HEEDAYA CHAPTER 19 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sudais ne ya shigo ward din shi ma yana kallon Junaid kamar ynda Sudais ma ke kallonsa, Heedayah tace “Mami
waye? Ya Sudais?” Mami tace “Eh” Sudais ya nufi Junaid yana murmushi ya basa hannu suka gaisa, Mami tace “Har
ka dawo” Yace “Ehh na dawo Mami” kujera ta nuna masa ya xauna, Shi dai Junaid na tsaye har sannan ya ki yrda su
hada ido da Maminsa, Heedayah tace “Yaya me ya sa baka xo tun daxu ba sai yanxu, Ya Sudais ne ya kawo mana
breakfast fa” Ya d’an kalleta yace “Ban xo din ba” Ta buda hannu ta tabe baki tace “Ae kai da Mami” Sudais dake
murmushi yace “Ko dai shi da ke?” Washe hakoranta tayi bata ce komai ba ta ci gaba da shan shayinta, can ta ajiye
cup din tace “Ya Sudais me ya sa baku xo da kaka ba, Ina missing dinta” a hankali ta kara da cewa “I am also
missing Abba” Sudais yace “Xa su xo in sha Allah” Junaid dake ta tsaye ya dake ya kalli Mami yace “Mami xan je
in dawo” Bata ko kallesa ba tace “Ohk” a hankali Heedayah tace “Yaya Ina xaka kuma? You are just coming fa” Yyi
banxa da ita ya fita dakin…. Rai bace ya koma hotel din ya bude kofar room din ya shiga ga mamakinsa Salima
kara gyara ma kayanta wajen xama tayi, ga gadon ta gyara sa fess sae kamshi ko ina yake amma bata dakin, daukar
kayan yyi ya fito fuska daure har haraban hotel din ya nufi gun masu gadi nan ya bar masu kayan bayan ya sanar
masu me shi xata xo ta amsa, yana komawa ya ga handbag dinta a dakin, har ya dauka sae ya tsaya ya bude ciki, duk
tarkacen kayan kwalliyanta ne ciki da prophylactic na mata har da maza and different types of pills ciki har da
aborticide, ya girgixa kai cike da takaici ya rufe jakar ya fita dakin ya kai can gun masu gadi sannan ya koma
dakinsa, wanka yyi ya shirya ya d’an kwanta, gaba daya jin sa yake wani iri, bayan kusan minti talatin ya mike a
hankali ya dau wayarsa ya fita ya kulle dakin da makulli ya bar hotel din. Asibiti ya koma kafin ya shiga ya kira line
din Salima, ba bata lkci ta daga tace “Jayyy” ya wani daure fuska kamar tana ganinsa, strictly yace “Ga kayanki can
gun masu gadi na ajiye ki dauka, and don’t ever try calling my line again idan ba haka ba xa ki sha mamaki, I repeat
don’t try calling my line again….” Salima ta marairaice tace “Ban gane kayana na gun masu gadi ba jay, me ya kai
kayan gun masu gadi juma? Ai na dau spare key kafin in fito” shiru Junaid yyi da mugun mamaki jin abinda tace,
can ya ciro makullin aljihunsa yana kallo, wani tsawa yyi mata yace “I swear to Allah kada ki yrda in dawo ya in
sameki hotel room din nan, duk abinda na maki ke kika ja ma kanki kinji na rantse….” Ta fashe masa da kuka tace
“Toh wai ina kake son in je yanxu Jay? Bayan na gaya maka wanda ya kawo ni ma yyi blocking dina kuma bani da
kudin komawa Nigeria? Haba Jay sai kace baka ta6a sanina ba” cikin fushi yace “Good… nima ynxu xan yi blocking
din naki but before then I am still warning you kada ki yrda in dawo in ganki dakina, wllh sai na maki abinda baki yi
tunani ba” Bai jira cewarta ba ya katse wayar yayi blocking din nata sannan ya shiga cikin asibitin trying to calm
himself, shi ma ciki bai wani ga fuskar Mami ba hakan ya sa ya fito haraban asibitin ya xauna…. Har aka yi azahar
Junaid na xaune ne haraban asibitin ya ki shiga ward din, bayan azahar kuma Sudais ne ya fita ya siyo masu abinci
ya kawo, Mami na xuba ma Heedayah, Heedayah tace “Mami ko dai Yaya ya wuce ne?” Mami bata ce mata komai
ba, Sudais yace “Yana waje, ko xa ki je?” Ta make kafada tace “Aa ba ruwana da shi ai” Da daddare bayan isha
Junaid ya shigo ward din da dinner da ya siyo masu, Mami da Heedayah ne kadai dakin Sudais baya nan, Yana ajiye
masu kuma yace “Mami xan tafi in kwanta” Mami tace “Good, Ka jira Sudais he went to get something sai ku tafi
tare” Da mamaki yace “I tot yyi lodging hotel ai” Mami tace “Yes he did, amma nace ku tafi tare naka hotel din”
Junaid yace “Ohk” daga ya nemi waje ya xauna ya d’an kalli Heedayah bai ce komai ba ya fiddo wayarsa yana
dannawa silently, sai wajen takwas da rabi Sudais ya shigo ward din ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace “Mami
Abba ya kira ku?” Mami tace “Yes Ina sllh ya kira but I followed the call yanxu” yace “Ohk” ya dau apple daya ya
kama hannun Heedayah ya saka ciki, kin sake hannunsa tayi a hankali tace “Thank you….” Mami tayi murmushi
bata dai ce masu komai ba, kallonsu kawai junaid ke yi amma ba directly ba, Sudais na juyowa ya maida idonsa
saman screen din wayar dake hannunsa da sauri, Mami tace “Sudais kai yake jira ku tafi hotel ynxu” Sudais yace
“Ohhh but ai nayi lodge a wani hotel Mami” Mami tace “Noo, ku tafi tare, you two should stay together” Junaid dai
idonsa na kan wayarsa amma Mami yake saurara, can ya mike ya maida wayar aljihu yace “Toh sai da safe Mami”
Daga haka ya nufi kofa, Mami bata tanka sa ba tace “Sudais baxa ka debi fruit din ba, ai sun yi yawa” Yace “Noo na
sha ai” tace “Ohk sai da safe” yace “Allah ya tashe mu lafiya” Heedayah tace “Yaya Sudais byee” yace “Bye dear….”
Junaid na tsaye bakin kofa bai fita ba, can ya tabe baki ya fita yyi wucewarsa, Sudais ya bi bayansa duk da har ransa
bai so bin junaid ba amma baya son yi ma Mami musu, sai bayan da suka fita Heedayah ta fashe da kuka a hankali
tace “Mami kinga yaya bai kulani ba koh, he don’t want to talk with me” Dariya ta ba Mami sai dai bata yi ba, Mami
tace “Kyaleni da shi xan yi maganinsa” Tunda suka bar hospital din Junaid bai ce da Sudais komai ba, haka shi ma
Sudais din, nan ko Junaid is just imagining ace su je hotel din ya tadda Salima a dakinsa, suna isa hotel din suka
sauka tricycle din Sudais ya bada kudi, Junaid ya jira aka basa canji sannan suka shiga hotel din a tare, Junaid ya
tsaya gun masu gadi yana tambayar ko mai kayan daxu ta xo ta dauka, suka amsa masa da eh, bin bayan Sudais yyi
xuwa cikin hotel din, a hankali Junaid ya fara murda kofar dakin ko makullin bai sa ba ya ji kofar a bude, lkci daya
xuciyarsa ya fara tafarfasa ya shiga dakin, Sudais ma ya shiga ciki, xaune suka samu Salima da takeaway din abinci tana ci a dakin, Sudais ya tsaya bakin kofa yana kallonta with so much surprise, Mikewa tsaye tayi ita kanta tayi
shock din ganin Sudais, Junaid ya nufeta a mugun fusace ya sauke mata wawan tagwayen Mari cikin tsawa yace
“Me na ce maki? What did I tell you???” Dafe kuncinta tayi tana kallonsa with shock, can ya fashe da kuka tace
“Toh wai ina kake son in tafi bayan nace maka bani da kudi Jay, Banda sbda kai me xai kawo ni kasar nan??” Gun
kayanta ya nufa ya dauke jakunkunanta biyu ya bude kofa ya watsar waje ya dawo ya nufota, tana ganin haka ta
shige bandaki da gudu ta sa makulli, Sudais na yatsine fuska da mamaki yace “Me ye hadin ka da yarinyar nan? Me
ya kawota nan? Dama da ita aka taho” Rai bace junaid yace “Saurayinta fa ta biyo ya koreta shine ta makale min nan,
I don’t even know her….” Katse sa Sudais yyi yace “Sorry but I can’t stay under same roof with this lady, dama na
kama hotel I can’t just say no to Mami, it’s better in koma can, but be careful with this lady she can be cunning”
Junaid ya dau jakarsa shi ma yace “Mu tafi hotel din naka, I am not staying here either, dama kudin kwana 15 na
biya for this hotel kuma nan da jibi xai yi expire so I prefer leaving too” Sudais yace “Better….” Daga haka suka fita
dakin xuwa hotel din Sudais. Salima na jin alamar sun fita ta bude kofar ta leko ganin ba kowa ta fito dakin, ba
karamin tsorata tayi ba ganin Sudais, ita a rayuwa ma akwai wanda ta tsana kamar shi kuwa, ko gaisuwa baya hada
ta da shi dama, cije yatsa tayi ta xauna gefen gado a hankali tace “Anya ma Junaid din nan na da lafiya kuwa, upon
everything yesterday he isn’t still moved” Da sauri ta mike ganin bbu jakar kayansa ta tafi window tana lekawa taga
Inda suka nufa, tricycle taga suka shiga, ta koma ta xauna ta marairaice tace “Dama Sudais ma na kasar nan ban sani
ba??” Can ta gyada kai tayi wani murmushi tace “idan ka san wata baka san wata ba Junaid” Tun da Mami ta tashi
yau da asuba take ta fargaba ita kadae don ranan xa a cire ma Heedayah eye pads din idonta, kuma ranan ake sa ran
xata fara gani, daren ranan Mami sae da tayi sllh ta roki ubangiji yasa an dace, ya sa karshen wahalan kenan…. Karfe
shidda da rabi likitocin suka fita da ita xuwa theatre, Mami dai na xaune bakin theatre din sae addu’a kawai take, ga
faduwar gaban da yyi mata yawa, da taji motsi sae ta kalli kofa da sauri amma bbu wanda xata ga ya fito har karfe
bakwai da rabi, kukan da ta ji Heedayah ke yi daga ciki ya fi daga mata hankali, tun daga nisa take kallonsa har ya
karaso tare da wani likita baindiye walking slowly, likitan ya gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa don da shi aka yi
ma Heedayah aiki 3 days back, shi ma dai yyi kasa da kai ya gaisheta, ta amsa tace “Ya hanya” Yace “Alhmdllh, ya
kokari” tace “Mun gode Allah” baindiyen yayi tapping dinsa a baya da harshen turanci yace sae sun hadu anjima,
daga haka ya juya ya wuce, dai dai fitowar wani likita yana kallon Mami yace “You can go in Madam, a Dr will
explain everything to you inside” mikewa Mami tayi amma ta kasa tambayarsa ba ayi nasara bane aka ce ta shigo,
kuma ta kasa shiga ciki, likitan yayi wucewarsa, kansa a kasa ya nufi kofar shiga theatre din walking slowly, Mami
ta bi sa da kallo har ya shiga ciki, Heedayah na xaune saman gadon ta takure waje daya ta rufe fuskarta da pillon
saman gadon tana kuka a hankali, likitoci biyu na tsaye suna jiran shigowar Mami, Daya daga likitan da turanci yace
“Her brother?” Ya gyada masa kai sannan ya karasa gadon yana kallonta, likitan yyi murmushi yace “Yes it was
successful, but it’s a new world to her…. And it will take sometime before she will adapt, like… she will have
problem with light, Human, infact everything, because she just left the world of darkness” Dago kanta yyi ta bude
jajayen idonta a hankali tana kallonsa suka yi ido hudu, lkci daya ta fasa ihu kamar warce ta ga mugun abu, ya
rungumeta, jikinta ya dinga rawa gaba daya a tsorace take, duk wnn abun Mami na tsaye bakin kofa tana kallonsu,
lkci daya hawaye ya kawo idonta tana hamdala a xuciyarta ta karaso gadon da sauri tace “Heedayah” cikin rawar
murya Heedayah na kara shigewa jikinsa tace “Mami tsoro nake ji, kice a rufe min idona” Likitan yace “She will
adapt slowly….” wheel chair ya jawo ya ajiye don a maida ta ward dinta in ji likitan, Shuraim ya dauketa har sannan
ta ki yarda ta kara bude idonta, bai daurata kan wheelchair din ba ya nufi kofar theatre din Mami ta bi bayansa, da
yake abokinsa likita sai da ya fara nuna masa ward din da suke kafin ya kawo sa theater din direct ward din ya nufa,
Mami dai na biye da shi, ya bude kofa ya shiga ya isa kan gadon ya kwantar da ita a hankali, har sannan taki yarda ta
bude idon, har runtse idon tayi gam, ya saki curtains din ward din gaba daya, ya kuma kashe wuta haske ya ragu
sosai, Mami dai na tsaye tana kallonsa, Wani likita ne ya shigo ward din ganin ynda Shuraim yyi ma dakin yace
“Very good” daga haka ya juya ya fita, Mami ta xauna gefen Heedayah ta dagota tace “Daughter” a hankali tace
“Mami” Mami tace “Bude idon ki” ta girgixa kai cikin rawar murya tace “Ina jin tsoro” Mami tace “Baki son ki gan
ni?” Kuka ta fara yi tace “I am scared” murya can kasa Mami tace “Don’t be dear, open it slowly” Shuraim dai na
tsaye bakin gadon yana kallonsu, a hankali ta fara kokarin bude idon maimakon ta sauke kan Mami sai ta sauke kan
Shuraim dake kallonta suka yi ido hudu, boye fuskarta tayi jikin Mami ta fashe da kuka sosai tace “Mami Noo, meye
shi din? I saw something” a sanyaye Mami tace “That’s Shuraim” Sake dagowa tayi da sauri ta bude idonta har lkcn
kallonta yake shi ma suka kara hada ido, knowing her condition sai ya sakar mata soft sweet smile, ta fi second biyar
tana kallonsa ko kiftawa bbu sai kuma ta kara boye fuskarta jikin Mami da sauri, Mami na jin yanda xuciyarta ke
bugawa, duk wnn abun bata kalli Mami ba har sannan, Mami ta kwantar da ita a hankali, Heedayah ta rufe fuskarta
da pillow, har bayan wani lkci bata dago ba balle ta bude ido, Mami xata dagota Shuraim na kallonta yace “Tayi
bacci fa Kwantar da ita Mami tayi ta mike a sanyaye ta tafi kan kujera ta xauna, Shuraim dai na ta tsaye kusa da gadon
idonsa kan Heedayah, Mami tace “Kayi breakfast ne?” Xai yi magana aka bude kofar ward din Sudais ya fara
shigowa junaid na biye da shi rike da leda, Sudais ya d’an tsaya xae fiddo wayarsa a aljihu ya haska dakin yace “why
is it dark here….” Kunna switch din Shuraim yyi ya ja blanket din saman gadon ya rufa Heedayah da shi, da mamaki
Sudais ke kallonsa, ya buda ido very amazed yace “You!!!” Sau daya Junaid ya kalle Shuraim ya nufi Maminsa,
ganin hka Sudais ya bi bayansa ya ajiye ledan breakfast din hannunsa saman table, nan suka gaida Mami, ta amsa
tana tambayarsu night dinsu, Sudais yace “Alhmdllh, ya mai jiki?” Mami tayi murmushi sosai tace “Alhmdllh, she
gained her sight, the surgery was successful Alhmdllh” Junaid ya juya da sauri yana kallon Heedayah, he couldn’t
help it but smile, Sudais wa wara ido yace “Alhamdulillah” a tare suka nufi gadon gun Heedayah, Mami tace
“Yanxun tayi baccin, she needs much rest sbda a tsorace take…” Junaid ya kalli Mami da sauri yace “Tsoron me
kuma?” Mami tace “Don’t forget, she is blind all her life, every image is exactly new to her now, likitan yace sae tayi
adapting a hankali” Junaid ya dinga kallon Heedayah cike da tausayinta, can ya bude blanket din a hankali yana
kallon fuskarta, Sudais ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, ta gefen ido Shuraim ya dinga kallonsu su biyun,
Junaid ya maida mata bargon ganin bacci take peacefully, xagayowa Shuraim yyi yana kallon Mami yace “Xan je in
dawo” Mami tace “Ohk” daga haka ya nufi kofa, Sudais ya tabe baki har Shuraim ya fita ward din, Mami na kallon
Junaid tace “Ba ku gaisa da shi ba Why?” Junaid yace “It’s not necessary Mami….” Mami ta hade rai tace “Ban gane
it’s not necessary ba” ya juya yana kallonta yace “Did he even do as if he noticed us here Mami” Mami tace “But
you met him here ko, Kuma kasan yau ya sauka hanya….” Sudais yyi murmushi yace “To Mami ni da nayi masa
maganan kin ga ya amsa? Ko kuma ya nuna ya gane ni” Mami tace “Eh I noticed wnn halinsa ne ai koh”
Disgustingly Junaid yace “Mugun hali kenan” Dariya sosai Sudais yyi, Mami ta tabe baki tace “So what’s the gain da
ba ku gaisa ba ynxu, kamar wasu yara?” Junaid bai kuma ce ma Mami komai ba ya ja kujera ya xauna, Sudais yace
“Anyway, Junaid that’s just Shuraim… haka nan yake, and am telling you ba da wata manufa yyi hakan ba wllh, he is
just different, totally different, he find it hard to speak at times, but he is lovely being with….” Junaid yace “But nima
ba da wata manufa nayi hakan ba, I was checking on Heedayah that’s why ban ma lura da shi ba ai” Sai kusan karfe
sha daya da rabi Shuraim ya dawo dakin, har lkcn Junaid da Sudais na tare da Mami suna mata hira, Kana ganin
Mami kasan tana cikin farin ciki, kai kace ‘yar cikinta ce Heedayah, Shuraim ya gaidata, Mami tace “But are you
sure you’ve eaten?” Shuraim yace “Na ci” Kujera ta nuna masa ya xauna yana kallonsu Sudais yace “Sannun ku”
Sudais ya rungume hannunsa daga xaunen da yake yace “Ciwo mu ka ce maka muke?” Junaid dai danna wayarsa
kawai yake bai dago ba balle ya kalli Shuraim, Shuraim bai tanka Sudais ba, Mami tace “Ya ka baro mutanen gida”
yace “Duk lfya lau” Mami tace “Kaka ta koma gidan ne” yace “Aa” tace “Ohk” Junaid ya mike ya maida wayarsa
aljihu ya nufi kan gado ganin Heedayah na kokarin cire blanket din kan ta, dukawa yyi dai dai fuskarta yana kallonta, ta bude idonta a hankali bayan ta cire blanket din, ido hudu suka yi da Junaid, ta fasa wani ihu, Sudais ya mike da
sauri yana kallonta shi ma, Junaid xai kama hannunta ta dinga komawa baya tana ihun, da ta kallesa sai ta kalli
Sudais dake tsaye sai ta kara sautin ihunta, duk sai suka tsaya suna kallonta gaba daya, shi dai Shuraim na xaune
yana kallonsu, Mami ta nufota tace “What happened daughter, Yaya Junaid ne, with Yaya Sudais, don’t shout, they
are ur brothers” Ta dinga girgixa kai tana boye fuskarta cikin rawar murya tace “I am scareddd” lkci daya ta juya
masu baya gaba daya, ta bude idonta a hankali tsoro karara a fuskarta, hada ido suka yi da Shuraim da ke kallonta
don ta direction dinsa ta juya, ta rufe idonta da sauri ta kara budewa, tayi hakan yyi sau uku, d’an murmushin da
iyakarsa lips dinsa yyi mata, tayi masa kuri da ido without blinking, Sudais ya xagayo toward direction din
Heedayah tana daura ido kansa ta fasa ihu ta boye fuskarta jikin pillow, kofa junaid ya nufa ya fita ward din, Sudais
xai karasa gun gadon Mami tace “Let her Sudais” Bai ta6a ta ba kawai ya tsaya, Mami ta iso kusa da ita ta dagota a
hankali tace “They are all your brothers Heedayah, Sudais and Junaid” ta fashe da kuka tace “I’m scared” Sudais ya
sauke ajiyar xuciya ya juya ya fita ward din shi ma. A hankali ta bude fuskarta jin karan kofa, Hada ido suka kara yi
da Shuraim, ta fi second goma tana kallonsa tun daga kansa har kafansa, can ta juya suka yi ido hudu da Mami, a
karo na farko kenan da ta kalli Mami, shiru tayi tana kallonta a hankali ta kai hannu fuskarta tace “Mami??” Mami ta
sakar mata murmushi, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta jawota jikinta ta rungume ta tace “Yess Daughter” Lamo
Heedayah tayi jikinta murya can kasa tana nuna Shuraim tace “Mami what is that?” Mami tace “He is Shuraim” kara
juyowa tayi ta kallesa sannan ta kalli Mami, Mami ta gyada mata kai assuring her he is the one, tace “Mami Yaya fa”
Mami tace “Ya fita ynxu” Tace “Ya Sudais fa?” Mami tace “Shi ma ya fita” Kallon gadon da take xaune kai ta dinga
yi tace “Mami wannan ne bed?” Mami tace “Yess” Mami ta nuna mata windown ward din tace “Wancan kuma
window” Kallonsa kawai Heedayah ke yi, Mami ta nuna mata kofa tace “Door” Heedayah ta gyada mata kai a
hankali tana kallon kofar, Shi dai Shuraim kallonsu kawai yake, Sakko da ita Mami tayi kasa, ta dinga kallon tiles
din tana daga kafarta tace “Mami wnn ne floor?” Mami na murmushi tace “Yess daughter” Mami na lura da yanda
take ta kallon jikinta tun daga kafa har hannunta sai kuma Mami ta ga tayi murmushi, Mami tace “Ki ce Alhmdllh”
A hankali tace “Alhmdllh” Mami ta rungume ta tana kara hamdala a xuciyarta…. Xaunar da ita Mami tayi saman
kujera tace “Let me make you tea now” Heedayah ta gyada mata kai, daga haka Mami ta tafi gun kayan shayin,
Heedayah ta juya tana kallon Shuraim, d’aga kai yyi ya kalleta shi ma, tayi masa kuri ko kiftawa babu, ya dauke
kansa ya ci gaba da danna wayarsa, har Mami ta kawo mata shayi kallon Shuraim Heedayah take kamar ta samu
television, Mami tayi murmushi ta kamo hannunta ta sa mata shayin, Heedayah ta maido da dubanta gun Mami tace
“Mami baya magana kaman ke” Mami tace “Yana yi mana, Ya Shuraim ne nace maki” Tace “Noo, I didn’t hear his
voice, ba shi bane” sai kuma tayi kasa da murya tace “But ya Shureen is wicked, this isn’t him, wnn bai yi fada ba”
Mami tayi dariya tana kallon Shuraim tace “Talk to her Shuraim” Murmushin kawai yyi shi ma bai dai ce komai ba
ya ci gaba da danna wayarsa, Mami ta xauna tana kallon Heedayah da sai da ta gama kare ma Cup din da shayin ciki
kallo na kusan minti biyu sannan ta kai baki a hankali kamar me tsoron yin hakan, sai da ta kusa rabi ta cire cup din
ta juya tana kallon Shuraim, har sai da Mami tace “Toh shanye shayin mana” sannan ta dauke kai ta ci gaba da shan
shayin, tana shanyewa kuma Mami ta amshi cup din ta tafi ta wanke, Heedayah juya ta ci gaba da kallon Shuraim,
ya d’an hade rai ya dago ya kalleta, wani ihu ta fasa tayi baya xata fadi ya mike da sauri ya rike kujeran, Mami ta fito
da sauri tace “What happened?” Heedayah ta boye fuskarta cikin rawan murya tace “I’m scared” Mami ta dagota ta
rungumeta tace “Don’t be dear, no one is harming you” ta hannun Mami ta bude ido a hankali tana lekosa kuma,
murmushi ya sakar mata, ta janye jikinta daga na Mami ta tsaya tana kallonsa da manyan idanuwanta da suka yi ja,
sosai hakan ya ba Mami dariya, Mami tace “Take her out Shuraim kuyi strolling but don’t go far…” Yana son ce ma
Mami hasken waje xai mata yawa amma kuma bai son yin maganan, Mami tace “Or… we shouldn’t, tunda likitocin
basu bada umarnin haka ba koh” Shuraim ya gyada mata kai, ta kama hannun Heedayah ta daurata saman gado, ita
fa ta samu TVn ta na farko a duniya wato shuraim da ya juya sai yaga kallonsa take keenly, Mami ma ta rasa kan
wannan kallon da Heedayah ke masa, mikewa Shuraim yyi daga karshe ya nufi kofa don ya gaji da kallon, da sauri
tace “Mami xai tafi” ya juya ya mata wani shegen kallo ta fasa ihu a tsorace ya bude kofa yyi wucewarsa. A waya
Mami ke nuna ma Heedayah da ta makale jikinta hoton Abba, Farida, da Junaid…. Da Mami ta tafi sai Heedayah ta
sa hannu ta dawo da hoton, sai ta kalla yyi na kusan minti biyu sannan Mami ta wuce, ana haka aka bude kofar,
Heedayah ta daga kai da sauri, Sudais ne ya shigo, Mami na nuna mata shi tace “Yaya Sudais, that’s him….”
Heedayah ta dinga kallonsa har ya karaso yana mata murmushi yace “Hi….” A hankali tace “Hello” yace “You get
my voice??” ta gyada masa kai tace “Ya Sudais” Ya wara ido yace “Yess, how are you?” Tace “I’m fine” ta kalli
Mami tace “Mami Yaya fa?” Mami ta kalli Sudais tace “Ina Junaid?” Sudais yace “He told me he will be coming
back later, ya fita” Mami tace “Ina yace maka xai je?” Sudais yace “I have no idea” Heedayah dai sai kallon Sudais
take, ya sakar mata murmushi, ta xaro ido tace “Mami” Mami ta kalli Sudais sannan ta kalleta tace “He smiled at
you, smile back” murmushin ita ma tayi kokarin yi masa. Har yamma Junaid bai shigo ward din ba, Mami da Sudais
ne kadai dakin, Heedayah ta tambayesa ya fi a kirga, daga karshe Mami ta kirasa, yana dagawa tace “Where are
you?” yace “Hotel” Tace “To ka taho yanxu” daga haka ta katse wayarta, ba a dau lkci ba Junaid ya shigo ward din, tun da ya shigo Heedayah ke kallonsa, ya karaso cikin dakin suka gaisa da Sudais ya gaida Mami sannan ya kalli
Heedayah, a hankali tace “Yaya” yace “Ba shi bane” Tace “Toh ai muryarsa ne na ji” Ya d’an saci kallon Mami ganin
kallonsu take yace “Kin san muryarsa ne kike ihu daxu?” Shiru tayi tana kallonsa, ya karasa kusa da ita ya sakar
mata lallausan murmushi ya xauna gefenta yace “How are you?” Ta kai hannu hancinsa a hankali tace “I am fine, is
that ur nose” Ya wara idanuwansa yace “Noo it’s urs” ta kai hannunta nata tana ta6awa, ya ja mata hancin nata yana
murmushi ta mayar masa da murmushin…. Throughout ranan komai Heedayah ta tambaya Mami bata gajiya da bata
amsa don she’s just so curious, she wants to know everything, idan Mami bata gaya mata ba Sudais xai gaya mata
har Magrib, Junaid ne ya kawo masu abinci, wajen karfe takwas xa su wuce hotel dinsu Mami tace “Wai Shuraim
fa” Junaid ya nufi kofa, Sudais yace “I don’t know, ba mamaki ya koma Nigeria ma” Da mamaki Mami ke kallonsa
ya fita yana dariya… Har washegari Mami bata ga Shuraim ba, ta kira Junaid da sassafe tace ya ba Sudais waya,
bayan sun gaisa tace “Ka turo min lambar Shuraim” Sudais ya amsa mata da toh, cikin few seconds kuma ya tura
mata, dialing number tayi, yana fara ringing aka daga, tace “Where are you…” Yace “Ina kwana” tace “Lafiya lau,
kana Ina ne?” Yace “Ina Abuja” Tace “Abuja?” Yace “Ehh, tafiyar ya xo min a gaggawa ne” tace “Toh yayi kyau”
daga haka ta katse wayarta. Dariya Sudais ya dinga yi da Mami ta gaya masa Shuraim na Abuja, yace “I told you, ni
nasan ba karamin aikinsa bane, kadan daga abinda xai aikata kenan” Junaid yace “That’s foolishness” Mami dai bata
ce komai ba… Haka suka ci gaba da kula da Heedayah da ta fara sabawa da abubuwa da dama yanxu, likitocin har
suka bada izinin a dinga fita da ita ana xaga clinic din, xuwa ynxu ta daina tsoron jama’ah sai dai fa idan taga
cinkoson jama’ah jikinta ya dingi rawa kenan, bata son crowd, a haka likitocin suka sanar ma Mami xa su sallamesu
nan da kwana uku. A bangaren Salima kuwa, hotel hotel ta dinga bi tana kwana har ta samu ta harhada kudin
komawa Nigeria, sai da a ranta ta dau kudurin bata kyale Junaid ba….