HAUSA ARAB CHAPTER 4
Wani irin tsoro da tashin hankali nagani cikin idanunta yayinda hawaye yaci gaba da zirga zirga akan fuskarta! cikin sanyi na riko hannunta na fara magana cikin nutsuwa!
“Aisha na dade da sanin wani abu game da tsakaninki da Imam! Tun ranar da kuka fara haduwa a gidanmu naga halin da kika shiga da yanda kika kasa sakewa dashi duk alwashin da kika dauka akan tambayoyin da zaki masa da gwajin da zaki mai! na futo ne da niyyar nayi miki tambayar hakan sai naga cikin kankanin lokaci kin batar da
wannan expression din kin dauko yanayinki nada. abun ya bani mamaki amma sai na zabi nayi shiru kawai! Ranar da zanje gidansu Imamu kika rakoni bakin mota naga irin kallon da kukewa juna wanda ya dau hankalina sosai na fara tunanin lallai akwai wani abu mai kama da so a tsakaninku! ban kuma gasgata zargina ba sai ranar birthday dina da na rokeki kizo gidanmu muyi wa Imamu cin cin kikayi zuwa! amma sai gashi kuzo school dinmu tare a mota daya! Duka yanda kike kaucewa idan na kawo miki zancen Imamu ina sane da shi da kuma rashin son haduwa da shi da kikeyi! tun abun bai soma damuna ba har na soma damuwa. da na tambayi Ihsan a ranar da kukazo school dinmu game da abinda ta fuskanta tsakaninki da Imamu sai tace mun da banyi introducing dinku a matsayin ke aminiyata bace shikuma fiance dina babu abinda zai hanata tunanin ke da shi babu soyayya a tsakaninku! tabbatarwar da nayi bani kadai nake ganin haka a tsakaninku ba ya daga mun hankali fiye da tunani!a hankali alakarmu ta soma sauyawa da ke ya zama muna wasan yar buya. idan kuwa har muka hadu mun dinga kokarin kawar da abubuwan da suke ranmu har mu rabu! watarana da baki da lafiya nazo gidan nan kuna asibiti da Umma baku dawo ba sai iky na samu na shigo dakin nan na zauna ina duba abinda zai tayani hira kafin ku dawo. kamar wasa naga diary dinki..abun ya ban mamaki don nasan tuni muka dena wannan shiryen rubuce rubucen! toh sai dai kuma cin karo da nayi da wani babban al’amari ya sanyani nutsuwa na karanta!”
Idanunta ta zaro gabadaya! tana kallona cikin mamaki da dimuwa! murmushi nayi naci gaba.
“Anan nagane kin soma son Imamu ne tun kafin nasan shi tun kafin nasan zan hadu da shi! acikin littafin nagane baki da burin da ya wuce samun Imamu toh amma kash! a ranar da kika fara ganinsa ganin ya zamto mummunan gani domin kin ganshi ne a matsayin wanda yake son aminiyarki! a take nagano dalilin sauyin yanayinki ranar da kuka hadu da Imamu da kuma dalilin da yasa kike gujewa maganarsa da ganinsa! na ga abubuwa masu yawa a diary din ciki harda text din da kika tura masa akan kin manta diary dinki a motarsa kina rokon kar ya bude miki!
Bansamu damar gane komai tar tar ba kuka dawo! in zaki tuna a gurguje na bar gidan nan don kar naci gaba da zama ina kallonki na kasa jure abinda nagani! tun daga ranar nake bibiyar duk wani motsinki da na Imamu. akwai ranar da na kira wayarki Iky ta dauka tace kinyi bako, bana mantawa ranar Mahmud ya dawo daga tafiya baizo wajena ba bayan al’adarshi duk sanda yayi tafiya ranar da ya dawo yake zuwa wajena. a jikina naji tabbas wajenki yazo don nasan baki da saurayi idan kuma dan’uwanku ne nasan gida zaki shigo da shi kuma Iky zata san ko wanene shi! Na tsani kaina Aisha a lokacin nayi dana sanin haduwa da Imamu nayi dana sanin kasancewa da abinda kika so a rayuwa sannan nayi damarar bar miki Imamu koda son shi zai mun illa.
sai dai na rasa ta inda zan bullowa abun, na rasa ta ina zan fara. ke kadai ce wadda take taimakamun idan na shiga damuwa mu gudu tare mu tsira tare mu samu mafita tare sai kuma ya kasance banida damar tarar ki akan wannan magana! da Ihsan muke tattaunawa kuma ita take bani shawarar nabi komai a hankali! Ranar dinner din Ihsan wani abu ya faru wanda ya daure mun kai ya sakani tunani domin bayan an tashi mami tace mun kunyi sallama kin tafi gida sai kuma da safe Umma take tambayata me ya sameki a gidan su Ihsan kin dawo ba lafiya. kafin na tambayi Ihsan din ita take cemun wai kin bar wayarki kafin mu tafi dinner kuma ta tabbatar mun baki kwana gidansu ba. ba zaki taba gane halin tunanin da na shiga ba Aisha! ban iya sanar da kowa wannan maganar ba sai yau da nake gaya miki amma wallahi bana awa ashirin da hudu abun bai fado zuciyata ba! tambayoyi ba irin wadda banyi zuciyata ba akan ina kikaje? da wa kuka tafi? a ina kika kwana? meye dalili? rashin sanin amsar ya sake dagula mun lissafi! Hakana kin rage walwala kin daina nishadi kin rage shiga sabga ta wannan ya sake sani tunani. a dai dai lokacin da nake tunanin neman Jidda naji ko zan samu wani karin bayani a wajenta domin acikin diary dinki naga kin rubuta kuna bukatar neman wadda zakuyi magana da shi kuma kika saka sunan ta don haka na yanke shawarar muna dawowa daga Saudi zan nemeta!
Game da Imamu kuwa na gama sarewa. don zuwa wannan lokacin bana yiwa kaina sha’awar aurenshi kamar yanda kema bana miki fatan auren mutum irinshi. naga alamomi masu yawa akan boyayyun munanan halayen Imamu. sannan akwai wani abu tsakaninsa da Ya Mahmud wanda na kasa ganewa. yana matukar kunyar Ya Mahmud kuma yana kaucewa magana da shi yayinda shikuma Ya Mahmud yake masa kallon “Nasan komai game da kai” sai dai daga haka bai sanar dani komai ba. bayan mun dawo daga Saudi mukaje Kano anan ne naga abinda ya daga mun hankali. wani mummunan hoto aka turamun ta email dina Aisha! Imamu da wata yarinya………
abinda ya gigitani har ya sakamun wani irin ciwon kai!Ya Mahmud ne ya bukaci muje wellcare mu siya magani, shigata ke da wuya Aisha naga Jidda tare da Imamu, sai lokacin na tuna cewa ai hoton da aka turo mun Jiddan ce aciki!”+
STORY CONTINUES BELOW

Da wani irin mugun tashin hankali ta ke kallona idanunta ya kafe kaf, zuciyarta sai luguden bugu takeyi.ta kasa cewa komai sai rawa lebbenta sukeyi jikinta ya dau wani huci!
murmushi nayi mai ciwo sannan na dafa ta “Aisha karki daga hankalinki, wallahi da minti daya ban ga lafinki ba, banga aibunki ba kuma bana zarginki Aisha domin na yadda da ke kuma na yarda da amicin da yake tsakaninmu! so nake Aisha ki aje komai gefe ki taimakeni mu kwance wannan kullin na samu na futa daga ramin da Imamu ya jefani na tserewa aurenshi!please Aisha!
Babu zato ta fashe da kuka mai tsanani ta rufe fuskarta da tafukanta tana ci gaba da rera kukan a hankali! bance mata komai ba sai da tayi kukan ya isheta sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta ta futo da karamun towel a hannunta tana goge fuskar!
A sanyaye ta dawo ta zauna kusa dani sannan ta soma magana cikin tsananin damuwa da sanyin jiki!
“Zara da farko ina neman afuwarki da yafiyarki akan duka abubuwan da suka faru! inaso kuma ki yadda cewa ban boye miki komai don na munafunceki ba ko naci dunduniyarki, Na boye ne saboda bansan da wanne ido zan kalleki ba, bansan ta inda zan fara miki wannan maganar kuma bansan abinda zai biyo baya tsakanina da ke ba a dalilin hakan! Wannan ya sanya mun tsananin tsoro da fargaba nake iyakacin bakin kokarina akan naga na boye miki komai nayi maganin komai na warware komai ba tare da kin sani ba! Saidai hakan bazaiyu ni kadai ba sai na samu taimakon wani, wanin kuma da nafi bukata bai wuce ke ba! Amma kash!abubuwan duka akanki ne don haka sai na yanke shawara na nemi Jidda! Zara ban sake sanin matsayi da daraja da girman amincin da ke tsakaninmu ba sai da na shigo da Jidda cikin private life dina! Ashe ba duka kawaye ne kawayen gaskiya ba,ba duka kawaye suke kaunar ka saboda Allah ba, ba duka kawaye suke da nagarta da amana da alkawari ba! Zara haka Jidda ta dinga dorani tana ingizani har ta jefani cikin ramin da bansan yanda zan futa daga ciki ba!
Nayi dana sanin yarda da ita, nayi dana sanin bude mata sirrina, nayi danasanin bata amanata kuma nayi kuskuren da bansan ta hanyar da zan gyara shi ba Zara!”
A sanyaye nake kallonta cikin wani irin tausayi da bakin ciki da kuma danasanin shigowar Imamu cikin nagaryacciyar tsaftatacciyar amintarmu! inama na zama kamar Aisha hawayen nan suka dinga kwaranyowa daga idaniyata ko naji sauki da sassaucin radadi da zugin da zuciyata take mun! bayan ajiyar zuciyar ta sauke taci gaba tare da dukar da kanta kasa sabanin dazu da take kallon kwayar idona.
“Zara tun ranar da na fara ganin Imamu a Tozalo magazine naji ya shiga raina na kuma fada tarkon kaunarsa! wani irin shu’umin so mara fassaruwa, na kasa ci na kasa sha na kasa bacci na kasa walwala a dalilin tunaninsa da soyayyarsa! ba karamar bakar wahala nasha ba kafin na saita kaina na bawa zuciyata hakuri son mutumin da ban taba gani ba. bai sanni ba, bai san ina rayuwa ba!
Duk da haka ban taba sallah nayi addu’a ban saka shi cikin addu’o’ina ba. tare da neman Allah ya hadani dashi ya mallamun shi!
Haka rayuwa taci gaba ina dauke da kaunar wannan bawan Allah.ban taba gayawa kowa ba domin a tunanina za’ai mun dariya ko kuma kallon mara hankali don haka na rufe maganar nikadai. idan naso lallai nayi magana saidai na dauki diary dinnan nayi rubuce rubuce na na ajiye.
Bazan taba manta ranar da kikai kirana kikace kin samu mijin aure ba. domin ji nayi gabana yayi wanin dokawa da fargaba wadda bansan ta mecece ba.Ranar kuwa da mukai ido hudu da Imamu a gidanku kiris ya rage ban zubar da tray din hannuna ba, na tabbatar Aisha addu’ar da nake yi kullum tayi tasirin karfafa mun zuciya na dake na samu nutsuwar tsayawa inuwa daya da Imamu.
Bayan na koma cikin dakinki kuka na fashe da shi mai tsanani akan kaddarar da ta fado mun. sai kuma na soma tunanin tuhumar da zakimun akan yanayin da kikaga ganni da shi a gaban Imamu. ji na dinga yi kamar kin gano komai a tare dani, ji nake kamar kina shigowa zaki tuhumeni akan alakata da Imam. cikin mintina kalilan na samo dauriya da dakewa da imanin yarda da jaddara na wanke fuskata na gyarata na futo na dawo wajenku da niyyar gyara kuskurena sai na tarar har kin futo yi masa rakiya.
Daga wannan ranar na shiga tsanani da fargaba da tashin hankali mara misali. wannan abun shine mafi tsaurin abinda ya sameni a duniya. Na dinga avoiding Imam ne Zara saboda karki gano wani abu a tattare da ni. na dinga gujewa duk hanyar da zanyi magana da shi ko na ganshi. cikin kankanin lokaci alakata da ke ta samu rauni mai yawan gaske. har Ihsan na shirin maye gurbina a wajenki wajen communication.
Zara bansan ashe Imamu kwararre a bangaren yaudara da sanin luggan mace ba. ashe tun ranar da ya fara ganina ya gano halin da nake ciki game da shi. Haka kawai ya soma shishshigemun, kullum sai ya kirani a waya wai na bashi labarinki, tun ina dar dari dashi har na saki raina amma can kasan zuciyata ina jin kamar akwai boyayyen wani sirri! Ranar da na manta diary dina a motarsa ranar birthday dinki ne, ina tsaka da rubutu a parlour ya kirani yayi muna bayani akan yanaso yayi surprising dinki! haka na mike na shirya. Umma ce tace na bata littafin taga wai me nake yini rubutawa, hakan ya sanya raina ya kasa kwanciya da barin littafin a gida na tafi da shi a hannuna. a karshe na manta shi a karkashin kujerar motar Imam! wannan shine silar duk wata masifa da take faruwa a yanzu Zara!”
Jikina a bala’in sanyaye nake kallon Aisha wadda tunda ta fara magana ta dukar da kai bata dago ba. sai jikinta da yake rawa a hankali.
“Ina dawowa gida Zara na tuna cewa na bar diary dina a motar Imamu. Nayi ta buga wayarshi bai dauka ba shine nayi masa text ina rokonsa akan kar ya budemun diary din nan! bai saurareni ba har bayan kwana biyu, sannan ya shigo mun da wani salon da ya gigitani ya tsundumani a fargaba da tashin hankali. Zara ya budemun sirrina ya karanta komai na cikin diary din har da abubuwan da basu shafe shi ba duka ya gani. Anan artabu ya balle a tsakaninmu, nayi masa kaca kaca don har lokacin bai bani littafin ba. tun ina masa ihu da barazana har na sauko na dinga bashi hakuri cikin lallami amma Imam bai saurareni ba. Rannan sai kawai ya turamun text akan cewa kamar yanda nake sonshi haka shima tunda ya fara ganina na shiga ransa don haka duk yanda za’ai sai ya sameni ta kowanne hali. hankalina yayi masifar tashi sai naga magana a waya ma bata da amfani a take na mayar masa da amsa cewa mu hadu a park and zoo.
A ranar nayi masa magiya nayi kuka nayi masa nasiha nayi masa wa’azi na fahimtar da shi alakar da ke tsakanina da ke, na kuma tabbatar masa da cewa na daina sonsa tun lokacin na ganshi a matsayin saurayin aminiyata! Zara wallahi idan da ace Imamu yana da Imani ko na kwayar zarra ne da ya saurareni kuma ya yarda da abinda na gaya masa ya girmama amincinmu amma sai yayi mun lamfo kamar ya amince a dai dai wannan lokacin ne kuma Jidda ta soma mummunan takunta a kaina tunda na bayyana mata sirrina. ita ta dinga bani shawara akan abubuwa masu yawa, akan na kwantar da hankalina komai zaiyi dai dai! sannan ta bani shawarar lallai babu abinda ya kamata irin na sameki nayi miki bayani mu warware komai. sosai na gamsu da ita da bayanin da tayi mun kuma na saka a raina ana kammala bikin su Ihsan zan warware miki komai.Ban taba tunanin bakinsu daya da Imam ba kuma bansan ta hanyar daya bi ya hade kai da ita ba, ni dai kawai nasan Jidda babu abinda ba zatayi saboda kudi ba.
A ranar dinner idan ba zaki manta ba zakiga na sakar miki fuska kuma na ware muna walwalarmu. na samu wannan nishadin ne a tunanin da nayi kan cewa zan fuskance ki mu warware matsalarmu.
Jidda ce ta dinga kirana a waya, ban dauka ba nayi mata text akan ina wajen biki akwai hayaniya. sai ta mun text cewa tana wajen bukin na futo.
Nayi mamaki kwarai domin ta tace mun ba zata samu damar halartar bikin ba don haka na futo da sauri.
ganinta ya bani mamaki don babu shirin biki a tare da ita. cewa tayi mun “Aisha taimakon zakiyi don girman Allah kizo muje” cikin rashin fahimta nace mata “ina zamuje bakiga ina cikin hidimar biki bane ya za’ai na tafi yanzu?” halin da ta nuna mun tana ciki ya sanyani tilas na hakura na bita. Anan muka hadu da Mami tana shigo da baki tace mun tafiya zanyi? sai kawai Jidda tace mata eh! ita kanta Mamin bakin da suke tare da ita ne suka dauke mata hankalin tsayawa bincikar mu dalilin tafiya. wajen motarta mukaje muka shiga ina kullo murfin motar na juyo nai mata magana kenan ta kadamun wani handkerchief a fuskata daga nan ban sake sanin inda nake ba sai farkawa nayi na ganni akan gado cikin wani dakin da ko a mafarki ban taba zuwa ba. a zabure na mike tsaye ina waige waige. sai naga rana gabadaya ta keto ta cikin fararen curtain din dakin wanda ya nuna mun cewa safiya ce. Anan nagane cewa kwana nayi a wajen….domin tunda muka shiga mota da Jidda ni dai ban sake tuna komai ba.
hankalina yayi masifar tashi nayi kofa da sauri zan bude sai naga ana kokarin murda kofar a shigo da alama da key aka kulleta daga waje. tsayawa nayi cak ina sauraren abinda zai biyo baya. Babu zato babu tsammani naga Imam ya shigo hannunshi dauke da tray wanda aka hada kayan abinci akai!”
********************************
zuwa wannan lokacin nidai na zama mutum mutumi ko yau na kasa samu a bakina na hadiye naji dadi. kawai kallon Aisha nake baki bude kamar sokuwa ita kuma idanunta banda aikin hawaye babu abinda suke ta kafawa yatsunta ido kamar ta cikinsu take karanto labarin! cigaba tayi cikin rawar murya:+
“Cikin mamaki nake kallonsa tare da tsabar kaduwa da bacin rai! da wani irin fushi nace masa ‘Daman Imamu kai ka kawo ni nan? me kake nufi dani? kai ka kawo nan tun daren jiya? me nayi maka?’ cikin wannan murmushin nasa na yaudara yace ‘calm down Aisha! zauna muyi magana ta fahimta a nutse’ da hargagi da masifa na soma ce mishi “wacce irin magana ce ta fahimta tsakanina da kai? meye kake tunanin zaka yaudare ni da shi? angaya maka ni sakarya ce dakikiya irinka da zan saurare ka?” murmushi ya sake yi tare da aje abincin sannan ya mike yace ‘Ashe kuwa baki shirya barin dakin nan ba kuwa. don idan har baki bari munyi magana ba toh ko shekara daya zakiyi anan gidan babu inda zaki leka! babu kuma wanda zai gano ki. ga abinci nan kici ki huta zuwa lokacin da kikaga kin shirya saurarata kwankwasa kofa kawai zakiyi mai gadinki zai sanar dani!’ yana gama fadin haka ya juya zai futa.
a take na gane cewa masifa da ihu da fada ba shine mafuta a gareni ba, mafuta daya na bar gidan nan kafin a soma nemana. don haka nace masa “ka dawo muyi magana” dariya sosai yayi yace “ban dauka zaki saurin karaya da wuri haka ba, well fara cin abincin sai kifi samun kwarin guiwar jin maganar sosai!” harara na zabga masa nace “ko yunwa zata kasheni ba zanci abincin da ya futo daga hannunka ba! wacce magana ce muyi ta ta kare na bar wannan bakin gidan”
cikin rashin damuwa yace ‘well, tunda haka kikace zauna!’ a kagauce na zauna bakin gadon kafin ya yi gyaran murya wani katon mutum ya shigo. cewa yayi masa “ka dauko mun laptop da envelope akan dinning a kasa” ya amsa tare da juyawa. ji nayi wani matsanancin tsoron Imamu ya kamani, hankalina ya ninka na dazu tashi na gigice don na tabbatar idan har wannan mutum aka baiwa tsarona to na kade har ganyena banga ta yanda zan iya guduwa ba! ban ankara ba ya dawo da abinda Imam ya umarce shi ya dauko! sannan ya janyo study table ya dora masa akai ya juya ya futa! Envelopes din ya dauko ya miko mun sannan ya shiga sarrafa system din.
A hankali na bude envelope din inda naci karo da mummunan ganin da bazan manta ba! Zara hotona a dakin aka dauka har guda shida tare da wani a gefenan a zaune. hoton was soo real da ni kaina sai da na shiga rudani akansa. juyowa yayi yana murmushi tare da turomun screen din laptop din gabana. Anan naji yan hanjina sun tsinke. Zara vedio ne na dakin nayi bacci, shi wancan mutumin yana ta aikace aikacenshi da waya da computer da takardu nikuma ina kwance ina sharar bacci Zara ko ke kika ga wannan vedio ba zaki yarda dani ba wallahi. “
Innalillahi kawai na dinga maimatawa ina hawaye tare da wani irin firgici da tsoro da fargaba, ban iya samun kalmar da zan bude baki nayi mishi magan ba!
sai da ya gama kallon yanayin da na shiga tsab sannan ya soma magana with serious tone! ‘Kada ki daga hankalinki, idan har zaki bi dokar da zan dora miki, kuma zaki kiyaye toh babu mahalukin da zaiga wannan hotunan da vedio har lokacin da zan baki su da hannunki ki kona su ki kuma goge na cikin system din! Nasan zuwa yanzu kin fara tunanin wanne irin mutum ne ni ko? kuma ya za’ai ki hana kawarki aurena? kin soma shirin gaya mata halina da boyayyun siririn da kika sani a kaina! hakan ya sanya na tilastawa kawarki yin dabarar dauko mun ke daga inda kike domin na hada wannan plan din.
warning kawai zan miki da wadannan hotunan da vedio wanda duk wanda na turawa babu makawa babu tantama zai gano bakin halinki da boyayyen bakin sirrinki! kidan yi tunanin yanda zakiji idan na linke envelope din nan na turawa mahaifinki office dinsa. ko kuma nasa yaro yayi sallama ya kai gidanku? ko kuwa a wayi gari hotunan sun bazu a social network? wanne bayani zaki yiwa wadanda suka yarda dake su fahimceki?
kallon horror kawai nake ma Imam a wannan lokacin jikina yana wani irin rawa kamar mazari yayinda yayan cikina suke kuwwa suna kugin tsoro.
Murmushi ya saki kafin yaci gaba da magana cikin sanyin murya da kwanciyar hankali wadda take nuna samun galaba akan wanda zakaiwa maganar ‘cool down my dear! Duk wadannan abubuwan sai kinso zasu faru idan kin dauki sharadin da zan gaya miki. sharadin kuwa shine ko da wasa, ko da subutar baki, kika yarda kika sanar da Zahra wani abu mara kyau game dani toh wallahi babu abinda zai hana abubuwan da na gaya miki faruwa! Idan kuwa kika janyo matsalar da Aisha tace ta fasa aurena toh wallahi sai na saka ki cikin bala’in da mutuwa ce kadai zata rabaki da shi! Duk wata hanya da kikasan Zara zata gano illata ki tosheta har zuwa ranar da za’a daura aurenmu da ita! idan kika cika wannan alkawarin toh kingama aikinki. ke da kanki zaki kona wadannan hotunan ki goge vedios dinnan shikenan an wuce wajen! sabawa daya cikin dokata na nufin kin shirya shiga gararin sa zan sanya ki a ciki. Karki damu bana bukatar amsarki a yanzu. kije gida ki nutsu kiyi tunani, kafin ki yanke zabin da zaki yi wa kanki.’ yana kaiwa nan ya hada laptop din da hotunan da suka tarwatse a hannuna ya mayar da su cikin envelope din ya futa. kawai jinayi kafafuwana na binsa don burina a lokacin bai wuce na ganni na futa daga wannan bakin gida ba kila ace mafarki nakeyi, idan na futa waje zan farka. motarsa na shiga ya kawoni har gida ba tare da wani yayi magana ba a cikin mu. Muna isowa na balle murfin motar na futa na. shigo gida. Da Umma naci karo a parlour sai dai duk yanda naso aro nutsuwa a jikina na gaza, hankali tashe ta shiga tambayata me ya faru, dakyar nace mata kaina ke ciwo na shigo dakina na kwanta. sai lokacin na tuna duka abubuwan da suka faru na kuma tabbatar ba mafarki bane, a zahiri komai yake faruwa. nayi kuka kamar raina zai futa, kaina yana wani irin dagargazar ciwo kamar zai tarwatse har bansan me yake faruwa dani ba. inaga a lokacin ne Umma ta nemi wayarki ta tambayeki me ya sameni!….Lokacin da kikazo babu yanda banyi da zuciyata na gaya miki komai ba amma tsananin tsoro da firgicin barazanar Imam ta sage mun guiwa. naji bazan iya yi miki maganar ba, sai dai in ba zaki manta ba abinda nace miki shine “nayi alkawari komai wuya komai rintsi bazan sauya daga yanda kika sanni ba” Daga ranar Zara ban sake sukuni ba wallahi, ban sake bacci me dadi ba domin tunanina naci amanar ki
sai wannan lokacin Aisha ta dago jikakkun idanunta da suka rine kamar garwashin wuta. ta kamo hannayena taci gaba da magana!
“Zara nasan cewa ban cancanci a kirani aminiya tagari ba, domin boye miki maganar da nayi har zuwa yanzu da kullum shirin aurenki da Imam yake kusantowa, kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi? ta ya zan zuba idanu na barki ki auri mutum irin Imam? kawai saboda ni na kubutar da kaina daga sharrinsa. ban kyauta ba idan nayi haka, nayi son kai da zalinci, Zara bazan bari ki auri Imam alhalin ina da yanda zanyi na kubutar da ke ba. ko da hakan na nufin faruwar duka abubuwan da ya lissafa zasu faru gareni. i am ready to face them to protect you! Zara fatana kawai idan haka ta faru ki zama wadda zata yarda dani, kada ki juya mun baya please zara! ki zama mutum guda da zata tsaya a gefena a lokacin da zan fuskanci wadannan kalubalen….Duk runtsi duk wuya kada ki barni Zara”
wani matsanancin kuka ta fashe da shi mai bayyanar da zallar tashin hankali da tsoro da fargaba da kuma sadaukarwa!
Kallon Aisha kawai nake tana kuka amma nikam zuciyata ce take wani irin suya kamar zata tarwatse, kaina yayi mun nauyi har bana iya juya shi yanda nake so! inama nima zanyi kukan da hawaye kamar yanda take yi? kila ko zan samu sassaucin radadin da nake ji. A maimakon na rarrasheta sai kawai na mike na bude Windows din dakin na tsaya a gabansu ina shakar iskar da hadarin da ya taso yake bayarwa don ji nayi sanyin Acn baya wadatar dani. mun kai mintina goma a haka kafin ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta ta futo! Gefena tazo ta tsaya ta dafani sannan ta soma magana “Zara bamu da isashshen lokacin tunani da maganganu mafuta kadai ya rage mana mu nema, wacce hanyar kike gani zamu fi samun saukin shawo kan al’amarin cikin sauki?Wa zamu tunkara da wannan maganar? ya kamata muyi hanzari domin bamu da lokaci isashshe, Ni a ganina mu samu Gwaggo muyi mata bayani dalla dalla tun daga farko ina kyautata zaton zata fi kowa fahimtar mu kuma kinga itace me yankewa, ita kadai ce zata hana aurenki ya hanu! ko ya kika gani?” kallonta kawai nake tana rattabo jawabi babu kakkautawa bansan lokacin da nayi murmushi ba!
Gyara tsayuwata nayi sosai sannan na fuskance ta kafin na soma magana a nutse! “Kina tunanin abu ne mai sauki bada wannan labarin ga Gwaggo? kina da tabbacin akwai wanda zai yarda cewa ba bakinmu daya da ke ba? kina tunanin ba za’a ce plan muka hada kawai don lalata wannan auren ba? idan bakiyi tunanin haka ba ki fara yanzu! A mutanen duniya kakaf ni banga wanda ya dau aure da muhimmanci irin Gwaggo ba, banga kuma wanda baya magana biyu irinta ba, Idan da akwai abinda yafi komai wahala a yanzu shine sauke ra’ayin Gwaggo akan Imam domin ya dade da siye zuciyarta da kyawawan halaye da nagarta da karramawa da mutuntawa! abu na biyu shine bamu da kwakwkwarar hujja a hannunmu wadda take da karfin da za ta iya rushe auren da ya rage sati uku a daura shi! Abu na uku kuma mafi muhimmanci shi ne Ni Zara wallahi tallahi bazan janye auren Imamu don kar na cutu ke kuma na jefa ki cikin matsala ba! ki sa a ranki wannan ba me yiwuna bane! Ikirarin da Imam yayi yana nufin bata miki suna da mutunci da daraja da kima ne a idon duka duniya ciki har da mahaifanki, da yan’uwanki da danginki da masoyanki da duk wani mai muhimmanci a raguwarki…..wani bakin Fenti zai goga miki wanda har abada ba zai goge ba, don ko da zai dawo yace karya ne, hakan ba zai wadatar da wasu mutanen su yarda da ke ba! Imamu hatsabibin gaske ne, kuma mutum me hadarin gaske, kina tunanin duk bai shiryawa faruwar hakan ba? ya san girman amincin da ke tsakaninmu da kuma soyayya don haka na tabbatar yasan zaki iya irin wannan sadaukarwar a kaina kamar yadda kikayi ta soyayyar da kike masa!
ina kuma tabbatar da cewa ta inda zai bullo mana sai ta fi wannan masifa da tashin hankali a garemu!
Kaddara ce ta shigo mana muna zaman mu Aisha! kuma dole ta fada akan daya daga cikinmu ko kuma ta raba amincin mu! babu yanda zamu iya guje mata domin ta sakamu cikin tarkon da babu kofa babu matsera!
Na yarda da kaddara Aisha kuma nayi alkawarin zan sadaukar da farin cikina domin gudun faruwar batanci ga rayuwarki. Zan auri Imamu ko da hakan na nufin fadawa cikin takaici da bakin ciki da tashin hankali. ni dai nasan kome zan fuskanta ba zai kai shi zafin ganin na zuba ido wani ya bata miki rayuwa ba alhalin ina da yanda zanyi na kareki! “
Cikin dauriya Aisha tace “wannan ba zai yiwu ba Zara! sam! wallahi ba zaki auri Imamu alhalin mun san halinsa ba, ya muna ganin kashi da rana zamu taka da daddare? aure wasa ne? ki aure shi? kome zaiyi sai dai yaje yayi amma ba zaki auri mutum irinshi ba” ta sake fashewa da wani sabon kukan me bayyanar da tsantsar bakin ciki da tashin hankalin da take ciki. Dafa kafadarta nayi nace “Aisha ki rage wannan koke koken domin idan kikace kuka zakiyi toh hawayen ki zasu kare baki gama amfani da su ba, ki karfafa zurciyarki Aisha! Duk abinda ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah kuma rubutacce ne! babu yanda zamu yi sai dai muyi ta addu’a akan Allah ya fiddamu daga tarkon da muka fada! Abinda nake tunani yanzu shine email din nan da aka turomun hoton da Imamu da Jidda da kuma address din nan! shi zan bi nagano kowaye don na tabbatar koma waye a bayan al’amarin baya tare da Imamu kuma akwai abubuwan da ya sani masu yawa game da shi! ina fatan kila ta wannan hanyar mu samu wata makama, amma fa ko mun samu Aisha ba yanzun nan zamu yi amfani da ita ba, domin a yanzu idon Imamu da shirinsa akanmu suke, don haka cigaba zamuyi da shirye shirye kamar babu komai kafin lokacin!”
Dakyar na shawo kan Aisha ta daina kuka amma har yanzu ta kasa yarda da na auri Imamu akan dalilin ikirarin bata mata suna da yace zaiyi! cece kuce me yawan gaske muka yi kafin na kamo hanya na taho gida.+
STORY CONTINUES BELOW

A daren yau ko kusa dani bacci bai iya takowa ba balle ya gwada satar shi a kaina! Nayi iya bakin kokarina nayi kuka ko naji dadi na rasa hawayen, email din da aka turomun sako na dubo na rubuta sako na tura! sannan nayo alwala na soma nafila ina kai kukana a wajen rabbis samawati akan ya kawo mun dauki cikin halin da nake ciki.
Kwanaki na mirginawa lokaci na tafiya yayinda shirye shiryen bikina da Imamu yake kankama! Gashi yau ya rage saura sati uku biki, zuwa wannan lokacin nayi saranda na saddakar cewa yankewar farin cikina da rayuwa mai dadi ce tazo! na karbi kaddara kuma shiryawa ko wacce irin rayuwa a gidan Imamu, abu daya kadai ke karfafun guiwa ya sanya shi shanye damuwata ya bani kwarin guiwa, wato sadaukarwar da zanyi akan Aisha! wata mutum me muhimmanci a rayuwata wadda na tabbatar zata yimun abinda yafi haka idan itace a matsayina, sai naji farin cikin kubutar da ita da nayi daga fadawa halaka da masifar da babu me iya kubutar da itan a wannan yanayi idan bani ba. A kullum sai munyi musu munyi tababa munyi kacenace munyi fada da ita domin har yanzu ta kasa nutsuwa da hukuncin da na yanke, ita a ganinta abinda yace zai mata yafi sauki akan auren shi da zanyi! duk da tasan irin abubuwan da tarkon nashi zai janyo ta fuskanta a rayuwarta ciki harda batawa da mahaifanta, da danginta, amma sam amincin da ke tsakaninmu kawai take kallo da yanda zata kubutar dani daga fadawa bakin ciki! hakika bana jin zan samu wani mutum kamar Aisha a rayuwata wai a matsayin kawa! duka wannan badakalar da mukeyi tsakaninmu ta tsaya domin ko Ihsan ban ji zan iya gaya mata wannan sirrin ba saboda gudun yanda zata fassara maganar da tunaninta da kiyasinta! sannan itama fama take da kanta kullum bata da lafiya don ko shirye shiryen munfi magana da ita a waya! ta fannin me turo email na makara, ko kuma shima hadin bakin ne da shirin Imamu ni bansani ba! tun ranar da na dawo daga gidansu Aisha nake tura sako har yau shiru, babu amsa babu dalilinta don haka na kara saddakarwa na fallawa mai duka komai!
Mami kam zuwa yanzu bata da wani motsi ko lokaci bana shirye shirye ba! tunda ta fuskanci zan dinga yi mata cikas akan zaben abubuwa da saukaka su sai ta dena sani a ciki, domin ko kayan futar biki ganinsu kawai nayi an kirani fitting room an bani na saka bansan ta inda aka zabo su akai order ba balle kuma dinkin! Abinda kawai nasani shine naira tasha kashi! sosai tausayin Mami nake yi fiye da kaina ma , don nasan idan na shiga matsala sai ta fini shiga damuwa da tashin hankali, da ace zata gano waye Imamu da ta daura damarar yaki da duk wanda yayi kokarin kulla aure tsakanina da shi ko wanene shi kuwa ko da hakan zai sanadin tsayawar numfashinta. kaico da wannan irin kullallen al’mari mai wuyar kuncewa! inaji ina gani zan fada ramin da bansan iyakar zurfinsa da hadarinsa ba!
kwanaki biyu bayan wannan rana wakilai mata na Imamu suka kawo kayan lefena gidanmu! saitin designer wedding boxes ne guda shida kowacce saiti me guda shida! idan aka tara akwatinan gabadaya guda talatin da shida! an shake su da kayan da hankali ba zai dauka ba lokaci daya! wannan kuwa yar madaidaiciyar kit box din Luis Vuitton ce aka shako ta taf da samfuran dizayin din gwal da zinare, kama daga samfurin Dubai, bahrain, da wasu irin siraran abubuwan wuya da na kafa da hannu harda hanci na kamafanin swarosvki masu aihinin tsada da daraja! Ni da idona ban zauna ba kalli kayan ko sau daya ba amma Ihsan ta bani labarin cewa taga agogon rolex guda daya wanda kimarsa ta kai miliyan biyar! agogo guda daya cikin agogunan da aka sa acikin wannan katafaren lefen na yan karya marasa sanin menene darajar kudi da hakkokinsu! Ai kuwa kafin kice kobo duka garin Abuja ya dau maganar lefen, kan ki sake cewa kobo social media ya rincabe da hotunan akwatunan lefen da kayan da ke ciki harda shafukan bloggers da suke daukar abubuwan da ke cikin lefen suna bincika darajar shi da kiyasin kudinsa a nairarmu ta Nigeria suna yadawa! mutanen kasa aka shiga cece kuce da positive and negative comments akan wannan shiryayyun dukiya da aka lafka cikin wannan lefe ana kuma zakulo tarihinmu ni da Imamu da na iyayenmu na karya da gaskiya ana shiryawa ana yadawa! taken kowanne fefen shirin cewa suke “Money marries Money” abubuwan basu ba mutane da yawa sha’awa ba domin yana nuna tsantsar takama ne da alfahari da abun duniya! karyar tayi yawa.
Yammacin larabar da ta rage saura sati biyu bikinmu da Imamu yamun waya akan zaizo mu futa! idan ina kaunar mutuwata a yanzu to ina kaunar ganin Imamu, amma ya zanyi? mai gyaran jikin da Mami ta dauko daga chad kwanaki hudu da suka wuce na jira ta kammala kalailaye mun jikina wanda ya soma rikidewa kamar na jarirai don tsananin taushi da santsi! Tunda tazo Gwaggo tace na tattara na koma gidan Mamin sai nafi samun nutsuwa da jin dadin gabatar da shirye shirye na!
Ina toilet ina wanka a zahiri amma a badini tunani kawai nake akan yanda aurena ya kasance, a kullum na zauna na kanyi tunanin yaushe zanyi aure? wanne mutum zan aura? wanne irin shagulgula za’ai a bikina? kayan da zan saka? kalar su? brand din su? wa zatai mun kwalliya? me hotona? haka zan zauna nayi ta lissafi ina kiyasta yanda nake burin komai ya kasance wani lokacin har Aisha ta tayani! lokacin kuwa dana hadu da Imamu sai nake jin mafarkin nawa zai zama perfect kuma zai kara armashi da kayatarwa, ashe ashe akwai wani boyayyen al’amarin da zai shigo ya tarwatsa komai! ashe Imamu shine bakar kaddarar da zai fado rayuwata ya tarwatsa farin cikina! yau gashi ana ta shirin aurena babu sa hannuna ko bakina cikin zabi ko shawara ko zartarwa! don tun ana tambayata ina cewa duk abinda suka zabarmun yayi har suka gaji suka daina sani cikin sabgar tasu! sau uku Mami na zaunar dani tana son jin matsalata game da auren sai kawai nayi karyar cewa banason rabuwa da gida ne, da ta gaji da ganin hakan kamar shirme ne ta zuba mun ido ta dena bi ta kaina ta hada kai da manyan aminanta da yan’uwanta suna shirinsu!
ban ankara a toilet nake wannan tunanin ba sai da na sakarwa kaina tafasashshen ruwa sannan nayi firgigit na dawo daga hayyacina! a gaggauce na karasa wankan na futo! Na gaya muku na manta rabon da na kalli mudubi don duba kyawun shigawa ko kwalliya? toh inaga rabon da nayi kwalliya na tsaya gaban mudubi cikin nishadi kamar yanda na saba tun kafin mu tafi kano!
Yanzun ma body butter na na body shop na shafe jikina da shi ban kula ko make up kit dina ba, ko da yake kalar da fatar jikina ta koma takanfi tsabar kyau da sha’awa idan babu kwalliya akanta! amma sam ba don haka naki yin kwalliyar ba, saboda kwalliyar bata cikin tsarina ne yanzun!
brocade getzner na mai kalar baki da ratsin lilac nagani saman akwatin kayana da na taho dasu wanda rashin nutsuwa ya hanani jerawa cikin wardrobe na dauka na saka! 6pieces gown ce akamun an kawata gaban da dinkin hannu mara tada hankali wanda ya kawata dinkin! ba tare da sanin kyawun da shigar tayi mun ba na tattara gyararren gashina cikin bakin band na yane kaina da lilac din gyale ba tare da na yi wahalar daura dankwali ba! ko turare jikina baya bukata domin wannan magic chadian din ta mayar da shi kamar furen flower don kamshi! ko abu na taba ya kama kamshin kenan, wani sassanyan kamshi me kwantar da hankali da tausasa zuciya! inajin kugin shigowar mota nagane isowarsa don haka na zari jakata da waya na futo ba tare da na dauki kiran nashi ba!
Hello my people…….✌ because i am soo nice it’s not even a week💃
here is another chappy for you😘😘
Enjoy…..
we meet next week Insha Allah👍
A zaune cikin motar na same shi cikin shigar farin armani trouser, farar shirt, da wata irin blazer royal blue wadda ta fiddo da zallar fara sol din fatarshi mai kashe ido! the guy is handsome and stylish! ya samu duka wata sura mai kyau da duk dan’adam din da ya samu zai alfahari! amma kash! zuciyar baki kirin take kwatankwacin bakin duhun daren da bazai kwatantu ba! kaicon wannan sura da ta butulcewa ni’imar mahaliccinta ta zabi gode masa ta hanyar bijirewa kyakyawan koyarwar addininsa da gargadinsa! A sanyaye na karasa gefen hagu na bude motar na shiga cikin sallama!
“Good day beautiful!” ya fada kamar yanda ya saba! ada wannan yar guntuwar sentence din mai dauke da kalmomi uku cikin wani matsanancin farin ciki da nishadi take jefani, sabanin yanzu da idan naji ta nake jin wasu zafafan kibiyoyin bakin ciki na tsirar zuciyata! daurewa nayi muka gaisa tare da cigaba da hirar da shi yake ta faman zakulota har muka isa tulip bistro! my (new favourite spot in abuja!) ni kadai nake tahowa tea room na dauki lokacina ina shan shayi ina tunanin rayuwa, hakan na ragemun yawan tension din yake kaina sosai!
Bayan mun zauna an cika gabanmu da abubuwan da mukai ordering ne yake ce mun “It’s really getting late beautiful, bamuyi prewedding shoots dinmu ba!” tabe baki nayi kafin na kai lomar cinyar crispy spicy chicken da na yago da hannuna! na tauna a nutse na hadiye. na kora da lemo kafin na dago na kalleshi! “Prewedding pictures baya daya daga cikin abinda yake burgeni! kuma bana fatan ka matsamun akan lallai sai munyi please!” sosai yanayin fuskarshi ya sauya wannan murmushin yaudarar na koda yaushe ya dauke! amma sai baiyi magana ba yaci gaba da cin nashi abincin! sai da muka kammala sannan yace ” for the first time nace ga abinda za’ayi a bikin nan kikayi rejecting why? na miki laifi ne?” da ina da iko a wannan lokacin mari zan sharara mishi akan wannan tambayar rainin hankalin toh yabi duk wata kafa da zata bani damar yin hakan ya tsoshe da bakaken plans dinsa na zalinci da mugunta! sai kawai nayi murmushi nace “Babu laifin da kamun! ra’ayi ne bani da shi akan hakan! Duka hotunan da za’ayi a hakura zuwa ranar bikin mana” numfashi ya sauke kafin yace “As You wish my beautiful bride! I can’t wait wallahi i just can’t wait for our big day ” sannan ya saki wani shu’umin murmushin da zaki rantse da Allah daga cikin zuciyarsa yake futowa! kai!! anya akwai mutum mayaudari a duniya irin Imamu? Idan yayi playing wani role din soyayya sai kice daya daga cikin jaruman bollyhood director ya dorawa camera, irinsu ShahruKhan da Shahid Kapoor! in kuwa yana rausayar da kai yana rangaji to ko Ali Nuhun kannyhood albarka.+
Muna hanya wayata ta dinga ringing! a tunanina Aisha ce, don haka naki dauka domin har yanzu bamu daina mujadala da ita ba! Imamu ne yace “ki dauka mana? it may be important” don kar ya zargi wani abu na bude jakar na ciro wayar! “Big Brother” screen din ya nuna! da wide smile nayi swiping na dau kiran! cikin murna nace
“heloo! Big brother i miss you sooo much! 2days wayanka not reachable! me ya faru? yaushe zaka taho?”
cikin dariya yace “huh! Little sister when will you change? wannan questions lokaci daya?”( Tun bayan dawowarmu daga tafiyar da mukai muka kallabawa juna big brother da little sister ) cikin dariyar nima nace “huh’ uh! someone cannot miss his brother kuma? duka fa doki ne” gyaran murya yayi yace “kina jina Zara?” Anan na gano maganar da zaiyi ta gaba mai muhimmanci ce don haka nima na nutsu nace “eh inaji” sannan ya soma magana! “Naso kwarai fiye da tunaninki na taho amma wani akwai……..” cikin sauri na katse shi da cewa “big brother can i call you later? muna hanya ne tare da Imam!” cewa yayi “all right! don’t forget to call me! take care!” daga nan muka ajiye! Motar shiru tayi na wasu mintuna kafin Imamu yace “menene ake son discussing ba’a gabana ba? me ake boyemun? ina cewa nima na zama family?” dariya nayi cikin zuciyata amma a fili cewa nayi “Me za’a boye ma kuwa? hirar ce naga zata iya daukan mu lokaci me tsayi shiyasa naga gara idan na koma gida na nutsu a kira shi!” girgiza kai yayi yace “hira ko magana?” cikin kosawa da zancen nace “Duka babu wanda babu” sannan na sauya maganar da wata!
Ana kiran sallar magriba ya ajeni a gidan Mami ya tafi!
Gidan cike na same shi da kawayen mami masu zuwa tayata tsare tsare, dakyar na samu kaina daga hannunsu na shiga daki na watsa ruwa na sanya kayan bacci na kwanta! take na tuna zan kira Ya Mahmud don haka na mike na dauko wayar na dawo gadon na kwanta ina latsa lambobinsa!
bugu daya ya dauka “Hello sister kun dawo” nace “eh mun dawo na kagu naji maganar da zaka mun Allah yasa dai lafiya” cikun nutsuwa yace “No lafiya kalau sai dai nasan ba zai miki dadi ba” gabana ne ya fadi kafin nace “kuma kace lafiya kalau? menene don Allah?” sai da ya furzar da hucin bakinsa sannan yace “Little sister kiyi hakuri, bazan iya tahowa bikin ki ba” cikin mamaki nace “what? bangane ba? ba zaka zo ba? idan baka zo ba waye zaizo?” sanyaya murya yayi yace “calm down sister! kiyi shiru ki saurare ni” raina a bace nace “inajin ka” yace “yauwa my little sister! kina jina? aiki ne ya taso mun zuwa America in less than two weeks kuma yana da matukar amfani ga career na! sannan ina gamawa akwai taron da hukumar WHO zata gabatar akan cutar Ebola tare da wasu kunguyoyin lafiya na kasashen Africa! ina kammala wannan aikin akwai patient dina guda biyu da zanyi wa CS wadanda nayi wa IVF kwanakin baya! kuma ni nakeso na tsaya akan aikin!
Nayi iya bakin kokarina Zahra naga na tattara ayyukan na cire ko kwana hudu ne nazo amma ba zaiyu ba! kinga na dade ina hutu ban dade da komawa aiki ba! I don’t know ko kin fahimci ba da niyya ne nayi wannan ba” ajiyar zuciya na saki a hankali! duk da nayi matukar rashin jin dadin zuwan shi amma hakan bai rufemun ido na kasa gano uzurinshi ba! don haka nace “Na fahimce ka Brother! na gamsu! kada ka damu wallahi babu komai, kaje kayi ayyukanka a nutse ka tayani da addu’a! but you have to promise me kana kammalawa zaka zo ka ganni” Cikin tsananin farin ciki yace “ohhh That’s my girl! dadina da ke akwai tunani mai zurfi! nagode sosai da kika fahimce ni! kuma nayi miki alkawari ina gamawa da aikina zan taho Nigeria kinji? addu’a kuma ba sai kin roka ba, kullum ina yi miki sister! Allah ya baki wanda zai kula da rayuwarki cikin amana da aminci da tausasawa! Allah yasa ki cikin farin cikin da ba zai yanke ba ya baki zuri’a mai albarka” Tuni hankalina ya soma tashi da addu’o’in shi domin nasan ba suzo dai dai da mutumin da nake shirin aura ba, farin ciki kuwa tun kafin auren mukai sallama da shi balle kuma bayan na shiga gidan, na tabbatar babu abinda zai biyo baya sai tarin bakin ciki da tashin hankali da masifar da bansan iyakar su ba!
“Zara! Zara!!” firgigit na dawo daga tunanin da na tafi tare da amsawa! cewa yayi “are you okay?” nace “i’m fine Brother bacci nake ji” a sanyaye yace “okay! take care of yourself!” daga nan mukai sallama na aje wayar!
Gabadaya ji nayi gajiya da baccin da ke tare dani sun gushe! wani mugun tashin hankali ya ziyarceni!
kullum kwanakin farin cikina ne suke karewa, wacce irin rayuwa zan fuskanta a gidan Imamu? wanne irin shiri yayi wa aurenmu? wanne irin plans ya tsara a kaina? wacce ukubar yayi niyyar jefa rayuwata ciki?” wannan tunanin ya haddasawa darena kunci da tunani da radadin zuciya! har Mami ta shigo dakin, nayi maza na kulle idanuna kamar na dade da bacci, har ta kammala shirin baccin ta ta kwanta ban motsa ba!
Haka na kwana tunkur ina tunani zuciyata kamar zata balle don ciwo da radadi!
Da safe haka tashi da wani irin slight headache mai nukurkusar kwakwalwa da jijiyoyinta! haka na futo nayi breakfast a kasalance sannan mai gyaran jikina ta soma aikinta a kaina! bani na samu kaina ba sai bayan azahar sannan nayi wanka na dau mota zuwa gidan Ihsan! yau muke meeting da manyan kawayenmu akan bukin! komai na bukin Aisha da Ihsan ne suke shiryawa babu hannuna babu yawuna, sai dai na bisu da “toh” kawai! Gidan a cike na same shi da kawayena, tsoffin class mate dinmu na secondary school da kuma course mate dinmu na yanzu duk da ni na daina zuwa makarantar!
Ganinsu ya sani sakewa muka dinga hira da wasa da dariya! harda masu reharzing rawan da zasuyi na shigo da amarya da step dance! ni dai na kan bisu da ido ne kawai ina fatan dama ace wannan auren babu wata sarkakkiya acikinsa, dama babu wani boyayyen al’amari aciki, da babu abinda zai hanani farin ciki da alfahari da dombin soyayyar iyayena, yan’uwana, da kawayena suke nuna mun!
Bamu muka tashi ba sai wajen karfe bakwai na dare! sannan kowa ya nemi hanyar gidansu. tare da Aisha muka taho gidan Mami zata kwana, yawanci yanzu takanzo mu kwana tare tunda lokacin bikin ya matso kusa.
Muna shigowa na tarar da A.Laila tazo! a guje naje na rungume ta ina murna! tace “kai Zara kinga kyan da kikayi? masha Allah! sai da kin rame sosai tunanin me kike yi?” murmushi nayi nace “A. Laila babu komai inaga zirga zirga ne da rashin hutu” mun dade muna hira kafin naja hannun Aisha zuwa kitchen, don duka abincin gidan an cinye! kallonta nayi nace “me zamu dafa Aisha? cikina ba zai dau Indomie ba” dariya tayi tace “meye kuke da?” nan muka shiga bude bude muna neman abubuwan da zamuyi amfani da su! a karshe muka futo da tarkacen kayan chicken shawarma! ita na bari tana hada sauce din da za’a saka a ciku nikuma na hada mana oreo milk shake! kafin wani lokaci mun hargitsa gidan da kamshi! daga yin shawarma biyu muka buge da yin guda goma don su Mami duk cewa sukai zasu ci! a Tray muka shirya namu abincin muka futa muka bar Aya tana gyara abubuwan da muka bata.
Dakin Mami muka koma muka barbaje muna cin abincin muna santi!
“Zara jibi zanje Katsina fa?” cikin yamutse fuska nace “katsina kuma? me zakiyi a katsina?” cewa tayi “visiting din Iky!” murmushi nayi “Allah sarki Iky daman ba busy nake ba mu tafi tare! amma kema dai Aisha ba dake ake zuwa kullum ba, ki bar Umma mana taje, kina ganin yanda muke tsakiyan shirye shirye” a nutse tace “Umma ba zataje ba, kinga gobe cikin dare Daddy zai dawo kuma baza taji dadi babu wanda yaje ba” da confusion nace “ah toh ke da waye zakije babu Umma ba Daddy?” sai da tayi tsaki sannan tace “Ya Aslam mana! daga dawowanshi zai fara shiga harkokin mutane” nayi wata muguwar dariya sannan nace “amma Ya Aslam ya dawo baki gayamun ba Aisha? what kind of sister are you? kice wani love trip aka shirya aka fake da visiting” pillow ta rarumo akan gado ta jefomun fuskata! nayi maza na tare ina dariya! idan akwai wanda Aisha ta tsana babu gaira babu dalili toh Aslam ne! Aslam dan yayan Umma ne Uncle Taufeeq suna zaune Kaduna! shi ba cewa yayi yana sonta ba ma kawai he is being so nice and caring to her amma tabi ta damu kanta akanshi!
bayan na gama dariyan ne nace “ok! naji a mota zakuje?” tace “flight zamu bi sai mu dawo a mota” nace “Allah ya kaimu, ki tunamun pls kafin ki tafi gobe zan baki sako ki kai mata” tace “in ban manta ba nima” na harare ta “da yake ba ke zan baiwa ba”
mikewa tayi ta tattara duka kayan da mukai amfani da su ta futa ba tare da tace komai ba! kullum jikinta a sanyaye yake amma kwana uku zuwa yau abun yayi yawa, sai tayi shiru ita kadai kamar me tunanin wani abu idan ka tambayeta tace ita babu abinda take tunani! Duka ta saka damuwa a ranta game da aurena da Imamu, tama fini ramewa!
If you are reading this on friday, don’t forget to read suratul kahf! jumu@ Mubarak to you all!
Hausa Arab yana ci gaba yana kara zafi, domin labarin na dab da sauya akala zuwa wani abu mai jan hankali? ko menene? akwai abubuwa masu yawa da zasu faru wanda yake nuna daga yanzu ainihin labarin yake farawa! da kuma wani abu wanda zai tsuma ranku da zuciya, gaba kadan kuma wani babban abun mamakin da baku taba kawowa ba zau faru!duka dai cikin wannan labari!
ku biyoni!Bayan mun kammala gyara dakin da muka bata munyi wanka tare da sauyawa zuwa kayan bacci ne muka shiga aikin futar da kaya! kayan buki, cikin katuwar box! kwalayen takalmana, purses, da sauran accessories din da zanyi amfani dasu duka wajen daya! daya akwatin kuma traditional attire dina ne kala biyu na ingantaccen sakin fulani, bayan tailolin Mami sun shirya masa tsararren dinkin iro and buba sai suka bi saman gaban rigar da adon gashin dawisu! yanda aka shirya dinkin dole ya baka sha’awa! wannan shi zan saka ranar Kamu sai dayan kuma kawataccen hand beaded ashoke ne gold colour wanda zan sauya bayan na cire wancan traditional fulani attire din da za’aimun kamu da shi! Cikin murmushi Aisha ta bude rigar tana cewa “Zara i can’t wait naga kayan nan a jikinki! ban taba ganin kalan da yake miki kyau irin gold ba, musamman idan Banke tayi magic din nan nata akan fuskarki! Allah this year amare zasu sha kunya idan suka ga shirinmu” dariya nayi sosai sannan nace “Aisha tawa! ya kukayi da Banke din ne? ni ban tambayeki ba!” hararata tayi sannan tace “ke wa yake ta taki! tun ranar da aka saka date din bikinki nayi booking! i wanted it to be a suprise gift, amma kawai Ihsan ta ruguza mun shiri ta kama ta gaya miki!” wasu kwalla naji na niyyar tahomun na tausayin Aisha! bana mantawa a waya muka ga bridal looks na wata amarya wadda banke tayiwa make up ta saka a shafinta na instagram. nace Aisha In sha Allah da bikina matar nan ce zatai mun make up! i love her simplicity and uniqueness! wai ashe ta rike a ranta ta yi alkawarin in dai na tashi aure zatai suprising dina da ita! Duk da yanda auren yazo ba yanda muke buri ba Aisha ta tsaya tsayin daka wajen planning din komai yanda ake bukata! bata gajiya bata tuna kanta idan tana hidima a gareni! bansan wanne irin so take mun ba!+
Murmushi nayi lokacin da na tuna nawa suprise din da na shirya mata wanda bazan nuna mata ba sai ana jibi a fara buki! mun dade muna wannan aikin kafin mu hada komai inda ya dace mu sake gyara dakin! sannan muka sa hakarkarinmu akan shimfida muka kwanta! mintina biyar bayan rufe idona naji Aisha tace ‘Zara! Zara kinyi bacci?” a sanyaye nace “idona biyu!” itama a sanyaye tace “Zara will i continue to be the first person da zaki gayawa damuwanki ko matsalanki idan ya taso bayan kinyi aure? ina fatan ba zaki sauya mun wannan wajen ba, don Allah Zara komai kankantar matsala kada kiyi shiru, kada kiyi tunanin zaki magance ta ke kadai, kada ki barta a ranki, ki dinga tunawa cewa akwai ni! ki saka a ranki ko zaki gayamun damuwa guda dari kullum bazan gajiya da sauraranki ba, bazan yi kasa a guiwa wajen baki shawara ba, idan ma abun yafi karfina toh zan kai kukanki ga Allah wanda yafi karfin kowa da komai Zara, idan na kuka ne ki kirani muyi kukan tare, idan na dariya ne ki kirani muyi dariyan tare, dan Allah promise me you won’t change my place in your
heart Zara! nasan ni naja miki komai, amma…….” kukan da take hadiyewa ne ya fuzgo kansa tare da futowa da karfin gaske, har sai da ta bani tsoro! tashi nayi na zauna inajin me zanyi nima nayi kukan naji sanyi! oh!! My Lord! i just wanna cry out all the heavy loads i have been carrying cikin raina kaman yanda take yi, wata kila radadin da nake ji zai ragu!. ok but not this time,i have to be strong for my friend. A hankali na soma bubbuga bayanta cikin sigar lallashi kafin na soma magana!
“Besty meye haka wai? zaki karya mun guiwa ne kuma? ina kece support dina a yanzu? to idan kinamun kuka ni kuma me zanyi? ki kwantar da hankalinki tunda muna addu’a ni ina da tabbacin Allah ba zai kyalemu haka ba! Allah muka mikawa lamarinmu kuma shi ne kadai yasan yanda zaiyi damu! ni na karbi kaddarar auren Imamu ko ya yake Aisha da zuciya daya! kuma ina da yakinin cewa Allah zai sauya mun shi zuwa nutsatstse kuma shiryayyen nagartaccen mutum idan har Ya rubuta mun zama na dashi me alkhairi ne! addu’ar da muke Aisha da babu abinda Allah yake nufi akan aurena da shi da tuni maganar ta watse! kada muyi wa Allah shishshigi, komai yayi tsanani sauki ne zai biyo bayanshi! komai yayi zafi maganin shi Allah! please Aisha ki daina kuka, ki daina karyamun zuciya! i have made my mind, kuma ina rokon taimakon Allah! ke dai ki tayani da addu’a kawai shi nake so! And i will never ever replace anyone with you har karshen numfashina! zaki ci gaba da zama aminiya kuma yar’uwar da babu kamarta! I promise you! i promise!
Bazan iya kayyade lokacin da na dauka cikin bayanai da nasihohi irin wadannan ba kafin na samu Aisha tayi shiru ta daina kukan da take yi!
“Yanzu tashi muyi alwala muyi nafila, karfe uku ne na dare, Allah baya mayar da bukatar da aka mike aka fuskance shi aka roka a wannan lokacin! babu musu ta mike ta shiga toilet tayo alwalan sannan nima na shiga nayo tawa! in takaice muku ranar nan bamu runtsa ba ko na mintina, muna having sisters time! Wasu maganganun ma tsakaninmu ne kawai ko ku masu karatu bazan iya bayyanawa ba!
bayan munyi sallar asuba mun kammala azkar dinmu bamu koma bacci ba! wata hirar muka sake daukowa ta daban akan makowar karatun mu! Daddyn Aisha na nemar mata wani gurbin karatun a Middlesex University zata karanta medical science and technology! nayi mata matukar murna domin karatun zai debe mata matukar kewa! nima mun fara magana da Imamu akan The American University of Paris da yake mun sha’awar tafiya! tunda shima akwai babban reshen su a Paris din, zama can ba zai masa wahala ba! Amma bamu zo matsaya akan maganar ba, balle kuma mu saka manya ciki! nice ban baiwa maganar muhimmanci ba don a tunanina hakan na daya daga cikin shiryayyun plans dinsa! Inajin tsoron Imamu kuma bana mamaki ko tantama akan duk abinda akace zai aikata akan kowa ma!
Mune nan zaune har lokacin breakfast hirar bata kare ba kamar yau muka soma ganin juna inji Mami! cikin dakin Aya ta biyomu da breakfast mukayi, ni kaina ina mamakin wannan hira tamu ta yau da taki karewa kamar wanda zamu rabu zuwa nahiyoyi daban daban! Muna gama wannan maganar zamu dauko wata. sai da Jainaba mai mun gyaran jiki ta shigo har dakin ta tasa keyata sannan muka hakura!
Bamu kammala ba Ihsan ta iso gidan, lokacin kuwa babu kowa sai mu don su Mami wataran basa break din suke futa wataran kuma suna kammalawa! kamar akaina za’a soma buki a garin Abuja.
Dakyar na kwato kaina daga hannun Jainaba na shigo daki inda Ihsan da Aisha ke ta magana kasa kasa wadda na tabbatar akaina ne! banza nayi da su na shige toilet nayi wanka na futo daure da towel! still na tsaya gabansu ganin irin kallon da suke mun! “Lafiya bayin Allah?” Ihsan ce tace “kinga kuwa yanda kika koma Zara? do you look at yourself cikin mirror kuwa? kinga yanda skin dinki yayi? tabdi! ai wallahi nima matar nan sai ta ganni ko na kwana daya ne! gabadaya kin koma wata kamar ba ke ba!” tsaki nayi na girgiza kai don na tabbatar idan na tanka shakiyanci zasu shiga yi mun wanda zan kasa kwatar kaina daga hannunsu! Duk tsokanar da suke mun ban tanka musu ba har na kammala shirina cikin gown din yellow voile mai manyan pattern! na nade kaina da karamin fashmina. sannan na dauko jakata da key nazo gabansu na tsaya! “Idan kun gama ku taho, idan kuma kuna nan ni na tafi” cikin dariya Ihsan ta mike tana cewa waye yake fada da amarya ai sai mahaukaci! lallabaki zamu dinga yi kamar kwai har sai mun kaiki gidan gilashi lafiya(sunan da suka sakawa gidan da zamu zauna da Imam kenan, domin kusan rabin gidan da glass akayi shi) bance komai ba nayi gaba suka biyoni.
“Ah! ina motar ki Ihsan?” na tambaya ina duba parking space; din babu alamar motarta! a sanyaye tace “Faisal ya hanani driving! shi ya aje ni idan na gama zai dawo ya daukeni” murmushi nayi bance komai ba na danna luck din motata da remote din hannuna ta bude! baya ta bude ta shiga Aisha ta zagaya gefena sannan na tada motar muka futa! ina barin gate din na dau titi Aisha ta soma magana “kunsan kuwa jiya wani mafarki da nayi?” Ihsan ce tace “ina fa zamu sani baki gaya mana ba” ni ban ma yi magana ba don nasan watakila wata tsokanar zata mun! cikin nutsuwa tace “ba zancen wasa ba Ihsan wallahi mafarkin da nayi jiya ya bani mamaki sosai har yanzu ina tunanin shi” sai lokacin na dube ta tsaf sannan na maida hankalina ga tukin da nake nayi nace “Ki gaya mana toh kin tsaya jan rai! mafarkin me kikayi?” cikin muryar mamaki ta sake cewa “mafarkin Aljanna nayi” Nida da Ihsan muka kyalkyale da dariya lokaci daya! Aisha ce ta hade rai tace “aww mahaukacciya kuka mayar da ni?” Ihsan ce ta guntse dariyarta tace “su wane mu zamu mayar da ke mahaukacciya? bamu musha don Allah labarin gidan aljanna!” tsaki tayi ta juyar da kanta muna ci gaba da yi mata dariya! mintina arba’in da biyar muka isa gidan Rabecca! wadda muka baiwa order ta shirya mana souvenir din kawayenmu! Aikinta kenan wanda ta kware akai sai sai bala’in tsada.
Awan mu daya a gidan tana nuna mana abubuwan da ta hada tare da bukatar shawarar mu akan yanda muke so ayi packaging dinsu! Ta bude computer tana nuna mana samples muka zazzaba sannan Ihsan tayi mata transfer din ragowan kudinta! Ihsan ce ta dauki nauyin wannan bangaren, da aljihunta! Tabbas na samu aminai kawaye masu kaunata tsakani da Allah!har rige rige suke wajen faranta mun da abubuwan da suke tunanin zasu sakani farin ciki! Tunda bikin nan ya karanto babu me zama acikinsu, babu me lokacin kansa, da karfinsu, da kudinsu da lokacinsu duka sun sallama a kaina don ganin komai ya tafi dai dai kuma sun fidda ni kunya! babu abinda zancewa Allah sai godiya!
Bayan mun futo daga gidan Rabecca ne Ihsan tace mu wuce “Tulip Bistro” muci abinci! a nutse na danna signal din shan kwana ina cewa “a’a ku idan kuka liqewa waje guda daya sai kowa ya tsane shi! Toh Gidanmu zamu je zanga Dada, koma me kike so Baba Rabi zatai miki” cikin murna Ihsan tace “kin tunamun wallahi, danwaken Baba Rabi tashin hankali ne! dariya nayi tare da duban Aisha wadda yanayinta ya sauya tun lokacin da tace tayi mafarkin Aljanna muka yi mata dariya! sai naji banji dadi ba, amma nasan halin kayata, ba zata fada yanzu ba tunda bamu saurare ta lokacin da takeson fadin ba!
ana kiran magriba muka shiga gida. don haka sallah muka soma yi, bayan na gayawa Baba Rabi tayi wa Ihsan danwake, nida Aisha kuma faten doya! a dakina na barsu na isa dakin Dada, tana bakin gado tana waya, don haka na nemi wuri kasan lallausan shudiyan rug din da ke gaban gadon na zauna!
“wannan maganar mai muhimmaci ce a wajena don haka abar ta sai na ture hidindimun da suke gabana, sannan ko da wasa bana bukatar ka sanya wani cikin maganar! kuma inason kwakwkwarar hujjar da kake da ita akan abinda kake shirin yi? saboda muna son shi ba zaiyu mu tauye wa yan’uwansa hakki ba tunda dai bashi kadai bane ,” A hankali na juyo na kalli Dada don jin furucin da take yi cikin tsananin nutsuwa da maida hankali ga maganar, ko wacce magana ce wannan? akan wa kuma akeyi oho!” tunanin da na tafi ne ya hanani jin karashen maganar sai da ta dafani tana cewa “Zahra’u tunanin me kikeyi?” ajiyar zuciya na saki a hankali kafin na ce “babu komai Dada! Mami tace kina nemana”
Do you smell something coming up?
ok! crack your brain, me zai faru ne ga wannan aure? za’a yi ko kuwa?
Note maganar da Dada take yi a waya domin mai matukar muhimmanci ce nan gaba! This is just the beginning!
stay tuned!!2
Ma’assalam!
THE HOTEL @ fifth avenue,
Manhattan, New York.
_______________________________
A hankali Mahmud ke takowa cikin dakin da mahaifin na shi yayi masauki a garin New York din amurika bakinsa dauke da sallama. cikin farin ciki mahaifin nashi yake amsawa tare da jin wani alfahari na kasancewar wannan halitta matsayin da a wayenshi! Musamman yanda ya futo a tantagaryar dangayen nashi a yau. futowarsa kenan daga dakin taron karawa juna sani na manyan likitocin duniya! Dogon gayen yafi kama da kyawawan bakaken turawa a yau fiye da balarabenshi na kullum! Yana sanye cikin rantsatstsun suit yan gidan “Saint Laurent” Navy blue daga ciki farar shirt ce wadda ta fiddo da tsarin kwalliyar tashi keeping everything classy and professional! gashinsa ya wani kifo kamar kwando, dagani ya samu extra care ta musamman a wannan safiyar! Ga wani rikitaccen kamshin turarukan Ralph Lauren da suka cakude suka bada wani kayataccen kamshi mai rikitarwa! a yau kam bai yi amfani da turarensa kwalli daya da ya saba ba!
A nutse ya soma sabule bakaken covers din da ke kafarsa samfurin Calvin Klein ya jerasu inda suka dace sannan ya karaso cikin dakin yana murmushi!+
“Daddy barka da yamma” ya soma gayar da mahaifin nashi cikin girmamawa da duka guiwoyinshi a gaban farar sallayar da Daddyn yake zaune da alama sallah ya idar! cikin murmushi Daddy ya amsa kafin su soma maganar da ya hadasu a wannan waje! tiryan tiryan Mahmud ya soma koro mishi jawabi game da IMAMU da muggan boyayyun halinsa wadanda kalilan din mutane suka sani.
“Daddy bama wannan kadai ba, har yara ne dashi twins yan maza wadanda suke zaune a Paris da matar da bai taba aura ba. ba’a san wacece mahaifiyar yaran ba amma da na bincika sosai an tabbatar mun yarinyar balarabiyar Egypt ce wadda ya hurewa kunne tun suna karatu a America! a dalilinshi ta bar iyayenta kuma a garin haihuwar yaran ta rasa rayuwarta! Daddy Imam ba karamun Shaidanin mutum bane me badda kama, wanda bai san shi ba bazai taba kawo wani abu mara kyau game da shi ba balle yayi tunanin mugu ne! Tun ranar da na samu labarin shine aka sakawa rana da zara hankalina bai kwanta ba, nine bin kowacce hanya ta diddigi don hado duk wata hujja da zan gamsar da ku munin dabi’unsa da halayensa! kai tsaye bani da daman kushe shi a wajenku don ya gama siye zuciyoyinku da yaudararshi sannan ita yarinyar tayi zurfi a kaunarshi ta inda raba su lokaci guda zai zama abu mai matukar wahala, banso lokaci har ya kure haka ba, amma duk da haka nagode Allah da ba’a kai ga daura aure ba”
Shiru Daddy yayi na wasu mintina baice komai ba! Amma fuskarsa ta bayyana matukar bacin rai da disappointment mai yawa! Ta wani bangaren kuma yana ji kamar ya gaza wajen zamewa Zara uba na gari, domin gashi yana shirin kulla aurenta da gurbataccen mutum irin Imam ba tare da ya sani ba, iya bakin kokarinsa yayi bincike akan iyayen Imamu da shi kansa amma bai samu wani abu wanda bai gamsu da shi ba!
Cikin tausayi Mahmud ke kallon Daddy yana karanta zuciyarsa da yanayin fuskarsa filla filla! ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya tausasa sauti cikin ladabi yaci gaba da magana!
“Daddy kada ka damu, ba laifinka bane, kuma ba gazawa kayi ba wajen yin bincike, ba kowanne bincike ne zai gano wannan biyayyun sirrin ba sai idan an soma binciken ne cikin zargi tare da hadin guiwar wadanda Imamu yayi rayuwa da su a kasar Paris da America! Nima din nasamu duka wadannan bayanan ne a dalilin sanin wasu abokansa da nayi shekaru da dadewa da kuma wani likita Dr. Philip anan Newyork yake! ba don haka ba, da wallahi sai bayan an yi auren rayuwar Zara zata fada cikin garari! Domin Imam mutum ne mai hadarin gaske!”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya waiwaya gefen drower gado yana neman ruwa don gabadaya makoshinsa ya bushe ya tsatstsage! Dasauri Mahmud ya mike ya dauko goran ruwan da cup yazo gabanshi ya tsiyaya masa ruwan rabin cup din ya bashi! Bai bar tsugunon ba har Daddy ya shanye ruwan yayi hamdala sannan ya karbi cup din ya hada da robar ya mayar! kafin ya dawo wajen da ya tashi ya zauna!
Sun dauki lokaci mai tsayi suna tattauna wannan magana da hanyoyin da za’abi wajen daukar mataki da warware matsalar! daganan Mahmud yayi wa Daddy sallama don shi a safiyar gobe zai bar kasar America ya wuce South Africa! Lokacin da ya futa daga dakin binsa Daddy yayi da ido yana jin wani irin feelings mara misaltuwa akan shi, Tun yana yaro Mahmud mai kaifin basira da hankali ne, mai sanin ya kamata ne, mai gaskiya ne, mai jin kai ne kuma me tausayi ne! Yana da halaye wadanda za’ai alfahari da su. A koda yaushe yakan dora bukatun dan’uwansa akan nashi, ya shige gaba akan farincikin wani ya manta da nashi, koda yaushe burinsa ya faranta ran mahaifinshi!
STORY CONTINUES BELOW

Wannan ya sanya Daddy ke kara jin sa a cikin zuciyarsa fiye da duka yayan da ya haifa! Amma duk lokacin da ya tuna boyayyen sirrin da ya shekara talatin da takwas yana boyewa sai zuciyarsa ta doka! Sirrin da wani mahaluki bai taba sani ba, sirrin da yake wa adanin da tattalin da ko dukiyarsa baiwa irinsa! Amma kuma lokaci yayi dole da zaiyi wani yunkuri, wanda yake fatan samun yinsa cikin nasara ba tare da wata baraka ta bullo ba! ba tare da kwan da yayi shakara da shekaru yana rairaito ya fashe ba! Duk lokacin da ya tuna wannan al’amari bacci kan yankewa idanunsa, tunaninsa kan tsaya cak, yayinda walwalarsa take daukewa! ko yaya abubuwan zasu kasance? Allah ne masani! Addu’ar da yake dai ita zaici gaba akan Allah ya kawo masa dauki yaci gaba da rufa masa asirinsa!
ABUJA NIGERIA
———————————————————–
cikin wani irin duhu nake tafiya hankalina a matukar tashe ga wani tsoro da fargaba mara misali da ya kamani! Dajin Allah ne ko kukan tsuntsu babu balle wata halitta, bana iya ganin ko tafin hannuna balle gabana! Haka naci gaba da tafiya ina tuntube ina faduwa ina tashi, na dade cikin wannan halin kafin naji ance mun “ki nemi taimako a wajen Allah” take na fara karanto ayoyin karshen suratul bakara cikin rawar murya ina cigaba da tafiya! A hankali naga haske yana ketowa kamar hasken farin wata, da kadan kadan yana karuwa har ina iya ganin gabana, cikin dakiku kadan hasken ya kewaye ko’ina kamar an kunna fitilu! Sai lokacin naga ainihin yanda wajen yake, fili ne katon gaske mai cike da manyan bishiyu da fulawoyi kala kala masu kamshi! an musu kwalliya da kananan fitilu reshensu na wani lilo yana rangaji…….ban gushe ba cikin kallon wannan kayataccen wajen naji an kwallamun kira! dasauri na juya, sai naga Aisha! Ta futo daga wani katon gida wanda bazan iya misalta kyawunsa ba, cikin wata irin kwalliyar fararen kaya kwalliyar da ban taba ganin irinta ba balle na misalta! Na saki baki ina mamaki bakina ya gaza cewa komai har ta matso kusa dani! murmushi ne akan fuskarta madaukaki tana wani irin kamshi. sai ta kama hannuna tace “Zara! kina mamaki ko? kina mamakin yanda kika ganni ko? kina mamakin kyawun gidana ko?” cikin mamaki nake kallonta kafin nace “Aisha ya akai kika koma haka? waye ya baki wannan gida?ya akai kika zama haka?” wani murmushin tayi sannan ta riko hannayena duka biyu tace “Zara zaki ci gaba da rikemun sirrina?” Ina shirin bata amsa na farka firgigit daga mafarkin! wani irin rawa jikina ya dauka mamaki ya lullubeni, wannan wanne irin mafarki ne? me yake nufi? me zai faru? kaina yayi matukar daurewa! jingina nayi jikin gadon Mami ina tuna mafarkin dalla dalla tun daga farko har zuwa karshe! to menene haka? ina cikin tunanin wayata ta soma kara! A sanyaye na mika hannuna na dauko, Ya Omar ne! nayi swiping tare da karawa a kunnena! “Hello Zara kin taho?” ya fada! cewa nayi a sanyaye “Ya Omar i’m sorry wallahi bacci ne ya daukeni amma yanzu zan shirya na taho” yace “ohryt ki hanzarta in less 2hrs zasu sauka!” na amsa “toh ganinan” da sauri na yaye duvet din da na lulluba da shi na duro daga gadon na fada toilet. Har nayi wankan na futo nayi sallar azahar ina tunanin wannan mafarki! gabadaya jikina yayi wani irin sanyi. haka dai na shirya na dau key na futo kamar kullum su Mami duk sun futa don haka na dau motata zuwa gidan Ya Omar! Ya Sofy ke celebrating birhday dinta zamu yanka cake, daga nan zamu wuce da shi airport mu dauko ya Nuratu wadda zata dira Nigeria a yau saboda bikina!
Sai da nazo gaban motar sannan na kalli shigar jikina wadda in idan an ritsani bansan lokacin da nayi ta ba! doguwar rigar bacci na saka da ke kan gadon Mami a maimakon peach gown din Oman da na ciro na aje a gadon! lallai na bace a tunani! cikin sauri na koma gidan na sauya rigar wadda tamun matukar kyau ta kuma dace da da yanda kalar fatar jikina ta koma! mayafin da na nade kaina da shi mai duhun kalar rigar ne sannan na feshe jikina da turarukan Mami na futo cikin sauri.
Ina shiga motar na kira Aisha tare da sakala earpiece a kunnena sannan na kunna motar na soma tafiya!
“Heyyy besty ya kike?” wata ajiyar zuciya na sauke ta jindadin Aisha na lafiya domin na tsorata da mafarkin da nayi ba kadan ba! kuma har yanzu gabana bai daina faduwa ba!
“Hello Zara bakya jina?” firgigit nayi tare da cewa “Inajinki ya hanya? kun taho?” dariya tayi tace “Kema dai zara, kwana zamuyi? in less than hour ma muna Abuja” hamdala nayi ta relief sannan nace “Ok. Allah ya kawo ku lafiya besty! Ya Nuratu ma ta kusa sauka, a sanyaye tace “Allah Ya kawo su lafiya” nima yanke hirar nayi da cewa “ok! taka care of yourself! see you” a hankali tace “I love you… see you dear” kan nayi magana tayi hanging call din! ko meyasa jikinta a sanyaye? har ma maganarta? nafi tunanin gajiyar tafiya ce.
Da wannan tunanin na maida hankali kan tukina na isa gidan Ya Omar! Nayi expecting dan karamin party ne sai na tarar da gidan a cike da kawayenta da yan’uwa an ware music ana raba abinci a babban falon da yafi kowanne girma a gidan! yasha wani irin decor me kayatarwa. Nan muka shashance muna cashewa, harda kannen Imamu Yasmeen da Yusra, suma biki ne ya dawo da su! banma san ta inda suka hadu da Ya Sofy ba ban kuma damu na tambaya ba!
Ihsan ma taje, da ita muka kebe muna hira har lokacin da Ya Omar ya bukaci na futo mu tafi Airport! Tare muka futo da Ihsan muka soma aje ta a gidanta sannan muka dau hanyar Airport. Har sun sauka kafin mu isa saboda nisan Airport din! a guje na karasa na rungume Ya Nuratu cikin murna, itama ta kankameni tana cewa “i miss you soo much” sannan ta sakeni tana kallona “Zara kinga yanda kika koma amaryar tun kafin bikin? your skin looks soo fresh and flawless! me kike shafawa?” kyale zancenta nayi na sunkuya nayi scooping Amal duk nauyinta ina mata oyoyo! pecking dina tayi a kunci itama tana murna daga nan na sauke ta, ta nufi Ya Omar tana murmushi shikuma ya rike hannunta muka tafi zuwa parking space!
Gidanmu muka wuce inda murna ta runguntsume cikin gidan domin duk sun hallara suna jiran isowar mu!
Mami, A.laila, Ya Sadik, duk suna zaune a falon!
Ganin murnar taki karewa nidai na shige dakina wayar Aisha na kira tana ta ringing ba reply! nasan dai zuwa yanzu sun shigo gari,tana can baccin gajiya ko wanka! sai na wuce toilet na hada ruwa mai zafi nayi wanka ko naji dadin jikina, domin yanayin da nake ji na gaza fassara shi! gajiya ce ko rashin lafiya ni ban sani ba! ina futowa nayi sallar magrib na saka simple A.line ankara gown na kwanta akan gadona ina maida numfashi!
Bansan lokacin da bacci ya daukeni ba, wani mugun mafarki nayi wanda ya tadani a firgici na tashi zaune ina kiran sunan Allah! Na kai mintina biyu kafin na samu nutsuwa sannan na kai hannuna kan drower na dauko wayata, har karfe tara da rabi, nikuwa wanne irin bacci nayi har awaya daya da rabi?kuma ba’a tasheni ba! a sanyaye na sauko daga gadon na shiga toilet na wanko bakina don na samu na ci wani abu! sannan na dauki dankwalin kayan jikina na daura bayan na cire hular kaina na futo falon!
STORY CONTINUES BELOW

Still na tsaya ina kallon su daya bayan daya a take kirjina ya doka! Dada na kuka mara sauti tana goge hawaye, Mami idanunta sun kada sunyi jazir da waya a hannunta, Ya Nuratu ma hawayen take sharewa, yan mazan kuwa kowanne ya dafe kai fuska kamar bakin hadari! “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” nake maimaitawa a hankali cikin zuciyata bakina ya kasa samun kwarin guiwar tambayar su abinda ya faru!
Dada na ganina hawayenta ya karu Mami kam bata daga ido ta kalleni ba!
Na bude baki dakyar zanyi magana Ya Omar ya mike ya iso inda nake cikin wata irin nutsuwar da ban taba gani a tare da shi ba! kamo hannuna yayi ya zaunar zani akan kujerar da tafi kusa damu sannan ya soma magana a tausashe!
” Zara! zan gaya miki wani abu amma inaso ki tattaro duka nutsuwar da na sanki da ita ki saurareni sannan ki dayanta Allah kiyi tawakkali idan na gaya miki” ji nayi kirjina ya sake wani dokawa jijiyoyin jikina sunyi bala’in sanyi! kaina yayi nauyi. cikin rawar murya nace “Me ya faru? Ya Omar go straight to the point don Allah” ajiyar zuciya ya sauke a hankali zai bude baki yayi magana Ya Sadik ya taso ya dawo gefena cikin dauriya yace “Zara baban Aisha ne Allah yayi masa rasuwa” Rass gabana ya buga! nayi sauri zan mike sukai maza suka zaunar dani! “calm down! ki nutsu mana Zara! duk mai rai mamaci ne, kuma duk wanda Allah yayi kira second bazai kara ba zai amsa! ki nutsu kinji, ki daure ki kwantar da hankalinki!” cewar ya Sadik.
Ina ai duka jawabin da yake korowa basa shiga kwanyata, kawai tunanin halin da Aisha take ciki nake! Daddy ya rasu? ya mutu ya tafi kenan? innalillahi wa inna ilaihi raji’un” wallahil azeem bansan me ya sake faruwa ba, bansan lokacin da akace za’a tafi gidansu Aisha ba,bansan lokacin da aka yafamun mayafi ba balle nagane wanda ya yafamun din, ban kuma tantance motar da muka shiga ba, nadai nasan duka yan gidan muka dunguma muka tafi! Babu abinda nake tunani illa halin da Aisha zata tsinci kanta a ciki na rashin mahaifinsu! Mutum tsayayye jajurtacce akan iyalansa, mai tsananin kulawa da kyautatawa da taimakon al’umma! zan iya cewa ko Umma basu shaku da Aisha inda suka shaku da Daddy ba, wata irin kauna ce ta musamman a tsakaninsu bayan ta ya da mahaifi! Idan kika gansu wani lokacin zaki rantse abokai ne, wata irin shakuwa ce da fahimta mara misaltuwa a tsakaninsu! ya za’ai Aisha ta jure wannan gingimemen rashi? ta ya zata karbi wannan katuwar kaddara da ta fado mata? wa zai cike mata wannan gurbin a rayuwarta?
Ire iren tunanin da suka daukemun duka hankalin da ke jikina kenan har muka isa gidansu Aisha! gate din har ya soma cika da motoci! a raina nace “Shikenan mutuwar ta tabbata kenan”
Ji nayi an bude mun kofa Dada da kanta ke rike da hannuna muna tafiya a hankali zuwa cikin gidan su Aisha sauran na bin bayanmu!
kofar falon a bude take don haka muka shige kawai ba tare da shamaki ba, wani mugun birki naci na tsaya cak! sakamakon arangama da nayi da wata fuska! ko dai gizo nake gani? To ai idan dai ba lissafin idona ne ya birkice ba fuskar Daddyn Aisha naci karo da. kwarai shine kuma yana ganina ya fashe da wani matsanancin kuka magigici wanda ba zaka taba tunanin jarumin babban namiji kamarshi zaiyi irinsa ba! take kwakwalwa ta ta tsaya, sai na soma scanning din tangamemen falon! Umma nagani a gaban 3seater akan carpet a zaune cikin hijab idanunta sunfi garwashin wuta ruruwar ja! yan kannen Aisha guda biyu sun rungume ta suna kuka a hankali! daga daya side din Uncle Taufeeq ne da matarshi da wasu matasa guda biyu wanda ban damu da tantance inda na sansu ba! daga nan sai wasu tsirarun mutanen da ko dai ban sansu ba ko kuma kwakwalwata ta samu rauni wajen yin aikinta shiyasa na gaza ganesu!
Daga nan sai su Mami da su Ya Sadik, da muka shigo tare suka zazzauna.
har yanzu hannuna na sarke a cikin na Dada! kamar ance dubi can angle din, sai na wurga idanuna dining area, wanda aka kwashe duka kujerun aka ja tebur din gefe! mutane ne guda biyu a kwance kan babbar tabarma daya yafi daya tsayi an lallube su da farin yadi wanda yake a jike da jini!
Ji nayi kaina yana juyawa! ko dai irin mafarkin da nake yine kwana biyu ya dawo mun? a hankali na zare hannuna daga hannun Dada na soma takawa zuwa wajen dinning din a slow motion! ke kya ce acikin duniyar mafarki nake. sai da nazo dab da mutanen sannan na durkusa! A sanyaye a darare kirjina yana bugawa hannuna na rawa na bude mayafi na farko! Nan naci karo da fuskar Ya Aslam wadda ta kurkuje ta sha ciwuka babu adadi abun babu kyawun gani! da sauri na saki mayafin na mayarda hannayena kan bakina na rufe ina zaro ido!me zan gani? gawa? ya mutu?Ya Aslam? me yake faruwa? Ji nayi an dafa kafadata! na dago cikin tsananin dimuwa, makuwa, firgita, rudani da zallar tashin hankali! Umma ce ta dafani tana wani irin magigicin kuka mai tsuma zuciya da daga hankali! har wani shidewa take tana ciccijewa! Wani madaukakin tsoro da firgici suka kamani! “INA AISHA?” abinda zuciyata ta tambayeni kenan! aikuwa cikina ya bada wani sauti “kulululuuuuu” na tantagaryar tsoro da firgici! AISHA ce kadai bangani ba.
Cikin dakewa da saddakarwa a hankali na saka hannu na soma dago daya mayafin jikina na wani irin karkarwa na yaye farin yadin daga fuskar gabadaya!
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!
kunsan me nagani?!
“Fuskar aminiyata, kawata, yar’uwata wadda duk fadin duniya babu wadda na amincewa kamarta! AISHA! fuskar tas tas! tana murmushi! yayinda jini ke diga a hankali daga cikin dogon bakin gashinta yana gangarowa kan yabarmar da take kwance! Wani mugun kallo na jefawa Umma kamar zautacciya na neman karin bayani!
cikin kuka tana kankame ni cikin jikinta tace “Zara munyi rashin Aisha! AISHA ta rasu, Aisha da Aslam babu Zara! Babu su! sun Mutu!
Assalamun Alaikum my dear readers! This is the longest chapter so far!and i guess the most emotional! it felt soo real to me wallah!
kullu nafseen za’ikatul maut! duk musulmin kwarai ya sani cewa zaman jiran mutuwa yake! bamu san yaushe zata zo ba! bamu san lokacin da za’a bukace mu ba, mu muna tamu Allahu Yana tashi! TASA itace gaskiya!wanda ya tafi baiyi sauri ba, mu da muke nan bamuyi jinkiri ba! sai dai fatan Allah ya cika mana da imani!
so Ina miko ta’aziyyar Aisha ga duk makaranta HAUSA ARAB! munyi rashi babba! Zara tayi rashin aminiya tagari! sai dai muce Allah ya bata hakuri da juriya da dangana!
if you are reading this on friday, don’t forget recite surat kahfi!
Send multiples salam and tasleem to the best of Man kind!
Allahumma salli ala sayyidna Muhammadin adada mafi ilmillahi salatan da’imatan bi dawami mulkillah💚💚💚
Ma’assalam
“And now you have gone away and left us with the memories of your smile”
Kallon Umma kawai nakeyi amma kwakwalwata ta kasa fahimtar dani abubuwan da take son na fahimta! Ga dai Aisha a kwance babu numfashi, amma sam na gaza gasgatawa dagaske Aisha ta mutu! Kaina ya kasa yarda ya dau kalmar mutuwa akan Aisha! wannan karon na karyata idanuna, na karyata kunnuwana kuma na karyata duka abubuwan da nake gani a zahiri wadanda suka fi dacewa ace a fefen majigi suke faruwa.
su Mami ne suka zo suka daga Umma daga gaban Aisha suna bata hakuri yayinda karfin kukanta yake karuwa. Dada ta riko hannuna ta taso dani zuwa inda take zaune tana nazarina!
babu abinda ake wannan falon banda kuka! wasu na fili wasu na zuci, wadanda basu yi kukan kuma idan kalli fuskarsu ba zaka so ka kara ba!
Nidai na zama mutum mutumi, bana cewa uhm balle uhm uhm! Kawai dai ina jiran lokacin da zan farka daga baccin da nake har wannan mummunan mafarki ya shigo mun!
mintina ashirin bayan nan yan’uwan Daddy na Kaduna suka iso, kowanne yana shigowa zai fadi ya rafsa kuka yana jajanta wannan gimgimemen rashi na matasan guda biyu! Yan’uwan Umma ma na kusa sun zo kafin zuwa safiya iyayenta su iso daga Bauchi!
Manyan matan cikinsu harma da Dada su suka shiga cikin dakin da aka dauki Aisha aka kai don yi mata wanka da sutura! daya dakin kuma Ya Aslam! karfe gomasha biyu dai dai aka kammala hadasu! Anan ne Ya Omar da Ya Sadik sukai sallama suka tafi gidajensu da cewa zasu dawo da safe jana’iza!
Bayan an kammala shiryata ne aka kira Umma da Daddy suyi mata addu’a! ba’a samu wanda yafi wani jarumta a cikinsu ba, zubewa sukai gaban gawar suna kuka na tashin hankali mai tsuma ran duk mai saurare! dakyar aminan Daddy suka futa da shi zuwa guess room dinsa suna bashi baki! ita kuma Umma aka maida dakinta aka kwantar a dalilin suman da tayi! sannan aka kira likita.
Lokacin da na shiga dakin Aisha tsayawa nayi cak ina karewa dakin kallo! komai na zaune tsaf inda ya dace qal qal! banda katuwar rug carpet din da ke tsakiyar dakin da aka nannade aka mayar da tabarmar da aka kwantar da gawar Aisha a sankame! An nade duka jikinta da farin yadi an daddaure ta.
A sanyaye na isa gaban drower gado na bude, diary dinta ne a farko har zan ciro shi sai kuma na mayar na rufe na bude drower kasan na dauko al’kurani!
Kusa da kanta na dawo na zauna tare da tsirarun mutanen da ke dakin ciki harda Ya Nuratu da Dada! surat Yaasin na bude na soma karatuna a bayyane! babu abinda nake ayyanawa a raina sai “Idan har mutuwa kikayi Aisha dagaske, to ai babu abinda ya dace na nuna miki na kauna da ya wuce na karanta miki al’kurani a kan gawarki!” cike da confidence nake karatun siririyar murya mai taushi! sai sauran matan suka dinga bina a hankali, ina kaiwa karshen sura zan dawo farko, Nakan sabunta alwala acikin toilet din dakin nayi karatun kamar sau biyar ko shida!
Karfe hudu wasu bakin suka kuma sauka, dakin ya kara cika, amma sam ban yarda anyi magana ko da sau daya ba, karatu mukeyi gabadaya da murya guda, cikin taushi da karyewar zuciya! Dada kam casbahar ta ce kawai a hannunta tana ja, idan ta dau lokaci ta kafeni da idanunta tana mun wani irin kallo mai ma’anar “Ba’a hayyacinki kike ba”
koda minti daya ban tashi daga gaban gawar Aisha ba sai dai yin alwala kawai. har akai kiran assalatu, muka tashi mukayi sallah gabadaya, ita kuwa tana kwance babu motsi babu numfashi! a parlour mukayi sallah, muna idarwa Yan Bauchi na isowa! kakar Aisha da yan’uwan Umma maza da mata motoci shida! Nan fa gida ya kacame da sabon koke koke! Ni dai ina rakube jikin Dada ina kallon mutane dai dai kamar wata sabon kamu!
Ana cikin haka Ihsan ma ta iso! taci kuka ga gode Allah! tana ganina ta fado jikina ta sake fashewa da wani matsanancin kukan! ni dai da ido nake binta kawai tunanina a tsaye cak! Dakyar Dada ta samo kan Ihsan ta nutsu ta daina kururuwar kukan da takeyi! Babban wan Umma ne ya shigo falon ya tsaya a tsaye ya soma nasiha da nuna rashin dacewar ihu da koke koken akan gawa, ya fadi abubuwan da ya dace muyi! sannan aka samu sautin koke koken ya ragu sai masu share hawaye da shashsheka! sai masu salati da kiran Allah!
STORY CONTINUES BELOW

karfe tara na safe akayi jana’izar Aisha da Ya Aslam! lokacin da za’a futa da gawar Aisha Umma yanke jiki ta sakeyi ta fadi! Nikam ina daga cikin masu bin makarar ina mata addu’a da fatan shiga sabon gidanta a sa’a! sai da muka futo bakin gate dakyar aka dawo damu gida, wasu na kururuwar kuka wasu na hawaye wasu na faduwa! Mahaifiyar Ya Aslam itama sai asibiti akayi da ita don bata san inda kanta yake ba, gashi tana da hawan jini!
Yinin wannan ranar wani irin yini ne da ban taba ganin irinsa a rayuwata ba! ban taba ganin rana mai tsananin ta yau ba, komai ganinshi nake kamar mafarki, kamar film, kamar labari! Ina zaune jikin Dada da carbina a hannu ina ja, babu uhm ba uhm uhm! babu kuka ba dariya, ba magana sai daga kai. Duk wanda yazo gaisuwa tsakanina dashi kallo, don gani nake ina magana mafarkin da nake zai tabbata! karfe tara na dare lokacin da su Dada sukai sallama don tafiya gida, aka sakani a gaba muka shiga motar Ya Sadik. Babu abinda suke tattaunawa sai mutuwar da yanda hadarin ya faru!
“wadanda accident din ya faru a gabansu cewa sukayi kawai gani sukai motar ta kwace daga hannun driver ta soma juyi akan titi kafin tayi can gefe ta daki wata katuwar bishiya, don ma Allah ya rufa asiri bata fada ramin da ke gaban bishiyar ba, da wuta zata kama!” cewar Ya Omar!
Dada ce tai gyaran murya tace “uhm Omar ta fada rami ko bata fada ba ai bai taso ba, abinda ake gudun dai ya riga ya faru.In ajali yayi kira, babu tsumi ba dabara sai an tafi.”
Ya Nuratu tace “Gaskiya Dada an tafkawa wadannan bayin Allah mutuwa! ko da ba’a garin nan nake ba, bakiji yanda nakejin mutuwar na dukana ba, Aisha mutuniyar kirki ce, mai far’a, mai son mutane, sai dai fatan halin ta nagari ya bita! ita kuma Zara Allah ya bata hakurin jure wannan rashi!” Duka suka amsa da Amin. Mami dai kawai kallona take yi bata ce komai ba, na tabbatar itama ba karamun duka mutuwar Aisha tayi mata ba, Don Aisha ta dauke ta ne tamkar Umma, ta sake da ita sun saba sosai. to wai waye ma a family dina bai san Aisha ba? waye baisan aminta da shakuwar mu ba? waye baisan tsakaninmu ba? Duk wanda ya sanni ya sanni da Aisha, duk wanda ya san Aisha ya sanni da ita!
Mami muka soma saukewa a gidanta sannan muka wuce gida! Dada da Ya Nuratu dani, Ya Omar suka wuce gidajensu. bayan mun shiga gida dakina na wuce direct na samu bakin gado na zauna, a hankali kwakwalwata ke tariyomun mafarkin da nayi jiya da safe, da abubuwan da suka biyo baya bayan mafarkin, da baccin da nayi a dakin nan bayan mun dauko Ya Nuratu daga Airport, na gangaro lokacin da muka tafi gidansu Aisha da tunanin Daddynta ne ya mutu, na tuno lokacin da naci karo da gawar Aisha a kwance kanta na digar jini, na tuno lokacin da nake zaune a gabanta ina yi mata karatun al’kur’ani,sannan lokacin da za’a fita da gawarta, rakiyar da nayi mata har zuwa bakin gate dinsu, da yanda komai ya faru a yinin yau!
Tambaya daya ce kemun yawo a zuciyata tana mun kuwwa a tsakiyar kaina “Wai dagaske Aisha ta mutu?” duk yanda naso na mayar da abubuwan da suka faru gaskiya sai zuciya ta ta karyani, kaina yayi nauyi, tunanina ya tsaya cak! Ji nayi an dafani na dago a hankali, Dada ce rike da kofi a hannunta, batai magana ba kawai ta kafamun shi a baki, banyi musu ba na hau sha, zan rantse bansan me nake sha ba, don bakina babu dandano babu taste! Amma nafi tunanin fura ce saboda tsaki tsakin da ke ciki. nasha ya kai rabi sannan ta kyaleni, Ya Nuratu da ke bayanta itace ta matso ta mikomun kwayoyin magani da ruwa, na karba na shanye ba tare da musu ba. sannan na mayar da jikina gabadaya kan gadon na kwanta tare da rufe idanuna, bana bukatar magana, bana bukatar wani kusa dani, banason jin komai, abu daya nake buri, na farka daga wannan mummunan mafarkin da nake ciki.
Inaga karfin maganin ne ya sanyani bacci da wurwuri ba wai nutsuwar zuciya da kwakwalwa ba. bani na farka ba sai da Ya Nuratu ta tasheni ana kiran Assalatu! ina farkawa na tashi zaune cikin sauri, na soma nazarin dakina, can kan mudubi na hango wayata nayi maza naje na dauka! number Aisha na lallatsa sannan nayi dialing! a maimakon Aisha ta dauka naji muryarta kamar yanda nake tsammani, sai baturiyar mtn ce ta soma koromun jawabin cewa number da nake kokarin kira a kashe take! Na sake danna kiran, sau biyu, sau uku, sau hudu amma bata dena cemun wayar a kashe take ba!
A hankali naji an zare wayar daga hannuna, na dago idanuna naga Ya Nuratu tsaye idanunta cike da hawaye tana kallona! da muryar kusa da fashewa da kuka tace “kije kiyi alwala Zara yanzu za’ayi sallah” banyi musu ba na wuce toilet na dauro alwalar nazo na shimfida sallaya nayi sallah! daga sallar kuwa ban iya ko azkar ba, sai tunani, “Wai har yanzu ban tashi daga mafarkin ba? yaushe zan farka daga wannan mummunan mafarki mai dan banzan tsayi haka?”
BAYAN KWANA BAKWAI
Yau ce safiyar Lahadin da ya kamata ace an daura aurena da Imamu! kamar yanda iyayenmu suka buga kati suka rabawa yan’uwa da abokan arziki! Amma a maimakon haka, da sassafe muka isa gidansu Aisha da shigar da nayi kwanaki bakwai da ita a jikina ban sauya ba!
zanyi alwala nayi sallah, zanci abinda aka bani a baki, zansha magani, amma a kwanaki bakwan nan, banyi wanka ba, banyi brush ba, ban sauya kaya ba. Duk iya yanda su Dada zasuyi dani sunyi amma ko gizau banyi ba! hasali ma har yau babu wanda yaji wata kalma daga bakina, tun lokacin da na isa gawar Aisha Umma ta tabbatarmun da mutuwarta ban sake marmarin magana ba, bakina bai kuma samun karfin futo da ko kalma ba, balle ta kai ga zance me tsaho! Ya Omar ya bada shawarar a kaini asibiti Dada ta dakatar dashi da cewa dimuwa ce da fargaba, addu’a za’ayimun a jira zuwa sati daya aga abinda zai faru! Toh yau sati daya babu chanji, babu alamun nasara!
Zuwa yamma gidansu Aisha ya soma yin sara sara, domin yan’uwa na nesa duk sun dauki hanyar garuruwansu, sai Hajiya mahaifiyar Umma da aka bari zata zauna da ita zuwa kwana arba’in da kuma Yayar Umman da suke uba daya Anty Mariya! har yau idan ta juyo wa Umma faduwa take ta suma sai anyi asibiti da ita! Daddy ne dai abun yayi mishi sauki, Allah ya bashi dakewa da juriya, shi yake rarrashin kannen Aisha! musamman Iky wadda bata da aiki sai kuka ko abinci bata ci! sai yazo ya tasa su a gaba da rarrashi da magiya sannan za’a samu su dan tsakuri kadan suci!
Karfe shida ne na yamma lokacin da su Mami da Dada suke sallama da su Umma zamu tafi gida, “Har yanzu yarinyar nan bata magana?” cewar Hajiyarsu Umma! a sanyaye Mami tace “har yanzu Hajiya” cikin tausayawa Hajiya tace “toh yanzu asibiti zaku kaita ko kuwa?” Dada ce tace “Ina ganin addu’a za’a dukufa da yi a kanta! ni nasan daman ba abu ne mai sauki wajen Zara karbar mutuwar Aisha ba, ban taba ganin shakuwa da aminta irin tasu ba” Umma ce ta share hawayen dake bin fuskarta sannan tace “Kinga rashin lafiyar da Aisha tayi Hajiya kwanaki? wallahi tana kwance babu yanda take ina jiran Dadynsu mu kaita asibiti Zara tazo gidan nan, Wai na shigo dubata na samu suna hira har da kyalkyala dariya! Duk wani abu na Aisha Zara ce, ban taba ganin wanda Aisha takeso irin Zara ba, ban taba ganin soyayya da shakuwa irin tasu ba, Ni dai tunda suke tare ban taba ganin sunyi fada ba, ban taba shiga tsakaninsu akan wata magana ba, ban taba jin kansu ba! Ashe Allah ya rubuta amintar bame dorewa bace!
Ta fashe da kuka! Sai kowa ya koma share hawaye a dakin….sallamar da ba’ayi ba kenan don kowa zuciyarsa ta karye!
Gabadaya gidan Dada muka taho har da Ihsan ma! Muna isa ana kiran sallah don haka saida kowa yayi sallar sannan muka tattaru a parlour! Ni daman tun zuwanmu da na takure akan 1seater ban sake motsi ba! Ya Omar ne ya shigo daga masallaci, akan handle din kujerar da nake zaune ya zauna yana kallona cikin tausayawa! “Zara! Zara!! talk to me please!” a hankali na dago na kalle shi sannan na mayar da kaina na sunkuyar! saukowa yayi daga inda yake zaune ya durkusa a gaban kujerar ya sake cewa “Zara speak to me! kiyi magana mana Zara! kinga yanda hankalin kowa ya tashi a kanki. kiyi magana Zara!”
Kallonshi nake kawai ina tuna waye Ya Omar? abokin tsokanata wanda bama taba zama lafiya kalau, yau shine da wannan seriousness da calmness yake mun magana har da wani tsuguno a gabana! bansan lokacin da na kyalkyale da dariya ba!
Dariyar da ta baiwa kowa magigicin tsoro da fargaba da tashin hankali! shi kansa Ya Omar din sai da ya razana! falon yayi wani tsit! kamar ruwa ya cinye su! wayar Mami ce take ta kuwwa tun dazu, hayaniya bata bari taji ba sai yanzu da akai shiru! cikin sanyin jiki ta duba me kiran sannan ta kara a kunnenta! bansan me wanda yayi kiran yake ce mata ba illa dai kawai dauriyarta ta kare da kawaicinta a kaina! don fashewa da kuka tayi tana cewa “Daddy Zara ta haukace! Zara ta haukace! na shiga uku!!
Assalam my dearies! how have you been? na kyale ku ne ku gama jimamin mutuwar Aisha!
korafi yayi yawa akan cewa bai kamata Aisha ta mutu ba, wasu na cewa labari ya mutu tunda na kashe Aisha!
Kun manta cewa Rayuwa tare suke tafiya da mutuwa? sannan ba abinda kakeso yake faruwa ba ko zahiri, idan labari zai tafi sasikai babu bacin rai ba kaddara ba mutuwa ba bacin rai sai nishadi da jindadi da farin ciki meye zai zama darasi a cikinsa? meye zai dauki hankalin jama’a? meye amfanin rubutun? karku yanke hukunci akan labarin tun yanzu! domin akwai tafiya me yawa a gabanmu! Shin dagaske Zara ta haukace? This is just the beginnig! stay tuned!!
Ma’assalam!!!
1
Ranar Juma’a da misalin karfe hudu da rabi na yamma Daddy ne a babban falon baki na gidanmu tare da Ambasada, da Uncle Aliyu da Uncle Rasheed suka kammala tattaunawa akan maganar aurena da Imamu da makomarsa kafin zuwan waliyyan Imamu wanda aka shirya zaman dominsu!
Sai karfe biyar suka iso aka tarbesu cikin mutunci da karramawa da kuma girmamawa! a tunaninsu sabon date za’a saka na biki tunda mutuwa ta shigo ta gibta akan wannan da aka sa na farko! basu san cewa mutuwar ce ta hana a aika musu sammacin kiran kafin ranar daurin auren ba!
Bayan sun nutsu sun taba abubuwan motsa baki da aka cika gabansu da shi Daddy yayi gyaran murya ya soma koro jawabin da ya rikitar da waliyyan Imamu ya jefasu cikin tashin hankali! Wasu acikinsu sun san kadan daga cikin halinsa wasu kuwa ma babu wanda yake masa kallon idan an saka masa yatsa a baki zai ciza. Amma dukansu sun girgiza da jin cewa wai Imamu na da Yara har biyu a waje! wa’iyazubillahi! Gashi manyan kwararan hujjojin da Daddy ya basu ba wadanda za’a musa ko a karyata bane! A karshe Daddy ya bukace da suke suyi bincike da kansu su tabbatar kafin a sake sabon zama inda za’a yanke hukuncin makomar auren namu!+
Da wata muguwar kunya da bakin ciki da haushi sukai sallama da su Daddy suka dau hanyar gidansu Imamu wajen mahaifiyarsa don mayar da mata da yanda suka yi a gidanmu! Shi Imamu kuwa yana Paris tun ana gobe mutuwar Aisha ya tafi! a cewarsa taron bikin cikar shekarar kamfaninsu za’ayi kuma kwanaki biyu rak zaiyi ya dawo! bansan yanda akai kwanaki biyun suke kokarin juyewa sati biyu ba! wayata na dade kasheta na jefa a drower don haka bazan gane ya kira ko bai kirani ba! Mamanshi da kannenshi dak duk sunzo mana gaisuwa har sau biyu! da manyan kulolin abincinsu da katan katan din ruwa da lemo kamar za’a bude shago! su a mutuwar ma sai sunyi karya sun nuna su masu kudi ne!
Bayan Daddy ya sallami bakinsa ne suka shigo cikin gida, su Uncle Raseed cousins din Daddy sukai wa Dada sallama suka wuce masaukinsu! ya rage daga shi sai Ambasada, sannan ya yayiwa Dada bayanin yanda suka yi da waliyyan Imamu! bayan sun gama tattaunawa ya kira Ya Nuratu taje ta kirani! lokacin ina dakina akan gado na kunna laptop ina kallon graduation dinmu na makaranta nida Aisha! kwanakina biyu kenan da soma wannan kalla kallacen a system dina! bikin Ihsan ne, prom night din mu da crazy vedios din da muke da Aisha! wani lokacin kuma na shiga images dina na saka slide view na koma gefe ina kallon hotunanmu! sallah kadai ke tadani! sai idan dare yayi a bani fura ko tea da maganin bacci na kwanta! Ina tashi da safe kuwa zan dora daga inda na tsaya a daren jiya! har yanzu bazan cewa ga duniyar da nake ba, bazan ita tantance ranar da muke ciki ba, bana gane safiya yamma ko dare, komai kallonsa nake a matsayin mafarki mai munin gaske! magana kuwa tsoron yi nakeyi ba wai kasawa nayi ba, gani nake ina yin maganar komai zai zama gaske, mafarkin zai zama zahiri! nikuwa na gwammaci zama cikin wannan rayuwar har lokacin da zan farka daga wannan mafarkin mai tsananin firgici da muni da masifa da bala’i! har yau kaya daya ne a jikina ban sauya ba, idan akwai kalmar da na tsana yanzu bai wuce naji ance nayi wanka ba ko brush ko taje hardadden gashina wanda ya koma kamar na tsoohuwar mahaukaciya ba!
Ya Nuratu ta dade a kaina tana kallona kafin tace “kizo Daddy yana parlour yana kiranki.” sai da na danyi jimm sannan na dau hijab din sallah ta na saka na biyo bayanta! A hankali na zauna daga can gefen su Daddy ina muzurai, duka idanunsu a kaina suna kallona cike da tausayi da bacin rai.
STORY CONTINUES BELOW

A sanyaye Daddy yace wa Dada “ina ganin Dada acikin satin nan za’a tafi da yarinyar nan London! Ni na gaza kwanciyar hankali akan dimuwar mutuwa kawai ya sanyata haka, sai dai ko a dalilin mutuwar ta fada cikin wannan mummunan yanayin. amma Dada Zara bata da lafiya, kwakwalwarta ta samu matsala ya kamata a tunkari abun tun baiyi zurfi ba. hankalina yana tashi idan na ganta cikin wannan yanayin, Zainab ma gabadaya ta fige cikin kwanakin nan bata cikin hayyacinta! kawaicinta ne kawai ya sanya bata magana, amma itama tana so a kai Zara asibiti”
Numfashi mai zafi Dada ya furzar sannan tayi gyaran murya ta soma magana.
“Banki ta taku ba, amma ku bani kwana bakwai tukunna, akwai abubuwan da nake shiryawa a kanta. idan sati dayan yayi babu wani cigaba toh sai a shirya tafiyar”
Ba don yaso ba ya amince amma idan son samu ne shi baiki goben nan ya daukeni mu tafi London a duba kwakwalwata ba! Ambasada kam yana zaune yana goge hawaye kasancewarsa mutum mai bala’in tausayi! Nidai ina gefe a zaune har suka kammala tattaunawarsu sannan na mike na shige dakina na kwanta kan gadona ina tariyo maganganun Daddy! dagaske bani da hankali? dagaske na samu matsalar kwakwalwa? meye yake faruwa dani?
BAYAN KWANAKI UKU
Zaune nake a gaban Dada a dakinta tana shayar dani rubutun da aka kawo mata cikin katuwar jarka mai dauke da saukar al’kurani. ina kammala sha take wankeni tun daga kaina har zuwa kafata da ruwan zam zam wanda ta tofe addu’o’inta. Daga nan sai ta umarceni na kwanta kan gadonta ta kunna rediyonta ta saka mun karatun alkur’ani. yini guda abinda nake yi kenan. kwanciyar bacci ke maidani dakina. A hankali sai na soma bacci ba tare da shan magani ba, har ma na farka cikin dare nayi nafilfilu na. Maganar ma idan anyi mun nakan amsa da kai ko na girgiza kaina. sai dai har yanzu na kasa karban abubuwan da suka faru a zahiri suke faruwa kuma dagaske ne Aisha ta mutu. wannan ne abinda kaina ya kasa dauka!
———————————————————–
GIDAN SU IMAM
A babban falon gidansu Imamu ya amsa kiran kanin mahaifinshi da kuma cousins din mahaifin nashi guda biyu wadanda sukaje nema masa auren Zara! da Mummyn shi ya soma cin karo a kujerar farko ta falon fuskarta kamar hadari don bacin rai. Dakyar dattijan suka amsa masa sallamarsa wadda ya tabbatar sanin darajarta ne ya sanya su amsawar.
kallo daya Mummy tayi mishi ta gano muguwar ramar da yayi da baki, ya zama wani cool kamar ba shi ba.
Sai da ya nemi waje kan lallausan carpet din falon ya zauna sannan soma gayar da su kanshi a sunkuye. A zafafe Alhaji Mudan ya daga masa hannu yace “bamu taru anan don amsa gaisuwarka ba! mun kira ka ne don jin ko kana sane da dalilin da ya sanya iyayen Zara suka janye baka auren diyarsu? ka yarda kuma ka gamsu da duk abinda suka fada ko kuwa akwai makaman da ka shirya na kare kanka da wanke kanka daga wannan munanan miyagun halayen da aka karanto akanka? sannan meye gaskiyar labarin yaran da akace kana dasu a waje?
Wani zazzafan gumi ne ya shiga tsatstsafo masa ta ko’ina duk yanda dakin ya dauki sanyin air kwandishan! jikinsa yayi masifar sanyi yayinda zuciyarsa ke bugawa da sauri kamar zata futo daga cikin kirjinsa.
Da tsawa Alhaji Mudan yace “Bakajin abinda nake tambayarka ne Malam? kayi mana bayani domin musan ta inda zamu sake fuskantan magabatan yarinya.”
A nutse Mummy ta bude baki cikin gadara tace “Ahh Ah Alhaji Mudan wannan tsawa kamar wanda kuka samu dan yaron goye? ai Imamu ya wuce wannan titsiyewar. kuma in banda shegen munafuncin mutane yaran da suke can Paris a ajiye waye yaje ya zakulo su har ya yada labarin su? Su kuma marasa rabo har wannan ya isa dalilin da zasu janye auren da ya rage sati daya? meye aibun Imamu? a fadin garin nan kakaf sun isa su samu yaro kamar Imamu mai kyau da kudi da wayewa da Ilmi mai aibun da bai kai na Imamun ba, su kadan ma suka ji! wani idan aka bude littafin shi ba zai karantu ba”
cikin tsananin mamaki Alhaji Mudan yake kallon Mummy wani irin bacin rai da tashin hankali mara misaltuwa! da sautin da yafi kowanne zafi cikin sautin da Allah ya bashi ikon sarrafawa yace “Aww Hajiya yanzu kinsan abubuwan da yake faruwa? batun yaran da ake masa daman dagaske ne? Imam yana da yaya a waje kuma kinsan da haka? toh ko kin tura wasu neman auren shi ne anyi auren an gama bamu sani ba?”
Hankali kwance tace “Babu daya kam! kaddara ce kawai ta shigo wadda kuma bata wuce fadawa kan dan kowa acikinku ba! kuma uwar tasu tana haihuwarsu ta rasu. toh idan bamu tallafi rayuwar marayu mun basu kulawa ba me zamuyi?”
Cikin tsananin zafin rai Alhaji Hamisu ya mike, ya bar falon kamar zai fadi. domin shi yasan baida matsayin yin fadi in fada da wannan gimshakimar mata wadda tun da ran dan’uwansu ta tattare komai tayi sama da fadi da shi, ta hana shi yi musu komai, ta hana su ko shigowa cikin gidan shi su gana a matsayin yan’uwansa na jini.
Matar da bata taba kallon wani acikinsu da kima da mutunci ba.
Alhaji Mudan ji yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu, bai taba tunanin wannan magana zata tabbata ba, dalilin ma da ya nemi jin ta bakin Imam kenan, yafi tunanin masu azarzabin kai da kawo da zance ne suka kara da sharri suka gayawa su Daddy. sai gashi ga matukar mamakin da bai taba samun kansa a ciki ba, wai Hajiyar ce da kanta ke tabbatar masa da haka da bakinta, babu nadama babu kaico babu tunanin rashin kyautawa. Wai Uwa da kanta ke goyawa da baya akan lalacewa, toh ai kuwa Imamu bashi da laifi, kuma ba a kasa ya dauko wadannan halayen nasa ba, tsotsar su yayi daga uwar da ta haifeshi, yasan Hajiya mace ce mahandamiya, mai son kai, mara son gaskiya, mara kirki, amma bai taba tunanin munin halayenta ya kai haka ba. bai tsammaci cewa zata ita gurbata tarbiyyan yayanta irin haka ba. wannan abun bakin cikin da me za’ai masa misali? toh yanzu ta ya zai fuskanci waliyyan Zara da wannan abun kunyar a matsayinsa na kanin mahaifin Imamu? mutane masu daraja da mutunci da karamci? ta ya Zai wanke kansa daga kallon da zasu yi masa a matsayin wanda tarbiyyan Imamu take kansa idan babu mahaifinsa.? a takaice dai baram baram aka rabu tsakanin su da Hajiya harda zage zage. suka bar Imamu na birgima yana kuka akan su taimakeshi su rufa masa asiri ta karbo masa auren Zara domin shi yasan ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba.
babu wanda ya kalleshi suka futa gabadaya cikin tsananin bacin rai da bakin ciki.
Gaban Mummy ya dawo ya gurfana yana wani irin kuka tare da rike kafafunta, “Mummy don Allah ki taimakeni kiyi kokari su bani auren Zara, wallahi ba son yaudara nake mata ba, inason Zara tsakani da Allah, da zuciya daya, son da idan ban samenta ba wallahi Mummy zan iya rasa rayuwata”
cikin mamaki take kallon matashin dan gayen nata wanda ya maida mata rigar sakawa, ya dau wacce yakeso ya saka, ya kuma tube ya sauya da wanda yaga dama, gayen da ya karya zuciyar daruruwan yanmata, wanda mata iri iri ke ribubi da muradi, wai yau shi yake kuka akan ya mace? shi yake cewa idan bai auri Zara ba zai mutu bayan yasha cewa shi bai yarda da akwai wani abu soyayya ta gaskiya ba. Lallai wannan abun mai girma ne.
Safiyar yau tayi dai dai da kwanakin Aisha goma shadaya da rasuwa. Ina cikin dakin Dada kan gadonta a kwance sautin karatun alqur’ani daga bakin Sheikh Ahmad Sulaiman cikin Surat baqara ya cika duka dakin. A hankali nakejin karatun na karade duka lunguna da sakuna na jikina da gabobina da jini da fatata yana saukar mun da wata irin nutsuwa. Na kurawa POP din dakin idanu kamar zan karanto amsar tambayoyina acikinsu, daga bisani na lumshe idanuna ina bin karatun a hankali, a jikina naji kamar ana kallona don haka na bude idanun nawa a hankali na wurga su wajen kofar shigowa.
kifta idanun nayi tayi, ina ganin kamar ba daidai nake kallon ba! yaushe yazo?
Tsaye yake cikin shigar wankakken Valentino jeans da farar T-shirt mai tanbarin “VLTN” da bakin rubutu, wuyanshi rataye da scarf din Burberry baki.sumar kansa tayi matukar yawa da tsayi alamar ya kwana biyu bai rage ta ba, kamar an kifa masa kwando ya kara wani fari da fresh. damtsen hannunshi wani kwandalelen agogon Chanel ne sai walkiya yake kamar an kunna taurari. Take nagano cewa Designer guy ne a tsaye, Hausa Arab din Mami.
a hankali lebbana suka furta sunanshi
“Ya Mahmud!!”
Assalamu Alaikum! so here we are, remaining two to three updates kafin muyi sallamar shiga watan Ramadan!!!
have a wonderful day!
ma’assalam!Kallona yake cikin zuzzurfan nazari hannunsa duka biyu cikin aljihunan trouser dinshi. ya dade yana kallona sannan yabi doguwar rigar atamfar jikina da kallo wadda ta yamutse, ta futa hayyacinta, hular kaina tana gefena don haka cukurkudadden gashina a matukar hargitse yake kamar dai mahaukaciyyar nan sabon kamu wadda ake gudun kusantarta don kar tayiwa mutane illa. yau kwanana shadaya banyi wanka ba, balle wata banza kwalliya. toh ni kaina ma ban gama sanin halin da nake ciki ba balle na kula da kaina na gyarashi.
A nutse ya soma takowa cikin dakin ya tsaya a bakin gadon yana kallona fuskarshi dauke da matukar tausayi, jimami da tashin hankalin yanayin da ya sameni. Amma kuma bayan abinda baifi dakika biyar ba sai ya daure fuskar tamau ya soma muzurai irin wanda na gani a tare da shi farkon haduwarmu a garin Jedda! ji nayi gabana ya fadi, don ya sauya daga friendly Ya Mahmud din sa’a daya zuwa mugun nan da ya kusa karyamun yan yatsu a garin Makkah.
cikin dakakkiyar murya yace “Taso ki biyoni parlour yanzun nan” yana gama fadin haka ya juya yana huci. ai babu shiri na mike na rufo masa baya cikin tsoro.
Dada da Baba Rabi da Ya Nuratu na zaune a parlour sai duk suka zubo mana idanu suna kallon yanda film din namu zai kwashe ni da shi. “Nuratu tashi ki hadamun ruwa mai zafi a toilet din wannan yarinyar?” ji nayi cikina ya sake bada wani sauti “kululuuuu”, wato sunan nawa ma ba zai fada ba! Toh wai ko dai Ya Mahmud din yana da twin brother ne. daya mai kirki daya mugu, nafi yarda da hakan gaskiya domin big brother dina da na sani mai jin kai da tausayina ne, mai kyautatamun ne mai son sakani farin ciki sabanin wannan wanda bai san far’a ko murmushi ba, balle wata kalmar tausayi ko tausasawa.
Babu musu Ya Nuratu ta mike ta shiga dakina don cika umarnin babban Yaya. wata muguwar harara ya watsomun sannan ya nuna mun hanyar dakin alamun na shiga.
cikin tsananin tsoro na shige ina waiwayenshi don gani nake kamar zai rufeni da duka ne.
Muna tsaye cirko cirko a dakin Ya Nuratu ta futo daga toilet, sai da ta wani dan risina ma sannan tace masa ta hada. cikin daure fuskar da tafi ta dazu yace “Maza bita tayi wanka ta wanke wannan bolar da ke kanta tas, na baku mintina ashirin da biyar ina dakin nan a zaune. Ke kuma (ya dubeni) wallahi idan kikai mata gardama sai nayi miki dan banzan dukan da zan sake tayaki badda kamanninki. wuce kuje.” Ai kafin ma ya rufe baki na kutsa kai cikin toilet din domin tuni ya soma kiciniyar zaro belt din jikinsa.
A toilet babu wanda yace wa kowa komai, illa dai ta bude drower da nake aje kayan wanka ta ciro mun shot da crop top ta mikomun sannan ta saki labulen da ya zagaye jacuzzin.
A hanzarce na sauya kayan daga doguwar rigata. sai da ta daidaici nagama sannan ta zuge labulen ta soma debo tarkacen mayukan wanke kai duka na kamfanin “BODY SHOP” ta soma wanke mun gashina tana tajewa cikin nutsuwa da tausasawa. duk da haka ba karamun zafi nakeji ba amma bance komai ba. bayan ta wanke gashin ya futa tas sai ta ciro karamun towel ta nade mun shi ciki. sannan ta hada wani ruwan cikin jacuzzin ta soma cudamun fatar jikina da ke sarari. har da tafin kafata sai da ta bata nata extra care din sannan ta sake sauya ruwan ta zuge mun labule ta futa. ta zuge mun labulen tana jirana.
Ni na karasa wankan gabadaya nayi alwala kamar yanda na saba sannan na saka jibgegiyar bath robe(rigar wanka) na har kasa fara sol da ratsin gold mahadin towel din kaina duka yan gidan “VERSACE” na futo ina jin wata irin sanyayyiyar iska na kadani me salama da rahma. lallai tsabta rahama ce.
Bakina ma mintina biyar nayi ina bashi nashi extra care din da kakkarfan toothpaste da mauth fresheners don a kwanakin nan shima yaga ta kansa.
Mintuna arba’in muka kwashe kafin mu futo hannuna sarke cikin na Ya Nuratu kamar wata wadda zata gudu. Ya Mahmud na zaune bakin gado da belt a hannunsa yana jiranmu! yana ganinmu ya mike tsaye sannan yace “maza ki shirya ku futo ina parlour ina jira! don stay long!” ta amsa mishi, sannan ya kada kai ya futa.
Gaban dressing mirror ta zaunar dani ta shiga busar mun da gashina tare da shafe shi da mayukan gashi na “Body shop” masu kamshi sannan ta nade mun shi cikin band ya kwanta lambau gwanin sha’awa! barina tayi ina shafa mai da body oils da sprays masu sanyi ta koma wardrobe dina ta ciromun kaya.
Cikin minti goma na kammala shiryawa cikin sassaukan skirt and blouse na super. tana cikin dauramun dankwali ne naji zuciyata tayi wani irin bugu a dalilin kamshin da ya karade dakina! kamshin mutum daya da tafi kowa amfani da wannan kamshin, kamshin amiyinata na yau da kullum, kamshin abokiyar sirrina, kamshin turaren “Empire oud” na gidan turaren “Al musbah” wanda bata rabo da shi ako da yaushe cikin jikinta da kayanta da handbag dinta.
tuni na fizge kaina daga hannun Ya Nuratu na rugo parlour a guje ina cewa “Aisha ce! wallahi kamshin Aisha ne” sai dai kash! ina zuwa falon nayi sak, a maimakon ganin abinda nayi harsashe da doki, da murdaddiyar fuskar Ya Mahmud na soma cin karo. A hargitse na nufi kofa ina dube dube sannan na dawo kusa da Dada na zauna na kalleta jikina na tsuma nayi magana ta kashin kaina a karon farko tun bayan rasuwar Aisha! “Dada kamshin turaren Aisha nake ji! tana ina? kamshin Aisha ya cika gidan nan wallahi” wani irin murmushi tare da Hamdala Dada ta saki tana kallon Ya Mahmud. hannunta na kama nace “Dada don Allah tana ina? wallahi dagaske na jiyo kamshin turarenta Dada” murmushin fuskarta ne ya sauya zuwa wani expression na tausayi da jimami! a sanyaye ta dube ni tace “Zara kin taba ganin wanda ya mutu ya dawo? Aisha ta rasu kuma ba zata sake dawowa ba” Ji nayi gabana ya yanke ya fadi, tsoro ya kamani. shikenan ta faru ta kare! abunda nake gudu kenan nayi magana komai ya tabbata, shiyasa nafi ganewa zaman da nakeyi na mafarki, ina jiran ranar da zan farka!
Sunkuyar da kaina kasa nayi kawai nayi shiru, yanzu Aisha ta ta mutu? Aisha ta rasu? ta tafi kenan?” Ya Mahmud ne ya taso ya komo gefena suka sani a tsakiya shi da Dada. cikin murya mai taushi da tsantsar nutsuwa ya soma magana.+
“Zara look at me!” shiru nayi sai da ya sake maimaitawa sannan na dago na kalleshi! “ke musulma ce?” na girgiza kaina cikin mamakin tambayar! ya sake cewa “Duk musulmi yasan imani! kinsan menene shika shikan imani?” na gyada kaina a hankali!
yace “Good! lissafamun su” a sanyaye na soma koro karatun islamiyyata har ina tuna muryar Malam Shu’aibu mai daukarmu Tauheed da lokacin da yake mana wannan darasin
“Shika shikan imani guda shida ne! Na daya shine an tu’u mina billahi’ ka gasgata cewa akwai Allah, kasan Allah da sunayensa da sifofinsa da ayyukansa!
‘Wa mala’ikatahu’: Kayi imani ka gasgata da akwai mala’iku. wasu halittun Allah da Allah ya wakilta ga wasu al’amura kamar saukar da wahayi, saukar da ruwan sama, rubuta lada ko zunubin dan’adam, karbar rayuka da sauransu.
(Wa kutubuhi) ka gasgata litattafan da Allah ya saukar ga Manzanninsa wadanda suke koyar da dan’adam ka’idoji da iyakokin ubangiji da yanda mutum zai gudanar da dukkan rayuwarsa.
(Wa Rusuluhi) Ka gasgata Manzannin Allah da duk abubuwan da sukazo da shi.
(Wal yaumil akr) ka gasgata cewa alqiyama gaskiya ce. akwai ranar karshe ranar da za’a nunawa kowa matsayinsa na abinda ya aikata a duniya na alkhairi ko na sharri.
(Wa tu’uminu bil Qadr! Khair wa sharr) ka gasgata cewa duk abinda ya sameka daga Allah ne, ka yarda da duk abinda yazo maka mai dadi ko mara dadi ka yarda da Allah ka dogara da shi. ka karbi kaddarar ka hannu bibiyu.” ina kaiwa nan Ya Mahmud yace “barakallahu feeki! toh akan na karshe nakeso muyi magana Zara! wato kaddara! ita kaddara wani rubutu ne akan mutum wanda baya gogewa, mai kyau ko mara kyau, mai dadi ko mara dadi, idan har kana rayuwa to tabbas dole kaddara ta sameka ta hanyar da bakayi zato ba, amma me? me yake nuna kai musulmi ne na kwarai? me yake nuna ka yarda da Allah kayi imani da shi? Zara shine ka karbi ko wacce irin kaddara ce da hannu biyu ka yarda da Allah kasan cewa da ikonsa da saninsa komai yake faruwa! hakurinka da juriyarka sune abinda Allah yake jarrabawa. hakane ko ba haka bane?”
A sanyaye na girgiza kaina! yaci gaba da cewa “Akwai wanda yafi karfin Allah ya jarrabe shi?” na girgiza kai ya sake cewa “Akwai wanda yafi karfin kaddara?” na sake girgiza kaina. ya kuma cewa “Imanin musulmi zai cika babu wannan sharadin na shida acikin shika shikan imani?” na girgiza kai! yace “Toh Zara menene dalilin da yasa ke ba zaki karbi jarrabar da Allah yayi miki ba? meyasa ba zaki yarda da kaddara ba? me yasa ba zaki yarda cewa Aisha ta amsa kiran mahaliccinta ba?! Zara Kullu nafsin za’ikatul maut! Dukkan rai sai ta dandani mutuwa, kin taba ganin wanda akace ba zai mutu ba?” na girgiza kaina. yace “kin taba ganin wanda yafi karfin mutuwa?” na kuma girgiza kai yaci gaba ” Toh Aisha ta mutu, Iya wa’adin da Allah ya dibar mata na numfashi kenan kuma sun cika akwai mahalukin da zai hana?” na girgiza kai! “Ina Dadynki?” a raunane nace “Ya mutu!” yace “toh mutuwar shi ta sa kin daina rayuwa? ta sa Dada daina rayuwa ko kuwa Mami taki hakura ta bishi?” na girgiza kai! yace “idan da mutuwa zata bar wani, wa zata bari? mafi girman halittar Allah! mafi alkhairin duniya da lahira Manzon Allah SAW! Zara bamu zo mun tarar da shi ba! toh Aisha wacece ita kuma yar wacece da ba zata mutu ba?” nace “babu” yace “Zara Aisha ta tafi, ta amsa kiran Ubangijinta kuma ba tayi sauri ba, mu da muke raye bamu yi jinkiri ba, kowa da lokacinsa Zara! ita nata ne ya cika ta tafi, muma zaman jiran tamu mukeyi! don haka ki kadaita Allah ki daina wannan shirmen Allah baya farin ciki da abinda kikeyi, Allah ba zai alfahari da ke cikin bayinsa masu imani da shi ba Zara kina son haka?” Wani matsanancin tsoron Allah da imani ne ya shige ni irin wanda ban taba ji ba a rayuwata! zuciyata tayi matukar rauni tayi laushi nadama mai yawan gaske ta kamani tare da tsoron fushin Allah a kaina. a sanyaye na soma cewa “Astagfirullah! Allah ka yafe mun, Allah nayi nadamar abinda nayi, Allah idona ya rufe da kaunar baiwar da ka dauke hankalina ya gushe! Allah na tuba ka yafemun! Allah na karbi kaddararka hannu bibiyu Allah ka bani hakuri da juriyar rashin Aisha! Allah na roke ka ka bani nutsuwa ka sanyaya mun kwakwalwata da zuciyata na samu danganan karbar wannan gingimemen rashi da nayi “
a lokacin da nake wannan furucin Dada kuka ta fashe da shi, Ya Mahmud na hawaye masu dumi, Nuratu ta rike Baba Rabi itama tana nata kukan mara sauti, amma ni sam idona bai kawo ruwan ba! hawayen basu samu damar sakkowa ba duk yanda zuciyata ta karye kuwa.
cikin dauriya nace
“Ya Mahmud nagode da tunasarwar ka! nagode da kulawarka! you are the best brother anyone could ever wished for! Allah ya saka maka da alkhairi! Allah yajiqan Aisha! Allah yajiqan Aisha! Allah ya sadata da Annabin rahma! Allah ka baiwa Aisha madaukakin masauki a gidan aljanna ka haskaka mata kabarinta ka fadada mata shi! Allah kayi mata rahamarka Ya Allah”
************************************karfe daya ne na dare! Amma sam bacci ya kauracewa idanuna, tun bayan tafiyar Ya Mahmud da yamma na dawo daki nake kwance ina tunani, sallah kadai ke tayar dani, bayan nayi shirin bacci kuma na kwanta baccin yace baisan hanyar gidanmu ba.
Tunanin daren da Aisha zata tafi Kaduna nakeyi, lokutan da muka dauka a wannan dare muna hira, kayan da muka shirya na bikina a akwatina, har ta daga kayan da zansa ranar kamu tace she can’t wait taga kayan a jikina, ashe har abada ba zata gani ba, ashe mutuwa zatayi? Na tuna lokacin da muka tafi gidan Rabecca a mota da ita da Ihsan take ce mana tayi mafarki da aljanna, muka mayar da ita shashasha muna yi mata dariya har taji ba dadi, ashe wai dagaske mutuwarta ake hasko mata! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! hakika babu abinda ya kai mutuwa ciwo! ashe shikenan mun rabu da Aisha sallamar da muka yi? bazan manta wayar da na kira ta suna kan hanya ba, ta dauka tace mun sun kusa shigowa Abuja ashe ba zasu shigo ba sai dai a shigo da gawarsu?kalma ta da ita ta karshe shine “i love you” bata taba gayamun haka a waya ba sai ranar, ashe bankwana take mun. Na tuna yanda ta tsangwami kanta akan Ya Aslam bai mata komai ba, ashe wai shine abokin ajalinta! kai!! wayyo Allah rayuwa! ashe kuna tare da mutum cikinku baku san wanda zai riga tafiya ba, ashe amintar mu da Aisha ba mai dorewa bace.
ire iren wannan tunanin ne suka cika kwakwalwata taf, suka hanani ko runtse ido, kodayake 90% din memoryn cikin kaina Aisha ta cinye shi, babu wani fegi a rayuwata da bata taba ba, ko lokacin da tana raye bana rabo da tunaninta domin tana cikin duka sabgogina da mu’amalata da rayuwata. ta yaya zan iya goge wannan tarin abubuwan cikin kaina naci gaba da da rayuwa babu Aisha cikin sauki? ba zaiyu ba!wani abu ne mai matukar wuya mai bakar wahala! ban ankara ba naji an soma kiran Assalatu sai na mike nayo alwala na shimfida sallaya na soma nafila ina neman sauki da yardar Allah da amincinsa da tallafinsa a kaina.
bayan na idar da sallar asuba kuwa carbi na dauka na karanta kulhuwallahu kafa dubu hadiyya ga Aisha!
Daga haka kuma bacci ya daukeni akan sallayar sai farkawa nayi Ya Nuratu na tashina wajen 12 na rana. sannan nayi break sama sama na koma daki na kwanta naci gaba da tunanin Aisha! sai bayan sallar azahar sannan nayi wanka na zura plain gown da hijab nayi sallah! ina cikin ninke kayan sallar Amal ta shigo a guje tana “Aunt Zara i’m back” wallahi sai yanzu na tuna bana ganin ta cikin gidan! rage tsayina nayi nace “ina kikaje Amal?” cewa tayi “Abbu ne yazo muka tafi gidan Hajiya” oh sai lokacin nagane. gidan kakanninta suka tafi da babanta! hannunta na kama muka futo parlour dai dai lokacin Ya Mahmud ya shigo cikin shigar fara sol din shedda karamun dinki kansa babu hula. tuni falon ya kacame da kamshin “La NUIT” sai da suka soma gaisawa da Dada sannan muka gaishe shi!
” Zara! shirya ki rakani gidansu Aisha nayi gaisuwa”
sai da gabana ya fadi, jikina yayi wani irin sanyi kafin na mike cikin rashin kuzari na nufi dakina. abaya na dora kan rigar jikina,ko turare bansa ba duk da jikina har yanzu yana wannan azababben kamshin amarcin. na zura slippers dina na dauko waya na futo!
A hanya babu wanda yake magana illa karatun shuraim da ya karade motar cikin surat yunus! har muka iso gidansu Aisha! wani irin bugu kirjina keyi kamar wadda tayiwa sarki karya. lokacin da mukayi parking cikin gate din kuwa kamar na koma nace na fasa! A hankali nake tafiya Ya Mahmud na bayana har mukaje kofar falon na danna kararrawa. minti daya Iky ta bude! ina ganinta hankalina ya tashi, ita kuma kawai sai ta rungumeni ta rushe da kuka! sai da tayi kuka mai isarta sannan ta gayar da Ya Mahmud wanda ya nemarwa kansa wajen zama a daya daya daga cikin kujerun falon. cikin tausayawa yayi wa iky gaisuwa sai ta kama hannuna tace “ki shigo su Umma suna ciki!” hannuna cikin nata ta tunkari dakin Aisha! wani irin feeling na tasowa tun daga tsakar kaina har kafata! muna shiga na kwace hannuna na tsaya still! a sakamakon ganin yanda aka hargitsa dakin, Umma, Hajiyarta, da Yayarta ke ta aikin hada kan kayan dakin an zubo da duk kayan cikin wardrobe dinta ana sakawa a akwatina! idona bai tsaya ko’ina ba sai kan wata abaya yar swarosvki wadda ta saka ranar da ta rako Imamu school dinmu ran birthday dina! sai lokacin na tuna da Imamu da maganar aurensa da ke kaina! a hankali na isa gaban kayan na dago rigar na rungume, sassanyan kamshin Aisha ya doki hancina, wannan ba “Empire oud” bane kadai har da karin turaren oil na “AJMAL” wanda ni na siyo mata shi a Jedda na kawo mata.
Wani katon lump naji makoshina ya hada, wani abu kamar amai ya taho makoshina da gudu da karfin gaske yayinda zuciyata tayi wani irin yunkuri, kan na gane me yake shirin faruwa wani magigicin kuka ya subuce mun! Na kifa kaina akan kayan na shiga kurma kuka mai tsananin karfi da radadi da ciwo da azaba irin wanda ban taba yi ba a rayuwata! Hakika babu akwai radadin da ya kai na mutuwa babu ciwon da ya kaishi zafi da tsanani.
Bamu samu gaisawa da su Umma ba bamuyi sallama ba dakyar suka banbareni daga cikin kayan dana dinga bi daya bayan daya ina sinsinawa ina kara gunjin kukana, Hajiya ce ta dankawa Ya Mahmud hannuna tace ya tafi dani gida, Umma ta futo dakin idanunta jajawur da katon diary din Aisha ta iso gareni ta miko mun
“karbi wannan Zara! ke kadai ya dace ki aje shi a wajenki. Nasan kece kadai kikasan abubuwan da suke ciki, bazanso a kona ba, kuma bazan so na bude mata siririn ta ba!” kamar zan shide saboda kuka, haka muka futo ina layi ina rangaji muka shiga mota! Na kifa kaina kan cinyata naci gaba har muka iso gida! Nan ma cikin sauri na balle murfin motar na sunkuci diary din na nufi gida a guje, ban saurari su Dada da ke parlour ba na wuce Dakina na fada gado inajin kamar zan futo da zuciyata gabadaya nayi kukan da ita.
Ya Mahmud ne ya shigo falon cikin sanyin jiki, shima yana ta share hawaye da handkerchief dinsa. Dada ce tace “Meye ya faru Mahmud? wani abun ta sake ji?” a hankali yace “Kukan ne samun relief dinta Dada kada ku rarrasheta, rashin kukan yafi kukan illa. ku kyale ta tayi tayi zuciyarta zatayi sanyi” yana gama fadin haka ya juya ya bar gidan cikin matsanancin tausayi da karyewar zuciya! yana cikin tafiya ya samu guri ya tsaya, kifa kansa yayi akan steering wheel ya soma kuka mai tsuma rai, ba kukan Aisha yake ba, kukan nashi rashin da yayi shekaru sama da goma yake, wanda ya dawo mishi fresh kamar sabon yanka, rashin da har abada yake tunanin ba zai mayar da gurbinsa ba! Rashin Jawahir, mace guda daya wadda yayi wa son da ko a labari baiji irinsa ba, mutum guda da bacci kadai ke rabasu, aminyarsa abokiyar shawararsa at the same time matar da ya dora dukkanin burinshi a kanta! wadda lokaci daya mutuwa ta shammace shi ta dauke masa ita kwanaki biyu bayan daurin auren su!
ba zai taba mantawa da 25th april ba
wata safiya mafi muni a rayuwarsa. har karfe daya na dare suna kan waya da Jawahir suna tattauna yanda tsarin zamansu zai kasance, Shi yana so su tattara su koma London su dora akan karatunsu kamar yanda suka faro shi tare yayinda ita take son su zauna a gida. a karshe ta hakura tabi ra’ayinsa domin ita ba mutum ce mai gardama ba.
ba suyi sallama ba, batir dinsa ne ya mutu ya cillar da wayar cikin jin haushi. washegari da safe ya wayi gari da mutuwar ta, babu ciwon kai ba zazzabi, babu zato ba tsammani, ruwa take sha kawai ta kware, daga nan ta fadi, a lokacin akayi aka gama Allah ya karbi abar shi! Idan ya tuna halin da ya shiga a wannan lokaci, sai yayi ta mamakin yanda akai rayuwarsa ta saitu yanzu, har yake dariya yake kwalliya yake shiga cikin jama’a! A wancan zamanin da shi da mutum mutumi basu da bambamci, rayuwa ya dinga yi mara hope ko building future, babu goal babu target babu sa rai da wani jindadi a rayuwar gaba.+
STORY CONTINUES BELOW

karar horn ne ya karade kunneshi ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya fada, ashe a hanya yayi parking din mutane sun soma taruwa a bayansa suna jiransa! cikin sanyin jiki ya gyara parking din sannan ya zaro tissue ya soma gyara hawaye da majinar da sukai face face a fuskarsa! ya sa hannu bayan motar ya ciro goran ruwa ya kafa kai yasha sannan ya jinginar da kansa jikin kujerar motar yana mayar da numfashi a hankali.
Tunda ya koma gida Mami ta kasa gane kansa, sai yace mata baijin dadi ne ya shiga daki ya kwanta. sai da sukai waya da Dada ta gano cewa mikin zuciyarshi ne ya motsa. har dakin ta bi shi da abinci da magani ta saka shi a gaba sai yaci sannan ta shiga yi masa nasiha mai kashe jiki kafin ta kashe masa fitila ta kullo dakin. lokacin da ta futo zama tayi a kujerar parlour ta soma nata kukan, yayan nata guda biyu suna cikin zafi da radadin zuciya, musamman Zara wadda abun nata yake fresh! idan son zuciyarta ne tana kusa da ita tana jin duminta tana rarrashinta tare bata irin taimakon da ta baiwa Hausa Arab har ya yarda ya karbi kaddara yaci gaba da rayuwa ya kutsa duniya neman ilminshi. Amma bata da wannan damar sai da ta bita da addu’a kawai.
Sai yanzu na yarda cewa ashe nima ina da hawaye kamar sauran mutane, daman ance wanda yace bai iya kuka ba uwarsa ce bata mutu ba! tabbas abubuwa masu muni da taba zuciya dayawa sun faru, amma ban musu kuka ba, zuciyata na da wani irin karfi da dakewar da ba komai ne yake lankwasa ta ba, shiyasa idan na juyawa abu baya bana dawowa, bana tankwaruwa kuma bana lallasuwa.
duk yanda su Dada suka sakani a gaba suke nasiha da lallashi ban bar kukan ba, na dai yi dauriyar shanye furar da Ya Nuratu ta dama mun da kuma maganin da suka bani.
************************************1
washegari sai yamma Ya Mahmud ya rarrashi kansa ya kwakwkwafi zuciyarsa ya saita hankalin sa saboda tausayin Mami da kuma samun damar cigaba da saita yar’uwarsa.
wanka yayi ya shirya cikin yadin kufta coffee wanda akai masa cikakken aikin hannu mai kyau. bai sanya hula ba ya taje sumarsa wanda ta zubo yalo yalo har kafadunsa da keyarsa tana walkiya. ya feshe jikinsa da “la Nuit” ya futo.
Mami ya samu a parlour da tray din da aka mata lunch ta zubawa abincin ido kawai tana kallo. gani yayi yau ta tsufa a idanunshi, ba komai ne kuwa ya kawo haka ba illa tarin stress da damuwar da ke damunta. tunda yazo bataje office ba, tana gida tana hidimarshi ga tunani da tasa a gaba.
A nutse ya isa gabanta ya zauna akan carpet tare da harde kafafunshi, hannu yasa ya cire mata tagumun da tayi. murmushi ta kakalo tace “ah Mahmud ka tashi? ka futo?” bai ce komai ba ya soma zuba abincin cikin plate ya dau cokali ya diba ya kai bakin Mami. cikin taushin murya yace “Mamina eat from your son please” dole ta karba, haka yayi ta bata abincin har tace ta koshi sannan ya tsiyaya mata ruwa tasha.
murmushi yayi mai kayatarwa yace “Now Mamina please yi wanka kiyi kwalliya muje gidan Dada, Zara needs you fiye da kowa…ki karfafa mata guiwa Mami, ki bata irin kulawar da kika bani lokacin mutuwar Jawahir Mami! har yanzu tana cikin dimuwar mutuwar Aisha, bata san an warware maganar aurenta da Imam ba. wanda nasan shima ba abune mai sauki a wajenta ba, don haka ba zamu zuba ido mu bari zuciyarta ta karye ba! Zara is a strong woman! A brave lady! kada mu bari zuciyarta ta karye.”
cikin tsananin kaunar Mahmud Mami ke hamdala a cikin ranta, da ya bata damar karbar kyautar Mahmud a lokacin da aka bata shi babu musu ba jin ba’asi ta mayar da shi dan da ko ita ta haifa ba zata yi mishi wannan so da gatan ba, yau gashi ya girma ya zama abun alfaharin da duk wata uwa zatai fatan ganin danta ya zama.
babu bata lokaci ta shiga dakinta tayi wanka ta shirya cikin super ruwan goro ta nade jikinta shudiyar laffaya mai yarfin kalar super sannan ta saka flat shoe da hand bag mahadinsa. sai gata ta futo a young and beautiful Mami dinta kirarin da Dada ke mata ya fado ranta (benu bakya tsufa).
Ita ke driving dinsu har suka isa gidan Dada.
Nikam lokacin na idar da sallar la’asar ne ina kan sallaya ina addu’a ina kuka sosai, Ya Nuratu ta shigo tayi lallashi mai yawa kafin na yarda nayi wanka na sauya zuwa bakin jeans da polo shirt mustard yellow. ita ta tajemun gashina taja hannuna zuwa parlour.
Amal ce ta taso da gudu ta fado jikina tana cewa “Aunt Zara mun dade bamu yi game ba, meyasa aunt Zara bakya dariya? Mama what’s wrong with aunt Zara? is it Dada?” ta karashe maganar tana kallon mamanta.
hannunta naja muka zauna a kujera Ya Nuratu ta ciko plate da “shrimps and prawns” ta hado da oreo mikshake ta aje mun akan cinyata. tasan yana daya cikin favourites dina haka babu musu na karba na soma ci.
“Zara this people make the most wicked shrimps wallahi”
wata murya tayi magana a kaina tana tariyomun shekara daya da rabi da mukaje wani restaurant da Aisha muka ci wani “garlic lemon shrimp” sai kawai naji hawaye na sun balle suna gudu kamar an balle famfo akan fuskata.
Amal ce ta kalleni itama idanunta taf da hawaye tace “what’s wrong with you Aunt Zara? please don’t cry” kafin ta rushe da kuka. yarinyar is very emotional, little little abubuwa ke sata kuka.
kafin su Dada suce komai sallamar su Mami ta katse su. ina ganin Mami na aje abincin na mike da gudu na rungumeta tare da fashewa da wani sabon kukan! bambareni take niyyar yi daga jikinta Dada tace “Haba Zainab, kyaleta mana! wannan kunyar dai yau bana bukatar ta, aje ta zakiyi ki rarrashi yarinyar ki idan ta nutsu sai ki dauko abarki” maganganun Dada ya sanya Mami barina jikinta har muka zauna sannan suka shiga gaisuwa.
“toh babban mutum naga kamar bakin ka da magana” cewar Dada tana kallon Ya Mahmud tana murmushi.
lankwashe kafa yayi shima yana murmushin sannan yace “Dada wani dan family trip na shirya mana mu uku nake neman izini wajenki da Mami” fadada murmushinta tayi sannan tace “ka dau wajen muhimmancin maganar ka dunkule da yaren nasara me zan fahimta?” murmushi yayi sannan yace “wai da inaso na dauki Mami da Zara muje Bangkong din kasar Thailand sati biyu zuwa uku mu dan shakata”
murmushinta ta fadada sosai sannan tace “ah lallai, yayi kyau! wato ku iku zaku tsame kanku kuyi tafiyarku ku barmu toh ai babu damuwa Allah ya tsare” cikin farin ciki yace “Mamina kin yarda mu tafi?” itama murmushin tayi tace “tunda Dada ta amince sai mu tafi” ya sake fadada far’arsa ya dubi kodaddun idanuna da ke sintirin hawaye yace “little sister kinaso mu tafi? Thailand is one of the best places to visit, you will enjoy it” ina goge hawayena ina girgiza kai! Ya Nuratu tayi pouting lips dinta tace “haba Ya Mahmud wato wareni za’ayi, sai nazo na tattara na tafi tunda abun hakane” murmushi yayi yace “to Nuratu ke da zaki koma garinku? wa zai daukeki ya tafi wata kasar da ke?” cikin muryar tausayi tace “Ya Mahmud wajen wata uku fa zanyi a Nigeria idan kuma don ta baban Amal ne bashi da matsala” yana dariya yace “toh naji za’a tafi da ke ki shirya jakarki da ta Amal ki bani passport dinku” wani dadi ya kamata harda tsalle. ni dai kallonsu kawai nakeyi ina tunanin randa zanji wannan genuine farincikin a rayuwa bayan mutuwar Aisha. ana jikin maganar ya Omar suka shigo da Ya Sadik! nan fa sukai tsallen albarka sai sunje! Ya Mahmud ya bata rai yace “bana son shashanci! daga jin magana sai ku like mun? dan family time zamu je mu samu haba! ai kuna da iyalai kowa ya dauki matarshi ya tafi inda yakeso amma ba zaku bimu ba” Dada me zatai ba dariya ba. nan fa jayayya ta sarke.
Ana haka sabon maigadinmu yayi sallama ya shigo yace da akwai bako a waje! Dada tace ya shigo dashi.
mintina uku akayi sallama! dagowar da zanyi naci karo da wani irin madaukakin mamakin da ban taba tsammani ba! kunsan me nagani?
Imam ne! cikin wasu yamutsatstsun kayan da babu tantama sunyi kwanaki bakwai a jikinshi! yayi baki ya rame gashinsa buzu buzu. kai sa ka rantse ka kuma ba wannan tantagaryar dan gayen mai baiwa sutura kunya bane. kafin mu futa daga cikin shock din da muke ciki ya kifa guiwoyinsa a kasa ya soma hawaye
“don Allah don Annabi don darajar mahaifanki Dada ki amince kiyi hakuri ki bani auren Zara! wallahi idan ban aure ta mutuwa zanyi”
tikisa! kaina ne ya daure tamau na soma mintsilin fatar jikina naji ko dai mafarki na sake yi ne irin wadanda nakeyi a wannan lokutan??
Dan! Dan!! Dan!!! me zai faru?