HEEDAYA CHAPTER 26 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 26 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Rungume kaka Heedayah tayi ta kankameta cike da murnan ganinta, rabonta da kaka tun da suka yi hutun jss3 third 

term, sae da kaka ta kare mata kallo daga sama har kasa sannan ta turata tace “Aa ni ki rufa min asiri kar ki cuceni ki 

kada ni kasa ana bikin jikokina, ki bar ganin kin tsayince kamar falwaya, nima ina yan mata haka nake duk da dai 

yanxun ma ni ba guntuwa bace” Mami tayi dariya ta xauna tace “Sannu kaka….” kaka tace “Yanxu Rakiya 

fisabilillahi auren ‘ya yan Umaru fa ake kika ki xuwa sai yau, ke da ya kamata ace tun ana sauran sati daya xaki 

tattaro kayanki ki dawo nan, xumunci fa ba abun wasa bane ba abun yadawa bane, idan ma ke baxa ki xo ba ai sai ki 

turo mana Heedayah tunda ta mu ce, ki bar ganin an sakar maki ita ki xata galaba kika ci a kanmu, ni ce nan nake ta 

tausan Amadu amma kiris ya rage ya kwace ‘yar sa tunda ba ke kika tsinto masa ita ba, Kuma ba ke kika warkar 

mata da idonta ba” Ba yabo ba fallasa Mami tace “Toh sai yah xo…. ina jiransa” A hankali Heedayah ta xamo kasa 

tace “Ina kwana kaka?” Ko kallonta Kaka bata yi ba tace “Ina da labarin sun yi hutu yau kusan sati biyu amma kin ki 

barin ta xo ta gaisheni ta gaida wan Amadu sannan ta tafi gidan shi Amadun ta gaishesa idan ya kama har kwana 

biyu tayi, wannan dai ba yi bane, fitina a kwance take dai idan kika tada ta ke kika sani… Ko jiya sai da Amadu yace 

xai je ya dauketa nace ban ki ta tasa ba amma yyi hakuri muyi bikinmu mu cashe lafiya, bayan biki sai yaje can ku ci 

kanku bbu ruwan wani, wllh tllh haka aka yi ki tambayi wnn yaro Shureen ai tare suka shigo jiyan” Shuraim dai na 

tsaye dakin yana danna wayarsa, Mami taki cewa komai, Shuraim ya gaida Mami, ta amsa da murmushi tana 

tambayarsa ya aiki, Farida dake danna wayarta ita ma tace masa “Ina yini” yace “Lafiya lau” Murya can kasa 

Heedayah tace “Ina yini” ya ci gaba da danna wayarsa bai ce komai ba, kaka tace “To dai wnn shine dalilin ma da na 

kira ki nace na ji ku shiru, Amadu ne ya xo nan xai daga mana hankali wai xai je amso yarinya, ni dai na samu na 

lallabasa ya wuce, wnn yarinya dai ya fi kowa iko a kanta kema kin sani sai dai idan kina da karancin tsoron Allah, 

don haka ki raba kanki da fitina ki daina kokarin rabata kwata kwata da uban rikonta ba wani ya tsinto masa ita ba, 

jifa jifa sai ki turata da wnn yarinya Farida su je suyi kwana biyu gidansa haka ake yi ba ki yi bake bake a kan 

yarinya ba ke kadai, da bai tsintota tana galantoyi ba a ina xa ki santa Rakiya? to ga dai akwatina nan, daya 

matsiyacin mijin kwara biyar ya kawo gasu can a gantale ko budewa jama’ah bana yi, dayan kuma d’an albarka guda 

takwas da uban kaya a wani jakar ya kawo… Ku yi ta dubawa tunda na yadda da ke baxa ki cuce mu ba, kinsan 

akwai masu sace kaya idan sun xo gani, yanxu dai kasuwa wnn yaran xa su rakani, in je in siyo masu mafici, 

matankadi, gwa-gwa, maburgi, ludayan miya, ‘yar kwalla karama me ado, turmi da kwarya, duk gantalallun iyayen 

basu siya masu ba basu san shi aka kai mana lkcn mu ba auren yyi albarka da izinin Allah, wai su ‘yan xamani to ba 

dani xa ayi wnn lalacewar ba, xan tafi yanxu da kai na in siyo masu a bakin dogo, nace wnn mutumi Shureen ya kai 

ni a mota ya ki, da yake tunda ya samu sojan nan ya fara saka ilifon dinsu yake ganin kowa bbu gashi, ynxu kafin ku 

shigo sae kinga fitsaran da yyi min, to sojan karya ma da bai isa rike bindiga ba har ynxu, uban wa xai basa bindiga 

dama, ni dai har yau ban gansa da bindigan wasan yara ba balle na gasken amma har shine xai dinga raina ma 

mutane wayo” Ta gefen ido Shuraim ya ke kallonta, Mami dae sai murmushi take ta ki cewa komai, Heedayah ta 

taba jakarta da sauri jin kamar vibration, mikewa tayi ta shige bandaki, Shuraim ya bi ta da kallo har ta rufe kofa, Jin 

rufe kofar bayin kaka ta bi dakin da kallo don ganin waye ya shigar mata bandaki, da sauri tace “Rufa min asiri kar 

ki min amfani da bayi ki fito ki tafi ki shiga na masu biki….” Heedayah har da sa makulli snn ta fiddo wayar a 

jakarta, miss call tagani guda daya na Khaleel, tana ta tsaye ko xa a kara kira amma shiru, ta jira ta jira har Mami ta kwalo mata kira ta fito dakin, kaka na tsaye da Farida ana jiranta xa a je kasuwa, Shuraim dai sae kallonta yake, 

kaka tace “Toh uwar me kike min a bandaki kika dade haka” Heedayah ta turo baki tace “Ni ba abinda nake yi” 

Kaka tace “Toh ni ba ruwana ki sa mayafi mu tafi kasuwan, ke muke jira” Heedayah na son bin kaka amma tana 

tunanin xa a kara kiranta a waya, ta marairaice kafin tace komai kaka ta ja hannun Farida tace “Mu yi ta kanmu ba 

xuwa xata yi ba gantalalliyar” Daga haka suka fita xuwa kasuwa, Shuraim yyi ma Mami sallama ya fita, Mami ta 

fara sauke akwatin don duba kayayyakin ciki. Farida kam tayi da ta sanin bin kaka kasuwa don tun daga kan Mai 

adaidaita aka fara don bata basa cikakken kudinsa ba, kafin magana tayi tsawo Farida ta bude jakarta ta fiddo dari 

biyu ta mika masa ya ja machine dinsa ya wuce, kaka ta shiga kasuwar tana xaginsa, Farida tace “Kaka tun daga 

gida fa ya dauko mu xa ki basa naira dari…” a mugun fusace kaka tace “Uwarki Rakiya ke nemo min kudina ko a 

bishiya nace maki nake tsinkowa, kawai yarinya baki da amfani na xo da ke kasuwa saura kiris a min duka kina 

kallo, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin haka ba, Ashe ke shashasha ce, da Jamila ce yau sai ko ita ko barawon, 

Aa barawo mana, banda barawo wani d’an adaidaita ne xai amshi dari uku hankali kwance bbu tsoron Allah kamar 

mun hau jirgi, ko xuwa makka daga nan nawa yake aka ce maki? Toh ba ruwana daga yau kika sake cewa xa ki bi ni 

kasuwa sai na miki barbadin bala’i” Farida kamar tayi kuka sbda tsaye mutane suka yi ana kallonsu, kaka taga wani 

me mafici ta duka ta dauka tana cewa “Kai nawa nawa wnn, jikokina ne xa ayi ma aure jibi, da yake barbadadu ne 

iyayen ko batun maficin basa yi….” Hayaniyar da ta ji gefenta ya sa ta mike da sauri tana kallon abinda ke faruwa, 

wata dattijuwa ta gani tsaye tayi mitsi mitsi da ido tana dungurin wani me siyar da kaya irinsu tafarnuwa, kanunfari, 

citta da dai sauransu, sai cewa take “Ni xaka gilla ma karya kace baka harareni ba??” Jama’ah suka fara taruwa ana 

bata hakuri, cike da bala’i take cewa “Ni sai ya gaya min wa ya tsaya masa a Najeriya da xai harareni…. daga nace ya 

bani tafarnuwar ashirin ya bani kwaya biyu nace ban so, kawai sae mutumi ya harareni?sannan ya kara da gilla 

karyar cewar bai harareni ba, ya san wacece ni kuwa?” Mutumin dake ta kasa kayansa yace “Na sani mana, tunda 

gashi kin kawo ashirin xa ki siyi tafarnuwar da ko na hamsin babu a kasuwa” kaka ce ta kai masa naushi a baya tace 

“Amma kai dai anyi lalatattce
, yanxu ka dubi wnn tsohuwar da ta haifi kakan ka ka rufe gwalmadaddun idon ka ka 

dinga xaxxaga mata fitsara??” Sai kallo ya koma kan kaka, Farida ta kasa motsi inda take, can kawai ta juya ta koma 

titi don neman adaidaitan da xai mayar da ita gida, Kaka da wnn yar dattijuwa suka hadu suka yi ma me kaya tatas, 

daga karshe shi kansa dariya abun ya basa don ko kallonsu bai kara yi ba sai kasa kayansa yake a ‘yar rumfarsa, kaka 

ta juya kan masu bada hakuri tace “Ku kuma meye xaku dame kunnanmu da bada hakuri, da ku wasu ne da suka san 

darajan iyaye ai matse d’an banxa xa ku yi ku daure ku nakada masa shegen duka….” Dattijuwar tace “Toh su ma din 

duk ba barayin bane, wa ya sani ma ko akwai barayin satan yara a cikinsu, ni abinda ya fi min ciwo shine hararata da 

yyi, ga fa yan dubu dubu a jakata kar yyi xaton gantalalliya ce ni, kanina na can Abuja wani babban mukami yake 

nema yanxu haka amma baxan fada ba don ban san xuciyar kowa ba a nan, to ina xan biye yan yunwa a titi inyi 

tashin hankali da su, tafarnuwar fa sadaka dama nake son inyi da shi ba wani abu ba” Kaka tace “Bar masa tsiyarsa, 

da xa ki bi ni mu tafi gidan d’ana Umaru buhun tafarnuwa gareni wllh, sai in debar maki rabin buhun” Tsohuwar tace 

“Ai kanina ya hanani shige shige, banda haka da na biki wllh” kaka tace “Ba wani shige shige, shi gantalallen kanin 

naki da ace ya ajiye maki buhun tafarnuwar me xai kawo ki kasuwa mutumi ya harareki??” Kaka ta bude jaka ta 

fiddo wayarta tace “Ni dai bani lambar ki, nima ina da ‘ya ya a Habujan nan, ana gama biki dama xan je can” 

Tsohuwar tace “Ni dai ban yafe hararata da yyi ba wllh” Kaka ta kara kai ma me kayan dundu a baya tace “Ai ba 

don su Amadu xa su min fada ba da mun ja sa mun tafi caji ofis yanxu, amma ce min xa su yi meye hadina da ke” 

Tsohuwar ta fiddo wayarta a jaka tace “Ni ban san kan waya ba ke ki sa min naki lambar” kaka tace “Aa bana gane 

kan waya da rana, da dai mu nemi wani ya fiddo lambobin” Da sauri kaka ta juya tace “Auuu, ae da yarinya na taho 

ina take?” Nan kaka ta shiga duba Farida a kasuwa bbu alamar ta, wani mutumi suka samu kaka tace “Na ganka fes 

fes kamar d’an boko, don Allah ga wayata ka ciro min lambata ka ba ma wnn tsohuwar ita ma ka cire nata ka bani, 

Ashe bata yi makaranta ba bata san kan wayar ba” Kaka ta linke d’an takardar da Mutumin ya rubuta lamba ta saka a 

jaka, ita ma tsohuwar ta saka nata a jaka, kaka tace “Ni dai da kin ji ta nawa mu tafi gida kawai daga nan sai na 

debar maki tafarnuwar” Tsohuwar tace “Toh ai ba a son ina shige shige, toh amma dai mu je kawai” Mai maficin 

dake ta jiran kaka ganin xa su wuce yace “Mama kin fasa siyan maficin ne” kaka tace “Kai rabu da ni na fasa, 

iyayensu su xo su siya masu ai ba ni na haifesu ba, ubansu kawai na haifa” Daga haka suka bar wajen. Kaka na shiga 

compound tace “Toh ni Hajiya kaka ake ce min, xuwa makkata yayi hamsin….” Tsohuwar tace “Toh ni wannan 

shekaran ma kanina ya biya min Umra, kafin a fara axumi xan tafi, duk shekara sai naje makka sau biyar” Kaka ta 

tabe baki bata ce komai ba, can kuma tace “Toh mu lkcn da muka yi yayin xuwa makka kuna ina, kawai dai mun yi 

hankali me yanxu” Mutanen dake parlon har da Mumy suka gaida kaka da Sabuwar bakuwarta, bbu yabo bbu fallasa 

kaka ta amsa tayi hanyar dakinta, dattijuwar na kallon mutan parlon tace “Haihuwa aka yi a gidan ne” Kawar Hajiya 

Amina tace “Aa biki dai ake” tace “Ayyoo, naga parlon kamar ana cin kasuwa” Daga haka ta bi bayan kaka xuwa 

dakinta, Bala’i kaka ta dinga yi don me Mami xata wuce bata tsaya ba, tsohuwar dake tsaye gefenta tace “Aa bata da 

mutunci ne kawai” Kaka tace “Wllh kuwa, tana nan fa kamar xabiya sai mugun abu a xuciya, idan xata tafi ba sai ta 

bar min yarinya ba, dama me muka hada da ita, ai yarinyar ce tamu, to ynxu xan kira Amadu in sanar masa rashin kunyar da ta min” Mumy dai na tsaye kusa da kaka jin fadan da take sai bata hakuri take kai kace ta kirki ce, wannan 

tsohuwa dai ta tabe baki tace “Toh ni ina tafarnuwata in wuce” Kaka na share xufar goshinta sbda fitina tace “Ai da 

satin da ya wuce muka hadu har buhu sai kin samu, to yanxu ni ina naga tafarnuwar da xan baki duk na rabar ma 

jama’ah” tsohuwar ta gyara yafin gyalenta ta fita dakin kan kace me tayi hanyar titi tana cewa “Ashe tsohuwar banxa 

na biyo” Da daddare Heedayah na kwance daki da jakarta a kusa da ita, Farida ta shigo dakin, ita dai tana ta 

mamakin me yasa Heedayah ke yawo da jaka tun dawowarsu daga gidan su Sudais, amma bata ce mata komai ba, 

Farida na kokarin cire kayanta tace “Mami tana kiran ki” Heedayah ta juyo tana kallonta, can tace “I tot tayi bacci” 

Farida tace “Bata yi ba” Daga haka ta shiga bandaki, Heedayah ta cire wayar jakan da sauri ta bude school bag dinta 

ta saka wayar a ciki sannan ta sa Hijab dinta kan kayan baccin jikinta ta fita xuwa dakin Mami, Mami na kallonta 

bayanta duka kusa da ita tace “Idan kin gama period dinki ki sanar min” Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, 

Mami tace “Kin ji abinda nace?” Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace “Ae ya tsaya” Mami tace “Tun yaushe?” 

Heedayah tace “Yau ban yi ba” Mami tayi shiru tana kallonta, can tace “Two days kenan kika yi flow?” Ta gyada ma 

Mami kai, Mami tace “Toh, sai ki sa ido xuwa gobe jibi idan still u didn’t see anything sai ki gaya min” Heedayah 

tace “Toh” Mami tace “You can go” Mikewa tayi tace “Sai da safe Mami” Mami tace “Allah ya kai mu lfya” Daga 

haka ta fita dakin. Kwance ta tadda Farida da ta rufe ido kamar me bacci, Heedayah ta kashe wutan dakin ta kwanta, 

bayan kusan minti talatin ta tashi ta nufi schl bag dinta tana waigan Farida ta bude ta jakar ta duba, bata ga miss call 

ba ta rufe sannan ta tafi ta kwanta, wajen karfe dayan dare Farida ta juya tana kallonta taga bacci take, tashi tayi ta 

dau wayarta ta haska schl bag din tana kallo sai kuma ta karasa ta bude tana duba ciki, still tayi tana kallon wayar, a 

hankali ta sa hannu ta ciro sa daga cikin jakar tana jujjuyawa, can ya kunna sai ga hoton Khaleel gaban screen din, 

Farida ta juya ta kalli Heedayah sannan ta tabe baki ta mayar mata da wayar ta rufe jakar ta koma ta kwanta. 

Washegari da safe, bayan sun idar da sllh a dakin Heedayah tace “Yau xa mu je siyo takalmi da kika ce ko?” Shiru 

Farida tayi, Heedayah tace “Are you sleeping?” Farida tace “No” Heedayah tace “Baki ji me nace ba?” Farida tace “I 

will use the one I am having, ke xa ki iya xuwa ki siya” Heedayah bata kuma ce mata komai ba ta mike ta fita dakin 

don ita ce da wanke wanke da gyaran kitchen yau, in dai suna nan toh Mami ta hana Zainab yin komai, Junaid ne 

kwance saman 3seater yana bacci, ta d’an buda ido coz basu ma san yana gidan ba, ta karasa kitchen ta rufe a hankali 

sannan ta fara aikin da xata yi. Bude kofar kitchen din aka Heedayah tayi still, sai kuma ta juyo tana kallonsa, ya 

jingina da kofa ya rungume hannunsa yana kallonta da lumsassun idonsa, ta dauke kai tana ci gaba da wanke 

wanken da take tace “Ina kwana Yaya” Jin bai amsa ba ta juya tana kallonsa, calmly yace “Lafiya lau, yau ma xa ku 

fita kenan?” Ta gyada masa kai tace “Xa mu je gidansu ya Sudais” yace “Me ake yi yau din?” Tace “Mothers day” 

shiru yyi yana kallonta, can yace “Why not stay back home ke da Farida, ai ba sai kun je ba, mother’s day ai ba 

ladies day bane, ko kun fi son ayi ta ganinku…” Heedayah tace “Ae Mami ce tace mu je, tare da ita ma xa mu je” Bai 

kuma cewa komai ba ya juya ya bar bakin kofar, Heedayah ta turo baki ta ci gaba da wanke wankenta.Bayan Azahar Mami ta gama sh
irin xuwa can gidan biki, tana xaune parlor tana jiransu farida dake sama suna 

shiryawa, sanin they need time to prepare ya sa bata takura su ba take xaune parlor patiently waiting for them, 

Farida ce kadai ke kwalliya ita Heedayah ta gama saka kayanta tunda ba kwalliya take ba dama, ta dai shafa powder 

da man baki, atamfa ce iri daya yau ma suka sa da Farida, sosai kayan yyi masu kyau ba kadan ba, tun safe Farida 

taki wani kulata ko magana a takaice take amsa mata, ita ma Heedayah bata sake ce mata komai ba har ynxu da suke 

shiryawa, tuni Heedayah ta maida wayar Khaleel jakar da xa ta fita da shi tana rungume da abarta, yau ma da safe 

sai da ta ga miss call dinsa hakan yasa ma ta cire wayar a total silent ta bar sa a vibration but very low with the help 

of side buttons din, vibration din wayar ta ji yanxu ma, da sauri ta kalli Farida dake ta kwalliyarta, can dai ta mike a 

hankali ta nufi bandaki ta shiga bandakin ta kulle, fiddo wayar tayi tana kallon screen din sannan ta daga ta kai 

kunne kafin ya katse, yyi mata sallama, murya can kasa ta amsa, sai da ya d’an yi shiru sannan yace “Me yasa baki 

daukan waya idan an kira ki?” Tace “Saboda ba yawo nake da wayar ba, kuma gidanmu bama rike waya, I am not 

allowed to do so” yace “Gidanku?” Tace “Ehh” yace “Ohk… I tot ba a gidanku kike ba” Shiru tayi tana naxarin abinda yace mata, sai kuma tace “How did you know that?” Yace “I only guessed, and lkcn da na san ki kamar…. you 

were unsighted….” kamar me counting words din yyi maganan, gaban Heedayah ya dinga faduwa tana sauraronsa, 

can ta marairaice tace “Plss a ina ka san ni ka gaya min don Allah, I can’t remember where I knew ur voice…only 

knew it sounds familiar” yyi murmushi da take iya ji, sannan yace “Na sanki Heedayah” Kamar xata yi kuka tace 

“To a ina?” Yyi kasa da murya yace “Wani waje mana” Turo baki tayi tace “Bana so” yace “Toh gaya min inda xa 

mu hadu sai in gaya maki inda na sanki” ta d’an yi shiru sannan tace “Mami will punish me, ba a barin mu fito…” 

Yace “Yes… not at home….” Tace “To a ina?” Yace “Anywhere, duk inda kike so you tell me” ta buda ido sosai tace 

“Nace maka ba a barin mu fita ai a gida” yace “To ranan da na ganku Ina xa ku? And who was the lady you were

together with” Tace “Mun je supermarket ne, she is my sister” Yace “A gidansu dai kike” ta d’an yi masa shiru 

sannan tace “Gidanmu ne nima” yace “Noo ba gidanku bane wllh” Cikin sanyin murya tace “To a ina gidanmu 

yake?” Bai ce komai ba haka yasa tace “Ka gaya min” yace “Wani makaranta kike?” Tace “Nigerian Turkish” yace 

“Why are you not in schl now?” Tace “Hutu” ya d’an yi shiru sannan yace “So bbu ranan da xa ki samu ki fito??” 

Tace “Ehh, but xa mu je biki yanxu” Kofa ta ji an bude a can daki da sauri tace “I need to hang up now….” Yace 

“Wait… to yaushe xa mu sake magana….” tace “Anjima” daga haka ta katse wayar ta saka shi jaka xuciyarta na 

bugawa, Mami ce ta shigo dakin tana kallon Farida dake makale bakin kofar bandaki wanda tana ganin Mamin ta 

bar wajen da sauri tana dube dube kamar tana neman wani abu a kasa, Mami tace “Meye hakan?” Farida tace “Aa 

barima na nake nema ya fadi ban san inda ya shiga ba” Mami tace “Ina Heedayar?” Farida tace “Ta shiga bandaki ne, 

ita nake jiran ta fito” Mami tace “To ni xan yi wucewata tunda abun naku walakanci ne idan kun gama sai ku samu 

adaidaita ya kawo ku, for almost an hour ina jiranku kamar masu shirin jaraba” Farida tace “Aa Mami wllh ni na 

gama, ita nake jira” Mami bata kuma ce mata komai ba ta nufi kofa ta fita dakin, Farida ta sake kallon kofar 

bandakin sannan ta dau jakarta ta bi bayan Mami, a hankali Heedayah ta bude kofar bandakin ta fito tana kalle kalle, 

ganin bbu kowa dakin ta fita xuwa downstairs da sauri. Back seat farida ta xauna, hakan ya sa ta bude gaba ta shiga, 

Mai gadi ya bude gate suka fita gidan. Sosai jama’ah suka cika gidan biki ana ta shagalulluka a katon tsakar gidan, 

lallai taron ya amsa sunansa na Mother’s day, don iyaye ne mata sun yi shiga ta kece raini, can Heedayah ta hango 

kaka cikin jama’ah yanda ta kankance ido ya isa kasan cewar ba maganar arxiki take masu ba a can don wasu sai 

tabe baki suke, Heedayah ta bi bayan Mami da Farida da suka shiga parlon, Hajiya Hauwa na welcoming dinsu, kiris 

ya rage ta ci karo da Mumy da ta mike xata bar parlon cike da isa don bai ma Mami access din ganin kwalliyarta da 

gwalagwalanta da kyau, Heedayah ta koma baya tayi kasa da kai ta bata hanya tace “Ina yini” Ko kallonta Mumy 

bata yi ba ta wani daure fuska ta fita parlon Heedayah ta shiga a sanyaye, da fara’a Step mum din Sudais ta amsa 

gaisuwan Farida da Heedayah sannan tace “Ga can Sudais xai ajiye su Zainab saloon ku bi su ku ma kuyi gyaran 

gashi” da sauri Heedayah tace “Aa gashin mu a gyara yake ai” Mami ta juya tana kallonta, Farida tace “Toh bari mu 

je Mama” Hajiya Hauwa tace “Su Zainab din na daki ku tafi ku samesu sai ku wuce tare” Farida ta tafi inda Hajiya 

Hauwa ke nuna mata, Heedayah ta turo baki ta bi bayanta ranta bai so ba, Zainab ‘yar Hajiya Hauwa ce, sai Jamila 

daya daga amaren, Daya Amaryar Safiyya dakinsu daya da Sudais sai Nafisa da Aisha, Zainab da Rabi’ah da 

Khadijah kadai xa su tafi saloon din don sauran sun je jiya tare da amaren, sae ynxu da Heedayah da Farida xa su bi 

su, Zainab na ganin su Heedayah tayi welcoming dinsu da fara’a tana masa sannu da xuwa, Aisha ma dai tayi masu 

sannu da xuwa sama sama, amma Nafisa tayi kamar bata gansu ba ballantana Rabi’ah da Khadijah, a haka dai har 

Sudais ya kira Zainab yace yana jiransu a waje, Zainab ta mike tana kallonsu Farida tace “Mu je yana jiranmu a 

waje” har ta fita ganin Rabi’ah da Khadijah basu fito ba ta dawo tace “Yana fa jiran mu a waje” Khadijah ta wani 

yatsine fuska tace “Ku je ku, anjima xa mu je wani saloon din” Zainab bata ce komai ba ta fita, a parlor Hajiya 

Hauwa tace “Ina sauran fa” Zainab tace “Wai baxa su ba” Mumy da shigowarta parlon kenan ta xo debar ma bakinta 

lemo tace “A kan me baxa su je ba??” Zainab tace “nima ban sani ba” da haka ta fita Farida da Heedayah na biye da 

ita, Mumy ta wuce sama fuskarta a tamke tana cewa “Bari in kira driver na ya xo ya kai su saloon din, ai ba dole 

dama su bi ku ba, ko wani saloon din ne sai ya kai su yanxu” Hajiya Hauwa dai bata ce komai ba balle Mami dake 

parlon. Zainab ta shiga front seat Heedayah da Farida suka shiga baya, Sudais ya amsa gaisuwarsu gaba daya yana 

kallonsu ta madubi yace “Yaushe ku ka xo?” Farida tace “Ba dadewa” yace “I see, ku ma xa ku yi gayun kenan” 

dariya kawai Farida tayi, ya kalli Heedayah da tayi shiru yace “Cutie kema gyaran gashin?” Murmushi tayi ta sauke 

idonta kasa tace “Uhn” yace “Toh idan kun dawo anjima sae a nuna min gashin in gani” Nan ma bata ce komai ba sai 

murmushi, sai da suka yi nisa Sudais ya d’an kalli Zainab yace “Wai su Rabi’ah sun fasa xuwa ne” Zainab tace “Ehh 

wai anjima xa su taho” yace “Ohk then” yana ajiye su saloon din ya ba Zainab kudin gyaran gashin nasu da kudin 

adaidaita da xai maida su gida sannan ya wuce. Sai kusan Magrib su Heedayah suka dawo gida, basu tadda Mami a 

gidan ba, Heedayah na kallon Farida da ta amshi gugan tiles din da kaka ke yi a dakinta tace “Toh mu wa xai kai mu 

gida?” Kaka ta juya da sauri tana kallonta tace “Wa xai kai ku gida kuma? Ba lafiya, Nan ba gida bane? To nice nan 

nace Rakiya tayi wucewarta kuna nan har bayan biki tunda ita baxa ta tsaya ba, idan ma ita faridar taga baxata xauna 

ba to ke kina nan, nan ne dolenki” Heedayah
ta xauna saman kujera kaman xa ta yi kuka, Farida dai bata ce komai 

ba. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh taji vibration din wayarta dake kusa da ita, bin dakin tayi da kallo, Farida da Zainab ne xaune dakin suna hira, sai wata yar uwar Umma dake dakin tana waya. Heedayah 

ta saka jakar cikin hijab dinta cikin dubara ta mike ta ta shiga toilet, ciro wayar tayi ta dauka kafin ya katse, sallama 

yyi mata ta amsa yace “Kince anjima xa mu yi magana kuma nake ta kiranki baki dauka ba” ta wani turo baki tace 

“Toh ni ai bana nan mun fita, kuma the phone isn’t ringing” Yace “Ina kika je?” Tace “Saloon” yace “Why didn’t you 

tell me?” Tace “How will I tell you?” yace “Call me” tace “A rufe wayar yake, you didn’t tell me the password” ya 

d’an yi shiru, sai kuma yace “I remember, so where are you now?” Tace “Gidan yayan Abbanmu” yace “A ina?” Tace 

“Unguwar rimi” yace “Wani layi?” Tace “Nima ban sani ba” yace “Toh ki tambaya” a hankali tace “Toh” yace “I will 

call back in few minutes” tace “Tell me the password” yace “Sai na xo….” daga haka ya katse wayar, fita tayi 

bandakin ta xauna gefen gado, Farida dai ta kalleta bata ce komai ba suna ci gaba da labarinsu da Zainab, Bayan 

kusan minti biyar Heedaya ta kwanta tana kallon Zainab tace “Ya ma sunan layin nan sis” Zainab ta kalleta tace 

“Wai anguwar nan?” Heedayah tace “Ehh” Zainab ta gaya mata sunan anguwar, Heedayah tace “Ohk” bata kuma 

cewa komai ba tana ta kwance, sai taji wayar na vibrate, mikewa tayi tace “Bari in je in amso abinci am hungry” 

daga haka ta fita, can bayan gidan ta xaga bayan ta fita, ta daga kiran having making sure that bbu kowa wajen, nan 

ta gaya masa sunan layin yace “Ohk I am on my way” komawa tayi cikin gidan bayan ta mayar da wayar jaka, ta ki 

komawa bangaren kaka ta xauna parlor duk da akwai mutane, wasu na yanke yanken kayan ganye, kowa dai da 

abinda yake yi, bayan kusan minti sha biyar sai ga kiransa, da sauri ta fita ta daga kiran, yace “I am outside” sosai ta 

ji gabanta ya fadi, a hankali tace “Toh amma idan aka gan ni fa?” Yace “Babu wanda xai gan ki, ki fito” A hankali ta 

katse wayar ta mayar cikin jakar dake cikin hijab din jikinta sannan ta nufi gate tana yi tana waige waige har ta isa 

gate din xata fita, tana dube duben inda xata gansa, karo suka kusa ci da Shuraim da xuwansa gidan kenan, Suna 

hada ido ta koma baya a tsorace tana xare ido, juyawa yyi yana bin layin da kallo as if wanting to figure out 

something, suka hada ido da Khaleel da yyi parking daga daya side din kafin a iso dai dai gate din gidan, Khaleel ya 

fiddo wayarsa ya fara danne danne ya kai kunne, magana ya fara yi a wayar yana driving a hankali, har ya iso dai dai 

saitin Shuraim sannan yace “Ohhh ba nan bane? But I am seeing no. 28 here, ohk sorry 38, but wait…. can you plss 

come out ka daina bani wahala??” Sai kuma ya ja tsaki yace “kasan ba karamin aiki na bane in koma gida ko” yana 

magana yana tuki slowly har ya wuce Shuraim, Heedayah dake xare ido cikin rawar murya tace “Inn… Innaa yini” 

ya hade rai sosai yace “Ina xa ki?” Bakinta na rawa tace “Ruwa xan siya….” Yana mata wani kallo yace “Bbu ruwa a 

duk gidan sai kin fito siya?” Kamar xata yi kuka ta gyada masa kai kamar kadangariya, yace “Go back inside now” 

juyawa tayi da sauri ta wuce ciki tana hade hanya, ya juya ya sake kallon motar ya gansa can tsaye 4 houses away, 

can wanda ke cikin motar ya sauka ya nufi me gadi dake xaune bakin gate din, sai kuma mai gadi ya bude masa gate 

ya shiga cikin gidan, Shuraim ya dauke kai ya shiga gida shi ma snn ya rufe gate din. Farida na balcony tana danne 

dannen wayar hannunta Heedayah ta wuceta sai a sannan ta bi ta da kallo, Shuraim ma ya wuce bata ce masa ba bai 

ce mata ba, mikewa tayi ta bi bayansu, Dakin kaka Heedayah ta shiga ta rakube can karshen gado har lkcn gabanta 

bai daina faduwa ba, kaka tace “Ga abinci ki diba ki ci, ni na rasa gane ko Rakiya bata baki abincin kirki ne, wnn 

sirancin haka ai yyi yawa kamar bafillatanar da shanu ya kare ma” Heedayah ta turo baki bata ce komai ba, bude 

kofar aka yi Shuraim ya shigo, kaka ta dauke kai kamar bata gansa ba, dubu ashirin ya ciro aljihunsa ya mika mata 

yace “Abba yace a kawo maki” Kaka ta amsa ta kirga gaba daya sannan ta yashe kudin gefen gado tace “Ni dai na 

shiga uku, meye dubu ashirin kuma Allah na tuba, wnn ai baxai isa liki ba wllh, snn duk a ciki in ba bakina da suka 

xo kudin mota me yasa Amadu ke min haka ne ni” Shuraim dai sai kallon Heedayah ta gefen ido yake yi, don kai 

kana ganinta kasan bata da gaskiya sai wani kokarin boye jaka take a cikin Hijab nan kuwa vibrating wayar yake, 

Suna hada ido da shi ta daburce, can ta mike ta nufi kofa ta fita da sauri, kaka tace “Ni kawai a kira min Junaidu bani 

da kowa sai shi, shi daya xai fitar da ni kunyar likin nan da xan ma yara, da tsofaffin nan da suka xo min” Heedayah 

na fita dakin su Zainab ta wuce da sauri ta shige bandaki ta kulle, tunanin inda xata boye wayar jakarta take, ta fiddo 

wayar tana kalle kallen bandakin, window ta bude ta jefa wayar ta waje sannan ta fito bandakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *