HEEDAYA CHAPTER 18 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 18 BY By Khaleesat Haiydar

Har suka isa train station din bbu wanda yace komai cikin motar, Abba yyi parking duk suka sauka suka shiga ciki 

with their luggages, shi dai Junaid na rike da hannun Heedayah, Abba bai bar tashan ba kuma sai da ya ga tashin 

train dinsu xuwa Abuja…. Kasancewar sai tara na dare flight din nasu na Qatar airways xai tashi kamar yanda aka 

sanar masu bayan sun je airport din, hotel kawai Junaid ya kama masu kusa da Airport din, Bayan Azahar Mami ta 

idar da sllh ta shirya xata tafi gun step sister dinta da ke nan garin Abuja, shigowar Junaid kenan daga masallaci 

yana kallonta yace “Ina xa ku Mami?” Tace “Xan je gidan Asiya ne in dawo yanxu” yace “Ohk…” Mami ta ajiye ma 

Heedayah dake xaune saman gadon hotel din takalminta ta kamo hannunta tace “Sauka ki sa takalmin ki” Heedayah 

tace “Mami da Yaya xa mu je?” Mami tace “Aa ina ruwanki da wani Yaya” Tace “Mami mu je da shi plss” Mami ta 

saka mata hijab dinta tana rike da hannunta ta nufi kofa tace “Sai mun dawo” junaid ya bi su da ido, sai kuma yace 

“Mami ko xa ki bar ta ki je ki dawo” Mami ta juya tana kallonsa tace “For what reason?” Da sauri yace “No naga

kamar bata son tafiya ne” Wani kallo tayi masa ta bude kofar ta fita, Heedayah dai kamar xata yi kuka take bin 

Mami…. Har la’asar Mami na gidan yar uwarta da Heedayah suna hiran yaushe gamo, Hajiya Asiya na kallon yar 

uwarta tace “To amma me yasa ba ku taho tare da Junaid ba? Mun kwana biyu ba mu hadu ba” Mami tace “Muna 

sauka daxu da safe yace min xai je gidan kawunsa so bna son ya kasance bai je ba, but in dai ta nan xa mu dawo xai 

xo gun ki in sha Allah….” Hajiya Asiya tace “Toh shkkn, Allah ya kai ku lfya ya dawo da ku lfya, ita kuma wannan 

yarinya Allah ya sa ayi aikin a sa’a” Mami ta amsa da “Ameen” karfe shidda saura Mami suka bar gidan, babu yanda 

Hajiya Asiya bata yi ba su tafi da abinci hotel din Mami ta ki amsa, Hajiya Asiya ta sa driver dinta ya sauke su hotel 

din nasu. Karfe tara da few minutes na dare jirginsu Mami yyi take off direct xuwa kasar India without stopovers,tafiyar kusan awa tara da minti arba’in da takwas, kafin tashinsu kuma sai da Mami ta tabbatar ta kira Abba ta sanar 

masa xa su tashin yayi masu addu’a yyi wishing dinsu smooth trip…. Tare Junaid da Heedayah suka xauna a jirgin, 

Heedayah na laluba hannunsa tace “Yaya me yasa Abba bai biyo mu ba” Junaid yace “He is very busy” tace “To 

kaka fa?” Yace “She’s old to journey with us” tace “To ya Sudais fa?” Yace “Shi ma he is busy amma xai xo….” 

Heedayah tayi shiru sai kuma tace “Dama bana son Shureen ya biyo mu” Murmushi yyi yace “Why?” Ta girgixa kai 

tace “Bana son sa” Junaid yace “Don’t tell anybody that” Tace “Why?” Ya ja hancinta ya kwantar da ita jikinsa yace 

“Sleep Lolly….” Lumshe ido tayi nan da nan kuma bacci ya dauketa throughout the rest of the journey. Bakwai saura 

na safiya Jirginsu ya sauka Indira Gandhi international airport new Delhi, Amma sai karfe goma saura suka shiga 

Indraprastha Apollo Hospitals da xa ayi ma Heedayah aiki, don sai da suka fara sauka hotel dake nan kusa da 

hospital din suka huta, Bbu bata lkci aka yi admitting din su a babban asibitin a ward dinsu su kadai, ba laifi ward 

din na da d’an girma, amma kana gani kasan dai kudi ne kawai aka kashe ba kadan ba…. Kamar yanda Abba yayi 

tunani haka ne don sun daura Heedayah kan allurai na sati daya, sai kuma some diet da aka daura ta kai, Likitar dake 

ma Mami bayani a office dinta da harshen turanci ta sanar ma Mami irin Disorder din Heedayah da ake kira da 

Congenital Blindness, sannan ta sanar mata Novel Gene therapy xa ayi mata to correct the disorder, probably 

through luxturna, Mami da duk jikinta yyi sanyi tace “But is there much chances of her gaining her sight?” Likitan 

tace “Hopefully, though it’s a rare disorder but we will try our best” Mami tayi ma likitan godiya ta mike ta fita 

office din ta koma ward dinsu. A kwanaki bakwan nan Mami kusan kullum sai ta tashi sllhn dare tayi addu’ar Allah 

ya sa ayi nasara a aikin da xa ayi, har ranta take tausayin Heedayah take kuma fatan Allah ya bude mata idanuwanta, 

bata san yanda xata ji ba idan aka yi aikin nan Heedayah bata yi gaining sight dinta ba, she can’t just imagine that, a 

hotel din da suka fara sauka na kusa da hospital din Junaid ke kwana, amma throughout the day yana asibitin tare da 

Heedayah da Maminsa, sai dai kawai ya fita ya siyo masu Nigerian dishes safe rana da daddare, ko kuma ya fita 

xuwa yin sllh… A kullum sai Abba ya kira ya sa a ba Heedayah waya sun yi magana, complain dinta kuwa a ko da 

yaushe shine idonta suna mata ciwo, don a hankali fararen idanuwanta masu kyau suka fara sauya kala xuwa ja 

kuma tayi ta sosa su, Sudais ma kusan kullum sai ya kira Mami ta ba Heedayah sun yi magana, ana haka har suka 

cika kwana goma cif a asibitin ya rage kwana biyu a shigar da Heedayah theatre…. Junaid na xaune tare da Mami 

ana gobe xa ayi operation din wayarsa ya fara ring, dauka yyi saman table dake kusa da shi yana kallon screen din 

dake nuna masa Beauty, to waye haka? ya dau lkci yana tunanin waye yyi ma saving da haka, sai kuma ya daga 

kafin ya katse ya kai kunne, Daga daya bangaren aka yi sallama cikin siririn murya, sai bayan kusan second biyar ya 

dau muryar ya amsa sallaman, Salima tace “Haba Jayyy shine bbu ko sallama kayi tafiyar ka India, to gani a new 

Delhi din nima, yanxun nan jirginmu ya sauka daga Nigeria wllh” junaid ya d’an yi shiru da mamaki, can dai yace 

“Ke da wa kika xo new Delhi?” Tace “Wllh wani saurayi na ne ya xo business trip shine kawai yace in rakosa, a 

hotel din kusa da Airport xa mu sauka ynxu…. Ku kuna wani asibitin ne?” Yace “Toh ki huta tukun xa mu yi waya” 

tace “Toh shkkn Jay, sai anjima dama duk na gaji, wanka xan yi ma yanxu” Yace “Alright” daga haka ya katse 

wayarsa, Mami na kallonsa tace “Wacece?” Ya kalleta da sauri sai kuma yace “Ohk wata coursemate dita ce from 

Nigeria….” Mami tace “Ya aka yi tasan kana India?” Yace “I told her I will be coming to India tun last week” 

Mikewa yayi ganin Heedayah xata sauko saman gadon ya nufeta yace “What happened?” Tace “I want to ease my 

self” Tashi Mami tayi ta kama hannunta xuwa toilet dake ward din. Washegari da asuba aka shigar da Heedayah 

theater, a asibitin Junaid ya kwana ranan, coz shi ma he is so tensed, he just don’t want to imagine the operation 

won’t be successful, haka ma Maminsa da bata yi wani bacci daren ranan ba, ita kanta Heedayah duk son baccinta 

bata yi baccin ba daren don idon na damunta sosai, Mami taji tausayinta ba kadan ba, har karfe goma na safiyan 

Mami na xaune saman darduma hannunta rike da carbi, Junaid yace “Mami baki yi breakfast ba, pls take something” 

Tace “Toh” Tea ya hada mata a cup ya mika mata ta amsa, Mami bata wani sha shayin ba ta fita ta xauna saman 

kujeran dake jere gaban theatre din da aka shigar da Heedayah…. Karfe sha biyu likitoci biyu suka fito theater din 

sanye da gown din operation, Mikewa Mami tayi wanting to hear something from them, da turanci daya likitan yace 

mata ta kwantar da hankalinta all will be well, daga haka ya wuce, Mami ta koma a hankali xauna, bayan minti 

talatin wasu likitocin uku suka fito su ma din dai haka suka ce mata, ita dai gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya, 

daga karshe nurse biyu suka fito, Mami ta kara tashi ta nufesu, su ma dai xancen daya ne suka yi wucewarsu. Sae 

kusan azahar aka kai Heedayah ward dinta tana bacci, Mami na xaune kusa da ita sai kallonta take an rufe mata 

idanuwanta da white eye pads, gaba daya she is disturbed and tensed, Junaid dai na tsaye daga gefen gadon ya 

rungume hannunsa shi ma yana kallonta, wayar Mami ya fara ring ta dauka ganin Abba ne ta daga a sanyaye ta kai 

kunne, gaisawa suka yi tace “Yanxu aka fito da ita, but akwai eye pads a idanuwan….” Daga daya bangaren Abba 

yace “Toh Allah ya sa an dace, can I speak to her now?” Mami tace “Bacci take” Abba yace “Toh I will call back 

later” daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar tana kallon junaid tace “Toh baccin me take haka, ko anaesthesia da 

aka yi mata ne?” Yace “No, anaesthesia din da aka yi mata iya aikinsa bangaren idon, she is not unconscious bacci 

take” Mami tayi shiru bata ce komai ba…. Har karfe hudu na yamma Heedayah bata farka ba, Junaid ya tafi yyi sllh 

ya dawo ya tadda Mami na sallahn ita ma, ya xauna kusa da Heedayah ya kamo hannunta yana kallonta ganin sai motsi take, a hankali cikin rawar murya ya ji tace “Mami idona na min ciwo” Ya dafa goshinta still holding her 

hands tight yace “Xai daina dear….” Ganin xata mike xaune ya dagata ta xauna ta kai daya hannunta idonta, da sauri 

ya rike hannun ganin cire pads din take son yi yace “Noo don’t….” Ta fashe da matsanancin kuka xata kwace 

hannunta tace “It’s paining me” ya ki sake hannun yace “Zanyi tafiyata in bar ki ke kadai a nan if you don’t stay still 

now….” Ganin kukan da take ya rungumeta yace “Toh yi hakuri xa a cire maki yanxu, ki daina kukan, I will call the 

doctor now” cikin rawan murya tace “Yana min xafi sosai” Mami na idar da sllh dama fita tayi kiran likita don yace 

idan ta tashi a sanar masa, yana shigowa allurai biyu yyi mata ya sa mata drip ya fita… Ba a dau lkci ba kuma tayi 

bacci junaid na rike da ita har sannan, Mami ta sake komawa gun likitan don jin abinda ake ciki, nan ya sanar mata 

nan da kwana uku xa a cire eye pads din a duba idon with hope that tayi gaining sight dinta clearly, kafin kwana 

ukun kuma xa ayi ta mata injections xa kuma ta dinga shan magunguna, Mami tace “But is there nothing to do about 

the pain pls?” Yace “The pain will subside before tomorrow….” Mami tace “Are you giving me hope that the 

operation is successful Doctor?” Likitan ya girgixa kai yace “We are also hoping it’s successful, but if it’s not, then 

we will try anoda operation…. The last” Mami ta kasa ce masa komai, can ta mike tayi masa godiya a sanyaye ta fita. 

Tana komawa ward din Junaid ya kwantar da Heedayah ya mike yace “Xan je in dawo yanxu Mami” Mami tace “Ina 

xa ka?” Yace “I want to get something, ba dadewa xan yi ba” tace “Ohk, ka siyo fresh milk when coming back” yace 

“Toh” daga haka ya fita, nan kuwa tun safe Salima ta ishesa da kira shine yyi deciding kawai ya tafi ya sameta inda 

tace masa take ko xata daina kiransa. Yana tsaya gaban hotel din ya kirata, tana dagawa yace “Ina waje ki fito” tace 

“Haba ka shigo ka jirani a reception mana Jayy…” Yace “But I can’t come in, ki daure dai ki fito Ina sauri ne” tace 

“Wllh tun safe kai na ke ciwo a kwance ma nake ynxu, bbu ynda Suraj bai yi in raka ba na ki fita, ka daure ka karaso 

ko reception ne plss Jayy” yace “Alright” daga haka ya katse wayar ya shiga cikin babban hotel din, Yana reception 

din ya kirata, sae ga ta ta sakko sanye da riga da wando sai black veil da ta daura a kai, shi duk wayar da suke ya 

kasa yrda da gaske tana India sai ynxu da ya ganta, ta sakar masa murmushi tace “Welcome, mu shiga ciki in daura 

after dress mu tafi hospital din, tun safe na damu Ina son xuwa wllh” yace “Aa ba a barin mutane fiye da biyu and 

yau ba visiting day bane” lkci daya mood dinta ya canxa tace “To yaushe ne visiting day din?” Yace “Nan da 3 days” 

Ta tabe baki tace “Toh mu je ciki” yace “No, na gaisheki, xan koma ynxu coz I need to get them food” Ta marairaice 

tace “Haba Jayyy, ae ba cewa nayi ka shiga ka dade ba, kawai mu je kaga Inda nake, ni fa bbu wanda yasan ma na 

taho India, tafiyar ce ta xo min cikin gaggawa, Kuma Suraj bai son tafiya shi kadai dama” Bata jira cewarsa ba ta 

kama hannunsa tace “Come on mu je plss” da mamaki yake kallonta, can ya janye hannunsa daga nata still 

following her slowly har xuwa hotel room din da take.

Junaid ya nufi kujeran dake makeken dakin hotel din ya xauna, gefensa ta xauna tana wani murmushi tace “Me xan 

kawo maka Jay? Ko in sa a kawo maka abinci?” Ya girgixa kai yace “Nothing, saurayin ki kika biyo India kenan?” 

Tace “Ehh shi na biyo amma wllh sbda kai na xo, India ai ba wani kasar xuwa hutu bane kasar xuwan marasu lafiya 

ne, wani saurayina fa tun last week yake son mu je dubai mu huta amma na gwammace in biyo wannan xuwa India 

duk don sbda kai wllh” Junaid ya gyada kai yace “Ni kuma me xan maki da kika biyosa India sbda ni?” Ta wara ido 

tace “Just to see you mana, Ina dawowa daga Abuja fa aka ce min kun taho India da makauniyar nan….” Yana 

kallonta da kyau yace “Kada ki sake ce mata makauniya” Ta d’an yi shiru, sai kuma ta tabe baki tace “Toh ka tafi ko 

sallama babu shi yasa da na samu opportunity kawai na biyo ka” ta karasa tana murmushi, Ya girgixa kai yace “So 

this the best life you think you are living right?” Tayi frowning face dinta tace “Ban gane ba, me ya kawo wannan 

maganan kuma?” Ya tabe baki yace “Anyway shkkn, so yanxu kin gan ni kuma mun gaisa, plss kar ki sake kiran line 

dina sbda a hospital nake da mara lafiya…. Pls don’t call again I beg you” Ta marairaice tace “Wllh tllh sbda kai na 

xo kasar nan Jay, ka kaini asibitin mana nima muyi jinyar tare” Yace “Aa, idan mun koma Nigeria sai kiyi jinya but 

not here coz bbu ma wanda yasan kin xo nan, I repeat don’t call me again, I don’t even want to ask what ur name is, 

but what ever it is plss don’t call my line again Lady” Kwantawa tayi jikinsa kamar xata yi kuka tana shafa kirjinsa tace “Haba Jay….” Turata yyi har sai da ta fadi kasa ya mike yana mata wani kallo yace “Are you stupid?” Shiru tayi 

tana kallonsa, yace “Tun da nayi respecting dinki na xo har Inda kike kada ki sake kirana, na xo ne dama don kada ki 

kuma kirana, idan kun gama abinda ya kawo ku ke da saurayin naki ku koma inda ku ka fito tare, we will meet back 

in Nigeria….” Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo ya bude kofar xai fita suka kusa cin karo da Suraj din, Junaid 

ya kallesa daga sama har kasa, ya bi gefensa ya fita dakin, Suraj ya kalli Salima da ta kauda kai da sauri, yana 

nunata da yatsa yace “Dama shi yasa tun jiya kike wasa da hankalina ashe appointment gare ki da wani? To maxa 

kwashe kayanki ki bar min hotel room dina yanxun nan” Ta masa wani kallo tace “Ae ba wani ya kawo ni kasar ba, 

yanda muka xo tare haka xa mu koma tare, kawai don ka kawo ni India sai aka ce maka haka xaka dinga samu na 

baxa ka biya ba kamar wata gareji, to ko garejin ma ae ana biya” ko amsa bai bata ba ya tafi inda jakar kayanta yake 

ya dauka ya bude kofa ya jefar corridor din hotel rooms din, ya koma ya dauko handbags dinta da sauran tarkacenta 

duk ya watsar a waje, bude baki tayi tana bin sa da kallo a tsorace ta kasa cewa komai ita ma ya tafi ya ja ta har 

kofan ya turata waje ya rufe kofar sa. Junaid na isa hospital din dab da magrib Mami tace “Where are you coming 

from Junaid?” Ya ajiye ledan madaran hannunsa ba tare da ya kalli idonta ba yace “Mami wata frnd dita ce da muka 

hadu online years back, she’s here in india, so shine naje muka gaisa” Mami ta ta6e baki bata ce komai ba, gadon da 

Heedayah ke kwance ya nufa ya xauna saman kujera yana kallonta, bacci take heavily, kana gani kasan alluran bacci 

aka mata, ya kai hannu goshinta a hankali ya ji da xafi, Mami tace “Ynxu naje nayi masu complain xafin jikin nata” 

Ya gyada kai bai dai ce komai ba, Mami tace “Shaheedah called me daxu bayan ka fita” Kallon Mami yyi yace 

“Ohk” tace “Baban nata ya ji sauki amma sosai koh?” Yace “Ehh ya samu lfya” Wayarsa da ya fara ring a aljihu ya 

ciro, ya ga Beauty gaban screen din, ya d’an saci kallon Mami dake kallonsa, ya mayar da wayar aljihu bayan ya sa 

shi total silent, yana ta xaune dakin har Magrib yyi, Mami ta shiga bandaki yin alwala sai da ta fito ya mike yace 

“Xan je inyi sllh” Mami tace “Ohk” daga haka ya fita, sai da ya fito haraban katon asibitin ya ciro wayarsa ya ga 

miss calls din Salima kusan ashirin, ya wani buda ido da mamaki yana kallon screen din wayar, sai ga kiranta ya 

kuma shigowa, dagawa yyi ya kai kunne kafin yace komai ta fashe masa da kuka sosai tace “Jay wllh ya koreni ya 

watsar min da kaya ganinka da yayi, gashi ni bani da inda xan je bamu da kowa a kasar nan, ko kudin kama hotel ma 

bani da shi balle kudin komawa Nigeria ni dai kawai biyosa nayi tunda mun saba tafiya tare, yanxu haka ina titi da 

kayana daga ni sai kudin Nigeria dubu uku a jakata, don girman Allah ka rufa min asiri, nayi ta kiran layinsa ko 

hakuri ne in basa amma yyi blocking dina wllh” Junaid yace “Amma baki da hankali, ni da kike kirana me xan 

maki? ni na kawo ki India da xa ki kirani ki ce min ya kore ki, look kar ki sake kiran layina idan ba haka ba duk 

abinda na maki ke kika ja wllh” Ta rushe da matsanancin kuka tace “To yanxu Ina xan je fisabilillahi, ni wllh bbu 

wanda yasan Ina India sai kai, don girman Allah Jay ka rufa min asiri” Ya ja tsaki ya kashe wayarsa ya tafi yin sllh. 

Da abinci ya dawo ward din, Mami ta kallesa da damuwa tace “Toh ita tana ta bacci bbu fa abinda ta ci tun safe 

wllh” Junaid yace “Ga drip an sa mata for that, xuwa can cikin dare xata tashi sai ki hada mata shayi” Mami tace 

“Toh ko in tasheta yanxu in bata?” Yace “Aa, ai baxata tashi ba, allura suka mata” Mami tace “Toh shkkn” Yana ta 

xaune ward din kusa da Heedayah har kusan sha biyu na dare, yana lura da da cewa alluran ya fara saketa don sai 

motsi take, ta juya can ta juya nan, kana ganinta kuma kasan she is still in pain, lkci lkci take kai hannu idonta, sai 

ya rike hannun ya mayar saman gado, yana mata haka kuma sai ta turo baki, yyi murmushi ya d’an kalli Mami da ta 

fara bacci ya ja bakin, kara tayi kamar jira take ta fara kokarin mikewa xaune, Mami ma ta farka ta mike xaune da 

sauri, Kamar xata yi kuka tana tattaba gadon tace “Mami kina ganinsa ko? Bakina ya ja min da karfi” Mami ta sakko 

saman gadon da take tace “Sai da safe tashi ka fita, good night” Tashi yyi kafin ta iso Inda yake yana murmushi ya 

nufi kofa making sure hotel key dinsa na aljihunsa, Heedayah tace “Mami to ina xa shi?” Mami tace “In xuba maki 

abinci ko in hada maki tea?” Heedayah ta 6ata fuska tace “Mami ina Yaya xa shi?” Mami tace “Ina ruwanki da shi?” 

Junaid ya kalleta sannan ya bude kofar ya fita still smiling. Yana fitowa wanka bandakin hotel room dinsa ya saka 

jallabiyarsa ya kwanta ya dau wayarsa, miss calls arba’in ya gani, ya mike xaune da sauri yana kallon wayar, sai ga 

kiran Beauty a screen dinsa, ya daga ya kai kunne a fusace yace “Ke wace irin Mahaukaciya ce wai? Draining din 

battery dina kike son yi? Why are you calling me for heaven sake???” Ta fashe masa da kuka da karfi tace “Wllh jay 

gani a bakin titi har yanxu ni ban san Inda xanje ba, ko asibitin ne ka taimaka ka fada min sunansa in je, gashi duk 

an watse an bar ni ni kadai kada yan sandansu su xo wucewa su gan ni su tafi da ni, don girman Allah ka gaya min 

asibitin in je jay….” Yace “Toh wai da kike ta kirana ni na kawo ki India ne baiwar Allah?” Tace “Amma silar ka na 

xo ai, Allah sbda kai na biyo Suraj duk da nasan Mahaukaci ne, to wa xan kira idan ba kai ba” Junaid ya ma rasa me 

xai ce mata, ita kuwa sai rera masa kuka take a kunne, can ya ja tsaki yace “Ina kike yanxu” Tana kuka ta gaya masa 

ya katse wayarsa, bbu ynda ya iya haka ya dau kudi ya fita hotel din ya kulle dakin, Tricycle ya samu xuwa Inda tace 

masa take, ai ko ya sameta gefen hanya ita kadai xaune kan jakan kayanta, yana sauka daga tricycle din ta mike 

xaune duk idonta yyi suntum sbda kuka, yana mata wani kallo yace “Ashe ke karamar yar duniya ce tunda har xa ki 

shigo India ki rasa wajen kwana duk yawon da kike da maxa kasashe daban daban” Ita dai bata tanka sa ba ta dau 

jakarta ta saka cikin Tricycle din da sauran kayanta sannan ta shiga ta xauna, yyi kwafa ya shiga adaidaitan suka 

koma hotel din da yake, Sai karfe kusan daya da wani abu suka shigo hotel din, tana ganin wani dakin xai biya mata tace “Aa jay kada ka wani kashe kudin ka, ni dai gwara kawai ka harhada ka biya min kudin jirgi in koma Nigeria” 

Bai tanka ta ba yyi wucewarsa sama ta bi sa da kaya tana tangal tangal don ko daya bai dau mata ba, yana bude 

dakin ya shiga ya bar mata a bude ta shigo sannan ta kulle tana bin dakin da kallo, saman gado ya nufa ya dau bargo 

da pillow ya jefa mata a kasa snn ya kashe wutan dakin yyi kwanciyarsa, ta ajiye kayanta ta dau pillon da bargon ta 

shimfida bargon sannan ta daura pillon a kai, a hankali tace “Nagode, amma xan d’an kunna dim light sbda xan yi 

wanka” Ko tanka ta bai yi ba ya juya mata baya yana danna wayarsa, bayan kusan minti goma ya ga ta kunna wuta 

mara haske sosai ta shiga bandaki, yana jin alamar tayi wanka ta fito, mamaki ne ya cikasa sosai ganin naked ta fito 

daga bandakin walking majestically, a hankali ya ajiye wayarsa ya rufe ido ya tsiri baccin da bai yi niyya ba a lkcn, 

ta gama buruntunta ta cika dakin da kamshin turare iri iri da ta fesa a jikinta, shi dai idonsa na rufe gam, xagayawa 

tayi kusa da shi tace “Don Allah ka d’an ban wayarka xan kira yayata, tun daxu take kirana sbda tashin hankali ban 

dauka ba gashi ynxu bani da isashen kati” yyi banxa da ita har sannan idonsa a rufe, ta kai hannunta me sanyi a 

hankali fuskarsa tace “Kayi bacci ne Jayy?” Lkci daya ya mike xaune ya sauke mata lafiyayyen mari yace “I swear 

to Allah ba karamin aikina bane in fitar dake hotel din nan yanxun nan, are you mad????” Mikewa tsaye tayi da rigar 

baccinta iya cinya bbu komai ciki ta dafe kuncinta tana kallonsa, yyi mata tsawa yace “Baxa ki tashi gabana ba sai 

nayi ball da ke” gyada kai tayi ta juya tana karkade karkade ta xaga Inda ta shimfida bargo ya bi ta da wani irin kallo, 

yyi wani kwafa ya koma ya kwanta ya rufe ido…. Daren ranan dai bai yi bacci ba sai juye juye yake shi kadai, sae 

dab da asuba bacci ya daukesa, hasken ray din rana da ya sauka fuskarsa ne ya farkar da shi, ya mike xaune da sauri 

yana kiran Allah a xuciyarsa, gefensa ya ga Salima kan gadon tana bacci hankali kwance, bbu abinda baya gani a 

jikinta ta cikin shegen kayan baccin da ta saka, tashi yyi da sauri ya shige bandaki, tun da yake dai da girmansa bai 

ta6a missing sllhn asuba ba ko a jam’i ko ba a jam’i ba, da asuban xai yi raka’atainil fijr snn yyi sllhn sa amma wai 

yau shine har kusan 8 bai yi sllhn asuba ba, ransa a bace ya wanke baki yyi alwala ya fito ya shimfida darduma ya 

tada sllh, ya kusa minti sha biyar saman darduman bayan ya idar sannan ya mike ya buga gadon da karfi yace 

“Dauki kayan ki mu wuce airport….” Ta bude ido a hankali tana wani juye juye tace “Anya ma da jirgin xuwa 

Nigeria direct kuwa yau??? stopovers…..” Yyi mata wani tsawa kafin ta karasa yace “Tashi ki dau kayanki ki fita ki 

samu wani wajen xama har a samu plane din Nigeria, not here anymore” ta marairaice tace “Toh amma ae ka jira 

inyi wanka in shirya tukun mana Jayyy” tana fadin hka ta mike tsaye dab da shi, ya dauke kai ya bar wajen, wayarsa 

ya nufa ya dauka ya ga miss calls din Mami har Uku, xaro ido yyi don kullum ana idar da sllh asuba yake shiga 

asibitin with breakfast, fita yyi dakin da wayarsa in a haste, sae da ya tsaya hanya ya siya masu breakfast snn ya 

wuce asibitin…. Mami na xaune kusa da Heedayah dake shan shayi a saman gado da kwai da bread, she looks very 

strong, an kuma sauya mata eye pads din idonta, tana jin an bude kofa ta dakatar da shan shayin tace “Mami Yaya 

ne?” Mami dai bata ce komai ba sae kallon Junaid take daga sama har kasa, coz duk a birkice yake, snn bai ta6a 

shigowa asibitin da jallabiya ba, kansa a kasa yace “Ina kwana Mami” Mami ta amsa ta dauke kai ta ci gaba da 

danna wayarta da take, yayi kasa da murya kamar munafuki yace “Mami na makara ne yau wllh….” Still bata kallesa 

ba tace “Ehh na ga alama” Yace “Ga breakfast….” Tace “Don’t worry an kawo mana” Da mamaki ya dago kansa yace 

“Who??” Kafin tace komai aka bude kofar ward din ya juya don ganin wanda xai shigo….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *