HEEDAYA CHAPTER 22 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Heedayah ta bude ido a hankali tana kallon fuskar Farida, murmushi tayi ta rungumeta ita ma tace “Farida” sai kuma
ta saketa tana kallon fuskarta, ta wara manyan idonta ta kai hannu dimples dinta tace “Kamar na Yaya” Dariya
Farida tayi tana kallonta, she is so happy seeing Heedayah, Kaka ta nemi waje ta xauna tace “Allah sarki, jininsu ya
hadu wllh, su Rabi’ah da Khadijah dama bakin hali baxae bar su suyi hka ba, uwar tayi kane kane ta hanasu, ko
kulata ma basa yi a gidan, ita ma Deedayar ta kanta take” Farida dake murmushi har sannan ta xamo kasa tace “Ina
yini kaka?” Kaka tace “Lfya lau Farida, ya karatu? Sae yau shi Honorable din ya ga daman sako ki kixo gun uwarki
knn” Farida tace “Aa naje gidan wani kawun mu ne fa kaka ba gidan Baffa nake ba” Kaka tace “Toh baku gaisa da
Shuraim ba, ko baki gansa ba” Juyawa Farida tayi ta d’an kallesa, ya ki juyowa fuskarsa bbu yabo bbu fallasa, ta kyabe baki tace “Ina wuni” still bai juyo ba yace “Lfya” Heedayah sae satan kallonsa take, Kaka tace “Tunda uban
ya samar masa Soja yake amsa gaisuwan kowa cikin isa da gadara, mu dai bamu kulasa ba balle ayi tashin hankali
da shi….” Farida ta mike ta daga Heedayah tace “Ki rakani in je in gaida Mamina” Kaka tace “Aa je ki gaisheta ki
dawo, baki ga ni daya bace parlon, ae ita ke taya ni xama” Farida ta sake hannun Heedayah tace “Toh” daga hka ta
fita dakin, Heedayah na kallon kaka kamar xata yi kuka tace “Kaka don Allah in bi ta, ae xan dawo…” Kaka tace
“Toh kya ci kanki, bi ta ku je, dama amfanin me kike min bnda kallo” Da sauri Heedayah ta juya xata fita parlon tayi
tuntube da kafar Shuraim ji kke tim ta fadi kasa, A tsorace ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace
“Wayyo kayi hkuri…” Ya janye kafarsa bai kalleta ba, kaka tace “Yau naga jaraba, Allah ne shi da xa ki basa hkuri
bayan tika ki da katon kafarsa yyi da kasa, Shureen fa ba Mala’ika bane da kike gigicewa ki tsorata idan kin gansa,
ko meye gamin ki da shi banda Ubansa da yayi sanadin xuwan ki gidan nan??” Mikewa Heedayah tayi ta fita da
sauri, duk gaba daya a tsorace take, kaka tace “Ni dai ba ruwana, kai kuma Shureen ya wnn yarinya Farida na gaishe
ka kana amsa mata a walakance kamar an maka dole? Ba fa yar banxa bace da ka ganta nan, da gatan ta wllh, kuma
da kyar idan ubanta bai fi naka kudi ba duk da ya rasu, snn ga kawunta shi ma gidansa gari guda yyi gaba daya
anguwar nan, bbu abinda bbu a gidan, to a kan me kuma kake amsa mata gaisuwa can ciki ciki? Ka fita kyau ne ko
gayu aka ce maka? kai da ko manyan kaya baka sakawa sae na tsigalallu” Ya juya yana kallon kaka yace “Na hada
wani abun ne da ita? Kin ga ki daina min shisshigi a lamarina, bbu ruwanki da harkata, dole aka ce maki sae na amsa
gaisuwarta ko ina da wani alaka da ita ne??” Bai jira cewarta ba ya mike ya fice daga dakin, kaka ta nemi kujera ta
xauna a hankali tace “Ikon Allah, Amadu dai ya ja mana bala’i, muna xaman xaman mu yace xai kai sa Soja gashi
tun ba a je ko ina ba ya fara kilewa…. To banda bala’i yaushe har Shureen ya fara magana da har xae xageni ya fita,
dama haka sojojin suke bani da labari??” Washegari Monday da safe Mami ta koma bakin aikinta, Farida ta gama
duk abinda xa su yi da Heedayah a bangaren Mami suka fito, Heedayah na sanye da wando da riga sai hula da ke
kanta, sosai kayan suka yi mata kyau kamar yar turawa ga gashinta da ta baxo ta cikin hular, Farida kuma Abaya ta
saka da veil dinsa, ta kulle bangaren Mami suka wuce gaida Kaka a dakinta, Kaka tace “To ita Deedayah me yasa
Rakiya bata siya mata irin wnn kayan na jikin ki ba, ko don ba ita ta haifeta ba sai tayi ta sa mata kayan anna??”
Farida dai bata ce komai ba, haka ma Heedayah, Farida ta mike tace “Kaka xa muje tsakar gida mu dawo” Daga
haka Farida ta kama hannun Heedayah suka fita dakin, Kaka ta kyabe baki tace “Wnn faridan ta fiye rawan kai da
iyayi kamar dai uwarta, ba don wannan halin nata ba dai Shureen xai aureta, banda dai kowa na son inda nasa xai
huta ai wnn rawan kan nata ya fi karfin Shureen” Garden din cikin gidan Farida suka tafi da Heedayah, suka xauna
kan kujeran dake garden din Farida na kallonta tace “Toh ko na nuna maki yanda ake operating wayar ai ba siya
maki Mami xata yi ba, nima fa Baffanmu ne ya siya min, kuma da kyar ta bar ni na rike…” Heedayah ta langwabar
da kai tace “Ae Yaya xan ce ya siya min ko Yaya Sudais” Farida tayi dariya tace “Toh shkkn, nasan Yaya xai iya siya
maki, shi kinsan babu ruwansa” Tsakaninta da Allah ta shiga nuna ma Heedayah ynda ake amfani da waya da
abubuwan dake cikin waya tun daga lock button, Heedayah ta maida hankali kai kace karatu take dauka… Tun da
suka shigo garden din Shuraim dake xaune sama yana karatu a laptop dinsa ya mayar da laptop din gefe yake
kallonsu, su kam ko lura da shi basu yi ba, can ya mike ya bar wajen, Farida ce ta fara hangosa yana tahowa toward
them bayan ya sakko downstairs, tayi kasa da murya tace “Wannan Yaya Shuraim din is coming” Sosai Heedayah ta
rikice a gun, ta dinga cewa “Farida tashi mu tafi yana yi ma mutane duka wllh, ki tashi mu tafi….” Farida ta hade rai
tace “Toh ba sai ya doke mu ba” Har dai ya iso kansu, yana kallon Farida yace “Me ku ke yi a nan?” Farida ta d’an
kallesa tace “kawai labarin mu muke” yace “You are showing her how to operate phone right?” Tace “Yea…. sannan
muna hiran makaranta” ya mika mata hannu yace “Bani wayar” Mayar da wayar Farida tayi bayanta ta hade rai tace
“As in how?” Yace “Baxa ki bani ba” A takaice tace “Gaskiya….” Mikewa Heedayah tayi ba tare da ta yarda ta
kallesa ba xata bar wajen yace “Kina kara step daya sai na 6allaki” Tsayawa tayi, tayi narai narai da ido, sai dai taki
yarda ta juyo ta kallesa, Farida ta mike xata bar wajen ya riketa ya kwace wayar a hannunta, tsaye tayi tana kallonsa
tana huci, yace “Daga yau…. Ina nufin daga wannan moment din ko by mistake kika sake xaunar da ita kina nuna
mata waya sai kin sha mamaki a gidan nan” Farida tace “Toh ai wayana na nuna mata ai ko? Kuma ni ka bani
wayata….” Ya mata wani kallo ce “Ki kwata mana” Kallon Heedayah yyi ya kara daure fuska yace “Uban me xa kiyi
da waya da kika xauna tana nuna maki ynda ake amfani da shi” Heedayah ta girgixa kai bata ce komai ba, strictly
yace “Juyo Ina maka maki magana” A hankali ta juyo tana facing dinsa idonta har ya kawo ruwa, ya kara shan kunu
yace “Ke kika ce ta nuna maki waya ko?” Ta girgixa kai bata ce komai ba, yace “Toh na sake ganin ki xaune ana
nuna maki waya sai na xane ki a gidan nan, daina kallona” Ta sauke idonta kasa hawayen ciki ya xubo, a fusace
Farida ta bar wajen kamar xata tashi sama, Shuraim ya bi ta da wani kallo har tayi corner, yana kallon Heedayah
yace “Start going” juyawa tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya har suka shiga cikin parlor sannan ta juya suka
hada ido, daure fuska yyi ta nufi dakin Kaka tana goge idonta, Kaka dake ta sauraron Farida ta sauke wani ajiyar
xuciya tace “Toh, a gaskiya ni dai baxan iya tunkaran Shureen ba ynxu don ya xama abinda ya xama, rashin kunya
yake ma kowa gadan gadan, Kuma ni ban san ko har sojojin sun basa bindiga ba inje in ja ma kai na, yo in ja ma
kaina mana, yanxu sai ki tashi mu tafi bangaren uwarsa nasan tana can tana baccin asara kin san me xaman banxa, nasan ita idan tayi masa magana xai ji” Heedayah na shigowa dakin kaka ta fashe da kuka ta fada kan gado har da
Shessheka, kaka ta mike da sauri tace “Lafiya, me ya faru, ni dai na shiga uku, kukan me kike” Kuka kawai
Heedayah take, Farida tace “Shine ya doketa kila” Kaka tace “Ya doke ki???” Da sauri Heedayah ta mike xaune tace
“Aa bai dokeni ba fa” Kaka tace “To kukan me kike” ta girgixa mata kai kawai, Kaka tace “Oho ni ban iya wahala,
tashi mu je gun uwar tasa Farida, dabanci kawai Shureen ke ji a gidan nan kwanan nan” Tare Farida suka fita da
kaka xuwa bangaren Mumy, Khadijah na xaune parlor tana kallo, kaka tace “Gantalalliya abinda kika iya kenan, Ina
Rabi’ar?” Khadijah ta wani daure fuska tace “Ta tafi gidan Aunty Asma’u” Kaka tace “Ta tafi gidan Asma’u? Shine
bata sallameni ba? Wai me yasa Amadu ke min haka ne a gidan nan kamar ba uwarsa ba, ynxu fa a kullum da kyar
ku ke shigo min bangarena sau daya, Mata duk ta kanainaye ku bata son ku ra6i kowa na gidan nan kullum kuna
kunshe a daki?? Toh bari ya dawo shi Amadun” Mumy na daki duk tana jin kaka, kafin ta karasa cikin dakin tayi
saurin fitowa, Kaka na ganinta tace “To Shureen ne ya kwace wayar Farida, kuma dubu dari biyu aka ce an siya
wayar, to siyarwa yake da niyyar xuwa yyi shine ban gane ba” Mumy tace “Ni kuma ina naga Shuraim da safen nan
kaka?” Kaka tace “Aa ba ruwana ki fita ki nemosa duk inda yake ya maido ma yar mutane wayarta kafin ya tafi
chechenia da shi a shiga uku” Mumy ta kalli Farida daga sama har kasa, Farida tace “Ina kwana” a walakance Mumy
tace “Lafiya” Kaka tace “Yar gidan Rakiya ce fa, daga makarantar kwana suka yi hutu ta xo mana shine har xai saka
mata ido a gidan ya kwace mata waya to ina ruwansa da ita idan ba neman fitina ba, daga ance an samar masa Soja
sai ya xame mana ibilisu a gida??” Mumy tana wani kyabe baki tace “Toh ni ban san inda Shuraim yyi ba tun asuba
da ya shigo ya gaisheni ban sake ganinsa ba wllh” kaka tace “Toh ai nemosa nace xa kiyi idan ba haka ba wllh sai in
ja ta mu tafi gidan yan sanda su san abinda ake ciki, muka san ko sojojin kwacen wayar mutane suka sa shi” Tana
fadin haka ta kama hannun Farida suka fita, Mumy ta bi su da wani irin kallo. Har Mami ta dawo da yamma
Shuraim bai ba Farida wayarta ba, barin gidan ma yayi gaba daya, Mami ta tabe baki bayan ta gama sauraron farida
tace “To uban wa xa kiyi ma kuka?” Farida ta kara rushewa da kuka tace “Wllh Mami bbu abinda muka yi masa
kawai ya amshe wayata” Mami tace “Me kike yi da wayar ya amsa?” Cikin kuka tace “Babu komai wllh” Mami tace
“Toh ai shkkn, dama nima na gaji da shegen wayar da kike rikewa” Tana fadin haka ta shiga daki, Heedayah dai na
xaune parlon tayi shiru, can ta mike ta isa gun Farida tace “I am sorry I caused you all this Farida, da bance ki nuna
min ba baxai amsa ba” Farida tace “Ai wllh sai ya bani wayata, you caused me nothing” Kaka ce xaune parlon Abba
da Farida, Heedayah ma na xaune kusa da kaka, Abba yyi shiru yana sauraron kaka, kaka tace “Toh a gaskiya bbu
ruwana kar ya ja mana fitina muna xaman xaman mu, a nemo sa duk inda ya shiga ya ba yar mutane wayarta” Abba
na kallon farida yace “Me kike yi da wayar ya amsa?” Ta girgixa kai a hankali tace “Babu abinda nake yi Abba, ni da
Heedayah ce ma a xaune lkcn” Kaka tace “To me xata yi da wayar banda karatu kaji ka da wata magana, bbu abinda
suke yi vanda karatu” Abba yace “Toh shkkn xan nemi Shuraim din” mikewa kaka tayi ta nufi kofa tace “Ku taso mu
je, shi da ya sa shi a sojan su karata can” Mikewa Farida da Heedayah suka yi suka bi bayan kaka. Shuraim na tsaye
dakin Mumy dake ta masa fada kamar xata ari baki, shi dai bai ce mata komai ba, tace “Banda ka haifi yaro baka
haifi halinsa ba ina ruwanka da lamarin su a gidan nan? Ka hada wani abu ne da yarinyar da xaka amshe mata waya
da sunan discipline? Ina ruwanka da ita nace” ya shafa kansa still bai ce komai ba, tace “Toh wllh ka kiyayeni a
gidan nan, banda baka kishina kai ko kallon yar nan xaka yi balle ka amshi wayarta Aliyu” Wayarsa dake hannunsa
ne ya fara ring, Mumy tayi shiru tana kallonsa, yace “Abba na kirana” Mumy tace “Wannan damuwarka ce, ni dai
idan har baxaka fita hanyar makiyana a gidan nan ba to wllh sai dai ka canxa wata uwar ba ni ba” juyawa yayi ya
nufi kofa ya fita, a main parlor ya tadda kaka tana dube dube kamar munafuka, tana ganinsa ta hade rai ta hau
kakkabe kujerun parlon tana cewa “Mata duk kazamai kawai” yayi wucewarsa bangaren Abba, tana ganin haka ta
nufi dakinsa da sauri ta shiga tana kalle kalle, saman madubi ta ga wayoyi har biyu a ajiye da dubu biyar ta kwashe
duka ta fice. Shuraim yace “Abba Heedayah take koya ma ynda ake operating waya shi yasa na amshe” Abba yyi
shiru yana kallonsa haka ma Mami dake parlon tana xuba ma Abba abinci, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda
take, can Abba yace “A ina ka gan su?” Shuraim yace “Can baya” Abba yace “That’s wrong, and you did the right
thing collecting the phone, ka rike wayar wajen ka nan da kwana biyu sai ka bata” Shuraim ya dago kansa yace “Ita
ma bai kamata ta rike waya ynxu ba, she still in Jss2 I think” Abba yace “Haka ne but assuming a gidan nan take ni
baxan bari ta rike waya ba, but tunda ba a nan take ba we have no say, ka maida mata wayarta after two days…”
Shuraim yace “Idan xata koma makaranta xan bata amma ba ynxu ba” Abba ya kalli Mami da bata kalli Inda suke ba
yace “Ur opinion Rahinah” Mami ta kallesa tace “Duk ynda kayi dai dai ne barrister” Abba yace “Alright, ka bar
wayan gun ka Shuraim” Shuraim yace “Toh shkkn” daga haka ya mike ya fita parlon. Karfe tara da rabi kaka na
xaune dakinta ta daura kafa daya kan daya ta gama cinye kazar da Junaid ya kawo mata tana sakace hakori Shuraim
ya shigo, tana ganinsa ta ci gaba da sakace sakacenta tana lumshe ido, ya bi dakin da kallo sannan ya juya ya fita,
bangaren Mami ya nufa ya bude parlon ya shiga, bbu kowa parlon amma yana jin muryarsu a daki, karasawa yyi
bedroom din ya bude kofar, Xaune suke kan gado suna kallo a laptop din Farida, Heedayah na sanye da yar rigar
bacci iya cinya haka ma Farida, Farida ta xaro ido, da sauri ta rufe jikinta da Pillow tana kallonsa, Heedayah ta
sauka saman gadon da gudu ta shige bandaki ta rufe, yana kallon Farida yace “Bani wayar da kika shiga dakina kika dauka” Ta xaro ido tace “Ni?? I didn’t take any phone wllh, tun daxu muna kallo a nan ban fita ba” ya fi minti daya
yana kallonta sannan ya juya fice daga dakin, ya koma dakin kaka, kaka ta kallesa tace “Sojojin ne suka baka pareti
da daddaren nan, naga ka shigo daxu baka ce min komai ba, gashi ka sake dawowa” Yace “Ina wayoyin da kika
dauka a dakina?” Kaka ta mike tsaye ta wani xaro ido tace “Wayoyi kuma?” Yace “Ehh” Ta nemi waje ta xauna har
ta fara salati sai kuma ta sakar masa kuka tace “Tunda uwata ta haifeni bbu wanda ya ta6a tsareni yana tuhumata a
kan sata, satar ma ta waya, Shureen in rasa abinda xan sata a gidan nan sai waya? Ashe ma gantalalliyar barauniya
ce ni, in saci motocin Amadu in gudu mana idan haka ne, Amma sai ka shigo min tsakar dare kace Ina wayar da na
sata??” Shuraim ya gyada kai ya juya ya fita dakin. Bai sake maganar wayar ba har gari ya waye, Farida na share ma
Kaka dakinta, Heedayah na kwance saman gado tana kallo a laptop, kaka tace “Shiru Shureen bai sake shigowa
nemo waya ba gashi har karfe goma ko dai ya hakura ne, ni dubu biyar din ma kasuwa xaku je min ku siyo min
kayan ciki in narka uban farfesuna mu yi sati muna ci, kayan cikin dubu biyar ai xai cika wancan kwallan ko?”
Farida ta juya tana kallon katon abinda kaka ke nuna masu, kaka tace “Har yawuna ya tsinke maxa gama sharan ku
tafi da wnn mara amfanin ku siyo min kayan cikin” Farida tayi kasa da murya tace “Ke dai kar kice masa komai a
kan wayar ki ci gaba da boyewa” Kaka tace “Toh da fa, ai ni tasa wayar ma da kyar idan ba chechenia xa ku rakani
ba in siyar da ‘yar banxa in siyo kan saniya inyi farfesuna” Farida ta fashe da dariya har da kyakyatawa, murya can
kasa tace “Xan raka ki wllh, gashi naga shi ma IPhone din ne har ya fi nawa” Kaka tace “Toh ko in shirya yanxu?”
Farida tace “Shirya” mikewa kaka tayi xata fiddo da sabon kayanta, Ganin cup da Heedayah ta sha shayi ta kalli
Heedayah dake kwance tace “Kai ni dai wnn yarinya ta isheni wllh, kwata kwata ba a morarta, son jikinta har tsoro
yake bani ni dai, to Amadu kike jira ya dauke maki kopin nan ko Rakiya??” Heedayah ta sakko saman gadon ta dau
cup din ta nufi kofa kaka ta bi ta da harara tace “Toh meye ma amfanin bude idon da Amadu ya kai ki aka yi idan ba
asaran kudi ba” Heedayah na fita dakin ta wuce kitchen, Khadijah dake xaune dining ta bi ta da harara, ita dai ko
kallonta bata yi ba, ta bude kofar kitchen din ta shiga, ta ajiye cup din a sink kenan ta ga Shuraim tsaye kitchen din
yana hada shayi, sunkuyar da kanta tayi xata fita, yace “Zo nan” kin tsayawa tayi ta ruga da gudu ya kamata kafin ta
isa kofa, kuka ta sakar masa a tsorace tace “Ni ban yi komai ba wlh, kaka ce tace in kawo cup din kitchen” leka
parlor yyi ganin Khadijah ya rufe kofar kitchen din, har wani rawa jikinta yake yi sbda tsoro, ya jinginar da ita da
kofa yace “Wa ya shiga dakina ya dau waya?” Ta bude hannu da sauri tace “Nima ban sani ba, bani bace wllh” kalle
kallen kitchen din ya fara yi taga ya kallo inda muciya yake, xaro ido tayi ta rungumesa a rikice tace “Wllh Kaka ce
ta dauka ta boye a dakinta, a cikin akwatinta ta boye” Bai san lkcn da yyi murmushi ba yana kallonta duk da ta boye
fuskarta jikinsa, a hankali cikin rawar murya tace “Yanxu xa su je su siyar da wayan da Farida”Bude kofar Shuraim yyi bata jira yace ta fita ba ta sakesa ta fice da sauri… Dakin kaka ta koma, kaka tace “Me ya
tsayar da ke kitchen din, ko wanke wanke kika yi?” Heedayah ta girgixa mata kai ta xauna gefen gado, gaba daya a
tsorace take har lkcn, kaka ta gama saka sabon kayanta na xuwa chechenia tace “Nima dai da neman magana nake,
wata Deedaya ce xata yi wanke wanke kamar an tsine mata Allah na tuba” Farida ta gama tattara dakin kaka tace
“Ajiye masu tsintsiyar da makwashin sharan a nan bakin kofa mai aiki xa ta kwashe ki shirya mu wuce, daga
checheniar dama sai mu biya bakin dogo bbu irin k’an san da basu siyarwa sae mu yi ciniki, ita wannan Deedayar
dama ta xauna gida kar taje tana mana lagwai lagwai a kasuwa in shiga uku” Farida tayi yanda Kaka tace sannan ta
dau mayafinta ta yafa, duk ta kagu su tafi siyar da wayar Shuraim, dama tuni ta amshi nata ta kai dakin Maminta ta
boye, kaka na bude akwatinta ta ciro wayar kenan Shuraim ya bude kofar dakin ya shigo, da sauri ta boye wayar
bayan jakan hannunta na rawa ta daga jakar ta mike tsaye, Kai kana ganinta kaga rashin gaskiya karara, cikin rawan
baki tana kallonsa tace “Ha’an… yau ma baka tafi Zarian ba? Sannan yaushe xa a fara kwasan sojojin ne” Yace “Ban
tafi ba, Ina kwana?” Tace “Lafiya lau, ynxu na shirya nace wannan yarinya Farida ta raka ni gidan Ta sallah kwana
biyu ban je ba ita ma bata xo ba, gashi ka shigo ni kuma xan fita” Yace “Ohk, ko in ajiye ki?” Da sauri tace “Aa ba
ruwana da ba mutane wahala ga dai adaidaita ta ko ina, kayi tafiyar ka kawai kar in wahal da kai” Farida dai ko
kallon Inda yake bata yi ba ta bi gefensa ta fita dakin, Heedayah tuni ta kwanta kan gado ta rufe idonta, kaka tace
“Toh mu je xan kulle dakina ne Shureen, kema Deedayah ki fita kije gun Rakiya ki kwanta baxan iya barin dakina a
bude ba” Shuraim ya karasa Inda take tace “Ina kuma xaka kana jin ina ce maka xan fita??” Bai saurareta ba ya isa gun akwatin ya duka ya dau wayarsa da yake hangowa bayan akwatin ya fice daga dakin, kaka ta kasa kwakkwaran
motsi inda take tsaye, can dai tace “Toh Allah ya isa” sai kuma ta xauna gefen gado ta goge xufan da ya karyo mata
a goshi cikin rawar murya tace “Allah dai ya isa” A cikin satin nan Abba ya ba Mami kudi don yi ma Heedayah
siyayyar da ya kamata na xuwa boarding, bbu abinda Mami bata siya mata ba har da nata karin, duk dakin kaka ake
ajiye kayan gudun fitinarta, ranan Friday karfe uku saura Heedayah na xaune Main parlor tare da Farida dake
karatun wani literature dinsu, Heedayah kuma tun safe take ta rubutu a exercise book kamar yanda Mami ta umarce
don har sannan writing dinta isn’t good duk da tana kokari, Salima da Rabi’ah kuma na can gun dinning, Rabi’ah na
mata tsifan uban attachment din kanta, sbda lalacewa kuma a kan dinning, Bude kofar parlon aka yi Sudais ya shigo
da sallama, daga Heedayah har Farida suka dinga kallonsa har ya karaso parlon, sanye yake da gezner fari kal,
mikewa Heedayah tayi ta sakar masa cool smile tace “Ya Sudais” Ya buda mata manyan idanuwansa a hankali yace
“Yes Cutie” karasawa tayi kusa da shi ta rungume sa tace “I missed you” Farida dai kallonsu kawai take, haka
Salima da ta juya kanta tana kallon ikon Allah, Sudais ya maida Heedayah gefensa yana kallon Farida yace “Hi” ta
d’an yi murmushi tace “Hello, ina yini” yace “Lafiya lau, Farida right” tace “Sure” yace “Ya hutu?” Tace “Alhmdllh”
ta gefen ido Heedayah ta bi Shuraim da ya shigo da kallo, direct dakinsa xai wuce ganin Salima da Rabi’ah a dinning
ya tsaya yace “Duk gidan nan ki rasa inda xa kiyi tsifa sae wajen cin abinci Salima” Ta kyabe baki sbda bata son
fitina ta fara tattara gashin dokin nata, yau dai shima manyan kaya ne jikinsa, Sudais dama sau daya ya kalli
direction din Salima shi ma sbda Rabi’ah da ta gaishe sa, ya amsa gaisuwarta, ya na kallon Heedayah yace “Kaka na
dakinta?” Heedayah tace “Aa ta je anguwa” Ya d’an bude ido yace “Anguwa Kuma?” Tace “Ehh gidan frnd dinta
tace xata tafi, Mami ce ta wuce da ita da safe” Yace “Ohk, ya preparation din tafiya makaranta?” A hankali tace “I
am scared ya sudais” yace “Noo don’t be dear, you will like it in there, many of ur mates are there” Tace “Toh baxan
kara ganin Mami da Abba ba?” Yace “No xaki dinga dawowa hutu ai, ba ga Farida tana dawowa hutu ba ita ma, tare
xa ku je sannan ku dawo tare” a hankali Heedayah tace “Toh” Ya kalli Farida yace “Junaid na nan kuwa?” Farida
tace “Yana Abuja, amma xai dawo Saturday” Sudais yace “Yes yace min xai je can, but two days ba mu yi waya ba”
Shuraim na fitowa daki Sudais ya mike Heedayah ta xaro ido, murya can kasa tace “Ya Sudais wucewa xaka yi?” Ya
mata murmushi yace “Yesss but xan dawo” tace “Me yasa ka daina xuwa?” Yace “Sbda bana nan Cutie” Tace “Toh
har in tafi makaranta baxan ganka ba?” Yace “Aa ni xan kai ki makarantar ai” Ya ja dogon hancinta yace “Byee sai
na dawo” Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo da sauri yace “Bye Farida” tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ya
fita, Heedayah ta koma gun Farida ta xauna. Salima ce xaune dakin yayarta tana sauraron abinda take gaya mata,
can dai ta tabe baki tace “Toh wai Yaya ke yanxu meye damuwarki, ita fa matar nan ba sanin kina yi take ba kullum
ta fita da safe sai yamma take dawowa, ita kanta wnn makauniyar da ta ja maki komai yanxu makarantar kwana xa a
kai ta aka ce to ba shkkn ba, a ina xaki dinga ganinta kina jin takaici kuma??” Mumy ta kunduma mata xagi tace
“Dama ke kinsan ciwo na ne, ai damuwata ba taki bace, kin gwammace kiyi ta yawo gari gari…” Mikewa Salima
tayi tace “Aa kar ki bata min rai Yaya, taya kike son in tafi in ajiye maki laya a dakinta bayan ba shiga dakin nata na
saba yi ba, ba gwara ki ba wa ennan fitsararrun yaran naki ba da basa girmama mutane” Mumy tace “Shkkn ni kuma
bani da sirri sai in bari yarana su ji wnn magana, ke ma don kina ‘yar uwata ne shi yasa nake neman taimakon ki”
Salima tace “Kai gaskiya Yaya Ina ga da kamar wuya…” Mumy tace “Haka xa kiyi min Salima?” Salima ta wani
murguda baki ta dauke kai, Mumy tace “Toh shkkn, tashi ki wuce, amma ai kina ma Salaha wanda ya fi haka”
Salima tace “To Salaha ai biyana take yi ita” Mumy tace “Toh ni nawa xan baki?” Tana taunar cingam din bakinta
tace “Dubu hamsin” Mumy ta mata wani shegen kallo tace “Toh bani da shi, idan xaki amshi dubu ashirin gashi nan
yanxu” Salima tace “Toh kawo” tashi Mumy tayi ta dauko mata dubu ashirin din ta bata, sannan Salima ta amshi
katon layan ta saka a karamar jakarta ta sa cikin handbag ta mike ta fita, Mumy ta sauke wani ajiya xuciya tace “In
sha Allahu komai ya xo karshe sai dai idan ba uban kudina na kashe ba” Da daddare Salima ta fito da uban kayanta
da aka wanke ta ba talatu Mai aiki tayi mata guga aka bude kofar parlon, Abba ne ya shigo tare da Junaid, Sosai
gabanta ya fadi ganin Junaid, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsarsa, bbu wanda xai kalli junaid
sau daya ya kauda kai, he is just too handsome, komai nasa is almost perfect, tayi kasa da kai ta gaida Abba, ya amsa
yayi wucewarsa Parlonsa, Bangaren Kaka Junaid ya nufa, Salima ta bi sa da kallo a hankali cikin sanyin murya tace
“Welcome Jayy” Banxa yayi mata har ya shiga dakin, Salima ta wuce bangaren Mami ta bude kofar ta shiga da
sallama, Mami na xaune parlon tana hada ma Farida da Heedayah kayansu don gobe ne tafiya makarantar, Mami ta
daga kai tana kallonta, Salima na murmushi ta gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa tace “Ya kike” Tace “Lafiya lau
wllh ya aiki” Mami tace “Alhmdllh” Farida ta gaida Salima, ganin haka Heedayah ma ta gaisheta, Salima ta amsa da
fara’a sannan tace “Dama wllh dutsen guga na xo amsa Aunty, na Mamansu Khadijah ya lalace, Shuraim kuma
kamar bai nan” Mami tace “Ohk yana can daki dauko mata Farida” Xaunawa Salima tayi saman kujera tana ta kallon
Heedayah ganin wani kyau take karawa kamar wata baindiya, ga gashinta da yyi tsayi sosai, Cikin dubara ta dinga
saka hannu cikin rigan mamanta da yake hijab ne har kasa jikinta kuma layan na cikin rigan maman, Har ta fiddo
idonta na kan TV kamar me kallo, a hankali ta ciro hannunta ta cikin hijab din tana kokarin tura layan cikin kujera
aka bude kofa, juyawa tayi da sauri, Junaid ya shigo da sallama, da sauri Heedayah ta mike xaune sai dai bata yi gigin xuwa kusa da shi ba sbda warning din da Mami tayi mata daxu don ta rungume Sudais da ya shigo, Junaid da
idonsa ke kanta shi ma ya xauna kujeran dake facing Salima, Mami na lura da kallon da yake ma Heedayah ta dai ci
gaba da hada kayan da take yi cikin jaka, Heedayah ta sakar masa murmushi tace “Good evening Yaya” yace
“Evening how are you?” Tace “I’m fine” Kallon Mami yyi yace “Mami ina yini” Mami tace “Lafiya lau ya hanya?”
yace “Alhmdllh” Salima da ta gama narkewa Inda take xaune tana kallon Junaid cikin tattausan murya tace “Ina
yini?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Lafiya lau” Farida ta mika mata iron din hannunta tace “Ga shi” amsa tayi tace
“Nagode” Kasa tura layan tayi cikin kujeran sai kallon Junaid kuma take, can ta mike hannunta na rike da layan a
cikin hijab tace “Toh nagode” Mami tace “No thanks” daga haka ta nufi kofa, Junaid ya bi ta da kallon gefen ido.
Salima na shiga dakin Mumy, Mumy ta mike da sauri tana murmushi tace “Kaddai har kin sa” Salima ta wani turo
baki tace “Gaskiya baxan iya ba Yaya” Still Mumy tayi tana kallonta tace “Baxa ki iya me ba?” A takaice Salima
tace “Yin abinda kika ce in yi mana” Mumy ta dake tace “Saboda me?” tace “Ni fa wllh yaya son Junaid nake, so ba
na wasa ba kuma, ni ban jin ma xan iya rayuwa babu shi, ganinsa fa ya sa na kasa saka layan a kujera wllh” Bude
baki Mumy tayi tana kallonta can ta mika mata hannu tace “Toh bani” Salima ta fiddo layan ta mika mata, Mumy ta
kwace a mugun fusace ta kunduma mata xagi tace “Amma ke dai Allah ya wadaran ki wllh, Junaid din banxa, meye
hadin ki da wani shegen junaid da xaki bakanta min sbda shi, toh bani kudi na tun wuri kada in fasa maki kai yanxun
nan a dakin nan” Mikewa Salima tayi ta nufi kofa da gudu tace “Har na bada deposit din Human hair weave-on da
kudin, bani da shi bani da dalilinsa” daga haka ta fice daga dakin. Kuka ne kawai Mumy bata yi ba ta rasa yanda
xata yi kuma ranan aka sa ta saka layan a bangaren Mami, ance mata duk runtsi kada ya wuce yau ganin lkci na
wucewa ta mike tana kallon agogo dake nuna karfe goma da wani abu, a jikinta ta saka layan sannan ta dau hijab
dinta ta sa, ta bude gun kayanta daga kasa ta dau sinkin sabulu biyu da omo manya biyu ta nemi yar leda me kyau ta
xuba su a ciki sannan ta fita xuwa main parlor, cike da karfin hali ta nufi bangaren Mami, ta bude kofar da sallama,
Kaka ta tarar a parlon tsaye Mami na kara fiddo mata sauran siyayyan da tayi daxu tana nuna mata, kaka ta juya tana
kallon Mumy tace “Waye wnn?” Mumy na murmushin karfin hali tace “Ni ce kaka, Ashe baki yi bacci ba” kaka tace
“Inyi baccin lafiya gobe yara xa su wuce makarantar kwana” Mumy tace “Allah sarki…” Xaunawa tayi saman kujera
tana kallon Mami tace “Mun yini lafiya?” Mami tace “Alhmdllh, ya aiki” Mumy tace “Mun gode Allah, da safe yara
xa su wuce koh?” Kaka tayi saurin cewa “Aa, mu ma dai bamu sani ba bamu da tabbas, kila a daga tafiyar tasu ma”
Mumy tace “Allah sarki, toh Allah ya kai mu lafiya, ga wannan dai babu yawa” Kaka tana kallon ledan da take
mikowa tace “Meye wnn din” Mumy tace “Aa d’an sabulu ne da omo” kaka tace “Toh ai gashi nan har ya masu yawa
naji Rakiya na cewa ma ba duka xa su kai makarantar ba” Mami na kallon Mumy ta mike ta amsa tace “Allah ya
amfana Hajiya, an gode” daga haka ta ajiye ledan gefen kayansu Farida, Mumy da har ta cusa layan hannun cikin
kujeran taji ya shige can kasa ta mike tana murmushi tace “Aa bbu komai wllh, sai da safe” Mami tace “Allah ya
tashe mu lafiya” Mumy ta fita parlon, kaka tace “Kiji Ina batun ta maida kayanta ki wani tashi ki karbe Rakiya?
Makira ce fa Maryam, to ni dai ba ruwana” Mami dai bata ce komai ba, Kaka tace “Haka kawai mata ta shigo mana
tsakar dare tana tambayar yaushe ne tafiyar, nasan da bana parlon nan tonawa xaki yi ki gaya mata, ai mugu baka sa
shi a harkan ka, muka san abinda ke xuciyarta” Mami still bata ce da kaka komai ba ta ci gaba da abinda take.
Washegari da ya kasance lahadi, karfe goma na safe Mami ta shiga parlon Abba ta dalilin kiranta da yyi, as usual
laptop dinsa na gabansa, ta xauna tace “I’m here barrister” Bayan kusan minti biyar ya dago yana kallonta yace
“Dama nayi wata shawara ne daga jiya xuwa yau Rahinah” Mami na kallonsa ganin mood dinsa is awkward, a
hankali tace “Shawarar me fa Barrister?” Abba yace “Ina ga xa a bar xancen tafiyar Heedayah boarding” da mamaki
Mami ke kallonsa, da farko kasa cewa komai tayi, can dai cike da karfin hali tace “Ko saboda me Barrister” yace
“That’s my decision” ta girgixa kai tace “Noo ba a yanke irin decision din nan without reason, ka gaya min dalilin
hakan Barrister” yace “You are not to question my order Rahinah” Da mamaki sosai take kallonsa, tace “I am not
questioning you, I’m asking for ur reasons” Yace “Nace Heedayah baxa ta je boarding ba, I think I have done all
what I am suppose to do for her, bbu wani da xai min tilas kuma, beside I have other commitments….” Mami tace
“As in?” Yace “That is it” Ta girgixa kai tayi shiru, can ta kallesa tace “Are you talking of the expenses?” Yace “If
you think so” Mami ta fi minti biyu ta rasa abun cewa, can ta girgixa kai tace “Ohk fine, the bills are on me you
don’t worry, in sha Allah” tana fadin haka ta mike xata fita, Abba yace “Bill or no bills banyi ra’ayin ta tafi boarding
ba, xa ki iya biya mata kudin day amma ba boarding ba” juyowa tayi tace “Sorry… but are you sure you are okay
Ahmad?” Yace “What are you insinuating?” Tace “Naga dai nace indai don kudi ne kada ka damu xan biya….” Abba
yace “Toh makarantar ma gaba daya nayi canceling dinsa, she should stay at home, you have no issues with that”
Mami ta kara kallonsa da kyau, bata kuma cewa komai ba ta fita, Dakin kaka ta wuce, Kaka da tayi wanka tun asuba
xata yi rakiyar yan makaranta ganin Mami tace “Komai mutum xai yi ya dinga yi ido na ganin ido, yanxu
fisabilillahi sai dare yyi muyi ta cin karo da juna xa mu kai yara makaranta?” Mami ta xauna saman kujera tace
“Kaka ban gane abinda Barrister ke nufi ba fa….” kaka ta xauna da sauri tace “Lafiya?? Cewa yayi kar aje da ni ko?”
Mami tace “Aa” nan ta koro ma Kaka duk yanda suka yi da Abba, kaka ta saki baki tana kallon Mami, can tace “To
wiwi ya sha daren jiya kafin ya kwanta ne, ko lalacewa ce ta samesa, ko bala’i ne ya fada masa duk a daren jiyan?” Mami dai bata ce komai, kaka tayi wani dariyan boss tace “Ahaf, ba ina yawan ce maku bamu san xuciyar Amadun
ba a kan Deedayah amma kun ki amincewa da ni, to yau dai anyi walkiya mun ganosa, yau mun ga irin xuciyarsa,
kuma makarantar kwana kamar Deedayah ta tafi ta gama, ai ba shi kadai na haifa ba a duniya, iyaka in kira Umaru
ya xo ya kai ta ya biya komai, ni ai ban gaji da amanar da Allah ya bani ba in shi ya gaji, Deedayah fa Amanar Allah
ce a wajenmu wllh wllh, to duka duka nawa ya kashe mata da xai nuna gazawa banda lalacewa ta samesa, Allah ya
sa ya kashe ya kai dubu dari a kanta, shi ma dubu darin sbda gyaran idon da ya kai ta aka mata, to wllh ki fita
harkarsa ga wayata ki kira min Umaru, idan shi ma yace bashi da kudi ban ki in daga fili na in siyar in kai Deedayah
makarantar kwana ba balle ma baxai ce min haka ba, d’an Albarka ne shi din” Tana fadin haka ta dau wayarta ta
mika ma Mami tace “Xa ki ga an sa Dakta ki kira min shi” Mami ta sauke ajiyar xuciya don har lkcn mamakin Abba
take tace “Aa ki d’an dakata kaka” A fusace kaka tace “Ki kira min shi nace Rakiya, in dakata a kan me, ki nemosa ki
kira min shi dalla” Amsan wayar Mami tayi ta nemo lambar Baffa tayi dialing sannan ta mika ma kaka.