HAUWA CHAPTER A
KANO+
Kallonta ya yi tare da girgiza kai cike da takaici ya ce “Haba Hauwa, ya za ki shigo Parlo haka ko Sallama babu? Cike da rashin kunya ta ce “ban iya ba”.
Bai ce komai ba, ya maida idanuwansa ga TV.
Jim kaɗan, Uncle Ahmad ya shigo ɗakin, jiki na rawa na zaunen ya miƙe tsaye ya karɓo Jakar hannunshi tare da cewa. “Barka da fitowa” cike da murmushi ya ce “ZAID kenan”.
Wanda aka kira da Zaid ya murmusa.
“Daddy Ina kwana?”
Uncle Ahmad ya kalli tilon ɗiyarshi ya ce “Hawwa, kin tashi lafiya?”.
Murmushi ta yi a taƙaice ta ce “Eh”.
“Makaranta fa?”
“Daddy ba zan je ba”
Ba tare da damuwa ba ya ce “kira mini Mummynki”.
Da shagwaba irin na sangartattun ‘Ya’ya ta miƙe ta shige cikin gida.
Jim kaɗan sai gashi sun dawo tare.
Matar ɗauke da murmushi tana mai kallon Maigidanta ta ce “har ka fito?”.
Ya amsa mata da “Eh, mun fito”.
Zaid ya ce “Ina kwana Aunty”.
Ba tare da ta kalle shi ba ta amsa tare da maida hankalinta ga Maigidanta.
Uncle Ahmad ya ce “Ku yi buɗa baki yau da Zaid, shi ma yana Azumi.”
Ɗan basarwa ta yi kafin ta ce “Za a yi”.
Uncle Ahmad ya ce “To mun wuce”
Ta ce “Sai ka dawo Allah ya bada Sa’a”.
Daddy “bye-bye”.2
Haka suka jera suka fita garage wurin parking motocin gidan, Zaid ya buɗe ma Uncle ƙofar Mota mai ƙirar High Lander, kafin ya zagaya ya shiga kujerar Driver ya ja motar, Maigadi ya buɗe suka bar gidan.
NASSARAWA
21/03/2015
Dariyar ƙeta kawai take yi. Dariyar har ya soma ƙular da ita. Tsaki ta buga ta ce “Dagaske Aisha ba zan sake gaya miki abu ba”.
Da ƙyar Aishar ta iya tsaida dariyarta ta ce “Yi haƙuri WATTY, na bari, rainin wayau ɗinne ya ba ni dariya, don ya raina mutane, ina ake wa Namiji Auren dole?”.
Watty ta ce “rabu da ɗan borin kunyan, Allah ni ba son shi nake ba, amma don ya rainani zai ce min Babanshi ya zaɓar mishi Mata, ɗiyar Abokinshi ce, shi ba ya sonta, waye-waye ɗin shi, yen-yen-yen, na ce to kana Namiji ya za a maka Auren Dole? Wai ai biyayya yake yi, can you Imagine? Mtsw, da Son shi nake da na kamu da hawan Jini.”
Aisha ta gumtse dariya ta ce “to wai sai cewa kike ba son shi kike ba, meyasa kike ta nanata maganar tun ɗazun ? Hmm, ke dai kawai an kasa ki”.
Watty ta wurga ma ta Harara ta ce “Za ki ga wanda zai sake baki labari” ta fincike hanunta.
Aisha ta guntse dariya ta ce “Ki yi haƙuri Sis”.
Banza ta yi ta ƙyaleta.
Sake kamo hanunta ta yi ta ce “Hauwati”
Kai ta rausayar ɗayan gefen.
“Haba Watty, meye abun fushi? Ko dai duk Kishi ne saurayi zai yi aure? Shi ne za ki huce kaina?”.
Hararrata ta yi ta ce “ke dai kika sani, ni ce ma na biye miki”.
Cike da zolaya Aisha ta ce “Dama mai za ki yi da wannan duna black ɗin? Ke da kike da saurayi Ready Made, son kowa ƙin wanda ya rasa?”.
Ba ta san murmushi ya bayyana a fuskarta ba, amma ta ɗan basar ta ce “Wa?”.
Aisha ta ce “Ya Bu mana”.
Hauwaty ta ɗan lumshe ido kafin ta buɗe ta ce “wai so nawa zan gaya muku ba soyayya muke ba?”
Aisha ta miƙe tare da ɗaga kafaɗa ta ce “Oho, rana bata ƙarya, ke ni na tafi gidan Inna.”
Watty ta ce “mu je tare”.1
KANO
Shigowa ta yi ta gansu kan Table suna Buɗa Baki, wuce su ta yi.
Ya san ba za ta ba, amma ƙila ya ci sa’a taje saboda idon Babanta.
Murya can ƙasa ya ce “Hawwa don Allah ɗauko min ruwan da bai da sanyi.”
Banza ta yi ta ƙyale shi, shiru ya yi daga inda yake yana kallonta.
Uncle Ahmad ya buɗe baki a kausashe ya ce “Hawwa!”
Baki ta turo ta ce “Daddy kallo fa nake yi”.
Baban ya ce “Hauwa tashi ki ɗauko mai ruwa marar sanyi”.
Tashi ta yi rai na ƙuna tana bubbuga ƙafa ta nufi kitchen tana ƙunƙuni.
“Shi mutum gurgu ne da ba zai iya zuwa da ƙafarshi ba? Ba dama a ga mutum zaune haka za a dinga takura mishi, gwara ma mutum ya zo ya tafi Gidansu.”
Murmushi mai ciwo Zaid ya yi, da alama Baban bai yi mamakin kalamanta ba, suka ci gaba da buɗa bakinsu, ta kawo ruwan ta dankwafar mai a gabanshi.
Daddy ya ce “Good Girl”.
Turo baki ta yi ta wuce cikin Parlo.
Daga Sallar Isha’i Zaid ya wuce gidansu bayan sunyi sallama da Uncle Ahmad da niyyar gobe zai fito da Safe.1
STORY CONTINUES BELOW

Da Sallama ya shiga Gidan, ba wuta, babu mai a Generator. A zaune ya iske ‘yan gidan a tsakar gida kan Tabarma.
“Ya dai, Gen ɗin ya buga ne?”.
Yayanshi Fahad ya ce “Petrol zan siyo Mama ta ce a bari sai gobe tunda Tara ta kusa”.
Wuri ya samu kusa da ƙanwarshi Batool.
Mama ta ce “Barka da shan ruwa Zaidu, fatan ka cika cikinka Gidan Uncle Ahmad ɗin”.
Kafin ya yi magana ya ji Batula na cewa “Barka da safiya, barka da yamma, Ina zan kai ka, barin share ma zufa Uncle”.
Kallonta ya yi, ya ga a tsaye take tana durkusa kamar tana gaida Sarki.
Yaya Fahad ya tuntsire da dariya, Amina da Baffa suka taya shi.
Hakan ya sa Batul ƙara ƙaimi wurin abunda take yi.
“Uncle na maka Firfita?” Dariya suka fashe da har Mama sai da ta Dara.
Kwaikwayon wani takeyi, Shi take kwaikwayo, shi suke ma tsiya, ya saba jin irin tsiyar da ‘Yan uwanshi ke mishi, ba su tashi mai irin haka sai randa ya yini tare da Uncle Ahmad.
Wai haka yake yi in ya ga Uncle Ahmad, a cewarsu in yana gaban Uncle Jikinshi rawa yake yi, wai harta Takalma in Uncle Ahmad zai sa, sai Zaid ya gyara mai tsayuwarsu a ƙafar shi ya saka Handky ya goge, a cewarsu fa.
Zaid ya murmusa ya ce “ku dai kuka sani, ko zubewa na yi ƙasa ya bi ta kaina ban faɗi ba, ƙanin Babana ne”.
Wani abu Batul tayi wanda ya saka su tuntsirewa da dariya.
Zaid ya girgiza kai ya tashi ya yi hanyar cikin Gida yana faɗin “ba zan biye muku ba”.
N A S S A R A W A
Watty ta kalli Kakarta ta ce “Inna da gaske Ya Bu ba so na yake yi ba”.
Inna ta ce “to ni me ya sa ya ce min kun ruga da kun haɗe kanku?”.
Watty ta ce “Ni Inna Wallahi ban sani ba, ƙila don kar da ku matsa mi shi kan sai ya yi aure ne”.
Inna ta ce “Ke Hauwaty ki fita Ido na, ko da ya ke, zai zo hutun ƙarshen mako, zan turke ku tare”.
Watty ta yi dariya ta ce “na yarda Wallahi”.
Saƙe-Saƙe zuciyarta ta fara. ‘Amma idan na samu Ya Bu a matsayin Miji ai na warke.’
‘Ya haɗu iya haɗuwa’
Da wannan tunanin ta isa ɗakin Mamarta. Zaune ta ganta tana cin Tuwo.
Zama ta yi kusa da ƙafarta.
“Sannu Mama”.
“Yauwa Watty, wai na tambayeki mana?”.
“Eh Mama”.
Mamar ta haɗiye lomar Tuwon ta ce “Me ya sa kike ɓoye mini abu a matsayina na mahaifiyarki, me ya sa ba kya gaya mini gaskiyar lamarinki?”.
Cike da rashin fahimta take kallon Mahaifiyarta.
“Mama ban gane ba?”.
“Hmm, Watty ke nan, ba tun yau na ke ji a cikin gida wai soyayya kuke da Abu, har Inna ta ce za a yi bikin ku bayan Sallah, ban san soyayyar ta yi ƙamari har haka ba, har ake maganar aure, magana har ta karaɗe dangi”.
Watty ta zaro ido cike da mamaki ta ce “Wallahi Allah Mama ban sani ba, ni ban taɓa tsayuwa da Ya Bu ba da sunan wai zance, Mama ki yarda da ni wallahi, ni ban san me ya sa yake ce ma mutane soyayya muke ba”.
Mama ta taɓe baki, ba wai don ta yarda ba ta ce “shi ke nan”.
Watty ta shige cikin ɗaki, haushi ya kamata, a kan me Ya Bu zai ta gaya ma dangi ƙarya? A kan me zai ce Soyayya suke alhalin ba ita suke ba, aurenta bayan sallah? To da izinin wa? Lallai, dole ta kira shi a waya, dole ta roƙe shi kan ya dai na cewa mutane soyayya suke, alhalin ba shi suke yi ba, gashi har mamarta mahaifiya ta yarda.
Can gindin window ta matsa, ta latso number Ya Bu.
Kira na biyu ya ɗauka.
“Hello”.
Shiru tayi ta kasa magana.
Cikin wani murdadden murya yace “Little, kina jina?”.
Ajiyar Zuciya ta sauke tace “Ya Bu ina wuni?”.
“Lafiya kalau” ya amsata “ya ‘yan Gidan?”.
“Alhamdulilah”.
Shiru ya biyo baya.
Yace “Yadai?”
Kwarjini ya mata kamar yana gabanta.
“Ehen, Ina jinki”.
“Uhm, wai dama a nan Gida ne a ke cewa wai Soyayya mukeyi”.
Yace “Toufa! Su ‘yan Gidan suke cewa haka?”.
Baki na rawa tace “eh haka suke cewa”.
Yace “kuma ba haka bane ba ko?”.
Tace “Eh mana”.
Yace “to bari na zo Gidan on Friday sai mu hadu tare mu ce musu ba Soyyaya mukeyi ba, kin yarda?”.
Tace “eh na yarda Wallahi”.
Yace “to my little take care kinji?”.
Lumshe Ido tayi ta bude tace “Bye-Bye”.
Ta katse Wayar.
Ba ta san Dalilin da ke sa Kirjinta bugawa a duk lokacin da take magana da Ya Bu.
A fili tace “Ya Abu, Ya Bu”.