HAUSA ARAB CHAPTER 8
Washegari da safe ina tashi na kira Mami muka gaisa, nutsuwar da naji cikin muryar ta ya kwantar mun da hankali sosai, duk da ina matukar son magana da Ya Mahmud, har yanzu na rasa karfin guiwar yin hakan. Na rasa ta yanda zanyi nayi magana da shi kuma me zance masa? Sai kawai nayi sallama da Mami ba tare da tambayan shi ba duk da na san cewa suna tare a wannan lokacin suna kalacin safe.
Bayan mun ajiye wayar nayi kasake ina ganin rashin kyautawa ta akan kin magana da shi amma duk yanda zanyi na tursasa kaina sai na kasa.
A maimakon haka sai na kira Dada na gaishe ta sannan Ya Nuratu da Ihsan. Shi ma Daddy na kasa yi masa wayar har yanzu, na rasa me yake damuna nake jin wannan yanayin. Da naga tunanin ba zai yi mun ba sai na mike na shiga toilet nayi wanka na shirya na futo.+
Babu yanda Inna Asma’u bata yi dani a rakani gidajen ýan’uwa na gaishe su ba nace gaskiya bazan iya shiga wannan kwalleliyar ranar ba. Allah yana kallo ban saba shiga rana ba kuma jikina baya so don haka ina kallon A.laila take sintirin ziyara taje can taje nan ko da wasa ban rakata ba. Nace da Baba sai lokacin da garin yayi sanyi zan dawo a rakani ko’ina. Dariya kawai yayi yace
“Da na sani a garin nan nayi miki miji na aurar da ke! Sai muga karyar hutu da zaman Abuja”
Ban taba tunanin zan iya tafiya babu Dada ko Mami na samu nutsuwa na sake ba sai wannan karon, bana jin ko America na tafi zan samu irin wannan nutsuwar da nake ciki. Ga abincin Inna Asma’u mai ďan karen daďi daman kunsan ni duk inda abun kusa da baka yake ina nan. Har wata qiba nayi mai kyau nayi haske saboda kwanciyar hankalin da na samu a wannan lokacin na daďe ban samu irin shi ba.
ABUJA, NIGERIA
……………………………………………………………….
Cikin waďannan kwanakin duk wata kauna da soyayya da kulawa da kwantar da hankali Mahmud ya samu a wajen mutanen da suka fi kowa kusanci da muhimmanci a gare shi. Saboda haka damuwar da yake ciki ba tayi tsamarin da ta tayar mi shi da ciwon shi ba. Duk da cewa tun daga wannan ranar da ya san cikakken asalin sa babu abinda yake ran shi irin tunanin mahaifan shi, da wata irin bukatar ganin su ko da kuwa a hoto ne.
Sannan yana son ya binciko inda dangin mahaifin sa suke saboda tamburan da aka soma kaďa masa akan rashin tabbacin halaccin haihuwar sa. Zai iya daure komai amma baya jin zai iya tsayawa ya fuskanci wannan kalubalen na kiran shi da kalmar “shege” da mutane suka fara yi. Mutum ne shi wanda yake matukar kare mutunci da alfarmar sa da iyakacin karfin sa da ikon sa, zuba idanu yana ji yana kallon waďannan zantukan zasu iya yi masa illar da zuciyar sa ba zata iya jurewa ba. Amma ta ina zai soma binciken? Yaya zaiyi ya fuskanci Daddy yace yana son ya fara neman dangin mahaifinsa ba tare da Daddyn yaji ba daďi ba? Ta ina zasu soma binciken idan zasu yi kuma lallai ne ya samu nasarar sake saduwa da mahaifin shi? What if shi mahaifin na shi ya daďe da mantawa da shi yaci gaba da rayuwar shi da ýaýan shi da dangin shi? Idan suka ki karbar shi fa?”
Irin waďannan tunune tunane da tambayoyin ke dakusar da duk walwalar shi, su suke hana shi samun karfin guiwar cigaba da murmushin shi, su suke hana shi zama cikin mutanen yayi hira yayi wasa da dariya kamar yanda suke bukata a wajen shi.
Shi kan shi ya san a wannan lokacin he needs space! Yana son kaďaicewa shi kaďai yayi tunani akan wannan sabuwar duniyar ta shi! Yana son kaďaicewa a wajen da babu kowa babu hayaniya sai shi kaďai da tunanin sa.
Toh tsananin overprotection na Mami ba zai bari ta bar shi ya ďara ko’ina daga kusa da ita ba a wannan halin balle ya batun barin Nigeria.
Iya takura a takure yake, iya dauriya kuma yana yi kar a gane gazawar shi da damuwar shi. Amma zuciyar shi babu abinda take yi a wannan lokacin sai zogi da raďaďi da ciwo mai azabtarwa. Ji yake yi kamar ya rufe idanu ya buďe ace masa duk abubuwan da suka faru mafarki ne.
Duk da haka ba zai ce da kulawa da soyayyar da yake samu a wajen su Mami komai ba, ta taimaka masa kwarai wajen rage masa strange feelings ďin da yake ji a jikinsa idan yana cikin su, suna kokarin dusashe masa wannan tunanin da yake tsorata shi na cewa
STORY CONTINUES BELOW

“babu alakar jini a tsakanin sa da su”
Kuma sun karbe shi, sun yarda da shi suna fatan cigaba da kasancewa da shi a hakan yanda yake. So far Zara ce kawai bai ji daga gare ta ba and he is highly disappointed! A gaban sa take kiran Mami ko tambayar sa bata yi, ya zata tana ďaya daga cikin waďanda zasu zauna kusa da shi su bashi baki, sai yaji labarin ta ma tattara kayanta ta bi Baban Mami Kurfi watakila saboda bata goyon bayan shi ko kuma ta tsane shi.
Gefe ďaya Amina na ba shi support da kwarin guiwa, da duk wata kulawa da zata hana shi shiga damuwar matsananciya. Ta tabbatar masa da cewa tana tare da shi a kowanne hali a kowanne yanayi a kowanne zamani kuma zata taya shi fuskantar kowanne irin kalubale a rayuwa. Bai taba tunanin cewa tana yi mi shi irin wannan son ba, kuma shi ma sai yanzu ne ya tabbatar da cewa yana matukar son Amina fiye da yanda yake tunani a baya. Ashe ba son Safna yake yi ba shirmen ta ne kawai yake burge shi, yanda yake jin Amina kamar sabuwar Jawahir aka kawo masa. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa da zurfin tunani kuma ta damu da shi fiye da misali don haka yake ganin zai iya fuskantar kowanne irin challenge tare da ita gefen shi. Ta kan kira shi sau goma a rana, wani lokacin idan tace
“How are you? When last did you smile? Ok smile for me now”.
Ba ya sanin lokacin da ya ke tuntsirewa da dariya. Sai ta kashe wayar taci gaba da harkokin ta, sai bayan awanni biyu ko uku zata sake kira ta kuma yi mi shi wata tsokanar.
……………………………………………………………….
BAYAN SATI ĎAYA.
Wanda yayi dai dai da saura sati uku bikin mu, don ma an kara sati biyu ne a dalilin rashin lafiyar Ya Mahmud da tuni nextweek ne.
Ranar da muka dawo Abuja da safe gidan Dada muka wuce gabaďaya. Ya Nuratu da Amal sai murna, da yake ambassador yace ta zauna ta haiwu a gida. Anyi sa’a Amal tana hutu don haka suka kara bararrajewa a gidan Dada suna kwasar garar girkin Nigeria a wajen Baba Rabi.
Bayan sallar azahar sai ga Daddy da amsabasada sun iso, sun daďe a ďakin Dada sannan naji Daddyn yana yi wa Mami waya wai suzo ita da Ya Mahmud yanzun nan. A raina nace wannan meeting na ga ranar kare shi, na shiga toilet nayi wanka na futo ina tsane jikina waya ta ta soma kara. Mubarak ne
Cikin murmushi na ďauka tare da sallama.
“Sweetheart ya kike? “
“I’m good how are you?”
Yace
“I’m missing you! I’m on my way to see you”
Cikin dariya nace
“Oh really?”
Yace
“Yes! Ina cikin jirgi yanzu haka! Zan sauka da yamma! Zan huta zuwa magrib, by 7 zanzo na ganki”
Nayi murmushi sosai nace
“Oh i feel honoured! Allah ya kawo ka lafiya!”
Daga nan muka yi sallama na ajiye wayar ina tunanin yanzu wai bikin mu saura sati uku.
Bayan na kammala wanka na kira Ihsan na gaya mata cewa zanzo gidanta mu haďu da Mubarak saboda gudun kada Ya Mahmud yazo mu haďu da shi. Ina tsananin jin kunyar haďa idanu da shi bayan abubuwan da duka faru, na kasa samun kwarin guiwar kiran shi ko a waya ne na nuna mi shi kulawata da tabbatar masa ina goyon bayan sa. Balle kuma na takw zuwa gidan Mamin na gan shi bayan Sarai na san yana can.
Ina gamawa na mike na shirya cikin kyakykyawar kwalliyar da take dacewa da jikina na kawo designer perfumes masu sanyi na feshe jikina sannan naje nayi wa Dada sallama. Na shiga motata kenan na tsinkayi wani text layi biyu kacal amma ruďin da ya saka ni ciki Allah ne ya san iyakar shi.
“Zara mu haďu a dunes center in 30 min. Billahil azeem abinda zamu tattauna mai matukar muhimmanci ne”
Sakon ya futo ne daga lambar wayar Imamu! Hankalina sai ya rabu biyu, ďaya na gasgata cewa ba zai cutar dani ba yayinda ďaya tunanin nawa ke gargaďina akan kada nayi saurin yarda da shi.
Dakyar na tayar da motar na bar gidan cikin sanyin jiki, sai dai bansan yanda akayi ba sai tsintar kaina kawai nayi a korar dunes center. Bayan nayi parking ne kawai na tsinkayi Imamu a gefena yana buga mun glass. Cikin dauriya na cire masa lock ya zagaya ya buďe kofar gefen mai zaman banza ya shigo ya zauna.
Abu biyu suka sanya naji hankalina ya kwanta da shi.
Na farko bai futo a old Imamu mai kallona kamar zai cinye ni ba.
Na biyu shi ne wani irin seriousness da nutsuwa ne a tattare shi irin waďanda ban san shi da su ba.
Kafin nayi mi shi magana ya katse shirun mu da soma magana ba tare da ko gaisawa mun fara ba. Tunda ya fara yi mun bayanin abinda ya sanya yace nazo jikina ya ďauki rawa kamar mazari. Hankalina ya kai karshen kololuwar tashi yayinda wani irin tsoro da bakin cikin suka baibaye ni.
Bai bata lokaci ba ya buďe jakar laptop ďin da ya shigo rataye da ita ya kunna sannan ya nuna mun abinda ya kusan ďauke mun numfashi saboda tsabar gigicewa. Hankalina ya ninka ďazu tashi, kaina yayi masifar nauyi. Bai bari na kammala kalla ya ba ya kashe ya mayar da ita cikin jakar ta sannan ya gyara zama ya soma yi mun bayani dalla dalla.
“Zara ban yi yunkurin sanar da ke halin da kuke ciki ba har sai da na tabbatar akwai taimako da agajin da zan iya baki. In my life, ban taba son wani abu kamar yanda naso ki ba! Kuma bana jin zan samu. But this is my past kuma nayi accepting kaddarata da hannu biyu, amma nayi wani alkawari cewa yanda na karya miki zuciya zan dawo nayi fixing ta hanyar da zaki yarda cewa lallai ni ďin sabon mutum ne ba Imamun da kika sani ba.
Yanzu abinda nake so da ke shi ne kiyi hakuri kiyi matukar dauriya don Allah Zara kada ko da wasa ko bari wani gane kinsan wani abu komai kankantar shi cikin wannan magana. Hakan ba karamun hatsari bane, sannan kiyi takatsan-tsan da abubuwan da zan gaya miki kuma ki zuba idanu a kai.”
Mun kai a kalla awanni biyu da Imamu muna tattaunawa kafin yayi mun sallama ya shiga tashi motar. Kamar yanda ya gaya mun ina futowa daga cikin gate ďin na ga abinda ya sake gasgata hajjojin Imamu kaifafa.
A yau kam ban bata hawayena ba saboda sanin cewa kukan ba shi ne solution ba a wanan gabar. Na kuma jinjinawa kokari da soyayyar Imamu a gare ni tare da hamdala ga ubangiji da ya sanya wannan al’amari bai zo mun a makaren da ba zan iya gyarawa ba.
Daga nan na wuce gidan Ihsan duk jikina babu amma daďi amma sai nayi matukar kokarin daurewa domin this time ko ita Ihsan ďin bana bukatar ta san wani abu game da wannan al’amari.
Karfe 7 dai dai Mubarak ya shigo cikin gidan, sai dai kamar ba shi ne wannan da muka yi wayar yana nishaďi da farin ciki ba. Duk yanda yaso boye damuwar shi kallo ďaya zaka yi ka gane yana cikin ta. Nima kuma dole na san zai gane akwai abinda yake damuna amma babu wanda yayi yunkurin yi wa ďaya tambaya akan haka.
Assalam dearies,
Kuyi da hakuri kwana biyu shiru babu update.
Don Allah ku saka kakarmu a addu’a yau kwanakin ta takwas da rasuwa.
Allah yayi mata rahama ya sada ta da Manzon Allah saw tare da sauran waďanda muka rasa gabaďaya.
Nagode.
Duka tattaunawar da muka yi yau masu muhimmanci ne, domin akan auren mu ne da tsarin family ďin shi da kuma yanayin zaman da zamu yi da matar shi duk da ba gidanmu ďaya ba.
Ni dai da “toh” kawai nake bin shi saboda har yanzu kamar almara haka nake jin maganar auren nan nawa da Mubarak in three weeks. Har yanzu bana jin wani feeling na cewa lallai auren zamu yi da gaske kuma shi ďin zan aura. Idan na gaya wa Ya Nuratu abinda nake ji cewa take yi.
“Naji fiye da wannan abun Zara! Saboda ni kawai wayar gari nayi a wata kasa ina rayuwa da mutumin da gani na da shi sau biyu ne tak kafin a ďaura mana aure. Ko wayar da muka yi zan iya kirgawa saboda a lokacin yana cikin exam ne, karewa ko bikin babu shi akayi sai ďaukata aka yi aka kaini kamar ýar Sadaka. But ba gashi ya wuce ba? A lokacin gani nake yi kamar an zubar mun da mutunci da daraja kuma ba’ai mun adalci ba, but yanzu I can proudly say marrying him is the biggest blessing in my life. Ba kowanne lokaci ne abinda kake so yake zama alkhairi a gare ka ba Zara! Sometimes you just have to let go abinda kake so komai son da kake mi shi and accept your faith, babu mamaki wannan wanda bakya wa kyakykyawan zaton shi zai juya ya zama amsoshin addu’o’in ki a dunkule”+
Ire iren waďannan nasihar ta Ya Nuratu ke bani hope da kwarin guiwa akan aurena da Mubarak ba wai soyayyar da nake mishi ba. Domin batun soyayya tun lokacin da Imamu ya karya mun zuciya nake kokarin healing daga ciwon, zuwa mutuwar Aisha wadda ta karasa shattering ďin zuciyar tawa into million pieces. Jinyar zuciyar nake yi cikin dabara da tausasawa domin idan na matsa mata da yawa zata iya bugawa kowa ya huta.
A cikin kwanaki ukun da suka biyo baya bani da aiki sai waya da Imamu da bincike akan al’amuran da muka sanya a gaba. Daga ni har shi hankalin mu a tashe yake matuka, ga wata mai gyaran jiki da aka lakaba mun mai shegen naci da cinye lokaci. Idan nayi complain Ya Nuratu da A.laila wadda ta dawo gidan Dada kacokan saboda shirin biki su sanyani a gaba suna kabli da ba’adi.
Don haka mun fi samun time da daddare, idan kuma na gama wayar bana bacci addu’a nake zama ina yi har a kira sallar asuba domin sanin cewa komai yayi zafi maganin shi Allah. Addu’a ce ta kubutar da ni daga hannun Imamu a wancan lokacin gaskiya ta bayyana haka nake fatan yanzu ma idan auren Mubarak shi ne alkhairina Allah ya shige mun gaba ya zama gatana ya kaďe mun dukan fituntunun da nake jin tsoro.
Washegari aka kawo kayan lefena daga gidansu Mubarak, 16 boxes ne na DKNY an cika su da abun arziki. Sai wata karamar LV box da aka shake da kayan zinare. Babu wanda bai yaba kayan ba, duk da basu kama kafar wanda Imamu ya kawo mun ba, wanda dakyar suka karba bayan an fasa auren, don ya dage lallai shi ya bar mun nafi karfin akwatina a wajen shi, Dada ce ta ce sam ba zaiyu ba, ta tattara kaya ta sanya a mota ta aika Baba Rabi da A.laila suka mayar musu da kayan su.
Mami ce ta haďa kayan Ya Mahmud tsaf! Akwatina 24 da kits guda biyu. Kuma da ita aka je aka kai kayan Kano bata zauna ba. Wani irin shiri Mami take wa wannan biki duk da mummunan halin da take ciki a baďini bata mayar da kanta baya ba. Sai dai wata muguwar rama da take yi wadda take baiwa kowa mamaki. Amma idan akai la’akari da abubuwan da suke ta faruwa da ita sai a danganta ramarta ta da su. Nan kuwa ita kaďai ta san halin da take ciki sai ubangijin da ya halicce ta. Har zuwa wannan lokaci bamu haďu da Ya Mahmud ba, duk wata hanyar da zata haďa mu na toshe ta, bana zuwa gidan Mami kuma idan naji kishin kishin ďin zasu zo zanyi maza na bar gidan ko me nake yi. Abun mamaki shima kuma bai neme ni ba.
Ranar alhamis ďin da bazan taba mantawa ba kaddarar rayuwa ta faru, a wani yammaci mai tsananin hadari, garin yayi baki kirin, da alamun idan aka kece da ruwa Allah ne kaďai ya san lokacin da zai tsaya. Ina hannun Sabrina tana dirje fata ta da siddabarun ta na ýan sudan text ďin Imamu ya shigo waya ta. Address ne kawai ya turo mun yana mai jaddada mun cewa lallai na kasance a wajen.
Dakyar na kwaci kaina na shiga toilet a watsa ruwa na futo, ko mai ban tsaya shafawa ba balle wata kwalliya na zura Armani Abaya da slippers dina na faki idanun mutane sai jin tashin mota ta kawai suka yi. Ya Nuratu ta kira ni a waya nace mata yanzun zan dawo na kashe kirjina na luguden bugu kamar zai balle.
STORY CONTINUES BELOW

Lokacin da na isa “tulip bistro” har an fara yayyafi, nayi maza na shige na zauna nesa kaďan da Ya Mahmud wanda ke zaune yana cin abinci hankali kwance, nice na koya mi shi zuwa wannan wajen da son abincin su har ya zama bayan abincin Mami baya cin kowanne sai na nan ďin.
Gabaďaya ya chanja kamar ba shi ne wanda na sani da ba, ashe daman shi yake wa kansa wasu abubuwan da suke dakile futowar nationality ďin shi. A yanzu kam ya zama balaraben usul a kamanni da yanayi da shiga da komai.
Ďan askin da yake yi idan Mami ta matsa mi shi ya daina sai dai ya gyara gashin da style ďin da duk ya ga dama. Ya rage sanya kayan hausawa sai jallabiya da kananan kaya, don yanzu ma sky blue ďin jallabiyar ce a jikin shi sanfurin Abu Dhabi.
Duba wayar yake yi jikinsa ya soma kaďawa yana rawa kamar mazari, sai kuma ya mike cikin hanzari da matsanancin ruďani ya futa daga wajen. Na bar abubuwa da aka ajiye mun nabi bayan shi cikin sauri.
Motar shi ya shiga ya tayar ya bata wuta kamar zai tashi sama. Na goya masa baya cikin tsananin tashin hankali da tausayin halin da yake ciki.
Tafiya muke yi ba tare da na san ina zai je ba, kuma da alama shi ďin ma bai sani ba. A karshe ya gangara gefen hanya yayi parking, da yake gilasan motar masu duhu ne ban iya sanin halin da yake ciki ba. Hankalina yayi azabar tashi a lokacin da na tuna cewa ko dai ciwon shi ne ya tashi.
Cikin haka Imamu ya kirani nayi maza na ďauka.
“Zara booking yake yi zai tafi London, bansan wane jirgi ba amma a yau zai tafi tabbas. Kar ki damu zaki iya komawa gida I will take care of the rest”
Da kin yarda nayi na tafi na bar Ya mahmud a wannan halin, amma tuna matakin da yake gaba da nayi ya sanya nayi reverse na hau titi na tafi gida ina kwararo addu’ar da duk tazo bakina.
Lokacin da na dawo ana kiran sallar magrib, ďakina na shiga na kulle na dinga safa da marwa ina tunanin abinda ya kamata nayi akan wannan al’amari da kuma taimakon da zan iya baiwa ya Mahmud. Kamar saukar aradu naji kalmomin cikin takardar da Mami ta rubuta wanda na karanta gab da bikina da Imamu sun dawo mun.
Wani matsananincin kuka ya subuce mun nayi toilet na gudu na kulle na kwanta akan dandaryar tiles na dinga zunduma ihu kamar zautacciya.
Na kai awa ďaya kafin na saita kaina nayi wanka na futo; sallah nayi na ďora da nafila nayi addu’a cikin karyewar zuciya sannan na ninke kayan sallar nayi shafa na shirya na futo.
Nayi matukar dauriya wajen haďiye duk wata damuwa da nake ciki, sai da na tabbatar kowa yana parlor sannan na shiga ďakin Dada nayi binciken abinda nake nema cikim ikon Allah kuma na samu. Nayi Hamdala sannan na koma ďakina na janyo laptop na shiga aikin da ni kaďai na san manufar sa ba tare da nemi shawarar kowa ba. Wani irin tsatstsauran kudiri na ďauka a raina wanda ban tsaya hango gaba ko baya ko gefe ba.
Ina kammalawa na rufe komai na haďa karamar trolley da abubuwan da ba zan iya rayuwa babu su ba sannan na futar da ita gate cikin dabara da takatsan-tsan na saka a booth ďin mota ta. Ko Imamu ban futo na gaya wa ainihin abinda nake shiryawa ba don haka na shiga daki muka ci gaba da tsare tsaren yanda komai zai kasance.
Mahmud
……………………..
A zaune yake cikin motar shi yana nana ta karanta rubutun da yake neman hargitsa mi shi kwakwalwa ya fasa mi shi zuciya. Rubutun da ya shammace shi muguwar shammata, rubutun da yafi takardar sakin aure raďaďi ga matar da aka bai wa. Rubutun da ya rushe duka sauran hope, kwarin guiwa, nutsuwa da kwanciyar hankalin da suka rage masa. Daga Masoyiyar sa Amina.
“Assalam Mahmud! Bansan ta inda zan fara ba saboda maganar ba mai daďin rubutawa bace, nayi matukar kokarin ganin na tallafawa halin da kake ciki na rufa maka asiri, amma a karshe na gama tunanin cewa akwai cutarwa ga ýaýan da zamu haifa. Bansan amsar da zan basu ba akan ka? Kuma ni kaina na kasa gamsuwa da wacce irin nasaba ka futo daga ciki kuma wanne irin mutane ne ahalin ka? Aure ba wasa bane Mahmud! Kayi hakuri, mu hakura da juna sai yafi alkhairi.
Ina yi maka fatan samun wadda ta fini.
Amina Ibrahim mai atamfa.”
Farkon faruwar wannan al’amari yayi tunanin hakan zai faru idan Aminar da iyayen ta suka ji wanene shi, sai suka ba shi mamaki ta hanyar nuna masa dattako da karamci da kauna. Soyayyar da bata nuna masa a baya ba ta dinga yi masa tare da kwantar mi shi da hankali da alkawarin kasancewa tare da shi kowanne yanayi na rayuwa komai tsaurin sa. Sai da ta bari ya sakankace da soyayyar ta, ya bata dukkan kauna da amana da gaskiyar sa sannan ta sauya shawara tayi mi shi irin wannan yankan kauna a lokacin da yafi bukatar ta fiye da komai.
A lokacin da auren su bai fi saura sati uku ba, ta zabi ta tozarta mi shi iyaye a irin wannan kurarren lokacin da katin gayyatar bikin su ya karaďe dukkan ýan’uwa da abokan arziki, a wannan lokacin da media take yunwar jin motsi daga gare su komai kankantar shi ta yaďawa duniya. A wannan lokacin da Daddy yake cikin matsanancin sarkakiyar kasuwanci, domin wani flour factory yake shirin buďewa a jihar Sokoto amma matsaloli sai faruwa suke yi, musamman da government ďin da ke ci a yanzu ba mai daďin sha’ani bace. Gabaďaya hankalin Daddyn ya karkata kan yanda zai shawo kan wannan matsala.
Mami kuwa zai ce ya kan tausaya mata fiye da kan shi a wasu lokutan, miji ne da ita tantagaryar ďan duniya kuma azzalumi wanda yake bata wahala a boye tana shanyewa. A wannan lokacin badakala suke ciki ta zunzurun kuďin ta naira miliyan ďari biyu da ya ranta lokacin yana cikin rigima da EFCC akan kuďin da ake tuhumar sa da sama da faďi da su lokacin yana kujerar minister yaki dawo mata da su yaki bata wata kadarar da zata maye mata gurbin su. A wannan lokaci tafi bukatar kuďin fiye da koyaushe saboda fashion house ďin ta da yake shirin durkushewa a dalilin rashin ba shi attention ďin da take yi kamar shekarun baya, harkar fashion design kamar competition ce idan kana so kayi surviving dole ka maida hankali wajen fiddo da sabbin kirkire kirkire a kullum da kokarin futar da kai daban daga rurumar yayi idan ba haka ba, kana zaune wani zai zo ya kwace maka kasuwa. Toh halin da take ciki kenan musamman da yake ita ce creative manager ta company ďin don haka komai yake komawa baya.
Toh a irin wannan halin da iyayen shi suke ciki wanne daga ciki zai dosa da wannan maganar da ya tabbatar zata iya gayyato musu hawan jini ko ciwon zuciya. Ya tabbatar Daddy da Mami na kaunar shi fiye da yanda yake kaunar kan shi kuma a halin da suke ciki da duniya a kan shi fasa auren nan shi ne karshen tozarci da abun kunya a gare su a kan shi. They have gone through alot a kanshi, wannan karon ba zai ďora musu dakon bakin ciki da tashin hankali ba. Wannan karon he will go through the pain alone, ba tare da yayi sharing ďin shi tare da kowa ba.
Toh tunda haka ne kuwa ai zaman Nigeria gare shi ya kare! Wa ya ajiye kuma me zai zauna yayi? Kasar bata karbe shi ba, kuma mutanen cikin ta basa bukatar shi. Wannan London ita ce rufin asirin rayuwar shi da kwanciyar hankalin shi, tunda babu wanda zai wayi gari yayi mi shi gorin uwa ko uba ko nasaba balle a hana shi aure saboda irin wannan dalilan. Babu ruwan kowa da shi da rayuwar shi kuma babu nauyin kowa a kanshi, yana da ýancin zaman duk awannin da yake so yayi kukan shi ta more ba tare da tunanin Mami zata gan shi ba, zai iya kwana uku a ďaki bai futo ya saka idon shi cikin na kowa ba ba tare an tursasa shi ba, garin London ne kawai yayi dai dai da rayuwar mutum irin shi don haka can zai koma ya karasa dukkan rayuwar shi without hope or building future. Zai yi ta taimakon bayin Allah yana ceton rai, yayi ibada da bautar Allah don samun kyakykyawar rayuwa a gaba.
Tunani yake yi cikin sadaukarwa da ihmani da yarda da kaddarar da ta faďo masa bai ďaga hankalin sa ba. Don haka a nutse ya kira wani agent ya tambaye shi jirgin da zai tashi a daren yau zuwa gobe da safe. Turkish airlines ya samu ya tura kuďin a take aka kammala mi shi komai sannan ya sauke ajiyar zuciya ya kifa kansa kan steering wheel yana futar da wasu kwalla masu tsananin zafi da ďaci.
Ba shi da ko lokacin da zai koma gida kuma idan ya koma ďin ma ya ďebi kaya kafin yaje aiport ďin an gama awo don haka ya ďau hanyar airport ďin daga nan, a hanya ya tsaya a kanti ya siya ýar trolley da kaya kala biyu da tarkacen da matafiyi yake bukata musamman da yake sai yayi transit.
Karfe shida na yamma ya isa filin jirgin Dr. Nnamdi Azikiwe na garin Abuja. Ya ajiye motar ba tare da tunanin ya za’ai da ita ba tunda ba ita ce a gaban sa ba, toh abubuwan da ya rasa a wannan rana har ayi comparing ďin su da mota? Mecece mota kuma me zaiyi da ita.
Babu bata lokaci ya kammala komai ya shiga first class lounge ya zauna tare da kashe wayoyin shi gabaďaya.
Yana zaune wani mutum yazo yayi mi shi sallama cikin far’a, Mahmud ya amsa yana kallon jakar kayan mutumin irin ta shi sak kamar sun haďa baki. Daga nan ya gyara zaman sa ya kifa kansa akan hannun kujerar da yake zaune saboda ganin take taken mutumin hira yake son jan sa da ita, shikuwa a halin yanzu futar dollar daga aljihun shi tafi futar harufa daga bakin shi sauki.
Bai ďago ba sai da aka neme su shiga jirgi, yana tashi ya ga wayam, babu mutum babu jakar shi, mamaki ya rufe shi, yana shirin ďaukar trolley ďin shi yaji wani tattausan hannu ya dafa na shi, a sanyaye ya ďago don ganin ko wanene, sai yayi arba wani bakin bafulatani dogo. Cikin tattausan harshen turanci yace+
“Kada ka shiga jirgi da jakar nan! Zata jefa ka cikin matsala, babu lokacin da zanyi maka bayani saboda jirgin ku yana dab da tashi. Amma idan ka sauka ka neme ni….”
Ya karasa maganar yana mika mi shi wata yar takarda. Kan Mahmud ya wani kulle, tunanin shi ya tsaya cak na wasu dakika.
“Mutumin da yazo yayi ma sallama ya zauna kusa da kai shi ne ya musanya maka jakar hannun sa da taka. And it is a set up…..”
A gigice Mahmoud ya waro idanun shi waje cikin tsananin tashin hankali da mamaki. Amma kafin yace wani abu tuni mutumin ya ďauki jakar ya juya da ita cikin hanzari da iya taku kamar ma’aikacin airport ďin Mahmoud ya bi shi da kallo kamar dolo har ya bacewa ganin shi, ýan tsirarun mutanen wajen tuni sun shige sun bar shi don haka ya soma ďaga kafarsa dakyar yana takawa kamar zai faďi don tsananin rauni da karyewar zuciyar da yake ciki.
Wannan shi ne karon farko a rayuwar shi da yayi tafiya bai kira Mami ya shaida mata cewa yana cikin jirgi ba. Balle ya samu wannan addu’ar da take kwantar masa da hankali ya samu nutsuwar zaman awanni a cikin jirgin babu tsoro ko fargaba. Wannan ne karon farko da yayi tafiya bai kira Daddy ba balle yayi mi shi wannan addu’ar da ke sanya shi jin ko da hatsari zai gifta da shi ta cikin jirgin nan a shirye yake yi saboda samun nutsuwar da iyaye kaďai ke iya ba da ita. Ashe ashe rana zata zo da sunan Daddy a matsayin mahaifi zai mi shi tsadar da babu mahalukin da zai iya siya mi shi, ashe ashe watan da zai rasa duk wani important abu na rayuwar shi ne ya kama.
Wasu irin kwalla masu zafi ya dinga zubarwa a lokacin da jirgin ya soma gara tayoyin shi akan kwalta. Ya juya wuyan sa ya dubi taga yayi wa Nigeria kallon karshe domin tafiya ce yayi wadda babu waiwaye babu juyowa babu dawowa. Jirgin na ďagawa ya fashe da kuka yana jin kamar ya tafi ya bar komai na rayuwar sa a baya, yana jin kamar ya bar duka muhimman kadarorin sa da farin cikin sa da kwanciyar hankalin sa a Nigeria ya tafi fanko, empty, zero ko ace sifili inji bahaushe.
That flight was his worst flight ever. Domin kamar mahaukaci haka ya sauka a Heathro Airport na London, don ma Allah ya taimaka basu sha wahalar transit ba kuma basu daďe ba, haka ya sauka sankyalkyal daga shi sai wayoyin shi sai katinan banki da wallet.
Kai tsaye hotel yaje ya kama kusa da airport ďin ya biya kuďin kwanaki uku.
Yana shiga cikin ďakin alwala yayi ya biya bashin sallolin da ake bin shi sannan ya kwanta yana tunanin da bai san iyakacin sa ba, kansa ya dauki matukar zafi da wani irin ciwo mai zogi. Sai ya fara kiran sunan Allah yana karanto “innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha”……..
STORY CONTINUES BELOW

ABUJA.
……………………
Karfe goma sha biyu na dare na mike na bar Ya Nuratu da nannauyan barcin ta nayo wanka ma shirya cikin doguwar rigar larabawa ruwan kwai. Agogo kawai na ďaura a hannuna, na fesa turare na futa daga cikim ďakin ina kwalla.
Dakin Baba Rabi na isa na same ta tana jin wa’azi a cikin wayar ta domin ita ba gwanar bacci bace. A hanzarce ta dago ta kalle ni cikin mamaki, musamman gani na da tayi cikin shirin futa.
A hankali na gurfana a gabanta na soma kuka mai tsuma rai
“Baba Rabi alfarma nazo nema a wajen ki”
A ďimauce ta rikoni jikin ta tana cewa
“Me ya same ki Zarau? Menene ya faru? Wacce irin alfarma kike so?”
Na sake fashewa da kuka nace
“Sai kin fara yi mun alkawari zaki yi mun sannan zan gaya miki”
“Nayi alkawari Zahra’u zan miki kowacce irin alfarma ai ni cikin alfarmar mu nake? Matukar ba sabon Allah bace alfarmar kuma ba bijirewa iyaye bace.”
“Baba Rabi London zaki rakani yanzu”
Da cikin hayyacina nake ba karamar dariya zaro idanun Baba Rabi zai bani ba. Ke sai kice wadda nace mata lahira zanje ta biyo ni.
“Ta yaya? Wacce irin landan? Bangane me kike nufi ba”
Cikin karyewar sauti nace
“Yaya Mahmud zamu je mu ceto Baba Rabi, ya tafi London a daren nan cikin halin da komai zai iya faruwa da shi. Bani da lokacin yi miki bayani dalla amma bayi alkawari ban shirya komai ba sai alkhairi. Na san idan na shiga jirgi ni kaďai na tafi London ni kaďai naci amanar Mami kuma nayi ganganci da mutuncina. Sai na tuna cewa kina da visa na nemo passport dinki na yankar mana tikiti ni da ke da yakinin ba zaki watsa mun kasa a ido ki kasa taya ni ceto ran Mahmud ba. Abinda Mami ne zata yi ne nayi, idan ta wayi gari ta gane Mahmud ya tafi ya barta kuma bata da visar da zata bi bayan sa a gobe komai zai iya faruwa da ita. Baba Rabi ki taimake ni na cika wani kudiri da na ďauka a rayuwata domin farin cikin mahaifiyata da cikar burin ta don Allah”
Ban sha wuya wajen shawo kan Baba Rabi ba, ta shirya ta saka mayafin ta muka futa daga cikin gidan a matukar wahalce saboda ba karamun dabaru muka yi ba kafin mu kautar da hankalin security mu bar gidan. A can farkon layi muka samu taxi ďin da nayi booking tun yamma tana jiranmu, ta ďauke mu zuwa airport zuciya ta babu ko ďigon tsoro ko danasani sai wani hope da strength da kwarin guiwar da ban taba tunanin ina da irin shi ba.
Tasirin addu’a ya sanya bamu sha wahalar komai ba, musamman da ba kaya ne da mu ba, muna tafiya ina wayar wa da Baba Rabi kai akan tsarin su da dokokin su har muka shiga jirgi.
A daren Egypt Air ya shilla duniyar sama da mu, munyi transit mai wahala, musamman da yake a matukar kagauce nake na isa garin London. Ba karamar sa’a da addu’a ce ta kwaci Baba Rabi daga hannun turawan ma’aikatan airport ďin nan ba, sai da na ga mun shiga mota mun zauna sannan nayi hamdala. Kai tsaye hotel ďin da nayi mana booking ya kaimu ana ta ruwa yif yif yif garin ya ďau masifar sanyi.
Munyi sallah munyi wanka sannan muka tsakuri abincin da suka kawo mana daga restaurant ďin hotel ďin. Na ďau waya na kira Helen mai kula da gidan Daddy na London ta tabbatar mun tana nan kuma gidan a buďe yake a sakamakon bakin Daddy da suka sauka wani Dr.Imran da matar shi ya je ganin likita, jirgin da ya kawo mu shi zai juya da su. Nayi Hamdala saboda tunanin kuďaďen da zan biya idan muka ci gaba da zama cikin wannam tsadadden hotel ďin. Washegari kuwa muka tattara muka shiga mota zuwa Sussex garden. Sannan na soma shirin da ya kawo ni garin, gefe guda ina jimamin halin da su Mami suke ciki a wannan wuni da zasu wayi gari babu Ya Mahmud babu ni babu Baba Rabi ba kuma labarin mu. Wannan ta sanya jikina yayi matukar sanyi, domin bazan taba iya buďe waya nayi magana da wani ba tare da na idda niyyar da na taho da ita ba! If I’m successful shikenan komai zai zo da sauki, if I fail, zan kira Mami nayi mata bayani na kuma gaya mata niyyata.
Ďaya daga cikin kawayena da muka yi secondary school tare mai suna Najwa a garin london take karatu, ita na tuntuba da sabon layin da na siya nayi mata bayanin duka abubuwan da nake so, ita ma sai course mate ďin ta mazauniyar garin ta tambaya sannan muka samu abinda muke so muka yi planning da komai. Muna gamawa na shirya muka ďauki hanyar Liverpool cikin jirgin kasa, Baba Rabi mamaki da al’ajabin wannan kasa duk ya lullubeta amma halin da ta shigo kasar a ciki bai bata damar walwala ko tambaye tambaye ba don haka ta sake kunshe kanta cikin jibgegiyar rigar sanyin da nake mana order a kantin “Argos” .
A hotel dai muka kuma sauka, ko zama banyi ba Najwa ta doko mun waya cewa gidan Ya Mahmud fa kulle yake kuma an tabbatar da cewa bai dawo ba.
Ai da cikina ya yamutse yayi wata danka; a wando na zazzago zawon tashin hankali. Wani tsoro ya kamani, musamman da nayi tunanin cewa kila ya Mahmud duniya ya shiga zuwa wata kasar ko garin da ba za’a iya gano shi ba.
Sai da na tsabtace kaina na nutsu sannan nayi tunanin neman Imamu.
Bugu biyu ya ďauka, yana jin muryata ya soma faďa
“Amma ba haka muka yi da ke ba ko? Wanne irin ganganci kika yi haka? Kin tayarwa da mutane hankali…..”
Katse shi nayi ta hanyar ba shi hakuri ina kuka, kuma kukan nawa ne ya sanya shi tsayawa ya saurare ni.
“Imamu Ya Mahmud ba London yazo ba, duniya ya shiga. Mun shiga uku Imamu”
Sai da yayi shiru na sakwanni sannan yace
“Yana cikin london a hotel bai karaso Liverpool ba sai gobe da safe! Ki gaya wa ýan surprise ďin naki kin chanja time “
“Ko dai Imamu aljani ne?”
Zuciyata ta gayamun cikin wani irin tsoro! Sai na kasa magana.
“Ki daina mamaki! Duka motsin ki a idanuna yake Zahra, ko motar da ta kai ki airport ni na turo ta. Tari idan kika yi inaji kuma ina kallon ki. I’m here, but I do more than my best to protect you Zahra! Banji dadi ba da baki gaya mun plan ďin ki ba bayan na tabbatar miki cewa ni yanzu aminci da ýan’uwantaka ne a tsakanin mu ba soyayya ba. Duk yanda nake sonki bana baiwa kaina goyon bayan sake shiga cikin rayuwar ki. Na bar soyayyar mu a matsayin wata kaddara wadda zata zama silar shiriyata, ke kuma ta koya miki lesson ta kuma mayar da ke zuwa hannun wanda kaddarar ta zaba miki. So batun soyayya ajiye shi gefe ki daina shakkar sharing irin waďannan batutuwan dani saboda ni brother ďinki ne ba saurayi ba.
Don’t worry akan halin da su Mami suke ciki da zarar kin kammala mission ďinki komai zai daidaita. I will then unveil my own surprises to you! For now, take a deep breath and plan your date perfectly”.
Yana kaiwa nan ya katse wayar ya barni da hangamammen baki da alajabi da mamaki. Amma kamar yanda yace ďin, wannan lokacin ba na tunani bane don haka ma tattara komai na ajiye na shiga shirya yanda goben zata kasance idan har Allah ya bamu aron rai da lafiya.
Karfe huďu na yammacin lahadi na kammala shirina tare da Najwa cikin wata abaya baka kirin ďanya sharaf da duwatsun Swarovski masu walwali. Daga ita sai mayafin ta ne a jikina, ko yari ban saka ba balle wani shafe shafe da iyayi.
“Ke kuwa Zahra maimakon ki baiwa wata shegiyar date gown ďin dior ko Ralph Lauren kunya sai ki saka wannan jikakkiyar bakar abayar ki naďe fuska kamar wata mai shirin tafiya umara”
Murmushi nayi mai ma’ana sannan na ajiye turaren “chanel no5” da ke hannuna nace
“Shi wanda zanje wajen sa ba ya bukatar wanka ko kwalliyata ko kyauna. Ina mai tabbatar miki cewa ko sarauniyar kyau ya gani a gabansa sai yayi niyya zai kalle ta sau biyu. His worth is more than just beauty and fame Najwa. He deserves anything in this world no matter how classy and expensive it is.”
Sai ta shafawa kanta lafiya ta daina magana tayi shiru da bakinta. Ke daga baya ma cire wannan abayar nayi da naga kyallin duwatsun ta zai dame ni na ďauko wata simple lace dress mara hannu na saka, na kawo sweater mai taushi baka na ďora akai bayan na naďe fuskata da farin gyale kamar yanda Najwa ta tsana ďin. To me, the most important thing is be myself, wearing my confidence is greeter than wearing any stupid expensive or fancy dress or whatever they call them.
…………………………………………………………………+
A gajiye tibis Mahmud ya isa Liverpool jikinsa na rawar sanyin zazzabin da ya kama shi. Cikin tsananin dauriya ya isa kofar gidan na shi yasa mukulli ya buďe sannan ya shiga yana mai sallama da karanto addu’o’in tsari.
Dakyar ya gyara ďakin da zai zauna duk da ba wata muguwar kura yayi ba, ya wanke toilet yayi wanka sannan ya haďa tea mai kauri ya kafa kansa ya shanye saboda sanin cewa idan ya kwanta bai cin ba babu mai tada shi ya ba shi, kuma yayi alkawari wannan karon ba zai bari damuwa ta kwantar da shi ba. He will be strong for himself!
Yana gamawa ya ware duk heaters ďin gidan ya shiga ďaki ya sanya pyjamas ďin shi na “Mac and Spencer” shuďaye sannan kwanta a gado yana addu’ar Allah ya sanya bacci ya ďauke shi kafin ya fara waďannan tunanin masu karya mi shi zuciya.
Yana cikin wannan halin yaji karar kararrawa, ya saurara don tabbatar wa a gidan na shi ne ya sake ji an ci gaba. Mamaki ya kama shi, amma sai yayi tunanin ko makotanshi ne suka gane ya dawo. Tsaki yayi ya tashi yana cuďa hargitsatstsiyar sumar shi wadda bata samu gyaran da ta saba samu ba ya duro daga gadon ya futo.
Yana buďe kofa yaci karo da abun mamaki da ďaure kai, masu busa ne ta sarewa cikin shiga iri ďaya kowanne hannu rike da abun busa suna tsaye a gaban shi. Kafin ya samu damar yi musu tambaya suka baiwa kansu izinin shigewa cikin gidan suna aikin da ya kawo su.
Masu busar na tsaye suna raira wata emotional busa mai tsargawa cikin kashi da jijiya da bargo yayinda wasu ke ta hidimar decorating falon nashi da wani irin classy romantic decor da kalar red and white.
Sai ya samu bango ya kame yana kallom su kamar gunki, yana so ya gane ko kwalwalwarshi ta soma juyewa tana yi mi shi gizau da abubuwan da ba a Zahiri suke faruwa ba.
Kafin kiftawa da bismillah parlor shi ta rikiďe ya sauya koma kalar jajayen candles masu azabar kyau. Ko ina zanen roses ne jajaye da farare da balloons na reto a jikin pop da chandelier suna ta tsalle.
A dandanyar wood tiles ďin take shimfiďe a falon aka yi zanen heart da wasu irin roses jajaye aka bi bayansu da candles farare.
Ko da a lokacin Mahmud ba’a cikin hayyacin sa yake ba sai da ya yaba kyau da tsarin wannan aiki mai ban mamaki. Ko motsi baiyi daga wajen tsayuwar sa ba tsayin awa guda har suka kammala komai suka dinga futa ďaya bayan ďaya ba tare da sun yi mi shi magana ba.
Sai masu zazzakar busar nan guda uku kawai aka bari suna raira busar su kamar a cikin mafarki.
Kulle idanun shi yayi yana addu’ar Allah ya futar da shi daga wannan mummunan halin da yake shirin sake zurmawa. Allah kada ya bari kwakwalwar shi ta zautu ya haukace bai kulla ayyukan alkhairan da ya ďauki niyyar iddawa a gaban shi ba.
Sai yaji wani kamshin turare na mata irin na Mamin shi, wanda yake siyowa ya feshe gidansa da shi idan yana missing ďin ta wato “chanelno5”
Wannan ya bashi damar buďe dara daran idanun sa masu kaifi akan abinda yake yake kalla.
STORY CONTINUES BELOW

Me zai gani?
Zahra ce a gaban shi a tsaye!and not even the normal classy Zahra! Wannan simple and Plain ce wadda bata kara komai akan sunan ta don armasawa ko kawata kanta ba. She is just her! And that’s all!
Ya rufe idanu ya bude! Ya sake rufewa ya buďe, ah ah! Ya ilahil arshi.
Sai ya saka hannayen sa biyu yana murza idanun amma sam Sam sun ki daina haska mi shi hoton wadda tana daga least din mutanen da yake tsammanin sake gani a rayuwa. Musamman ita da bai ma san a gwadaben da ta ajiye shi ba tun bayan bayyanar tushen asalin sa. Wadda har yau ko kalma bata shiga tsakaninta da shi na jajantawa da jimami da nuna support ba. Wadda ta kasa tafiyar mintina talatin a cikin abuja ta je ta ga lafiyar shi da halin da yake ciki mai zai kawo ta London tafiyar awanni barkatai cikin kwanaki uku kacal da tahowar sa???
Wannan ba Zahra bace sai dai idan aljanu aka fara jifansa da su don su karasa illata tunani da zuciyar sa. Yana cikin wannan sake saken kunnen shi ya soma kawo mi shi sautin muryar da ya tabbatar Zaran ce kaďai me irin ta da wasu irin tarin kalamai masu barazanar ďauke numfashi.
“It’s me Ya Mahmud! Zahra ce! Your only sister, the only person you share Mami with! Your mother’s daughter Ya Mahmud!
Ka bude idonka ka kalle ni! Ka bude kunnuwanka ka saurare ni!
Ka kwantar da hankalin ka ka fuskance ni!
I’m here for no one but for me and you! Just the two of us!
Na taho da ba izinin kowa ba, ba da sa sanin kowa ba, ba da kuďin jirgin kowa ba, ba da guzurin kowa ko taimakon kowa ba.
Na taho nan hopeless, helpless homeless, loveless, heartbroken and empty hearted!
Na zo ne na tabbatar da abinda yake ckin zuciyata na gaskiya da amana babu wasa ko shiri ko tursasawa ko shawara ko haďin baki. I’m here for myself
I’m lost! I have searched everywhere i couldn’t find myself…….
I’ve tried so many times but I failed, but now, i have finally realized where exactly I belong, where my home, my peace, my comfort,my love and my happiness are………
You know where?”
Ta karashe maganar cikin sigar tambaya da karyewar sauti.
Ko da cikin duniyar da yake ba irin wannan tamu ce ta mutane da aljanu ba, baiyi missing ďin kowacce kalma da fa futo daga bakin ta ba kuma bai kasa girgiza kansa ba a lokacin da tayi masa tambayar.
Taci gaba da magana tana nuna shi da yatsanta manuni
“Right here in your heart! I have realized that I belong to you! Only you!!!…. and that’s the reason why I don’t find myself whenever I’m in love with any man! Because I’m not made for them, I do not belong to them. You are my home, my life and my only love!2
Kai kaďai ne kafi kowa sanin daraja ta da kima ta duk fadin duniya
Kai kafi kowa yarda dani a inda nake ba tare da bukatar na chanja ba
Kai ne kafi dacewa da rayuwata da soyayya ta da kuma zuciya ta da amana ta, kai ya cancanta kaja ragamar rayuwata.
Saboda kaine ba zaka cutar dani ba
Ba zaka tozarta ni ba
Ba zaka guje ni ba
Ba zaka wulakantani ba
Ba zaka aibantani ba
Ba zaka watsar da ni ba
Ba zaki yi mun gori ba
Ba zaka ci amanata ba
Ba zaka yaudare ni ba
Ba zaka kaskantar da ni ba.
Tell me? Do I belong somewhere else?
Do I deserve any man apart from you?
Who on earth would fill this empty spaces?
Who deserves me better than you?
So I’m right here in front of you with a broken heart, will you accept my love?
Will you marry me Ya Mahmud?”
Ta karasa maganar tana kokarin kai guiwoyinta kasa kamar yanda maza suke wa mata proposal.
Kamar an tsikare shi sai yayi duk wani nauyi ya bar shi, yayi maza ya riko kafadunta ya tada da ita tsaye. Sannan ya riko hannayen ta guda biyun shi ya durkusa a gabanta cikin wasu irin siraran hawaye masu zafi.
STORY CONTINUES BELOW

“If you really mean everything you said and that I’m your home and I deserve you, then I have opened all the gates of my body not only my heart to you Zahra! Please complete me! I’m shattered and broken! I’m lost in the middle of nowhere! I need love……..”2
Sai suka barke da kuka dukansu kamar an aiko musu da Sakon rasuwar dangin su. Kuka na farin ciki da samun relief daga raďaďi da ciwo da zogin daga zukatan su suke ciki, before they finally broke into a bone crushing hug kamar za’a kwace ďaya daga hannun ďaya.
Tun daga kan Baba Rabi zuwa Najwa da uwa uba masu busar hawaye suke futarwa cikin wani irin emotion, ko a cikin film ďin turawa ko larabawa aka yi wannan love scene ďin zasu ajiye babban tarihi! Abun was beyond kalmomi da tunani, ganin duka su biyun sun yi fiffike sun futa daga wannan duniyar ta mutane ya sanya Baba Rabi share hawayenta tare da yin gyaran murya mai karfi wadda ta dawo daga sabbin masoyan daga duniyar da suka tafi.
Cikin mamaki da amusement Mahmud yake kallon Baba Rabi
“Har da ke Baba Rabi?”
Ta sake share kwallan idanunta tana girgiza kai tana murmushi mai sauti.
Najwa kam tuni ta bar gidan kamar yanda masu busar suka yi domin ita gabaďaya ba zata iya cigaba da kallon wannan emotional scene ďin mai karairaya zuciya ba.
………………………………………………………………….
A babban falon Daddy na gidan shi da ke Mississippi a Abuja, abun almarar yake faruwa, tun daga lokacin da Imamu ya kira Daddyn a waya ya sanar masa da cewa yana son kebewar sirri da shi da Mami a wani kebantaccen waje Daddyn ya shiga ruďani. Sai da Faisal ya kira shi ya sake wayar mi shi da kai akan sauyin da Imamu ya samu da kuma muhimmancin abinda ,zasu tattauna a akai sannan ya yarda.
Tun ranar da Mahmud ya tafi Imamu ya samu Faisal yayi mi shi bayanin komai, a cikin daren kuma da jirgin su Zahra ya tashi sai da ya sake kiransa ya gaya mi shi tare da yi masa bayanin tsarin shi na yanda zasu bullowa wannnan al’amarin. Sun kai awanni biyu da rabi suna tattaunawa da shi kafin suyi sallama. Washegari ana idar da sallah Faisal ya nemi wayar Daddy yayi mi shi bayanin komai saboda kar safiya tayi a wayi gari da tashin hankalin rashin Baba Rabi da Zahra bayan na tafiyar Mahmud.
Da safiya tayi aka tashi da kace nacen ina Baba Rabi da Zahra sai Dada ta hade fuska ta dubi Ya Nuratun da ta shigo tana tambaya a sakamkon ganin babu kowa a kitchen da ta shiga, a wannan lokacin kuwa Baba Rabi bata rabuwa da kitchen ďin sai ta kammala kalacin safe tayi wanke wanke.
“Na aike su! Zainab zata sa a kawo kayan karin kumallo kafin tazo”
Mamaki ya kama Ya Nuratu amma da yake ba’a question ďin Dada sai tace toh kawai ta futa ta koma kitchen ďin ta soma sarrafa abinda take bukata domin yunwar da take ji ba zata iya jiran a kawo ďin ba duk da cewa tana ta tunanin wanne irin aike ne Dada zata yi wa Baba Rabi da Zahra da sassafen nan? Akwai dai wani abu.
Da rana kuma sai ta ga cook ďin Daddy ya dawo gidan domin cigaba da yi musu abinci, Mami tazo ta shiga wajen Dada sun daďe sannan ta futo, da ta kasa daurewa ta tambayi Mamin sai tace mata Baba Rabi da Zahra suna Katsina. Zata je sallamar aure ta zaga family a bisa umarnin Baban. Da wannan ta rufe bakin Nuratu ta tafi gida ba don kan Nuratun ya ďauka ba.
Hakika Daddy da Mami sun shiga wani hali a sakamakon rushewar auren Mahmud da Amina, Daddy yayi kuka yayi kuma Allah isa ga Alhaji Ibrahim mai atamfa yafi shurin masaki a wannan rana, ashe amini kan rikiďe ya koma makiyi? Ya tuno irin taimako da alfarma da yayi wa Alhaji Ibrahim wanda ba zasu lissafu ba amma wai yau ya rasa wanda zai ci amana ya tozarta sai shi? Me yasa bai ce ya fasa baiwa Mahmud Amina ba tun ranar da yaji asalin Mahmud? Me yasa yayi masa shigo shigo ba zurfi da lumbu lumbu sai da biki yazo dab, katin gayyata ya je hannun kowa da kowa sannan ya zai masa haka?
“Ka rabu da shi Ahmad! Ko a waya kada ka neme shi, bar shi da Allah da cin amanar da yayi mana! Allah ya kaddara Amina ba matar Mahmud bace! Kuma da izinin Allah sai ya samu wadda ta fita in dai riko da gaskiya yana futar da bawa kunya Ahmad albarkacin rikon da kayi wa Mahmud Allah ba zai tozarta ka ba. Bar shi kawai, akwai manakisar da yake kullawa da wasu, duk da bansan komai ba amma na tabbatar wannan shiri ne. Sai dai Allah ya fi su kuma shi ne zai mana maganin su”
Da irin waďannan nasihun da maganganun Ambasada ya shawo kan Daddy hankalin sa ya kwanta. Amma idan ya tuna halin da Mahmud kan iya shiga a dalilin hakan sai ya ji zuciyarsa ta karye.
Mami kam kuka kawai take yi tana shaidawa Allah ya taimake su ya baiwa Mahmud juriya kada wannan al’amari ya zamo silar tashin ciwon sa. Kada wannan tashin hankali ya kwantar da shi. Bugun duniya wayoyin shi a kashe, duk da Faisal ya gaya mata cewa Imamu yana sa ido akan kowanne motsin sa kuma ya tabbatar mata cewa lafiyar Mahmud kalau amma bata samu sukuni ba.
Ita kanta Dada a wannan lokacin babu abinda yake gallabarta illa tausayin Mahmud da iyayen na shi. Duk abubuwan da take yi matukar dauriya da karfin zuciya ta sanya ta yin su amma ba don son ranta ba. Tayi hakan ne don ta nuna wa Daddy kuskuren sa na boye irin wannan al’amari mai girma, domin na bayan shi su hankalta su wa’azanta su ďauki darasi. Na biyu saboda ta kwatowa Mahmud ýanci, ta tabbatar idan bata yi irin wannan boren ta tayar da hankali ba Daddy ba zai maida hankali wajen nemar wa Mahmud dangin shi ba, wanda hakan shi ne karshen gatan da zai masa. Ta tabbatar ko da a yanzu Mahmud bai bukaci iyayen sa da asalinsa ba, gaba zai nema, watakila lokacin babu ita ba Daddyn da Mamin da zasu tsaya masa ya fuskanci irin wannan tashin hankalin da tsangwama da cin fuska daga al’umma. Babu wanda ya san gawar fari, mutuwa na iya zuwa kowanne lokaci, idan har suka mutu suka bar Mahmud da wannan cakwakiyar a kansa basu warware masa ba, toh lallai sun zalince shi, zalincin da ko shi ya yafe musu Allah ba zai yafe musu ba. Don haka tayi alkawarin tsayawa tsayin daka har sai ta dangana Mahmud da dangin mahaifin sa da yardar Allah.
Tana son Mahmud soyayya irin wanda bata yi wa jikokin ta na jini, sanin asalin sa bai rage ko burbushi daga son da take masa ba, illa tausayin sa da ya kara mamaye ta. Mahmud kyauta ce daga Allah a gare su, a lokacin da suke bukatar ďa ido rufe, don haka har abada ba darajar sa ba zata ragu a zukatansu ba.
Nan da nan ta shiga buga wayoyi zuwa manyan malaman ta masu riko da takama da alkur’ani, ta bada umarnin yin saukoki da addu’o’i da sadakoki irin wanda ta saba yi idan wani al’amari mai girma ya taso, sannan aka tashi bayin Allah zuwa kasa mai tsarki suyi addu’ar neman ďaukin Allah akan wannan al’amari. Ita kuma bata da aiki sai addu’ar, musamman da ta ga kan iyalin na ta na son tarwatsewa gabaďaya a dalilin wannan magana.
Ita kanta Dadan sai ta zama abar tausayi domin abubuwa ne masu yawa suke cin ranta.
………………………………………………………………….
Daddy,Mami da Faisal na zaune a gaban kyakykyawar computer Imamu kirar apple, yayi ýan dannen sa ya shiga Skype, sai ga rangaďeďeiyar fuskar Najwa tana futowa a cikin mudubin computer.
Sallama tayi sannan ta ďora da cewa
“Ina kan hanyar tafiya Imam! You will see everything live i promise”
Daga nan Daddy da Mami suka gyara zama sosai domin ganin ikon Allah, ta wani bangaren zuciyoyin su na ta bugawa saboda fargaba da tsoron abinda zasu iya gani ďin.
Sweetest chapter right?
You all have been waiting and hoping for this union?
A karshe alkawarin Allah ya cika akan Zahra da Mahmud?
What will you say about this chapter?
Doest it worth the wait?
I’m sorry for not being able to reply your comments, I have been so busy.
I will do that insha Allah.
It’s Friday!
Recite surat kahf and send salam and taslim to the best of man kind.
Allahumma Sally ana sayyidina wa habibina wa rasulina Muhammad. Saw.
Cutyfantasia…….
Ma’assalam.Babu idanun da suka kuskure gotawa daga kan screen ďin computer ďin nan har Najwa ta kammala parking a inda ya dace sannan ta futo tana boye wayar a aljihun ta. Kusan mintina goma suna jin maganganu sama sama kafin abun almarar ya fara faruwa. Sun fara kallon ne daga lokacin da masu busa suka shiga gidan suna rerawa, Mahmud yayi suman tsaye yana tunanin mafarki yake yi ko kuma aljanu ne ke shirin buďe mi shi idanu
Babu zato ba tsammani sai ga Zahra ta shigo, ya dinga kallonta da mamaki da son gasgatawa ko ita ďin ce ko kuma aljana mai kamarta aka turo masa ta hargitsa masa lissafi. Sai suka ga ta soma magana, amma busar da masu busa keyi bata barsu sunji abinda take cewa sosai ba, amma duk da haka suna jin wasu kalaman, tiryan tiryan suke kallon komai zuciyoyin su na wani irin kiďa da tsalle na ganin wannan al’amari mai ban mamaki da al’ajabi.+
Mami bata karasa kallon ba ta mike tsaye tana rangaji ta shige ďakin da yafi kowanne kusa da inda take zaune,
Tana shiga ďakin ta faďi kasa cikin sujjadar da ake kira “sujoodush shukur”
Hawaye marasa kakkautawa na sharara daga idanunta suna jika tattausan kilishin da take durkuse a kai, babu abinda zuciyar ta take nanatawa sai
“Ashe daman burina zai cika? Ashe daman zan ga wannan farin cikin? Ashe wannan alkawarin zai tabbata? Ashe Allah kana sane da halin da nake ciki kuma kana tare dani?……….”
Ita kanta ta san cewa wasu kalmomin na ta sabo ne tsagwaran sa wanda kiďimewar farin ciki ta sanya ta take ta kwabawa. This is truly the biggest shock of her life, the greatest blessing she has ever received and the best news she has ever heard. Wannan shi ne mafi girman burin da zuciyar ta take dako tsayin shekaru ashirin da ďoriya. Wannan shi ne fatan da take tayi babu kakkautawa, shi ne abinda take yi wa addu’a ko ba akan sallaya ba, shi ne al’amarin da yafi kowanne muhimmanci a gare ta kuma shi ne kololuwar farin ciki da walwalarta da nutsuwar ta a wannan rayuwa da take ciki? Shin hawaye zasu iya tsayawa mutumin da ya cimma irin wannan buri da ke sarkafe da waďannan manyan alamura kuwa??
A falon ma dai bata chanja zani ba, domin nemar dauriya da karfin zuciya irin na Daddy aka yi aka rasa. Shima kukan ya fashe da shi mai karya zuciyar mai sauraro da tabbatar da cewa wannan al’amari bashi da na biyu wajen matsayi a zuciyar Daddy!
Wani irin ďauki ubangijin sammai da kassai ya kawo mi shi a lokacin da yake cikin tsananin neman ďaukin, wata irin mafita Allah ya kawo masa a lokacin da duka kofofin kubuta suka kulle mi shi. Wata irin alfarma da karramawa Allah yayi mi shi a lokacin da yake gab da fuskantar tozarci da kunya a idanun duniya. Wani irin farin ciki Allah yayi mi shi kyauta a lokacin da bakin ciki yayi mi shi talala da ďaurin goro,
Wata irin ni’ima Allah yayi mi shi 3 in 1 irin wadda wani mahaluki bai isa yayi mi shi ko tunanin samun irin ta ba.
Toh idan bai yi kukan farin ciki da godiyar ba me zaiyi?
Jikin Faisal da Imamu yayi sanyi kalau, tsananin tausayi da mamakin soyayyar waďannan bayin Allah ga Mahmoud tana lullube su. Basu taba jin wannan soyayya da kauna mai ban mamaki ko a labari irin soyayyar da take tsakanin Daddy da Mami da ďan rikon su Mahmud ba. It is beyond comment and thought don haka suka zuba idanu suna kallon wannan scene mai ban sha’awa da tausayi.
Sai da aka yi kiran sallar magrib sannan Allah ya kawo wa waďannan bayin nasa nutsuwa da samun hayyacin su. Aka yi alwala aka yi sallah sannan suka zauna a tebirin tattauna abubuwan da suke tunkaro su da hanyoyin da zasu bullowa kowanne shiri cikin sauki da takatsan-tsan.
………………………………………………………………….
Daga can kasar sanyi kuwa bayan Zahra ta kammala cika alkawarin da ta ďaukar wa kanta sai hankalin ta da nutsuwar ta suka dawo jikinta.
Ta kalli gefen damanta ta dubi Mahmud, mutumin da ta ďauki tsayin wasu shekaru tana jin labarin sa ba tare da ta gan shi ba, labaran kuma marasa daďin da ba zasu bata sha’awar tambayar wani ainihin tarihin sa ba balle ta fahimci al’amuran da suke kewaye da shi, zuwa lokacin da suka haďu a Saudi, shine ganin farko da tayi mi shi da hankali da wayon ta, sai dai shi ma a wannan karon da wata salon mugunta da kiyayya ya futo mata wadda ta hana ta gano nagarta da alkhairin sa ta gasgata munin halin sa ta kuma yarda da abubuwan da ake faďa a kansa wanda ya sake janyo tsanar shi me tsanani a cikin zuciyar ta , a karshe zuwan shi bikin Faisal da Ihsan ne ya warware mata komai, ya zama sanadin da ta san shi ba sanin shanu ba, ta fahimce shi ta kuma ta gano alakar shi da Maminta kafin wata irin shakuwa da soyayya irin ta ýan’uwan jini ta ratsa a tsakanin su.
Tun daga wannan lokacin kuma bata mi shi kallon komai sai na babban yayan da kanne dubu basu samu irin shi ba, wani mutum mai matukar daraja da girma da kima da mutunci a idanun ta, wani mutum mai matsayin da ba zai iya ce mata “eh” tace “a’a” ba.
Akwai wani irin respect, love irin na jini, da trust a tsakanin su mara misaltuwa don haka bata taba ďaga idanu tayi mi shi kallon raini ko wasa ba.
A ranar kuwa da tsautsayi ya kaita bankaďa asirin Mami a cikin ďakinta har ta karanta sai take jin wannan burin na Mami kamar ďaukar dala ba gammo ne, idan ta ayyana faruwar hakan kuwa sai tayi sauri tayi istigfari don ita gani take yi kamar tayi sabo.
Wani al’amari ne mai nauyin da kanta ba zai iya ďauka ba, don haka taje can kololuwar ma’ajiyar sirrin zuciyar ta ta ajiye wannan magana ta kulle da kwaďo don ko tunawa bata son ta sake yi.
Ta kalli gefen hagunta ta dubi Baba Rabi, dattijuwar da ko Dada mutuntata da girmama ta take yi saboda kyawun hali da nagartar ta. Wata mace mai daďin zama da sanin darajar ďan’adam, mai matukar saukin kai da gudun bacin ran duk wanda take zaune tare da shi.
Sun sha tonewa su mayar su binne ita da Baba Rabi babu wanda ya sani, sannan a ko da yaushe nasiha da faďin gaskiya ce tsakanin ta da ita, kiyi kaza me kyau ne, ki bar kaza bashi da amfani, saboda haka Baba Rabi mutum ce mai mutunci da kima da daraja a idanun ta.
Kwatsam Zarah taji wata irin matsananciyar kunya ta yi mata diran mikiya kamar tace kasa ta kece ta shige ciki ga boye ta.
Kamar walkiya ta wulkita da gudu ta shiga ďakin Mahmud ta kullo kofa ta barsu suna yi mata dariya.
STORY CONTINUES BELOW

Tun suna ganin kamar abun na ta wasa ne da zolaya har suka tabbatar cewa ba da zata futo daga wannan ďaki ba idan dai har suna nan domin awannin ta huďu a ciki cur. Sai Mahmud ya lallaba ya fuce daga gidan yayi tafiyar sa hotel ya kwanta, daman yana matukar bukatar kaďaicin, yana so ya gan shi shi kaďai yayi tunani akan abinda ya faru, da abubuwan da suka faru, da wanda zasu faru a gaba.
Zara ta ba shi karshen mamakin da har abada ba zai manta ba, ta nuna mi shi halaccin da bai taba tunanin har yanzu akwai masu yin irin shi ba kuma ta nuna mi shi kauna da soyayya a lokacin da yake tsananin bukatar su. Ya tabbatar kuma zai iya rantsuwa cewa babu soyayyar shi ta aure a cikin zuciyar ta kamar yanda shima bai taba yi mata wani kallo baya ga na kanwar sa da suka futo ciki ďaya ba. Wata irin maďaukakiyar sadaukarwa tayi mai ban mamaki da saka zuciya ruďani, ga wasu tarin tambayayoyi da suka lullube shi da yake bukatar amsoshin su, gashi kuma yana jin nauyin kiran Mami ya doshe ta da wannan zancen.
Yana cikin wannan hali yaji wayar sa ta soma ringing, yana dubawa ya ga sunan Faisal, wanda ya zauna yayi mi shi dogon bayani akan abubuwan da suka faru tun daga farko har karshe tare da taimakon Imamu.
Kan Mahmud ya ďaure tamau da mamaki da tashin hankali, wani irin tsoro da fargaba suka mamaye shi a lokacin da ya tuno irin abubuwan da zasu faru ba don taimakon Imamu ba.
Hakika Allah ya dubi tsarkakkiyar zuciya da niyyar Daddy ya kawo mi shi ďauki da mafita a lokacin da yake gab da faďawa haďari.
Kwana yayi akan sallata yana nafilfilu da addu’o’i na godiya ga Allah da neman taimakon shi akan wannan lamari har zuwa karshen shi.
Daga nan kuma ya sake kiran Faisal inda ya haďa musu conference call da Imamu yayi mi shi cikakkiyar godiya kafin su ďora akan tsare tsaren da suke yi.
Washegari muka kamo hanyar dawowa Nigeria ni da Baba Rabi a bisa umarnin Daddy! Ko da wasa ban kuma kallon Ya Mahmud ba, da na gaishe shi sau daya lokacin da yazo ďaukar mu zuwa airport ban sake yi mi shi magana ba, shi ma kuma share ni yayi yaci gaba da harkokin sa da Baba Rabi. Haka muka shiga jirgi babu ko sallama kamar ba nice wadda ta ďauki kafa tun daga Nigeria taje London tayi proposing ďin shi ba, da na maimaita kalmar a bakina sai naji wani bambarakwai.
Allah dai yasa ban zubar da kima ta a wajen Ya Mahmud ba! How on earth is it normal mace taje rokon namiji soyayya da aure? Me ta siyawa kanta kenan?
Kamar Baba Rabi ta karanta abinda zuciyata take sakawa, kamar ta san me nake tunani, ji kawai nayi ta dafa ni ta soma magana cikin taushi.
“Ko da wasa kada kiyi tunanin danasani akan abinda kika yi! Kinyi abinda yafi komai cancanta da dacewa kuma kinyi halacci da biyayya da kyautatawa ga iyayen ki.
Sannan shi wanda kike jin kamar tallan kanki kika yi mi shi ba sunan shi namijin gari ba, wani mutum ne wanda yake alfahari da soyayyar iyayen ki, yake kuma burin farin cikin su a kullum, wani mutum ne wanda babu wanda babu wani abu mai daraja a gare shi kamar mahaifiyar ki babu abu me kima a gare shi kamar mahaifi ki Daddy kuma babu burin da yake da shi sama da ya faranta musu.
Ina mai tabbatar da miki da cewa baki zubar da kimar ki ba a wajen Mahmud illa ninka ta da kika yi domin shi ya san ke abinda ma baki sani ba kuma ba kallon macen gari yake miki ba, ke me daraja ce da mutunci a idanun shi, ya kuma tabbatar da cewa shi kaďai zaki iya yi wa wannan girmamawar duk duniya. Toh meye abun tunani da damuwa Zara? Ba godiya zaki yi wa Allah ba da ya kasance kece kika cika burin iyayen ki na shekaru ashirin da uku bayan sun fidda ran cimma shi?”
Cikin mamaki nace
“Baba Rabi kema kinsan cewa Mami da Babana suna da wannan burin?”
Cikin murmushin dattijai masu hikima da hangen nesa tace
“Ke a ina kika sani?”
A hankali na soma yi mata bayanin ranar da na kwana gidan Mami nayi mata gyaran ďaki, na buďe wardrobe ďin ta naci karo da wata drawer da kullum take a kulle ranar ta manta ta bar mukullin a jiki bata kulle ba.
Da na buďe sai naga tulin hotuna ne da muhimman takardu da wasiku; inda tsautsayi ya sanyani buďe wata envelop da ke tsakanin wasu hotuna da Mami da Babana da kuma wanda aka yi mana ni da Ya Mahmud ina shekara ďaya.
Na buďe cikin ďari ďarin tsoro kada Mamin ta shigo ta same ni sai naci karo da wani rubutu da ya gigitani. An fara ne da kwanakin wata sannan akai bismillah aka soma rubutun
“Ďaya daga cikin manyan burina ni da mahaifin Zara shi ne haďa aure tsakanin ta da Mahmud idan Allah ya raya su sun fahimci juna da kansu. Idan kuma kowanne ya kawo wanda yake so ba zamu tilasta su ba, amma bani da buri akan su wanda ya wuce naga sun auri junan su, wannan shi zai kasance karshen kwanciyar hankalina da farin cikina. Zan rayu da wannan buri da addu’ar Allah ya cika mun shi idan har da akwai alkhairi a cikin sa. Ko mutuwa nayi ina fatan Allah ya sanya hakan ya kasance, Allah ya cika mun burina”
A gaskiya Baba Rabi a lokacin na shiga wani ruďani da tashin hankali, amma da yake ba’a nutse nake ba sai na tattara maganar na mayar da ita keya saboda wani abu ne da nake ganin kamar babu yiwuwa a cikin sa, ya za’ai mutumin da nake kallo da kima da daraja irin Ya Mahmud wata magana irin wannan ta shiga tsakanin mu? Ina dai ta tunani, toh a lokacin ina cikin taskun Imamu da tashin hankalin sa, don haka ba wani mahaluki da na gayawa wannan maganar domin ni nauyi ma take yi mun a zuciya ta balle kuma na furta da baki.
Ana cikin haka kuma Aisha ta rasu, abubuwa suka dinga faruwa waďanda suka shuďar da maganar a cikin raina.”Wata irin tafiya muka yi mai daďin gaske tare da Baba Rabi, domin ta warware mun kullika da yawa da suka dagula mun lissafi ta kuma fahimtar dani abubuwan da suka shige mun duhu sannan ta bani shawarwarin yanda zan bullowa abubuwan da suke gabana cikin sauki da kwanciyar hankali. Daga bisani na gyara kujera ta na kwanta akan kafafunta na soma baccin da na dade bana samun irin shi, wato baccin kwanciyar hankali, ban ankara ba naji ana shelar saukar jirgin airport ďin Nnamdi Azikiwe.+
Faisal ne yazo ďaukar mu, wai don shirme shima sai naji kunyar shi nake ji, a dalilin na san yaji komai. Suka haďu da Baba Rabi suna tsokana suna yi mun dariya. A maimakon gidan Dada, sai naga Faisal ya ďauki hanyar Mississippi Street, na kasa hakuri nace
“Ya Faisal ko gidanku zaka kaimu ne??”
Murmushi yayi yace
“Zuba idanu ki gani amaryar Mahmud”
Ya bani kunya sosai, wai nice amaryar Ya Mahmud! If feels so awkward wallahi! Ya Mahmud of all men? Allah mai iko.
Ina wannan tunanin na ganmu cikin tangamemen gidan Daddy na Mississippi Street, gidan sirri, gidan da na jiyo maganar da har gobe take bani al’ajabi da karyamun zuciya.
Hannuna cikin na Baba Rabi muke bin Ya Faisal zuwa cikin gidan, kamar wata sabuwar amaryar da za’a kai ďaki.
Safiya ce karfe takwas da rabi, amma sai ga Dada da Daddy da Mami zaune cikin falon tsaf a shirye, kowanne haiba da kamala da farin ciki da murna da annashuwa ta cika shi har ba ta boyuwa. Don shakiyancin Baba Rabi sai da muka zo tsakiyar falon ta saki hannuna ta koma gefen kujerar Dada.
Wata irin matsananciyar kunyar da bansan ina da ko rabin ta bama ta lullube ni, da ina da hali sai nace kasa kece ki boye ni. Cak na tsaya kaina a kasa idanuna na kallon tattausan brown ďin kilishin da nake tsaye a kai. Bansan me ya faru ba ashe Daddy ne ya taso da kanshi ya janyo hannuna ya kaini gefen shi ya zaunar.
“Haba Zahra? Yau kuma Daddyn ake jin kunya? Kin barwa Mahmud ni kenan surukuta kike so mu fara ko?”
Da Daddy ya san kunyar da yake tara mun da bai yi wannan maganar ba.
“Zahra’u ai kunya ta kare daga lokacin da kika ďau kafa kika je neman auren Mahmud har garin landan……”
Cewar Dada tana tauna goron ta hankali kwance, fuskar ta shimfiďe da murmushi.
Daman nasan Dada ba zata bar maganar nan ba idan taji, shikenan ta dinga terere da ni kenan!..
Faisal ne yayi murmshi ya gyara zama yace
“Haba Dada ke da ake son a shawo kan amaryar zaki dinga tsokano ta kuma?”
Kawai sai na fashe da kuka na tashi da sauri da shige daki, su kuwa suka dinga kyalkyala dariyar su me bayyanar da zallar farin cikin da suke ciki. Banda Mami da take ta aikin basarwa tana gwada lambar Mahmoud a karo na barkatai bai ďauka ba. Tun tana tunanin ko wata matsalar ce har ta gano cewa Mahmud ďin na ta matsayin sirika yake so ya bata tunda a gabanta suka yi waya da Daddy da Faisal amma ita ya kasa ďaukar tata. Haushin sa ya turnuke ta! Wato iyashegen da zai shirya mata kenan kawai saboda zai auri Zahra? Yo nan duniya akwai wata alakar da zata janyo irin wannan ýar jin kunyar a tsakanin su? Aikuwa idonta idon shi zai gane kurenshi..
Ta ajiye wayar ranta a jagule, Daddy da ya fahimci abinda yake faruwa tsab yayi murmushi ya kau da kai yana burin ganin yanda wannan drama zata kare.
Ganin ina so lallai na shigo musu da wani shirme Daddy ya shigo ďakin da nake da kansa yayi mun faďa tatas akan kada na kuskura nace zan mayar da shi abokin jin kunyata. Shi ubana ne a kowanne fanni a kowanne yanayi a kowanne mataki, kuma babu abinda zai goge hakan, idan har na shigo masa da wannan shirmen kamar na rage masa matsayi ne don haka na shiga taitayi na zubar da waďannan sabbin mu’alamar da nake shirin kullawa da su ko kuma yasa kafar wando ďaya dani.
A dole na na warware na futo muka yi kalacin safe, duk da ba wata magana da ta futo daga bakina, muna kammalawa Dada tayi gyaran murya ta shiga samun albarka
STORY CONTINUES BELOW

“Kinyi halacci kinyi biyayya kuma kunyi adalci da tunani mai kyau Zahra. Naji daďin abinda kika yi musamman ďaukar Rabi da kika yi ba ki shiga jirgi kin tafi ke kadai ba. Kin ceto ran marayan Allah, kin ceto mutuncin iyayen ki, kin ceto kwanciyar hankali da farin cikin mu da ke walagigi a kan hanya. Allah ubangiji yayi miki albarka.
Allah ya tabbatar da alkhairi, daman kowa yana da irin wannan buri cikin ransa a kanku furtawa ne bamu yi ba, babu wadda ta cancaci auren Mahmoud kamar ki, shima babu wanda ya kai shi cancantar ki. Saboda haka wannan abun alkhairi ne da farin ciki, ban furta bane tun farko saboda shi sha’anin aure ba’a yi masa shishshigi amma wannan yaro Mubarak bana yi miki sha’awar sa. Haka kawai hankalina bai kwanta da shi ba, nayi addu’a da istihara a kan shi amma banji na samu nutsuwa da gamsuwar da nake so ba, ashe akwai abinda Allah ya boye, babu abinda zamu ce da Allah sai godiya. Su kuma waďannan shaiďanun da suke wannan makirci mun mika su ga mahaliccin su, kuma munyi Imani ba zai bari suyi galaba a kanmu ba…..”
Sai maganar Dada ta soma rawa, duk jikinmu yayi sanyi; kwarai akwai ciwo da bakin ciki ace naka ne yake irin waďannan abubuwa, akwai bacin rai ace kullum kana kokarin haďa kan iyalin ka wani yana bata maka shiri, akwai bakin ciki ace ka haifi butultaccen bawa mugu mai bakar zuciya. Amma kuma kowanne bawa da irin tasa jarrabawar, bai yiwuwa ace kana bin Allah kuma hankalin ka kwance baka da matsala, dole kayi ta gamuwa da ibtila’i.
Dakyar Daddy da Mami suka shawo kan Dada ta daina kuka, sannan akayi addu’a aka shafa. Gabaďaya muka futo, Faisal ya ďauki Dada da Baba Rabi zuwa gida, Mami ta ďauke ni zuwa gidanta a bisa umarnin Dada, wai naje na huta kwana biyu sannan na dawo. A gidan muka bar Imam da Daddy suna tattanawa akan wasu al’amuran da Daddy yake son fahimta da kuma hanyar da za’a bi a shawo kan matsalar.
………………………………………………………………….
Tun ranar da muka dawo da muka yi waya da Mubarak bamu sake yi ba sai bayan kwanaki huďu, duka wayoyin shi a kashe suke, wani zubin ya kan bani tausayi amma da na tuna cewa komai soyayyar mutum a gare ka yafi son kan shi idan wasu al’amuran suka shigo sai na tattara shi na ajiye a gafe.
Shirin biki ake yi babu kama hannun yaro, wannan karon cikin zumuďi da walwala da matsanancin farin ciki ake yin komai amma a sirrance.
Imamu ya zamo tamkar wani ďan’uwan jini a gare mu, domin a kullum ta Allah ina magana da shi sau biyu ko uku a waya, ina matukar mamakin yanda aka yi ya chanja ya koma irin wannan nutsatstsen mutum mai nagarta. Wani lokacin kuma ya kan bani tausayi, domin duk yanda yaso boye feelings ďin shi a kaina ni ina ganewa. Sometimes ma wayar gagara take yi sai muyi charting kawai ko kuma yayi mun dogayen voice note.
A cikin waďannan kwanakin babu inda labarin fasa auren Ya Mahmud da Amina bai karaďe ba, wani zubin tunani nake yi anya kuwa ba biyan waďannan bloggers ďin da media ake yi ba suke rubdugun posting waďannan labaran? Da muna rayuwar mu salin alin, bamu ďaya daga cikin masu kuďin da media ta damu da rayuwar su ko son rawaito rahotanni akan su, amma tunda labarin ya Mahmud da Daddy ya futo wanda shi ma bamu sam uban da yaje gidan jarida ya saka a wallafa shi ba shikenan rayuwar mu ta koma talla; kowanne motsi muka yi sai an baza a duniya kowa yaji.
Ya Mahmud kam bamu sake magana da shi ba, ya kira babu adadi bana iya ďauka, a duk lokacin da na tuna abinda naje London nayi sai naji kunyar kaina ta kamani, wai a ina na samu wannan courage ďin da na iya abinda nayi? A ina na samu karfin zuciya da kwarin guiwa da zeal ďin da naje nayi abinda nayi a gaban Ya Mahmud? And after everything kuma na sake ďaukan wayar shi? Toh nace mi shi me? Ai kawai a tafi a haka. Ina ga shima ya gane bazan ďaukan bane ya hakura ya daina kira.
Biki ya rage saura sati ďaya dangi da ýan’uwa da abokan arziki suka soma cika gidan Dada, ko’ina ya ďau harami, dalilin da ya sanya na tattara yanawa yanawa ni da Ya Nuratu da Amalie muka koma gidan Mami, duk da cewa akwai wasu bakin na Katsina a gidan amma tsirari ne. Ýan mata ne ýaýan cousins ďin Mami tsala tsalan Katsina kamar su su kayi kansu don kyau da tsarin halitta, tun kan a fara bikin basu da aiki sai ware music suna tikar rawa da ciye ciye, abun nasu har mamaki yake bani, duk da akwai waďanda ma suka girmeni amma ni banga zan iya shiga wannan shirmen sharholiya da shashanci ba, ko da yake rainon Dada ai ba karya bane. Ko music sai da na kusa kammala secondary school na fara ji, rashin sabo ma ya sanya har yau basa yi mun daďi a kunnena balle su shagaltar dani jinsu. Lokacin nishadi da bakin ciki karatun alqurani aka horar dani na ji, wata irin kyakykyawar tarbiyya na taso a ciki wadda ta tsareni daga sharrin fituntunun zamani irin na masu shekaru kamar nawa. Kamar yanda ake cewa goyon kaka lalacewa suke yi da tabara da rashin tarbiyya a kaina lallai wannan hasashen ba haka yake ba domin za’a haďa ýanmata guda ďari a garin Abuja ba’a samu me nutsuwa ta ba. Wannan kenan!
Yau ta kama alhamis, biyar ga watan February, wanda yayi dai dai da sauran kwanaki takwas a ďaura aurena da Mubarak a zahiri, amma a baďini bansan shirin da suke yi wa yanda zasu juya wannan al’amari ba. Ni kaina idan na tuna cakwakiyar da take gabanmu sai naji jikina yayi sanyi, hankalina ya tashi domin na tabbatar akwai ďan karamin yaki.
Ina kwance akan lallausan English bed ďin Mami wanda kamshin channel no5 ya huda ina tunanin rayuwa, tsoron Allah na kara tsarga zuciyata da cikin jikina ina tasbihi ga sarkin sarakuna almusawwiru mai sauya al’amari naji tattausan hannun Ihsan a bayana tana girgiza ni. Firgigit na tashi na zauna ina murmushi.
“Amarya guda da tunani?”.
Ta faďa cikin sigar zolaya, murmushin na mayar mata sannan nace
“Hmmm! Wannan amaryar ba irin kowacce bace Ihsan! Ya kike? Ina Amani?”
Gyaran zamanta tayi tana cewa
“A gida na sauke su sannan na taho nan!”
Na kai mata duka ina cewa
“Shine baki taho mun da ita ba, naga yanzu wani rashin m kike ji ba ma kya zuwa ko’ina da ita, sai dai ki murza ďauri ki ďauki mukullin mota kina yawo kamar wata budurwa! Toh wallahi zan haďaki da Ya Faisal a chanja wannan tsari sam baiyi ba….”
Dariya kawai take yi tana buďe ledar da ta shigo da ita a hannun ta
“Toh ai yazo gidan sauki tunda ga maman ta zata yi aure, sai na tattara miki ita ta taya ki zaman ďaki ni kuma na ďora gayuna daga inda na tsaya”
Nace “kamar har zuciyar ki…….”
Tace “toh bari kigani Allah ya kai mu ranar da zamu kai ki Lagos!”Gift bag Ihsan ta ciro daga cikin ledar da ta shigo da ita ta miko mun.
Na karba cikin rashin fahimta sannan na sa hannu na soma warware jan zaren da aka kulle box ďin da shi.
Na sa hannu na buďe box ďin cikin mamaki domin zargin da zuciyata take yi akan abinda yake ciki. Ina kokarin buďewa card ya faďo wanda aka yi wa rubutun taya murnar aure da tsararrun kalamai na turanci.
A sanyaye na buďe box ďin sai ga wata irin siririn saitin diamond, ďan kunne da sarka da bracelet da anklet da zobe ýan siri siri kamar zasu tsinke sai shegen kyau da walwali kamar zasu kashe maka idanu. Idan akace kiyasta kuďin su za’ayi za’a baiwa naira kunya don haka nayi dagalo kawai ina kallonta idanu na cike da kwalla.
“Ki karba da hakuri, it is the little I have saved for you Zara! Zan haďa miki da addu’a da fatan alkhairi da kuma kasancewa a tare da ke a kowanne yanayi a kowanne hali na rayuwa. Any time you need a shoulder to cry on, anytime you need a company, anytime you need a listener I’m ready to serve you! Duk da nasan bamu yi irin shakuwar da kuka yi da Aisha ba amma ina fatan zaki yarda dani kamar yanda kika yarda da ita kuma zaki kasance mai neman taimakona a duk lokacin da bukatar taimako irin na aminiya ko ýar’uwa ta jini ya taso miki.+
Kiyi hakuri da zaman aure Zahra, kowanne aure da kika gani yana da irin na shi matsalar da kalubalen babu wanda yake cikin zaman lafiya da farin ciki ďari bisa ďari a gidan aure. Amma hakuri, juriya, addu’a da kokarin kyautatawa juna yana kawo matukar kwanciyar hankali da masalaha a zaman tare. Ki koyi mantawa da sharrin wanda kike zaune da shi da tunawa da alkhairin shi, zaki fi jin daďin yin mu’amullah da shi. Ki saka a ranki komai sharrin me sharri kinfi shi da iko da izinin Allah kuma ba zai ci galaba a kanki ba, ki guji mummunan zato da zargi ga abokan zamanki musamman kishiyar ki, babu ruwanki da ita, tsakanin ku ya zama hirji da kyautata zato da kuma mu’amulla mai sauki daga nesa nesa ba wadda zata kawo sabani ko illa a gare ku ba.
Ki rike addu’a da gaskiya da amana da juriya da hakuri da ladabi da biyayya, idan kika rike su, babu inda za kije ki zauna lafiya ba. Ina yi miki fatan samun dukkan alkhairin da yake cikin aure ina nema miki tsari da duk wata fitina da sharri da tashin hankalin da yake ciki. Allah ya sanya ki dauwama cikin farin ciki da jindaďi da kwanciyar hankali a gidan auren ki Zahra ya baki zuri’a ďayyiba mai albarka.”
I got very emotional da bansan lokacin da na dinga hawaye ba, hawayen farin cikin samun masoya masu kaunata irin Ihsan, da kuma kewar Aisha mai yawa da ta taso mun, har abada bazan iya haďa wani mahaluki da Aisha ba cikin zuciya ta. Amma kulawa da kaunar Ihsan a gare ni tana yawan tuna mun da Aisha, suna kaunata lillahi wa rasulihi ba don wani dalili ba har wani lokaci sukan bani mamaki.
A hankali ta sanya hannunta mai kama da glass wajen haske da kyalli saboda tsabar jindaďi da kulawa da ya ratsa ciki da wajen shi ta dinga goge mun hawayena without realizing ita ma hawayen take yi. Na rungume ta na fashe da kukan kewar Aisha kamar a lokacin gawarta take gabana, wata irin kewar ta ta lullube ni kamar na buďe idanu na ganta a kusa dani.
Sai da Mami ta shigo ta rarrashemu sannan muka samu muka tsagaita da kukan. Ta zauna a bakin gadon tana yi mana nasiha akan rayuwa da muhimman abubuwan cikin tare da bamu shawarwari akan zamantakewar rayuwa da mutanen da Allah ya hada mu zama inuwa ďaya tare da su. Ya Nuratu ta shigo ta same mu itama ta zauna jin kayatacciyar lecture ta Ilmi da wayewa da exposure na rayuwa daga wajen Mami. Bamu muka tashi ba sai da aka yi kiran sallar la’asar sannan na shiga wanka su kuma suka tafi sallah.
A gaggauce na shafa mai nayi sallah sannan ďauko kaya na saka. Duk wanda ya kalleni ya ga amarya, domin Sudanese ďin da tayi mun gyara ta dame chadian ďin da tayi mun wancan gyaran na bikin mu da Imamu iyawa da kwarewa. Wani irin kyalli fatata take kamar madubi, na koma wata ďanya sharaf kalar furanto mai haske, idan kika taba jikin nawa kuma kamar atafa don laushi da taushi ga wani sahihin unique qamshi mai sanyaya zuciya na bin duk wata gaba ta jikina yana karaďewa. Gashin kaina kansa abun kallo ne, don duk wannan karfin babu, ya koma soft ya kwanta lambau a gadon bayana kamar an jera shi, shima kalar kamshin sa daban ne amma kamshin lavender yafi tasiri fiye da kowanne acikin gashin.
STORY CONTINUES BELOW

Ihsan na ďauka muka tafi gidan su Aisha a dalilin kiran da Umma tayi mun cewa naje suna nemana! Har yau ban daina jin faďuwar gaba ba idan nazo kofar gidansu Aisha, kuma ban daina sa ran zata leko ta window tayi waving ďina idan taji horn dina ba kamar yanda take yi. Shiyasa wani zubin idan na shigo gidan nakan daďe cikin mota ban futo ina jin kamar hakan zata faru.
Ikram ce ta budè mana kofa, tana gani na ta rungume ni tana murna sannan muka shiga ciki. Dukansu suna nan a parlour har da Abba, muka zauna muka gaishe shi ya amsa cikin farin ciki da kulawa mai yawa, har yanzu idan nazo gidan su Aisha sai launin idanun iyayenta sun chanja idan suka ganni, dalilin da ya sanya nake zuwa gidan akai akai saboda su saba da ganina ni kaďai na daina tuna musu da ita a kowanne lokaci suna jin babu daďi.
Nasiha Abba yayi mun sosai Umma tana taya shi, daga nan yace wa Iky ta ďauko masa ajiya a ďakinsa. Bayan ta ďauko ya miko mun da hannun sa, envelope ne mai nauyi alamar kuďaďen da suke ciki masu yawa ne. Na shiga yi masa godiya cikin ladabi da tausasawa.
Kafin na gama godiyar hidimar Abba Umma ta futo daga ďakin da ta shiga tana janye da katuwar luggage bag ďin “Victoria secret” tazo gabana ta ajiye sannan ta koma gefen Abba ta zauna a sanyaye, shikuma ya mike yana amsa waya ya shiga ciki
“Zahra ga gifts ďina nan babu yawa! da Aisha muka yi order a America lokacin da muka je bata da lafiya! Ban samu na baki ba aka yi rasuwar daga baya kuma zancen auren ya sauya Salo……buďe ki gani”
Ihsan ce ta ta kwantar da jakar ta buďe itama jikinta a sanyaye, wasu irin customized kaya ne a ciki, irin su lingerie, pyjamas, soft panties, bras, da wasu silk gowns jikakku masu azabar kyau irin wanda duk haďuwar kayan lefen Imamu basu saka irin su a ciki ba. Mun sha maganar wannnan siyayyar da Aisha nace mata Mami ta hanani kuďin wai sunyi yawa kuma komai ina da shi fitina ta tayi yawa, ashe shi ne ta gayawa Umma siya mun su a matsayin gudunmawa.
Wani lump ya haďu a makoshina na kasa daurewa kawai na fashe da kuka sosai na kifa kaina a jikin kujera. Iky ta taso ta rungume ni itama tana kukan cikin karyewar zurciya. Umma ce tayi karfin hali ta soma yi mana faďa1
“Menene haka Zara? Meye na kukan? Yaushe ne zaku daina irin wannan kukan don Allah akan Aisha? Addu’arku tafi bukata amma bashi da amfani ace duk lokacin da aka yi maganar ta sai kunyi kuka. Kowa na haka ne, dukanmu zaman jiran ta muke yi ita da ta tafi bata yi sauri ba. Don Allah kada ku bari Abba ya futo ya same ku kuna wannan kukan ya isa!”
Ni dai bansamu bakin magana ba har muka futo daga gidan ina share hawaye, Abban ya futo parlour ya same mu shima ya zauna ya fara yi mana nasiha da rarrashi, kai kawai nake ďagawa hawaye na kwaranya a idanuna, cikin zuciya ta ina yi mata addu’a da fatan alkhairi da ni’imar Allah a gare ta.
Ragowar yinin ranar haka nayi shi cikin kewa da maraici, sai da na kunna karatun alqurani na dade ina ji sannan na samu ýar nutsuwa. Wajen karfe shaďayan dare ina kwance a ďakin Mami Ya Nuratu ta shigo kawai ta saka mun wayar ta a kunne ta juya ta futa, duk tunanina Dada ce, saboda ta bugo mun wayar babu network tana ta ďaukewa. Cikin nutsuwa nace
“Yauwa Dada yanzu kina jina?”
A maimakon muryar Dada sai kunnena yaci karo da muryar Ya Mahmud. Cikin murya mai kaushi da bacin rai ya soma magana
“Don’t cut my call Zara kuma ki tsaye ki saurare ni attentively! I want you to drop this nonsense abubuwan da kika tsiro da su idan ba kina so mu bata ba.
Me kike nufi da daina ďaukar waya ta Zara? Are regretting your decision? Uh? Tell me?( kina danasanin hukuncin da kika yanke ne?)”..
Yanayin yanda mugun bacin ransa ya futo cikin sautin shi ya sanya jikina yayi sanyi.
“I will never regret what I have done (bazan taba yin danasanin abinda nayi ba)”
Na faďa a hankali.
Ya sake cewa
“Are you forcing yourself to accept me(kina tursasa kanki ne ki karbeni?”
Na sake cewa
“No at all”
Yace
“Tell me meye matsalarki ki dani? Meye uzurin ki? Gaya mun? Forget abinda ya shiga tsakanin mu let’s talk like the brother and sister we are”
Cikin sanyi na soma magana
“Ya Mahmud ina jin kunyar abinda nayi, I sometimes feel as if na……”..
Sai na kasa karasawa.
Murmushi yayi mai sauti yace
“As if kin zubar da ajin ki da kimar ki? Ko? Do you even know what you are thinking? Toh ki kwantar da hankalin ki baki zubar ba! Wasu ma masu yawa kika siyo kika kara akan wanda kike da su! Kuma idan da duk mutanen duniya zasu daina ganin aji da darajar ki, ni ba zan daina ba. Kuma ina tabbatar miki cewa babu wani abu mai aji da daraja da mutunci a gare ni da ya kai ki.
Zahra ni waye? Kuma wacce darajar nake da ita da har zan daina ganin ta wani? Gaya mun sauran mutanen da nake da daraja a idanun su a duniyar nan? You saved me Zahra! You saved me from heartbreak, from embarrassment from the greatest kunyar da duniya taso bani, kinyi saving Daddy da Mami daga faďawa damuwa, kinyi saving repetition ďin su, kinyi saving family name gabaďaya Zahra! You are a warrior and Allah is surely going to bless you abundantly and He will never let you down!
Kinji?”
Wata nutsuwa kalaman na shi suka saukar mun irin wadda zuciya da kwakwalwata take bukata! Hankalina ya kwanta, zuciyata tayi sanyi yayinda jikina ya gamsu ďari bisa ďari da cewa ban zubar mi shi da darajar shi da ajin shi ba.
Jin nayi shiru ya sake cigaba da maganar cikin sanyi
“Another thing da nake so da ke shi ne ko daina tursasa kanki akan lokaci ďaya zaki chanja mun matsayi, No! It doesn’t go that way! Zaki yi stressing kan ki da yawa, kuma zaki baiwa zuciyar ki wahala! Just let everything fall into place on it’s own. Kici gaba da mu’amala dani as your Ya Mahmud, as that brother you feel free and safe with!
A hankali komai zai yi daidai Insha Allah! Just take care of yourself ok?”
Cikin matsanancin farin ciki nace
“Ya Mahmud you are too nice wallahi! I lo……”
Sai na kasa karasawa kamar yanda na saba faďa da, yana mun abinda naji daďi zance “I love you soo much Ya Mahmud”
Ashe I love you kala kala ce, waccan ma’anar ta iri daban da wannan.Bamu ankara hira muke yi ba sai da Mami ta shigo ďakin da shirin bacci tana cewa
“Wai Zahra me kike yi ne har yanzu?”
Sannan Ya Mahmud yayi sauri yace
“Goodnight Zahra ki gaida Mami”
Ko jiran amsata bai yi ba ya kashe wayar, ni kuma na mayar da hankalina ga Mami da ke tsaye tana kallona tana jiran amsata. A sanyaye nace
“Mami wai Ya Mahmud yana gaishe ki?”
Cikin mamaki tace
“Wai wayar da Nuratu ta kawo miki ce tun ďazu?”
Na ďaga kai ba tare da na kalle ta ba, itama bata sake cewa komai ba ta nemi waje ta kwanta a gefena ta soma addu’o’in ta. Nima na gyara kwanciyata na soma bacci a dalilin nutsuwar da na samu cikin wayar da muka yi da Ya Mahmud!
RANAR TALATA
………………………………………………………………….
Ranar talata aka soma hidimar biki, Ya Nuratu ce ta shirya kayataccen “henna party” a harabar gidan Mami ita kuma ta ďauki nauyin dukkan henna artist din da aka ďauko a garin Abuja, wasu na daga Kano aka hayo su.
Ina zaune cikin wata ýar bukkar da aka shirya saboda ni, an kawata ko’ina da fitulu da flowers, ga wani tattausan music yana tashi na larabawa.
Sabrina, sudanese ďin da tayi mun gyaran jiki ita ce take yi mun zanen lallen mai kama da ana zanawa da allura saboda sirantar shi, kwarkwaro biyu ne a gefenta, baki da ja, idan tayi da bakin sai ta kawo jan ta ratsa abun gwanin ban sha’awa.+
Ba’a tashi ba sai karfe tara na dare, a gajiya na shiga cikin gida na samu ruwa mai zafi nayi wanka na saka kayan bacci na kwanta domin idona har wani yaji yake yi, nayi baccin kenan wayata ta soma rurin neman agaji na buďe idanuna dakyar na ďauka ba tare da ko kula da sunan me kiran ba……
“Hello my bride”
Cikin sanyin jiki na tashi zaune a take kuma baccin ya wartsake daga idanuna, na jingina jikina a jikin pillow nace
“Where have you been( ina ka shiga)?”
Shima a sanyaye yace
“Issa long story sweetheart but I miss you so much”
Duk da kalmar bata shiga kunnena ba sai na mayar mi shi da irin martanin da yake so. Sannan yace
“Gobe da safe ne flight ďin su Hajiya! Su 20 ne gabaďaya daboda kinsan bikin ya haďu da na cousin sister na a Sokoto Saboda haka suka rabu biyu wasu zasu tafi can”
Nace
“Allah ya kawo su lafiya! Kai kuma sai yaushe?”
Sai da yayi wani dum! Na seconds kafin yayi magana
“Wanne events zanyi attending ne?”
Nayi murmushi nace
“Daga gobe kowanne event da kai banda walimar ranar Friday bayan ďaurin aure.”
Ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan yace,
“Insha Allah gobe da yamma zamu sauka! I’m so sorry Zahra wallahi I’m having a very difficult time from my side, I’m sorry!! I’m very sorry!!!”
Na ji tausayin shi , amma da na ayyano yanda abun zai kasance ba domin Allah ya tsallakar dani ba sai naji tausayin na shi da nake ji ya ragu sosai. Cikin karfin halin nace
“Me yake faruwa? Surayya ce? Ko office?”
Ya sake yin jimm! Sannan yace
“Daga office ne! I’ve handled Surayya kuma ba zata sake bada matsala ba insha Allahu”
Nayi ajiyar zuciya nace
“Allah ya warware komai ya kawo maka mafuta”
Ya amsa cikin sauri da
STORY CONTINUES BELOW

“Ameen ya rabbal alameen”
Daga nan muka ďan taba hira mara bala’in armashi kamar ba masu shirin yin aure a wannan satin ba kafin muyi sallama mu ajiye. Daga nan ban sake komawa baccin ba saboda tunanin da suka yi mun rubdugu.
Washegarin kuwa ýan’uwansa da iyayen sa suka sauka a garin Abuja, Daddy ne ya ďauki nauyin saukar su a wani tafkeken gidan sa da ke Wuse 2 a maimakon manya manyan hotels ďin da suka yi booking. Cooks ma guda biyu Daddy ya ajiye a gidan saboda kula da bukatun abinda zasu ci.
Gidan Dada ma a ďinke yake da mutanen Yola da Katsina har da Kano, wato oganniya Inna Badi’a da iyalanta.
Da mutanen Lagos Kawu Sulaiman da nashi iyalin, da sauran ýan’uwa da abokan arziki waďanda halartar bikin nawa ya wajabta a gare su.
Misalin karfe biyar na yamma aka soma hidimar tafiya wajen Kamu, a lokacin ina ďakin Mami tare da Ihsan da make up artist ďina “Banke”
Matsanancin kukan da na sha ne ya sanya tsaiko wajen kammala kwalliyar akan lokaci, bayan na buďe akwatin kayan nawa naci karo da kayan kamu na kala biyu, sakin fulani da hand beaded asoke wanda zan sauya sai kawai hirar da ta faru a tsakanina da Aisha ta dawo mun daren da tazo ta kwana gidan Mami muka harhaďa kayan biki.
“Zara i can’t wait naga kayan nan a jikinki! ban taba ganin kalan da yake miki kyau irin gold ba, musamman idan Banke tayi magic din nan nata akan fuskarki! Allah this year amare zasu sha kunya idan suka ga shirinmu”
Dariya nayi sosai sannan nace “Aisha tawa! ya kukayi da Banke din ne? ni ban tambayeki ba!”
hararata tayi sannan tace
“ke wa yake ta taki! tun ranar da aka saka date din bikinki nayi booking! i wanted it to be a suprise gift, amma kawai Ihsan ta ruguza mun shiri ta kama ta gaya miki!”
Wai yau ga ranar tazo babu ita, ashe wai ba zata ga aurena ba, balle nata. Na fashe da wani irin matsanancin kukan da ya gigita su gabaďaya. Duk yanda naso tsayar da shi da rarrashin da aka taru a kaina ana yi mun bai tsaya ba. Ya Nuratu ce ta kira Ya Mahmud ta karamun wayar a kunnena bayan ta gaya mi shi abinda yake faruwa.
“Zarah ya muka yi da ke? Wanne alkawari kika ďaukar mun akan Aisha? Uhmmm… tell me?”
Cikin shashshekar kuka nace
“Nayi alkawari duk lokacin da na tuna da ita zanyi mata addu’a ba kuka ba”
Cikin sauri yace
“And what are you doing now(me kike yi yanzu)?”
Na tsagaita da kukan nace
“It’s not easy Ya Mahmud! Ba abu ne mai sauki na tuna Aisha a rana irin ta yau na hana kaina kuka ba, bayan duk wani shiri na bikin nan ita ce jigon sa! Bayan ko bikin ta bata ci masa burin da tayi wa nawa ba. Ashe mutuwa zata yi, ya zanyi na hana kaina kukan rashin masoyiya irin Aisha? Ba zaka taba gane kewar ta da nake ji ba…………
Ba zaku gane me nake ji a cikin zuciyata ba, ba zaku gane raďaďi da zogin da zuciyata take yi na rashin Aisha ba! Ku barni nayi kuka don Allah…..”
Ba sake fashewa da wani matsanancin kukan da yafi na ďazu sauti.
Cikin sanyin murya ya soma magana.
“Aisha ta rasu Zahra kuma muna yi mata fatan inda ta tafi ya fiye mata nan duniyar daďi! Kuka ba zai amfane ta da komai ba Zahra, kukan ki a gare ta ba shine zai tabbatar mata da kaunar da kike mata ba. Addu’a tafi bukata fiye da komai a wajen ki, and let me tell you wani abu
Believe me Aisha na tsaye a ďakin nan tare da ku tana taya ki farin ciki, tana nan tana kallon ki, kuma da ita za’ayi duka taron bikin ki, bambamcin tana raye da yanzu kawai shi ne ba zaki ganta a zahiri ba kuma ba zaki yi magana da ita ba. Wannan kukan da kike yi tana tsaye tana baki hakuri akan ki daina yi mata shi, ba zaki ji bane saboda Allah bai bamu damar jin maganganu irin nasu ba. But trust me tana nan tare da ke! Ki nutsu ki saurara sosai, you will feel her spirit all over you! Idan baki karbi rarrashin kowa ba ki karbi nata Zahra, saboda ita kaďai take magana da sautin da kunnuwanki ba zasu iya saurara ba. Don Allah kiyi shiru ka share hawayen ki ayi kwalliyar nan cikin kwanciyar hankali Zahra”
A hankali kalaman shi ke saukar mun da nutsuwa suna wanke damuwata ďaya bayan ďaya zuciyata na tabbatar mun da eh da gaske ne Aisha tana ďakin nan tare dani, kuma dagasken rarrashina take yi nayi shiru na yarda ayi mun kwalliya. Ke har ma hoton ta zuciya ta take zana mun cikin ďanďasheshiyar kwalliyar biki tana wannan murmushin da kowa ya santa da shi. Ban gushe ba ina sauraren shi har na samu nutsuwa na goge hawayen tsaf naje toilet na wanko fuskata wayar na makale a kunnena ina jin sa.
“Na wanke fuskata za’a fara kwalliyan Ya Mahmud”
Na faďa cikin kwarin guiwa da strength mai yawa.
“Yauwa amaryar Ya Mahmud ki tsaya make up artist tayi miki kwalliya mai kyau, your groom will be waiting to see your……”
Nayi kirif na ajiye wayar ina murmshin muguwar kunyar da ya bani. Kai! Ya Mahmoud ya san ta kan tsiya.
Tun daga kan Mami, Ya Nuratu, Ihsan da Banke ďin tsayawa sukai suna kallona kamar sokwaye saboda mamaki.
Na sunkuyar da kai ina dariya a hankali, wadda ta sanya Mami girgiza kai tare da juyawa ta bar ďakin, daman ita tuni ta shirya zata tafi wajen bikin har ta futa wajen mota aka je aka yi kiranta akan tazo ta rarrasheni ko zanyi shiru na bari ayi mun kwalliyar.
Lokacin da aka kammala kuwa ni kaina kasa ďauke idona nayi daga kan dogon madubin da nake tsaye a gabansa.
Yadin Sakin da na saka ruwan madara ne an mi shi wani irin embroidery mai ďaukar hankali da gold din zare da pearls da duwatsu, ďinkin kamole ne wanda ya fidda kyawun jikina ya zauna daidai, amma bai matseni da yawa ba. Da mara kwalliyar yadin aka yi mun irin naďin fulani a zamanance, doguwar tufkar da aka yi wa gashina gud biyu ta futo daga kowanne gefen kunnena gashin na kyallin gyaran da yasha.
Kunnena da wuyana wasu irin tafkekiyar sarka da yari ne Indian design masu kyalli da ďaukar idanu, sai wani irin dutse ruwan goro mai kama da murjani da aka ďora mun akai.
Hannun haguna awarwaraye ne guda goma shabiyu sirara da zobuna guda uku. Hannun dama kuwa wani ubansun bangles ne masu mugun kauri guda biyu da zoben su.
Haka ma sawun kafafuna guda biyu siraran sarkoki ne ka jera wajen hawa biyar kowacce dukan su kuma disayin din India ne masu kyalli sosai.
Takalmina half cover ne customized daga “Laura Ahman” da fatar python zalla aka yi shi sannan aka yi mishi ado da gashin ďawisu wanda ya nayar da shi wani irin abun kallo da ban sha’awa.
Sannan aka kawo katon ďanďasheshen mayafi mai aikin sequence launin ja aka rufe ni tun daga sama ruf har fuskata da ke kyallin amarci da soft glam ďin bankspro wanda ya mayar dani the most classy African queen ďin wannan shekarar; ni na fara baiwa kaina wannan award ďin.
Karfe bakwai da rabi na dare ina kwance a bayan sabuwar “Rolls Royce luxury bridal car” wadda Daddy ya siya mun a matsayin gift ďin aure a kofar Bluevelvet Marque ina jiran a bani damar futowa na shiga wajen bikin.
Gefe guda ina tunanin dalilin da ya sanya Mubarak kashe wayar sa tun bayan da muka yi magana daren jiya, sannan da alamu basu zo ďin ba don da ya kirani. Kaina ya ďanyi nauyi a dalilin tunanin yanda zamu kwashe da wannan kullalliyar matsala mai sarkakiya.
Ina cikin wannan tunani Ya Nuratu ta dawo ta buďe kofa bayan ta lullubeni sosai da mayafina, duk da tsohon cikin da take fama da shi bai hana ta yin ruwa da tsaki cikin hidimar bikin nan ba. She is not my cousin, she is my sister, yes the sister I never had.
Ina futowa daga motar George Okoro da mukarrabansa suka ce da wa Allah ya haďa su bada ni ba? Ga sauran kananan photographers suma na aikin su, ga team ďin “nategenius” suma suna abinda ya kawo su, kowanne na kokarin ďaukar best moment ďin shigowar amarya cikin wajen biki.
Kawayena suka soma cikin marque ďin cikin ashobin su Ihsan na gaba tana jagorantar su. Sannan Ya Nuratu da A.laila suka kama hannayena side by side suka shiga dani cikin hall ďin suna taka rawa, wakar Nura m inuwa mai taken “Amarya ýar amana” tana tashi tana baiwa taken namu armashi har muka isa cikin ýar bukkar da aka tanada saboda kamu suka shigar dani suka ajiye ni sannan kowa ya koma ya zauna.
Babu bata lokaci aka soma gundanar da shagalin biki, Inna Badi’a aka kira ta buďe taro da addu’a, ta taso tinkis tinkis cikin wannan kasaitaccen takun na ta tasha kwalliya ta iso ta karbi mic ďin, babu wanda baiyi mamakin far’a da farin cikin da take yi a wannan rana ba, abun gwanin ban al’ajabi. A wannan lokacin sai da na share kwalla, wai cikin wannan duniyar ace mafi kusanci da kai shi yafi tsana da son ganin bayanka. Na sauke ajiyar zuciya ina mai hamdala ga Allah da ya kubutar da mu daga sharrin da makiya suka kulla mana.1
A.laila ce tayi jawabin barka da zuwa da godiya ga baki sannan Mc ta nemi kawayen amarya suzo su kasa su tsare ýar bukkar da nake ciki suyi ciniki da ýan uwan ango kafin ayi kamu.
Nan fa su Ihsan da Najwa da sauran kawaye suka taso aka soma ďauki ba daďin ciniki, domin cewa suka yi mikiyan goma suke bukata ko kuma a fasa kamun.
Dakyar da cibin goshi aka sasanta suka karbi 2m lakadan a cikin paper bag ba ajalan ba. Nan guri ya kaure da sowa da tafi sannan suka bada hanya aka zo aka feshe ni da sassanyan turaren “Swiss Arabian” ana ta faman guďa tare da yaye mun mayafin da aka rufa mun.
Daga nan aka soma hotuna iri iri kafin a futar dani ta kofar baya zuwa dressing room, inda nayi sauri na sauya kayana zuwa hand beaded asoke ruwan gold, duka costume ďin jikina sai da A.laila ta chanja mun da wasu gold ďin design ďin Dubai. Aka yi mun kyakkyawan naďin gwargwaron da ya dace da fuskata sanann aka feshe ni da turare.
A yanda aka tsara wannan shigowar ta biyu da ango za’a yi, rashin samun yanda ake so ya sanya na shiga ni kadai cikin taku mai aji, mc na koďa kwalliyata fiye da ta ďazu har naje na hau steps ďin da zasu sada ni da wajen zamana acan sama.
Shagali fa ya kankama, aka soma hada hadar rabon abinci irin wanda za’a irga bukukunan da akayi irin shi. Duk wanda kika kalla a wajen raha yake yana darawa saboda nishadi, Mami bakin ta kamar gonar auduga tana zaune cikin manyan aminanta da kawayen ta tun na secondary da na jami’a da wanda harkar kasuwanci ta kulla su aminci.
Sannan Mc ta kira Ali jita yazo tsakiyar fili ya gwangwajewa yana raira wakar da aka sanya ya raira ta bikin mu da sarewar muryar sa mai zaki. A hankali na taso na sauko tsakiyar fili bisa ga umarnin Mc, wayyo! Nan fa ruwan liki ya balle kamar ruwan sama. Mami da kawayen ta da dollars suka dinga manni, ýan’uwa da abokan arziki sunyi mun kara! Naso sake wani kukan a lokacin da Umman su Aisha da iky suka iso gabana suna lika mun kuďi, cikin sakin fuska tace
“Idan kika yi kuka a yau Aisha ba zata yafe miki ba Zahra!”
Duk da haka sai da na share hawaye, dai dai nan Ali jita kuwa ya soma wakar “wayyo Allah Mamana”
Na rungume Mamina na fashe da kukan da suke ta kaffa kaffa kar nayi, ita Mamin rushewa tayi da kukan muka kankame juna gwanin ban tausayi da burgewa. Allah ne ya taimaka kwalliyar bata lalace ba amma nayi kuka sosai, Ihsan na gefe tana goge mun fuskar da tissue tana bani baki akan kada na lalata musu kwalliya ba’a gama hotuna ba.
Karfe goma taro ya watse cikin kwanciyar hankali da farin ciki kowa ya sa albarka domin iya kayatarwa bikin ta kayatar. Iya haduwa ya haďu kuma iya burgewa ya burge.
Bayan mun dawo gida ne Mubarak ya kirani ya dinga bani hakuri akan cewa delaying đin flight ďin su aka yi sai yanzu suka sauka. Nace babu komai waye bai san halin rashin tabbas na ďanadam ba. Kamar yaso ya gane magana na gaya masa kuma sai ya sauya zancen da wani. Nayi maza nace masa bacci nake ji saboda gajiyar da nayi, da haka muka ajiye wayar kowanne rai ba daďi.
STORY CONTINUES BELOW

Washegari aka yi mothers evening wanda Mami ta shirya a “Transport Hilton” . Bansan tsakanin shi da Kamun wanne yafi haďuwa ba, kuma bansan wacce rana nafi kyau ba, yau ďin Rose gold ne a jikina na luxury net lace da na siyo a wani kantin fabrics a “Florida” ďin “America” acan kuma wani hamshakin fashion designer ya ďin ka mun. Wata irin gown ce mai ďaure kai tamau da mamakin yanda aka ďinka ta,sai dai sam bata fidda surar jikina kamar an zana ďin nan ba, amma kuma ta zauna sosai, ko’ina kuma a rufe ruf babu tsaga ko raga raga. Sannan aka ďora mun wata irin alkyabba ta wani stoned lace mara nauyi mai shara shara kalar shi pitch, sai ya haska rigar itama ta haska shi. Custimes đina ba irin na jiya bane, waďannan kirar Bahrain ne masu nauyin gaske kamar a jikina aka kera su don dacewa. Tsayawa yaba kyawun adona zai ďauki muhimman lokuta don haka mun tsaya daga nan.
Bikin yayi armashin da ya fi na jiya a dalilin zuwan ango taron bayan an fidda rai da shi, sannan Sarkin waka ya armasa wajen da salon basirar shi, wuri ya kaure da tafi da sowa da annashuwa ana ta liki, tun abun na burge ni har na soma igtigfari a raina, domin Allah yana kallo ana barnatar da kuďi kamar babu masu bukatar su a duniya.
A daren ranar duk yanda naso bacci ban iya yi ba, ko na minti ďaya kuwa, safa da marwa nake yi cikin ďakin Mami ina hawaye, kaina yayi matukar nauyi a dalinin tunanin abinda zai faru a gobe. Ya zata kaya? Ta ina al’amarin zai bullo? Ya za’a warware matsalar daga baya?
Ji nayi an dafa ni ta baya, na san Mami ce a dalilin kamshin chanel no5 da ya cika hancina. Ina juyowa na faďa jikinta ina kuka sosai, jikina sai karkarwa yake yi kamar ana kaďani, wani zazzabi ya dinga ratsa ni kamar ana hura mun wuta.
Bata ce dani komai ba ta jani zuwa kan gado na kwanta a jikinta ina kukan tana shafa mun baya, sai da nayi na gaji sannan na soma sauke ajiyar zuciya a hankali. Ta zame ni daga jikinta ta shiga toilet ta haďo ruwan sanyi da towel tazo ta fara goge mun jikina saboda zafin da ya ďauka. Bayan ta gama ta ballo paracetamol ta bani tare da shafe jikina da man habba tana yi mun tofi. A hankali na samu nutsuwa, zazzabin ya sauka har ina yin gumi.
“Ki daina tayar wa da kanki hankali Zara! Ki daina damuwa da yawa, Allah yana tare damu kuma ba zai tozarmu ba. Da ace bamu san komai game da wannan al’amarin ba fa Zahra? Da tuni fa haka rayuwar mu zata lalace lokaci ďaya mu shiga cikin kwandon bakin ciki da tereren duniya! Insha Allahu komai zai zo cikin sauki da salama, alfarmar Manzon Allah saw Allah ba zai baiwa makiya galaba a kanmu ba.”
A hankali na ďago kaina cikin sanyin jiki da dushewar murya nace
“Mami abina yake bani tsoro rashin sanin target din su akan yanda auren zai kasance, kada suje su kulla mun wani sharrin suce akan wannna dalilin MUBARAK ZAI SAKENI! ina tunanin yanda abubuwan zasu faru cikin tsakiyar biki ace ango ya saki amarya Mami duk da cewa muna da madogara kuma mun samu mafuta amma still bana son hakan ya faru dani Mami. Banason igiyoyin auren Mubarak su hau kaina”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace
“Zahra ya zamu yi da kaddarar Allah? Wannan hanyar ce kawai mafuta a gare mu, duk yunkurin da muka yi wajen hana faruwar hakan sai dai ya tona asirin mu! Abu mafi muhimmanci shi ne kowanne irin sharri zasu kulla miki zasu yi ne don su hana wani sha’awar auren ki ko kuma su bata ki a idanun mijin da zaki aura, toh Allah ya yayi miki wannan rufin asirin da kwanciyar hankalin, mijin da zai maye miki gurbin Mubarak ko kuturta da makanta da kurumta ne suka same ko lokaci ďaya nayi imanin ba zai guje ki ba.
Ki bar mutunen duniya da maganganun su, duk yanda aka ďaukaki wani al’amari ake magana a kansa watarana za’a gaji a daina. Babu abinda bai shuďewa sai mulkin ubangiji da kasaitar sa. Mu kuma gare shi muka dogara muna da tabbacin kuma ba zamu tozarta ba.
Tunda al’amarin nan ya taso kullum sauka goma sha ďaya Daddy ya saka ake yi a Yola, malamai goma sha ďaya ne suka tafi umra musamman da wannan niyyar sannan kullum sai an zazzage buhun shinkafa shida an dafa an bayar sadaka.
Ba ina nufin yawan abinda ake yi ne zai kubutar da mu ba, No! Allah da muka dogara muke yi domin sa mun kyautata niyyar mun shigar da waďannan ibadun a cikin bukatar mu da kyakykyawar niyyar Ubangiji zai dubi lamarin mu ya kawo mana ďauki.”
Nasiha da kwantar da hankali mai yawa Mami tayi mun a wannan dare kafin mu tashi mu ďaura alwala mu fuskanci qibla har zuwa lokacin assalatu. Sai da nayi sallah na kwanta, ita kuwa Mami baccin da bata yi ba kenan ta shiga sabgogin ta.
Kasancewar sai bayan sallar juma’a za’a ďaura auren ya sanya nayi bancina sosai, Mami tace su kyale ni sai na tashi don kaina saboda bana jin dadi.
Sai karfe goma na tashi nayi breakfast sannan nayi wanka aka soma yi mun shirin kwalliyar ďaurin aure.
Leshin da na saka yau mai nauyin gaske ne, domin duk jikinsa zare ne da aiki mai kayatarwa, kalar shi sky blue mai haske sosai, an ratsa fari da silver.
Fitted gown ce wadda ta zauna a jikina sosai, ta dinku iya ďunkuwa. Gabaďaya custumes ďin jikina silver ne na ďanyen diamond samfurin “Swarovski”.
Kaina kuwa wani irin turban aka naďan mun da raw silk fari sannan aka mayar da wani kyakykyawan netlace fari sol aka yafa mun tun daga saman kaina har kasa.
Fuskata light make up ne mai ban sha’awa, ba don bugun fanfalakin da zuciyata take yi ba wanda ya ďauke annuri da far’ar fuskata kyawun da zanyi sai yafi haka nesa ba kusa ba.
Na tabbatar yau akwai rikici, akwai hatsaniya kuma akwai tashin hankali mummuna da zamu fuskanta.
Ita kanta Mami jikinta rawa yake yi, duk yanda take kokarin boye damuwa da fargabar da take ciki kallo ďaya zaka yi mata ka gano cewa a diriri ce kuma a ruďe take.
Saura awa ďaya a ďaura aure muka isa gidan Dada tawaga guda cikin motoci na alfarma. Tun da na shiga gidan kirjina ya kara tsananta bugawa, bakina babu abinda yake yi sai ambaton Allah da neman gudunmuwar shi akan wannan al’amari.
Tunda muka zauna cikin ďakina su Ya Nuratu da Ihsan da sauran kawayena suke tsokana ta, amma sam ban ma gane abinda suke ba, ganin haka ya sanya Ihsan ta dawo gefena tana yi mun magana kasa kasa
“Zahra ko akwai matsala ne? You look worried and disturbed! Me yake faruwa don Allah?”
Duk iya dauriyar da nake yi da kaffa kaffa akan hawayena sai da suka zubo, domin da wani irin speed suke futowa magudanar su ta yanda ba zan iya rike su ba komai saurina. Ta dafa kafaďata jikinta a sanyaye tace
” Surayya ko?”
Na girgiza kaina a hankali ina kokarin tsayar da wannan hawayen domin hankalin sauran kawayen namu ya fara dawowa gare mu, amma ina, kamar cewa nake yi su zubo.
Bude baki tayi zata sake magana muka ji wani maroki ya rafka sallama daga can waje, sannan yayi hamdala ya sake yin hamdala ya kuma yin hamdala. Kafin ya koro bayanin da ya kaďa ýan hanjina, ya sanya dukkan wanda yake cikin gidan Dada cikin maďaukakin mamakin da bai taba shiga irin sa ba ya kuma firgita kunnuwa da zukata, ya gigita tunani da hankalin duk wanda ya ji shi. Ba wani bayani bane illa jawabin da marokin ya koro kamar hakw
“Al’amarin Allah sai kallo sai gani sai kyalewa, alkawarin Allah baya tashi, hakika matar mutum kabarin sa, wannan abu shi ne tuwo na maina miyata nama na, wannan abu shi ne ake kira da kai da kaya duk mallakin wuya ne. A yau juma’atu babbar rana da misalin karfe ďaya da rabi dai dai na rana Allah ya kaddara ďaurin aure tsakanin Likita bokan turai balaraben asali Alhaji Mahmud Ahmad lamido da tauraruwa sha kallo sha haske Hajiya Zahra Yakubu Lamido akan sadaki naira dubu ďari lakadan ba ajalan ba.
Allah……………”
Iya abinda kunnuwa da dama suka iya ji kenan wata irin matsananciyar hayaniya da sowa da kakabi da firgici suka kaure.
Iya kaďuwa na kaďu, iya tsorata nayi, iya mamaki nasha, iya confusion na shiga, har sai da na zamo daga zaune akan gadon da nake na zauna a kasa kaina na wani irin juyawa wadda tsantsar mamaki da firgici suka haifar.
Ihsan da Ya Nuratu suka kalli juna suka kalle ni sannan suka sake kallon juna, sai kuma suka runtuma waje cikin sauri kamar masu wasan tsere.
Kawayena da suke cikin ďakin suka dafa musu baya kowa na son zuwa ya tabbatar wa da kansa abinda kunnuwansa suka jiyo masa.
Aka barni ni ďaya cikin tsakiyar ďakin a zaune kamar gunki, jin rurin wayata ne ya dowo da ni daga hayyacina na mika hannu kan gado na janyo ta hannun nawa yana ta rawa nayi swiping screen ganin sunan Imamu a kai.
“Congratulations Zahra! We have made it!! We have made it!!! Mun yi nasara Zahra! Allah ya bamu nasara fiye da yanda muka yi tunani! Alhamdulillah!”
Duk yanda naso yin magana harshe na bai bani dama ba, yayi mun nauyin ba zai sarrafu kalma ta futo daga cikin sa ba. Ina ga shima tunanin hakan ya sanya shi katse wayar ba tare da ya damu da jin maganar tawa ba.
A guje Ya Nuratu ta shigo kamar ba mai tsohon ciki ba, tana zuwa ta rungume ni tana fashewa da kuka, kuka mai tabbatar da matsanancin farin ciki da murna.
“Ohhh sister I’m soo happy for you! Ya rabb I’m soo glad! Bansan irin yawan farin cikin da nake ciki ba a yau! Zahra Ya Mahmud kika aura! Ya Mahmud of all people! Ya rabb wacce irin sa’a ce da ke? Wanne irin al’amari ne wannan mai ban mamaki?”
Ban ce komai ba, toh me zan iya cewa bayan har yanzu kwakwalwata processing al’amarin take yi kamar cikin mafarki? Ni daman idan na shiga shock magana ta ďaukewa take yi na dinga kallon mutane da ido kawai kamar sabon kamu.
Bansan irin budurin da aka yi a ďakin Dada ba lokacin da labarin ya iso cikin gida duk da cewa ita ma ta san komai domin Daddy yayi alkawarin ba zai sake boye mata wani al’amari ba komai kankantar sa. Mami kuka take yi tana karawa, masu kaunar mu na taya ta murna wasu na rawa wasu na tsalle wasu na rangaďa guďa. Musamman a lokacin da Ya Omar ya shigo ya bayyana musu cewa sai da aka hallara tas duk wani mai ruwa da tsaki cikin ďaurin auren ya gabata a gidan Daddy da ke Mississippi sannan Mubarak ya kira uncle ďin shi a waya yace a dakata da ďaurin auren akwai matsala.
Daga karshe yace ai shi ya fasa gabaďaya yana bada hakuri, Uncles ďin na shi kuka ne kawai basu yi ba saboda tozarcin da ya janyo musu, Daddy yayi wani irin ni’imtaccen murmushi ya dubi Kawu Sulaiman wanda farin cikin sa akan wannan al’amari ya kasa boyuwa yace
“Shin ba ka zama waliyyin Zahra a wajennan na karbarwa ďana auren ta ba?”
A tunanin Kawu Sulaiman Umar ko Sadik Daddy yake nufi, don bai ma yi tunanin Mahmud wanda suke da tabbacin yana can turai yana jinya ba. Ransa ya baci, hankalinsa ya tashi domin su cikar burin su a tashi daga wannan waje babu ďaurin auren Zahra kamar yanda na Mahmud ya lalace a bar Daddy da kunya da tozarci a idanun manya manyan mutanen da ya gayyato wannan waje.
Rabuwa Daddy yayi da shi ya baiwa ambasada damar zama waliyyin Zahra, a take aka ďanyi ýan maganganu tsakanin su da Baban Mami, sai kawai ji Kawu Sulaiman yayi ana cewa
“Ni wane ina nemarwa ďana Mahmud auren Zahra a hannun ka…….”
Bai sake gane me ake nufi ba sai gani akai ya tattara babbar riga ya ďau waya yana cewa gashi nan zuwa. Abun gwanin ban dariya ga waďanda suka san halin da ake ciki, sauran mutane kuwa na ďaukar hakan a matsayin ruďewa da tashin hankali.
Cikin mintina al’amari ya juya, a gaban waliyyan Mubarak aka ďaura auren Mahmoud da Zahra akan sadaki dubu ďari wanda Daddy ya karba a hannun Ya Omar domin shi ba yawo da kuďi yake yi ba.
Da wuya idan akwai ranar da Daddy ya taba irin farin cikin da yake yi a wannan rana, wani irin murmushi yake irin wanda yake tabbatar wa da duk wanda ya kalle shi cewa bai taba shiga tsananin farin ciki irin wannan ba. Duk wanda yayi mi shi tambaya akan sauyin al’amarin kuwa cewa kawai yake yi
STORY CONTINUES BELOW

“Alkawarin Allah ba ya tashi”
………………………………………………………………….
Karfe biyu na rana private jet ďin Daddy ya sauke Mahmud a garin Abuja. A lokacin da jirgin yake kokarin taba kasa, hawaye masu sanyi suke gudu akan fuskar shi, yayi tunanin ba zai sake dawowa Nigeria ba, yayi tunanin shi da farin ciki sai dai ya kalla a fuskokin wasu, yayi tunanin rayuwar shi ta gama lalacewa a wancan karan da ya tafi London bai taba tsammanin wani dalili babba ko karami zai dawo da shi ba, balle kuma dawowar ta kasance ta daďi da farin ciki irin wannan! Sai da jirgin ya sauka dai dai sannan ya shiga yayi refreshing kanshi ya futo aminin da babu kamar shi ya samu a tsaye yana jiran shi.
Suka rungume juna cikin matsanancin farin ciki sannan suka yi musabaha.
“Congratulations friend! I’m sooo happy for you! Allahumma barik!”
Kalmomin da Mahmud ya tura mi shi kenan a lokacin da aka ďaura mi shi aure da Ihsan. Sai suka sa dariya suka kara rungume juna kafin su shiga dalleliyar motar da Faisal yazo da ita domin tarbar the newest ango in the universe. Gidan Faisal suka yi, anan Mahmud yaci abinci yayi refreshing kansa. Faisal kawai ya tsaya yana kallon balaraben da sabon askin da aka yi masa wanda shi kansa ya kasa ďauke idanun shi akai, a ransa yana tunanin mutane nawa ne Allah yayi wa baiwar kyawu da kyawun hali irin Mahmud! Sau da yawa idan yana kallon shi ya kan tafi tunani akan girman ubangijin da ya halicci halittu masu tsananin kyau irin su Mahmud, ya dinga tasbihi gare shi yana tsarkake shi, musamman idan ya tuno mai rainon twins din shi, wata bakar mace ce wadda yake ganin duk inda muni ya kai ta kai, sai kuma ya tuna cewa ubangijin babu ruwan shi da kyau ko munin, hali nagari da biyayyar ka gare shi kawai yake so, komai munin ka idan imanin ka yafi yawa toh kafi kima da daraja a wajen Allah fiye da kowanne irin kyakykyawa komai kyansa har in dai na shi imanin bai kai naka yawa ba. ALLAHU AKBAR! Sai ya tsinci kan shi da jero kabbara ga Al-khaleequ…….
Tunanin shi ne ya katse da jin sautin Mahmud
“Idan kuma kai da kasan ni kamar yunwar cikin ka ka zauna kana yi mun irin wannan kallon ta ya kake so na shiga cikin mutanen da basa gani na kullum da kuma waďanda basu sanni ba? Do i look like an alien?”
Mahmud yayi maganar a lokacin da yake balle mabbalan gaban rigar kayan ďaurin auren na shi, wani irin luxury filtex da ba’a faďin kuďin shi sai an shiga ďakin sirri. Hango blue black akan farar fatar da hutu da jindaďi da zaman kasar sanyi ya huda. Ga wani ďanďasheshen đinkin zare ruwan gwal dizayin ďin Morocco da aka bi yadin da shi wanda ya kara mayar da shi the classy he is.
Ya kawo babbar riga ya ďora a kai ba tare da jin amsar da Faisal ďin ya kasa bashi ba. Ya saka special comb ďin shi ya soma gyara gashin dai dai yanda hular malam bahaushe zata zauna akai tayi tsari kafin ya miko wa Faisal hannu ya karbi hular da ya karya mi shi dai dai bukatar ango mai aji da daraja irin shi. Ya ďora ta akan kwalliyar, sannan ya kawo rantsatstsen sabon agogon “Omega” ruwan gwal ya ďaura.
Ya janyo karamar trolley ďin da yazo da ita ya ciro “La Nuit” a kwalin shi. Ya kara da wasu sabbin collection ďin LV ya feshe jikinsa da su sannan ya zauna a bakin gadon yana saka socks, Faisal ya taimaka mi shi da ciro sabon takalmi sawu cikin da zai saka a kwali mai jagwalgwalon chanel a jikinsa.
“Kasan Allah da ba Zahra ka aura ba sai amaryar ta biya kudin kwalliyar nan kafin ta ganka? Idan nace a tarihin Abuja ýan karya da kwalisa association ba’a taba futar da ango hadaďďe irin ka ba na tabbatar banyi karya……”
Yatsina fuska Mahmud yayi yana katse shi
“Do you know how awkward it is idan namiji yana complimenting ďan’uwansa namiji?”
Dariya Faisal ya kece da ita saboda yanda fuskar Mahmud ta nuna how irritated he was, ya mike yana ďaukar tashi babar rigar farar sheddar da ya ke ta yawo da ita a hannu bai saka ba saboda rashin sabo. Haka ya dinga tsokanar Mahmud yana kallon yanda kumatun shi ke komawa red yana blushing shi kuma ya tikar dariya. Kunyar Mahmud na bala’in amusing ďin shi, kai zai iya cewa komai na Mahmud ďin abun burgewa ne.
Bai ďauki kansa wata tsiya ba balle ya ďorawa kansa girman kai da jiji da kai, kamun kanshi ne ke sanyawa mutane suke ganin kamar wulakanci ne da shi amma kana mu’amala da shi za ka gane saukin kai da sanyin halinsa.
Yana da raunin zuciya mai tausayi kamar mace, abubuwa kanana suke sanga shi hawaye don haka mutane da yawa suke taking advantage đin shi.
Yana da far’a da son kyautatawa mutane da kuma alkhairi, wannan halayyar take ba shi daraja a zukatan duk wanda ya zauna tare da su.
Idan akace yayi defining Mahmud cikin sentence ďaya zai iya cewa
“Mahmud mutum ne nagari”
Kalmar nagari ce zata iya ďaukar duk wasu halayen Mahmud a dunkule, sai wasu kananan aibukan da baka raba ďan’adam da su domin kowa tara yake bai cika goma ba, cikakken mutum guda ďaya Allah ya halitta kuma ba zai sake irin shi ba alaihissalatu wassalam.
Da wannan shiga da wannan kama da wannan yanayi suka dumfari gidan Daddy. Daga nan zasu wuce gidan Dada wanda ya cika ya batse da ýan’uwa da abokan arziki, masu murna da wannan al’amari da masu kukan zuciya da na fili, irin su Inna Badi’a da ke kulle a ďakin baki tun lokacin da Kawu Sulaiman ya kira ta a waya ya guntsa mata yanda ramin da suka gina ya zurma da su. Yanzu abinda suke so su ji ido rufe shi ne shi Mahmud ďin yana ina? Wanne hali yake ciki da har aka ďauki aure aka ba shi? Ashe har yanzu basu tashe shi a aiki ba kamar yanda suke tsammani? Ya za’ai shirin su yaci gaba? Wanne mataki zasu ďauka. Wadannan lissafe lissafen suka taru suka hana waďannan butultattun bayin sakat da nustuwa da kwanciyar hankali.
Lokacin da Mahmud ya isa wajen taron ďaurin auren kai tsaye gaban Daddy ya isa ya tattare babbar rigar sa zai durkusa ya gaishe shi, Daddyn yayi maza ya ďaga shi tare da janyo shi jikinsa yayi masa wata irin runguma mai barazanar karya kasusuwa. Mahmud yaso daurewa amma gabaďaya ya gaza daure farin cikin ganin shi da Daddy sun shaida wannan rana mai tarin farin ciki da albarka wadda suka sha kukan zuci da fili, suka sha faďi tashi, suka sha fargaba da tashin hankali da ruďani kafin su gan ta. Sai ya fashe da kuka mai karya zuciya, kuka mai bayyana ma’anoni masu yawa, kuka irin wanda yake tahowa daga can karkashin zuciya.
This time shi Daddy daurewa yayi ya dake bai zubda nashi hawayen ba, yasa hannu kawai yana bubbuga bayan Mahmud, kafin ya ďago shi yana murmushi yasa hannu yana goge mi shi ambaliyar hawayen da ke zurubtu akan fuskar shi.
“Nooo! Don’t start this crying Mahmud! Ai yanzu kuma ka girma! You are not a baby anymore, yau mun yaye ka ni da Mami! You are a now a man who is ready to start his own family and give birth to his own kids! Ohhhh! ALLAH ka nuna mun babyn da Mahmud zai haifa…..”
Zo kaga blushing a wajen Mahmud, ya ma kasa kallon Daddyn saboda kunya sai murmushi yake yi kumatun shi yayi jajazur abun gwanin ban dariya.
Daman abinda Daddyn yake so kenan, shiyasa yawancin lokuta yake ajiye matsayin uba ya mayar da kansa kamar abokin Mahmud ya tsokane shi yanda ransa yake so ya more.
Assalamu alaikum dearies,
I am happy to introduce to you my skin care brand @ cutyfantasias_beauty.
We sell natural raw materials like body butters eg Avocado, mango, shea, cocoa, and carrot butter.
We have the best essential oils including castor,almond,argan,lavender,papaya oils etc at the best price.
We also have amazing oil perfumes and musks and many more.
We have the best body butter in town which is enriched with different butters and essential oils which repairs worn out and damaged skin, it moisturizes and hydrates the skin, it smoothen and softens the skin.
Please take some minutes and go through our page on Instagram
@ cutyfantasias_beauty.
Like, share and patronize us.
It will means more than alot.
Thank you!
Cutyfantasia.