romance ba! da yaren yan garin nan fa na gayar dake” tabe baki tayi tace “bazan iya zaman unending surutunki ba! ki shirya Yayanki ya tafi dauko Faisal da Ihsan a Airport kar tazo ta tarar dake buzu buzu haka! wani tsalle nayi ina murna! Mami dai kawai kallona kawai takeyi tana girgiza kai! watakila kallon haukan kuruciyar da kullum take ganin shekaruna basu wuce su ba take mun! Toilet na fada na barta anan nayo wanka da brush! cikin sauri nayi sassaukan shiga na sauko kasa ina jira! mintina ashirin suka iso! haba wani ihu muka sa muka rungume juna muna tsalle tsalle! Mami ta dubi Faisal tace “Aww itama Ihsan irin Zaran ce?” girgiza kai yayi yana cewa “Mami tama fi Zara wallahi!” tace “toh Allah ya shirye su” bamu damu da maganarsu ba mukai sama muna kankame juna! ashe ihunmu ya tada kowa! Dada da saurinta ta futo ta zata wani abun ne ya faru! Mami tace “babu komai mahaukata muka samu a gida” muka kyalkyale da dariya! dakyar na bar Ihsan suka gama gaisawa dasu Dada muka shiga daki! wanka zatayi kayanta kuma suna kasa nace “kiyi kisa nawa kawai” sai da Mami tazo ta kiramu sannan muka futa yin breakfast! Shima Ya Mahmud da alama yayi mugun missing din amininsa don suma sai da Mamin taje ta taho dasu! bayan mun kammala aka zauna hira har wajen azahar sannan mazan suka tafi masallaci mukuma muka shiga daki! muna idarwa Ihsan tayi bacci duk yanda naso muyi hira na gagara tada ita sai hakura nayi na sauko wajen Hajiya ina tayata aiki!

WASHE GARI

Karo na hudu kenan Mami na zuwa tashina ina cewa tohh zan tashi!kwana mukai muna hira da Ihsan! bani na samu bacci ba sai bayan munyi sallar azahar! lokacin kuma akace kowa ya kammala shirin umra ana sallar magriba zamu futa! amma ina baccin da ke kaina ya hanani ko motsawa!ko sallar la’asar ban tashi nayi ba balle magrib din! haba kawai sai jin saukan ruwan sanyi nayi a jikina jikin roba! wata irin zabura nayi na tashi zaune cikin tsananin jin sanyin ruwan!naso ace wani ne yayi wannan gangancin ya gane kurensa! amma me? Mami nagani a tsaye cikin shirin Umra! dagowar riga farin voil da farin hijab! kawai ji nayi na fashe kuka! don abun ya taba raina dagaske! ita kanta nagane jikinta yayi sanyi kuma tayi danasanin abinda tayi domin duk wanda yayi nasarar sakani kuka a duniya ka kalleshi ka kara! ni da kaina wataran so nake nayi kukan amma bana iyawa! ni da aka tashi yimun tawa halittar ruwan hawaye kadan aka samun don haka kuka wahala yakemun indai ba abu yayi mugun taba zuciyata ba! a maimakon ta rufeni da fada sai kawai ta juya ta fuce daga dakin ta barni ina kyarma!
ganewan da nayi kowa ya shirya ni kadai ce a kwance ya sanya na mike na fada toilet inaci gaba da kukan! cikin azama nake wankan tare da niyyar umra! ina futowa na zura abayar da ke kan jakata domin bani da lokacin nemo haramin nawa acan kasan akwati! ko waya ban dauka ba na futo idona yayi jajawur!
acike falon yake kowa ya hallara! kowanne cikin fararen kaya ko Hijab fari! mazan daure da haraminsu zani da mayafi! Ya Omar ne ya soma cewa “ke kuma meya samu idonki? kuka kikai?”
gabadaya hankalin kowa ya dawo kaina! banza nayi dashi na wuce gaban Dada da ke miko mun hannu alamun nazo! sai da na durkusa a gabanta sannan tace “menene Zara? me akai miki?” cikin shashsheka nace “Dada yau Mami da ruwan kankara ta tasheni a bacci”
Salamu Alaikum my dear readers! idan kunyi hakuri kadan duk zakuga amsan tambayoyin ku! nan gaba kadan zamu gane kan matsalolin da ke cikin labarin da abinda zai biyo baya! inabin komai a sannu ne!
thank you!!”Ashsha! Ashasha!! Ashsha!!! Zainab meyasa zaki tashe ta bacci da ruwan sanyi?” cikin daurewar fuska Mami tace “Dada sau hudu ina zuwa tashinta akan ta shirya idan na futa sai ta koma baccin bayan tasan ana magrib akace za’a tafi” cikin nutsuwa Dada tace “Duk da haka Zainab kar ki kara tashinta a bacci da ruwa ko ba na sanyi ba! Na lura akan Zahra kawai hakurinki yake gazawa, idan da wancan tuzurun dan naki ne kinsan yanda zakiyi ki kareshi” bansan dalilin da ya sanya naji banji dadin kiran Ya Mahmud tuzuru da Dada tayi ba! Mami ce tace “Dada kiyi hakuri ba’a sake ba insha Allah” tace “yauwa! ke Zara ina haraminki kika saka wannan bakin kayan?” a sanyaye nace “Dada suna can kasan jakata ne kar na tsaya bincikawa na bata lokaci” Dada tace “Allah ya kyauta! jeki ki zuba abinci kici kafin motar ta karaso!” a ladabce nace “Dada bari nayi sallah idan motar batazo ba har na idar sai naci abincin” ta girgiza kai cikin gamsuwa! Nikuma na tashi na shiga daki!

sallar la’asar da magriba nayi cikin rashin jin dadin lattinsu da nayi da kuma ruwan da Mami ta watsamun! ina idarwa na sake nade kaina da mayafin abayar na dau yar jakata na zuba tarkacen da zan bukata da wayata na rataya na futo! har lokacin motar ake jira don haka na dira kasa na shiga kitchen na hada tea nasha raina duk ba dadi! ina futowa Ihsan da Faisal na shigowa! sai lokacin na tuna ma da ita!bayan mun gaisa da faisal nace “ke kuma kina ina?” cewa tayi “wallahi pharmacy muka je! babu irin tashin da banyi miki ba ko motsawa bakiyi ba kamar gawa” nace “ko? ai a karshe ruwan sanyi ya tasheni” cikin gumtse dariya tace “ba dai Mami ce ta zuba miki ruwa ba” na maka mata harara tare da fadin “Malama wuce mu tafi kafin na huce haushina akanki!”+

karfe takwas lafiyayyar luxury bus ta iso ta kwashemu zuwa garin Makkah! kowannen mu ya nutsu da duk nutsuwar da yake da ita! Ya Mahmud na karanto “Labbaikallahumma labbaik,Labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda, wan ni’iamata, laka wal mulk, la shari kalak” mu kuma muna bi a hankali! don haka babu batun surutu ko hayaniya!

hakika addinin musulunci addini ne na rahma da tarin baiwa da ni’ima da kwanciyar hankali! addini mai koyar da ladabtacciyar tarbiyya da jinkai da tausayi da karamci da hakuri da kaunar juna da hakuri da juna!

Tafiyar awa daya tak ta iso damu garin Makkah! dukanmu muka futo muka fuskanci masjidil haram da niyyar umra cikin kaskantar da kai ga Sarki mabuwayi wanda bashi da abun tarayya cikin mulkinsa! sai da muka tsaya marasa alwala suka jaddada tasu sannan muka dunguma cikin masallacin! Muna shiga Ya Mahmud ya wuce da Dada cikin wheelchair dinta don yi mata nata umrar! mu kuma muka dauki tamu hanyar!

karfe shabiyu duk mun kammala muna zaune a harabar masallaci muna hutawa! kasancewar gabatowar karshen shekara hutu ya samu garin ya zama a cike sosai don haka ba karamar wahala muka sha ba! sai da muka kammala hutawa muka shiga restaurant acikin Zam Zam tower muka ci abinci! daga nan muka dawo masallaci,

Bamu bar garin Makkah ba sai da mukayi sallar asubahi sannan muka dawo Jeddah! muna isa kowa ya nemi dakinshi ya sa hakarkarinshi a makwanci domin gajiyar da mukayi!

Nikam ina baccin ina farkawa domin ina fara baccin sai naji kamar Mami zata zubamun ruwan sanyin nan! kai wlh na tsorata da ruwan nan ba kadan ba!ganin bazan iya baccin mai tsaho in peace ba ya sanya na tashi nayo wanka nayi sallar azahar sannan na shirya!

Da na futo parlour shiru babu kowa sai na sauka kasa zuwa kitchen! Mami na hango tsaye tana hidimar girki, Ya Mahmud na gefe gaban tebur yana firar dankali! suna magana kasa kasa da alama wani abun suke tattaunawa!

da sallama na shiga dukansu suka amsa lokaci daya. da alamun tambaya Mami take kallona sannan tace “ke kuma meye ya taso dake yanzun?” a sanyaye na matsa gabanta nace “Mami na kasa baccin ne, ina rufe ido sai naji kamar zaki zo ki watsamun ruwan sanyin nan! nayi nayi baccin baizo ba sai na hakura” cikin tausayawa da nadama ta dafani tace “ayyah! I’m so sorry my dear!raina ne ya baci ganin sau hudu ina zuwa tashinki idan nadawo na tarar kina nan kwancen bayan an gaya miki zamu je umra jiyan bansan lokacin da na bude fridge na dauko ruwan ba ” ajiyar zuciya nayi na kalleta nace

“Mami ba sai kin bani hakuri ba na fahimceki !Nima don mun kwana muna hira da Ihsan ne bansamu bacci ba shiyasa da na kwanta na kasa tashi! i’m sorry too” rungumeni tayi tana bubbuga bayana a hankali kafin ta sakeni!

STORY CONTINUES BELOW

Gurin Ya Mahmud na juya wanda ke kallon mu cike da sha’awa yana murmushi! rage tsaho nayi nace “masa’al khair Ya Mahmud” fadada murmushinsa yayi yace “masa’an noor ya ukt kaifa halik?” nace “Alhamdulillah ana bikhair Shukran” yanda nake qaqalo sautin nawa yayi kama da na balarabiyar ya bamu dariya gabadaya! nace “Ya Mahmud ya kamata ace you are fluent in Arabic how comes baka iya ba?” dage giranshi yayi yanamun alamun tambaya. na dora da cewa “Mami fa Hausa Arab take ce maka! yayi dariya yace “and so?” naci gaba “you have to be fluent in Hausa and Arabic! wai Ya Mahmud me yayi spoiling Hausa accent dinka kake magana haka? ba wanda zai ce kai bahaushe ne idan kana magana! kuma rannan ma naji a waya kana wani yare shi ba french ba shi ba spanish ba menene? sannan kuma…..”

Cikin high tone Mami ta juyo tace “keee! spare him from those questions mana! kamar wata parrot kin shigo kin samu a gaba da surutu ba kakkautawa?” pouting lips dina nayi zan tafi Ya Mahmud yace “Mami kyalemu mana! duk zan amsa mata! zo ki zauna kiji” murmushi nayi na dawo na zauna kusa dashi! bayan Mami ta juya bayanta ne ya kalleni cikin rada yace “anjima zaki rakani ki zabomun abayas masu kyau da kuma perfumes ” cikin amusement nace “wow! Ya Mahmud this woman has won your heart iswear!amma fa saidai custom made kasan tsayinta” dasauri ya dora hannunsa kan bakinsa alamar nayi shiru sannan yace “ke ba’a sirri da ke ko? sai Mami taji!” dariyara na hadiye dakyar da na tuno da zankala kokin budurwartashi! “tohm nayi shiru! zamuje! amma you did not answer my question! wanne yare kakeyi rannan me kama da yaren tattabaru kamar me magana da aljanu?” kyalkyalewa yayi da dariya yana rike ciki! da karfi yace “Mami daman haka Zara take ko daga baya ta zama haka?” ba tare da ta juyo ba tace “tama fi hakan tunda can! har yanzu kuma hankali yaki karasowa inda take” dariya nayi nace “Mami wallahi irin compliments din da nake sha akan nutsuwa da hankali zaki mamaki” girgiza kai tayi ta tabe baki “da ko an cuci nutsuwar” Ya Mahmud na kalla nace ” you still didn’t answer my question wanne yare kakeyi?” cewa yayi “Turkish! nace “wow! a ina kuma ka iya Turkish kai da kake London?” gyara zama yayi yace “bakisan acan nayi karatu ba?” na girgiza kai sannan nace secondary?” ya sake kyalkyalewa da dariya! cikin kosawa nace “did you win a lottery Ya Mahmud? komai amusing dinka yake yau!” girgiza kai yayi yana murmushi “no i didn’t win a lottery, i just gat a crazy little sister”

“to ai abubuwan ne duk nake kasa ganewa ni duk ina ina komai ya faru? ko irin dan visiting din nan da ake zuwa ba’a taba zuwa dani wajenka ba! duk yaushe akai haka?” Mami ce ta sake juyowa tace “kina gidan uwaki! toh lokacin da aka haifeki Mahmud na ss2! sai ki gayamun ta yanda za’ai kisan labarin kuruciyarsa” bakina ne yayi forming O shape idanuna suka zazzaro! cikin mamaki na kalleshi nace “wai haka Ya Mahmud?” hade hannayenshi yayi a kirjinshi yace “Mami zatai miki karya?” na sake kallonshi kaina a daure nace “are you this old? ko nifa i’m around 22! innalillahi ya Mahmud kai tsoho ne” cikin sauri ya rarumo chopping board zai kwadamun na mike na zura a guje ina dariya!

“Ihsan ya kike ganin zan bullowa wannan al’amari? kinga har yanzu wayar Aisha a kulle take kuma na kasa samunta a duka social media! me yake faruwa da ita?”

Ni da Ihsan ke zaune a farfajiyar masallacin Madeena kan tattausar dadduma bayan mun idar da sallar isha’i! kwananmu biyu kenan da zuwa Madeenatul Munauwara!

cikin sanyin murya Ihsan tace “Zara gaskiya akwai wani babban al’amari behind all this! akwai abinda yake faruwa mai muhimmanci wanda bamusan da shi ba! I am sorry to say Zara, gaskiya ban yarda da Imamu ba! dan zaman da nayi da Aisha na fahimci kyakykyawan halinta kuma na gamsu da amana da soyayyar da take miki, idan har akwai wani abu a tsakaninsu toh gaskiya sai dai idan daga wajen Imamu ya bullo! kiyi tunani, Aisha ta dade da daina walwala ta sauya daga mai nishadi da tsokanar da muka santa! bansani ba, amma inajin kamar akwai abinda Aisha take boye miki saboda kar ta shiga tsakaninku da Imamu”

shiru nayi ina nazarin maganganun Ihsan! duk abinda ya fada gaskiya ne kuma duk hasashenta dai dai ne idan na cire sirrin Aisha da nagani cikin diary dinta akan ta dade tana son Imamu da kuma musayar sakonni da sukeyi ta kafafen sadarwa harda haduwa wani waje idan hakan ta kama! Sake cewa tayi

“Zara kina ganin ba zaki zauna kuyi magana da Aisha ba kuwa? banaso fa sai lokaci ya kure wata magana ta bullo! aure ba maganar wasa bane, Zara ki fahimceni! ba nufina na sa miki kokonto akan alakar ki da Imamu ba, amma a yanda muka yarda da juna bazan ga abinda zai cutar da ke nayi miki shiru ba wai don kar kiji dadi! A good friend tells the bitter truth! kiyi zuzzurfan nazari da bincike before it’s too late!”

Girgiza kaina nayi a hankali sannan nace “hakane Ihsan kuma kullum kokarina kenan! ba zaki gane halin da nake ciki ba Ihsan! hankalina a tashe yake. Na dade da dorawa Imam question mark. akwai abubuwa dayawa akanshi wanda suka shigemun duhu! gabadaya na rasa ta hanyar da zan bullo na fahimci abinda nake ciki”

kafadata ta dafa tana bubbugawa a hankali cikin nutsuwa take magana “Zara take your time! ki nutsu kibi komai a hankali! sannan ki tsananta addu’a! Allah ya zai bayyana miki komai kuma zai shiga cikin lamarinki ya kawo miki agaji! But you have to be strong!!”

A hankali na sauke numfashi sannan na girgiza kai! haka muka ci gaba da hira har lokacin shiga Ziyara Rawdah yayi muka mike muka dunguma cikin sallama da salati ga fiyayyen halitta Alaihissalam!

Bayan nayi nafila raka’a biyu sai na koma sujjada na sanya goshina a kasa cikin kaskantar da kai na fashe da kuka mai tsanani ina gayawa Allah damuwata tare da kamun kafa da MasoyinSa abin zabinsa Sayyidna Rasulallahi SAW! bangushe ba ina cikin wannan hali har sai da naji lallai a raina bukatuna sun karbu domin babu kokonto anan wajen ba’a nema a rasa! ba’a juya bukatar mai nema!

bayan na idar na koma gefe naci gaba da salati ga Shugaban halitta! Sai wajen karfe daya muka futo kowanne zuciyarsa fess!

a zaman da mukayi a Madeena da Makkah gabadaya ban tsaya shiririta ko bata lokacina ba, na maida hankalina kacokan wajen addu’a! a kullum ina yin dawafi sau uku! bayan sallar asuba, bayan sallar la’asar da kuma cikin dare! bansan nafila raka’a nawa nake ba! idan kuwa na dora goshina a kasa bana sanin mintunan da na dauka sai na dago! kwarai hakan ya sanya mun sanyi da salama da nutsuwa acikin zuciya da gangar jikina! Hakika Addu’a tana dauke damuwa da bakin ciki, tana sanya haske da nutsuwa acikin zuciya!

sai da mukai kwanaki hudu a Makkah sannan na samu Aisha a skype! ajiyar zuciya na saki sannan nace “Aisha kin tsoratani! kinsani a tunani! ina kika shiga don Allah?” itama ajiyar zuciyar tayi sannan ta soma magana “I am very sorry bestie! wannan kwanakin ko? wallahi it was the toughest time of my life! na shiga tashin hankali amma Alhamdulillah! komai ya warware Allah ya kubutar dani!”Shiru nayi kirjina yana bugawa gabadaya zuciyata ta kasa baiwa bakina kwarin guiwar da zai bude ya tambayi Aisha abinda ya faru! sai da taji babu alamun zan tambayetan sannan tayi dariya tace “ohh! Bestie! are u scared? shiyasa ban kira na gaya miki abinda yake faruwa ba wallahi nasan zaki fini shiga wani hali! amma daga hannu ki godewa Allah bestynki ta tsallake rijiya da baya” cikin shock na lashe busassun lebbana nace “Aisha don Allah jinina zai daskare kiyimun bayani ki daina dagamun hankali” dariya tayi sannan tace “kinsan na gaya miki tun ranar da results din asibiti suka futo naga hankalin Daddy a tashe ko? sannan shine dalilin da aka soke tafiyata school?” a kagauce na amsa “eh nasani” taci gaba “Zara ashe wai wani abu suka gani a jinina basu gane ko menene ba! kuma abun ya basu tsoro sosai! shine Daddy yace mutafi America kawai ba tare da ya bari nasan komai akai ba!” sai da mukazo naga an kawo ni asibiti! Zara kullum akwai abubuwan da za’ai mun! tun ina tambaya suna kwantar mun da hankali har na hakura nasa ido na saduda da rayuwa! Ranar da akamun CT scan test kuwa na shiga tsananin firgita da tunani! nidai Zara bansan abinda nake ciki ba sai bayan 2wks! duka result suka futo sannan likitan yake mana bayani dalla dalla abinda suke tunani bashi bane! shi kansa yayi mamakin yanda ma kubuta daga cutar Zara kuma yayi mana murna! sai lokacin da nagane abinda ake nufi, sai lokacin na fahimci ashe a tsakanin rayuwa da mutuwa nake! Sai lokacin nagano dalilin da sanya Daddy janye tafiyar da ya dora burinsa akanta yayi asarar kudinsa! sai lokacin nagane dalilin rashin nutsuwar Umma da kodewar idanunta mafi yawan lokuta! idan na kiraki a lokacin bansan me zance miki ba tunda nima bansan exact abinda yake faruwa ba! nasan hankalinki ne zai tashi sai kawai na hakura nace kila ba zamu sake ganawa ba Zara”+

Hawaye nake wani nabin wani kamar an balle famfo! this time basu jamun rai ba suka dinga tahowa daga can karkashin karyayyiyar zuciyata! Rayuwar Aisha wata aba ce mai matukar muhimmanci a tare dani! i just can’t imagine wani abu ya faru da ita balle ta kai ga mutuwa! innalillahi! Allah karka nunamun wannan bala’i! gaskiyarta da tace idan ta gayamun zan fita shiga tashin hankali! Aisha a rayuwata kamar jinin da ke makale jikin hanta ne! wata irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninmu irin wadda ba zata fassaru ba! bansan cikinmu wanda yafi san dan’uwanshi ba, abinda nasani kawai anan duniya banga abinda bazan iya yiwa Aisha ba komai wahalarsa matukar bai sabawa shari’ah ba! Halin da na shiga bayan tayimun wannan bayanin ba karamar dimuwa da bugun zuciya bane! kawai hasashe nayi abun ya tabbata! sai naji zuciyata ta karye!

shirun da taji yayi yawa ne ya sanya ta busa wayar tana cewa “hello are you there? Zara kina jina?” kuka ne yaci karfina na aje wayar! na mayar da kaina kan pillow nayi kukan da ya isheni na kara harda na farincikin kubutar yar’uwata sanann na mike nayi nafila na godewa Allah tare da neman tsari da kariya akan duk wani ciwo da zai daga mana hankali!

Yayinda Aisha bata gaji da kiran wayata ba, tana katsewa zata sake bugowa! har na shafa addu’ar na mike naje na dauka!

“ohhh bestie kuka? ina dauriyanki da karfin zuciyarki?tun ma ban mutun ba? idan wataran na mutu ya zakiyi?” cikin bacin rai nace “Aisha this is not a joking matter! don Allah mu bar maganar nan! nayi sallah nagodewa Allah! kuma Shi zai ci gaba da tsaremu daga dukkan sharri da bala’i! chapter closed! “

Dariya ta saka mai sauti wadda take bayyanar da zallar farin ciki da nishadi! rabonda naji irin wannan dariyar ta Aisha tun kafin Imamu ya shigo rayuwarmu! sai naji wani sanyi da salama! hira mai dadi mukayi tare da tambayar lokacin da kowanne zai koma gida! suma daga America Saudi zasu taho amma lokacin mun tafi gida! don haka ba zamu hadu ba sai bayan 3wks idan sun dawo Abuja! da haka mukai sallama!

HOME SWEET HOME

satinmu daya a Makkah muka juyo Jiddah! su Ihsan sun rigamu tafiya gida da kwanaki uku sannan muka biyo su daga baya! Bamu koma makaranta ba don ana cikin hutun sabuwar shekara! a lokacin ne kuma su Daddy suka sake tambayar Ya Mahmud idan lallai dagaske yake akan maganar Safna domin asan abinda za’ayi! ko da wasa banyi tunanin Ya Mahmud da gaske zai iya auren Safna ba! nafi aje hankalina akan kawai tayata shirmenta yake yi akanshi! Ga mamakin kowa kuwa sai gashi ya amsa ya kuma tabbatar da yana sonta kuma zai aure ta! ban masa sha’awar mace irinta ba, bama ni kadai ba kowa ma, saidai matsuwar da akayi yayi auren ya sanya aka sa kafa aka take duk wani aibu na Safna aka je aka tambayo masa aurenta! Su Kawu Sulaiman basu bar gidan kakannin Safna da ke unguwar Lamido cresent a garin Kano ba sai da akace an basu!(toh who will say no to a man like Ya Mahmud?) take aka aje musu makuden kudade a matsayin kudin zance da na gaisuwar Iyaye!

sai da yaga komai ya kammala sannan ya soma haramar tafiyar domin hutunsa ya kusa karewa!

Asabar din da ta biyo baya karfe tara alarm ya tasheni domin zamuje da Mami Kano don ta kagu ta gana da sirikanta! ta gansu su ganta!(Yan’ uwan Safna da Aunties dinta)

a gurguje nayi breakfast nayi wanka nayi nafilfilu na sannan na shirya cikin skirt and peplum blouse din super fara sol mai adon ganyayyaki purple! da pattern din atamfar aka kawata dinkin! na yane kafadata da karamin gyale fari! sannan na feshe kwalliyar da turaren Rasasi mai suna “while in love forever” cikin purple din katuwar jakar michel kors na hada duka tarkacena da wayoyina sannan na janyo karamar troleyn da na hada jiya ta kayana na futo!

Wajen Dada na shiga mukai sallama sannan na futa gate na shiga motata!

STORY CONTINUES BELOW

A shirye na samu Mami cikin lafayarta mai kara mata kwarjini! Kayana kawai na ciro daga motata na saka a motarta muka dau hanyar Airport tare da Ya Mahmud da Faisal! Ya Sadik ne ya kaimu sai da yaga tashin jirginmu ya juya!

karfe uku muka sauka a garin Kano ta dabo! muna futowa muka samu Driver Inna Badi’a (idan kun manta itace Autar Dada kuma mahaifiyar Ya Nuratu) cikin zuciyata nake addu’a Allah yasa muje mu rabu lafiya domin Inna Badi’atu wuta ce ba’a rabarta a zauna lafiya! sam bata da kirki musamman gamu da ta dorawa karan tsana kamar ba yayan yan’uwanta ba! hakan ba zai rasa nasaba da kiyayyar da takewa Mami ba! gabadaya Ya Nuratu bata kwaso ko daya daga cikin halin mahaifiyarta ba kuma bata bin ra’ayinta! babu wata shakuwa mai karfi a tsakaninsu ko jituwa tunda daman ba ita ta riketa ba! Wannan ya sanya bana son zuwa Kano ko kadan!

Tafiyar mintina arba’in da tara mai cike da cunkuso ta kawo mu gidan Inna Badi’atu da ke unguwar Sokoto Road! mijin Inna Justice Hassan Koguna shine chief Judge of Kano state! Inna Badi’atu itace mata ta biyu a wajenshi! uwargidanshi da yayansu suna ainihin gidanshi! wannan gidan na Sokoto road Daddy ne ya siyawa Inna Badi’atu shi a sakamakon gajiya da sukai da raba fada tsakaninta da uwagidan nata, duk da cewa kullum za’ai fadan itace bata da gaskiya! sai da aka raba musu gida aka samu sawaba, duk da haka idan aka tabo ta bata kasa guiwa zata dauki mota ta tafi gidan taci mutunci yanda ranta yake so! Yayan Inna Badi’atu tara! Ya Nuratu ce ta fari sannan jerin maza guda takwas!

Da far’a da murna Ya Nuratu ta karbemu tare da mana jagora zuwa babban parlour gidan! sannan tayi serving dinmu da kayan motsa baki! mun samu mintina ashirin a zaune har su Ya Mahmud na shirin mikewa su tafi masallaci ta sakko daga bene cikin kwalliyar da take kara mata jin cewa ita wata ce! sai da gabana ya fadi na karanto addu’ar Allah ya rabamu lafiya kafin ta iso ta zauna tana wani fadi kamar zata ce mu kwanta tabi kanmu!

“Mutanen Abuja Sannunku” abinda ta soma fada kenan! Mami ta amsa tare da dorawa da gaisuwa! ta amsa ba yabo ba fallasa! sannan Ya Mahmud ya gaishe ta, bayan ta amsa tace “ashe kuma ai kai kudi? duk wannan shekarun a ragowar turawa ka tsaya? na zata zaka dauko mana jinin sarautar larabawa?” Baice komai ba amma nan da nan ya cire duk wani annurin fuskarshi ya murtuke ta kamar bai taba dariya ba! sai da na hadiye yawun tsoro sannan na gaisheta!bata amsa ba sai cewa tayi “Amare ansha siyayya ko? sai aka gayyaci laila dake wata uwa duniya tunda ita me kudi ce kuma yar gayu tafi kowa sanin abu me kyau” kaina na sunkuyar kasa ina wasa da hannuna! Mami ce tace “Ba haka bane Badi’a itama tsintar zancen tayi lokacin yayi dai dai da hutu shiyasa tazo kuma ba takanas saboda siyayyar muka tafi ba, Yaya ne yace tunda munje kawai ayi siyayyar! amma idan ranki ya baci kiyi hakuri” tabr baki tayi zata sake wata maganar Ya Mahmud ya mike cikin wani irin daurewar fuska da dakiya ya dubi Faisal yace “taso mu tafi!” sannan ya kalli Mami yace “Mami sai munyi waya” Tuni Faisal ya mike suna shirin barin falon Inna Badi’a tace “Aww ina zakuje? a gadarance ya juyo ya kalleta tsab sannan yace “Hotel!” cikin daga murya tace “wanne irin hotel duk fadin gidan nan da dakunan da suke cikinsa? meye zai kaiku hotel in ba neman magana da halin banza ba” har ya bude baki zai yi magana sai naga ya kalli Ya Nuratu sai ya mayar da kalamansa ya juya kawai suka tafi! Na tabbatar darajar Ya Nuratun taci wajensa da sai ta samu amsa dai dai da ita! ita kam Ya Nuratu kuka ne kawai bata fashe dashi ba, ko ido ta kasa dagowa ta hada da mu! haka mukai zaman gurun gurun kafin Mami tace zamuyi sallah sannan Ya Nuratu ta mike ta jagorance mu zuwa daki! Anan ne ta dubi mami idonta taf da kwalla tace “don Allah Mami kiyi hakuri da Inna! bansan meyasa take haka ba!” murmushi mai ciwo Mami tayi sannan ta dafa Ya Nuratu “meye abun damuwa Nuratu? tare fa muka taso da Badi’a! idan ban fahimci halinta na hakura da ita ba sai yaushe?ko ba komai yar’uwata ce ta jini kinga dole nayi hakuri da halinta! kema kiyi hakuri da ita Nuratu kinji? ki bita a hankali mahaifiyarki ce” tana share kwalla tana girgiza kai sannan ta juya ta futa!

nikam ko bakin magana rasawa nayi! toh me zance?! haka mukai wannan yini da kwana babu dadi! Amal na samu take debemun kewa da surutunta kafin muka kwanta bacci!

Washe gari wajen shabiyu muka kammala shiryawa saboda gudun zuciya Mami tace wa Inna tazo mu tafi amma budan bakinta tace babu inda zataje! sai Ya Nuratu ce ta shirya muka tafi tare! A kofar gidan muka samu su Ya Mahmud domin ya rantse ba zai sake takowa gidan Inna ba sai kwatance yayiwa Driver da ya dauko mu!

Lamido crescent muka soma zuwa ainihin gidansu Baban Safna da kuma mamanta marikiyarta a yanzu! Gidan Family house ne!Kakar Safna ta rasu sai sai kishiyoyinta guda biyu da uncles dinta guda uku da ke zaune a gidan! sosai suka karramu suka kuma nuna farin cikin zuwanmu! bamu dade sosai ba mukai musu sallama sannan muka wuce Korau Road gidan kanwar baban Safna Jamila anan muka samu Shukra da Farida Y’ay’an Engineer! Suma sun karrama mu sosai kuma sunyi farin cikin ganin mu! illa iyaka dai dukansu ni banga mai tarbiyya ba! idan nace tarbiyya ina nufin nutsuwa ta fannin magana, mu’amala da kuma sutura! daga su Faridan har yayar Maman tasu banga na zabi ba! dukansu irin rayuwar turai sukeyi a Nigeria! babu ladabi babu kamun kai! Amma suna da kirki sosai kuma sun iya karbar mutane!

Daga can guest room kuma mazajen su Farida ne da su Ya Mahmud! wanda suka saba a dalilin ita Faridan da matsalar rashin haihuwa ya kai garin London ganin likita inda aka hadata da Ya Mahmud a matsayinsa na Reproductive Endocrinologist! Cikin wata daya kacal suka samu abinda suka dade suna nema! har gashi ta haifi twins dinta sun yi wayo! wannan ne asalin abinda ya hada Mahmud da Iyalin Engineer!!

Amma tunanina me Ya Mahmud ya hango a wannan family da ya bashi sha’awar hada jini da su? meye yagani a jikin Safna da babu shi wajen daruruwan matan da ke kaunarshi? abinda kwakwalwata take ta tunani kenan tun zamammu a falon!

bayan munyi sallar azahar sai da suka tsaremu lallai muci abincin da kukunsu ya shirya mana tukunna mukai sallama da su! har bakin motocinmu suka rakamu suna yi mana godiya da manyan ledojinsu cike da kaya! sai da suka ga futar mu suka juya suna dago mana hannu!

Muna cikin mota naji alamar shigowar sako a wayata ta hanyar dan kidan da wayar tayi! Na futo da ita daga jakata na kunna tare bude email dina don ganin sakon!

Ya ilahi! a take nayi wani mummunan ganin da har abada bazai disashe a idona ba!cikin taki daya idanuna suka juye kaina yayi wani irin sarawa! nayi maza na rufe wayar na saka a jakar ina kiran sunan Allah!

helooo! its been a while! i wasn’t feeling soo good but Alhamdulillah i am recovering!

back to our story! zaku dinga jin sabbin characters cikin labarin tare da dan takaitaccen note akansu kafin lokacin da zamu ji tushen labarin gabadaya! mafari, tarihi da sanin ainihin mutanen cikin labarin tare da alakar kowanne da kowanne! Amma kafin nan, me kuke tunanin an turowa Zara? me yake shirin faruwa? ko asirin Imam zai tonu kafin suyi aure? kuci gaba da biyo labarin kar ku gaji!

WELLCARE,Kano!

Bansan ta yanda akai mukai wannan tafiyar ba naji kawai Mami na cewa a biya ta gidan Alhaji Rabo aminin Abba(mahaifina) mu gaishe shi! ban ankara ba ashe anyi parking zamu koma motarsu Ya Mahmud domin Driver Inna zai tafi dauko yara a Islamiyya! Faisal ne yake tukin Ya Mahmud na gefensa! kamar a saman iska haka nake jina lokacin da na balle murfin motar na futo! muka shiga cikin bakar Jeep din muka zauna kaina yayi masifar nauyi yana ragargaza kamar zai tsage! ban ankara ba naji mun iso gidan wanda shima din yake cikin GRA!+

Duk da na rufe wayar na gaza dauke hoton da na gani kan screen din wayar cikin kwakwalwata da zuciyata! bakina ya gaza daina furta kalmar “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun” i can’t believe this! wallahi i never thought bakin halin Imam zai iya kaiwa haka! Na shiga uku! He is my fiance for heaven sake!! Ya Rabb! take me out of this horrible situation!

Mami ce ta dafani tace “lafiyarki? anzo bude mu futa! cikin tsananin dauriya na dago kai ina runtse jajayen idanuna nace “Mami i can’t go in! kaina kamar zai tarwatse wallahi!” Gani nayi duka su hudun sun juyo da idanunsu kaina! babu tantama yanayina ya bayyanar da tsantar halin da nake ciki. Akan goshina Mami ta dora hannunta taji kuwa zafi rauu don tuni temperature dina yayi sama! “all of a sudden?” inji Ya Mahmud! Mami tace “lafayarta kalau fa da ta tashi! har ma muna gidansu Safna! Sannu suka shiga yimun Ya Mahmud yace “kinga Mami ku shiga bari mu samu pharmacy a samar mata magani! Faisal ina zamu samu pharmacy mai kyau?” cewa yayi “muje Wellcare” Mami ce tace ita zasu shiga da Ya Nuratu muje mu siyo maganin mu dawo! sai da suka shiga Faisal ya juya akalar motar muka tafi Welcare!
Bayan mun hau titi ne Ya Mahmud yace “ina ganin ma ya kamata ki fara blood test, in ban manta kwanaki ma haka kikayi!” ni dai shiru kawai nayi ina binsu da toh domin ni nasan ainihin ciwona ba maganin asibiti ko allura ne zai warkar dashi ba! sai da muka biya wani Lab a Bomfai sukamun gwajin muka tsaya result ya futo muka karba! duka abubuwan da yake tunanin suna damuna negative! Na lura daga lokacin ya dan shiga tunani don sai jefi jefi suke magana da Faisal har mukazo Wellcare!
Su biyu suka futa don cewa nayi bazan iya shiga ba! na gyara zamana a bayan motar ina rike kaina da ke mugun sarawa! ga wani amai da yake tasomun na musamman! waya na ciro na kira Ya Mahmud nace masa ya hadomun da maganin amai don nasan idan na fara babu sassauci! tana shiga na soma jin ringing a motar, ya manta wayar! kawai yanke shawara nayi na shiga na gaya masa duk da ban taba zuwa wajen ba amma nasan bazan kasa gano su ba!
A hankali na bude motar na futo na maida lock sannan na rufe! dakyar nake takawa don tsananin ciwon da kaina yake mun! murda kofar da zanyi na shiga wani tattausan sanyi da kamshi suka daki hancina! “wajen yana da kyau sosai!” tambayar da gefen da zanbi nayi naje wajen maganin nayi! daya daga cikin ma’aikatan ya nuna mun. har na soma tafiya na tsaya cak! a dalilin kamshin da ya cika mun hanci, kamshin Tomford! kuma kamshin Imamu a koda yaushe! Daga idanun da zanyi naci karo da wata santaleliyar budurwa cikin wata irin shiga mara sha’awa wadda bata boye komai na halittar ta ba. what! Jidda? wannan Jidda ce! kawar Aisha! kan na sake cigaba da wani tunanin sai ga Imamu ya rufo mata baya da da uwar siyayyar da suka lodo! Ya hayyu ya qayyum! da sauri nayi kwana na labe ina fidda wani nannauyan numfashi! mintina biyar na sake lekawa suna ficewa daga wajen fuskokinsu cikin annuri da walwala!
Take na tuna hoton da aka turomun dazu a wayata! it is the same girl! wallahi itace!Jidda kawar Aisha wadda ta yarda da ita! Jidda ce a hoton! dimaucewar da nayi ne ya sanyani gaza tsayawa duba fuskar wadda nagani tare da Imamun sosai!
what on earth is happening to me????
Dai dai lokacin Ya Mahmud da Faisal suke tahowa amma me? blurry nake ganin hotunansu a kwayar idona, da sauri Ya Mahmud ya karaso yana cewa “lafiya? meyasa kika shigo?” bude baki nayi ina kokarin yi mishi magana amma ina……wasu manyan taurari nagani suna tartsatsi kafin tunanina ya dauke diff!

STORY CONTINUES BELOW

A hankali na bude idanuna inajin kaina na wani irin sarawa! a kwance nake flat a kasa kaina akan kafar Ya Mahmud daga gefe kuma Faisal da wasu mutanen da bansani ba duka sun rufu a kaina! laimar da naji ta jikamun fuska nagane cewa suma nayi aka zuba mun ruwa na farfado!
“Zara! Zara!!are you okay?” cikin rudewa yake magana. a hankali na girgiza kaina! sannan na tashi zaune ina dafe kaina! ya sake cewa “me yake damunki yanzu?” a hankali nace “kaina ne yake ciwo” Faisal ne yace “kaga ba wannan tambayoyin ya kamata ba mu tafi asibiti kawai” da taimakon Ya Mahmud na taso muka futo na shiga mota! bayan Faisal yaja motar ne Mami ta kira Ya Mahmud taji muna ina shine ya gaya mata abinda yake faruwa sai tace mu taho kawai nasha maganin da ya siyamun gobe mu juya Abuja! Tafi amincewa da asibitin can da kuma likitan da na soma gani wancan rashin lafiyar
Parking mukayi a gefen hanya Ya Mahmud ya ciro ledar abubuwan da ya siyo! kwalin fresh milk ya mikomun na fara sha sannan ya ballomun magungunan na kora da ruwa mara sanyi! cikin kankanin lokaci nayi bacci bansan lokacin da mukaje muka dauki su Mami ba sai farkawa nayi Mami na tashina mun iso gidan Inna Badi’a! Ita da Ya Nuratu ke rike dani muka shiga gidan su Ya Mahmud suka juya akan sai goben zasu dawo!
Cikin mamaki Inna take kallonmu ganin yanda suka rirrikeni gefe sa gefe ina takawa a hankali! mikewa tayi tana salati! “me zan gani? me ya faru?” sai da suka kwantar dani akan lallausan sofan falon sannan Mami tace “wallahi ciwon kai! kamar wasa bayan mun futo daga gidan yan’uwan su Safna! sai Mahmud yace bari suje su siyo mata magani! kamar wasa wai har da suma tayi wajen siyan maganin!” cikin zaro ido Inna tace “suma? kingani ko? kunga irin jajibe jajibenku ko? a garin neman suna zaki kwasowa yarki ciwo! Daman na dade da jin cewa family dinsu mayu ne! nayi shiru da bakina ne don naga ba’asa dani ba! Amma ai ga zahiri yanzu!. daga zuwa an samu wanda ya lashe ta.”
Duk halin da nake ciki bai hanani dago kai na dubi Inna ba! wace irin mutum ce kam ita? haka kawai ki likawa mutane Maita babu gaira babu dalili?kawai don bakya son Ya Mahmud!
Mami kam ajiyar zuciya ta sauke sannan tace “Badi’a babu kyau irin wannan mummunan zargin! ciwo ne kawai daga Allah ya sameta kuma ba yau ta fara ba kwanaki ma tayi wannan ciwon kan har admitting dinta akai a asibiti! inaga shine ya dawo yanzu amma don Allah ki daina yarda da wannan jita jitan na mutane”
wani shegen kallo Inna tayi wa Mami kafin tace “oh haka kikace? sharri nayi musu ko? to ai shikenan. sun lashe miki ‘ya bayan lafiya kikazo da ita lokaci daya ta kwanta amma kice sharri ko? zaki gane zargi ne! Allah ya bamu rai da lafiya” tana gama fadin haka ta mike ta haye benenta tana ci gaba da kunkuni da masifa!
Ya Nuratu ta girgiza kai kawai tana bakin cikin wannan hali na mahaifiyarta! “Mami nima fa jibi zan tafi In Sha Allah!” Mami ta dage gira tace “Ahh jibi kuma?ba sai 15th January ba?” cikin tsananin damuwa Ya Nuratu tace “Mami nagaji wallahi! nagaji da zaman gidan nan! gashi Baba baya nan kullum cikin fada muke da Inna gara na tafi sai hankalina yafi kwanciya sai bikin Zara zan dawo” cikin tausayawa Mami tace “sai hakuri Nuratu! in dai mutum ya haifeka ya gama da kai! dole kayi mishi biyayya ko yaya halinsa yake, kici gaba da hakuri kina binta a hankali”! girgiza kai kawai take tana share kwalla da alama akwai abubuwa da yawa da bata tona ba wadanda suka faru tsakaninsu!
Washegari mukai shirin komawa garin da muka fi wayo wato birnin tarayya! Muna dira daga jirgi Ya Sadik na isowa!sai da ya fara sauke Faisal a gidanshi sannan ya kawo mu gida gabadaya! muna gaisawa da Gwaggo na shiga daki nayi wanka da ruwa mai zafi sannan nayi sallah kafin Baba Rabi ta kammala shirya mana abinci!
sai wajen karfe biyar Mami da Ya Mahmud sukai mana sallama suka tafi bayan Mami ta sanar mun cewa gobe na shirya da wuri zamuje ganin Doctor! cewa nayi “Mami na fa ji sauki ba sai munje ba” kallon baki da hankali tayi mun sannan tace “idan kinji sauki sai me? ciwon da zai dinga sa mutum fita daga hayyacinsa abun wasa ne? karma nazo nayi jiranki na gaya miki!” na amsa da toh sannan suka tafi.

Duk yanda naso bacci ya daukeni a daren na gaza saboda tunanikan da suka cika kaina! Idan akwai relationship tsakanin Aisha da Imam to meye kuma ya kawo Jidda tsakaninsu a matsayinta na kawar Aisha? Itama cin amanar Aishan tayi kenan? Imamu kam na gaza tantance a dabbobi da wanne zan hada shi! yana sona yana son aminiyata yana son kawar aminiyata! ko da yake na dade da tunanin babu wani sona a tattare da shi tantagaryar yaudara ce kawai da cin zarafin yaya mata a cikin ransa. Ana gobe zamu tafi Kano yazo gida yayi mun sallama akan washegari zai tafi Lagos zasuyi clearing wani kayansu da custom suka rike ashe karya yake yi yawon abinda ya saba yi zai tafi! toh inama suka hadu da Jiddan bayan itama a garin nan take? binshi tayi ya dauketa zuwa Kanon ko kuwa a Kanon suka hadu? haka na dinga sakawa da kwanacewa da lissafin da bansan adadin shi ba har karfe uku na dare. bacci kam duk iya kwarewar satarsa bai yi nasarar daukana ba!ko na fara jin baccin ina tuna cewa wata biyu ya rage aurena da Imamu zanji nayi firgigit na farka cikin razana da tsoro! a karshe na mike na shiga toilet na dauro alwala na fuskanci ubangiji domin a halin yanzu daukinshi kadai nake nema akan futa daga wannan tarkon da na fada!
Lokaci yana ta tafiya kullum ina kara cin karo da shaidar da ke tabbatar mun da munanan halin Imam amma nayi tunani kakaf na rasa gane ta hanyar da zan bullowa bijirewar aurensa. wa zan fara tunkara nace na fasa aurenshi? wacce hujja zan kawo? ya zanyi nayi bayanin sa za’a gamsu da halinsa ba tare da na saka sunan Aisha sa na kawarta a ciki ba? Idan kuwa har nayi shiru na tabbatar zan tafka babban kuskuren da ba zan iya gyarawa ba nan gaba! Auren mutum irin Imam dai dai yake da fadawa ramin da bashi da iyakar zurfi!
Haka na kwana tunkur ban runtsa ba wanda ya haifar mun da ciwon kai na gefe daya! bayan nayi breakfast na samu nasha paracetamol na kwanta! koda banyi bacci ba nasamu ciwon kan ya dan ragu sannan na tashi nayi wanka na danyi light make up din da zai boye kumburarrun idanuna da damuwar kan fuskata.nayi sassaukar shiga na fesa turare sannan na zauna jiran isowar Mami.
Ko shigowa batai ba tayimun waya na futo gana gate! na shiga wajen Dada nai mata sallama sannan na futo muka dauki hanyar asibiti! tsorona Allah tsorona abinda zan gayawa likitan yana damuna musamman idan wannan dan jaridan muka samu mai bin kwakwkwafin tsiya! sati biyu ya bamu mu koma wancan zuwan bamu koma din ba shima dakyar na tserewa tambayoyinsa masu wuyar amsawa kafin ya sallameni. Ban ankara ba ina tunani har muka zo asibitin. cikin sanyin jiki da fargaba na balle murfin motar na futo muka shiga asibitin Mami na rike da hannuna kamar wadda in ta sakeni zan gudu!

Mami rike da hannuna muka shiga consulting room din! ina saka idanuna a dakin suka dira kan Dr.Sherif! addu’ata bata karbu ba. a hankali nake takawa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki har muka isa kujerun da aka tanada don patient muka zauna! babu bata lokaci Mami ta kwararo mishi bayanin abubuwan da suka faru! BP dina ya soma gwadawa sannan heartbeat! ya kalli Mami yace “Mama ko zaki ban bamu minti biyar?” kallona tayi a nutse sannan tace “babu komai Doctor” ta mike ta futa nabi bayanta da kallo! ina juyawa muka hada ido da Dr.Sherif! na kawar da idona a hankali! kafin ya soma mun magana cikin ruwan sanyi fararen incisors(hakoran gaba) dinsa duka suka bayyana suna sheki suna haska bakar fatar fuskarshi! kome yakewa hakoran sukai wannan farin Allah masani don da hakoran nashi da farar wankakkiyar labcoat dinshi bansan wanda yafi wani haske ba!
“Miss or Mrs Zara?” nayi maza na daina kallonshi nace nace “Miss”
da dan high tone yace “Nooo! look at me! yanda idan kinmun karya zan gane!”
yanda yayi maganan ya bani dariya sosai amma banyi ba!
“Yanzu gayamun a shekarunki guda ashirin da biyu a tunanina matsalarki mai girma bata wuce ta zaban kayan da zaki sa acikin wardrobe dinki ba, ko kuma kalar jambakin da zaije da kwalliyarki ko kuma gyalen da zai kala da kayanki! Idan matsalar tayi tsamari ta zama kin jefar da IPhone dinki screen ya fashe, ko kuma hoton da kika dauka jiya ya goge? “
Bansan lokacin da na soma dariya ba ba don kalaman da yake amfani da su ba illa rainamun shekarun nawa da yayi har yake ganin wadannan sun isa matsaloli a wajena!
pouting din lips dinsa yayi yace “i am not joking Madam” Ya salam! this guy is adorable!! na fada a zuciyata. cikin nutsuwa yaci gaba da magana
“Duka dai babbar matsalarki wadda zata daga miki hankali bai wuce zuwa wajen tela amsar kaya ki tarar bai miki ba! ko a samu sabani dinkin bai miki wanda kike so ba? uhum? toh duk wadannan matsalolin ko lokaci daya zasu faru tare sun kai ace jinin mutum ya hau saboda su?”
a hankali murmushin fuskata ya dinga raguwa har ya dauke cif! “hawan jini?” na maimaita!
“Yes jininki ya hau! a yan shekarunki! wanne damuwa kika sa ranki? meye kika nema kika rasa? gayamun?”
a sanyaye na girgiza kaina. “Noo you have to tell me otherwise zan gayawa Mamanki komai!” shiru nayi ina nazari. nace masa me? wanda zan aura dan iska ne? ko kuma aurena nake so a fasa? ko kuwa wanda zan aura ne yake son aminiyata? banga wanda yafi saukin fada ba! don haka sai nace “ciwo ne dai daga Allah amma ni bani da wata matsala” murmushi yayi sosai sannan yace “kin dauka zaman da nake akan kujerar yau na fara shi? kin gama tunanin kakaf ba zaki iya fadin mini matsalarki ba sai kika zabi kice babu komai ko?” shiru nayi bance komai ba!
“Look you have to tell me this Miss Zara!ko auren dole za’ai miki? murmushi nayi na girgiza kai! ya sake cewa “are you in a relationship?” na daga kai tare da cewa “aurena saura watanni biyu” yace “wonderful! ok fada kukayi da fiance din naki ko kuma events din da za’ayi na bikin ne sukai miki kadan kikeso a a kara?” sai da na danyi nazari sannan nace “Inaga dai stress ne da yawan zirga zirga akan shirye shiryen bikin ya janyomun ciwon kan” sosai ya tsaya yana kallona kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ya shiga rubutu!A nutse yace “bari mu barshi akan stress din ne kamar yanda kikeso zuwa sati daya! idan har stress dinne kika dawo zan gani, idan kuwa banga chanji ba toh ki shirya bami cikakken labarin matsalarki! bai tsaya jin ta cewa ta ba ya mike da kanshi ya leka yayi kiran Mami ta shigo!
a kagauce tace akwai wata Matsalan ne Doctor? me yake faruwa? a nutse ya soma magana “Mama ina ganin stress ne yake damunta so ya kamata ta samu hutu sosai da bacci ga drugs din da zatai amfani da su zuwa sati daya mugani insha Allah zata samu sauki!” ajiyar zuciya Mami tayi sannan tace “Doctor sau biyu fa tana faduwa a dalilin ciwon kan” murmushi yayi yace babu matsala Mama zata samu sauki karki damu! sannanya kalleni yace “ki kula da shan magani akan lokaci, bayan satidaya inaso naga chanji kin gane?” a hankali na girgiza kai! sannan yayi mana bayanin drugs din Mami tai mishi godiya muka tafi!+
A mota kuwa Mami cewa tayi “kinji abinda Doctor ya fada don haka kar naji labarin kafarki ta taka kofar gida kafin sati dayan nan! sannan ki kula da shan magani. idan bana ganinki Allah yana ganinki duk lokacin da baki sha ba! nace “Mami zan kula karki damu” sai da takai ni gida tayiwa Dada bayanin yanda mukai da likita sannan ta tafi. Ina shigowa daki na dau waya na kira Ihsan! bayan mun gaisa nace “Ihsan don Allah idan kin gama lectures da wuri ki biyo ta gidanmu” cewa tayi “yanzu nake niyyar kiranki naji lokacin da zaki dawo makaranta! naga lokacin bikina banyi fashin da kikeyi ba amma kullum sai kinmun tsiya ke gashi bikin ma saura 2months amma kin watsar da karatu” cikin kosawa da maganar nace “Ihsan idan kinzo zamuyi magana!” a sanyaye tace “wani abun ne ya faru?” nace “ke dai kizo kawai” tace “toh shikenan zanzo Zara” mukai sallama!
muna gamawa da Ihsan wayar Imamu ta shigo! tsayawa nayi na zubawa lambar idanu har kiran ya katse wani ya sake shigowa! nan ma ban samu damar dauka ba har ta katse! na mayar da kaina kan pillow na lumshe idanu ina tunanin rayuwa! watanni takwas da suka wuce idan akace zan shiga irin wannan halin ko da a mafarki ne zan karyata! gabadaya shigowar Imam rayuwata bai zama alkahiri ba.
A cikin wannan tunanin nannauyan bacci ya kwasheni dalilan magungunan da nasha! bani na farka ba sai karfe uku da kwata! sosai jikina yayi mun dadi kaina ya dan rage nauyin da yake mun! alwala nayi na gabatar da sallar azahar sannan na futo parlour! Dada ce zaune da Baba Rabi suna hira naje na zauna gefen Dada! “kin tashi? hala maganin ne ya saki bacci haka?sau uku ina aika Rabi tana cewa baki tashi ba” murmushi nayi nace “inaga da maganin ma kuma da gajiya” tace “to ya kikejin jikin naki” nace “Na samu sauki Dada” ta sake cewa “kan naki fa?yayi sauki?” nace “baccin da nayi yayi sauki ba kamar dazu ba” tace “toh Allah ya kara sauki! Baba Rabi ma tayi mun sannu sannan ta shirya mun abinci a gabana! wainar shinkafa da miyar ganye da kuma farfesun kayan ciki! ina cikin cin abincin naji nishin lafiyayyar motar Ihsan, minti biyar ta shigo gidan cikin sallama! Dada da Baba Rabi suka shiga yi mata sannu da zuwa sannan suka gaisa! Baba Rabi tace “kice kawar taki mun kusa zuwa shan suna?” Ihsan ta rufe fuska tana dariya! nace “kinji gulma wai rufe ido take kamar gaske” ta miko mun harara ta cikin gyalen nata! Daga nan muka shiga dakina! aje mayafinta tayi tace “Zara bani abinci tukunna biyu biyu nake gani” dariya nayi nace “wa zai hana Maman twins abinci?” cikin harara tace “aniyar ki ta biki! insha Allah daya zan haifa” na kyalkyale da dariya nace “watakila ma triplet ne Allah dai ya kawo mana su lafiya” na futa ina dariya ban tsaya jin abinda take gaya mun ba!
Bayan ta kammala cin abincin munyi sallar la’asar ne muka zauna bakin gado muna fuskantar juna! a tsanake na labarta mata duka abubuwan da suka faru a Kano! tayi matukar mamaki domin kuwa a tsarin da muka shirya Jidda zamu nema ta warware mana tsakanin Aisha da Imamu kamar yanda nagani a diary din Aishan cewa zata nemi Jidda suyi magana! kasamcewar bayan ni bata da wata kawar da ta kaita. kuma ta wani bangaran ma yar’uwarta ce daga side sin family din Babansu!
“Ihsan yanzu meye abun yi? ” na fada a sanyaye! cewa tayi “the best is to have a talk with Aisha. Zara dole kiyi haka, idan har kin yarda da ita kuma kin amince ta yarda da ke ni ina ganin gara ku fuskanci juna ku warware matsalar nan a tsakaninku! duka amsar da muke nema tana wajen Aisha gara kawai ayita ta kare tun lokaci bai kure mana ba” kwarai abinda Ihsan ta fada gaskiya ne sai dai ni har yanzu banji ina da kwarin guiwar yiwa Aisha wannan tuhumar ba. bansan amsar da zata bani ba, bansan ya zata dauki maganar ba kuma bansan me zai biyo baya ba!
Ji nayi an dafa kafadata “Zara! baki da lokacin tunani, lokacin tunani ya kare sai neman mafuta kawai! idan kikai wasa zaki wayi gari an daura aurenku da Imamu baki yi komai akan hakan ba. baki sani ba itama Aishan kila tanaso tayi miki maganar amma bata san ta inda zata fara ba! kuma banajin ta san akwai wani abu tsakanin Imam da Jidda! Aisha na da muhimmanci wajen solving case din nan Zara babu abinda ya kamata irin ku zauna da ita tayi miki bayani!” a hankali na girgiza kaina cikin gamsuwa! “yaushe zasu dawo?” cewar Ihsan! na amsa “jibi ne” tace “toh kiyi kokari acikin satin nan ki sameta kuyi magana Zara don Allah muyi mu warware maganar nan mu wuce wajen!” zan magana wayata tayi karar shigowar text! nayi maza na mika hannuna na dauko ta akan side drower! ganin sakon email ya sanyani kaduwa don bazan manta da mummunan sakon da naci karo da shi ba shekaranjiya! Ihsan ce ta lura da yanayina tace “menene?” shiru nayi ina tunani, sai ta karbi wayar a hannuna nayi maza na fizge tare da bude sakon!

“Bakisan wanene Imamu ba shiyasa kike dokin auren sa! ina mai son sanar dake cewa babu abinda zaki tsinta a auren shi illa takaici, nadama,dana sani da tashin hankali! idan kina tantamar magana ta yanzu kije adreshin da zan turo miki bayan minti goma”

Abinda sakon ya kunsa kenan! ji nayi ilahirin jikina yana kadawa kamar me shigar sabon Zazzabi! kafin na mike da sauri na dauko hijab dina na saka!A hanzarce Ihsan ta rikeni tana cewa “meye haka? ina kike tunanin zuwa?” cewa nayi “zuwa zanyi ko inane na kama mutumin nan dumu dumu da hannuna yasan nasan abinda yake yi” zaunar dani tayi a bakin gadon sannan ta zauna! “No! ba haka za’ai ba! babu inda zakije, bakisan waye me aiki sakon ba kuma bakisan manufarsa akan ki ba! hakuri zamuyi zuwa dawowar Aisha muji ta bakinta kafin musan abinyi” dakyar ta shawo kaina na hakura da bin adreshin da aka turo yanzun nan! amma sam na kasa nutsuwa hankalina ya ki kwanciya. sai bayan magriba Ihsan ta tafi gida.
Asubar washgari Ya Mahmud yayi mana sallamar komawa garin London! bansan munyi sabo da shi haka ba sai yanzu da zai tafi. har Airport mukai masa rakiya suna ta faman share hawaye shi da Mami! ina mamakin yanda kuka ba yayi wa Ya Mahmud wahala kamar karamin yaro! he gets emotional easily.bayan an gama emotional scenes dinne ya rungume kowa ya wuce muna daga mishi hannu! bamu bar Airport din ba sai da muka ga tashin jirginsa. haka muka dawo gida jikinmu a sanyaye. musamman Mami wadda kallo daya zakai mata ka gane damuwar kan fuskarta! bansan wanne irin so takewa Ya Mahmud a duniya ba. shima kuma banga wani abu ya kai masa Mamin ba a rayuwarshi! ranar Laraba su Aisha suka dawo. washegari na dau waya na kira Mami akan inason naje nayi wa Ummansu Aisha sannu da zuwa dakyar ta barni sannan naje na gayawa Dada.
Daki na dawo na daura abaya akan riga da wandon jikina na dauko jaka da mukulli na futo. Kudi Dada ta bani tace na tsaya a hanya na siya musu ruwa da lemo na amsa nayi mata godita sannan na tafi.

Lokacin da na isa gidansu Aisha dukansu suna parlour tare da baki. cikin jindadin ganina Aisha ta taso ta rungumeni sannan na isa wajen Umma na gaisheta da sauran bakin gabadaya kafin Aisha taja hannuna zuwa dakinta. ko bari bata yi mun zauna ba ta soma binciko manyan akwatin da tazo da su tana zakulo kayayyakin da ta siyo mun a America! galala na tsaya ina kallonta ganin uwar tsarabar da tayo mun akwati guda don duk abinda ta siyo kanta saita siyamun sai dai bambamcin kala kawai!” banyi mamaki ba don duka haka muke wa juna idan munyi tafiya. yanzu haka nata kayan da na siyo mata suna dakina a je don ban samu sukunin zama duba kayan bane ya sanya ban taho mata da su ba.
bayan mun nutsu ma dubeta cikin dauriya nace “Aisha!” dagowa tayi ta kalleni cikin rashin fahimtar dalilin da ya sanya na kira sunanta cikin wannan yanayin! hade yawuna nayi dakyar nace “Aisha magana nakeso muyi a matsayin mu na aminai wadanda suka mayar da komai na rayuwarsu daya suka amince da juna suke kaunar juna suka kuma yarda da juna! Aisha ina cikin wani hali da duk duniyar babu wanda zan iya fuskanta dashi sai ke! ki taimakeni Aisha!”
Gabadaya yanayinta ne ya chanja, tsoro, firgici, tashin hankali, da fargaba duka suka bayyyana akan fuskarta! dafa kafadarta nayi cikin sanyi sanyi da karyewar sauti nace “Aisha feel free dani akan wannan maganar zan miki please! taimakeni Aisha kafin zuciya ta ta buga ki warware mun abinda ya shigemun duhu game da halin da nake ciki”
A hankali hawaye ya soma gudu a kan fuskarta jikinta ya fara rawa lebbenta suka shiga motsi amma ta gaza cewa komai! cikin dakewa da dauriya na kwato kalaman dakyar daga harshena nace “Aisha menene tsakaninki da Imamu? kuma me kika sani game da shi?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *