HAUSA ARAB CHAPTER 9
Hotuna a ranar sai da Daddy da Mahmud suka gaji da shi, dukansu bakin su ya kasa rufuwa saboda murna da farin ciki. Ya Sadik, Ya omar, Faisal da Imamu sune masu takewa ango baya kasancewar ba wasu abokai ne da shi a Abuja ba.
Bayan an kammala daga nan tawagar tasu ta ďunguma zuwa gidan Dada cikin azababbun motoci na garari sabbi fil, kowacce tana nishin lafiya da nagarta.
Sun isa gidan Dada suka samu gidan a rincabe da murna da farin ciki, mata kamar kasa ko’ina ya cika ya batse.
Maroka sun cika a kofar gidan suna aikin da suka saba, ga masu bushe bushe na ta yi ba kakkautawa, har mutum bai jin abinda na kusa da shi yake cewa, Ya Sadik da Faisal suka dinga balle bandiran kuďi suna bayarwa dakyar suka samu kansu zuwa cikin gidan.
A babban falo suka samu Dada cikin matsananciyar murna, ta nade jikinta da koriyar laffaya mai asalin kyau, kyakykyawar fuskar ta sai annuri take yi a dalilin farin cikin da take ciki.
Daddy da amsabasada suka zube a gabanta sukai gaisuwa sannan aka soma yin hotuna cikin nishaďi da farin ciki.
Ina cikin ďaki A.laila tazo ta tattagoni da kyar muka futo kaina lullube duk inda muka wuce ana rangaďa guďa kamar kunnen ka zai toshe.
Duk yanda aka yi dani na sauke mayafin nan daga fuskata ki nayi, Dada tace a rabu dani. Ko Daddyn a wannan rana ban gaisar ba saboda kunyar da nake ji! Everything looks like a dream, ban taba tunanin bazan buďe ido naga ba mafarki nake yi ba, saboda haka kawai kallon kowa nake yi ďai ďai a raina ina cewa+
“Allah kasa idan na farka abubuwan su zo mana da sauki irin haka!”
Yini aka yi ana shagali babu kama hannun yaro, da yamma aka yi walimar da aka shirya a gidan Dada, sai wajen karfe tara taro ya watse.
Ko cikin gidan ban koma ba na hango motar Ya Omar na shige cikin muguwar gajiya.
Shi kaďai ne a ciki yana jiran Ya Sofy ta futo.
“Amaryar Ya Mahmud”
Ya faďa yana murmushi.
Na kalle shi fuskata very serious na sauke kasa ba tare da nace komai ba. Mun kai minti uku a haka sannan ya sake magana.
“I’m so happy for you Zara! Ke everyone is happy for you da auren mutum irin Mahmud! Ina yi muku fatan alkhairi
Allah yasa hakan ya zamo alkhairi da albarka ga rayuwar ku baki ďaya”
Ni dai bance komai ba kaina a sunkuye ina ta sarrafa kalaman da zanyi amfani da su wajen tambayar shi abinda nake so amma na kasa.
“Auu! Ko dai na zama in law ďin ki ne Zara? Yau ni ake jin kunya?”
Kawai sai na fara kuka wanda ni kaina bansan dalilin sa ba. Shi kuma ya tsaya yana kallona cikin mamaki, bai ce komai ba ya kyaleni nayi na gaji naci gaba da sauke ajiyar zuciya. Dai dai lokacin Ya Sofy ta futo, na murďa murfin motar zan futo na koma baya tayi maza ta bude gidan baya tana cewa
“Yi zaman ki amaryar Ya Mahmud”
Na soma kuluwa da wannan sabon sunan da suka tsiri gaya mun amma da yake yau bakina a mace yake bance komai ba.
Duk tsokanar da suke mun ban kula su ba har ya kaini gidan Mami, sai da na buďe zan futa sannan nace wa Ya Sofy
“Ki gaida mun twins! Kuma idan kika sake tahowa basu kama sai kin koma”
Na karashe maganar ina juya idanu.
“Angama amaryar Ya Mahmud”
Na harare su gabaďaya na rufe motar na shige cikin gida ina rike da riga ta wadda ta dame ni sosai saboda nauyin ta. Nayi sa’a duk ba’a dawo ba, na san ana can ana nemana don ko waya ta ban ďauko ba ban kuma ce zan taho ďin ba don kada a tsayar dani, a halin yanzu kuwa kaďaici da hutu kawai nake bukata.
Ina ta tunani akan abinda ya faru har na cire kayan jikina na shiga toilet na tara ruwa na kwanta cikin jacuzzi ďumin ruwan na ratsa ni ina jin daďi.
A zuciyata kuma tunanin nan ne dai bai sauya ba, dakyar nayi wankan na ďauro towel na futo.
STORY CONTINUES BELOW

Sai kawai naci karo da Ya Nuratu da Ihsan a kan gadon ďakin suna kwance suna hira. Na kalle su da mamaki ina cewa
“Ku kuma yaushe kuka taho?”
Ya Nuratu tace
“Ko zaki kore mu ne kamar yanda kika boye mana abubuwan da suka faru!”
Anan na lura gabaďayan su basu ji daďin yanda komai ya faru ba da sanin su ba, a ganin su kamar darajar su ta wuce a boye musu wani al’amari da ya shafeni mai girma irin wannan.
Ban bi takan su ba sai da na shirya cikin kayan bacci nayi sallar isha’i da shaf’i da wuturi sannan na dawo kan gadon na kwanta a tsakiyar su ina sauke nannauyar ajiyar zuciya. A sanyaye nace
“You guys have no idea the hell we’ve gone through! Na tsallake rijiya da baya, na kubuta dakyar, ba don taimakon Allah da na Imamu ba da tuni a wannan lokacin koke koke muke na bakin ciki ni da ku ba tuhuma ta kuke akan rashin sanar da ku abinda ko ni bani da ikon sani ba.”
Sai fuskokin su suka sauya zuwa mamaki da damuwa, cikin karfin hali Ya Nuratu ta tashi zaune ta dafa kaina tana cewa
“Don Allah Zara ki gaya mana me ya faru?”
Nima sai na tashi zaunen, na kalli Ihsan da ke kallona kamar zata cinye ni don tsananin kaguwa taji labarin.
Nace mata
“Yaushe zaki tafi gida?”
A sanyaye tace
“Faisal suna tare da Ya Mahmud da wasu abokan su a Chelsea hotel.”
Na sake cewa
“Ina Amani?”
Tace
“Mummy ta tafi da ita”
Zan sake tambayar ta tayi maza tace
“Don girman Allah drop this questions ki warware mana kullallun kawunan mu “
Nayi murmushi kawai na gyara zama na sannan na soma basu labarin ainihin abinda ya faru.
“Zuwan da Mubarak yayi last munyi zamu haďu da shi a gidan Ihsan. So da yamma na shirya zan tafi, na shiga mota kenan text ďin Imamu ya shigo waya ta akan cewa yana so mu haďu da shi a dunes center.
Kamar ba zanje ba saboda har wannan lokacin ban gama yarda da shi ba amma rantsuwar da yayi cewa maganar me muhimmanci ce ya sanya na tsinci kaina a kofar dunes center.
Abinda ya bani mamaki shi ne ganin Imamu a wata kama da siga ta daban sannan hankalin shi a tashe don ko gaisawa bamu yi ba ya soma yi mun bayanin abinda ya sanya ya kirawo ni.
“Zahra akwai matsala mai yawa kuma mai tsauri wadda take fuskanto ku ko nace mu gabaďaya. Matsala mai girman da take bukatar dukkan hankalin ki da tunanin ki da jajircewa da kokarin ki.
I’m sorry you have to know and go through this, da akwai yanda zanyi na gama komai bada sanin ki ba dana yi.”
Cikin kaguwa nace
“Imam just go straight to the point please”
“Tun lokacin da muka haďu da Mubarak a gidan ku kika gabatar da shi a gare ni na ďora mi shi question mark. Saboda na tabbatar na taba ganin shi a wani waje wanda bazan iya tunawa ba amma tabbas akwai wasu abubuwa da na ke hasashe a tare da shi wanda naji dole sai na bibiye shi na gano su.
Duk bincike na nayi ban samo komai ba illah abubuwa akan hatsabibiyar matar shi wanda wannan ba shi ne damuwata ba. Sai kawai na sanya a saka mun ido a kan kowanne motsin sa da rayuwar sa 24/7.
Abu na farko da ya fara shigowa shi ne rikewa su Alhaji Ibrahim Mai atamfa kayan su da Office din su Mubarak suka yi, bai ma san Mubarak ba sai a wannan lokacin, sai a lokacin ne yake gano cewa shi ne wanda zaki aura. A tunanin Alhaji Ibrahim, shi Mubarak zai shige mi shi gaba saboda sanayyar da take tsakanin ku yayi mi shi alfarma a sakar musu kaya, sai Mubarak ya nuna shi akan aikin sa ba sani ba sabo.
Har Daddy ya kira yace ko zaiyiwa Mubarak magana, sai Daddy yace hakan bai dace ba a tsakanin su, kuma in dai kaya ne, shi yayi alkawarin zai ba shi kuďin sa idan basu futo ba, 25% ne share ďin shi a cikin kayan, haka Daddy ya lale kuďinsa ya ba shi yace shi zai jira har lokacin da za’a saki kayan idan komai ya warware sai ya dawo masa da su, idan kuma basu futo ba ya bar masa kuďin.
A maimakon Alhaji Ibrahim ya kalli kyautatawar da Daddy yayi masa da adalci sai ya yi wa abun wata fassara daban, wannan ya faru ne a dalilin haďuwar su da Kawu Sulaiman, cikin zirga zirgan da ya dinga yi a garin Lagos. Kullum Kawu Sulaiman ba shi da aiki sai na aibata Daddy da Mahmud a wajen Alhaji Ibrahim Mai atamfa, cikin hikima da makirci irin nasa ya dinga yaďa manufar sa akan shi ba tare da ya sani ba har ta kai ga sun zama abokai sun jone sosai ba tare da sanin kowa ba.
Tun kafin maganar asalin Mahmud ta bayyana suke tsara plans ďin su akan Daddy! Shi Alhaji Ibrahim Mai atamfa wasu makuden kuďaďe yake so a hannun Daddy tun lokacin da Daddyn yayi mi shi wannan kyautar zunzunrutun kuďin a dalilin kayan shi ba tare da tabbacin kayan zasu futo ya biya shi ba yaji hankalin sa ya tashi, hassada da kishi mai yawa suka ďarsu a ransa, ya san Daddy yana da kuďi amma bai yi tunanin yayi wannan shaharar ba. Shikuwa Kawu Sulaiman ba shi da buri illah kawai ya bata wa Daddy suna, ya tozarta shi ya kuma durkusar da shi.
Ina da cikakkun shaidu akan duk abubuwan da nake gaya miki Zara, shaidun sahihu wanda zamu yi amfani da su a matsayin manyan evidence ko’ina bukatar hakan ta taso.
Suna cikin wannan halin ne kwatsam wannan al’amarin na Mahmud ya faru, wanda ya sanya su jin kamar su zuba ruwa a kasa su sha duk a dalilin kullin Kawu Sulaiman, shi ya zaunar da Alhaji Ibrahim ya ba shi shawarar cewa ya janye auren da ke tsakanin Amina da Mahmud domin zai cuci ýarsa ne kawai a banza babu wani amfani da auren zai masa, na farko dai shi Mahmud ba shi da gadon Daddy balle ya sa ran watarana idan babu Daddyn zai samu wani kaso na dukiyar sa ta hanyar ďiyar sa Amina, kinsan yanzu Zara auren jari iyaye suke yi da ýaýansu basa baiwa kowa sai wanda suka san zasu mora zasu kuma amfana da shi. Na biyu ya gaya mi shi cewa Mahmud ba shi da nasaba kuma ba shi da isashshiyar lafiya ma, sannan likita ne kawai, duk abinda yake yi da bazar Daddy yake rawa, shi ko hanyar da ake sarrafa dukiya bai sani ba da albashin sa kawai ya dogara out of their foolishness. Basu taba tunanin Mahmud ďin shekarun sa goma yana aiki a babban asibiti a kasar turai ba, basu san irin nasibin sa akan aikin sa ba, basu san kuma irin yanda kasar take ji da shi a fannin aikin sa ba. Su dai hauma haumar su kawai suka sani, don haka Kawu Sulaiman bai sha wahala ba wajen juyar da ra’ayin Alhaji Ibrahim ya fasa baiwa Mahmud ďiyar sa.
Inna Badi’a tana daga gefe tana basu kwarin guiwa da shawarwari irin na ta, domin itace tace kada su raba Mahmud da Amina a dai dai wannan gabar da asalin sa ya bayyana. Itace ta tsara musu wani kyakykyawan plan kamar haka.”
Sai ya karkata ya buďe laptop ďin da ya shigo mun da ita ya kunna ya lalubo abinda yake son nuna mun ya kunna.
Daddy ne da Kawu Sulaiman takanas a garin Kano gidan Inna Badi’a cikin falon bakin ta suke tattaunawa. Ya tariye mun zuwa yanda take koro musu bayanin na ta.
“Abinda nayi tunani nake ganin za’ayi shine, kada kayi saurin hana Amina magana da Mahmud, domin akwai mamora mai yawa a jikinsa a nan gaba. Ita uwar tasa tana can tana haďa lefe na alfarma abun kamar hauka, wai ita zata yi auren ďa, toh dole mu bari a kawo wannan kaya wanda na tabbatar ko an fasa auren ba zasu karba ba.
Na biyu ku bari sai Mahmud ďin ya sakankace Aminar ba zata juya masa baya ba hankalin sa ya kwanta ana dab da biki bayan katin gayyata ya isa hannun dukkan wanda suka gayyata sannan za’a sa ta tura mata text cewa ta fasa, babu ruwan wani a ciki maganar ta zama tsakanin su ce.
Na tabbatar ciwon sa zai tashi, kuma ba zasu bar shi anan ba tafiya zasu yi da shi can London ganin likita.
Idan ciwon Mahmud ya tashi mun gama samun damar da zamu aikata komai cikin sauki, saboda Daga Ahmad ďin har Zainab hankalin su zai tashi daga kan komai ya koma kansa, na tabbatar ma bin sa can zasu yi su bar komai.
Wannan dalilin zai sa ya bar duk wasu harkokin buďe factory ďin sa a hannun yaran sa ya tafi, anan zamu yi amfani da damar mu ta gaba mu jagula komai, deputy governor ďin Sokoto aminin ka ne ko?
Ta faďa tana kallon Alhaji Ibrahim Mai atamfa+
Yace
“Kwarai kuwa.”
Taci gaba
“Toh kai ne zaka yi shige da fucen da zai lalata buďe wannan factory ďin, a shigo wata matsala a siyasance a hana shi buďewa. Wannan labarin zai kara tada mi shi hankali, a wannan lokacin na san ko nawa aka dinga yankowa na kuďi akan maganar babu musu zai dinga turo wa don dai ya samu license ďin da wannan factory zai tabbata wanda yaci wa buri babba.
Anan zamu yi dabarar da zamu karbi abinda muke so ta hanyar deputy da babban yaron Ahmad, manager ďin da ya wakilta akan harkar. Daga baya kuma a hana shi samun damar buďewar. Kun ga ciwon zuciya goma da ashirin kenan, ga asarar kuďi ga rashin nasara, ga zullumin yanda zai fuskanci al’umma akan maganar Mahmud wanda media ta gama yaďawa…..”
Kawu Sulaiman ya tare ta da cewa
“Ke ai baki san kuďin da muka kashe a kan yaďa wannan labarin ba! Ai sai da na tabbatar duk lungu da sakon kasar nan kowa yaji wannan labari sannan hankalina ya kwanta”
Tayi wani murmushi taci gaba da cewa
“Wannan plan idan har ya tafi dai dai akwai nasara mai yawa a gare mu.
Abinda zaku yi shi ne ku samu manager ďin Ahmad ku cika masa aljihu domin ya cika muku aiki, ku samu deputy kuyi magana da shi sannan a nemi malaman da zasu yi taimako akan lamarin, wannan bangaren ku bar shi a hannuna. Daga nan komai zai tafi dai dai”
Gabaďayan su suka yi na’am da shawarar Inna Badi’a sannan suka ci gaba da tattaunawar da Imamu bai bari naci gaba da gani ba don ganin yanda hankalina ya tashi.
“Zara ba wannan ne kawai target ďin su ba, a halin yanzu sun danawa Mubarak tarko, suna bibiyar sa saboda su karasa yin abinda zai tarwatsa sunan Daddy da farin cikin sa. Na gaya miki cewa nayi tunanin na san Mubarak a wani wajen ko? Toh ba wani waje bane illa wani shahararren club da nayi tashen zuwa a Lagos. Duk da bai fi sau biyu ko uku muka haďu da shi ba amma tabbas yana zuwa.
Akwai yarinyar suka daďe tare da shi tun kafin yayi aure mai suna Leena, yar asalin garin Jos ce, bayan ya gama yaudarar ta ya bar ta ya auri Surayya, kamar ta rabu da shi sai daga baya kawai ta ďana mi shi tarko hanyar yi mi shi barazana da vedios din da ta dinga yi musu lokacin suna tare ba tare da sanin shi ba. A dole ya dawo yana kula Leena domin tsira da mutuncin sa, club ďin da na gan shi a ciki duk ita ce sanadin zuwan sa, ba’a son ransa yake bin Leena ba, sai don tsoron kaidi da sharrin da take shirin kulla masa a kowanne lokaci yayi yunkurin rabuwa da ita. Daga gefe kuma ashe itama Surayyan bai dace ba, domin kusan ita lesbian ce ma bai sani ba. Ba abinda ya shafeni bane game da ita don haka ban wani zurfafa bincike akan ta ba, sai dai na tabbatar tana da tsannanin kishi akan Mubarak kuma babu abinda ba zata iya aikatawa a kan duk wacce ta rabe shi ba, ba barazana take yi miki ba duk abubuwan da take gaya miki zata iya aikatawa tabbas.
STORY CONTINUES BELOW

A wannan rana Kawu Sulaiman da Alhaji Ibrahim zasu yi amfani da Leena akan Mubarak suyi masa barazana da kashedi, suyi deal da shi ya zaba tsakanin abu biyu.
Tsira da mutunci da kimar sa ko kuwa Auren ki!
Sun siya vedios ďin nan na hannun Leena a wajen ta da kuďade masu yawa, da kuma alkawarin zasu saka shi ya aure ta, da wannan vedio zasu yi masa barazanar cewa ya bari aci gaba da komai na sha’anin bikin ku da shi, sai ranar da aka ďaura aure bayan an watse zai miki text din saki uku da kuma kazafi akan cewa an gano kina da ciwo…………
“Bai karasa ba amma na gane wanne ciwon suke so su ce.”
Kinga ya kawo hujja mai girma da mutane ba zasu tsine mi shi akan abinda yayi ba sannan zasu ninka bakin cikin da zaku shiga bayan na sakin ki a ranar da aka ďaura aure dalilin sakin ma sai yafi komai zafi da tashin hankali tunda zai miki silar da zai kore kowa zuwa neman auren ki”
Wani irin kuka Ya Nuratu take yi kamar za ta shiďe don tsananin bakin cikin hali irin na mahaifiyar ta da tashin hankali da tsantsar jin ciwon abinda suka yi. Ni da Ihsan muka dinga bata hakuri, sannan naci gaba bayan mun samu ta saurara.
“Ganin tashin hankalin da na shiga Imamu yayi murmushi yaci gaba da magana with alot of care and love”
“Zahra wallahi billahillazi da ban samo miki mafita ba akan wannan al’amari da bazan zo miki da maganar ba. Ki ďauki wannan abubuwan as wasu games da zasu zo su faru mu yi playing da su kuma mu cinye.
Na gama tsara komai, na gama shirya duk wani tsarin da ya kamata, tsarin kuma shi ne, zamu bi su ta yanda suke so, zamu yi folding hannunawa muna kallon su suna gudanar da mission ďin su kamar bamu san komai ba. We will let everything happen according to their plans, sai sun zo gabar karshe zamu nuna musu cewa, ragamar wasan a hannun mu take ba’a hannun su ba.
Ko bamu yi nasara ďari bisa ďari ba, ina tabbatar miki da cewa ba zasu yi nasara a kan mu ba. Na zauna da Manager ďin Daddy, na zauna da deputy kuma na zauna da Leena, duk wani motsin su yana kan idona.
Abu ďaya zuwa biyu ne bani da iko akai, bani da guarantee cewa ba zasu faru ba, sune halin da Mahmud zai shiga idan Amina ta gaya masa cewa fa fasa auren shi. Wannan kam sai dai muyi addu’a mu bar wa Allah.
Abu na biyu kuma shi ne ďaurin auren ki da Mubarak, bansan ta yanda zamu iya tsayar da shi ba tare da munyi yunkurin da zasu ďago mu ba, amma kar ki damu, wannan sharrin da zasu yi miki da duk wasu maganganu will be in vain, na gama tsara yanda zan tari komai.”
A lokacin idona bushewa yayi ko alamun hawaye babu, sai kunar da zuciyata take yi na tsantsar bakin ciki da tashin hankali.
“Zahra don Allah ki kula! Kada ki bari ki nuna wata alama da wani zai gano halin da ake ciki, please ki karfafa zuciyar ki kuma ki yarda da Allah, ki yarda cewa ya bamu damar sanin shirin su Kawu Sulaiman ne saboda mu samu mafuta. Da izinin Allah kuma ba zasu samu nasara a kan mu ba”
Mun daďe da Imamu yana yi mun bayani da kuma kalaman kwantar da hankali kafin muyi sallama akan cewa zamu dinga waya yana sanar dani halin da ake ciki.
Ilai kuwa ina kokarin futowa daga cikin wajen na ga motar da Imamu yayi mun bayanin cewa Kawu Sulaiman da Alhaji Ibrahim ne a ciki, kuma a wannan yammaci zasu haďu da Mubarak su bayyana masa manufar su.
Idan kin lura da yanayina Ihsan a ranar bana cikin hayyacina, duk kuwa yanda naso na boye jikina a bala’in sanyaye yake, a haka Mubarak yazo ya sameni da sanyin jikin da ya ninka nawa, he was sooo calm, kallo ďaya nayi masa na tabbar su Kawu Sulaiman sun idda nufin su kuma sunyi nasara a kan shi, don na tabbatar ba zai zabi tonuwar asirin sa akan aure na ba, tunda ya san ko ya zabi asirin na sa ya tonu akai na waye zai bashi ni bayan halinsa ya futo.
Da kuwa yayi biyu babu ai gara ya hakura da auren nawa.
Haka muka yi hirar kowa ran shi a dagule muka yi sallama ya tafi.
Tun daga wannan lokacin muke cikin waya da Imamu yana gaya mun halin da ake ciki da jaddada mun muhimmancin rufe bakina kada wani yaji komai game da shirin mu.
Ranar alhamis ďin da Ya Mahmud ya tafi London, Imamu ne yayi mun text ďin cewa naje tulip bistro, ba don komai ba dai gudun kada ciwon na shi Ya tashi babu kowa a tare da shi, kamata yayi naje gabanshi ya ganni na zauna da shi har ta turo text ďin gabana amma kuma ba zan iya hakan ba tunda har lokacin wasan ýar buya muke yi da shi.
Bamu yi da Imamu zan bi Ya Mahmud ba, ni ce na zauna nayi wannan tunanin, domin nayi saving ďin shi, na tabbatar idan aka wayi gari babu shi, Mami zata shiga matukar damuwa, kuma last month ne visar ta ta kare bata riga tayi renewing ba. Na biyu ina so nayi wani yunkuri na cikawa Mamin burin ta wanda ta rubuta da hannun ta cewa bata da wani burin da ya kai shi. Wato aure tsakanina da Ya Mahmud! A lokacin da na karanta na ďauki al’amarin wani abu wanda ba zai taba faruwa ba, na tattara shi na ajiye cikin wani loko a zuciyata wanda bana bincikawa balle na tuna domin nauyin sa da girmansa a gareni. Above all, Ya Mahmud ďin na da wadda zai aura nima ina da wanda zan aura sooo tunani akan maganar ma bai taso ba duk da naji matukar ba daďi na sanin cewa Mamin ba zata cika wannan burin nata ba.
So sai na jefi tsuntsu biyu da dutse ďaya, ko nace tsuntsu uku ma ko huďu ko biyar, zan yi amfani da wannan damar na goge laifina a zuciyar Ya Mahmud na rashin nuna mi shi kulawa da jajantawa akan al’amarin da ya faru da shi, zan kuma zauna da shi na kula da shi idan ciwon na shi ya tashi, atleast Daddy da Mami hankalin su zai kwanta idan suka ji muna tare da shi.
Sannan zanyi saving family name da status din mu wanda su Kawu Sulaiman suka gama tsara yanda zasu yayyaga shi su fatattaka su mayar da mu abun kwatance da misali. Zan kubutar da Daddy daga tozarcin da zasu yi mi shi a ranar da ya ďaura mun aure aka dawo mi shi da takardar saki da kuma kazafi mai girma bayan yasha cewa alkawari ya daukar wa kan shi lokacin da Babana ya rasu cewa zai bani dukkan wata kulawa da gata fiye da wadda Baban zai bani, zai inganta rayuwata na zama abar alfahari a karshe zai tabbatar da cewa na auri miji nagari wanda zai kula da ni da rayuwata…….
How would he feel idan haka ya faru?
Waďannan hujjoji suka bani cikakkiyar kwarin guiwa da dama da karfin zuciyar da na shirya mana tafiya zuwa London ni da Baba Rabi a wannan daren.”
Ban taba sanin Imamu shu’umin mutum bane sai a wannan lokutan, wai duk wani motsi da nayi babba ko karami yana kallo na, yana da rohoto akan duk wani shige da fucena da tsarina. Ko kawata Najwa ashe ba ni take yi wa aiki ba Imamu take wa.
Yaji haushin rashin sanar da shi da nayi plan ďina, ni kuma gani nayi kamar zai tunanin naci fuskar sa idan na buďe bakina nace masa zanje nayi proposing Ya Mahmud, kuma zai iya kawo mun cikas wajen tafiyar tawa.
Duk da haka baiyi kasa a guiwa ba wajen cigaba da bani dukkan goyon baya da taimakon da nake bukata har zuwa lokacin da komai ya faru.
Kullum zulumina da tashin hankalina yanda Mubarak zai sake ni a ranar da aka daura auren mu da kuma kazafin da zai yi mun wadda nake tunanin cewa komai wankewar da za’a yi mun idan wani ya yarda wani ba zai yarda ba and that will not change tha fact that an sake ni a ranar da aka ďaura mun aure. Na tabbatar da wuya a samu wani al’amari da zai yi trending ďin da labarin mu zaiyi a kasar nan a wannan shekara, abubuwa daki daki ďaya bayan ďaya kamar almara.
A ranar da muka dawo gidan Daddy muka sauka, a ranar ne kuma Imamu ya warware wa su Daddy duka abubuwan da suke faruwa, duk da cewa yana sanar da Faisal wasu daga ciki amma shi ma sai ranar ya tabbatar da shaidar da Imamun yazo musu da ita.
Sun tattauna yayi musu bayanin komai da kuma tsarin sa da shirin sa bayan Dada sun sha kuka kamar ransu zai futa a dalilin jin cewa wai Kawu Sulaiman da Inna Badi’a ne suka shige gaba wajen tarwatsa rayuwar iyalanta da sunan ta gabaďaya………”+
Share hawaye na nayi ina kallon Ya Nuratu da ke ta faman ajiyar zuciya abun tausayi, don haka na fasa faďin abubuwan da suka faru a gidan Daddy na wuce kai tsaye zuwa yanda Mubarak ya rage yi mun waya, da yanda damuwar shi take futowa karara a cikin muryar shi da kuma sanyin jikin shi. Da rashin zuwan sa Abuja har sai bayan an fara biki
“A karshe bansan abinda ya faru ba! Bansan komai game da yanda akai wasan ya sauya salo ba, bansan me yaje yazo ba? Bansan ya akai aka chanja ďaurin auren daga kan Mubarak zuwa Ya Mahmud ba! Yanda kuka ji shelar nima haka naji! Kuma har yanzu ban nutsu munyi magana da Imamun ba balle ya warware mun…….”
Cillar da pillow ďin da Ya Nuratu tayi wanda take kishingiďe a kai ne ya sanya ni tsayawa cak cikin tsoro, daga ni har Ihsan ido muka zuba mata muna sauraren mai zai faru? Hannunta guda ďaya ta ďora akan cikinta ďayan kuma tana yarfa shi irin yanda mutum yake yi idan yana cikin azabar raďaďin ciwo.
A take muka gano cewa nakuda ce ta taso mata, hankalina yayi masifar tashi domin na tabbatar ciwon ba don kansa yazo ba wannan mummunan labarin da taji ne ya tayar mata da shi, duk da cewa edd ďin ta yana dab da cika.
Gabaďaya daburcewa nayi, na rasa me zanyi ma, kawai na soma kuka ina rungume da ita a jikina cikin tsananin tsoro da tausayi. Sai Ihsan ce ta lalubo number Mami ta danna mata kira, aka yi sa’a a lokacin suke shigowa cikin gate ďin gidan kenan ita da A.laila.
Kafin mu isa asibiti Ya Nuratu ta futa daga hayyacinta, tayi ligib kamar matacciya, wannan ya sake ďaga mana hankali sosai. Muna zuwa asibitin suka yi ďakin haihuwa da ita, suka bar mu a reception muna zarya cikin tashin hankali matsananci. Tuni Mami ta kira Dr.Mansur ya iso, dai dai lokacin da likitar ta futo tana yin bayanin cewa Ya Nuratu ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata cs.
Da gudu Dr.Mansur ya sanya hannu aka shiga da ita theater room domin ceto rayuwar ta da babyn da ke cikinta.
Ana shiga da ita Dada na isowa da Ya Sadik, Inna Badi’a ta biyo bayan su tare da Muhsin kanin Ya Nuratu, har yanzu babu wanda yake nuna mata wata alama da zata saka mata zargin an san halin da suke ciki don haka bata raragefen shiga ko’ina tayi mu’amala da kowa kamar ba abinda yake faruwa, kamar kuma da gaske murnar bikin take yi har cikin zuciyar ta.
Domin mutanen irin su Inna Badi’a ba’a gano su, ba’a defeating ďin su saboda tsabar baiwar kissa da siyasa da kissina da suke da shi idan suna kulla abubuwa.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin awa ďaya aka yi mata cs ďin cikin aka ciro kosashshen ďa namiji mai kama sak da babanshi da Baba ambasada.
Tuni fargaba da tararrabi suka koma murna, aka dinga rige rigen karbar baby.
Mami ta riga Inna Badi’a karba ko nace ta ture ta tasa hannu ta karbi yaron, a karo na farko da Mami ta ja wa Inna Badi’a burki, ta kuma nuna mata cewa Ya Nuratun ta Dada ce ba tata ba. Duk iskancin Inna Badi’a bata isa ta yi shi a gaban Dada ba, musamman akan Ya Nuratun da kullum daman ake mata gori tana rashin kunya dayawa a kanta saboda ýar fari ce, ba’a la’akari da cewa ita kaďai ce mace a cikin ýaýan na ta don haka ta koma gefe ta zauna a ranta a masifar jagule tana gunanin abubwan da suka faru a yau.
Kaďan ya rage bata sume ba lokacin da tayi arba da Daddy da Ya Mahmud cikin koshin lafiya a garin Abuja a gidan Dada yana matsayin mijin Zahra. Sai da tayi awanni biyu a ďaki tana tausar zuciyar ta kafin ta iya futowa, ta fake da cewa kanta ne yake ciwo tunda kowa ya san tana da hawan jini bata cika son hayaniya da yawa ba.
Ya Nuratu har wannan lokacin bacci take yi irin na allurar mutuwa, ta fyaďe ta rame lokaci ďaya kamar tayi jiyya, kamar ba energetic and charming kirjin bikin nan da ake yi ba. Gabaďaya sai ta bani tausayi, akwai kuwa bakin cikin da ya wuce rashin sa’ar iyaye nagari? Musamman ma uwa? Gaskiya babu. Allah ne ma ya taimake ta Dada ta karbe ta daga hannun Inna Badi’a tun tana karama, da ko bata yi poisoning ďin kwakwalwarta da muggan halinta ba, zata tsinci kanta cikin depression da ciwon zuciya.
Waya ta ce ta soma ringing na futo daga ďakin ina kokarin amsawa ganin sunan Imamu, amma me? Cin karo da nayi da waďanda suke kokarin shigowa ďakin ya sanya ni komawa cikin ďakin da sauri ina katse kiran?domin hakan ne kawai zai kubutar dani daga magana da su. Aikuwa na samu gefen carpet jikin A.laila na zauna ina murza hannu, ba don hankalin su ba’a kaina yake ba da sun ramko ni.
Ko second goma banyi da zama ba suka shigo, Faisal a gaba, Ya Mahmud ya biyo bayan shi, ya cire kayan ďaurin auren ya sauya da coffee ďin shadda mai sulbi da maiko, kanshi babu hula sai himilin ďan gatan gashin nan da yasha wani irin askin ban mamaki da sha’awa kamar yan kifa kwando, curly and shiny. Tuni ďakin ya buďaďe da kamshin “la Nuit”.
Suka durkusa a gaban Dada suka fara gaishe ta sannan suka koma ga su Mami da da A.laila, ko na baku labari har yanzu Mami da Ya Mahmud basu haďun ba? Lolz! Wasan ýar buya yake mata ita kuma ta zuba mi shi idanu ta ga iya gudun ruwan shi kafin ta zazzage masa kwandon punishment ďin da tayi mi shi tanadi.
Mami ce ta mika musu babyn yana ta bacci an sinkife shi cikin saitin kayan jariran “Versace” ruwan madara.
Ya Mahmud yayi kissing ďin goshin sa sannan ya saka bakinsa a kunnen babyn yana yi masa addu’a, kamar ba zai baiwa Faisal ďin shi ba. Son yara musamman ýan babies sabbin haihuwa a cikin jikinsa yake.
Ana cikin haka Ya Nuratu ta soma buďe idanu tana karanto sunan Allah!….
Na mike da sauri na isa gefenta na rike hannunta, nurse ta shigo itama da sauri domin sun sai ta abinda ke monitoring ďin ta. Sai da ta duba ta sannan ta futa kiran likita bayan tace lallai mu tattara mu futa daga ďakin basa bukatar mu da yawa haka. Inna Badi’a ce ta fara mikewa, ko me ta tuna oho! Amma har da rashin iya jure zama cikin inuwa ďaya da mu tana kallon farin ciki da annashuwa a fuskokin mu.
Taje gaban Dada tayi mata sallama tunda dai ta san ba ita ce zata zauna a wajen Nuratun ba. Tayi wa su Mami sallama muka bi ta Allah ya kiyaye ta futa Muhsin yabi bayanta.
Sai Dada ta kalli Mami tace
“Toh ya za’ayi ga haihuwa tazo kuna cikin fama da jama’a Zainab?”
Murmushi Mami tayi tace
“Tunda an sauka lafiya ai sai barka Dada! Laila ta tafi da ku saboda sha’anin baki. Ni zan zauna, idan kun koma sai a ďauko mun Binto(ďaya daga cikin ýan’uwan su da suka zo biki) mu zauna tare. “
Dada tace
“Ke uwar taro kya zauna a asibiti? Ko dai…..”
Cikin sanyi Mami tace
“Au taron ma nawa ne Dada? Ita Nuratun ya take a wajena? Ya za’ai na tsallake ta na tafi naje gida na kwanta.
Haba Dada”
Cikin dariya Dadan tace
“Daman son tsokanar ki nake yi! Nasan abinda zaki ce kenan. Allah yayi miki albarka. Allah ya baki ladan zumunci.”
Duk muka amsa.
Dada ta dubi Ya Sadik tace
“Toh kai zo ka kaimu gida ni da Laila ka dauko Binton dare yana yi….
Kai ma Faisal ďauki matar ka ku tafi gida ka huta, wannan hidima da kuka sha yau.”
Kamar yace ai Ihsan ďin tana tare dani a gidan Mami tare zamu kwana amma sanin ba’a yi wa Dada musu a zauna lafiya da ita sai ya lallaba yace toh.
Duk a tunanina tare da Mamin zamu zauna a asibitin,murna ta cika ni kamar nayi tsalle musamman saboda wannan jaririn da bana son ďauke idanuna a kansa. Wai kawai sai tsintar sautin Dada nayi cikin kunnena tana cewa.
“Ke Zara tashi ku tafi da su Faisal ďin dan suka ajiye ku sai su wuce gida.”
A.laila ta gumtse dariyar ta tana yafa mayafi; nikuwa nayi kamar bansan yaren da Dada take magana da shi ba.
Nace
“Dada gidan da babu kowa? Ai daman dani da Ya Nuratu da Mami muke kwana, duk ýan matan ma ai suna Garki Dada, su Baba Asma’u ne kawai a gidan”
Tana jin haka ta dubi Ya Mahmud tace
“Kai kuma a wanne gidan kake kwana? Ko har yanzu kuna hotal ďin?”
Ya Mahmud cikin ladabin da ya karo a yau da safen nan yace
“Eh”
Sai Allah ya taimake ni ta barni a asibitin muka yi sallama suka wuce suka tafi. Ni dai babu abinda nake yi sai faman kallon babyn Ya Nuratu wanda yayi kane kane cikin raina kamar Amal. Ban ďauki Ya Nuratu a matsayin cousin ďina ýar Inna Badi’a ba, kallon ta nake kamar Mami ce itama ta haife ta, da yake kuma gida ďaya muka taso sai wani irin aminci da soyayya ya kullu a tsakanin mu.
Na rungume babyn na kalli Mami cikin damuwa nace
“Mami kinsan kuwa labarin abinda ya faru ne ya tayar wa da Ya Nuratu nakuda?”
Cikin rashin fahimta ta kalle ni.
“Ita da Ihsan suka sa ni a gaba wai basu ji daďin yanda aka boye musu abubuwan da suka faru ba, lallai sai na basu labarin abinda ya faru….
And then tashin hankali da bacin rai suka sanya ta shiga wani hali, nakudar ta tashi….!
Mami ina jin tausayin Ya Nuratu wallahi, mutum ya wayi gari Inna Badi’a ce ta haife shi yana cikin gagari da tashin hankali.”
Cikin tausayawa Mami tace
“Hmmm! Dalilin kenan da ya sanya tun farko Dada ta rabo ta da Badi’an ai, tana tsoron Badi’a ta gurbata mata tarbiyya da irin tunanin ta da ďabi’unta irin wanda babu wanda ya san inda ta kwaso su.
Tun muna yara Badi’a halinta daban yake, ra’ayinta daban sannan bata kallon abubuwa da fuska ta fahimta masalaha, komai a wajen ta na tashin hankali ne……..”
Motsin farkawar Ya Nuratu ya katse mana hirar Mami ta tashi ta kira nurse aka sake dubata.
Motsin Ya Nuratu ne ya katse mana hirar Mami ta futa ta kira nurse suka zo suka sake dubata sannan suka kara saka mata wani drip ďin.
Kwana muka yi da Mami muna hira irin wadda muka ďauki lokaci bamu samu nutsuwar yi ba. Ta daďe tana yabawa kokari da karamcin Imamu cikin wannan al’amari, da kuma mamakin chanjawar shi da shiryuwar shi.
Karfe uku Ya Nuratu ta farka, a lokacin ta dawo hayyacin ta sosai, muka yi mata sannu ta amsa a sanyaye, Mami ta ďauki babyn ta nuna mata amma sam babu wani karsashi da murna a tare da ita wanda na tabbatar akan abubuwan da suka faru ne. A karshe ta rufe idanunta kawai hawaye sirara na zirarowa kan kuncinta tana sharewa cikin dabara.
Mami ta tashi ta koma gefen kanta ta zauna a kan kujerar gaban gadon sannan ta dafa kanta ta soma yi mata magana a tausashe.
“Haba Nuratu! Kuka kuma? Ba zaki godewa Allah ba? Allah ya sauke ki lafiya kin haiwu da ran ki da lafiyar ki kin samu ďanki cikin koshin lafiya amma ki dinga kuka?
Idan maganar su Yaya Sulaiman da Badi’a ce Nuratu inda sabo ai yakamata ace mun saba da halin su! Tun suna kanana suke da wannan tsatstsaurar ďabi’ar har suka girma. Tsakanin mu da su kawai sai addu’ar shiriya, Allah ya ganar da su gaskiya ya mayar da su kan tafarki madaidaici!
Laifin Badi’a ba naki bane Nuratu kuma ba zai taba shafarki a idanun mu ba, haihuwar ki ce kawai ba zamu goge cewa ita yi ba amma komai naki namu ne! Billahil azeem baku da maraba da Zara a cikin zuciyata, ban taba kara ki da Badi’a ba sai a lokutan da nake miki nasiha akan biyayya a gare ta saboda haqqinta na uwa da yake kanki. Ban taba tunawa da alakar ki da ita ba idan na kalle ki kuma ban taba kawo wani tunani cewa wani abu tsakaninmu zai chanja saboda ita ba.
Yanzu ba gashi ita ta tafi nice nake zaune tare da ke ba? In ke ďin tata ce zamu zo mu zauna ne ko kuwa ita zata sa kafa ta tafi? Ki cire tunanin abubuwan da take yi kina alakanta kanki da su, baki da alaka da komai cikin wannan al’amarin. Nasan da ciwo, naka naka ne, kuma ba’a taba chanjawa tuwo suna, ba zaka taba jin daďin cewa mahaifinka ne yake aikata ayyuka irin waďannan ba.
Amma sai kiyi tauhidi ki saka a ran ki cewa kowannne bawa da irin rayuwar sa da kuma irin jarrabawar sa, ke taki irin taki kenan sai dai kiyi ta addu’a Allah ya shiryar da ita ya dawo da ita hanya madaidaiciya. Kuma dole kiyi mata biyayya ko yaya take domin ita din mahaifiyar ki ce komai lalacewar ta, kiyi kokari ki sauke wannan haqqin da take da shi a kanki bayan wannan duk wani abu da ýa take bukata a wajen uwa kizo wajena! A shirye nake a kowanne lokaci na baki dukkan gata da kulawar da kike bukata komai girmansu. Kada ki taba raba ďaya biyu tsakanin ki da zara a wajena, sharawara ce, damuwa ce, matsala ce, tallafi na gaba ko na kuďi ki gaya mun indai bai fi karfin ikona ba zanyi miki shi……
Don Allah ki cire wannan damuwar a ranki kinga yanayin da kike ciki ba’ason kina damuwa saboda gudun faruwar matsala! Ki tattara komai ki bar wa Allah kamar yanda muka yi, insha Allah komai zai warware cikin sauki albarkar fiyayyen halitta saw.”
A kalla Mami ta ďauki awa daya tana yi wa Ya Nuratu nasiha da ban baki da kwantar da hankali kafin ta shawo kanta tayi shiru ta daina kukan tana rungume da hannun Mami tana sauke ajiyar zuciya. Daga nan kuma tace kanta ciwo yake yi, aka je aka gayawa likita, ya sake yi mata wata allurar sannan ta koma bacci.
Karfe takwas na safe Daddy da Baba ambasada suka zo asibitin, lokacin an tashe ta har anyi mata wanka an bata tea. Amma ciwon kan da bai sauka ba ya sanya suka ci gaba da saka mata drip da allurai, ta sake komawa bacci saboda hutun kawai take bukata a wannan lokaci.
Bayan mun gaisa da su na tashi na ďauko babyn cikin gadonsa an sake yi mi shi wanka an sauya mi shi kaya da wasu brown din colour na H and M. Kyawun shi da kamannin shi da su Baba ambasada ya kara futowa.
Daddy ya dinga shafa kansa yana cewa
“Masha Allah! Masha Allah! Ambasada yaron nan bai mun kara ba, sai yayo photocopying ka! Ko dai cin hanci kake bayarwa ne ni bansani ba?”
Mukayi dariya! Amsabasadan ya karbe shi shima yana murmushi sannan ya yayi mi shi addu’a. Ya sake mikawa Daddy shi yace
STORY CONTINUES BELOW

“Kayi masa huďuba da duk sunan da yayi maka”
Daddy yace
“Baban shi bai zo anji ra’ayin su ba sai ayi haka?”
Ambasada yace
“Mansur yana da ra’ayin da ya wuce nawa ne? Kaima kasan ina nan ba zai taba bayyana zabin da yake so ba…
Bare ma sai da na tuntube shi yace duk abinda na yanke shine daidai.”
Daddy yayi murmushi ya gyara kwanciyar yaron a jikin sa ya soma yi masa huďuba. Bayan ya kammala ya miko wa Mami shi yana cewa
“Allah ya raya mana Ahmad!”
Dukanmu muka yi murmushi saboda la’akari da muka yi da Daddyn da Baba ambasada sunayen su ďaya. Duk da shi ambasada Baffa iyayen shi suke kiransa sauran kannen shi kuma da ýaýan sa da ýaýan ýan’uwa dukansu Baba ambasada suke ce masa saboda haka sai Ahmad ďin yaso ya bata.
Na taba baku labarin family ďin ambasada? Matar shi haifaffiyar garin kano ce Rasheeda, amma tun bayan haihuwarta ta biyu ta haďu da wata lalura bayan tayi matsanancin zazzabi. Lalurar kuwa ita ce ta rashin son hayaniya komai kankantar ta, ko cokali aka cillar da karfi sai ta suma, ko kuma ta rike kanta tana wani irin abu, duk inda za’a je neman magani anje likita yace bai ga komai ba, sai aka koma addu’a da maganin musulunci, anan ne aka ďan samu afuwa, ta daina suman, amma fa babu zancen ta shiga hayaniya ko taron mutane masu yawa. Daga nan rayuwar ta ta chanja daga gida sai gida, babu inda take zuwa, lokacin ambasadan yana garin Abuja yana aiki da hukumar shige da fuce ta kasa.
Tun ana tada hankali akan matsalar har aka gaji aka fawwala Allah.
Ýaýa uku suka haifa duka mata, Rahma da Sadiya da Rukayya.
Waďannan ýaýa babu inda suke zuwa sai makaranta ko da yaushe suna tare da mahaifiyar su, sun saba matuka da yanayin ta suna kuma takatsantsan da lalurarta.
Bayan sun koma saudiyya sai zaman ya fiye musu kowanne daďi saboda su kaďai suke rayuwar su.
Dukansu kuma acan aka aurar da su, Rahma tana Kuwait, Rukayya tana Abu dhabi sai Sadiya ce da har yanzu bata samu tayi auren ba, domin alamu sun nuna kamar itama tana da shigen ciwon uwar duk da cewa nata bai yi tsanani sosai ba.
Wannan ya sanya iyalan ambasada basa shiga ko’ina kuma ba’a ganin su a komai na family, ba’a zuwa gidansu suma basa zuwa gidan kowa. Shikuma irin ta shi kaddarar kenan, duk da haka yana da son zumunci da taimakon ýan’uwansa. Takanas yake zuwa Kano ziyara ya duba family dinsu, tun ana matsa masa da zancen kara aure har suka gaji suka daina saboda kullum amsa ďaya yake bayarwa
“Idan da rabo zanyi ne! Ba saboda lulurar Zainab ba, shi aure nufin Allah ne ba son zuciya bane”
Toh wannan kenan!
Nice na laqabawa Ahmad Asaad, sai kowa ya kama, a washegarin ďaurin aure ya kamata ayi grand dinner sannan a karasa buki. Sai lamari ya juya, Daddy ya ďaga bikin sai bayan sati uku domin yaci burin yin wannan buki kuma ba zai fasa ba.
Kwanakin mu uku a asibiti da Mami a maimakon Bintun da tace a kawo mata. Ya Nuratu ta samu sauki kuma hankalinta ya kwanta a sakamakon kulawa da riritawa da take samu daga gare mu, ciwon kan da take yi ne ma ya sanya akayi delaying sallamar mu daga asibiti….
Karfe biyu na rana na idar da sallah a ďakin asibitin na kwanta jikina cike da gajiya, Dada wadda kullum take wuni a asibitin ta kalle ni tace
“Zahara’u ya kamata kije gida ki huta ko zuwa dare ne sai ki dawo idan gajiya ta kama ki ba za kiji da dadi ba. Baki samu kin huta ba tunda aka fara hidimar biki”
Nima inason zuwa gidan ko don saboda nayi wanka mai kyau ba irin na asibitin ba, kuma ina bukatar kebewa nayi magana da Imamu na samu karashen bayanan da nake nema a wajen sa. Yazo asibitin shi ma kuma munyi waya har sau biyu amma ban samu lokacin magana mai tsayi da shi ba saboda mutane.
“Shikenan Dada idan Ya Omar yazo anjima sai ya kai ni gidan!”
Minti sha biyar tsakani aka kwankwasa kofa sannan aka turo aka shigo da sallama.
A.laila ce da katon kwandon abincin da Baba Rabi take yi na asibiti kullum take tahowa da shi bayan azahar.
Kafin su Mami su gama amsa sallamar ta, sai ga Ya Mahmud biye da ita da manyan ledojin Sahad a hannun shi. Na mayar da kaina sosai na lumshe idanuna kamar me bacci domin tun bayan ďaurin auren wata magana bata shiga tsakanina da shi ba. Shima kuma sai ya share nin kamar yanda nayi wannan ya kara bata mun rai, duk na ďauki laifi na ďorawa kaina, da ban zub da daraja ta naje London na roke shi ya aure ni ba ai da nayi saving aji da mutuncina. Ko yaya muke da shi dai sunan shi namiji ni kuma mace, wadda aka sani da kunya da kara da kawaici, garin rawar kai naje nayi fatali da nawa a gaban shi, yanzu gashi nan hakan na barazanar haifar mun da raini a wajen sa. Toh wai ma sai akace sai lallai naje London da kaina na durkusa a gaban sa nace ya aure ni ne zan ceto rayuwar sa na faranta wa su Mami rayukan su? Ko kuwa lallai sai na gaya mi shi da bakina ne hakan zai faru? Wai ma da waye nayi shawara na aikata wannan aikin?
Gashinan ai tunda aka daura auren kowa ni yake yi wa murna nayi sa’ar miji nayi dacen auren mutum irin shi, wato ni kenan bai yi sa’ar mace iri na ba ko? Ni ba wata tsiya bace shi ne ma ya taimake ni. Kiri kiri su Ya Omar da Ya Nuratu sun daina kiran sunana sai amaryar ya Mahmud da yake shi ne nasu kuma sunan shi yafi nawa haske shiyasa suka ajiye nawa suka koma yi mun laqabi da shi.
This is too much! Mai yasa kowa yake fifita shi a kaina? Me yasa aka fi son shi?
Wannan tunanin ya sanya na kara cika nayi fam kamar zan fashe! Bansan abinda yake faruwa ba ina can duniyar tunani sai naji Dada tana tashina, a dole na tashi zaune ina murtsuka idanu kamar mai baccin gaske. Kafin na warware tace
“Tashi kibi mijin ki tunda gidan zai koma”
Kalmar miji da tace ya sanya Ya Nuratu da A.laila gimtse dariya suna kallona.
Mami kam ko kallo bamu ishe ta ba, musamman Ya Mahmud da a kwanakin nan ta futa harkar sa, daga gaisuwa sai tayi mi shi banza, shi kuma duk sai jikinsa ya kara sanyi sai ya kasa zama ya tafi. Kowa ya fahimci abinda yake faruwa amma ko Dada bata yi shishshigin shiga tsakanin wannan uwa da Ďa ba balle wani. Kowa ya zuba idanu ya ga yaya zata kaya.
Cikin kuluwa na zumbura baki nace
“Dada na fasa tafiya ai na warware……”
Kafin na kai aya naji saukar farantin da yake cikin kwandon abincin gabanta a bayana. Duk da ba da karfi ta kwaďa mun ba amma ya shige ni sosai. Da yake kuma a kusa nake sai naji haushin dukan ya kamani, na mike cikin sanyi ina share hawaye na yafa gyalena na futa ba tare da jiran shi ba.A parking space ya same ni a tsaye ina cika ina batsewa, bangane motar da yazo da ita ba sai da naga ya buďe ya shiga, duk yanda aka yi shi ma Daddyn ne yayi masa kyautar ta domin na san shi dai ba zai saka kuďin shi ya siya irin wannan mota ba. A wannan zamani da matasa da masu kuďi suke yayin motoci na gagari da kece raini, Shi wannan gayen motar ba ta cikin tsarin sa. Kowacce hawa yake komai saukin kudin ta, mota takan shi ma bashi da ita a Abuja da extra ta Mami yake amfani idan driving ďin ya zamar mi shi dole, idan ba haka ba koda yaushe Faisal ne yake kai shi duk inda yake bukata. Da waya da mota basa cikin shirgin shi, idan kingan shi da waya latest, toh Faisal ne ya siya ya tura mi shi, har yanzu an kasa raba shi wata iPhone 5 da yace akwai muhimman documents din sa a ciki da yake so, ya ma fi amsa kira da ita don jin daďi.
Ba kuma wai son kuďi ne da shi ko tattali ba, akan sutura da turare da kayan gyaran jikin shi musamman wannan ďan gatan gashin na shi ko miliyan nawa ce zata tafi baya lissafi. Yakan ce yana siyan abu mai tsada ne domin nagarta ba wai don ya burge wani ko wata da yawan kuďin su ba. Hakana idan kyauta zai yi baya kai komo, komai yawan kudi ko darajar abu yakan kyautar da su ba tare da wata damuwa ba. And this is the person he is, very simple is his own way.
Ko da muka shiga cikin motar bai kula ni ba, sai ma fuskar shanu da yayi wadda ta tuno mun da Ya Mahmud ďin da na fara gani a Jidda. Iskancin da nake ji ya kau tsoro ya soma shiga ta domin yayi kama da zai iya tsayawa ya zazzabga mun mari idan na kawo mi shi raini. Don haka na haďiye kuka na na koma ajiyar zuciya wadda na kasa hana kaina yi.+
“Hello Ezike! Please i want two tickets to Heathrow airport today”
Bansan me Ezike ďin yace ba na sake jin yace
“Furtunately? Ok! Thank you! I will see you!”
Da farko ban gane abinda yake nufi ba, hankalina yafi tunanin wasu mutanen shi ne suka zo ko zasu tafi ko mutanen Daddy ko dai something related to that.
Sai naji kuma ya kira Faisal
“Friend kazo Airport don Allah ka karbi mota ta ka mayar da ita gida”
Sai naji cikina yayi wata danka ya saki, ya sake yi wata ya saki, ta ukun kuwa da yayi bai saki ba kamar zanyi zawo a jikina.
“Toh da wa zan tafi? Da matar da aka aura mun! Wait bana son waya ina driving you know! Let’s meet at the airport please”
Yana gamawa ya ajiye wayar ya kara speed! Nayi tunani na tabbatar cewa tickets ďin da yake shirin siya guda biyu ne ďaya na shi ďayan kuma ba wata yake nufi matar da aka aura mi shi ba illa ni, a wannan halin da ake ciki da wannan fuskar ta shi mai kama da ďaurarren bakin hadari.
Bakina ya soma motsi ina kikkifta idanu amma na kasa cewa komai, sai dakyar na samu wasu hawaye masu zafi shar shar! Suka soma sauko mun!
Da yaga zan dame shi sai ya kunna cd ďin motar ya saka wakar Chris brown.
Wato yau ba me karatun bace ba alamar ba sassauci, na saka kaina tsakanin guiwoyina na soma kuka sosai.
Na dai san ya tsaya sau ďaya yasha mai, daga nan bamu sake tsayawa ba cikin parking space ďin airport. Ganin ya kashe motar yana shirin murďawa ya futa nayi azamar buďe bakina na soma yi mi shi magana
“Don Allah don Annabi Ya Mahmud kayi hakuri! Don Allah kayi hakuri!”
Sai ya dawo ya zauna sosai yana kallona
“Nayi hakuri da me?”
“Kayi hakuri don Allah da maganar tafiya”
“Au hakurin akan tafiyar zan yi?”
Kikkifta idanuna kawai nake yi bansan me zan ce ba kuma.
Sai ya soma magana da muryar da take bayyana fushin sa wanda ba kasafai yake yi ba, sai idan ka kai shi bango.
STORY CONTINUES BELOW

“Wannan hakurin ba zanyi shi ba gara ma akan wani abu daban! Kuma bazan yarda mu yi wata magana ta fahimta da ke ba har sai mun dangana da gidana da ke Liverpool inda kikayi confessing da bakin ki cewa zaki aure ni kuma ba akan ra’ayin wani ko wata ba. Ba don tursasawa ko takurawa ba.
Anan zan yi miki tambayoyi akan iskancin da kika tsiro mun da shi sai nafi ganewa idan bayan saukar ki a London ďin a wancan lokacin wasu shakiyyan shaiďanun kika haďu da su suka tsara miki komai ko kuma anan Nigeria suke ďawainiya da ke domin dai bazan ďauki wannan rainin wayon ba”
Sai lokacin na soma gano inda yasa gaba da kuma laifin da yake ganin laifina ne bayan shi ne yake mun laifin. Ashe kowa haushin kowa yake ji kenan.
Ban kai ga magana ba Faisal ya kwankwasa mana glass, Ya Mahmud ya cire lock sai kawai ya shigo motar ya zauna a seat ďin baya. Cikin rashin fahimta da damuwa ya kalli Ya Mahmud sannan ya kalli fuskata da tayi jage jage da hawaye.
“Me yake faruwa?”
Ya faďa a sanyaye cikin tsoron kada ace nima ďin halin ýan duniya zan shuka musu.
“Gata nan tambaye ta”
Faisal ya kwantar da harshe yace
“Bansan ki da rigima da tada hankalin mutane ba Zahra? Kullum ina yi miki shaidar yakana da kyautatawa ga duk wanda kike mu’amala da shi! Meye yake faruwa gaya mun? Wanne laifin aka yi miki?”
Da yake masalahar nake so a wannan lokacin sai na nutsu na soma sakin batutuwan da suke cikin raina wanda suke sosa mun zuciya suke kuma matukar son samun wanda zai saurare su kafin su futo amma sun rasa. Domin shi wanda zanyi batun akan sa favourite ďin kowa ne.
“Ai nasan bayan shi zaka bi kaima”
Cikin sauri yace
“I will not! I promise”
Na sanyaya murya na soma bayani tiryan tiryan wanda suke tahowa bilhaqqi daga cikin zuciyata.
“Wulakanci ake yi mun akan shi! Shi ma wulakanci yake yi mun kawai saboda na zubar da ajina na tafi London naje nace ina son shi! Shikenan na zama mara value a idon kowa, ko Sunana an daina kira wai sai amaryar Ya Mahmud saboda ni nawa sunan is useless, kowa idan ya buďe baki sai dai yace mun nayi sa’a nayi dace etc amma shi ba’a gaya mi shi, saboda shi bai yi dace dani ba ko? And this makes him hates me soo much that he ignores my being. Yake acting as if he has never known me, a maimakon ayi mi shi fada kowa supporting ďin shi yake yi, dubi yanda Dada ta kwaďa mun plate a kafaďata saboda nace bazan biyo shi ba……..”
Tun suna daure dariyar su har suka shiga yin ta a fili, making me feel kamar mahaukacciya! Wani bacin rai ya sanya ni kara volume din kukana.
Cikin dariyar Faisal yace
“Ohk! Okk! Let me judge….”
Ya sake cigaba da dariyar da take cikin sa sai da kyar ta tsayar da ita sannan ya soma magana serious.
“Zarah wannan tunanin ki ne! Kuma tunanin ki bai gaya miki dai dai ba!”
Na ďago idona da yayi jajazur nace
“Saboda ni mahaukacciya ce ko? A garin rashin tunanin nawa ai naje London nayi abinda ya janyo mun gori……! I don’t want your judgment”
Ya sake fashewa da dariya.
Ya Mahmud ya danna lock ya buďe motar ya dubi Faisal yace
“Ga hanya futar mun daga mota tunda kai babu abinda ka iya sai karawa wuta mai! “
Faisal ya kama handle ya buďe yana cewa
“Ai ko ban futa don komai ba na futa don kar cikina ya kulle.”
STORY CONTINUES BELOW

Sai da ya tafi sannan Ya Mahmud ya juyo yana kallona looking very very serious.
“Look at me?”
Yayi maganar cikin ba da umarni.
Na ďago idona na kalleshi shi na sake mayar da su kasa.
“Waďannan su ne accusation ďin ki? Uhm? You really think this way? You really believe I would ever look down on you Zara? Ni din? You really think ke da kike da uwa da uba da dangi da asali da komai wani mahalukin zai fifita darajar ki a kaina mara uwa da uba da dangi da asali? Does it even make sense? Idan har za’a kalle ni da wata daraja saboda wasu abubuwa ne kamar haka
Iyayena Daddy da Mami da darajar family ďin su ya sanya ake kallona mutum mai daraja
Na biyu ilmina da ďaukakata akan aikina wanda ba wani ne ya tsaya mun na same su ba illa Daddy.
Abun duniyar da ake tunanin na tara wanda ban same su ba duk sai ta hanyar Daddyn da Mamin.
Duk wani abu mai kyau da sanya ayi alfahari da yake kewaye dani idan akayi tracing ďin origin ďin shi wajen Mami da Daddy zai koma and this Mami da Daddyn kuma da nake ta magana akan su waye su?
You really want me to insult myself kafin ki yarda cewa da bazar iyayen ki nake rawa kuma da sunan su nake ado? ……
He got very emotional hawaye suka taru a cikin idanun shi wanda suka sanya jikina yayi bala’in sanyi. Na soma danasanin faďin maganganun da nayi kai tsaye.
“Ko me zan zama a rayuwa, kowanne irin mataki zan taka kowanne irin girma da kima mutane zasu kalle ni da shi will never change me as wannan marayan da Daddy ya ďauko daga London cikin maraicin mahaifiya da mahaifi mai raunin da ba zai iya ďaukata ya kaini wajen dangin shi ba. It will never change those memories, those sacrifices da challenges ďin da Daddy ya fuskanta a kaina.
A hakan kike da karfin guiwar tunanin cewa wai mutane ke suke yi wa murna da aurena when all i have is your parent kuma kome nake da shi I got it from them?
Kinyi adalci kuwa kenan?
Ya soma share hawayen da suke sauko mi shi yana ci gaba da magana.
“Ba kiyi adalci ba ko kaďan kuma baki kyauta mun ba to think that I will ever look down on you ko kuma zanyi miki gori watarana akan alfarmar da kika yi mun wadda na rasa daga duk matan duniya. Idan kuma har na iya buďe bakina nayi miki gorin rashin aji ni kuma gorin rashin me za’yi mun?
Gorin zama mafi butulcin ďanadam ko na wanda yafi kowa iya rama alkhairi da sharri?
How many times do I have to clear this to you? Cewa ni ďin ba kowan kowa bane? Wannan halittar ta wa da kuke kallo kuke ganin kamar na bambamta da sauran mutane saboda ni ďin ba kabilar ku bane Zara. Babana balarabe ne mamana baturiya and you expect me to look like a normal Nigerian? Idan na shiga cikin su bacewa kyauna zai yi mu saje da su, bambamcin yare da kalar fata ne kawai ya sanya na futa daban a cikin ku ba wani abu ba.
Nagartar da ake kallona da ita ba kyau ne ya bani ba samun kyakykyawar tarbiyya da ilmi da kyawun hali ne irin wanda Daddy da Mami suka bani.
I’m nothing in this world without your parent Zahra! I’m nothing! I would be nothing without them kuma ban taba regretting rayuwa ta a karkashin kulawar su ba, I might have lived with my parent amma ba lallai na samu irin waďannan tarin baiwa nasarorin da na samu a dalilin rikon Daddy da Mami ba…….
So duk wanda yace miki kinyi dacen miji kara kawai yake mun idan shi din masoyina ne, idan kuma makiyi na ne cin fuskata yaso yi ……..”
Ganin yana kuka sosai hankalina ya kuma tashi! Haushin kaina ya kamani, nayi nadama da danasanin abinda na aikata! Cikin kukan da na kasa dannewa na haďa hannayena guda da sigar roko na soma bashi hakuri
“Don Allah don Annabi kayi hakuri Ya Mahmud!
I do not mean a word akan abinda na faďa, billahillazi ba haka nake nufi ba kuma ba tunanina kenan ba kuma bansan ranka zai baci ba.
Don Allah ka rufa mun asiri kayi hakuri ka janye waďannan tsauraran kalaman a kaina, stop saying all this, you deserve everything in this world, you deserve more than this. Idan kana alfahari da Daddy da Mami su ma ďin basu da wanda suke alfahari da shi irin ka….
Kuma babu wanda zasu baiwa irin matsayin ka, because you have given them duk wani haqqi da ďa yake baiwa iyayen shi and even more. You have given them more than they expect. Ka shigo rayuwar su as wani blessing da suke fafutukar nema ido rufe! Ka share musu hawayen kukan da suke yi kuma ka zame musu sanadin alkhairan da ba zasu iya lissafawa ba.
You are a great person! You have a good heart! You have the best character and qualities So duk inda rayuwa ta kai ka waďanda suka zauna da kai zasu samu albarkar ka kuma zasu yi alfahari da kai…….
Everyone in the family is proud of you!
Everyone is happy you are in their life!
Everyone wants to call you theirs
And I’m the most happiest, the most luckiest, the most proud to call you my husband……”
Na karashe kalmar karshen da sauti karyayye.
And then sai muka ci gaba da kukan mu mu biyu cikin mota kamar irin yan yaran nan da babar su ta tafi unguwa ta bar su ko waďanďa iyayen su suka shiga shopping mall suka kulle su a mota.(lolz)..
Assalamu alaikum
Kuyi hakuri da rashin replyn messages ďin ku don Allah! Uzuri yake mun yawa, but I do appreciate every single like and comment wallah.
I love you all.Sai da muka yi kukan mu muka koshi sannan wayar ya Mahmud ta soma ringing kamar daman jiran namu take yi muyi shiru. Sai da yayi gyaran murya sannan ya ďauka
“Hello Ezike!………”
Banji me yace masa ba naji ya sake cewa
“Oh Faisal has told you! Ohk thank you!”
Tissue ya zara ya gyara fuskar shi kamar yanda nake yi, domin munyi kukan mun gaji kuma mun fuskanci juna saboda haka hawayen suka tsaya.
Ya sake gyara zama yace
“Now I want us to drop everything aside mu fuskanci rayuwar da take gaban mu! Ban yi miki alkawari zan dawwama cikin faranta miki ba, amma nayi alkawari bazan bata miki rai da gangan ba.
I will respect you, I will serve you and I will worship you! I will be the best husband da zan iya zama a gare ki and I promise not to fail you.
Na lura a wannan stage ďin ba soyayya ce ta dace da mu ba, so let’s give it time! Muci gaba as the brother and sister we were! Kallona da kike as your husband shi yake gayyato miki all those negative thoughts da awkwardness ďin da bana so.+
Friends can still be friends even after marriage right?
And a sister and brother can still maintain wannan relationship ďin na su ko bayan aure ko?
Ina so naci gaba da zama yayanki kuma abokin ki, all those husband and wife stuffs will come naturally we do not have to force our minds. But all we need right now is good communication and understanding, we need to make good foundation a cikin auren mu mai matukar kwarin da ba zai rushe ba.
Can I be your brother and your best friend??”
Ya karashe maganar yana miko mun hannun shi, exactly yanda yayi a garin London, watarana da nace zan bi Daddy saboda Dada da Mami sun haďe mun kai shi kaďai suke kulawa kuma bazan manta ba a ranar muka fara shiri ni da shi…..
Ban bata lokaci ba na mika mi shi nawa hannun ina cewa
“You are my favorite brother and my best friend”
Muka kyalkyale da dariya kamar wasu wawaye. Wai kuma shikenan mun shirya, sai hira ta balle muka dinga baiwa junan mu labarin noty abubuwan da suka faru muna dariya. Ya kunna motar ya hau titi muka juya cikin gari cike da farin ciki da annashuwa kamar wani sabani bai taba shiga tsakanin mu ba.
Ana kiran magrib muka isa gidan Mami! Shi ya tafi masallaci ni kuma na shiga cikin gida, direct ďakin Mami na isa na saka mukulli na buďe sannan na mayar da kofar na rufe.
I’m off! Don haka wanka na shiga nayi da ruwa mai zafi saboda na warware gajiyar da take tare da ni sannan nayo alwalar da bana raba kaina da zama cikinta saboda muhimmancin ta na futo.
Komai na jikina sai da na bashi lokacin da yake bukata kasancewar na kwana biyu ban yi gyara da wanka mai kyau ba sai a asibiti. Nayi sauri na shirya cikin kaya masu sauki sannan na futo na shiga kitchen na soma tunanin abinda zan sarrafa mana muci ni da Ya Mahmud domin banga sabon abinci a gidan ba.
“Don’t stress yourself, nayi mana order yana kan hanya”
Muryar Ya Mahmud kenan da ke bayana a tsaye a kofar kitchen ďin.
Nayi murmushi na buďe fridge na haďo masa drinks na futo da su zuwa dinning. Muna zaune muna hira har abincin ya iso muka baje shi cikin plates ďaya muna ci domin tuni mun koma normal Ya Mahmud and Zaran mu na da ba waďannan sabbin couple din ba. And it feels sooo good!
Anan yake gaya mum cewa Imamu yayi mi shi sallama yayi tafiya.
“Ko shi yasa wayar shi a kashe tun shekaranjiya? Nikuwa bai gaya mun ba”
Murmushi Ya Mahmud yayi sannan yace
“Yace na gaya miki ai tun da kina London yace “he will suprise you ko” wai idan ya dawo zaki ga suprise ďin”
STORY CONTINUES BELOW

Na tabe baki! Negative thoughts ďin nan suka sake zuwa kaina!
“Me yasa Ya Mahmud ba ya kishin Imamu? He is my ex for heaven sake amma ya mayar da shi kamar wani ďan’uwana ba ya jin ko haushi idan ina magana akan shi!”
Sai wata zuciyar tace
“Because he doesn’t have feelings for you as his wife!”
Na girgiza kaina ina mai tabbatar wa da kaina cewa wannan shi ne sahihin dalili. Don haka duka far’ar fuskata ta ďauke “ďuf” sai kace Nepa.
Ban sake cewa komai ba kuma banci gaba da cin abincin ba sai wayata da na janyo kawai ina dannawa.
“Zara”
Nayi mi shi banza
“I’m talking to you”
Na ďago na kalle shi, looking very serious.
“Do you want to see the jealous Ya Mahmud?”
I was shocked! He actually read my mind?
Nayi shiru ina al’ajabi
“Zara I know you very well and I can read every little move you make, ba sai kinyi magana ba nake karanta abinda yake kan fuskarki da wanda yake cikin zuciyar ki!
I don’t want to pressure you! Bana son na takura miki, especially on Imamu! Mutumin da yayi mana alkhairin da ba zamu iya rama mi shi ba. Wanda ya tsaya tsayin daka akan kare mutunci da daraja da martabarmu ba domin komai ba saboda yana sonki tsakani da Allah.
Forget about his past, a yanzu kam Imamu nutsatstsen mutum ne kuma nagartacce kuma ya zama family, abinda yayi mana ko Sadik da Omar ne suka yi za’a yaba musu.
So saboda ni ne sarkin shirme da sokanci sai nace zan yi kishi akan sa bayan ba domin shi din ba da kila ina can a kwance rai a hannun Allah ko kuma ina tsare ina fuskantar hukuncin laifin safara da cocaine a turai? Atleast ina da shekarun da ya kamata na dinga danne wasu al’amuran komai tsaurin su saboda yakana da alkunya da kuma mayar da alkhairi da alkhairi.
Not because I don’t love you, I really do, more than anyone can imagine! but if you insist, I will go ahead and show you the jealous and romantic me…….”
Kafin ya karasa na tashi a guje na shige ďaki na haye kan gado with alot of feelings da bazan iya bayyanawa. I just realized that I’ve started falling for this guy! He is just too adorable…….
Daga wannan tunanin nayi bacci, bacci mai daďin gaske irin wanda na daďe ban samu yin irin shi ba. A cikin baccin wayata ta dinga kara wanda ya haifar mun da buďe idanuna dakyar na ďauki wayar ba tare da kallon screen ďin ba saboda hasken shi.
“Kin fasa komawa asibitin ne?”
Ya Mahmud ne.
Da sauri na kalli bed side alarm clock naga time, na zaro ido cikin mamaki domin karfe 11 ne na dare idona ya nuna mun
“I slept off! Don Allah gani nan futowa”
A guje shiga toilet nayi brush da uzurorina sannan na futo na shirya cikin pyjamas ďin “Victoria secret” pink na ďora hamshakiyar abaya baka mai sulbi bayan na wadata ta da oil perfumes din gidan turaren “Abdussamadul Quraish” na birnin makkah har da na feshi ma.
Kafata ta flat Vinci shoes ne masu kyau, na chanja jakar hannuna da chanel ruwan hoda looking very classy and charming!
Na kulle mata ďakin na futo, already yana mota don haka ko maids ďin gidan ban tsaya kalla ba na fuce cikin sauri ina mamakin yanda akayi nayi bacci me yawa haka.
“Amaryar Ya Mahmud”
Abinda ya fara ce mun kenan ina zama cikin motar.
Nayi murmushi kawai, domin maganar ta ďauke a dalilin baccin da nayi.
“Golden Tears Oud by Abdussamadul Quraish?”
Na kalle shi ina mamakin yanda aka yi ya gane turaren da na fesa bayan tarukan oils mabambamta da suke jikina.
STORY CONTINUES BELOW

“I love duka turarukan su!”
Nayi gyaran murya nace
“But bansan lokacin da ka fara son oud da arabian perfumes ba.”
Yayi murmushi idon shi akan hanyar da yake bi yace
“Kin taba ganin balarabe yana kin oud?”
Nima nayi murmushin, na fahimci yanzu komai kankantar magana sai yayi linking ďinta da yaren shi da kabilar shi, abu kaďan za’ayi zai tuna miki cewa shi ďin balarabe ne.
“Toh me yasa baka sakawa?”
Ya sake kankame steering wheel ďin da yake tukin kamar wanda yake shirin kwace masa sannan yayi magana da karyayyen sauti
“They reminds me of Jawahir! Kullum turarukan larabawa take sakawa, duk da ni na koya mata amma har ta fini son su. So duk lokacin da naji kamshin oud ita take zuwa raina. When I relocated to UK, a kokarin gyara rayuwa ta ne ya sanya na goge duk wani abu da zai tuna mun da ita musamman kamshi wanda yafi komai tasiri wajen dawo da memory.
Ko yanzun nan da kika shigo motar rikiďemun kika yi kamar ita…………….”
Yayi shiru alamun ba zai iya cigaba da maganar ba.
“Kayi parking Ya Mahmud”
Bai yi musu ba ya gangara gefen hanya yayi parking, sai na buďe kofar na futa na zagaya wajen zaman driver, ba musu ya tsallaka ya koma wajena, na tashi motar naci gaba da tukin sannu a hankali ina jin ajiyar zuciyar sa.
Sai da muka isa cikin asibitin nayi parking sannan na juyo na kalleshi cikin sanyi nace
“Ya Mahmud you cry too much! You are not a boy for goodness sake! Ya za’ai ka dinga kuka akan kowanne abu karami da babba? Mata fa aka sani da rauni da maza ba!……”
Murmushi yayi irin me ciwo ďin nan sannan yace
“Saurin kuka da raunin zuciya bashi da gender Zara. Kowa da yanda Allah hake halittar shi, ni tawa halittar me rauni ce, zuciyata me tausayi ce kuma hawayena masu yawa ne, wani lokacin nima ba’a son raina suke sauko wa ba.
Amma ko na daina kuka akan komai ba zan daina akan Jawahir ba!”
Bansan lokacin da na maka mi shi wata harara ba sannan nace
“Saboda ita ce sarauniyar matan duniya ko kuwa da gold ko diamond aka kera ta? Wannan Jawahir shekara goma kamar jiya akayi jana’izar ta….”
Dariyar da yayi ce ta sanya na tsaya da maganar ina juya idanu. I hate this Jawahir wlh….
“Me tayi miki kika tsane ta?”
Kama bakina nayi saboda bansan lokacin da maganar ta futo ba. Amma banyi karya ba bana son ta duk da ta mutu, kuma na tsani soyayyar da yake mata.
“Is this the jealous Zara? Wonderful”
Shi abun dariya ya ďau maganar.
“Na ga dai kai ne kake mun lecture akan Aisha, kace mun idan na tuna ta na daina yi mata kuka addu’a take bukata. Amma ita wannan hamshakiyar kamshin turaren ta kawai kaji ka fara hawaye.
Ita Aisha ba mutum bace ko? Saboda ba’ai mata baiko da mai sonta kamar Ya Mahmud ba”
“La’ila! Zara har kin kai haka? So kishin naki ma da wadda bata raye zaki yi? Yau naga ikon Allah”
Yana maganar yana dariya.
Na sake bata rai nace
“Wai don Allah wacce iri ce Jawahir din nan bani labarin ta? Me tayi maka kake son ta da yawa haka?”
Ya sake yin wata dariyar, wannan karon idon shi a cike da hawaye
“She is unique and special! She has given me kowanne dalili da zan so ta na kuma girmama ta tana raye ko a mace.”
Then I became very curious, so nake naji komai akan Jawahir ďin nan da tayi zamani da mijina har ta cinye duka filin zuciyar sa bata bar masa wani space ďin da zai rakaba ni ba.
“I know she is unique! I know! “
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli kyakykyawan agogon hannun shi “Rolex” yace
“It’s late Zarah! I will tell you everything about her insha Allah! Nayi alkawari”
Na sauke ajiyar zuciya sannan na kama handle ďin motar zan buďe, but he held my hands…
Na juyo cikin alamar tambaya
“Jawahir is my past! Kuma ina respecting ďin ta ne saboda irin love, trust and respect ďin da ta bani. But that doesn’t mean she is better than you or I love her more than you! She is my past! But You are my present and my future.
And I love you with every fiber of my being, as a sister, as a friend as my darling wife and as the mother of my ch….”
Na kwace hannuna a sukwane na bude motar na futa.
“This guy will be death of me.”
Tare muka shiga cikin asibitin, sai da ya kai ni har barandar da zata sadani da ďakin sannan yayi mun sallama.
“Ba za ka shiga ba?”
Girgiza kai yayi sannan yace
“Ki shiga ina kallon ki sannan na tafi! Dare yayi”
A sanyaye na juya na tafi, na san saboda Mami ne baya son shiga, saboda irin shakulatin bangaro da take mi shi, saboda rashin sakin fuskarta gare shi idan ba haka ba, ai nasan Ya Mahmud mai zama ya kwana a asibitin nan ne ko don saboda wannan jaririn na Ya Nuratu.
Sai da na muŕďa handle ďin kofar zan shiga sannan na juyo na kalle shi, murmushi yayi mun sannan ya ďago mun hannu alamar “bye bye”
Na mayar mi shi da murmushin tare da sa kaina cikin ďakin.+
Daga Mami sai Ya Nuratu, kowa ya tafi kasancewar dare yayi. Na gaishe da Mami tare da yi wa Ya Nuratu sannu da jiki.
Mami tace
“Waye ya dawo da ke?”
Cikin sanyi nace
“Ya Mahmud ne”
Ya Nuratu tayi murmushi amma Mamin bata ce komai ba. Bana jin daďin abinda yake faruwa don haka nayi alkawarin gyara matsalar da yardar Allah.
Kwanaki biyu bayan nan aka sallami Ya Nuratu da Asad muka tattara zuwa gidan Dada. Ďakin da yake kusa da nawa aka buďe aka gyara tsab sannan aka kawo kayan bukatar mai jego da jariri aka shirya. Baba Rabi ce take yi wa Ya Nuratu wanka, A.laila ta shirya baby ta kula da shi tare da taimakona.
Ba’ayi wani taron suna ba domin duk ýan’uwa suna nan lokacin da akayi haihuwar, kafin sunan kuma kowa ya kama hanyar garin su ciki kuwa har da Inna Badi’a da family ďin Kawu Sulaiman. Don haka gidan yayi matukar daďi, musamman wannan baby da ya shige raina yayi kane kane. Amal na can Kano babanta ya tafi da ita don haka babu kiriya a gidan, wani lokacin har twins ďin Ya Omar Asim(Daddy) da Arif(Daddyn A.sofy) nake ďaukowa su taya mu jin daďin gidan.
Ina cikin baccin da na kwanta bayan azahar naji ringing wayata, na buďe idanu cikin sauri na saka hannuna kan drawer na ďauko wayar, mamaki ya kamani ganin sunan Imamu, domin tunda yayi tafiyar nan bamu sake magana da shi ba, time to time Ya Mahmud ya kan ce Imamu yana gaishe ni, ni kuma ban taba tambayar shi yana ina ko yaushe zai dawo ba saboda duk su biyun haushi suke bani.
“Hello”
Ya sake maimaitawa for the third time ina can ina tunani. Sannan na nutsu nayi mi shi sallama muka gaisa. Ya ďora da cewa
“Kin ji ni shiru ko?”
Nace
“Ai na ďauka yanzu me karamin karfi ba ya ganin ku”
Yayi dariya sosai sannan yace
“Lallai Zahra baki da kirki amma ba kya jin sakon gaisuwa ta a wajen Mahmud?”
Nace
“Ya Mahmud ne ya haďa ni da kai?”
“No! Ki fahimce ni, I don’t want to cause misunderstanding a tsakanin ku! Duk yanda abubuwa suka sauya tsakanin mu ai ba’a chanjawa tuwo suna, it will never erase the relationship we had. So wasu abubuwan sai mutum yana yi yana takatsantsan.”
Nayi ajiyar zuciya nace
“Ya Mahmud ba shi da matsala Imamu”
Cikin kaguwa yace
“I know that better! Well yanzu dai ba wannan na kira mu tattauna a kai ba. Akwai important maganar da nake so muyi.”
Sai da gabana ya faďi domin ni Imamu tsoro yake bani, abubuwan da yake zuwa yana zakulowa kuma masu matukar nauyi da ďaga hankali ne.
STORY CONTINUES BELOW

“Tsoro ko? This time ba mummunan labari bane but may be ke ki ďauke shi a mummunan labarin idan aka yi la’akari da cewa baki san komai game da maganar ba.”
Cikin sanyin jiki nace
“Don Allah cut it short ka gaya mun, kirjina har ya fara racing”
Ya soma yi mun bayani.
“Kinsan cewa akwai case ďin kuďi a tsakanin Mami da Alhaji Muktar(maigidanta)?”
A tsanake nace
“Eh nasani amma ba wani ne ya gaya mun ba, maganar naji tana yi da Ya Mahmud watarana.”
Ya sauke ajiyar zuciya yace
“Mami tana bin shi naira miliyan ďari biyu wanda ya ranta lokacin da suke cikin case da EFCC, bayan kura ta lafa ta nemi ya biya ta kuďinta amma kullum cikin excuses yake. Tun bata damuwa har ta shiga damuwa, I’m sorry to say! Alaji Mukhtar ba shi da kirki ko na cikin cokali, yana da kuďi amma matan sa basa ci sai matan waje! Zaki iya tuna watarana da yayi sati biyu baiyi tafiya ba?”
Na ďaga kaina ina tunanin tun auren Mami da shi sau nawa muka haďu? He is always busy, kullum ba ya gari, lokutan da yake garin kuma harkokin siyasar shi ne kawai a gaban shi. Ban tuna watarana da na taba ganin shi ya wuni zur a gida ba ko ya kwana biyu cif kamar yanda ya kamata a gidan Mami. Don haka ko kaďan bamu saba da shi ba, da wuya wani al’amari ya faru na family yazo, ko bikin su Ya Umar babu shi, bikin mu kuwa ko leke bai yi ba. I use to think wanne irin busy mutum ne shi da bai da lokacin kowa da komai sai kansa? But da wa zan tattauna wannan matsalar? Mami? Bata bani fuskar da zan mata magana akan shi ba. I’ve ones tried nayi maganar da Ya Mahmud amma bai bani dama ba ya katse ni.
Daga nan nima na shiga cikin wasu rikirkitattun al’amuran da suka shafe wannan na bar maganar. But this time, ina so nayi wani abu, I would really love to make a move nayi wani abu akan rayuwar Mami wadda bata da aiki sai inganta rayuwar wasu da nemo hanyoyin da zata sa saka mu farin ciki. Ita kuma tana cikin wata irin rayuwa wadda ita kaďai ta san abinda take haďiya a cikinta.
Katse mun tunanina yayi yaci gaba da magana!
“Alhaji Mukhtar yaci kuďin Mami kuma ba shi da niyyar biyan ta ko sisi duk da cewa ko ba shi da kuďi a banki yana da kadarorin da zai iya bata a madadin kuďin amma zaluncin sa ba zai bari yayi ba. Kullum yana kan hanyar wuraren shakatawa da ýanamatan da ya haifa a cikinsa a gida da wajen Nigeria. Ba wata tsiyar yake zuwa wani wajen yayi ba sai iskanci, idan ya dawo kuma ayyuka su kacame masa ya bar komai ya kammala su. At long last Mami tayi deciding ta karbi hakkinta ko da kuwa ta karfin Shari’a ne, amma sai yayi threatening ďin ta da cewa idan har ta kai shi kara zai bata mata suna, nayi imanin ba zaki so kiji wanne irin sharri ya kulla mata ba don haka bazan gaya miki ba, amma girman wannan abun ya sanya Mami ajiye duka makamanta ta zuba masa idanu yana cin karen sa ba babbaka.
Da farko Mahmud yaso kwato mata hakkinta duk da cewa bai san abinda Alaji Mukhtar ďin ya shirya ba, amma Mami ta bata rai tace babu ruwan shi yayi hakuri zuwa wani lokacin.
Ya sha yunkurin yin wani abu akan maganar amma duk ta hanyar da ya bullo sai ya ga dole sai da haďin kan Mami ita kuma ba zata ba shi abinda yake so ba don haka jikinsa yayi sanyi.
Abinda Alhaji Mukhtar bai sani ba shi ne, yana taku yana barin footsteps ďin shi ne, akwai abinda ya haďa ni da shi, dalilin da ya sanya na fara bincike a kan shi kenan, sai kawai naci karo da case ďin shi da Mami don haka na lashi takobin he will pay for it.
Abinda nake so da ke yanzu guda ďaya ne! But it may be hard for you amma dole kiyi kokari ki samo mana.
Na share hawayena nace
“Ina jinka”
Murmushi yayi yace
“Wai when did you become this soft? Ni Zaran da na sani babu abinda yake sa ta kuka komai girman shi. She is as strong as a rock! Amma yanzu kuka yafi komai yi miki arha!
Ban zo miki da maganar nan ba sai da na tabbatar na samo mana mafita, ba don abinda nake son kiyi mun ba ma da sai komai ya warware zan neme ki.
Don haka ki share hawayen ki kiji abinda zaki yi, kukan will not help us.”
A sanyaye nace
“Me zan yi?”
Yace
“Good! Alaji Mukhtar ya baiwa Mami takardar saki 2months ago, amma bansan dalilin da ya sanya ta kasa gaya wa kowa ba kuma ta kasa yin komai akai ba! Da farko na ďauka abubuwan da suka dinga shigowa ne marasa daďi da matsalar Mahmud; but then after everything was over hankali ya kwanta still ba ta yi yunkurin yin komai ba.
Matakin da na ďauka da tarkon da na ďana mi shi bana son yayi aiki alhalin da igiyar auren shi akan Mami, musamman da babu wanda ya san da maganar sakin daga shi sai ita.
Ina so kowa ya tabbatar yayi sakin, kuma basa tare kafin ya gurfana a gaban Shari’a don nayi imanin cewa zai yi bai san da maganar sakin ba ko kuma yace ya mayar da ita.
Kuďin Mami kuma a halin yanzu suna kwance lafiya kalau a cikin account ďina, i had to make sure na kwatar mata haqqinta kafin dukiyar da ya tara ta shiga rurumar gwamnati wanda I’m sure a lokacin da zai futo daga hannun EFFC ba shi da komai.
Nayi mi shi tallan filaye a sabuwar estate ďin da muke yi, a yanzu haka kuďin filayen 45ml ne, but by the time aka kammala tsara estate ďin aka soma gini kuďin su zai ninka biyu, so da haka nayi convincing din shi ya siya guda biyar da assurance ďin ko nan da shekara ďaya ya tashi siyarwa zai yi mamaki. And he knows land in Abuja, tuni ya tura kuďin aka kammala komai. But he will never get to know that duka papers ďin hannun shi fake ne, and not even his lawyer can defend him.
Hmmmm! Kinsan yanzu me nake so da ke?”
Hawayen dai na sake sharewa ina tunanin wanne irin mutum ne Imamu kuma da me zan biya shi taimakon da yayi mun a rayuwa?
“Gidan Mami zaki je ki duba inda ta ajiye takardar nan ki tabbatar Dada da su Daddy sun gani sun karanta! Ina nufin ki fasa kwai kowa yaji!”
Wani irin faďuwa naji gabana yayi saboda girman aikin da Imamu yake nufin naje nayi mi shi da kuma tsoron abinda zan fuskanta daga wajen Mami.
“You can do this Zara! You can! And you really need to idan har kina so mu ceto Mami daga hannun wannan azzalumin! She needs peace da kwanciyar hankali itama.”
Toh daga nan ne fa na shiga tunanin hanyar da zan bi na nemo inda Mami ta ajiye wannan takarda which I’m sure ba zan gane shi cikin sauki ba. Sau uku ina zuwa gidan na ta ina buďe buďe da bincike bincike na amma ban samu komai ba, there was a time da na samu mukullin safe ďin ta na buďe cikin exitement don ban taba tunanin bazan same ta a ciki ba, but to my greatest suprise babu ita ba alamar ta a ciki.
Sai hankalina ya soma tashi, ganin na ďebi sati ďaya ina abu ďaya, kuma Imamu kullum azalzalata yake yi da nuna mun cewa lokaci zai kure.
At long last wani yammacin lucky asabar Mami tazo gidan Dada sai wata client ďin ta tayi mata waya sai naji tana cewa
“Wallahi kuma bana gidan yanzu gabaďaya na manta munyi maganar zaki karba!”
Sai ta sake saurarawa sannan tace
“No! Ba damuwa zan saka a ďauko sai ki biyo nan Gwarimpa ki karba”
Bayan ta ajiye wayar ta dube ni tace
“Zara don Allah zo na aike ki gidana! Wata ce wallahi tazo yin fitting ta manta ýan kunnayen ta a fitting room ďin. Na manta munyi da ita yau zata zo ta karba.”
Nace “toh” Ina mikewa.
Dada tace
“Ita kuwa don wasu ýan kunnaye zata damu haka? Mutane suna da son abun duniya”
Mami tayi dariya tace
“Dada na diamond ne fa!”
Tace
“Oho! Toh Allah ya taimake ta masu aikin naki suna da amana….idan wasu ne ai sai dai tashin labarin…….”
Suna cikin maganar na futo daga ďaki bayan na ďora bakar abaya kan short gown ďin da take jikina. Na durkusa na karbi mukullan da take miko mun
“Ki buďe ďakina na can ciki, ki tsaya ki nutsu kuma bana son wasa ko bincike, ki buďe drawer gado zaki ga ďan karamun envelope suna ciki ki ďauko”
Na karba cikin ladabi na mike ina yi wa Dada sallama.
“Zara ban da gudu don Allah kuma ki nutsu ki tabbatar kin kulle mun ďaki ya kullu kafin ki taho, bana son garaje”
Na amsa
“Mami insha Allah”
Zan buďe kofar falon Ya Mahmud yana shigowa. Ya kalle ni da question mark alamar ina zanje?.
Assalamu alaikum
I’m sorry kuci gaba da hakuri please!
I’m busy, very busy amma zan yi kokarin yin update duk lokacin da na samu dama.
Thanks.
A nutse na kalle shi, he looks disturbed and tired, wannan gashin duk ya hargitse da alama bai samu yanda yake so a wajen mamallakin na shi ba. Na bashi amsa ina tabbatar da cewa babu wanda yake jin me muke fada a cikin falon domin muna daga wajen kofar futa ne.
“Mami ce ta aike ni!”
Ya girgiza kai zai wuce nayi maza nace
“What’s wrong with you?”
He raised his eye brows kaďan sannan yace
“I’m okay! Wannan weather ďin ta Abuja wahalar da ni take yi idan na futa. Zafin is too much, kamar ana tsira mun allurai a jikina gashi Allah ya haďani wicked brother…..”
Nayi murmushi, bai taba zuwa Nigeria yayi irin wannan daďewar ba, kuma idan yazo yana cikin gida yana hutawa cikin Ac, a mota ma Ac ce kuma wuraren da yake zuwan ma duka basu san ana rana ba, but this time Faisal ya mayar da shi tantagaryar ďan kwadago, kullum suna hanyar Kano, Kaduna da Lagos akan ýan kuďaďen da ninki ukun su suke shigo ma shi Ya Mahmud ďin cikin account hankali kwance duk da cewa ba wanda ya san hakan sai shi kaďai.
But he enjoys it sosai, yana son rayuwar Malam bahaushe da yanda yake baiwa neman kuďi muhimmanci domin ya sauke hakkin iyalin shi ya wadatar da su. Shi kuma Faisal is a jack of all trades, Duk arziki da alfarmar mahaifin shi being the only son a wajen shi kuma hakan bai hana shi neman na shi na kan shi ba.+
Duk wata harka da zata kawo kuďi na halaliya Faisal yana tsunduma kansa a ciki, baya girman kai kuma baya raina riba komai kankantar ta.
Don haka kullum kara habakewa yake yi arziki yana karuwa, yana kuma saka Mahmud cikin harkokin ne a kokarin shi na rage mi shi tunani da damuwa akan matsalar shi ba wai don yana bukata ba. Shi ya san Mahmud baya sha’awar kasuwanci ko kaďan, burin shi yaje office yayi aiki ya dawo gida ya kwanta, komai na rayuwar shi a lissafe yake yin shi, kuma baya son wani abun ya shiga lokacin wani, don haka yake jin kasuwanci bai dace da shi ba, duk naci da dabarar Daddy yayi masa amma sam yaki amincewa ya fahimci komai akan harkokin Daddyn balle ya saka shi a ciki.
Wannan lokacin kuwa shi kan shi yana bukatar abinda zai ďebe mishi kewa ne, da kuma rage tunani shiyasa yake bin Faisal da yanda yake so.
A hankali nace
“Have you eaten ma kuwa?”
Yace
“Daga gidan Faisal nake, cook ne yayi musu girkin, ina ganin shi naji bazan iya cin abincin shi ba, ya bar farce duk ya taru a hannun shi…. so kawai nace musu Dada tana kirana………”
Jin muryar Dada muka yi tana cewa
“Toh bayin Allah ku shigo ku zauna kuyi hirar a zaune mana ko ku futa ku nemi wajen zama, ko kafafun ku basu fara ciwo bane?”
Dariya muka yi duk mu biyun, na bashi hanya ya shiga, amma sai na koma cikin kitchen na haďa mi shi salad da lemo mai sanyi na dawo falon na ajiye masa a gaban sa. Believe me mantawa nake yi wai munyi aure da shi, ni a Ya Mahmud ďin da na saba ganin shi nake kallon shi wallahi kuma babu komai a cikin raina.
Ina ajiyewa na dubi Baba Rabi nace
“Baba Rabi ki dafawa Ya Mahmud doya don Allah na ajiye source ďin da nayi da safe a fridge sai ki ďumama masa. Kuma ki tabbatar ya cinye tass ni nasan abinda zan baki……”
Saukar pillow ďin da naji akan fuskata ne ya dakatar dani, na ďaga ido da sauri na kalli wanda ya jefa mun, ashe wai tunda na kawo mi shi salad ďin Dada take kallona kallon zuru tana kwafa, nikuma banzar ku ban ma kalle ta ba balle nasan abinda take yi, sai da suka ga Dadan na niyyar kaiwa karshen kulewa A.laila ta jefeni da pillow!4
“Ohchhhh! A.Laila ne nayi miki?”
Na faďa ina shafa hancina da pillow din ya daka.
“Ki wuce ki tafi aiken da akai miki kin tsaya neman magana! Bako ne shi Mahmud ďin? Ki kiyaye ni fa Zara”
STORY CONTINUES BELOW

I’m sure bani kaďai na haďiye dariya ta ba, domin A.laila tayi amfani ne da irin kalaman Dada ta ari bakinta taci mata Alabasa! Sai lokacin na gano abinda nake aikatawa kunya da dariya suka kamani. Na juya a guje ina toshe bakina na futa na bar gidan.
Kai Dada drama Dada rigima Dada danger wutar baya. Yanzu da nayi banza da shi ba kyale ni zata yi ba, wani faďan zan sha na rashin nuna kulawata a kansa, na nuna mi shi kulawar kuma nayi rashin kunya. Ohh! This is African parent for you! Allah yayi wa iyayen mu albarka.
A nutse nake driving har na isa gidan Mami, nayi parking na buďe motar na futo na shiga gidan kai tsaye na danna kararrawa masu aiki suka buďe mun tare da gaishe ni.
Babu bata lokaci na wuce ca cikin ďakin Mami na ciki wanda ba kasafai take amfani da shi ba kuma bata cika barin sa a buďe ba. Na saka mukulli na buďe nayi sallama na shiga sannan na kunna fitila ina bin ko’ina da kallo. Komai tsab yake, ga kamshin Chanel no5 na tashi a hankali.
Na wuce kai tsaye drawer ďin gadon na buďe, ina buďewa naga envelope ďin na ďauko na saka a jakata sannan na mayar da drawer ďin na rufe. Har na juya zan futa wani abu ya ďau hankalina, na dawo cikin sauri ina kallo, littafi ne guda wanda aka rubuta akan patient masu fama da hawan jini, wanda ya kunshi duk wani bayani akan ciwon hawan jini, yanda ake yake kama mutum, alamominsa, maganin sa da hanyoyin da za’a bi a zauna lafiya, dokokin ciwon irin abincin da mai ciwon zai ci, wanda ba zai ci ba da dai sauransu.
“Me ya haďa Mami na da ciwon hawan jini?”
Na jefawa kaina tambayar ina jin wani irin tashin hankali da fargaba, na saka hannu na ďaga littafin sai envelopes guda biyu suka faďo, nayi maza na ďauko su, na farke cikin sauri ba tare da tunanin yanda zanyi idan na karanta na mayar da su daidai ba.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!!
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!!!”
Na dinga maimaita kalmar cikin tsakanin tashin hankali da masifar tsoro da fargaba.
Result ďin likita ne har guda biyu, ďaya test ďin sugar ne wanda aka tabbatar tana da shi, ďayan kuma na STDs ne, na dinga bi ďaya bayan ďaya bakina yana rawa, a wannan fannin kam ko’ina negative bata da matsala.
Sai na durkushe a wajen ina kuka kamar raina zai futa! Yanzu Mami is going through all this alone? Mami tana ďauke da ciwon hawan jini da sugar amma bata gayawa kowa ba? Bata nemi ďauki ko shawarar kowa ba kuma bata ďauki mataki ba? Why? Why? So take yi mu wayi gari mu tsinci gawar ta a ďaki?so take ta bari sai ranar da ciwon yayi mata illar da likita ba zai iya magani ba?
So take sai bakin ciki da damuwa sun nakasta ta idan kwananta bai kare ta mutu ba? Why? Me yasa Mami take going through this pain?
Wani irin fushi da tsanar Alhaji Mukhtar suka taso suka mamaye zuciyata.
Na tattara duka abubuwan da na gani na zuba cikin leda, har zan bar dakin na juyo, na soma buďe duk inda idona ya kai ko zan binciko wasu abubuwan, ko akwai wani ciwon da take da shi take boyewa bayan wannan, ko akwai abinda ya kamata na sani bayan waďannan.
And then i found it! Cikon Allah ban samu komai ba sai da na daga pillow sannan na gamu da abinda na sha zuwa gidan takanas saboda shi ina dubawa, wato ambulan ďin takardar sakin Mami. Ban kara ko second ba na tattara komai cikin ledar da na saka sauran abubuwan da na samu a wannan bakin ďaki na na futo na mayar da kofar na kulle na futo daga cikin gidan cikin sauri na shiga mota.
Ina driving ina kuka na futar hankali ina zabga gudu na wuce ka’ida domin a wannan lokacin ba’a cikin hayyacina nake ba kuma babu nustuwa ko kankanuwa a tare da ni.
……………………………………………………………….
Ikon Allah ne ya kai ni gida lafiya ba irin tukin da nayi ba! Ko da nayi parking na daďe a motar ina kokarin tsayar da matsananincin kukan da yake tahowa daga can karkashin zuciyata na kasa.
A kalla nayi mintina ashirin a haka kafin na samu kuzarin buďe kofar motar na futo kaina yana sarawa kamar zai tsage biyu. Na dinga takawa a hankali kamar mai koyon tafiya har na isa cikin gida, na murďa kofar falon na shiga! Suna nan har lokacin a zaune, Ya Umar da Ya Sadik sun shigo su ma ana hirar tare da su, A.laila tana shirya Asad bayan tayi mi shi wankan yamma, Ya Mahmud yana cin abincin da aka girka masa bayan tafiya ta.
Sai kawai gani na suka yi cikin falon kamar mahaukacciya fuskata tayi jajazur naci kuka na koshi, ko idanuna bana iya buďewa sosai.
Sai falon yayi tsit for seconds, kafin Ya Nuratu ta taso da sauri zata kamani, nayi baya ina dakatar da ita!
Mami nake kallo with alot of anger and disappointment, ta wani bangaren kuma ina jin matsanancin tausayin ta, amma a yanzu haushin da nake ji yafi tausayin tasiri, a ganina Mami bata da hujjar da zata boye mana irin waďannan al’amuran.
Ita ma ďin ni take kallo, kallo na tsoro da fargaba da guilt da kuma kashedi, irin yanda take mun idan tana so ta gargaďeni akan wani abu ba tare da wani ya fahimta ba. Ina ganin tayi hakan kuma nake ganewa na bi umarnin ta, but today, akan wannan issue ďin, ko idanun Mami zasu faďo saboda warning ba zasu hana ni yin abinda nayi niyya ba.
“Zara me ya same ki? Me ya faru? Ke da waye? Me aka yi? Waye ya mutu?”
Tambayoyin da Ya Sadik ya jero mun kenan cikin kaguwa da tsoro da fargaba.
Shi kuwa Ya Mahmud ya kasa ko motsi sai idanu da ya zuba mun baya kiftawa.
A hankali na tako zuwa gaban Mami na tsaya na soma magana cikin wata irin murya mai cike da anger, bitterness da disappointment hawaye na zirara daga idanuna!
“Mami me yasa zaki yi mana haka? Me yasa kika zabi kiyi mana haka? Why?
Mami me yasa kika yi mana haka? Me muka yi miki don Allah? How did we deserve this from you?”
Sai naga a hankali fuskar ta ta juye daga waďancan expressions ďin zuwa alamar tambaya da kuma wani gingimemen tsoron da yaci uban na da. Wanda na alakanta hakan da may be tunani take yi ko Alhaji Mukhtar ya tunkare ni da sharrin da yace zai yi mata ne idan ta kuskara tace zata yi yunkurin daukar mataki akan shi domin a yau ďinnan ma sai da suka yi waya da shi suka rabu baram baram.
“Me Mamin tayi? Me yake faruwa?”
Dada ma tayi magana cikin sanyi da fargaba.
“Mami ki bani amsa how did we deserve this from you? Mami kin bani mamaki! Kin bani mamaki wallahi kin bani mamaki kuma I don’t think I will forgive you and myself for this…..
I will not forgive you if something happens to you……! Mami baki kyauta mun ba wallahi baki kyauta mana ba, baki kyautawa kan ki…….”
Bugun da aka kaiwa bakina ne ya ya tsayar da ni na ďago na dubi Ya Mahmud da ke huci yana zabga mun harara. Daman nasan shi ďin ne tun kafin na kalle shi, ba ya tolerating nonsense akan Mami komai kankantar shi.
Zagaye shi nayi na dawo gaban Mami ina ci gaba da magana sai ya funcikoni na koma baya musamman da ya ga yanda Mamin take sauke numfashi cikin wahala kamar me haďiyar allura.
Nayi taga taga zan faďi Ya Omar yayi sauri ya tsayar dani, sannan ya kama hannuna da niyyar barin falon dani naja na turje cikin wani irin karfin da fushin da nake ciki ya bani.
“Kyale ta Umar! Sake ta”
Dada tayi maganar a kausashe, sannan ta kalle ni tace
“Zara zo nan”
Bai sake nin ba sai da ya kaini har gaban Dada na tsuguna sannan ya nemi gefenta ya zauna hankalin kowa ya dawo kaina.
“Zara ki nutsu kiyi mun bayani me yake faruwa? Me Mamin tayi? Me kika ji ko kika gani?”
Sai naji zuciyata ta sake karyewa, but Dada ce take tambayar don haka ban ja lokaci ba na soma magana cikin dushewar muryar da taci kuka ta koshi.
“Dada kunsan cewa Mami tana ďauke da ciwon sugar da hawan jini?”
Cikin kaďuwa Dada ta zaro idanu tana kallona, bama ita kaďai ba babu wanda bai shiga mugun shock da jin wannan maganar ba.
“Dada Mami ta daďe cikin damuwa da bakin ciki a gidan ta amma cikin mu babu wanda ta ga ya cancanci ta gaya mi shi, babu wanda tayi sha’awar yin sharing damuwar ta da shi balle ya bata shawara not even A.laila. haka ta dinga rayuwa cikin tashin hankali da ciwon zuciya a karkashin azzalumin mutum irin Alhaji Mukhtar………….+
“Wannan result ďin yayi watanni shida da futowa amma Mami bata gaya wa kowa komai a kan shi ba……tana cikin damuwa bata faďa ba, ta zauna a ciki to the extent ďin da damuwar ta haifar mata da manyan ciwuka irin wannan still bata gayawa kowa ba taci gaba da zama a ciki tana hakurin da watarana zai iya yin sanadin ranta……
“Dada Alhaji Mukhtar ya karbi kuďin Mami naira miliyan ďari biyu ya hana ta, still bata gayawa kowa ba, yayi mata barazana mai muni still bata gayawa kowa ba, ya nuna mata true colour ďin shi ya tabbatar mata da kowanne irin mutum ne shi amma Mami bata gayawa kowa ba.
“And finally Dada yau watanni biyu kenan da Alhaji Mukhtar ya rubuta takardar saki ya bata amma bata gaya wa kowa ba tana zaune cikin gidan…..
Dada yaushe Mami zata yi magana akan damuwar da take ciki?
So take sai ranar da bakin ciki ya kashe ta mu je gidan mu tsinci gawar ta? Me Mami take nufi da ajiye wannan sirrin a zuciyar ta ita kaďai?………..”
Salati Dada ta ďauka tare da fashewa da kuka, haka A.laila da Ya Nuratu,
Ya Mahmud ne yayi maza ya koma gefen Mamin da jikinta yake wani irin rawa kamar ana kaďata ya rike ta sosai yana zubar da na shi hawayen.
And then……..
Daga wannan rawar jikin tayi loosing balance daga zaunen ta faďi, Ya Mahmud ya tallafota yana kiran sunanta, amma ina….tuni ta futa daga hayyacinta.
A guje Ya Omar ya tashi yana cewa
“Mu tafi asibiti! Mu tafi asibiti!”
Dukan mu muka mike cikin tsantsar tashin hankali, Ya Sadik ya taimakawa Ya Mahmud suka ďaga Mami cak suka futa da ita zuwa mota.
This is something da bai taba faruwa ba, ban taba ganin Mami cikin halin matsananciyar rashin lafiya ba balle ta kai ga kwanciya a asibiti.
She is a strong woman! She is as strong as a rock……..
Kullum tana tsaye da kafafunta akan iyalanta, kullum cikin hidima da mu take da dukkan karfin ta da aljihunta da kokarin ta da tunanin ta….
Burinta kawai ta ganmu cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba tare da kallon kanta ko la’akari da nata farin cikin ba.
She always puts us first a kowanne hali a kowanne yanayi a kowanne lokaci.
Bamu taba tunanin zamu kai asibitin da ranta ba, musamman ni da na soma kukan danasanin tona wannan maganar, da nasan abinda zai faru kenan da ban bi ta wannan hanyar ba ko da zan faďa ďin.
Muna zuwa nurses suka ďauko gadon marasa lafiya aka shimfiďe ta kamar gawa aka shigar da ita emergency likitoci suka dukufa kanta suna bata taimakon gaggawa domin su kansu sun tsorata da halin da take ciki
STORY CONTINUES BELOW

Idan ka kalle mu a wannan lokacin sai mun baka tausayi domin tsantsar damuwa da tashin hankalin da muke ciki. Ya Nuratu kawai aka bari a gida da babynta ba don taso ba, Dada ce ta hana ta tahowa suka zauna da Baba Rabi.
Sau biyu likitan da yake duba Mami yana futowa ya wuce mu ya dawo ya koma cikin emergency ďin cikin sauri, sannan wata nurse tazo ta wuce tana tura oxygen cylinder sabuwa zuwa cikin ďakin.
Hankalina yayi masifar tashi jikina ya soma rawa kamar ana kaďani, na tashi na futo corridor ďin dake bayan emergency ďin kaina na wani irin sarawa, wani irin mamakon tashin hankali da fargaba suna tsirgamun,
“What if she dies? What if abunda na faďa ne ya bata mata rai ta futa daga hayyacinta? What if ta mutu cikin wannan halin tana fushi dani? What if nayi sanadin ran mahaifiyata ta hanyar amfani da kausasan maganganu a gare ta kai tsaye babu ladabi babu tausasawa? Ina kallon yanda take bani umarni da idanun ta akan kar na sake na faďi abinda nake niyyar faďa amma nayi kamar ban san ma me take nufi ba na zauna na warware mata sirrin da ta daďe tana boyewa in few seconds without thinking ko tana da kwakwkwaran dalilin da ya sanya tayi hakan?
Why didn’t I think with my brain??
Ya Allah!!!”
Durkushewa nayi ina fashewa da wani irin marayan kuka domin babu abinda kwakwalwata take hasko mun sai gawar Mamina ana yi mata sutura, gata nan kwance sai yanda aka yi da ita ta tafi ta barni a duniyar nan da bani da wanda zai maye mun gurbinta.
Ji nayi an dafa ni tare da kokarin mikar dani tsaye! Na mike da saurin gaske domin fargaba da tsoron abinda za’a zo mun da shi!
Sai naci karo da fuskar Ya Mahmud, this time baya kukan da ya saba, sai dai kallo ďaya zaka yi mi shi ka gane tashin hankalin da yake ciki.
“Ya Mahmud me ya faru? Ina Mami na?”
Nayi maganar ďaya bayan ďaya da karyayyen sauti cikin matsanancin tsoron amsar da zai bani……
He looked at me with soo much love and affection….
Sannan ya fara magana a hankali
“Mami will be fine! Doctors are doing their best(Mami zata samu sauki, likitoci suna matukar kokarinsu)”
Zuciyata ta sake karyewa na soma magana hawaye masu zafi na saukowa daga idanuna.
“Ya Mahmud……
Whaaaa…..tttt
Wha……t if…..ma…..Mami die……..s?”
Na haďo kalmomin a tsitsitsinke cikin masifar tashin hankali
“Nice nayi sanadin ta kenan? I’m a bad daughter ko? Nice na saka ta cikin wannan halin! I shouldn’t have broken the news the way I did, da na ji gargaďin da take mun nayi shiru ban faďa ba, kila tana da wani dalilin da ya hana ta faďa.
Da na fara shawara da ita ta bakinta…….”
Na ďago galabaitattun idanuna na kalle shi
“I’m scared Ya Mahmud….
I’m very scared……..”
Na sake fashewa da wani irin kuka, he couldn’t say a word, he just gave me a soothing hug that stopped my entire world for some seconds, then I continued crying on his chest ina jin cewa shikenan na zama marainiya babu uba ba uwa.
It took us time ďin da ban sani ba cikin wannan halin, tun ina kukan matsananci har ya soma yin kasa na koma ajiyar zuciya da hawayen da nake jin ba zasu taba tsayawa nan kusa ba.
A hankali ya ďagoni using his fingers yana goge hawayen da suke kan kuncina ba tare da damuwa da waďanda suke sake saukowa ba.
Sai ga Ya Omar ya leko yana neman mu….his expression said it all.
Yayi mana magana da hannu ya juya cikin sauri, it was then nayi realising cewa Ya Mahmud ne yake supporting ďin tsayuwata da tuni na zube a wajen.
STORY CONTINUES BELOW

Kafafuwa basu da karfin da zasu taka da kansu da bada taimakon kowa ba, so da taimakon shi muka soma tahowa zuwa reception ďin da su Dada suke zaune. Lokacin da muka iso yayi dai dai da lokacin da likitan ya futo yana goge goshin sa da hankici fuskar sa a matukar wahalce.
Ganin ya taho wajen mu ya sanya duk waďanda suke zaune suka mike tsaye, mu kuma da muke tsayen muka sake matsawa ga likitan…
Ya dubi Dada a sanyaye yace
“Ahm! Mama kuyi hakuri ………”
“kuyi hakuri……………”
A ko’ina wannan kalmar me daďin ji ce kuma positive ce banda wajen likita.
Idan likita ya soma da baka hakuri toh lallai ka shiga uku ka lallace!
Don haka iya abinda kunne na ya iya ji kenan wani irin ‘dummm” ya biyo baya.
Wannan kalmar ita ta shiga kaina ta katse mun tunanina ta toshe mun dukkan magudanun jinin jikina ta sarke mun numfashina na tafi luuuuuu sumammiya
Ya Mahmud yayi maza ya tare ni duk da cewa daman da support ďin shi nake a tsayen.
……………………………………………………………….
BAYAN AWANNI SHIDA
Ba ni na farfaďo ba sai misalin karfe goma sha biyu na dare, ina buďe idanuna na saka shi cikin na Ya Mahmud wanda ke zaune gefen gadona akan kujerar roba hannun shi sarke cikin nawa wanda babu drip ďin a jiki.
Na buďe idanuna na rufe na sake buďewa na rufe hoping abubuwan da suka faru su zama mafarki don haka na kasa furta ko kalma guda ďaya ina tsoron yin magana ya gayamun abinda tsoron jin sa ya sumar da ni.
“Zara! Are you ok?”
Yayi maganar a hankali.
Na runtse idanuna ina jin wani irin tsoro da tashin hankali da fargaba tare da fatan na sake komawa unconscious ko na kubuta daga jin abinda nake gujewa ji.
“Zara are you ok? Kina jina? Wake up please Mami is worried about you”
A sukwane na buďe idanuna nayi kokarin tashi zaune a sukwane, shikuma yayi sauri ya mayar dani yana cewa
“Be careful! Take it easy!”
Sai lokacin talalar bakina ta buďe na furzo kalmomin da suke cikin bakina da wani irin speed.
“Ina Mamina? Me ya same ta?”
Sai da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan yace
“Mami is fine Zara! She is doing fine! Ta samu sauki”
Na sake cewa
“Dagaske Mami tana nan? Babu abinda ya same ta?”
Ya girgiza kai yana share hawayen da suma zubo ma sa.
“Mami is alright!”
“Toh tana ina? Ina so na ganta please!”
Ina rufe bakina wata nurse ta buďe kofa ta shigo, Ya Mahmud ya dube ta yana cewa
“Ta tashi! Don Allah cire mata cannula ďin nan muje ta ga Mami sai mu dawo”
Cikin ladabi tace
“Umarnin da Dr ya bani kenan idan ta tashi a kaita Maman ta ta is soo worried about her ko za’a samu jinin ta ya daidaita.”
Da taimakon Nurse da Ya Mahmud na tashi daga gadon suka futa dani zuwa dakin da ke kallon wanda nake ciki, and that was when I realized that ni kaďai ce da Ya Mahmud a can ďin, kowa yana nan ďakin
Ina shiga nayi ido huďu da Mami kwance akan gado fuskarta tass alamun ta dawo hayyacinta.
Bansan lokacin da na fuzge daga rikon su Ya Mahmud ba na tafi gadon na ta a guje na kwanta akanta ina sakin kuka mai ban tausayi wanda ya karyawa mutanen da ke ďakin zuciya aka kacame da share sharen hawaye da shashsheka.
A hankali take shafa kaina tana cewa
“Ya isa Zara I’m fine! Ki kwantar da hankalin ki kinji.. i will be fine”
Sai naji muryarta ta ta zama sabuwa a kunnena kamar ban taba jin ta ba sai yau, kuma kamar kunnena bai taba sauraron wani sauti da ya kai wannan daďi da soothing ba. Hannunta da yake shafa kaina kuwa, jinsa nake yi kamar wani tanti ko lema da yayi protecting duniyata gabaďaya, jikinta da na kwanta kuma, jin sa nake yi the most safest place in the entire universe……..
Kamar wannan moment ďin kada ya wuce kamar mu dauwama a haka har karshen rayuwar mu idan son samu ne ma mai ďaukar rai yazo ya ďauke mu a tare cikin wannan position ďin kuma a tona rami a saka mu tare mu kasance tare har abada…………
This is mother’s love which cannot be compared with anything else a cikin duniyar. It is the purest form of love and the strongest…….a mother’s body is the safest and warmest place of her child….. the love and comfort is just immeasurable!
FIVE DAYS LATER
………………………………..
Kwanakin Mami huďu a asibiti ta samu sauki sosai aka sallame ta! Muna shiga mota Dada ta baiwa Ya Sadik umarni ya wuce da mu Gwarimpa.
Motar tayi tsit! Domin fuskantar da muka yi cewa Dadan tana nufin dawo da Mami gabanta kenan!
Muna isa muka tarar Baba Rabi ta gyara ďakin da yayi saura a cikin falon namu, an shirya komai tsab sai kamshi yake yi, cikin shi Mami ta zauna. Washegari ni da A.laila muka je muka ďebo mata kayan da zata yi amfani da su na wani lokaci sannan muka kulle ko’ina muka sallami masu aikin gidan a bisa umarnin Dada.
Da yammacin ranar sai ga Daddy, saukar shi kenan daga London ko hutawa bai yi ba. Na fahimci zafin da ya ďauka har yafi na Dada domin rantsuwa yayi da ransa akan sai Alhaji Mukhtar ya biya bashin zaluncin da yayi wa Mami, ko abincin da aka wuni ana shirya mi shi bai kalla ba ya tafi…
A maimakon jimami sai gidan namu yayi wani masifar daďi, dukanmu parlour muke futowa mu zauna a dinga raha ana hira, musamman da yamma idan Ya Omar da Ya Sadik sun taso daga aiki sun yada zango anan, most of the time da Ya Mahmud wani lokacin har da Faisal suna shigowa, sai muke ďebewa Mami kewa sosai ya zama ko lokacin damuwa bata da shi, we treat her kamar kwai a gidan nan, a ďakinta nake kwana tunda ta dawo a kwakwume a jikinta, tun tana faďa tana korata saboda Dada har ta gaji ta hakura don ko na tafi idan tayi bacci sai na lalubo na dawo, karfe huďu kuma take tashi tayi ibadarta, sai take tashi na nima muyi tare, sai munyi sallar asuba munyi azkars sai na gaishe ta sannan na koma ďakina nayi baccin safe a can, kafin mu tashi Baba Rabi ta haďa breakfast mai rai da lafiya, A.laila tayi wa Asad da Amal wanka, Ya Nuratu ta shirya Amal ta shirya itama, Dada na futowa duk sai mu futo mu haďu a tsakiyar falon mu karya tare cikin farin ciki. Bayan mun kammala yawanci bama tashi daga wajen sai azahar, sai kowa yayi abubuwan da suke gaban shi a ciki, bamu cika yin lunch tare ba wanda zai ci zai je ya ďiba yaci abinsa.
sai wajen 5pm zamu kuma haďuwa a falon, anan ýan mazan suke shigowa su same mu, sai magrib ake tashi, bayan sallar isha’i a sake zama ayi dinner wani lokacin har da su, wani lokacin kuma basa zama sai suyi sallama su tafi, wani lokacin kuma sai daren suke shigowa.+
But abinda na lura these days, Ya Mahmud gabaďaya ba shi da walwala kuma ba shi da kuzari.
Yayi wani sanyi kalau, da nayi tunanin case ďin Mami ne amma daga baya sai na fahimci there is something else.
Imamu har yanzu bai dawo ba, kuma har yanzu bai gaya mun a wanne gari yake ba da abinda yaje yi, the guy is unpredictable and complicated don ni tsoro ma yake bani da al’amuran shi masu ban mamaki.
………………………………………………………………
Weekend ne yau, tun da nayi sallar azahar na koma na kwanta a gadona ina tunanin rayuwa, musamman auren mu da Ya Mahmud wanda aka yi sati biyu da kwana huďu da ďaurawa, yanda maganar auren ta shigo da yanda komai ya faru.
maganar sabon bikin da Daddy yace zai yi ba’a sake tada ita ba kuma ni bansan stand ďina ba, ina zamu zauna? Yaushe? Menene shiri na gaba duka bansani ba.
Sai naji ina kewar school sosai, tare muka fara da Ihsan gashi ita saura watanni ta kammala ni ina walagigi bansan makomata ba, which makes me feel soo sad.
Na sake juyawa akan gadon ina tunani wayata ta shigo, na ďauka cikin sanyi na kara a kunnena ba tare da magana ba.
“Zara get ready, by 4 zan futo, zan fara ajiye Amani a gida sai nazo na ďauke ki! Please don’t waste my time”
Ihsan ce! Sai lokacin na tuna da bikin course mate ďin mu Neerah! Gabaďaya na manta kuma bani da sha’awar futa ko ďaya, amma kuma yarinyar tana da mutunci, ko da bana school ďin bata daina zumunci da ni ba, har gidanmu tana zuwa lokaci lokaci don haka ba zaiyu naki zuwa bikinta ba, tunda har asoebi ta kawo mun siya mun ďinka, bikin nata was supposed to be kafin nawa bikin sai aka yi musu mutuwa aka ďaga.
“I will be ready on time insha Allah”
Daga nan muka ajiye, naci gaba da tunanina inajin ba daďi, ban aune ba naji ana kiran sallar la’asar!
Da sauri na mike nayi toilet na watsa ruwa tare da alwala nazo nayi sallah sannan na koma gaban mudubi na shafa mai, na kwance gashina na taje nayi oiling ďin shi na haďe shi cikin band daga can kasan wuyana ya cure kamar alkaki.
STORY CONTINUES BELOW

Na gyara fuskata da soft make up sannan na shirya cikin atamfar kamun embellished wax wax ruwan toka mai blue da ratsin fari, ďinkin nawa very stylish, fitted gown ce aka yi mata ado da wani irin yadi fari mai gashi a jiki, pattern ďin kuma duka handwork aka bi su da shi na farin beads.
Na dankara English gold ďina mai shake wuya, na karya ďankwali ya zauna daram sannan na feshe jikina da sassanyan turarena “smokey rose” na “body shop” Ina yaba kyawun da shigar tayi mun.
Daga takalmina har jaka ýan gidan Gucci ne duka silver sai gyale royal blue kalar jikin atamfar da yafi kowanne yawa a jiki. Na haďa tarkacen abubuwan da nake bukata na zuba a jakar sannan na kullo ďakin na futo.
Da Ya Mahmud na fara yin tozali a falon yana zaune gaban Mami yana bare mata lemon fata, tsakiyar falon baja baja da kayan marmari da lemuka, kowa ya hallara a falon, Asad na mika hannu na ďauka a hannun Ya Nuratu sannan na wuce gaban Dada na zauna ina cewa
“Barka da yamma Dada!”
Cikin murmushi ta amsa
Sannan na juya na gayar da Ya Mahmud casually ya amsa yana kallona, da alama mamakin kwalliyar da naci yake yi domin tun bayan bikina ban sake yin irinta ba.
Na juya gasu Ya Omar da Ya Sadik duk muka gaisa cikin raha da farin ciki tare da tambayar iyalin su
“Futa zaki yi ne?”
Cewar Ya Omar yana kallon jakar hannuna.
Na ďan gyara zama nace
“Biki zan je”
A.laila ta kalle ni sama da kasa tace
“Bikin wa?”
Nace
“Friend ďina ce”
“Wacece friend din ki?”
Cikin rashin damuwa nace
“Neerah! Don ba zaki gane ta bane, amma tazo gidan nan sau biyu kina nan”
Ta sake cewa
“Ke da wa zaki tafi?”
Ahhh. Wannan tambaya kamar wani sabon abu ne zuwa biki? Nayi maganar a raina, kafin na bata amsa sai ga sallamar Ihsan, ta shigo cikin irin kayan jikina amma ita fitted bou bou aka yi mata, tayi masifar kyau cikin shigar.
Cikin far’a aka amsa mata sallamar ta sannan ta shiga gaidasu Dada cike da ladabi, ta zauna gefena ta amshi Asad a hannuna tana yi mi shi wasa.
“Ke da kika ce 4 zaki futo, kalli agogo almost 6 kin shanyani”
Murmshi tayi tace
“Wallahi mantawa nayi ban gaya wa Faisal zan futa ba, kuma wayar shi a kashe, har ma zan kira ki nace ki tafi sai kuma ya dawo! Sorry! Ai nasan karshen ta ma ba’a fara ba.”
Na mike ina gyara zaman ďan siririn mayafin jikina wanda bai boye komai na kwalliyar tawa ba sannan na mika hannu na karbi Asad na mayar da shi wajen Ya Nuratu ina cewa
“Ko na tafi da kai ne baby? Kaima kasha iskar duniya….”
A.laila tace
“Toh ko zaki gwada, askarawan Riyad na nan suna jiranki”
Nayi dariya na soma yi musu sallama. Nazo tsakiyar falon naji Dada ta kira sunana a nutse.
A ladabce na juyo ina amsawa.
“Da izinin wa zaki futa?”
Dum! Dum!! Dum!!!
Ji nayi kirjina ya wani buga, hantar cikina ta kulle! Sai lokacin wani sense ya shige ni, wallahi na manta ban futo na tambaya ba, ni nama manta sai nazo na fara gayawa Dada zan je wani wuri kafin naje na shirya. Toh ai na daďe ne rabona da irin waďannan fuce fucen na karan kaina, kullum ina gida, idan kuma futar ta kama bani kaďai bace.
Jiki babu kwari na koma gaban Dada na durkusa a sanyaye nace
“Don Allah afuwan Dada! Wallahi tallahi na manta ne, shima bikin gabaďaya ban tuna da shi ba sai da Ihsan tayi kirana tace na shirya gata nan tahowa…! Kiyi hakuri Dada”
Wani kallo Dada tayi mun irin wanda ita kaďai na sani da irin shi a duniya, idan tayi maka shi sai kaji kamar kace kasa ta buďe ka shige ta boye ka don tsoron abinda zai biyo bayan shi.
Ta sake watso mun tambayar da ta daďan ruďani.
“Kin nemi izinin mijin ki?”
Tashin hankali! Nan na sake yin tsuru tsuru ina satar kallon Ya Mahmud wanda ya haďe girar sama da ta kasa yana shan lemon da ya bare musu wanda kana ganin yanayin yanda yake shan ka san ba daďin shi yake ji ba”
“Ba magana nake miki ba?”
Ta faďa a kausashe!
Ni dai sunkuyar da kaina kawai nayi jikina yana rawa ina danasanin shirin zuwa wannan biki.
Ta dubi Ya Mahmud tace
“Ko ta tambaye ka zata futa?”
Sai ya sukuyar da kansa bai ce komai ba.
“Da izinin wa zaki futa?”
Ta sake tambaya ta kamar zata rufeni da duka.
Tuni hawaye ya taru a idona! Rabon da Dada tayi mun irin wannan ďaga muryar har na manta, tunda nagane ta kanta na daina bari sabanin da zai sa tayi mun irin wannan faďan nata ya shiga tsakanin mu. Saboda tsawar Dada da faďanta da hararar ta sun fi bulala azaba da raďaďi. Idan ran Dada ya baci kai kan ka da ba kai kayi laifin ba tsoro kake ji balle kuma wanda yayi mata laifin.
“Irin tarbiyyar da na baki kenan? A ina kika ji labarin matar aure tana futa ba tare da izinin mijin ta ba? Yanzu ba a gabanki kawar ki tace ta kusa fasa futar saboda bata samu wayar mijinta ba? Ke naki mijin raina shi kika yi ko kuwa auren naki ne baki ďauke shi a matsayin aure ba? Ba dake nake magana ba?
A ina kika koyi wannan ďabi’ar? A ina kima samo wannan halin? Waye yayi miki wannan huďubar don uwarki?
Haka kika ga ana yi? Kawai ki tashi ki shirya tsilli tsilli kisa kafa ki futa inda ran ki yake so ba tare da izinin kowa ba saboda kin isa?
Wacece ke? Me kike ji da shi? Don uwarki har da uban naki a ina kika ga yanda ake raina miji? Ko kuwa don kinga mun zuba miki ido kina zaune a gida bamu yi komai akan tarewar ki ba shine kika maida auren shiririta?
Waye sa’an wasan ki? Mu ne ko kuwa shi Mahmud ďin? Shi zaki raina saboda kina ganin shi kullum? Idan banda rufin asirin Allah ke kin isa ki aure shi? Nace kin isa ki aure shi? Ko babu darajar aure wacce girmamawa ce bai cancanta a wajen ki ba? Shi baki ga yanda yake mana ba? Da girman nan na shi da ilmi da duk abubuwan da ke baki da su bai taba tafiya bai bugawa uwarsa waya ya nemi izininta yayi mata sallama ba, bai taba yin gaban kan shi ba tare da shawarar iyayen shi ba! Sai ke zaki zo mana da wani iskancin banza?………”
Na taba gaya muku Faďan Dada yafi bulala zafi? Na taba gaya muku idan Dada tana yi ma faďa sai taci maka mutuncin da zaka ji ka naked a gaban mutane? Tsokano bacin ran Dada is like playing around fire. Idan ta fara zayyano maka tijara har iyayenka ba zasu tsira ba.
Haka ta dinga faďan nan ta inda ta shiga ba tanan take futa ba tun karfe shida da minti goma sai bakwai saura kwata da aka soma kiran sallar magriba,
Sai da ta zageni tatas, sai da gwammace duka mazan falon ta baiwa darbejiya tace suyi ya zabgamun, sai da naji ina ma ban san wata Neera ba balle bikinta ya tashi nayi shishshigin zuwa.
“Tashi kije ki ba shi hakuri”
Ta faďa cikin sautin bada umarni.