HEEDAYA CHAPTER 29 BY By Khaleesat Haiydar
Mikewa Khaleel yyi carefully surveying the street and he saw nobody apart from her, Mai gadin ya hango Heedayah
shi ma da sauri yace “Au to ai ga daya daga yan matan gidan can ranka shi dade” Juyawa Khaleel yyi yana facing
dinsa amma bai ce komai ba, nan kuma bai son ta gansa ne, ita kuma ta riga ta gansa, sai da ta wuce su snn ya juyo
ya bi bayanta, tsayawa tayi da ta gane yana bin ta, ya karasa gefenta ya tsaya, murya can kasa yace “How are you?”
Ta wani hade rai tana kallonsa da kyau tace “I’m not fine, and I am begging you ka daina bi na, kana ja min matsala
a gida….” Shiru yyi yana kallonta, ganin ya ki cewa komai ta ci gaba da tafiyarta walking faster, bin ta yyi suka kara
jerawa, ta juya kamar xata yi kuka tace “Don Allah ka kyaleni ka daina bi na tunda dama kawai sbda in kulaka ya sa
kake min karya kace ka san ni” ya girgixa mata kai a hankali yace “Ki daina cewa babba yana karya…” Ta yi facing
dinsa da kyau fuska daure tace “But you lied to me” yace “No I didn’t….” Tace “To a ina ka san ni??? Tell me now”
Ya kalli motarsa da yyi parking can farkon shigowa layin snn ya kalleta yace “But we can’t talk here” tace “Sai a
ina?” Yace “Toh wai da mu shiga gidanku….” Ta wani xaro manyan idanuwanta a tsorace tana kallonsa, ya dage
girarsa yace “Yess akwai matsala ne idan na shiga gidanku, daga nan ma ba sae in gaida mutanen ciki ba….” Kamar
xata yi kuka tace “Ni dai don girman Allah ka daina bi na, you are a joker…. Plss let ur joke end here now and
forever” yace “Billah na san ki Heedayah, what’s my gain lying to you cewar na san ki bayan ban san ki ba”
Kallonsa kawai take, yace “Nasan ba tare da iyayenki da suka haife ki kike ba, nasan cewar probably few years ago
or even recently kika fara gani coz you were unsighted as at the time I knew you, a lkcn da na sanki kina ‘yar
karama” cikin sanyin murya tace “Toh a ina ka san ni plss? And did you know my real parent?” ya nufi inda motarsa
yake walking slowly yace “Mu je mota, I can’t talk here” Bin bayansa tayi a sanyaye maganganunsa na mata yawo a
kai, ya bude mata front seat yana kallonta ba musu ta shiga ya rufe sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga
ya kulle. Juyawa tayi tana kallonsa bayan ya shiga motar tace “Tell me plss, ka gaya min inda ka san ni” yace “I will,
but waye wnn sojan na jiya?” Tace “Ya Shureen” Khaleel ya dinga kallonta kafin yace “Did you mean Shuraim?”
Ta bude hannu tace “Ni dai Shureen naji kaka ke kiransa” yace “Who is he, I mean the Shuraim, and waye kaka?”
Tace “First son din Abba ne shi Ya shureen, kaka kuma Grandma dinmu ce….” Yace “Grandma dinsu dai, and Waye
Abba?” A hankali tace “I call him my father….” Yace “Nan ne gidan Abban?” Ta girgixa kai tace “Aa, gidan Mami ne
nan” yace “Waye Mami” a hankali tace “I call her my mother” shiru yyi yana kallonta snn yace “Shuraim din ne yyi
picking call dina jiya da na kira?” Ta girgixa kai tace “Aa that’s Ya Sudais” da mamaki yake kallonta yace “Shi kuma
waye?” Tace “Cousin din Ya Shureen” tabe baki yyi bai kuma cewa komai ba duk da she just confused him with her
explanation but he isn’t willing to know anything anymore, tace “Toh ka gaya min inda ka san ni” yace “Nasan dai
kamar an ta6a kidnapping din ki, is that so??” Cikin breaking voice dinta tace “Ehh, kuma ban kara ganin Ammina
da Abbana da Yakumbo ba har da Nanny, and nobody is willing to take me to them, I’ve missed them so much,
nobody is saying anything about them to me, nobody is willing to take me to them, Ina son in ga Ammina….”
Kallonta kawai yake yi, hawayen da ya makale idonta ya gangaro sai kuma ta fashe masa da kuka a hankali tana
kallonsa, ya dauke kansa daga kallonta, cikin rawar murya tace “Ni ina son in ga Ammina, I want to meet with my
mother…” Shi dai bai ce mata komai ba tayi kukanta me isarta tayi shiru, Ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya
jinginar da kansa da kujeran motar cikin cool voice dinsa yace “Xa ki ga Ammin ki in sha Allah” Tana kallonsa cikin
sanyin murya tace “When, and did you even know them?” Ya girgixa kai yace “Ban san su ba…. amma in sha Allah I
will take you back to ur parent soon, I am promising you this…. But… you just have to trust me” Ta goge hawayen da
ya ki tsaya mata tace “How long will that take??” Yace “Not so long” tace “Tell me who are you pls” yace “Khaleel
Muhd” Tayi shiru tana kallonsa, soft smile ya sakar mata murya can kasa yace “Trust me Heedayah” ta gyada masa kai kawai, yace “So anyi seizing wannan wayar da na baki ko?” Ta gyada masa kai nan ma, sai kuma da sauri tace
“Toh me yace maka da ka kira wayar?” Ya d’an buda ido yace “Nothing much, I didn’t even listen to him…” Yana
magana yana kokarin ciro abu a aljihunsa, ya ciro wani karamin waya sosai kamar na wasan yara ya mika mata yace
“If there is anything I will call you, or you call me, xa ki ga numberna Brainiac….” Ta marairaice tace “Aa ni dai
kaga Ya Sudais ya kamani da waya bana son wani ya kara ganina da waya” Yace “Then if there is anything how will
I communicate with you Heedayah” shiru tayi kamar me naxarin abinda yace, kamar xata yi kuka tace “Tsoro nake
ji” yace “Wannan wayar ai bashi da girma, it’s very portable ko a dankwalinki xa ki iya barinsa no one will know of
it” Tana ta kallon wayar taki amsa gabanta na faduwa, ya kamo hannunta ya sa wayar a ciki ta xaro ido tana kallonsa,
shima yana kallon kwayar idonta yace “You have to collect it” Bata ce komai ba ya sake hannunta, yace “Xa ki shiga
ciki yanxu kar a nemeki ko?” Ta gyada masa kai cikin sanyin murya tace “But you promise that I will meet my
parent, should I confide in you?” shiru yyi yana kallonta, yace “But you have to be patient, and naga you are so
much comfortable with ur guardians here, I can see they love you wholeheartedly….” Ta fashe masa da sabon kuka
tace “Basa ce min komai a kan iyayena” ya kwantar da murya yace “That’s because they love you dearly, and sun
daukeki kamar ‘yar su” Goge idonta tayi bata ce masa komai ba sai dai hawayen ya ki tsaya mata, yace “Tunda basa
maki maganan parent din ki kema kar kiyi masu, u will look so ungrateful…” Tace “Amma kai ai xaka samar min
iyayena ko?” Yayi murmushi yace “I owe u that” murya can kasa tace “Thank you” Yace “No thanks” tace “Xan
wuce gida” ya bude lock din motar yace “Ohk….” kafin ta bude motar, yyi kasa da murya yace “But did you have
anything to do with that soldier?” Ta turo baki tace “Noo…” Daga haka ta bude motar, sai kuma ta juyo da sauri tana
kallonsa tace “How did you know I was kidnapped?” Kallonta yake ko kiftawa babu, sai kuma ya sauke idonsa kasa
yace “That wil
l be story for another day…” Tayi narai narai da ido ta dawo cikin motar tace “Tell me plss” yace “Xan
gaya maki amma sai mun sake haduwa, ki wuce ciki kar a nemeki, it’s already getting dark” Bata kuma cewa komai
ba ta sauka motar yyi mata murmushi, ta rufe motar ta karasa katin dake layin, ta baya ya fice daga layin snn yyi
reverse ya hau saman titi, duk wnn abun tana tsaye gun me shago tana kallonsa ko kiftawa bbu. Hadadden parlor ne
me dauke da maza hudu sai aikin shan giya suke suna caca caca duk sun cika parlon da hayaniyarsu, yana daga tsaye
jikin wani pillar kusa da dinning area na parlon ya rungume hannunsa yana kallonsu yyi supporting kansa da kafarsa
a jikin pillar din, 3 qtr ne jikinsa sai singlet, idonsa na kan abinda suke but hankalinsa baya kai, daya daga wa enda
ke xaune cikin parlon na kyakyata dariya kamar ta6a66e yace “Kayy… xo ka barar mana da wnn mutumi ko bakinsa
xai rufu don Allah” Sauke kafarsa yyi kasa ya karaso cikin parlon cikin tafiyarsa ta kasaita, ya ja wani tsadadden
kujera me kama da na office ya xauna, daya daga cikinsu da suke kira Maska yace “Genius akwai damuwa ne, two
days u are dull, ko miskilancin ne ya taso” Khaleel bai ce masa komai ba, Zayyad din cikinsu ya dau kwalin
cigarette ya jefa masa yace “May be u need this” Dauka Khaleel yyi ya jefar saman center table din da suke caca
caca yace “Yyi min kadan sae dai in kai xan kyatta ma ashana” duk suka kwashe da dariya, Khaleel ya shafa sajensa
yace “Ina son maku wata tambaya” Maska ya d’an gwalo ido yace “Tohhhh Brainiac ne xai yi ma learners tambaya,
are we safe at all, anyway muna jin ka” Khaleel ya daura kafarsa kan center table yace “1…2…3… To 4 years back…”
Duk suka xuba masa ido da kunnuwa suna sauraronsa attentively, ya langwabar da kai yace “Anyi kidnapping wasu
yara kananu duk mata guda hudu….” Sai kuma yyi shiru, Maska yace “Ehen muna jin ka, what about that” Khaleel
ya sauke idonsa kasa yace “Shine nake son sanin ko xa ku iya tuna wa enda suka daukosu kuma da inda suka dauko
su” Kamar hadin baki duk suka fashe da wani mahaukacin dariya nonstop, bin su ya dinga yi da kallo har bayan
minti biyu suna dariyar, can ya mike ya fixgo Zayyad ya kai masa naushi a baki, kan kace me, Zayyad ya kai masa
shi ma, nan kuma suka yi charging kansu, don da kyar aka samu aka rabasu aka rike Khaleel, Salim ya janye Zayyad
suka bar parlon, Khaleel ya share xufar fuskarsa ya koma saman kujeran da yake ya xauna, Maska yace “Dama duk
yau baka fita workout ba, you are just lying down all day, ko ba komai you will feel strong now” Sufyan da Saif da
shigowarsa parlon kenan suka tsaya bakin kofa suka kalli d’an show din da aka gama suka karaso parlon da ledojin
gasassun kaji, Saif yace “Are you really okay Khaleel?” Ko kallonsa Khaleel bai yi ba, Maska yace “Wai wasu yara
da aka yi kidnapping 4 years ago yake tambayar inda aka dauko su kamar wani wasan kwaikwayo, yara nawa aka yi
kidnapping 4 years ago” Sufyan yace “4 years ago kuma? kai ko ka so kanka da yawa Kay, lkcn muna yaku bayi fa”
dariya sosai duk occupant din parlon ke yi, Khaleel ya shiga bin su da kallo, Saif ya xauna yana facing din Khaleel
yace “Su waye suka yi kidnapping din yaran a cikinmu, snn idan shekaru hudu kake magana ai yawanci wasu
cikinmu duk an kashe su, su Gwaska, Kamilu, Fago, Rabilu, Ahmed… Su ne masu kidnapping din a lkcn ko ka
manta, ynxu Fago kadai da Kamilu ke raye, su xaka tambaya” Khaleel yace “Har da Maska aka dauko yaran idan shi
ya manta ni ban manta ba” Maska yace “Ni Maskan?” Khaleel yace “Ehh, warce aka nemi daya aka rasa a wnn lkcn,
har oga yace duk ynda xaka yi, kayi providing dinta kayi kawai” Maska ya koma ya xauna thinking deeply, can ya
wani tafe hannu yace “Ohhhhh…. Ohkkkkk I remember, wnn makauniyar????” Khaleel ya kallesa smiling a hankali
yace “Exactly” Maska ya xaro ido yace “Kai ai yarinyar nan har yau ban yarda ba aljana bace wllh wllh, she just
disappeared, ko sama ko kasa bbu ita, Allah fa ya so ni lkcn nan da kwanana ya kare, so what about that now?”
Khaleel yace “Inda aka dauko yaran nake son sani?” Maska yace “Oho, ni kawai mun hadu ne a bakin daji muka wuce da su, I don’t know inda aka dauko su, amma fa ina jin Gwaska da Ahmed ne suka taho da su daga wani
kauye” Sufyan yace “Kayy but may I ask you?” Khaleel yace “Go on” Yace “Meye ya tado da batun kusan shekara
hudu?” Khaleel yace “Ba komai, Ina wani research ne kawai” Saif yace “Research akan matattu, wa ennan yara ai an
rufe babinsu a duniya tun yaushe, tunda dai duk an yanke su a wancan lkcn” Khaleel yace “Gwaska ya mutu, Ahmed
ma haka, amma Fago na nan ai” Maska yyi tsaki yace “Toh me xai maka?” Khaleel yace “Tare da shi aka daukosu,
don haka baxai rasa sanin garin da aka dauko yaran ba” Tanko dake ta sauraron su a parlon tun farkon fara xancen
bai ce komai ba yyi wani dariya irin na bossawa yace “Tunda shi Fagon ance maka bashi da wani memory me
ma’ana da xai ajiye a kwakwalwarsa sai wannan abinda baxai amfaneka ba baxai amfane mu ba baxai amfane kowa
ba, Kayy ka fito ka fada mana gaskiyar abinda ke faruwa da kai, meye na binciko maganar shekara 4?? ko dai ghost
din yaran ne suka sa ka gaba suka ce sai ka je garinsu, share with us plss…” Mikewa Khaleel yyi yana kallonsa
fiercely ya nufesa, dai dai nan aka bude kofar parlon, hakan yasa ya juya, wasu mutane ne su biyu suka shigo parlon
cike da isa ana taku dai dai, tare da wani dake biye da su a baya hannunsa rike da bindiga, kowa na parlon ya mike
ya gaida su, kana gani kasan manyansu ne, su suka kafa gagarumin kungiyar, Khaleel ya koma ya xauna, bakikirin
cikin mutane biyun da suke kira da Oga Arne ya kalli Khaleel yace “Genius jiya Ina ka tafi da Magrib kasan akwai
meeting, kowa ya hallara amma banda kai” Khaleel yace “Na shiga cikin gari ne” Oga Manga na bin duk kowa na
parlon da kallo yace “Ina Zayyad da Salim” Maska yace “Suna sama” Oga Arne yace “Ayi kiransu” Saif ne ya tafi ya
kirasu suka sakko gaba daya, Oga Manga yace “Ynxun nan dawowar mu kenan daga gidan d’an takarar jam’iyyar Ac
wato Alhaji Sammani Abdulkadir Gaya…. Mun kuma gama magana da shi ya biya abinda muka bukata bbu ja in ja….
ynxu abinda ya rage kawai sai ynda xa ayi kidnapping din abokin hamayyarsa…. Nan da kwanaki kadan, to dai idan
mun samu irin wnn aiki daga sama mu kan xauna mu nutsu mu tsara yanda komai xai tafi bbu wani mishkila, don
kunga ba karamin aiki bane kidnapping din me takarar mukamin gwamna gaba daya, don haka Kayy xa mu so mu
fara jin yanda kaga ya dace mu bi, yana xama a Abuja, Kano… Wani lkcn har Kaduna, snn mun samu rahotun yana
lagos ynxu hka, sae dai baxa mu bi sa Lagos ba xae xo nan ya samemu” Khaleel dake ta sauraronsu yana shafa
sajensa da ya kwanta ya dai yi shiru bai ce komai ba, Oga Manga yace “Ya ne Genius kayi shiru” Khaleel ya sauke
kafarsa daga kan kujeran da ya daura yace “I will think about that overnight” Oga Arne ya karasa yyi patting dinsa
yace “We trust you Brainiac, sai dai duk plan da thinking dinka kada ya wuce nan da sati uku, duk da dai there is till
much time sosai, amma deadline din da aka bamu kenan daga sama, and we have not to disappoint them….” Bai ce
masu komai ba duk suka bar parlon. Heedayah ce ta shigo dakinsu ta kulle kofar a hankali ta jingina jiki tana kallon
Farida da dawowarta kenan daga gidan biki, kayanta take cirewa, Heedayah tace “Me yasa na maki magana baki
amsa ni ba?” Farida ta ki kallonta tace “Ohh ban ji ba, Ina ta sauri
in xo in cire kaya na gaji” Heedayah tace “Nop,
kin ji” Farida ta juyo ta kalleta, sai kuma tace “Of course yes na ji” Heedayah tace “Then why did u ignore me?”
Farida tace “Because that’s what you want, u need privacy this days” Shiru Heedayah tayi tana kallonta, can tace
“Ohk about that guy Khaleel? Bbu abinda ke tsakaninmu believe me, he just wants us to be frnds, nothing more, and
I didn’t tell you ya bani waya ya Sudais ya gani yyi seizing da muka je gidansu biki, I think that’s all that u think I
am hiding” Farida dai ta tabe baki bata ce komai ba tana ci gaba da cire kayanta, a hankali Heedayah tace “I am
sorry if you think I am hiding things away from you Farida, but I am scared…” Lkci daya hawaye ya kawo idonta,
Farida ta kasa kallonta, can tace “I am just trying to be a protective sister, nowadays ba ko wani namiji ake kulawa
ba, most especially someone like that man…. I won’t say he didn’t look responsible amma ae ba a goshi ake rubutawa
ba, ni dai i want you to be extremely careful with him, ba mu san xuciyar sa ba, kuma kar ki manta inda muka gansa
bakin hotel though we don’t judge a book by just it cover, bamu san me ya kai sa can ba, amma samarin Kaduna sun
wuce tunanin ki Didi” Heedayah bata iya tace komai ba, Farida ta juya tana kallonta tace “Be careful plss Heedayah”
Heedayah ta gyada mata kai murya can kasa tace “In sha Allah sis, but ya kara bani wani karamin wayar” tana fadin
haka ta tafi gaban mirror ta bude ta daga dictionary ta dauko wayar tana nuna ma Farida, Farida tace “But tell me did
you like him” Heedayah ta d’an yi shiru sai kuma tace “He is kind… And gentle” Farida tayi murmushi tace “Toh me
da me yake ce maki a waya” Heedayah ta d’an juya ido tace “Nothing, kawai labarin duniya, sae kuma labarin
karatu…. He is always telling me to study hard, very hard… ” Farida tace “Ohk that’s good, if there is anything apart
from that you let me know” Murmushi Heedayah tayi tace “Alright” daga haka ta juya ta fita parlon ta koma kasa
don Mami take taya girkin dinner coz it’s already six. Bayan Magrib Heedayah na xaune parlor da Farida suna cin
rice and stew da veggies da Mami ta girka da pepper chicken sai tamarind drink me sanyi, Murya kasa kasa Farida
ke ba Heedayah labarin abubuwan da suka faru gidan biki kar Mami ta jiyosu don ga fadan gulma da ta kawo take yi,
snn kuma ga fadan abinci na gabanta tana surutu which is a bad table manner, irin abubuwan da kaka ta dinga ma
jama’ah take fadi ma Heedayah, da ynda ta laka ma wata satan zinarinta kunne daya, daga karshe aka ga zinarin a
bandaki ya fadi alamar dai da kaka ta shiga alwala ne ya fadi, Heedayah ta tabe baki tana girgixa kai tace “Will kaka
ever change?” Farida tace “I don’t think so gaskiya, har sai da aka kira Baffa ya dawo gidan, Abba ma ya xo wllh,
matar sai kuka take gwanin ban tausayi ta harhada kayanta xata wuce, Kuma fa wai step sister dinsu Abba ce she is
staying in kano, tana ma da manyan yara kaman mu…” Heedayah tace “Toh me Kakar ta ce da aka ga dankunne a toilet dinta?” Farida tace “Kuka ta xauna ta dinga rusawa wai wani ne dama ke son hadasu fada da matar shine ya
kai dan kunnen bandakinta ya boye” danna bell din parlon aka yi, Zainab me aiki dake xaune kusa da kofar dakinta
tana kallon Tv ta mike ta nufi kofar ta bude, gaishesa tayi ta basa hanya ya shigo parlon, Tun da Heedayah tayi ido
hudu da green ta dauke kai da sauri ta ci gaba da cin abincinta, Ya karaso cikin parlon Farida ma bata sake kallonsa
ba tace “Ina yini?” Yace “Ina Mami?” Farida tace “Tana sama, sis Zainab kiyi mata magana” mikewa Zainab tayi ta
wuce sama, ya ajiye ledan hannunsa saman table sannan ya xauna kan kujera, da kyar Heedayah tace “Ina yini” Bai
ce komai ba, Mami ce ta sakko tace “Shuraim” ya daga kai yace “Ina wuni” tace “Lafiya lau, ya aiki” yace
“Alhmdllh, kaka ta bada a kawo maki” Mami tace “Toh nagode kuwa, Allah ubangiji ya basu xaman lafiya su kuma
amaren” Yace “Ameen” Mami ta kalli Farida tace “Ki kawo masa abinci” ya mike yace “Aiki xan wuce ynxu, daga
can gidan nake shine ta bani in taho maki da shi” Mami tace “Kai kullum kana da excuse one way or the other idan
aka ce a xubo maka abinci Shuraim, Farida bring him the food idan kin kawo kar ya ci ya wuce” Daga haka Mami ta
wuce sama, Farida ta mike ta wuce kitchen, murmushi ya d’an yi ya koma ya xauna, Heedayah dai sai juya abincin
gabanta take ko da wasa ta ki yrda ta kalli direction dinsa…. Can ta mike ta dau plate din abincin ta wuce kitchen, a
saman tray Farida ta daura abincin da spoon sae drink da glass cup, ta xuba veggies din a wani bowl duk a kan tray
din, farida na kallon Heedayah rike da tray din abincin tace “Kinsan bana son Shuraim din nan kwata kwata Didi,
amma Ina son uniform din jikinsa, wllh Ina bala’in son uniform din, suna masa shegen kyau sosai, may be because
he is a kind of huge, kuma baya dariya….” Heedayah ta jingina da cabinet din kitchen din ta langwabar da kai tana
kallonta so amazed, sae kuma ta fashe da dariya tana tafe hannu tace “Tell me something, really??? But ai in dai kina
son uniform din da gaske to son wanda ke cikin uniform din ba abu bane me wahala, Kinga perfect match kawai,
bari ki ga inda xa ki kai sa idan kun tsaya yin pre wedding….” Ganin Farida na kokarin ajiye tray din hannunta
Heedayah ta fice da gudu tana kyalkyala dariya ta wuce sama, Shuraim ya bi ta da ido.Farida ta fito ta ajiye masa abincin ita ma ta wuce sama, da ido ya bi ta, can ya kalli agogon wrist din sa ya ga
bakwai da rabi, ya dau bottle water da ke saman tray din kawai ya mike, fita gidan yyi, yyi wucewarsa. Washegari
Tuesday da sassafe wajen shidda da rabi Mami na kitchen tare da Farida da Heedayah suna hada breakfast, Zainab
Mai aiki kuma na gyaran gida ta gama shara tana mopping aka bubbuga kofar parlor, Zainab ta ajiye mopping stick
din tafi ta bude kofar, kaka ce tsaye da katon jakarta a sakale a hannu, Zainab ta duka ta gaida kaka, kaka ta amsa
tana kokarin shigowa parlon tace “Ina Rakiyar, duk tsiyarta dai na san bata fita opis ba yanxu” Zainab tace “Tana
kitchen” Kaka ta ajiye jakar hannunta ta wuce kitchen din, Washe baki tayi bayan ta shiga tace “Ina kwana Rakiya”
Mami na kallonta da mamaki tace “Aa, daga ina da sassafe haka kaka?” Kaka tace “Gidan Umaru mana, ai bani da
wani gun bayan nan” Mami tace “Ikon Allah, amma kawo ki aka yi dai ko” Kaka ta marairaice tace “Wa na ajiye xai
kawo ni Rakiya?? Kamar dai suna tsorona, d’an adaidaita na samu ya kawo ni har nan, na basa nera dari don ya mun
mutunci, kuma kinsan na samu kudi sosai da bikin nan shine ma na xo nuna maki kudin ko xa ki bani shawara in
siya fili” Mami tace “Aa gaskiya kam gwara ki siya fili in dai kudin na da yawa Kaka” Kaka tace “Yawa kai, ya kusa
dubu talatin da biyar fa, don ma ina xara kadan kadan” Mami ta dauke kai tana ci gaba da yanka green pepper da
take yi tace “Ehh kam da yawa gaskiya, sai ki ba ko Baffa ko Barrister wani ya samar maki fili a anguwa me kyau”
Kaka tace “Shkkn kuwa, shi yasa na fi son inyi shawara da ke a kan kowa, baki da kyashi, kinga idan da canji ma sai
su maido min kayana don ba basu xan yi ba, ynxu dai xuwa nayi in maki bangajiya duk da dai a gantale muka dinga
ganin ki gidan bikin, daga nan kuma bayan na karya sai wnn yara su rakani gidan Amadu inje can shima inyi masa
ban gajiya, miliyan daya ya bada tasa gudunmawar wllh, in gaya maki gadaje bibbiyu aka yi ma yaran, shi dai
Amadu yace bashi da kudi ynxu… amma ga miliya
n daya ayi duk abinda xa ayi, ke kuma naji labarin kin basu dubu
dari ko? Kawun Junaidu bai bada ko sisi ba duk kudinsa” Mami tace “Aa dubu dari biyu ya saka ma Junaid ya kai
masu” Kaka tace “Abu ya lalace, ya cinye kenan wllh don kwandala bai kawo masu ba” Mami tace “Aa ya kai masu
Ina gidan ma ya kawo, ki tambayi shi Baffan” Kaka tace “Atoh da kyau… Toh duk Allah ya saka, Allah ya nuna
mana na ‘yan baya, yanxu sai ayi harin na Farida nan da yan watanni ko?” Mami bata kuma ce mata komai ba, Farida da Heedayah suka gaida kaka, kaka ta amsa tace “Toh kuyi maxa mu karya mu wuce gidan Amadu shi ma
kafin ya fice” daga haka ta juya ta fita kitchen din tana cewa “Ita wancan xalben ma ban ganta gidan yinin ba, tana
fama da tsayi kamar daren sllh” Sai da kaka ta ci tayi nak sannan ta kishingida a parlor tana jiransu Farida su shirya
su wuce gidan Abba, Mami ta shigo parlon tace “Kaka ko xa ku tafi da Farida kawai, don Heedayah bata wani jin
dadi, kafin in tafi aiki xan fara ajiyeta a asibiti” Kaka ta mike xaune da sauri tace “Aa Rakiya ki rufa min asiri don
Allah, ga dai likita Shureen a can gidan na samu labarin yana nan da safe yawanci, ba sai kawai ya dubata ba, amma
ni dai dole da ita xan tafi, yaushe rabon ta je gaida uban rikon nata?? Ki dinga abu sbda Allah mana Rakiya”
Komawa tayi ta kishingida bata kuma cewa Mami komai ba, Har ta fara gyangyadi ta bude ido da sauri jin ana
gaisheta, Junaid ta gani xaune yana kallonta, tace “Kana gidan dama Junaidu?” Yace “Ehh nan na kwana” Kaka tace
“Shikenan ya xo gidan sauki bbu ni bbu fada da masu adaidaita sai ka ajiyeni gidan Amadu kawai” ya kalli agogo
yace “Toh amma yanxu xa mu tafi sbda aiki xan wuce” Kaka ta mike da sauri tace “Toh me nake jira, wa encan
rubabbun ne idan basu gama ba muyi wucewarmu kawai ban iya wahala” daga haka ta dau jakarta ta nufi kofa, bin
ta yyi da kallo snn yyi murmushi ya mike ya bi bayanta. Bata yadda sun tafi ba duk da Junaidu yyi kokarin
convincing dinta don baya son Heedayah taje gidan amma kaka tace sai dai ya sauketa ita baxata iya wahalansa ba,
sai da Farida da Heedayah suka fito snn hankalinta ya kwanta, Farida ta bude front seat ta shiga, Heedayah ta xauna
tare da kaka a baya, kaka tace “Wnn ai walakanci ne kawai daga ku yi wanka ku sa kaya sai ku bar mu a walakance
a mota muna jiran ku, ko ita Rakiyar ce tace ku dade??” Ganin Mami kaka tayi shiru, Mami ta karaso gun motar tace
“Toh Allah ya tsare kaka, mun gode” Kaka tace “Yauwa Rakiya Allah yayi maki albarka, in sha Allahu anjima xan
dawo maki da su ni ma ban fiye son xama gidan mutane ba ai kin sani, ko da azahar ne Shureen sai ya dawo da mu
gaba daya mu ajiye su ni kuma ya maida ni gidan Umaru tunda can nafi wayo” Mami tace “Toh Allah ya kai mu,
Allah ya kiyaye” daga haka ta koma ciki, Kaka tace “Toh Ameen dai” Junaid ya ja motar suka bar compound din
don Mai gadi ya riga ya bude masu gate, Farida na kallonsa tace “Ina kwana Yaya?” Yace “Lafiya lau” Heedayah ma
tace “Ina kwana” Yace “Lafiya lau” kaka ta tabe baki tace “Abun bai yi ba oo, dama baku san yana gidan bane? Tun
wayewar gari sai ynxu xaku ce Ina kwana” Junaid yace “Duk sun shiga daki kafin na dawo jiya, so basu san ina
gidan ba ma” Kaka tace “Ni duk sai na ganka wani iri Junaidu, ko baka da lafiya ne” yace “Lafiyata qlau” kaka tace
“Toh ku ma dai ku yi kuyi ku fiddo da matar nan dai a maku aure ku bar yawo a titi bakwa wancan gida bakwa
wannan gida, auren shi ya fi maku daga kai har Shureen, don shi Sudais naji uwar na cewa cikin shekaran nan ne
idan Allah ya kai mu, dama shi me yan mata ne iri iri, xaba kawai xai yi ya darje” Murmushi kawai junaid yyi, Kaka
tace “Ba abun murmushi bane, har da rashin auren ke damun ka kai da Shureen, Kai kuma naga ai wayayye ne a kan
Shureen da yake nan dunkum, Kai baxa ka rasa yan matan ba ynxu hka, shi kuwa Shureen da kyar idan ba hadin
gida xa ayi masa ba, idan ba haka ba kuwa sai yyi shekara hamsin bbu aure, duk da dai shi da maganarsa da wata
yarinya a kasa don har naje na nemi alfarman a bamu ita gidan iyayen yarinyar kuma sun amince, sa rana kawai ya
rage idan yarinyar ta gama karatun sakandari, ta ma kusa gamawa” daga Farida har Heedayah kallon kaka suke,
Junaid ya kalleta ta madubi kawai yyi murmushi bai dai ce komai ba, Heedayah tace “Da gaske kaka?” Kaka tace
“Wllh, ai maganan ya fi shekara uku ynxu…” Heedayah tace “Kuma ya san maganan?” Kaka tace “Haba wane
mutum, ai baxa a bar sa ya san da maganan ba, ni dai ai ban biye ta rashin kunyar da yake min ba nayi masa gata a
matsayin warce ta haifi ubansa, Amadun ma yasan da wnn xancen kuma” Heedayah ta kyalkyale da wani dariya tace
“Allah ya sa kwanan nan xa ayi” kaka tace “Aa baxai dau lkci ba dama” Farida tace “Toh auren dole xa ayi masa
kenan” Kaka tace “Kaji gantalalliya, auren dole ai tun xamaninmu aka daina, ai baxai ki yarinyar ba tunda tana da
kyau kamar uwarta, Allah na tuba me xai nuna mata banda matsayinsa na soja, ai son kowa ce k’in wanda ya rasa”
Heedayah ta kara kyalkyalewa da dariya, Kaka tace “Ke ma auren xa a maki kwanan nan ai” Ta dakatar da dariyar
da sauri, Junaid dai sai kallonsu yake, ta turo baki tace “Yar yarinya da ni” Kaka tace “Wace yarinya, bayan naji
labari a wajen Rakiya kin fara al’ada” Farida ta kauda kai tana dariya kasa kasa, Heedayah tayi shiru bata kuma cewa
komai ba, kaka ma tayi shiru jin kowa yyi shiru. Suna isa gidan Abba Junaid yyi parking a waje, kaka tace “Toh
Alhamdulillahi Allah ya maka albarka Junaidu, Allah ya nuna min bikin ka” Daga haka ta sauka motar Heedayah ma
ta sauka Farida ma ta sauka, Farida ta daga masa hannu tace “Allah ya kiyaye” Heedayah ta kallesa tace “Sai
anjima” ya gyada mata kai ta bi bayan kaka da har ta shiga compound din. Hamdala kaka tayi ganin motar Abba da
na Shuraim, ta wuce ciki tana cewa “Allah ya so ni, idan Amadu ya fita ai xuwan banxa nayi kenan” Abba ya fito
parlonsa cikin shigar fita office tare da Shuraim dake rike da brief case dinsa kenan kaka ta shigo parlon Heedayah
na biye da ita, Kaka ta washe baki tace “Sannu Amadu Ina ta sauri kar ka fita, Allah ya so ni….” Kallon Heedayah
kawai Abba yake, hakan ya sa ta karasa inda yake tsaye ta rungume sa cikin sanyin murya tace “Abba…” Kaka tace
“Atoh, ai Rakiya ta shiga uku ta lalace, ta tarwatsa xumunci” Abba ya d’an yi murmushi ya maida Heedayah gefensa
yana kallonta yace “How are you” tace “I’m fine good morning” Yace “Ya karatu” tace “Alhamdulillah” Farida ta
karasa ita ma ta gaida Abba da ladabi, ya amsa da murmushi yace “How are you Farida” tace “I’m fine sir” Abba
yace “That’s good” Kaka ta tafi parlor ta xauna tana cire hijab din jikinta tana kara gode ma Allah ta samu Abba,
Abba ya karasa ya xauna ya gaisheta tace “Lafiya lau Amadu ya taro? Fatan duk kun watsa su lafiya” Yace Alhmdllh” kaka tace “Toh Allah ya maku albarka ya mayar maku da dubun abinda ku ka kashe, saura na wnn yaron
naka Shureen kuma” Shuraim dake ta tsaye ya kalleta ta gefen ido, Abba dai yyi murmushi ya mike yace “Na
makara Baaba, kuna nan har in dawo ai” Kaka tace “To ina xa ni? Ai ina nan in sha Allahu har ka dawo, yi tafiyar ka
Allah ya tsare” Yace “Ameen” hannun Shureen ya amshi briefcase dinsa yace “You didn’t greet her” Shureen ya
karasa parlon yana kallonta yace “Ina kwana” kaka tace “Lafiya lau, jiya ka kai ma Rakiya su dubulan da alkaki da
cincin din kuwa, naje gidan na manta ban tambayeta ba wllh” Wani kallo ya mata bai ce komai ba, Abba na kallon
Heedayah yace “Sai na
dawo” Tace “Allah ya tsare Abba” ya amsa da “Ameen” Farida tayi masa Allah ya tsare ita
na snn ya fita parlon, Farida da Heedayah suka dawo parlon suka xauna, kaka tace “To ita Maryam din bin ta xa mu
yi parlonta kenan, toh ai bbu komai ku tashi mu je, mu ba bakin xafi bane, baxan biyeta ba, amma kuma ban ji kun
gaida Shureen ba” Farida ta mike ganin kaka ta mike, tace “Ina kwana” Heedayah ma ta tashi tace masa “Ina kwana”
Duk bai amsa masu ba, Suka bi bayan kaka xuwa parlon Mumy, Mumy ta fito bedroom dinta kenan ganin kaka ta
d’an canxa fuska tace “Kaka ce…” Kaka tace “Wllh ni ce, ina ta sallama shiru, ashe kina can ciki” Mumy juya xata
rufe kofar dakinta tana yatsine yatsine tace “Ehh ina ciki” Heedayah ce karshen shigowa parlon, Farida ta xauna
kusa da kaka, Heedayah ta xauna gefenta duk suka gaida Mumy, lkci daya fara’a ya bayyana fuskar Mumy ganinsu
tace “Aa ashe baki muka yi hka, to sannun ku da xuwa” Kaka tace “Ehh cewa suka yi sai sun xo sun gaishe ki, su
Rabi’ah kuma can na barosu gidan Umaru basu ma san xan yo nan ba” Mumy na washe baki tace “Allah sarki,
Sannun ku da xuwa, bari a kawo maku breakfast” Kaka tace “Aa ni kwai kawai xa a soya min, idan akwai d’an
farfesu a hada min da shi, kwanan nan ba wani cin abinci nake ba” Daga Farida har Heedayah suka kalleta, Mumy
tace “Toh su kuma ‘yan matan fa” Kaka tace “Su ma soya masu kwan kawai a hado masu da d’an dankali” Farida
tace “Aa mu mun koshi” Kaka tace “Da yake sun karya su” Mumy bata ce komai ba har ta fita parlon sai kuma ta
dawo ta shiga bedroom dinta tace “Bari in maida wayata caji” rufe kofar dakin tayi ta nemo wani karamin purse
dinta da ta adana sosai ta bude ciki ta dau wani kullin xani, ta fi minti daya tana kallon kullin da xai yi shekara uku a
ajiye cikin jakar, “Ko nan da shekara goma ne bbu abinda xai hanasa aiki” murya wanda ya bata ne ke dawo mata,
tayi wani murmushi ta kunce habar xaninta ta kulle kullin maganin a jiki snn ta daura xanin ta fito parlor tace
“Sannu kaka, bari in je inyi masa in soya maki” kaka tace “To yi maxa” daga hka ta fita parlon, tsaye ta ga Shuraim
har sannan a Main parlor, Tace “Aliyu tun da sai yamma xaka fita bari in baka sako ka kai ma Hajiya Sadiya
yanxu…” Ya kalleta yace “Akwai aikin da nake yi ban gama ba, ki bada sakon idan na fita anjima sai in kai mata” Ta
wani hade rai tace “Toh ni yanxu nake son ka kai mata ba sai anjima ba” Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen ya bi
ta da kallo, sauke ajiyar xuciya yyi ya xauna saman kujera, Mumy na tsaye kitchen ta sa mai aiki ta soya lafiyayyen
kwai da ya ji albasa da tsire a ciki na kaka, sauran tsiren kuma ta saka a plate daban daban guda biyu, tana kallon
Mai aikin tace “Duba min Shuraim na parlor ne” Mai aikin ta fita ta dawo tace “Aa baya nan” Mumy ta dau plate din
kwan kaka ta mika mata tace “Ki kai ma kaka, idan tace wa ya soya kice ni ce…. Sai ki tafi ki ce ma driver yyi
wucewarsa nayi baki sannan ki dawo ki kai ma yan matan nan tsire” Mai aikin tace “Toh Hajiya” daga haka ta nufi
kofa ta fita, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofar, kallon window din kitchen din tayi snn ta kai hannu gefen
xaninta, cikin few minutes ta gama abinda xata yi ta barbada ma naman yaji snn ta dau plate din biyu ta fita xuwa
parlonta, ta ajiye daya gaban Farida, na hannun hagunta ta ajiye ma Heedayah tace “Naji kaka tace kun karya wnn
kuma ai abun marmari ne, da asuba nayi ma Barrister ashe baxai ci ba, wnn nawa ne da na Shuraim, shi ma nasan ba
lallai ya ci ba” Kaka tace “Atoh, rabonsu ne, ku yi maxa ku ci”